Share this page
san ya tafi sallah ne. Don haka na shiga gidan kai tsaye, sai na zagaya ta baya sai nake jin sautin kukan jaririya. Wanda na leƙa ta window a na ga jaririyar kwance kan gado. Take zuciya ta raya na ɗauke ta na kai wa matata da na baro tana jego amma ba jariri ba ta haife shi da rai ba. Sai kawai na zagaya saboda na san irin lokacin ba kowa gida Alhaji na kasuwa yara suna Makarantar boko. Na shiga na tura ƙofar a hankali, jin saukar ruwa a banɗaki na fahimci wanka kike yi. Na ɗauke ta da sauri na saka cikin wata babbar jaka na cire Safar ƙafarta na saka ma ta a baki gudun kuka ya fito. Har na fita maigadi bai dawo masallaci ba. A hanya na haɗu da wata mata na ce ma ta ta taimaka ta biyo ni ta rike jaririyar nan muna sauka a gare ki sai ta juya ta dawo mu je Kaduna zan ba ta ko nawa take so. Na ɗebi kuɗin da ke aljihuna ma su yawa na ba ta. Ta kalli jaririyar ta kalli kudin sai ta amince ta kebe ta muka tafi a matsayin ita ce mai jaririyar . Sai dai muna sauka a Kaduna ta nemi motar da zai koka Katsina ta shiga ciki. Na nufi gidana da jaririyar sai dai nuna zuwa na tatar da labarin mutuwar matata. Na shiga tashin hankali sosai. Na rasa yadda zan yi da jaririyar sai na kira abokina dake unguwar mu kuma yana aiki a gidan marayu, sai na mika masa jaririyar na ce ya kai ta gidan marayu ta tashi a can . Don ban isa na koma da ita wajan iyayenta ba . Wanan shi ne Abun da ya faru shekaru arba'in da suka wuce. Yarinyar da ya kamata ta tashi cikin gata da kulawar iyaye amma ta tsinci kanta a gidan marayu. Yarinyar da iyayenta suke taimakawa suke ciyar da bayin Allah ta tashi a inda sai an kawo taimako sanan ta samu. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page8️⃣1️⃣ "Yarinyar da ya kamata a ce ta tashi cikin gata da kulawar iyaye amma ta tsinci kanta a gidan marayu. Yarinyar da iyayen suke taimakawa suke ciyar da bayin Allah ta tashi a in da sai an kawo taimako sannan ta samu." Kuka ne yake yi yana tari wanda ko a hanya ka gan shi sai ka tausaya ma sa. "Daga na kuma sai me ya faru?" Captain Kabeer ya yi tambayar bayan ya ga tarin ya tsagaita ma sa. "Eh to nikan tambayi halin da yarinyar take ciki, yana sanar da ni tana cikin kishin lafiya . Har zuwa lokacin da yarinyar ta cika shekaru goma sha Bakwai, aka yi ma ta aure, hankali na ya tashi da na ji labarin, amma kasancewar na ji an ce shi wanda ya aure ta mahaifinsa ne yake ɗaukar nauyin kaso saba'in na gidauniyar marayun. Kuma sanannen mutum ne ya yi suna Mutumin kirki ne daga nan hankalina ya kwanta. Sau tari nikan ji kamar na dawo m ku da ƴarku tun da wacce na kai wa jaririyar Allah ya karɓi rayuwarta. Amma gani nake za ku hukunta ni don ban san matakin da za ku ɗauka a kaina ba. Ga shi dama ba wanda ya san ni na sace jaririyar, ko da muka haɗu da Ɗan uwana da na bari yana ma ku gadi na bugu cikinsa ta hanyar tambayar ya kuke ya yaran ku zuwan yanzu yaranki nawa? Sai yake sanar da ni iya Sulaiman da Fatima ne kun sake haihuwa aka sace jaririyar har yau ba'a san waye ya sace ta ba. Haka na cigaba da rayuwa ta duk da ba na cikin natsuwa yadda ya kamata har na yi wani auren matata ta haifa ma ni yara biyar. Duk da auren sake jefa ni cikin tashin hankali ya yi sakamakon bana da kwanciyar hankali ga matata masifafdiya mulkin sake sakani damuwa take yi. Ga bakin cikin yaran da na haifa da sam ba sa jin magana. A haka dai wata rana na ji labarin yarinyar da na kai gidan marayu har ta haihu ta haifi ƴa mace sunan jaririyar Ma'eesha, wato ita jikar taku ce Ma'eesha. Daga nan ban sake jin halin da suke ciki ba sakamakon mai sanar da ni Allah ya yi ma sa rasuwa. " Shiru falon ya ɗauka idan ban da ajiyar zuciyar da Dada ke yi, dama ita tana ji a jikinta ƴarta tana raye sai dai ba ta san in da za ta samo ta ba. Shi ya sa ko fa mahaifin yaran nata kafin ya rasu ya tashi rabawa yaransa dukiyarsa ta ce ya raba har da Babyn da aka sace wata rana Allah zai bayyana ma su ita, har yake cewa yau shekaru talatin da biyar ba wanda ya sani tana raye ko tana mace. Amma duk da haka ya raba aka ajiye ma ta kason ta yau shekaru biyar kenan. "Yanzu idan har muka je wajen shi mahaifin da ya aura wa Ɗan sa ƴar uwar mu za mu same shi yana raye?" Cewar Alhaji Sulaiman sauƙi. Tabbas yana raye sai dai baya ƙasar. Amma na tabbatar matarsa na nan garin Kaduna har gidansa na sani saboda ba ɓoyayyen mutum ba ne." Sai a lokacin Barrister Haidar ya yi magana ya ce . "Ina ganin ba can ya kamata mu fara dosa ba. Shi wanda ya kai yarinyar gidan marayu za mu je da shi, na san gidan marayun dole sai ya bayar da sunan sa da ranar da ya kai yarinyar da komai da photonsa an tabbatar shi ne kafin su ne za su hada mu da asalin wanda ya dauki yarinyar." Jinjina kai ya yi "Tabbas an yi haka sai da suka yi ma ni tambayoyi na samar da su tsintar ta na yi, sai da aka karbi sunana da passport ɗina aka yi cike-cike sanan suka karɓe ta, suna da ƙa'ida da tsari." "To me muke jira maza ku dauko motoci mu kama hanya!" Cewar Dada jikinta har rawa yake yi . "Kin ga ki kwantar da hankalinki Dada, yanzu yamma ta yi ki bari gobe da asuba mu za mu tafi ni da Kabeer da Haidar." Ɗaura hannu aka ta yi ta fashe da kuka . "Anya Sulaiman kana farin ciki da bayyanar ƴar uwarka kuwa? Ta ya zamu bari sai gobe sannan ka ce wai ba da ni za'a je ba to da waye za'a je idan na da uwarta ba?" "Ba haka nake nufi ba Dada, kin ga dare zai ma na a hanya kuma yanzu ba samun jirgi da zai tafi Kaduna ba zai yiwu ba. Don haka tun da ba wai an ganta ba ne, bincike za'ayi sai mun fara zuwa gidan marayun an bincika an tabbatar aka hada mu da mutumin ya hada mu da iyalansa muka tabbatar da gaskiyar magana sai a ɗauko ki ki zo ku mu kawo ma ki su." "Yanzu kana nufin kai da Soja da Lauya ne za ku tafi?" "Eh in sha Allah, daga baya sai ki ganta idan an tabbatar." Da ƙyar aka shawo kanta ta yarda akan za ta zauna , gobe sai su kama hanyar zuwa Kaduna tare da Maude da zai ma su jagora. BQ aka kai Maude ya zauna aka kai ma sa abinci da ruwa . _Nadra_ Fitowar ta kenan daga wanka tana ɗaure sa babban towel da kuma wani ƙarami a hannunta tana tsane ruwan da ke kanta. Handrayer ta jona a socket ta nusar da ruwan dake ya jiƙa ma ta kai. Man shafawarta ta shafa da turaren jiki mai sanyin ƙamshi. Dama ita ba ma'abociya yin makeup ba ne. Tana kokarin shiga closet ɗin kayanta sai ta ji ƙarar buɗe kofa, Fahad ne ya shigo bakinsa dauke da sallama. Ta amsa tana kallonsa, sanye yake da wando three quarter da ƙaramar riga sai ƙamshin turarensa mai daɗin ƙamshi yake yi. Ɗaya daga cikin akwatin kayan lefe ya ɗauko daga cikin closet ɗin. Ƙananun kaya ne a ciki, irin ma su nuna jikin nan da kuma marasa nauyi. Don wasu kayan ma gani take da su da babu duk daya ne . Tana kallon da ya fito da wata figaggiyar riga da siket. Rigar kamar bra take daga sama kasan rigar ma duk saukan rigar ba za ta rufe cibiya ba. Siket din kayan iya rabin cinya zai tsaya ma ta. Mika ma ta rigar ya yi tana cewa . "Daga yau idan ina gida irin wanan kayayyakin nake bukatar ki dinga saka ma ni ina gani. Dan gaskiya na gaji da ganin kullum cikin manyan kaya da Abaya. Ke da saka su sai dai idan fita za ki yi ko kuma ba na gidan . Idan kin ji sallamar baƙi ki saka hijabi kawai . Kallon kayan take yi ba ta karɓa ba, take sai jikinta ya yi sanyi sakamakon tuna Sidra da ta yi wacce da ba don ƙaddara ta ƙaddaro cewa ita ba matar Fahad ba ne da yanzu ita ce a matsayinta. Tuna yadda Sidra da Fahad suka je kasuwa suka yo siyayyan kayan ta yi, tana tuna yadda Sidra take ba Sady baby labarin irin kananan kayan da ta siyo wanda banbancin su da babu kadan ne. Da ƴan iskan kayan barcin da suka zaɓo ita da Fahad ma su bayyana jiki. Ko rigar da yake ba ta ba ta sake kallo ba don ta san shi da Sidra suka zaɓo shi don ta burge shi. Har ta buɗe baki da niyyar yi wa Fahad zancen Sidra sai ta tuna ya ce baya son tana maganar Sidra don haka sai ta fasa. Amma jikinta ya yi sanyi sosai tuna cewa wannan kayan fa da sunan Sidra aka siye shi ko ma ita ta zaɓe shi amma yanzu ita ce za ta yi amfani da shi. "Tunanin me kike yi?" "Ba komai." Murmushi ya yi yana cewa. "Ina fatan kin gane me nake nufi ko? Na fi son kananan kaya matata za ta dinga saka min dan haka ki saba." Shiru ya yi tana rike da kayan ba ta saka ba "Bari na saka ma ki tin da baki iya sakawa ba ." Jin haka ya sa ta yi saurin cewa. "Zan saka da kaina." ,"okay ina jiran ki a falo." Ya fada yana ficewa daga ɗakin . Dole ta bi umarnin sa ta saka kayan, amma sai ta ji ba za ta iya fita da shi ya ganta a haka ba. Sai ta ɗauki dogon hijqbi ta saka tana tafiya a hankali kanta ƙasa kamar munafuka. Jin ƙarar kofar ya sa ya juyo yana washe baki, take fara'ar fuskarsa ta ɗauke yana kallon ta cikin hijabi take ya tsuke fuska. _Sidra_ Da maɗaukacin mamaki take kallon matashin malamin. Duk da cewar ba zai haura shekaru talatin da biyu zuwa da uku ba, amma ta yi mamakin jin kalamansa. Sanan kuma Sady baby ba ta damu ba. "Mallam ka san me kake faɗa kuwa ?" "Ke Mallama idan har zan yi ma ki aiki to fa ba zan karbi kudin ki ba, jikinki kawai nake so ki bani haɗin kai ku ga aiki da cikawa ." "Wai ƙawata ba ki ji me yake cewa ne? Wai sai ya yi lalata da ni fa?" 'Eh yi meye ai idan bukata za ta biya ba wani abu ba ne , ku tuna Fahda kike so ba kowa ba kuma za ki mallakar shi sai yadda kika yi da shi a rafin hannunki don haka ki Amince kawai kamar biya ma sa bukata shi ma ya ya ma ki aiki ki ga biyan buƙatar. Idan kuma ba ki aminci ba ba to ba wani Mallam da na sani sai dai ki koma gida ki je a kai kuma ƙauye a aura ma ki ɗan kauye ku je can ku ƙarata ki lalace. Tana faɗar haka ta fita waje ta janyo ma su ƙofa ta koma cikin mota tana jiran su gama abun da za su yi . _Jalaluddeen_ Tun bayan jin hukuncin mahaifinsa jikinsa ya yi sanyi da hukuncin, domin shirin sa ta gama wargaje wa shirin sa ya lalace. Kallon Yasmeen ya yi wacce farin ciki ya cika ta da jin zancen Dad din. "Za ki tashi mu tafi kuwa?" Da sauri ta tattara kayanta ta shirya tana murmushi. "Hankalinki ya kwanta ko?" "Abun da kike so kin samu hankalin ki ya kwanta ko?" Murmushi kawai ta yi ta nufa hanyar fita daga ɗakin ta fice. Sai da ya dauki sakanni sannan ya samu zarafin fita daga cikin ɗakin ya fice kai tsaye. Tana jiransa a gefe ya ganta daga nan suka fice a tare. Bayan ya ba d key din ɗakin ya yi gaba tana bin sa a baya har suka fice daga hotel ɗin . Kai tsaye gidan Alhaji Tanko Abokin Dad ya kai ta. Yana zaune a bayan motar shi da Yasmeen sai yaronsa dake driving motar . Shi ya nuna wa yaron hanyar gidan kasancewar ya taba zuwa sau ɗaya, wani zuwa da Dad ya yi ɗaurin auren ƴar Alhaji Tanko, ya kira Jalaluddeen ya sanar da shi yana garin, shi ne Jalaluddeen ya zo bisa kwantancen da Dad ya ma sa . Bayan ya yi horn a ƙofar gidan ne maigadi ya leƙo ya ƙaraso wajen motat ba tare da ya bude gate ɗin ba ta karamar ƙofa ya fito. "Assalamu alaikum." "Wa'alaiki salam." "Don Allah waye kai Yallaɓai an ce na tambaya ne?" "Jalaluddeen ne" Ya faɗa daga bayan Motar da yake . Da sauri Maigadi ya wangale ma su gate suka shiga ciki. Jalaluddeen ya fito bayan direban ya yi parking, ita ma ta fito riƙe da jakarta. Direban na bayan motar yana jiransu yayin da suka nufi main door din gidan . Ya kai hannu zai danna ƙararrawar kofar kenan sai ga ɗaya daga cikin ƴan matan gidan ta buge ƙogar za ta fito. Idanunta ya sauka akan Jalaluddeen, ta zuba ma sa idanu tana kallon sa ita ba ta matsa ta ba shi hanya ba. Sai da Yasmeen ta dawo ta tsaya gaban Jalaluddeen sanan wanan budurwar ta ɗauke ido yana barin wajen cike da kunya. Da sallama suka shiga Alhajin yana falo tare da matarsa . Bayan sun gaisa ya sanar da shi saƙon Dad, Alhajin ya ce Dad ya sanar da shi ba damuwa zai iya tafi gobe sai ya zo ya kai ta airport. Sallama ya yi ma su ya fita yayin da matar gidan ta ƙwalawa ɗaya daga cikin yarinya kiraz ta fito Nam ta sanar da ita je da Yasmeen ɗakinta su kwana zuwa gobe. Tashi Yasmeen ta yi ta bi bayan yarinyar wacce ta ɗauki kakar kayan . Jalaluddeen na cikin mota sai kiram Ma'eesha ya shigo wayar. Bayan ya ɗaga ne ta nemi izinin fita gidan Mallam Liman ana biki sam ta mance sai kusan yamma ta tuna shi ne ta kira shi da yamman . Ya ba ta izinin fita sanan ta yi godiya ta katse kiran wayar. Kai tsaye hanyar gida ya ce wa yaronsa ya kai shi. A bakin layin ya sauka ya dauki sandarsa a bayan motar ya yi wa yaron sallama sannan ta fara tafi zuwa cikin layinz don can baya ta sauka sau da ta tabbatar ba mai ganinsa ta fito da sauri. Tafiya yake yi cike da damuwa, ya so kafin a tayar da zancen aurensa da Yasmeen ya sanar da su auren Ma'eesha da ya yi, ga shi zuwan Yasmeen ta lalata ma sa shiri. A haka ya karasa cikin damuwa har cikin gidan, ba ta nan kasancewar ya san in da take ajiye key kan window ne sai ya ɗauka ya buɗe kofar. Ya shiga ciki tana safa da marwa a cikin ɗakin Vibrating na wayarsa ya ji daga cikin aljihu, ya ɗauka Dad ne, amma sai ya ga abokin sa Khalil ne . Ya amsa sallamar bayan ya daga wayar. Daga cikin wayar abokin ke cewa. "Ya na ji muryarka wani iri?" "Dole ka ji muryata wani iri ma na, wai ranar jama'a ne aurena da Yasmeen." "To me ye na damuwa bayan ka san da wanan zancen ba tun yau ba, ka sanar wa abokanmu kawai Malam . "Ba wanda zan sanar, dama ka san ba wai na fiye yawan mu'amala da aboka ba ne." Daidai lokacin da Ma'eesha ke shigowa gidan, sakamakon tuna zai iya dawowa ga yamma ta yi lokacin dawowarsa ne, don haka ba ta zauna s gidan bikin ba ta ma su Allah sanya alkhairi ta dawo don ta tarbi mijinta. Cak ta tsaya bakin ƙofar sakamakon jin muryarsa yana cewa. "Rabo na da wasu abokan fa tun da muka gama karatu a America ban sake haduwa da su ba, sai dai wani lokaci da na je London na haɗu da su Faisal a can . Sai kuma Ahmad da ya matsa sai na je bikinsa to a lokacin na tafi ƙasar Canada. Daga nan ban sake bi ta kansu ba, sai yanzu kawai dai na kira su na sanar da su cewa ranar Juma'a ne ɗaurin aure na da Yasmeen? Ba wani gayyatar da zan yi kai ma ɗan ka kira ni ne kuma ban ce ka ma ni gayya ba, ba abun da za'ayi daga an ɗaura auren shi kenan kowa ya watsa ba ruwana da wani events ko wani bidi'a." Kalamansa sun matukar gigita ƙwaƙwalwar Ma'eeha wanda ta ji wani jiri na ɗibarta ga numfashinta dake barazanar ɗaukewa. Kalaman da ta ji tana yi ne suke ma ta amsa kuwa a cikin kunnenta kamar za su fasa ma ta dodon kunnen. "Dad ya ce na bar garin nan dole na koma Abuja na halarci bikin aurena da..." Kafin ya karasa maganarsa ya ji faɗuwar abu kada tim. Da hanzari ya daki wayar kasa ya fito da sauri, Ma'eeha ya gani kwance kada ba ta numfashi." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page8️⃣2️⃣ "Dad ya ce na bar garin nan dole na koma Abuja na halarci bikin aurena da..." Kafin ya karasa maganarsa ya ji faɗuwar abu kasa "Tim." Da hanzari ya saki wayar ƙasa ya fito da sauri. Ma'eesha ya gani kwance kasa ba ta numfashi. Taune lips ɗin sa ya yi har sai da ya fashe jini ya fito, ya san ta ji komai kuma yadda ta ji ta wanan hanyar zai yi wuya ta fahimce shi. Ƙarasawa ya yi wajan da take ya dauke ta ya shiga ɗakin da ita. Ruwa ya yayyafa ma ta amma ba ta farfaɗo ba. Sau uku yana zuba ma ta ruwa ba ta farfaɗo ba. Don haka hankalinsa ya fara tashi ya ɗsuki wayarsa ya danna ma wata lamba kira. Bayan an ɗaga kiran wayar ne ya yi magana cikin bayar da umarni ya ce. "Ka zo karamin gidan da nake kwana yanzu-yanzu." Daga haka ya katse kiran wayar yana Safa da marwa a cikin dakin. Tsayuwar motar da ya ji a kofar gidan ne ya sa ya ɗauko hijab ya saka ma ta sanan ya dauke ta ya nufi hanyar fita daga gidan . Yaronsa na ganinsa ya bude bayan motar da sauri, yayin da Jalaluddeen kwantar da ita s bayan motar. Sanan ya koma ciki ya ɗauki wayarsa ya rufe gidan suka bar unguwar. A saman cinyarsa ya dora kanta yana kallon fuskarta. Wani tsadadden asibiti aka nufa da ita a nan cikin garin . Yana parking din motar Jalaluddeen ya fito da sauri ya dauke ta ya nufi ciki da ita . Emergency aka kai ta likitoci biyu suka tsaya a kanta. Sai Safa da marwa Jalaluddeen yake yi gabaɗaya ya rasa nutsuwarsa. Kiran sallar magrib da ake yi ne ya sa shi fita zuwa masallacin dake jikin asibitin. _Sidra_ Tana ganin Sady baby ta fita ta tsaya tana nazari . "Kin ga Mallama ba dole sai kin amince taimaka ma ki zan yi ki auri wanda kike so, ku yi rayuwa na har abada ki mallake shi sai yadda kika yi da shi, komai zai yi sai da izininki. Idan muka ba ki son shi ki haƙura kawai ma na ." "Ba zan iya hakura da Fahad ba." Jin ta yi shiru alamar amincewa ya yi murmushi yana shafa siririn gemunsa. Tura ƙofar ɗakin ya yi ya sa sakata ya rufe window. Tana ji tana gani ya umarce ta da ta cire kayanta, ba ta yi musu ba ta cire kayan kamar yadda ya buƙata. Idanunta ta rintse tana hawaye, a yadda ta tsara rayuwar ta da Fahad a daren farkon auren su amma yanzu duk ya rushe ga wani banza nan zai raba ta da mutuncinta na ƴa mace. Ƙara ta saki lokacin da ya shige ta da ƙarfi sakamakon azabtar da ta ji. Sanin asirinsa zai iya tonuwa ne ya sa ya saka hannu ya toshe ma ta baki, ta yadda muryaryarta ba zai fita ba. Hawaye kawai take ya babu sautin kukan baya fita ya toshe bakin. Sai da ya biya buƙatsrsa sanan ya bar ta nan kwance. Kayan jikinsa ya saka sannan ya kunna hasken ya ganta jini ya ɓata ma ta jiki. tishu fefa ya yago ya mika ma ta. "Karɓi ki saka cikin pant ɗin ki kada jinin ya ɓata ma ki kaya." Kakan takaici da nadama ta saki a lokacin da bai da amfani. Karɓa ta yi ta saka ta mayar da kayan jikinta, ba ta iya tafiya sosai haka ta ke ɗingisa ƙafa ta fita idanunta a kumbure. Sady baby na ganin tafiyar ta san aikin gama ya gama . Murmushi ta yi wanda ita kadai ta san ma'anarsa. Tabbas ta ji farin cikin rasa budircin Sidra, domin kuwa dama burinta ta ga rayuwar Sidra ta lalace. Ba ƙaunar Sidra take yi ba, hasalima tsanarta ta yi. Ba ta son ganin rayuwarta ta inganta. Bayan ita ma tana son Fahad din amma ko da ba ta son sa ba za ta bari ta ga rayuwarta ta yi kyau ba. Shi ya sa ta ba ta shawara ta gudu ranar aurenta gara ta samu ɗaukaka ta yi suna lokacin kowa zai ƙaunace ta fiye da yadda take, kuma hakan zai sa ta rama wulaƙanci da aka yi ma ta. Tabbas Sidra ta yarda Sady baby mai ƙaunarta ce yake ɗaukar shawararta. Duk da halin da ya shiga bai ishe ta ba sai da ta saka ta rasa budurcinta. Tafiya Sidra ke yi tana hawaye. Da sauri Sady baby ta fito daga motar ta taimaka ma ta ta shiga. Sanan ta bar ta cikin motar ta koma wajen Mallamin nata. Bayan kamar mintuna goma ta dawo ta ce. "Ya ce daren yau zai fara aiki akan Fahad din, jibi zan zo na karbi maganin da zan kawo ma ki ki yi amfani da shi." Ba ta ce ma ta komai ba illa hawayen da take yi . "Mu je na ajiye ki gida ne ko gidana za mu je?" "Gidanmu za ki kai ni." "Okay to, idan kin je ki gasa jikinki sosai da ruwan ɗumi ki zauna ciki, sanan ki bi kofar baya kada wani ya ga shiganki, ki tabbatar sai kin gasa jiki kafin ki fita wajan iyayenki, idan so samu ne ki kwanta kawai sai da safe." Ba ta ce ma ta komai ba ta cigaba da goge hawayenta, dansani take yi da ba amfani . _Jalaluddeen_ Har ya dawo masallaci sallar isha'i amma ba Ma'eesha ba ta farfaɗo ba, ganin yadda ya tayar da hankali ne ya sa suka kwantar ma da da hankali. Ko ruwa bai saka a cikinsa ba ballantana abinci . Da misalin karfe goma sha ɗaya na dare ne yana zaune s kan kujera ya zuba ma ta idanu. A hankali ta fara motsa ƙafarta sanan hannunta. Zuwa can ta sauke idanunta akansa. Tana kallon sa sai ta rintse idanunta da ƙarfi, hawaye na zuba a idanunta ba abun da take tunawa illah maganar Nasreen da take ta kokarin fahimtar da ita akan sanin waye asalin mijinta, amma sai take ganin laifin Nasreen tana kalubalantar ta ashe tana da gaskiya ita ce ta ƙi ta fahimce ta. Ganin ta farfaɗo ya saka shi sakin murmushi. "Ma'eesha sannu ko?" Wani takaici ne ya sake cika ta har ya fashe da kuka. "Ka yi nisa da inda nake ba na ƙaunar ganin ka, ka san yadda na tsani maƙaryaci da mayaudari kuwa? Ashe kai na kama da laifin da na fi tsana a rayuwata? Da a mafarki na yi wanan mafarkin idan na tashi sai na yi sadaka. Dama na faɗa ma ka duk ranar da na gane ka yi ma ni ƙarya za mu samu matsala, ƙarshen rabuwa ta

Chapter 46 of 49