Share this page
cikar halitta. Don ta fi Sidra nono da hips. Dan ko tela ma idan zai yi ma su ɗinki na Nadra yakan fi na sidra kaɗan. Don haka pant ɗin dai ta saka ya shiga ma ta, amma bra bai shiga ba don rabin nononta a waje suke kuma sai ya maste ta, kasancewar da sunan Sidra aka ajiye komai to komai size ɗinta ne ita kuma ba ta da nono Sosai ƙanana ne da ita. Don haka Nadra ba ta wahalar da kanta Wajan saka bra din ba ta bar nononta haka nan, kasancewar nonon nata irin ma su kan tasa ɗin nan ne a tsaye suke ƙyam. Wata doguwar rigar material mara nauyi ta saka bayan ta sa turare sannan ta saka dogon Hijabinta ta ɗauki sallaya ta fito ta shimfiɗa. Sallar nafila ta yi kafin ta yi sallar asuba ta zauna tana azkar. Duk da kasancewar ta mai yawan karanta Alkur'ani ne da safe amma Yau kam ba ta jin za ta iya karatun Alkur'anin nan da ta saba. Kwanciya ta yi a nan saman sallayar da ta yi sallah. Don ciwon kanta nan nan ba ta daina jin sa ba, ga sanyi tana ji. Don haka sai ta ƙudundune kanta cikin Hijabin a nan saman sallayar ta yi barci. Da misalin karfe takwas na safiya a cikin ɗan barcin da ya ɗauke ta ne ta ji ƙamshin turarensa ya ziyarci hancinta. Wani faɗuwar gaba ta tsinci kanta a ciki. Duk da ba ta son bude idsnunta da suka yi ma ta nauyi amma sai ta ɗan tashi zaune daga saman sallayar ta kalle shi da kyar. Sanye yake da farar jallabiya a jikinsa ya tsaya a tsakiyar ɗakin yana kallon ta. Daidai lokacin da wayarta dake kan gado ta soma ruri, tana son ta miƙe amma ta kasa. Sai ta ga ya nufi gadon ya ɗauki wayar. Sunan da ya gani a screen ɗin wayar yana yawo shi ne an rubuta YA SAYYADINA. Sannan aka saka emojis na love da kuma emoji na heart a gaban sunan. Miƙa ma ta wayar ta yi ba tare da ya yi magana ba. Kuma ya tsaya a saman kanta. Har kiran ya katse wani ya sake shigowa sannan ta ɗaga tare da yin sallama. "Assalamu alaikum Ya sayyadi" "Wa'alaiki Salam warahmatullah ya Sayyadata." Shiru ba ta sake magana ba, sai dai tana da yaƙinin Fahad ɗin ma ya ji maganar Ya Sayyadi, dan wayar sauti na fita wanda ke kusa da kai zai ji maganar na cikin wayar. "Sayyadata an watse taron biki lafiya ko?" Ban samu zuwa..." Sai kukanta ya ji ta fashe da shi. "Subhanallah, subhanallah ya sayyada me ya faru ne, ki faɗa ma mi make faruwa ne?" Ya faɗa a ruɗe saboda jin kukanta. Fahad ya karbi wayar daga hannunta ya ce. "Kai daga yau kada ka sake kiran wayar nan?" "A'uzubillahi me ya haɗa Sayyada da rijalu kuma, ke sayyada waye Wannan kuma? Subhanallahi A'uzubillahi minash shaiɗani rajim ƙato da wayar Sayyada da sanyin safiyar nan. Wa'iya zu billahi a'uzu billahi." Cike da takaici Fahad ya ce. "A'uzubillahi akanka. Kai bari na yi ma ka gargadi na karshe, idan har ka sake kiran wayar nan sai na sa an koya ma ka hankali, za ka san waye Fahad Majidaɗi." Da sauri Ya Sayyadi ya ce. "Fahad Majidaɗi da na sani mijin Sidra?" Bai ba shi amsa ba ya ce. "Ina mai maka gargadi wallahi ranar da ka sake kiran wayar nan duk inda kake a faɗin ƙasar nan sai na saka an kamo ma ni kai, ban damu da wanzuwar soyayyar dake tsakanin ka da Nadra ba, amma a halin yanzu ta yi ma ka nisar da ba zai ka iya kamo ta ba, watakila dai nan da lokaci kaɗan idan na sallame ta za ka iya zuwa gidansu ka ci gaba da alaƙa da ita ko ka aure ta wannan ba damuwata ba ce, amma a halin yanzu tana ƙarƙashina kam ƙarya ne na bar ka ka yi wata alƙa da ita, idan za ka iya jira ka je ka ci gaba da jiranta har zuwa lokacin da za ta fito, amma kam sake kiranta bayan tana ƙarƙashin iko na shi ne kuskure ma fi muni da za ka tafka a rayuwarka." Yana gama fadar haka ya katse kiran wayar tare da yi wa Nadra wani mugun kallo." "Ke!?" Ya kira sunanta da kakkausar murya. Idanunta da suka yi nauyi ta daga ta kalle shi da kumburarrun idanunta. "Idan kika sake magana da wani ƙaton gardi a cikin gidan nan bayan kin san akwai igiyar aurena a kanki sai na shayar da ke madaran mamaki." Ba tare da ya sake magana ba ya fice rike da wayar a hannunsa bai ba ba ta wayar ba. Kuka ta sake fashe wa da shi wanda ya ƙara sa wa ta ji kanta na barazanar tarwatse wa. Yana zuwa falon ya ji ƙarar ƙararrawar ƙofa, sauka downstairs ya yi ya nufi ƙofar ya zai buɗe. _Makaho_ Ko da ya dawo daga masallaci sallar asuba ƙarfe bakwai na safiya. Zuwa lokacin Ma'eesha ta kammala aiyukan gidanta. Ta gyara ɗaki ta share ta yi mopping ta yi wanke-wanken ta wanke toilet sannan ta yi wanka. Dadai lokacin da ta fito da Gas da za ta hada ma su abun breakfast kenan ta ji sallamar sa ya shigo gidan. Ta amsa ma sa sallamar ya shigo ta zuba ma sa idanun tana kallonsa. Sai da ta durƙusa cikin girmamawa ta gaishe shi duk da baya ganinta. "Ina kwana?" "Lafiya lau Mar'atusaliha." Murmushi ta yi ba tare da ta ce komai ba. "Kin tashi lafiya?" "Alhamdulillah." "Ma sha Allah, sannu da ƙoƙari Allah ya saka ma ki da gidan Aljanna Firsausi." "Amin ya rabbil izzati." "Me kike yi ne haka, na ɗauka za ki kwanta sakamakon juya ba ki samu isasshen barci ba jiya." "Ai na yi barci kai ne dai ya kamata ka wanta ka huta ko za ka samu barcin da ba ka samu ka yi ba." "Ni da zan fita neman na kai ne zan kwanta na huta?" "Wai nawa kake samu a rana wajan gyaran takalmin da kake yi ?" "Eh to mutane da yawa ba sa yarda su ba ni aiki, kasancewar ni makaho ne ba na gani to ba sa yarda su ba ni aiki, sai su ce wai ba aikin da na iya, sai su kai wani wurin, amma wasu na bayar wa sai dai ba su da yawa. Abun sai sa'a ne wata rana ma bai wuce na samu ɗari biyu wata rana dari biyar amma ban taba samun dubu ɗaya ba. Shi ya sa nake ganin cewa ba zan iya riƙe ki ba, ban cancanci na ajiye mata ba, saboda ba na da halin ciyarwa da me zan ciyar da ke? Sam na kasa dalilin da ya sa iyayenki suka aura ma ni ke, bayan kin saba da cin abinci mai kyau mai tsada, ruwan sha mai tsada sutura mai tsada kayan kwalliya ma su tsada ta ya zan iya yi ma ki duk abubuwan da kika saba da su?" Murmushi ta yi tare da cewa. "Dama haka rayuwa ta gada, ba komai yake tafiya a yadda yake a da ba." Haka ne Ma'eesha, amma na rasa gane me kike son ki ci ma wa a rayuwa, ko me kike so ki zama meye burin ki?" Murmushi ta yi kafin ta ce. "Ina son na zama mace tagari mai tsoron Allah a fili da ɓoye, tare da biyayya ga manzon Allah mai biyayya ga iyayenta ɗari bisa ɗari da kyautatawa, mai biyayya ga mijinta, idan ya hana ta hanu, idan ya sa za tayi. Wacce take ɓoye adonta ga mazan waje, ta bayyana shi ga mijinta. Wacce take da kunya, gaskiya, adalci da tausayin mijinta. Wacce ba munafuka ba, ba ta sharri dan ta jingina karya a mijinta. Mace mai girmama iyayen mijinta da yan uwansa saboda Allah mace mai gudun duniya da neman na kanta kamar Nana Khadija. Mace mai tallafawa mijinta da dawainiyar gida kamar Nana Fatima. Mace mai kishin mijinta kamar Nana Aisha." Allah sarki ƴar aljanna, yanzu kina ganin za ki iya karɓa ta a matsayin mijin aurenki, za ki rayu da ni a cikin kowane hali?" "Me ya saka ka yi Mani wanan tambaya?" "Saboda na ga kin fi ƙarfin na, ke ba ajina ba ce kin wuce sa'ar aurena, a matsayina na nakasashshe miskini ta ya ke da kika rayu cikin daula da wadata za ki iya zama da ni?" "Me za hana na zauna da kai idan ƙaddarar aurena da kai ne Allah ya tsara?" Ba na son na fita daga cikin salihan bayi ma su godiya da duk abin da Allah ya aiko ma su da shi? Mai daɗi ko mara daɗi, ma su jiran ƙaddara duk daɗinta duk raɗaɗinta su haɗiye ta, ko ba ka san cewa Allah ya fi mu sanin abun da ya dace da mu ba?" Jinjina kai ya yi tare da cewa. "Haka ne?" Murmushi ta yi kafin ta ce. "Ina son ka ba ni tarihin rayuwarka ban san kowa naka ba, ina son sanin Asalinka?" *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page2️⃣1️⃣ Ina son ka ba ni tarihin rayuwarka ban san kowa naka ba, ina son sanin Asalinka. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Yanzu aiki kike yi, ki ci gaba da yin aikinki idan muka b zauna ba ki aikin komai ni ma ba na komai sai na baki." "To shi kenan, bari na haɗa ma na breakfast." Shiga cikin ɗakin ya yi ya bar ta nan tana kiciniyar ɗora girki. Tana nan zaune ta ga ya fito daga ɗakin rike da wasu kayan a hannunsa, da alama wanka zai shiga. "Ka bari na sa ma ka ruwan zafi ka yi da shi don akwai sanyin safiya." Murmushi ya yi tare cewa. "Ma'eesha kenan, ni da na saba da ruwan sanyi me zai dame ni kuma yanzu? In dai wannan ne na saba da shi kar ki damu kanki, babu irin rayuwar da ban gani ba." "Na sani amma ya kamata ka san cewa tsakanin da da yanzu akwai banbanci, da ba ka da aure ba ka da wacce za ta dafa ma ka ruwan zafi ka yi ji wanka, yi yanzu Allah ya ba ka ya kamata ka san cewa akwai banbanci tsakanin lokacin da kake da aure da yanzu. Yanzu fa ɗan gata kake mai cikakken iko, ka saka ayi ka haka a hani ai kuwa ka ga da banbanci ko?" "Haka ne." "To ba ni mintuna biyar kaɗai zan dafa ma ka ruwan zafi yanzu." Zama ya yi akan dangaramar ƙofar ɗaki ta zuba ruwa a cikin tukunya ya yi zafi sannan ta juye ma sa cikin bokitin ta mai ma sa har cikin ɓanɗaki." "Na mai ma ka ruwan cikin banɗaki." "Na gode ma ki Ma'eesha Allah ya yi ma ki albarka." Da Amin ta amsa sannan ya shiga banɗaki, ta fara kiciniyar haɗa ma su breakfast. Bayan ya gama ya fito sanye da wasu kayan a jikinsa, waɗanda ya cire kuma suna a hannunsa. Kallonsa ta yi sannan ta ce. "Wai me ya saka da ka yi wanka kake saka kaya ne, kar ka damu ko da ba ka gani na ai idan za ka canza kaya zan fito daga cikin ɗakin na ba ka wuri ka shirya ne, amma ace daga yin wanka ba ka tsane jiki ba kuma ba ka shafa man shafawa ba kawai sai ka ɗauki wasu kaya ka saka?" "Za'a daina in sha Allah." "Da ya fi." Ta faɗa tana mai cigaba da fere dankalin turawar da take yi. "Bari na tso na ba ka man shafawa da turare ka shafa." Ta mike ta bishi cikin ɗakin. Man shafawar da ta ba shi ya shafa ne ya shafa ya kuma ya shafa turaren da ta ba shi. Tana nan zaune ya fito yana yana cewa. "Aikin me zan yi ma ki ne na fara yin yanzu kafin na fita ." "Ka fita ina?" "Neman na kai mana." "Yau da alama za'ayi rana a garin nan, ka je kana ta wahala a cikn rana bai fi ka samo Naira ɗari biyar ba. Don haka cinikin yau na siye zan ba ka Naira dubu ɗaya ka ga ai na ba ka fiye da cinikin da kake yi ." Ga mamakin ta sai ta ga ya tsuke fuska alamar ransa ya ɓaci. _Fahad_ Kafin ya karasa bakin ƙofar har an dake danna wata ƙararrwar. Yana bude ƙofar ya ga ƙanwarsa Rumaisa ce rike da basket na abinci. Sai wasu ƴan mata guda biyu tare da ita, yan matan duk danginsu ne da suka zo biki daga wani garin. Basket ɗin abinci ne a hannun Rumaisa. A tare suka haɗa baki wajen cewa. "Yaya Fahad ina wuni?" Bai amsa ma su gaisuwar da suke yi ma sa ba, hannu ya mika wa Rumaisa alamar ta ba shi basket ɗin hannunta. Ta mika ma sa ya karba zai mayar da ƙofar ya rufe ta ji saurin cewa. "Yaya Please za mu ga Amarya." Tsuke fuska ya yi kafin ya ce. "Wani lokacin za ku ganta." Marairaice fuska suka yi suka hada baki wajen cewa. "Yaya Please." Rumaisa ta ɗora da cewa . "Kuma dama Mama ta ce idan mun zo mu shiga mu gaishe ta mu ce kuma tana gaishe ta." Sauran suka hada baki wajem cewa. "Eh haka ne." Ba su hanya ya yi alamar su shiga ba tare da ya ce komai ba. Suna shiga ya mayar da kofar ya rufe. Suka Zazzauna a fakon kan kujerun dake downstairs. Upstairs ya haye sannan ya ajiye abincin a dinning table ya nufi ɗakinta. Kuka take yi har lokacin tana kuɗudune kan sallayar. Ba ta ji shigowarsa ba sai ƙamshin turarensa da ta ji ya ne ya sa ta tsaida kukan nata, ta ɗago kumburarrun idanunta ta kalle shi. Tana ɗan dafe kanta. "Tashi ki fito ƙannena suka zo kawo abinci Mama ta ce su gaida ke idan sun zo." Tashi ta fara yinƙurin yi tana cije lips din ta na ƙasa. "Ki shiga bathroom ki wanke fuska ba na bukatar sake ganin wannan hawayen." Bathroom ta shiga ta wanke fuska kamar yadda ya umarce ta. Bayan ta fito ne ya yi hana tana bin sa a baya suka fita. A tunaninta suna nan upstairs ne, ganin ya nufi downstairs ta na tafiya a hankali tana jine lips sakamakon ciwon kan da ya sa ta gaba. A hankali take tafiya tana sanye da hijabinta har ƙasa sai flat shoe dake ƙafarta. ",Zuba ma su idanu suka yi suna kallon su. Musamman Nadra da da duk wanda ya kalle ta ya san tasha kuka. Cike da ƙarfin hali take tafiya don har wani jiri take ji. Daf da za su sauka daga matattakalar kenan ta ji kanta na juyawa ta yi kamar za ta faɗi. Ganin haka ya saka ya yi saurin rike ta ya ga ta yi luu za ta yi baya. Cikin zafin nama ya taro ta ya ɗaga ta cak ya koma da ita sama ba tare da ya karasa da ita wajen su Rumaisa sun gaisa ba. Kallon kallo aka fara yi tsakanin Rumaisa da cousin sister ɗin ta guda biyu da suka zo tare. Ɗaya daga cikinsu ce ta saka dariya yana cewa. "To fa, Yaya Fahad ya ɓaro aiki kenan, to amma ba an ce baya son ta ba? To ya hakan ta faru?" Rumaisa ta kalle ta tare da cewa. "Me kenan ya faru?" "Ba ki ga alamar Yayanki ya sha romon amarci ba daren jiya, ki kalli yadda idanunta suka kumbura tsabar kuka, sannan tafiya ma ta kasa yi sai da ya ɗauke ta." Cike da tausaya wa Rumaisa ta ce. "Allah sarki." Ɗayar wacce ba ta yi magana ba ta ce. Ku ga fa da yake cewa baya son auren har jiya fa da ƙyar Mama ta saka shi gaba ya bar gida, da cewa ya yi ba zai zo nan gidan ba Sa sanya ga ɓacin ran Mama sannan ya zo ya tare, amma da ke namiji munafiki ne har ya iya azabtar da ƴar mutane ta kasa tafiyar don jaraba. Gabaɗaya suka saka dariya da shewa. Dadai lokacin ne suka ji ƙamshin turarensa suka juya suka kalle shi. "Ku tashi ku tafi kun zo kuna ma ni ihu a gida." Kamar suna jira kowacce ta mike suka nufi hanyar fita. Komawa ya yi sama ya shiga kitchen ya haɗa ma ta tea sannan ya nufi ɗakinta don kai ma ta, ya dawo ya zo dinning ya ɗauki basket ɗin da Mama ta aikio ma su da shi, sannan ya ɗauki plate a kitchen ya wanke da cokali sannan ya koma ɗakinta. Food flask ɗin ya bude ɗaya, farfesun kan rago ne, ya zuba ma ta. Sai ya bude wani ya ga wainar shinkafa ce sai miyar taushe daban. Tea ya miƙa ma ta. "Karɓi ki sha." Ba ta jin shan komai don haka ta ce. Ta girgiza ma sa kai ba tare da ta yi magana ba., "Ba na son sake maimaita magana ɗaya." Ya faɗa cikin tsare gida. Karɓa ta yi ta fara sha. "Na kawo ma ki bread?" Kai ta girgiza alamar a'a, sai ya miƙa ma ta farfesun. Da ƙyar ta iya cin guda uku ta ajiye. Bayan ya karbi kofin da plate ɗin ne ya fice da su, sannan ya dawo tare da magani a hannunsa. Ruwa ɗauka a cikin fridge dake nan cikin ɗakin. Ya ɓalli magani ya ba ta sannan ya zuba ruwa a glass cup ya ba ta ta sha. Jingina ta ji da kan filo da ke kan gadon, ba tare da ta kwanta ba. Fita ya yi daga cikin ɗakin bayan ya ɗauki basket ɗin abinci ya fita da shi ya ajiye a dinning table. Bedroom ɗin sa ya nufa ya ciro wayar Nadra da ta karɓa ya kunna yana dubawa. Ba ta amfani da social media sosai don what's up kawai ya ga tana yi, ya shiga ya duba shi ma daga ƴan uwanta sai ƙawarta da Ya Sayyadi ne suke yin chatting da shi. Ba ta da groups har wurin text message sai da ya duba. Nan ma ya ga ba wani abu ba rashin daidai da take yi. Ya tuna idan ya karbi wayar Sidra ita ce TikTok, Instagram, Facebook, twitter da sauran su, ga tarin groups kamar Hauka groups ɗin na na maza da mata ba wai iya mata zalla ba. Kuma bai ga group ɗin ƙaruwa ba ko na faɗakarwa sai irin su. Manyan mata, ƙasaitattun mata, mata ma su aji, ma su ji da kansu, wayayyun mata. Da sai sauran su. Amma nan wayar Nadra ya ga ba ma kullun take hawa what's up din ba, wa'azuzzuka na ma manyan malamai ne suka cika wayar video da Audio. Kashe wayar ya yi gabaɗaya ya bude side drawer ya saka ta a ciki. _Rumaisa_ Bayan direba ya ajiye su a gida ne suka fita duka su uku ne dama suka je gidan. Rumaisa, Rahina da Sahiba. Suna fita daga motar jikinsu na rawa suka shiga cikin falon. Nan suka ga gabaɗaya mutanen gidan suna falo har da ɓaƙi da suka zo daga wasu garuruwa. Dariya suka shiga suna yi gabaɗaya mutanen suka mayar da hankali suna kallon su. Inna wato kakar su Fahad ta kalle su ta ce . "Waɗan nan sabbin mahaukatan fa?" Sahiba ta yi saurin cewa "Wallahi ba hauka ba ne Yaya Fahad ko?" "Me ya yi Fahad ɗin?" Cewar Hajiya Jummai mahaifiyar Farida. Rahina ta ce. "Jiya nan ya dinga cewa baya son auren nan, har sai da aka kore shi daga gidan nan ya tafi wajan Amaryarsa. To ga Amarya can idanunta sun kumbura tsabar kuka tafiya ma ba ta iya yi sai ya ɗauke ta kinga yadda ta koma yake wani tarairayarta ko tafiya sai ya ɗauke ta Allah ya sa bai illata ta ba." Rahina ta yi maganar kasancewar bazawara ce ta yi aure shekara ɗaya auren ya mutu. Gabɗaya falon aka yi shiru Mama ko ta yi farin cikin jin haka yayin da bakin ciki ya kama Hajiya Jummai saboda tana taya ƴarta Farida kishi. Farida ko kasa haɗirye ƙincinta ta yi sai kawai ta tashi ta bar wajen tana kuka Dinning area ya nufa ya zauna ya ci waninar da Mama ta kawo ya sha farfesun kaɗan sannan ya tashi. Yana shiga bedroom ɗin sa ya ga wayarsa na ruri. Ya duba ya ga Mama ce. Ɗauka ya yi tare da yin sallama. "Assalamu alaikum." Daga xan bangaren ta amsa tare da cewa. "Ya kuke?" "Alhamdulillah." "Ya Nadra take ƙannenka sun ce ba ta da lafiya ko?" "Eh haka ne." "To ka kula da ita, ta zauna cikin ruwan zafi ba wanda zai kuma yi ma ta illa ba, sannan ka bar ta ta huta a ƙalla ko na sati ɗaya ne kar ka takura ma ta, don Allah ka bi ta a hankali, na tabbata da daren jiya ka bi ta a hankali da ba za ta jigata haka nan ba." Shiru ya yi bai iya cewa mahaifiyar tasa komai ba, don bai gane in da zancen ta ya dosa ba,kafin ya yi magana ya ji ta katse kiran wayar. Maganganun nata ne suka fara yi ma sa yawa a ƙwaƙwalwarsa. Me zai saka ta zauna a cikin ruwan zafi, kuma akan me zai ɗaga ma ta ƙafa na sati ɗaya. Mama tana magana ne kamar ya kusanci Nasra alhalin ba abinda ya shiga tsakaninsa da ita. To me ya saka ta ce haka. Ya san dai haka nan kawai Mama ba za ta ji zargin wani abu a tsakaninsu da Nadra ba. Tuna zuwa ƙannensa da suka yi kawo ma su breakfast ya sa shi tunanin akwai maganar da suka yi. Mai yiwuwa don sun ga alamar ta sha kuka ne, to me zai saka su faɗi abin da ba su da tabbas akan sa. Daga nan ya tashi ya shiga bedroom ɗin sa. Kayan jikinsa ya rage ya shiga wanka. Yana tsaye yana kallon kansa a madubi kamar yadda ya zame ma sa ɗabi'a. A da idan ya ga Tattoo dake jikinsa ya kalli sunan Sidra da butterfly yakan yi Murmushi. Amma yanzu ji yake yi da zai iya da ya goge sunan daga jikinsa. Ji yake yi kamar ya samu reza ya ya kankare fatar jikinsa. Wanka ya yi da shower gel din sa mai ƙamshi sannan ya ɗaura towel ya fito yana tsane ruwan kansa. Man shafawarsa ya shafa ya fesa body spray ya shiga closet ɗin sa. Shirya wa ya yi cikin ƙanan kaya farar Tshirt mai tsada da wando jeans, ya duba ɓangaren takalmominsa kambas masu tsada, saidesigner sneaker ya saka a ƙafarsa shi ma fari ya ɗaura tsadadden agogonsa Rolex GMT- master ll pepsi sannan ya fesa turarensa Bleu de Chanel (farfum) duk wanda ya gansa ya ga gentleman na gaske mai tsafta da kuma classy. Fitowa ya yi daga cikin closet ɗin ya ɗauki wayoyinsa da makullin motarsa ya fice cikin takunsa na ƙasaita. Har zai wuce sai ya tuna da ita ya koma ɗakinta _Maeesha_ Ganin makaho ya tsuke ne ya ba ta mamaki don ita a fahimtar ta ba ta san ta jmyi ta yi wani abu na rashin daidai ba. "Ka yi hakuri idan na faɗi wata magana da ba ta yi ma ka daɗi ba." Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce. "Ma'eesha mutane suna raina sana'ar nan da nake yi ba na jin daɗi, domin ni albarkarta nake nema. Amma yau ke da kanki kike raina sana'ar? "Ka yi hakuri ba yadda ka fahimta ba ne, ni so nake ka huta saboda ana rana, ina tausaya ma ka ne shi ya sa na ce kudin da kake samu bai fi ɗari biyar ba zan ba ka dubu ɗaya ka zauna ka huta a gida." "Ba na so ki rike kudin ki ni zan fita na nemi gumina da kaina. Ba son raina ba ne na zauna a ce kina ɗaukar nauyin da ya rataya a kaina, na san ba zan iya ɗaukar nauyin ki ba, amma ina son ɗaukar ko da kwatankwacin nauyin ki ba, zan kwatanta, domin ma wata rana zan yi alfahari da cewa na yi wa matata wani abun kuma ta karɓa ta yi amfani da shi. Ki yi hakuri idan kin ji ba daɗi kinji ƴar aljanna ." Murmushi ta yi tana cewa. "Allah ya buɗa ma ka hanyar samu mijina." "Amin matata." Tea ta haɗa ma sa ta bashi bread sai soyayyen dankalin turawa da ƙwai. Suna ci suna ɗan taɓa fira sama-sama. Kafin ya ce. "Yanzu Ma'eesha idan aka wayi gari kayan abincin da kuma siyo sun ƙare, musamman waɗan nan na ku na gayu da kika saba ci kuka ya kasace ba na da kuɗin siya ma ki irin su fa?" "Ba damuwa Allah ke ciyar wa ba mutum ba, duk abinda Allah ya hore ma ka ka kawo

Chapter 14 of 49