kau da kai a daren farkonsa ya kyale matarsa ba."
Kuka ta saka tana dora hannu aka .
"Wayyo na shiga uku na lalace, kai ba zai yiwu ba na san ba zai taba son ta ba, ba na fata wata alaƙa ta autatayya ta shiga tsakaninsa da Nadra domin ba abinda zai yi da ita ni yake so ba ita ba."
A gaban tangamemen gate ɗin gidansa ya yi parking ya tsaya yana danna horn. Security ya leƙo ganin maigidan ne ya saka ya koma da sauri ya wangale ma sa gate ɗin gidan ya shiga da matarsa.
Parking lot ya nufa ya yi parking, sai da ya kwashe mintuna ashirin ba a cikin motar bai fito ba.
Ganin shiru ya saka security biyu da ke harabar gidan ɗaya ya karasa wajen motar yana knocking glass ɗin.
A hankali Fahad ya dago da kansa da ya kwantar a sitiyarin motar sannan ya zuge glass ɗin motar.
"What happened?"
"Am sorry sir, are you okay?"
"Am okay."
Ya faɗa yana kokarin fitowa daga cikin motar yayin da security ya bar wajen. Don sun ga ya ɗauki lokaci bai fito ba ne ya saka suka fara tunanin ko wata matsala ce ko bai da lafiya ne.
"Wayoyinsa a hannunsa ya nufi main door ya tura ya yi sallama ciki-ciki wanda ko kawai wani a falon ba jin sallamar zai yi ba.
Ƙamshin turaren wuta da room freshener spray suka yi ma sa sallama.
Ba tare da ya kalli ko ina ba ya nufi upstairs ɗin.
A hankali ya tura ƙofar falonsa ya shiga, wayoyinsa ya ajiye saman Centre table sannan ya zauna a daya daga cikin lafiyayyun kujerar da suka yi Falon ƙawanya.
Jinginar da bayansa ya yi da jikin kujerar. Wayarsa ce ta soma ruri ya duba ya ga Mama ce ke kiransa. Sai da ya sauke ajiyar sanan ya daga kiran wayar.
"Mama."
Ya fada cikin shagwaɓa murmushi ta yi Murmushi irin tasu ta manya ta ce.
"Ka isa gidan lafiya?"
"Uhm."
Ya faɗa kamar ba ya so yin magana.
"Shagwabar ce ta motsa ko?"
Bai ce komai ba idanunsa a lumshe yana rike da wayar.
"Ina Nadra take."
"Ban sani ba amma ina tunanin tana ɗakinta."
"Kai kana ina?"
"Ina ɗakina."
"Me za ka yi yanzu."
"Zan yi wanka ne na kwanta."
"Fahad."
"Na'am Mama."
"Yanzu ko dabba ce aka kai ma ka gida aka ajiye ta ai ka duba lafiyar ta ko?"
"Tana lafiya Mama."
"Ka je ka haɗa ni da ita a waya. Nan da mintuna biyar zan kira ka."
Tana fadar haka ta katse kiran wayar.
Fuska babu walwala ya mike ya nufi ƙofar fita, dama kofar falonsa da kofar falonta suna kallon juna ne.
Hannunsa ya daura saman handle ɗin kofar ya buɗe ya shiga da sallama ciki-ciki.
Ba kowa a falon sai kanshi da sanyin A.C dake tashi .
Bedroom ɗin ta ya nufa ya shiga da sallama.
Tana kwance a saman gado ta kudundune mijinta wuri ɗaya sai ajiyar zuciya take sauke wa. Da alama ta ci kuka har ta gaji.
Ƙamshin turarensa ne ta ji ya saka ta ɗago kanta ta zuba ma sa kumburarrun idanunta da suka yi ma ta nauyi saboda tsabar kuka.
Shi ma idanunsa ya a zuba ma ta ba tare da ya yi magana ba. A hankali ta mayar da idanunta ga kanta dake bala'in sara ma ta da ciwo.
Wayarsa ce ta yi ruri yana ganin Mama ce ya karasa bakin gadon ya miƙa ma ta wayar bayan ya yi picking call ɗin ya saka a handsfree.
"Assalamu alaikum."
Cikin disashshiyar muryarta da ta disashe da kuka ta amsa da.
"Wa'alaiki Salam warahmatullah. Ina wuni ."
Duk da ba ta san waye ke magana ba amma zuciyarta ta ba ta cewa
"
Mahaifiyarsa ce .
"Wa'alaiki Salam warahmatullah Nadra ya kike?"
"Alhamdulillah."
"Daga jin muryarki kin sha kuka sosai, ki yi hakuri kin ji komai muƙaddari ne daga Allah, Fahad shi ne mijin ki ki yi hakuri ki zauna da shi a matsayin mijin ki, idan ya yi ma ki wani abun da ba daidai ba ki kira ni ki faɗa ma ni, ni ce mahaifiyar sa zan dauki mataki akansa kin ji Daughter."
Cikin Muryar kuka ta ce.
"To Mama."
"Yauwa Allah ya yi ma ki albarka kin ji."
"Amin Mama."
Ta fada tana goge hawayen da ke ma ta sintiri a idanunta.
"Zan ce ya tura ma ni lambarki sai ya tura ma za mu yi magana da safe."
"To Mama."
"Kin ci abinci kuwa?"
"Ba na jin yunwa."
Tun karfe nawa kika ci a abinci?"
"Tun da rana."
"To yanzu ki samu ki ci abinci zai kawo ma ki. Sai da safe ko?"
Daga nan ta mikawa wa Fahad wayar ya karɓa yana karawa kunnensa.
Kafin ya yi magana ya ji ta ce.
"Ka siya ma ta kaza ne?"
"Wace kaza kuma Mama?"
"Ka fita ka je ka nemo kaza ka kawo ma ta ba ta ci abinci ba."
Tana fadar haka ta kashe wayarta.
Jiki ba karfi ya fice daga dakin ya koma nasa ɗakin ba tare da ya sake kallon in da take ba.
Key ɗin iya ɗauka ya fida daga cikin gidan ransa babu dad'i.
In da ake gashin kaji ya tsaya. Ba tare da ya fito daga cikin motar ba ya yi horn wanda ya janyo hankalin daya daga cikin ma su aiki a wajen.
Ya ƙaraso wajen daidai lokacin da wayar Fahad ta sake ringing.
Ya yi picking still bai yi magana ba don ya san lambar ɗazu ce.
"Ka kawo mun kaza guda daya da fresh milk guda biyu."
Maganar sa ya sauka a cikin kunnen Sidra dake rike da wayar tana jiran ya yi picking.
Katse wayar ta yi tana fashewa da kuka.
"Wai fa kaza ya zo siye da fresh milk, ita zai kai wa su ci kenan? Kazar da kowane ango ke siya wa matarsa a daren farkonsu shi ne ya siya ma ta. Kazar ba shi da idan ta ci sai ta biya kenan fa."
Lokaci daya ta rikice da kuka wanda hakan ya saka Sady baby rarrashinta.
"Ba zai yiwu ba dole na bar garin nan gobe na koma Kaduna, duk abinda zai faru ya faru amma sai Fahad Majidaɗi ya dawo mallakina."
_Makaho_
Bayan ya idar da sallar isha'i daga masallaci gida ya nufa. Don karfe tara ne yanzu, sai sa ya tsaya ya yi karatun Alkur'ani mai girma. Da sallama ya tura kofar fale-falen gidan ya shiga
Daidai lokacin tana fitowa daga wanka daga ita sai towel da ta ɗaura rabin cinyarsa a waje suke.
Sai ƙamshin shower gel din ta take yi. Amsa ma sa sallama ya ji ta yi tana ma sa Barka da shigowa.
Ya amsa yana lalube har ya ji ya kawo bakin kofar sannan ya shiga da sallama.
Lokacin akwai wutar nepa,
Tsane ruwan jikinta ta ke yi ganin shi makaho ne ba gani yake yi ba ya sa ta warware towel ɗin ta shafa man shafawar ta ta shafa.
Zama ya yi kan tabarmar da ya kan zauna , har ta gama shafar ta ta saka turaren ta ma su kamshi sannan ta saka kayan barci ta .
"Ka yi hakuri ina shirya wa ne."
"Ba komai Ma'eesha."
"Na ga abincin nan ya rage ne ya sa ban yi sabon girki ba kada ya zama ɓarna."
"Kada ki damu Ma'eesha ba wani yunwa nake ji b."
"Kar ka ce haka tun breakfast ba ka ci komai ba, ta ya mutum zai yi ta zama da yinwa ana rayuwa da yunwa?"
Murmushi ya yi tare da cewa.
"Ba iya abinci muke buƙata don mu rayu ba, muna buƙatar mu riƙa ji a ranmu cewa akwai wanda yake sonmu, yake fahimtarmu, yake taya mu alhini a lokacin damuwa, yake fahimtar maganar da ke ranmu a lokacin da muka yi shiru, yake fahimtar damuwarmu a lokacin da muka rufe ta da murmushi. Mutum zai iya jure talauci, ya yi haƙuri da yunwa, amma ya kasa jure rashin masoyi mai kulawa. Kalma ɗaya mai daɗi da masoyinka zai gaya maka za ta iya haska tsakiyar zuciyarka da sanya maka farin ciki da natsuwa a lokacin da kake fuskantar ƙalubalen rayuwa."
Ƙwalla ta goge yayin da take ƙokarin ajiye ma sa abincin a gabansa. Sannan ta kawo ruwa da Maltina ta ajiye ma sa.
Ya fara cin abincin kenan suka ji sallama daga tsakar.
Amsa wa ta yi sannan ta janyo hijabi ta saka daidai lokacin da ake ƙara bude murya an rangaɗa wata uwar sallamar.
_Nadra_
Yana fita daga dakin ta saka sabon kuka Har ya dawo ba ta daina ba . Cikin kuka take cewa.
"Sidra ina kika tafi kika bar ni a muhallin da bai dace da ni ba. Ke kika dace kina nan don Allah ki dawo zan tafi na bar ma ki komai naki ne, wannan gidan gidan tamkar gidan aro ne a gare ni, ki dawo na bar ma ki gidanki mijin ki komai na ki ce ni ba mazauniya ba ce."
Ƙamshin turarensa da ta ji ya haifar ma ta da faɗuwar gaba.
Dara-daran idanunta da suka kumbura ta kalle shi da su
Wani kallo yake yi ma ta wanda ya sa ta faduwar gaba.
*Ku yi hakuri da wannan*🙏🏻
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page1️⃣4️⃣
Wani kallo yake yi ma ta wanda ya sa ta faɗuwar gaba.
Da sauri ta ɗauke idanunta daga kallonsa ta mayar kan yatsun hannunta tana wasa da su.
A hankali ya ƙaraso gaban gadon hannunsa rike da faranti da ya ɗora rabin kaza akai, sai dayan hannun nasa wanda ya rike robar fresh milk da glass cup.
"Ki zauna da kyau."
Tsintar kanta ta yi da bin Umarninsa. Bayan ta tashi daga kwancen da take ta yi kanta a ƙasa har lokacin ba ta daina hawaye ba.
Sai lulluɓe jikinta da mayafinta take yi.
"Ga shi nan ki cinye shi, ko na kawo ma ki tea ne?"
Ma ta girgiza ma sa alamar alamar a'a.
_Sidra_
Bayan ya ci kuka ta ƙoshi ne sai ta kalli Sady baby tana cewa.
"Yanzu dama namiji baya da kunya?"
"Tofah, me aka yi ne?"
"Wallahi In fada ma ki siyen kaza ya tafi kazar amarci wanda a sani na idan ta ci kazar nan fa kin san me zai biyo baya."
"To sai aka ce ma ko sai zai yi abu da ita ne zai siya ma ta kaza?"
"Yau ne fa daren farkonsu hakan yana nufin yana da lokacin ta kenan, ban taɓa tunanin hakan daga wurin Fahad Majidaɗi ba. A baya fa shi da kansa idan kika fahimce shi za ki ga kamar ya tashi Nadra ce. Musamman da yake ganinta kullum cikin dogon hijab da yadda take sunkuyar da kai sai yake ce ma me ya sa ƙanwata take yin abu kamar munafuka ce shi baya son haka. Sai na ce ma sa wai kunya ce nan. A lokacin ya ce baya son mace mai kunya haka ba zai iya auren duk mace mai wannan yanayin ba, amma da ke namiji munafiki ne har da zuwa siyen kazar amarci."
Hawaye ma su zafi ta goge tana cewa
"Ba zan zauna a garin nan ba, dole na tafi na koma Kaduna gobe, na tari yaƙin dake gabana."
"Ba za ki hakura da Fahad ɗin nan ba kuwa Sid?"
"Ba zan zan iya ba Sady baby ba zan iya ba ƙarya da ciwo. Ba abinda ya ragu cikin son da nake ma sa.
Gajeren murmushi Sady baby ta yi kafin ta ce.
"Sai dai addu'ar da za ki yi kada wani abu na autatayya ya shiga tsakaninsa da Nadra. Domin idan wani abu ya shiga har ya yi sex da ita a wannan daren komai zai lalace ma ki, domin hakan na nufin sun zama abu ɗaya ne shi da ita. Musamman idan ya kasance ita virgin ce, to saboda samun ta da cikakken budurcin ta ko ya ya ne sai ya ga darajarga da ƙimar ta a idanunsa. Kuma ba zai taba mance wannan halaccin nata ba, ke ɗaiɗaikun maza ne fa suke sakaci da irin wannan mace domin shi ne saka ta yi daraja a idanunsa. Amma idan ya ga cewa ya aure ki ya fahimci ke ba virgin ba ce wallahi duk son da yake yi ma ki sai ya ragu mutuncin ki zai zube a idanunsa Sosa da sosai."
Ta yi maganar tana kallon Sidra wacce ta yi mutuwar tsaye kamar ba ta jin ta .
"Shi kenan komai zai lalace na tabbata Nadra virgin ce, saboda ita mai tsoron Allah ce, mai horo da bin Umarninsa da hani ga saɓonsa, ba za ta taba bari a raba ta da mutuncin ta ƴa mace ba. Infac ma ba in da take zuwa daga guda sai makaranta, ko kawaye bata da aji sai wata yarinya daya A'isha Humaira. Ke ko za mu fita da ita sai da dalili ba iri na ba ce mai yawan tsiya ko satar hanya ina ji na fita, kuma idan na yi satar hanya na fita duk da tana ba ni shawara na daina amma duk da haka tama rufa ma ni asiri wajan iyayen mu ta ce ina ɗaki ina barci."
Goge hawaye ta yi ta ce.
"Bari na sake kiransa ."
"Kada ki kira shi ki ji abun da zai tayar ma ki da hankali."
Ba ta saurare ta ba ta kira lambar Fahad Majidaɗi.
_Fahad_
Shigowarsa ɗakin kenan ya miƙa wa Nadra ruwan shayin da ya haɗo ma ta duk da ta ce ba ta so.
Miƙa ma ta shayin ya yi daidai lokacin da wayarsa ta so ma ruri, sai ya duba still numbern da aka kira shi da ita ne.
Ya ɗaga daidai lokacin da da Nadra ya kai kofin da ke hannunta bakinta ta kurɓi tea, jin zafi ya sa ta saki wata ƴar ƙara wanda ya sa Fahad ɗan rikicewa ya ce.
"Am sorry na yi ma ki shi da zafi ko?"
Nan ma aka yi katarj da Sidra ta ji su kuma sai zuciya ta ake kitsa ma ta wani abun daban. Don haka sai ta katse kiran wayar zuciyar ta na tafarfasa sosai da sosai. Kuka da nadamar barin gida ya zo ma ta lokaci guda, ta kalli Sady baby ta ce.
"Ba na faɗa ma ki tun da ya je siyen kazar kazar nan na san me hakan ke nufi . Yanzu fa ihunta na ji ta yi tana ƙara shi ma daga jin muryarsa a rikice yake har yana ce ma ta sorry ya yi ma ta shi da zafi ko?"
Ta ɗora hannu akai tana kuka mai tsuma zuciya. Allah wadaran halin maza wallahi, Nadra karamar yarinya ce fa dududu shekarunta 18 amma shi ne har ba zai iya kawar da kai akanta ba. Ai ba sa'ar aurensa ba ce. Don ko da aka haife ni sai da Ummanmu ta sake haifar yara guda biyu suna mutawa kafin aka haife ta ita ce ta rayu ai ko kusa da ni ba ta kai ba. Don na ba ta shekaru bakwai a duniya. Don idan ba ki manta ba yanzu ina 22 years ne ita kuma yanzu take 18 ai ba kusa ni da ita. Kuma wallahi ba ta isa ta raba ni da Fahad ba shi ma munafiki ya ba ni mamaki."
Nan da dinga sambatu ita kadai a ba wanda ya tanka ma ta. Kafin ta kalli Sady baby ta ce.
"Za ki iya saka diraba ya mayar da ni Kaduna gobe da safe?"
"Eh amma ki bari zai kai ni wani waje da safe zuwa karfe goma za mu dawo na san kin shirya zuwa lokacin ko?"
"Har karfe goma?"
"To ya za'a yi fitan nawa ya zama dole ne, kuma idan ya tafi kai ki da motar ba yadda zan yi."
Jinjina kai ta uku tana cewa.
"Shi ke nan zan jira karfe gomar."
"Yauwa ƙawar arziki, kaya ce da na yi order matar ta kira zan je na karɓa shi ya sa, amma muna dawowa zai kai ki har gida."
Godiya ta yi ma ta sannan ta Sady baby ta fice ta bar ma ta dakin bayan ta karbi wayarta.
_Ma'eesha_
Tana saka hijabi akan kayan barcin na ta ta fitq waje don duba mai sallama. Don Muryar mace ce ta ji ba ta namiji ba.
Ba kowa ba ce fa ce Larai Dillaliya wacce makaho ya fara kai Ma'eesha gidan ta kasa zama ciki ta ce za ta kama haya.
Ita dai Ma'eesaha ba ta gane ya ba , amma Larai sai washe baki take yi tana jin daɗi.
"Sannu da zuwa."
"Yauwa sannu amaryar Khalifa ya kuke ya Khalifa?"
Jin haka ya saka Ma'eesha ta yi tunanin cewa. Ko Larai dangin Khalifa ne. Don haka da fara'a ta ce.
"Bismillah shigo ciki ma na."
Ta yi gaba Larai na bin bayanta suka shiga ɗakin.
Da sallama suka shiga Larai Dillaliya ta kalli gaban Khalifa makaho ta Maltina da bottle water.
"Ma sha Allah."
Sannan ta kare wa ɗakin kallo ta ga komai sabo ne ba tsoho ba, sai ta fara tunanin dama akwai canji a hannun yarinyar kenan. Sai dai ba ta ji dadin haka ba, don ta fahimci yrinyar ta fiye kayan bukata. Ta dauka ba su da komai ne sai ta ce ma ta tana siyen kayan saka wa da takalmomi da handbag ta siye a wulaƙance don ta fahimci komai na yarinyar mai tsada ne kuma kamar tana cikin matsala ko nawa aka ba ta za ta karba.
Muryar Khalifa ta ji yana cewa.
"Ina wuni?"
Sai a lokacin ta daina kalle-kallen da take yi ta ce.
"Lafiya lau Khalifa ya amarya?"
"Alhamdulillah."
Daga nan ba wanda ya sake magana. Ma'eesha ce ya mike ta kawo ma ta ruwa ta ajiye ma ta. Ta dauki plate za ta zuba ma ta abinci kenan sai ta ji Muryar Makaho na ce wa.
"Baiwar Allah lafiya a daren nan ko?"
Don sarai da ya ji muryar ta ya gane ta.
"Am dama na ce bari n zo ne don na ga kamar za ku bukaci kuɗi sai na siyen abun da amarya ke da su, kamar ko akwati haka da kayan saka wa da takalmomi da handbags da sarƙa da ƴan kunne da sarƙa duk...,"
Tsawar da Ma'eesha ta daka ma ta ne ya ba ta mamaki ta mike da sauri .
"Tashi ki fita!"
"Ban gane ba daga taimako?*
"Kin ga jin zo wajen ki neman taimako ne?"
"Ba ku zo b amma na san sai kun zo wata rana, sai kun zo wata rana kuna nema ma da kanku. Don wannan makahon mijin naki Makaho ba ya iya ɗaukar ɗawainiyar ki zai yi ba. Don Allah na tuba ai ba na tunanin cewa a yini ɗaya yana haɗa Naira ɗari biyar. Tun da kuma ha ba kowa zai ba wa maka..."
"Mallama tashi ki fita kafin na ba ki mamaki a gidan nan, dama abun da ya kawo ki kena"
Jiki ne rawa Larai ta mike ta bar gidan.
Ranta ya ɓaci kasa magana, illa iya kai ta kawar da komai ta yi shirin.
Bayan ta yi shirin kwanciya barci duk da tana jin zafi haka dai ta rufe ƙofar ɗakin.
Ba zai yiwu ma ta a ce wa makaho ya zo su kwanta tare ba, Hakazalika ba ta jin ta yi ma sa adalci idan ta bar shi ya kwanta ƙasa kan tabarma. Don haka sai ta rasa yadda za ta yi don ita ma ba za ta iya kwanciyar a ƙasa ba. Amma sai ta yanke shawarar bari shi makahon ya bi zaɓin abun da ke ransa. Idan ya hau katifar ya kwanta kusa da ita ba za ta hana shi ba, don haka ta kalle shi yana zaune kamar wanda yake tunanin wani abu ta ce .
"Ni zan yi barci sai da safe."
"Jinjina kai ya yi yana cewa.
"Allah ya tashe mu lafiya."
Da Amin ta amsa ma sa sannan ta yi addu'ar kwanciya barci ta kwanta abun ta.
Kashe hasken wayarta ta yi don dama shi ta kunna. Duhu ya gauraye ɗakin .
Sai dai ta kasa barci kwata-kwata sakamakon zafin da ta ji ya addabe ta .
Don ta saba kwanciya cikin sanyin A.C nan kuma zafi da sauro ne suke addabar ta suna kuka.
Sosai ta rikice tana ta mutsu mutsu.
Jin motsinta ya yi yawa baya. Kamar awa ɗaya da kwanciyar ta ya saka ya kira sunanta.
"Ma'eesha lafiya, ko zafin ne ke damunki"
Kamar za ta yi kuka ta ce.
"Na kasa barci wallahi."
"Kamar jira yake yi ya taso da lalube ya ƙaraso wajan katifar yana cewa.
"Ki yi hakuri na yi ma ki fifita kin ji?"
Yana nan zaune gefen katifar ya ce ta bashi abun fifita.
Tashi ta yi ta je ta nemo ma sa ta kawo ma sa bayan ta kunna fitilar wayar.
Tama ba shi ta kashe ta kwanta.
Daga nan ya dinga yi ma ta fifita ba daɗe wa barci ya yi awon gaba da ita.
Shi kuma yana nan zaune har ya soma gyangyaɗi, sakamakon rashin barci jiya da bai yi ba ya kwana juya yana ma ta fifita ga yau bai yi ba har dare ya raba yana ma ta fifita. Idan ya daina take cikin barci za ta ji zafi na shig busowo za ta fara motsawa shi kuma da ya ji motsi zai cigaba.
Farkawa ta yi ta ga shi zaune yana yi ma ta aikin fifita.
Ta tuna haka jiya ya kwana zaune yana ma ya fifita. Sai ta ce.
"Am ka bari ya isa haka nan na gode."
"Ba za ki iya ba."
"Sanyi nake ji ka bar shi kawai."
Sanyi a yanzu ko ba ku da lafiya ne?"
"Lafiya lau nake amma na gaji da fifitar ne ya na sa na ji sanyi."
Daga haka ya daina ita kuma ta kudundune cikin sani har kabta da ƙafarta na ciki. Ta rasa yadda za ta yi tausayinsa ya sa ce ma sa haka amma ba wai don tana jin sanyin ba. Tana addu'ar a ranta Allah zai kawo ma ta mafita.
*Wace ce Ma'eesha?*
Ma'eesha Ibrahim Khalil, shi ne cikakken sunanta. Ibrahim Khalil shi ne cikakken sunan mahaifinta. Mahaifiyarta kuma sunanta Saliha.
Ibrahim ya haɗu da Saliha ne a gidauniyar tallafawa marayu wanda mahaifinsa Shamsuddin ke daukar kusan rabin ɗawainiyar marayun. Duk lokacin da Alhaji Shamsu kan shigo gidan marayun tare da Ɗansa Ibrahim Khalil yake zuwa. Ya kan taya mahaifinsa raba wa marayun kaya da sauran abun bukatunsu.
Wanda anan ne Ibrahim Khalil ya ga Saliha ya ji yana son ta. Lokacin da ya sanar wa mahaifinsa zancen auren Saliha mahaifinsa ya nuna jin fadinsa domin shi mutum ne mai son marayu da tausaya ma su. Sai dai Ibrahim Khalil ya fuskanci ƙalubale daga wajan mahaifiyarsa kan rashin amincewar ta da auren Saliha. Saboda an yi bincike ba'a san daga ina ta fito ba wai ba ta sani ba ma ko ba ƴar Sunnah ba ce. Wata kila cikin shege aka haife ta ta aka jefar da ita.
Sai da Mahaifin Khalil ya tsaya tsayin daka sannan aka yi auren Ibrahim Khalil da Saliha. Ta tare a gidansa dake nan cikin garin Kano.
Zama suke yi cikin soyayya da ƙaunar juna. Yana son ta saboda nagartar ta, don tana da hakura juriya da hangen nesa. Alhaji Shamsuddin yana son sirikar tasa ganin yadda Ɗansa ke son ta, sai sai tsakanin ta da uwar mijinta ce kadaran kadahan. Ba ta nuna ma ta soyayya kuma ba ta nuna mata tsana.
Bayan shekaru ɗaya Allah ya albarka ce su da haihuwar ƴa mace. Ranar ya kasance ranar farin ciki ne a gare su.
Farin ciki a wajen Ibrahim Khalil da Saliha ba'a magana. Haka ma Alhaji Shamsuddin, ya yi farin ciki sosai, ɓangaren Hajiya A'isha ma ta yi farin ciki sosai duk da ba ƙaunar Ma'eesha take yi ba amma tana ƙaunar Ma'eesha.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Ma'eesha na girma har ta isa shiga makaranta aka sanya ta makarantar kuɗi. Sai sai duk weekend akan kai ta gidan kakannin ta ta yi hutu. Don Hajiya takwarar Ma'eesha ce ta tsara haka duk weekend sai an kai ma ta takwarar ta can gidanta ta yi ma ta kwana biyu. Idan kuma ana cikin hutu can take ma ta weekends.
Haka rayuwa ta cigaban da tafiya har Allah ya raya Ma'eesha ta kammala primary school. Kuma har lokacin iyayen ta ba su saka samin wata haihuwar ba.
Sai dai arzikin Ibrahim Khalil ya kara bunƙasa, don kasuwancinsa saidai yake samun cigaba.
Har wata rana Saliha ta samu Ibrahim Khalil da zancen za ta fara kasuwanci ita ma. Sai ya nuna ma ta ai mahaifinsa ma ya yi maganar ta fara kasuwanci har ya ce ta ke ta fadi sana'ar da take so zai ba ta jarin da za ta fara.
Ta yi farin ciki sosai washegarin ranar dama ya kama weekend ne za su
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 49