Share this page
ta haife ki za ki iya ƙawance da ita ballantana wacce ta girme ki. Kasancewar ina matsayin yar mijinki ba yana nufin ki dinga jin kunya ta kina ɗauka ta sirikar ki ba. Ki ɗauke ni kamar ƴar uwarki ta jini. Na san cewa kina cikin damuwa idanunki ma ya nuna hakan. Idan bakin ki ya ɓoye damuwar da kike ciki to idanunki da da fuskarki ba za su yi karya ba. Na san dole akwai damuwa ki faɗa ma ni zan ba ki shawara. Kuma na yi ma ki alƙawari ba wanda zai ji abun da muka tattauna. Ko mahaifiyar da ta haife ni ba za ta ji komai ba, zan rike ma ki sirrinki domin ina ƙaunarki fisabilillah. Shiru Nadra ta yi domin kuwa tana buƙatar wanda za ta fada wa damuwar ta ko ta yi shawara da ita. A duniya dama mutane biyu ne abokan shawarar ta . Ummanta ce sai kakarta Ammi. To ga Umma kwance ba lafiya, ta ya za ta iya faɗa ma ta abun da zai tayar ma ta da hankali, sai kuma kakarta Ammi ,to ita kuma idan ta sanar da ita ta san za ta sanar wa Abba ne sai sun saka Sidra ta bar gidan nan. Amma ta ji hankalinta ya kwanta da Aunty Rahama. Shin ta faɗa ma ta damuwarta ko ta yi shiru? _Sidra_ Gudu take yi a saman titi kamar wacce za ta tashi sama. Tana driving tana jin ƙuna a ranta. A cikin ƙanƙanin lokaci ta isa gidan Sady baby. A waje ta yi parking motar ta sannan ta tura ƙaramar kofar ta shiga. Madaidaicin gida ne sai motoci guda biyu a harabar gidan. Knocking ɗin kofar falon ta shiga yi. Ta kai mintuna biyu har ranta ya ɓaci sai ga Sady baby ta buɗe ƙofar wani saurayi ya fito, kallo daya Sidra ta yi ma sa ta ɗauke kai. Murmushi Sady baby ta yi ma ta tana cewa. "Babban yarinya kin iso ?" Ba ta tanka ma ta ba ta shiga cikin falon. Taɓe baki Sady baby ta yi tabi bayan Sidra. Suna zama kan kujera Sidra ta watsa ma ta harara tana cewa . "Kin ga abun da kika janyo ma ni ko? Ga shi a dalilin bin ki na ina neman rasa Masoyi na wanda nake mafarkin mallakarsa a matsayin mijin aure na. To abinda ba zan yarda da shi ba kenan. Dole na same shi ta kowace hanya." "Yanzu ya kike so a yi?" "Na mallaki Fahad Majidaɗi." Shiru Sady Baby ta yi kafin ta ce. "Ƙanwarki da yake aure fa?" "Ya rabu da ita ya aure ni?" "Kina ganin iyayen ki da iyayen sa za su yarda da hakan kuwa?" "Ban damu da amincewar su ko akasin haka ba, abu ɗaya nake buƙata shi ne amincewar Fahad. Ko da ya amince idan iyayen sa suka hana shi fa zai hanu. Saboda yana da biyayya. Ko ƙanwarki ai ba don yana son ta ya aure ta ba, ya yi biyayya ne kawai. Hanya daya za mu bi shi ne Fahad ya amince da auren ki ya saki ƙanwarki, sannan iyayen ki da iyayen sa ba za su iya hana wa ba za su yi shiru kamar ba sa ganin komai. Amma hakan zai faru ne ta sanadiyar aikin da wani Mallami zai yi ma na." Wani kallo Sidra ta yi Sady baby kafin ta ce "Ni na je wajen wani neman taimako?" Girgiza kai ta yi kafin ta ce. "Is not possible." "To idan ba haka ba ban hango himmatuwar cikar burinki ba. " Wani dariya ta yi kafin ta ce . "Ba wani Boka ko Mallam da zan je wajen sa, domin duk maƙaryata ne, a baya sun yi ma ni aiki ba abinda na gani, kuma na saka wa raina ba zan sake bin kowane Boka ba." "Rally?" Kau da kai Sidra ta yi kafin ta ce . "Kawo wata hanya amma ban da wannan." "Okya ina da wata hanyar da za ki iya cika burinki na raba Fahad da Nadra amma ba lallai iyayen sa su yarda ya aure ki ba, kuma su iyayen naki ba za su ba ki auren sa ba." "Na yarda in dai zai rabu da ita, saboda idan ina kallon ƙanwata a matsayin matarsa zuciyarta za ta yi bindiga ne." "Okay raba su ba abu ne mai wahala ba, saboda ba wai suna son juna ba ne , dukkansu sun yi biyayya ne." "To ya za'ayi ?" "Na san yanzu baya kasar idan ya dawo sai ki zo mu fara shirya planning yadda shirin zai tafi cikin tsari." _Umma_ Zaune take a falonta tayi tagumi lokaci zuwa lokaci take goge hawayen da ya cika ma ta idanu. Kallon Abba wanda ya murtuke fuska take yi. "Abban Sidra." Ko kallon ta bai yi ba ballantana ya amsa. Sai da ta sake fada a karo na biyu sannan ya fara magana a kausashe "Sau nawa na faɗa ma ki ba ni da ƴa mai wanann sunan, ita ba ƴa ta ba ce a yanzu, daga ranar da ta zubar ma ni da ƙima na cire ta daga cikin zuri'ata. Na sha faɗa ma ki kada ki sake yi ma maganar yariyar nan kin kasa dainawa ko?" "Ba'a canza wa tuwo suna duk in da za'a je a dawo kai ne uban Sidra ba wanda ya isa ya sauya hakan. Ai hannunka baya ruɓewa ka yanke ka yar da shi." "Idan hannuna zai ruɓe tuni zan yanke shi na yar tun kafin ya fara cin sassan jikina." Cikin damuwa Umma ta ce. "Yanzu yadda ka kore ta ba ka tunanin halin da za ta je ta saka kanta a ciki? Kora ba shi ne mafita ga yaran da suka aikata kuskure a rayuwarsu ba, saboda za su iya shiga wani halin da ya fi wanda suka shiga aka kore su, don Allah ka bari a kira ta ta dawo." "Kin san wani abu?" Abba ya tambaya yana kallonta "Sai ka faɗa." "Daga yau kada ki sake tayar ma ni da wanan zanen." Yana gama fadar haka ya fice ya bar ta. Umma na kuka ta nufi part ɗin Ammi tana sa ran samun sassauci idan ta yi wa Abba magana a matsayin ta na mahaifiyarsa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page4️⃣7️⃣ Umma na kuka ta nufi part ɗin Ammi tana sa ran samun sassauci idan ta yi wa Abba magana a matsayin ta na mahaifiyarsa. Ammi da ke zaune tana waya da Gwaggo Laraba ta ji kukan Umma ta kashe wayar. Cikin tashin hankali ta ke cewa Umma. "Ke lafiya?" Cikin Muryar kuka Umma ta ce. "Don Allah ki saka baki Mahaifin Sidra ya yafe ma ta ko za ta dawo gida." Tsuki Ammi ta ja tana cewa. "Ba zan taɓa saka baki Abdullahi ya dawo da wannan gantalalliyar yarinyar ba." "Haba Ammi ke fa mahaifiyarsa ce ke, kuma ke kadai na san cewa za ki iya yi ma sa Magana ya saurare ki. Da zaran kin saka baki shi ke nan." "To ba zan saka baki akan wannan yarinyar ba, idan ya ga dama ya yafe ma ta wannan ra'ayinsa ne ta dawo ban damu ba, idan bai yafe ma ta na kuma ta yi ta zama a duk in da take. Akan me za ki damu da yarinyar da ba ta gujin ɓacin ranki. Yarinyar da ba ki isa ki saka ta ko ki hana ta ba, yarinyar da ba za ta faranta ma ki ba sai dai ta baƙanta ranki.Ni ba ruwana da sabgar ta tun can dama, ballantana yanzu. Ki shawo kan mijinki idan ya yafe ma ta shi ke nan." Cikin sanyin jiki Umma ta bar ɗakin Ammi ta rasa tudun dafawa. _Maeesha_ Murƙususu take ta yi a jikin Makaho cikin azabtar ciwon da take ji. Makaho kuwa jin yadda take yi ya san tana cikin mawuyacin hali ne. Alluran da da ya kamata a ce ta yi shi tun last month ne ba ta yi ba, wanda hakan y saka ta cikin wannan halin. Kasancewar dama alluran *Depo-provera* ne da yake yi kowanne wata uku amfanin alluran dama ana yin sa wajen rage ciwon mara lokacin haila muka yana daidaita haila idan tana da matsala, ciwon haila na raguwa sosai. Kuma alluran tana da tsada sosai fiye da painkillers. Ta san cewa ba za ta iya jure ciwon marar da take yi ba, don rashin kwanciyar hankali da nutsuwa ya sa ta mance da cewa duk wata uku alluran ke aiki, ga shi tun last month ya dace ta je likita ya yi ma ta amma ta kasa. Ta san cewa ba ta da kudin da za ta yi alluran kuma ba za ta iya jurewa ba. Cije lips ɗin ta take yi wanda sai da ta ji gishiri-gishiri alamar ta fasa lips ɗin ta da hakori ne. Wayarta ta laluba a nan kan katifar bayan ta zame jikinta daga na Makaho. Lambar wayar ƙawarta Nasreen ce ta nemo ta danna ma ta kira. Bugu biyu ta ɗaga tare da cewa. "Hello ƙawata ya aka yi ne?" Yadda ta ji saukar numfashin Ma'eesha ya sa ta ce . "Are you okay." Ba ta ba ta amsa ba sai sheshsheƙar kukan da take yi. Hakan ya saka Nasreen ta katse kiran wayar, dama tana driving ne za ta koma gida. Don haka ta juya akalar motar zuwa hanyar unguwar da Ma'eesha suke . A cikin mintuna goma ta iso kofar gidan, daidai lokacin da makaho ke rarrashin ta yana cewa maganin me zai siyo ma ta. Sallamar Nasreen ne suka ji wanda Makaho ne ya iya amsa wa. Cikin ɗakin ta shigo ganin halin da ƙawarta take ciki ya sa ta ji tausayin ta. Don a baya lokacin da ta ce wa Ma'eesha ta rabu da makaho ba sa'ar aurenta ba ne sun dan samu rashin fahimta, musamman da Nasreen ta ba Abdul adireshin gidan Ma'eesha ya zo ran Ma'eesha ya sake ɓaci da Nasreen. Sai yau da ta kira ta a waya. Ganin kayan jikinta ya fara ɓaci ya sa ta gane halin da ƙawarta ke ciki. "Oh my God." "Nasreen ta faɗa tana dafe goshi." "Mu je ki gyara jiki mu tafi asibiti." Ta taimaka ma ta ta tashi suka fita har banɗaki ta kai ta, sanan ta fito ta duba bokiti ta dauka sai a lokacin ta lura da ruwan zafi dake kan murhun gawayi. Don haka ta ɗebi ruwan zafin ta sirka ya ɗan yi ɗumi sannan ta kai ma ta a banɗaki. Bayan ta ajiye ma ta ta fito yana ƙarewa gidan kallo tana mamakin yadda Ma'eesha ke rayuwa a cikin wannan akulkin gidan. Wanda ko maigadin gidan uban Ma'eesha ya fi karfin wannan gidan. Taɓe baki ta yi tana cewa. "Idan ta gaji ko ta ga uwar bari da kanta za ta saka ya sake ta, na san dole za ta zo ta same ni da wanan zancen. Muje zuwa. Yanzu da ta dawo gidan mu kamar yadda na ba ta shawara da yanzu tana cikin rufun asiri, da gangan na ki taimaka ma ta da kudi na bar ta sai wahala ta koro ta. Tsuki ta ja a ƙasan ranta, zuciyarta cike da takaici. Motsin Ma'eesha dake fitowa tana dafe bango ne ya sa ta fito. Taimaka ma ta t yi suka shiga ɗaki. Akwatin kayanta ta buɗe ta duba pad wato audugar mata, da pant ta ba ta ta saka da ƙyar. Doguwar rigar material ta ba ya ta saka sai hijabin da ta saka. "Wani asibiti za ki kai ta?" "Ko ma wane asibiti ne ni na san wanda zan kai ta kuma ni zan kashe kuɗin ko nawa ne duk da ba a wuya na hakkokin ta suka rataya ba, idan ban da kankanba ina kai ina Ma'eesha alhalin ba za ka iya daukar ɗawaini..." "Ya isa haka Nasreen, ban kira ki dan ki ci zarafin mijina ba, yana da hakkin sanin in da za mu je, ke ƙafata ƙafarsa ko..." "Really? Kina cikin ciwon ma bakinki ba zai iya jure aci Mutuncinsa ba, tun da na zo kin kasa magana, amma akan mijinki kin yi karfin halin magana duk da maganar daƙyar take fita ma ki." Cikin jigatuwa Ma'eesha ta ce . "In dai akan kare mutuncin mijina ne zan yi." Cikin sanyin murya ya ce . "A'a Ma'eesha ki ji da kanki, ku tafi Allah ya dawo da ku lafiya ya yaye ma ki lalurar da ke damunki." "Idan tare da kai ba na fasa zuwa." Sanin halin Ma'eesha ya sa Nasreen ta ce. "Ku fita mu je." Sandarsa ya laluba suka fita a tare. Duk da bai so bin su ba, amma bai so zuwa ba don dai Ma'eesha ta ce dole sai da shi za su tafi. Bayan motar ta bude ma su da taimakon ta Ma'eesha ta shiga ciki har lokacin tana dafe da kasan mararta tana hawaye. Makaho ya zauna gefenta yana ma ta sannu . Nasreen ta yi wa motar key suka bar unguwar. Wani tsadadden asibiti suka nufa. Asibitin da Ma'eesha ke zuwa ganin likita. Daidai lokacin kuma Doctor Irfan likitan da yake duba Ma'eesha ya fito daga office ɗin sa. Ganin Ma'eesha ya sa ya tsaya yana kallonta da mamaki ya ce. "Hajiya Ma'eesha lafiya?" Kallo ɗaya ya yi ma ta ya gane matsalar, don haka ya ce . "Me ya hana ki zuwa akan akan lokaci?" Wai Nurse mata biyu ya kara ya da suka shigar ma sa da Ma'eesha ciki Kallon Makaho ya yi kafin ya ce . "Yaushe aka fara bari mabarata suna shigo ma na asibi..." Kasa karasa maganar ya yi sakamakon jin Muryar makaho. "Ni ba mabaraci ba ne, ban taɓa nema a wajen kowa ba, don ina makaho ba shi zai ba ku damar wulakanta ni ba, ba don lalura ba ine zai kawo ni asibitin nan?" "Doctor tare muke da shi kada ka damu." Bai sake magana ba ya bar wajan don zuwa duba Ma'eesha. Wani ma'ikacin asibitin ne ya zo wuce wa, ganin Makaho ya sa ya taimaka ma sa ya zauna, kasancewar akwai kujerun zama a wajen. _Nadra_ Haka nan take jin za ta iya yarda da Aunty Rahma. Don ta rasa da waye za ta yi maganar ta ji sanyi. Kallon Sunyi Rahama dake sakar ma ya murmushi ta yi kafin ta ce. "Aunty wai da gaske na ci amanar Aunty Sidra?" "A'a ba ki ci amanar ta ba, waye ya ce kin ci amanar ta?" "Na ga yata ce uwa daya uba ɗaya, kuma ita ce take soyayya da Yaya Fahad suke son juna, wata ƙaddara ta saka ta bar garin a ranar aurenta da Yaya Fahad. Ita a tunanin ta idan ta idan ta tafi za'a dakatar da ɗaurin aure sai bayan ta dawo sanann za'a ɗaura. Amma iyayenmu suka kasa hakuri suka ce ba za su fasa daurin auren ba sai sai za su ɗaura da ni a madadinta. Wallahi Aunty Rahama ban san cewa aure na aka daura da Yaya Fahad ba, na ɗauka cewa da ita aka ɗaura ma su, sai dare ake sanar da ni wai ta gudu an maye ma sa gurbinta da ni. Ba ni da yadda zan yi ba dan yi jayayya da hukuncin iyayena ba, dole na yi masu biyayya. Na zauna da shi da niyyar idan ta dawo ya sake ni ya zauna da ita, saboda tare suka tsara rayuwarsu. Amma bayan ta dawo sai na lura da ita take son sa amma shi kamar ya fitar da ita daga rayuwarsa. To tun da har yanzu tana son sa ai bai dace a ce na cigaba da zama da shi ba ko?" Dariya sosai Aunty Rahama ta yi kafin ta ce. "Ke ba ki son sa ne?" Tura baki gaba ta yi tana cewa. "Ni ina da wanda nake so?" "Auzubillahi. Kina da aure kina maganar akwai wanda kike so? To ki daina ba kyau." "Shi ma Yaya Fahad ɗin fa baya so na, da kansa ya ce zai sake ni wai na je na auri shashashan wanda yake so na, Ya sayyadi yake kira da shashasha." Yadda ta yi maganar ne ya sake ba Aunty Rahama dariya sosai. "To na ji, amma ya fada ne ba zai sake ki ba." "Wallahi da kansa ya ce zai sake ni kuma ba da wasa yake yi ba, baya so na sai ya dinga ce ma ni wai ban waye ba bagidajiya ce ni, sanann Aunty Sidra tana ca ma ni wai Yaya Fahad baya son bak'ar mace sai fara kamar ta. "Ƙarya ne wannan , shi a familynsa ba bakake ne , ko mahaifinsa baki ne da sai ya tsane shi ko ya?" Shiru Nadra ta yi kafin ta ce. "Ki taimake ni ya sake ni sai ya auri Aunty Sidra." "Ba zai yiwu ba, Fahad na da ɗabi'a daya, idan ya so abu bai same shi a lokacin ba to abun ya kan fita ransa duk son da yake yi ma sa kuwa. Ko aka ja masa rai kafin a ba shi abu to yakan yi zuciya da shi ne. Don haka idan ba wani karfin ikon Allah ba to ya hakura da Sidra kenan. Kuma na tabbatar zai so ki kuma ke ma za ki so shi. Ba don yana ƙanina ba ne amma na tabbata ba macen da Fahad zai ce yana so ta ce ba ta son sa karya ne, don ya hadu ta kowane fanni, ke ba ki jin son sa?" "Tab ni kan ba na son sa kuma ba zan taba son mutum mugu mara imani irinsa ba." "Fahad ba mugu ba ne, abun da ya ma ki kowace mace cikakkiyar budurwa takan tsinci kanta a yadda kika tsinci kanki, sai dai ya danganta da yadda kowane namiji yake zuwar wa matarsa. Na san bai kyauta ba tun da ya tafi ya bar ki a cikin wanan halin, amma ki yi ma sa uzuri ba haka kawai y tafi ba, tafiyar dole ce ta kama shi." Nisawa ta yi kafin ta ce . "Ya jikin naki?" "Da sauki." "Ma sha Allah, an ce na kai ki za ki zabi motar da kike so, Baba ne ya ba su ki gift." "Aunty ba sai na je ba na ba ki zabi kowacce ne kika samu indai ta yi ma ki to ta yi ma ni." "Kin ba ni zaɓi?" "Eh." "To shikenan sai kin ga sako, sannan zan kawo ma ki wasu sabulai na wanka da maiyukan shafawa da wasu magungunan gyaran jiki da za ki dinga amfani da su." "Gyaran jiki kuma su ne har da na sha?" ",Eh haka suke, anjima zan dawo in sha Allah. Ko akwai abun da kike so ne?" "Ba komai na gode." Sallama ta yi ma ta sannan ta fice daga ɗakin. A ranar da yamma sai ga Aunty Rahama ta kawo galleliyar motar da ta zaɓawa Nadra,sai ɗaukar idanu take yi. Sannan ta shako manyan ledoji guda biyu na kayan gyaran jiki na ciki da waje. Daidai lokacin Sidra ta yi horn maigadi ya wangale ma ta gate, ta shigo da motar Mama da ta fita da ita, idsnunta ta sauke akan galleliyar motar dake sheƙi da daukar idanu. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page4️⃣8️⃣ Daidai lokacin Sidra ta yi horn maigadi ya wangale ma ta gate, ta shigo da motar Mama da ta fita da ita , idanunta ta sauke akan galleliyar motar da ke sheƙi da ɗaukar idanu. Cike da mamaki ta furta . "Mercedes Benz G Class ?" Ba ta gama cika da mamaki ba sai da ta ji muryar Aunty Rahama na cewa. "Sidra ga motar ƙanwarki ta iso." Cike da basarwa da kokarin danne bakin cikinta take murmushin yaƙe. "Ta yi kyau sosai na taya ta murna." Tana faɗar haka ta karasa wajan motar. Mota ne da mata ke so, tana da karfi sosai da nuna Class (matsayi) Ƙare wa motar kallo ta yi duk da ba z ta iya cewa ga kudin motar ba, amma ta san cewa an kashe miliyoyin kuɗi. Aunty Rahama ta fito da ledojin kayan gyara da ta siyo wa Nadra. Sidra ta bi ta da kallo har ta shiga ciki sannan ta mara ma ta baya, sai dai idanunta na kan Sunyi Rahama sakamakon ganin ta zagaya ta ƙofar da zai shigar da ita part ɗin Fahad ba tare da ta ji cikin main falon gidan ba. Cije lips ɗin ta na kasa ta yi kafin ta tura kofar falon ta shiga ciki. Da fara'a Aunty Rahama ta shiga cikin part ɗin Fahad. Kayan da ta siyo ne ya ya ma ta bayanin yadda ake amfani da su . Key din motar ta karkaɗa wa Nadra. "Motarki ta iso Farin ciki Nadra ta nuna kafin ta yi wa Aunty Rahama godiya. Sai da ta tabbatar ta saka Nadra ta fara shan magungunan nan na gyaran jiki sannan ta bar ta. Downstairs ta nufa da niyyar sanar wa su Mama motar Nadra ta iso. Mama da inna ne kawai a main falon suna fira. Sallamar Sunyi Rahama ne ya ba su mamaki don ba su san ta dawo gidan ba. Bugu da kari kuma ga shi ta fito daga part ɗin Fahad. "Ke dama har yanzu kina cikin gidan nan?" Cewarsu Inna bayan ta ɓalli goro ta tauna. "A'a yanzu na dawo, na kawo wa Nadra motarta ne?" "Ma sha Allah." Inna da Mama suka hada baki wajan fadar haka. Tashi suka yi Inna na mita ciwon ƙafa da take yi ya sa ta gaba. Suna isa harabar gidan sai ga Rumaisa da Farida sun shigo gidan. Su biyu ne a bayan motar yayin da direba ke driving nasu. Suna fitowa suka ga su Mama wajen motar Nadra suna addu'ar Allah ya kare ya sa ya more. Farida kam ko wajan ba ta karasa ba ta yi shigewar ta ciki yayin da Rumaisa ta karasa wajen motar cikin farin ciki. "Wow wanann motar na mata ma su aji ne. Na taya ta murna wallahi dama ni ma a siya ma ni irinta." _Ma'eesha_ Tana zaune bayan an kammala ma ta allura ne Nasreen ta shigo. Kallonta ta yi da alama ta samu saukin ciwon marar da ke damunta. "Ƙawata ya jikin naki?" "Da sauƙi" Murmushi ta yi tana cewa. "Na ga alama ai." Doctor ne ya kalle ta ya ce. "Za ku iya tafiya yanzu. Amma ki dinga kula sosai, sai nan da wata uku sai ki sake dawowa." "To Doctor na gode sosai." Nasreen ne ta kalli Doctor ta ce. "Shi ke nan ko?" "Eh ai ba wani abun da ya rage kin riga kin biya kuɗin." Godiya suka yi ma sa, suka fice. A in da Makaho ya zauna a suka same shi, Ma'eesha ce ta karasa in da yake zaune ta yi ma sa sallama. Ya amsa yana miƙewa tsaye rike da snadarsa. "Ma'eesha ya jikin naki." Murmushi mai sauti ta yi tare da cewa. "Alhamdulillah na ji sauƙi sosai sai abun da ba za'a rasa ba." Farin ciki ne ya ziyarce shi ya furta kalmar Alhamdulillah. A tare suka fito Nasreen na gaba su suna baya sun jera a tare suna tafiya. Bayan sun shiga motar ne Nasreen ta yi wa motar key suka bar asibitin. Har ƙofar gida ta sauke su, suka fita ta yi ma su sallama, Khalifa ya nufi cikin gidan, Ma'eesha ta tsaya tana yi wa Nasreen godiya sannan ta shiga gidan, Sa da ta shiga Nasreen ta ja motarta ta bar kofar gidan. *BAYAN SATI ƊAYA* Baba ya dawo daga tafiyar da ya yi da kwana biyu kenan ya ce wa Sidra ta shirya don ya kai ta ta ba wa Abba hakuri. Ita kam ba ta so hakan ba don tana zaune gidan ne saboda Fahad. Tana so da zaran ya dawo za ta ɗana tarkon da take ganin shi ne tsakanin da zai kai ta ga masoyinta Fahad Majidaɗi. Ba yadda ta iya haka ta shirya cikin shiga ta kamala da mutuntaka. Don ranar hijabi ta sanya a saman doguwar rigar amtamfar da ke jikinta. Sallama ta yi wa mutanen gidan in da Nadra ta rako ta har wajen motar Baba. Sai da suka bar gidan ta koma ciki tana addu'ar Allah ya sassauta zuciyar Abba ya yafe ma ta. Sai dai addu'ar ta ba ta karɓu ba, domin Abba shafa ma idanunsa toka ya yi ya ce sam ba zai karbi Sidra ba ya riga da ya yafe ta a matsayin ƴarsa. Duk yadda Baba ya kaɗa ya ya raya Abba ya ƙi. Domin shi kaifi ɗaya ne, idan ya faɗi magana ya fada kenan ba zai taɓa sauya wa ba. Sidra har ga Allah ta ji dadin hakan a zuciyarta sai dai ba ta bari hakan ya faru ba, don dai kukan karya take yi. Don Abba bai faɗa wa su Umma zancen

Chapter 28 of 49