Share this page
yana godiya a gaishe ki da jiki." Ta yi maganar tana riko hannun mahaifiyarta, sai ta ji hannunta ya saki yaraf. Gabanta ya tsananta faɗuwa fargaban ya ƙaru. Ta kira sunanta sau uku shiru, don haka tana kokarin fita ta kira Inno kenan sai ga Inno ta shigo. Da sauri ta karasa bakin gadon tana kallon Mummy. Shafe ma ta idanun ta yi tana hawaye. Sannan ta kalli Ma'eesha dake kallon ta kamar wata sokuwa ta ce. "Sai dai mu yi hakuri Allah ya yi wa Mummy rasuwa ta riga mu gidan..." Tim ƙarar da ta ji ne ya saka ta juya da sauri, nan ta ga Ma'eesha kwance ta sume a wajen. Ihu ta saka wanda ya janyo hankalin Mamy dake zaune a falo. Kuma daidai lokacin ne Daddy ya shigo falon. Yana jin abun da Inno ke fada ya yi hanzarin nufar ɗakin . Wajen Mummy ya nufa ya duba ta sosai ya tabbatar rai ya yi halinsa ya sa shi lulluɓe ta har da fuskarta yana mai zubar da hawaye. Yana jin kamar ya dawo da hannun agogo baya da ya mayar ya canza wani abu. Ruwan sanyi ya ɗauka a cikin fridge dake cikin dakin, ya watsa wa Ma'eesha. Ba ta farfaɗo ba har da aka yi sau uku sannan ta farfaɗo tana matsanancin kuka. Faɗa wa ta yi jikin mahaifiyar tata tana kuka mai tsuma zuciya. Tana rungume da gawar tana surutai. "Mummy ta za ki tafi ki bar ni cikin wannan duniyar mai cike da tarin kalubale? Mummy ba zan iya ba, ke ce gatana, ban san ya zan yi ba. " Haka ta dinga ihu tana sambatu Inno na rarrshin ta. Mamy kam ko magana ba ta yi ba ta juyabta bar ɗakin. Daddy ya kira mutane ya sanar da su. Lokacin da Alhaji Shamsuddin ya ji labarin rasuwar Inno ya shiga tashin hankali sosai ba kadan ba. Yana tuna rayuwar da ta yi a gidan marayu da yadda take yi ma sa addu'a idan ya kawo ma su abu. Dole ya shirya ya bar ƙasar dak da cewar yana fushi da ɗan nasa Daddy. Domin gabadaya sauyawar da Daddy ya yi ya shafe su har da su ma. Domin ya daina kiran su a waya ko sun kira baya ɗaga wa. Ba don komai ba yake ma su haka sai don sun nun ba sa son auren nan fa ya yi musamman da bai sanar da su ba sai bayan bikin da yadda Ma'eesh ta ba su labarin yadda auren ya kasance, da kuma wace ce ita Mamyn da yaranta da zo da su. Dalilin haka ya saka Mamy ta ce wa Daddy ya hana Ma'eesha zuwa gidan kakannin nata tana week end. Duk yadda Daddy ke tsoron iyayensa yanzu ba ya yi sai tsoron Mamy da bin umarnin ta. Sai abun da ta ce yake yi. Ko da Hajiya ta yi ma da maganar Ma'eesha ta daina zuwa week end gidanta ya ce wai ta daina zuwa daga yau ya raba ta ya gidan ya kuma yi wa Ma'eesha gargadi sosai akan zuwa gidan kakannin nata har cewa ya yi bai yafe ma ta ba. Nan da nan labarin rasuwar Mummy ya karade unguwar. Ta yi jama'a sosai har daga wasu unguwannin da dama sun zo . Bayan an yi ma ta sutura za'a kai ta makwancinta anan Ma'eesha ta dake rike cewa har tana kokarin fita waje za ta bi su Sai da Inno ta rike ta. Daga nan ta sai ta liƙe wa Inno a jiki, don ko kakarta Hajiya Turai ba ta lyarda ta je kusa da ita ba, saboda Daddy ya yi ma ta iyaka da ita. Ta canza kamaar ba ita ba, gabadaya ta yi sanyi duk da cewa dama ita ba mai hayaniya ba ce. Har aka yi kwana bakwai ba ta wani iya cin abinci, Inno ke kokarin ba ta abinci ba ta ci sai dai ta sha ruwan tea idan ta matsa ma ta ma ne take sha. Kasancewar ba ta da dangin uwa na uban ma Mamy ta sa Daddy ya yi ma ta shamaki ita da danginsa. Ba ta taɓa jin ciwon rashin dangin uwa ba sai yanzu, da tana da su to ba shakka can za ta je ta nemo su. *Bayan sati ɗaya* Yau juma'a ya yi daidai da ranar da Mummy ta cika sati biyu da rasuwa. Gidan kamar ba gidan mutuwa ba, sai harkokin su suke yi, idan aka cire Ma'eeha da Inno. Don su ne ka kalle su har yanzu ka san suna cikin damuwa. Sai kuma Jamil babban yaron Mamy shi ma mutuwar ta shige su, amma iya su ne suka da mu sauran sai a hankali. Haka dai rayuwa take ta tafiya . *Bayan sati Uku.* _Makaho_ Tafiya yake yi rike da sandarsa ta jagora ya tsaya a ƙofar gidan su Ma'eesha. Maigadin baya nan don haka direba ne zaune a bakin gate ya ji ana ƙwanƙwasa kofar ya buɗe. Ganin makaho ne ya ce . "Mallam Khalifa kana lafiya?" Don haka ya ji Mummy da Ma'eesha na kiransa da Khalifa ba su ce ma sa makaho. "Ya amsa da lafiya lau ya ƙoƙari?" "Alhamdulillah." "Ma sha Allah." Ya haƙurin Hajiya kuma?" Cewar Makaho. Direba ya ce. "Haƙuri namu ne duka." Daidai lokacin mota ta yi horn sai Direban ya bar makaho ya tafi ya bude gate. Laila ce ta shigo da motar ta yi parking space. Idanunta ya sauka akan motar Ma'eesha dake gefe. "In sha Allah wata rana sai na raba ki da wannan motar ta zama mallakina. Wato saboda ke ƴarsa ce ya siya ma ki tsadaddiyar mota, amma ni kuma ya siya ma ni mai sauƙin kuɗi. Mu ba je zuwa komai ma sai na raba ki da shi ba iya motar ba." Fitowa ta yi tana yi wa Khalifa wani ƙasƙantaccen kallo ta ce. "Shi kuma wannan makahon me ya kawo gidan nan, bayan wacce ta ce ya dinga zuwa ta mutu sai dai idan kabari zai bi ta can ta bashi abincin da take ci." Muryarta kawai Khalifa ya ji ya gane ita ce ranar ta yi ma sa maganar mabarata. Kafin ya yi magana sai Direban ya ce. "Ina ganin wajan Hajiya Ma'eesha ya zo." Laila ta yi ɗan jim sannan ta ce. "Ma sha Allah." Daidai lokacin Mamy ta fito tana kallon su kafin ta ce. "Lafiya kika tsaya a nan?" "Wai ina ganin baƙon Ma'eesha ne." Sai a lokacin Mamy ta lura da Makaho, ta kalle shi sama da ƙasa. Wasu kuɗaɗun kaya ne a jikinsa ma su arha, dai hula taɓa ni ka ji hadisi da ya sanya a kai, sa hankali silifas a ƙafarsa. Wani tunani ya zo wa Mamy ta yi dariyar mugunta ta ce . "Wajen Ma'eesha ka zo ko?" "Eh na zo ne na yi ma ta ta'aziyya da bankwana don daga yau na gama zuwa gidan nan, tun da Hajiya Allah ya karbi abinsa Allah ya jikanta da rahama. Direba ne kawai ya amsa da Amin. Kallon Direban ta yi ta ce. A kai shi ɗakin baki, yanzu zan tura ma sa ita . Daga haka ya bar wajen Laila ta mara ma ta baya. Suna shiga falon ta damu Daddy ta ce . "Dama Alhaji akwai maganar da nake so mu yi ne." Ya ajiye wayarsa ya ce "Ina jin ki." "Ya kamata a tausaya wa yaron nan kullum sai zuwa zance yake yi, tun uwar na da rai har ta rasu , bayan rasuwar ma kullun yana zuwa ɗebe ma ta kewa yanzu haka ga shi can ɗakin baƙi." "To ai Ma'eesha ta fi karfinsa makaho ne fa." "Kamar ya ta fi karfinsa makaho ba mutum ba ne, ai idanunsa ne kawai ba sa aiki, amma idan aka aura ma sa ita an samu lada taimako ne ai za ta taimaka ma sa tunda ita mai kula da gida tana gani, kuma idan suka haifi yara ita ce mai kula da su ba shi ba." Shiru ya yi cikin rashin yarda da zancen, ganin haka ta ɓata rai cikin bayar da umarni ta ce. "Ina son daga yau juma'a gobe Asabar a ɗaura auren makahon nan da Ma'eesaha." Shiru ya yi tana tunani ta sake cewa. "Ko ba ka ji ba ne?" "Na ji shi ke nan duk yadda kika ce haka za'ayi." Laila dake tsaya tana jin su ta wuce ɗakinta cikin farin ciki. To ba damuwa ka je ka sanar da ski gobe ya nemi sadaki ya kawo a ɗaura ma su aure, idan bai da kudin a bashi sadaka kawai kowa ya huta. Don gobe ko ana ha maza ha mata sai an ɗaura wa yarinyar nan aure da makahon nan." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page1️⃣9️⃣ To ba damuwa ka ke ka sanar da shi gobe ya nemi Sadaki ya kawo a ɗauara ma su aure, idan bai da kuɗin a bashi sadaka kawai kowa ya huta. Don gobe ko ana ha maza ha mata sai an ɗaura wa yarinyar nan aure da makahon nan." Da mamaki Daddy ke kallon ta amma ya kasa yi ma ta musu. Don duk abinda take so ko ta furta sai ya tsinci kansa da bin Umarninta ko da ba ya son hakan, amma ba ya iya yi ma ta gardama. "Ka tashi mu ke ka same shi ya san da zancen." Tashi ya yi ba don ya so ba sai don zuciyarsa na azalzalarsa da ya bi umarninta. Ko da ta tura ƙofar falon baƙin ba ta yi sallama ta shiga, a tunaninsa Ma'eesha ce amma yanayin takun ƙafarta da kuma ƙamshin turaren ya ji ba irin na Ma'eesha ba ne. Muryar Daddy da ya yi sallama ya saka shi ya amsa da. "Wa'alaika Salam warahmatullah. Daddy Barka da rana." "Yauwa Barka dai." "Khalifa sunan ka ko?" "Eh Daddy." "Kana da mata ne?" Sai da ya ɗan yi jim yana mamakin dalilin tambayar kafin ya ce. "Ba na da mata Daddy." "Shi kenan faɗuwa ta zo daidai da zama." Cewar Mamy tana Murmushin mugunta. "Na ba ka auren Ma'eesha gobe ka nemo sadaki ka kawo za'a ɗaura ma ka aure da ita." "Sai da ya kike tsaye daga zaunen da yake, tsabar mamaki da al'ajabi." ",Daddy Ma'eesha ba sa'ar aurena ba ce, ta fi ƙarfina, ni fa makaho ne, faƙiri wanda ba shi da cin yau bare na gobe, ta ya zan iya ɗaukar ɗawainiyarta, bayan ina makaho ballantana a ce zan iya yin wani aikin da zan riƙe ta." Mamy ta yi saurin cewa. "Ba mutum ke yi ba Allah ke yi, baƙin da Allan ya tsaya baya hana ma sa abincin da zai ci. Kai dai ke nemi sadaki ka kawo ko nawa ne, idan ma ba ka samu ba ka zo za'a ba ka ita Sadaka." Tana gama fadar haka ta ce "Ko ba haka ba Alhaji, sannan a wannan masallacin za ka so kafin sallar azahar, don ana idar da sallar sai a ɗaura aure kawai." "To na gode Allah ya saka da alkhairi." "Mu je Alhajina." Cewar Mamy tana jan hannunsa ganin ya karaya kamar ba yadda zai yi ne. Suka fice suka bar shi cike da mamaki. Yana cikin wannan mamaki ne ya ji sallamar Ma'eesha cikin siriryar muryarta. "Assalamu alaikum." "Wa'alaiki Salam warahmatullah." "Sannu da zuwa ina wuni?" "Lafiya lau Alhamdulillah." Ya amsa yana tunanin abun da mahaifinta ya ce ma sa. Kafin ya buɗe baki ya ce. "Ya ƙarin haƙurin Mummy." "Alhamdulillah." "Allah ya jiƙanta da rahama ya sa Aljanna maɗaukakiya ce makomar ta. Sannu da imani kin ji Ma'eesha." "Amin na gode." Ta amsa tana goge ƙwalla. Muƙe wa tsaye ya yi yana cewa. "Dama na zo ne na yi ma ki ta'aziya tare da sallamar bankwana, don ba zan sake zuwa gidan nan ba, dan wacce ta kawo ni nake zuwa yanzu babu ita a doron duniya. To me zai da na ci gaba da zuwa, sai dai kuma yanzu Daddy ne ya zo da wani al'amari mai girma." "Wane Daddy ya zo da al'amari mai girma?" Ji ya yi ba zai iya fada ma ta ba, don haka sai ya ce. "Cewa ya yi na zo gobe." "Ma sha Allah, to sai ka ci gaba da zuwa ai tun da ya baka dama. Bari na je na kawo ma ka abinci." "Ba na jin zan iya cin abinci yanzu." "Okay bari na kawo ma ka snacks da lemu ka tafi da su ." Tana gama faɗar haka ta fice, bai tsaya jiran ta ba shi ma ya fice, don ya shiga damuwa sosai. Ko da ya dawo ta yi mamakin rashin ganinsa, ta tambayi maigadi ya ce ya ga ya fice. Komawa ciki ta yi ta tarar da Daddy zaune shi kaɗai. Bayan ta yi masa sallama ta ce tana son gobe ta je saloon, kai ya jinjina ma ta kawai ya kasa magana . _Makaho_ Yana barin gidan su Ma'eesha ya nufi unguwar da yake , kasancewar masallaci yake kwana dama. Bayan an idar da sallar la'asar ya keɓe shi da limamin masallacin ya sanar da shi abun da Daddy da Mamy suka ce na ba shi auren Ma'eesha. Mallam Liman ya yi mamaki sosai ba kaɗan ba, kasancewar ya san cewa Ma'eesha ita ce ƴa ɗaya tilo da Alhajin ya mallaka, to wane dalili zai sa ya aurar da ita ga makaho talaka. Ya san cewa za ta sha wuya sosai ba kadan ba, ya kuma san wannan ba an yi ba ne dan farin cikin yarinyar sai dai bakin cikinta. "To yanzu na ga a masallaci kake kwana, to kana da ɗakin da za ka ajiye ta ne?" "Ba na da shi ." Ya fada cike da damuwa. "To akwai wani gidan haya nawa da nake da shi, akwai wani ɗaki guda ɗaya can ƙarshen cikin gidan. To zan ba ka ka zauna da ita a ciki sai dai ba'a shafa siminti ba, zan saka a yi wata dabara da za ku zauna cikin rufin asiri." "To na gode Allah ya ƙara arziki." "Amin ya Allah, kana da kudin sadaki?" "Sun ce wai na je ko nawa ne na kawo, idan ba na da shi ko sadaka za su bani, don haka zan duba ƴan kudin da nake turawa ko nawa ne zan bayar." Addu'a da fatan alkhairi Mallam Liman ya yi ma sa Sannan makaho ya sa nemi alfarma yi ma sa wakilci ya karba ma sa auren Ma'eesha ya amsa ma sa . A yammacin ranar Mallam Liman ya tura iyalinsa ta je ita da maƙociyarsu suka je da buhun siminti aka shimfiɗa suka yi ƴan dabaru sannan suka ja kofar suka tafi. A daren ne Mallam Liman ya kai Makaho gidan nasa har ɗakin da za'a saka Ma'eesha ya raka shi. Godiya sosai ya yi masa suka fito a tare. Washegari aka ɗaura auren Khalifa da Ma'eesha akan sadaki Naira dubu uku da Khalifa ya bayar. Ɗaurin auren da ya ba wa jama'a mamaki da al'ajabi, kamar Alhaji Ibrahim Khalil ne zai aurar da ƴar sa ɗaya tilo ga wani makaho kuma faƙiri. Ya koma cikin gidan cikin sanyin jiki ya ke sanar wa da Mamy kuma komai, wanda duk maganar da yake yi na auren a kunnen Inno. Wacce ta kaɗu da jin zancen, ta shiga kitchen tana goge hawayenn tausayin Ma'eesha. Wayarta ta fara tunanin ɗauka ta kira Ma'eesha ta sanar da ita kada ta dawo ta gudu. *Cigaban labari* Ƙarfe huɗu na asuba Ma'eesha ta farka daga barci da take yi. Sautin muryarsa mai amo ta ji ta ji yana karatun Alkur'ani mai girma. Yana zaune saman sallaya da alama sallama sallah ya idar. Sauraron muryarsa take yi yadda yake ba wa kowane harafi hakkinsa, yana karanta suratul Yasin. Lumshe idanunta ta yi tana jin wani sanyi da nutsuwa na ratsa ta. Ya idar ya kama wata surar. Har sai da aka kira sallar assalatu ya juya bangaren da Ma'eesha ke kwance kamar wanda idanunsa suke gani. Ita kuma sai ta yi saurin lumshe idanunta kamar mai yin barci da gaske, ko ta mance makaho ne baya gani oho. Tashi ya yi ya karasa bakin katifar bayan ya yi lalube. Da ya ji ya taɓa pilow ne ya bubbuga pillow ɗin a hankali. Dama ba barci take yi ba hasalima ta buɗe ifsnunta da ta ji takun tafiyarsa. "Ma'eesha." "Na' am." "Ki tashi ki yi alwala ki yi sallah lokaci ya yi ." "To zan tashi." "Allah ya baki iko." Ya fada yana laluben Sandar jagoransa. Bayan ya taɓa ta ne ya saka ya ce. "Ni zan tafi masallaci." "A dawo lafiya." Tashi ta yi tana jin alamar cizon sauro a jikinta. "In sha Allah gobe ba zan manta ba zan siye maganin sauro in sha Allah. Ko ma na nemi zanin sauro." _Nadra_ Ta kasa haɗa idanunta da nasa saboda wani irin kwarjinin da yake yi ma ta. Sai ta ya kamar za ta kalle shi sai ya kasa saboda kaifin idanunsa gare ta. Kallon ta ya yi ba yabo ba fallasa ya ce. "Ki shanye shi duka, ki ba ni kofin." "Gabaɗaya tea din jinsa take kamar tana shan magani. Bakinta ba daɗi don jin zazzaɓi take yi ma a jikinta, ga kanta dake bala'in sara ma ta, kuma baya rasa nasaba da kukan da ta sha. Hawayenta ya gani yana sauka a hannunta da take rike da tea. "Wai ke kuka baya yi ma ki wuya ne, yanzu me na yi ma ki daga ba ki abinci shi ne za ki dinga yi ma ni kuka?" Kai ta girgiza ma sa alamar a'a. "To me aka yi ma ki na kuka ne haka?" Shiru ba ta ce komai ba. "Saboda an aurar da ba ke ba ga wancan ustazun ba ko?" Shiru ta yi ma sa ko motsin kirki ta kasa yi tana dai rike da kofin a hannunta. "To idan ma don ba'a ba ki wanda kike so ba ne ya saka kike kuka to ai ba ke kadai ke da kuka ba, ni ma da kukan zan zauna na yi ta yi, saboda masoyiyata Sidra da nake so ta gudu aka aura ma ni ke kin ga ni na sai na zauna mu yi kukan tare ko?" Sai a lokacin ta ɗaga kai ta kalle shi, ta ga ya zuba ma ta rikitatun idanunsa yana kallon ta. Kafin ya ci gaba da cewa . "Ban taɓa kawo wannan ranar a tarihin rayuwata ba." Cikin kuka ta ce . "Yaya Fahad." "Na'am." Ya amsa yana kallon ruwan tea dake hannunta, don kazar ma ta ce ba za ta iya ci ba. "Ina neman wata alfarma a wajen ka." "Ina jin ki?" "Na san kuna son juna kai da Aunty Sidra, kuma ban san dalilin da ya sa ta tafi ranar aurenku ba, amma na san tabbas za ta dawo. Kuma soyayyar da take yi ma ka ba za ta iya cire shi daga cikin zuvuyarta ba. Ina son duk ranar da ta dawo matukar ta nuna tana son zama da kai to ka sauwaƙe ma ni sai ka aure ta, ni ma na je na auri Ya Sayyadina." Shiru ya yi yana kallon ta kafin ya ce. "Na ji alfarma da kika nema, zan yi ma ki ɗayaba cikin biyu. Ma'ana zan sake ki sai ki je ki auri Ya Sayyadi da kike so, amma ban ma ki alƙawarin Auren Sidra ba." Za ta yi wata magana kenan ya ɗaga ma ta hannu. Dole ta yi shiru. Ba tare da ya kalle ta ba ya ce. "Gud night." Ya fita daga cikin ɗakin bayan ya rage hasken ɗakin ya ja ma ta kofar ɗakin ya rufe. Ajiye kofin shayin ta yi ta fashe da kuka mai cike da ƙunci. "Ta ya zan iya za zaman gidan nan da aka gina da sunan Yayata, na yi amfani da kayan ɗakin da ka ajiye da sunanta, sannan na yi amfani da kayan lefenta sannan na mallaki masoyinta da tafi kauna fiye da komai a rayuwar ta, yau a ce shi ne mijina anya za ta fahimce ni kuwa da wani ido zan kalle ta ?" *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page2️⃣0️⃣ Ta ya zan iya zaman gidan nan da aka gina da sunan Yayata,na yi amfani da kayan ɗakin da aka ajiye da sunanta, sannan na yi amfani da kayan lefenta, sannan na mallaki masoyinta da ta fi ƙauna fiye da komai a rayuwar ta, yau a ce shi ne mijina za ta fahimce ni kuwa da wani ido zan kalle ta. _Fahad_ Yana komawa part ɗin sa kai tsaye ya nufi bedroom, bai tsaya ko ina ba sai bathroom. Don shi baya gajiya da yin wanka. Kayan jikinsa ya cire ya tsaya jikin babban madubin dake cikin bathroom ɗin, ffaɗan ƙirjinsa ya zuba wa idanu yana kallon zanen Tattoo da ya sa aka yi ma sa , daga gefen ƙirjinsa har zuwa damtsen hannunsa. An yi ma sa zanen butterfly da kuma sunan sa haɗe da na Sidra. Wani ɗaci ya ji a ƙasar ransa ji yake yi ina ma a ce zai iya goge wannan zanen Tattoo dake jikinsa da ya goge ko ya daina ganin sunan Sidra a jikinsa. Wanka ya yi don shi akwai shi da yawan wanka sosai. Almost 30 minutes ya ɗauka yana sakawar wa kansa ruwa kafin ya yi wanka da shower gel din sa mai ƙamshi. Towel ya ɗaura a ƙugunsa dai wani ƙarami da yake tsane ruwan kansa da shi. Gaban dressing mirror dake cikin bedroom dinsa ya tsaya. Yana kallon kansa a jikin madubin, da alama shi mutum ne mai yawan don kallon kansa a madubi. Body spray ɗin sa ya shafa sannan ya shiga cikin closet ɗin sa. Bai sanya wasu kaya ba sai wando three-quarter fari da ya saka, ya zo ya hau saman tangamemen gadonsa ya haye daidai lokacin da wayarsa ta soma ruri. Dubawa ya yi still number wayar ɗazu ce, kamar ba zai ɗaga ba sai kuma dai kuma ya ɗaga har lokacin bai yi magana ba. Jin shiru ya saka ya kashe wayar gabaɗaya ya kwanta. _Sidrah_ Gabaɗaya daren ranar ba ta yi barci ba sai kuka da ta kwana tana yi. Ta yi danaasanin tafiya ya bar aurenta, ga shi yanzu ta yi biyu babu, ba ta ga tsunsu ba ta ga tarko. Ita ba ga samun abinda ta fito nema ba don yin suna da ɗaukakar da take so ta yi. Sannan auren da ta tsallake ta baro da niyyar idan ta koma ta ba iyayenta haƙuri su haƙura da sake saka ranar ɗaurin auren sai ga shi an maye gurbin ta da ƙanwarta. Ko da a mafarki yadda ta san Fahad wayayyen mutum ɗan gaye ji da kansa ba zai taɓa amincewa ya karbi Nadra ba, amma abun mamakin sau ta ga ya amince da ita yarinyar da yake cewa kamar ba ta waye ba shi ne ya amince ya aura. Har yana iya keɓe wa da ita kenan a wanann daren, wa ya san me suka yi? Wannan tunane-tunanen ne ya hana ta barci yake saka ta zubar da hawaye. Fatan ta gari ya waye ta ɗauki hanyar komawa gida. Ta roki iyayenta kuma dole Nadra ta bar ma ta Fahad Majidaɗi. _Nadra_ Bayan fitar Fahad daga ɗakin ta dinga riskar kuka kamar ranta zai fita. Don har sai da ta ji kanta na sara ma ta kamar zai fashe sannan ta yi shiru, don idanunta ko gani ma ba ta yi saboda tsabar kumburin da suka yi ma ta. A haka ta ƙudundune waje guda da misalin karfe ukun dare ne barci ya yi nasarar ɗaukarta. Da misalin karfe biyar na asuba wayarta ta fara ƙara kamar yadda ta saita ta. A hankali ta motsa tare da kokarin bude kumburarrun idanunta da suka yi ma ta nauyi sosai. Addu'ar tashi daga barci. Ta tashi zaune tana dafe kanta da hannayenta biyu, dan ciwon kan nata sosai ya ƙaru. Saukowa ta yi daga saman gadon tana rike da kanta ta nufi bathroom ɗin dake cikin ɗakin. Tana shiga ta ji jikinta na rawa sanyi take ji sosai. Tana kakkarwa ta tashi daga duƙen da take, ta lallaɓa ta yi wanka da ruwan zafi sannan ta sake amfani da ruwan ɗumi ta gabatar da alwala ta fito ɗaure ta towel. Da kyar take yin tafiya har ta karasa cikin closet. Komai na kayan sabo ne a ciki. Tun daga kan kayan lefe har da kayan da aka ɗinka wa Sidra wanda iyayen su suka ɗinka ma ta, sai waɗan da Fahad ya kawo ma ta ya ce sun burge shi ne. Cikin kayan da aka kawo ma ta daga gida ta duba bayan ta saka underwears sai sai sun matse ta kasancewar ta fi Sidra

Chapter 13 of 49