Share this page
damuwa sosai daga jin kuɗinta sun ƙare ta ce. "Komai ya yi zafi maganinsa Allah, a cikin tafiyar rayuwa babu wanda ba ya fuskantar ƙalubale. Wani lokacin abubuwa sukan yi zafi har mutum ya ji kamar ya kasa, ko kuma ya fitar da rai, talauci, rashin aikin yi, bacin rai, ko rashin lafiya na iya sanya zuciya ta yi nauyi, amma babban sirrin samun natsuwa shi ne haƙuri. Komai yayi zafi maganinsa Allah hakuri ba yana nufin gazawa bane, yana nufin jiran lokacin da Allah ya sanya maka ne cikin natsuwa da yaƙini.Ka tuna dukkan waɗanda suka yi nasara a rayuwa sun sha wahala kafin su sha daɗi, Wahalar yau ita ce labarin gobe. Watarana idan ka waiwaya baya, za ka yi murmushi ka ce Alhamdulillah, domin duk waccan wahalar ta zama tarihi. Kada ka bari halin da kake ciki yau ya sa ka manta alkawarin Allah ci gaba da hakuri, ci gaba da addu'a, kuma ci gaba da aiki tukuru, Allah ya sa mu wanye lafiya, ya kuma canza mana kuncinmu zuwa farin ciki." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page3️⃣0️⃣ "Komai ya yi zafi maganinsa Allah, a cikin tafiyar rayuwa, babu wanda ba ya fuskantar kalubale. Wani lokacin abubuwa sukan yi zafi har mutum ya ji kamar ya kasa, ko kuma ya fitar da rai, talauci, rashin aikin yi, ɓacin rai, ko rashin lafiya na iya sanya zuciya ta yi nauyi. Amma babban sirrin samun natsuwa shi ne hakuri, Komai yayi zafi maganinsa Allah haƙuri ba yana nufin gazawa ba ne, yana nufin jiran lokacin da Allah ya sanya maka ne cikin natsuwa da yaƙini.Ka tuna dukkan wadanda suka yi nasara a rayuwa sun sha wahala kafin su sha daɗi wahalar yau ita ce labarin gobe. watarana idan ka waiwaya baya, za ka yi murmushi ka ce Alhamdulillah, domin duk waccan wahalar ta zama tarihi, kada ka bari halin da kake ciki yau ya sa ka manta alkawarin Allah. Ci gaba da hakuri, ci gaba da addu'a, kuma ci gaba da aiki tukuru. Allah ya sa mu wanye lafiya, ya kuma canza mana kuncinmu zuwa farin ciki." Cike da burgewa yake sakin murmushi saboda kalaman ta na hikima da burge wa, wanda ke sanya da cikin shauƙi a duk lokacin da ya ji fararen zantukanta ma su daɗin saurare, yakan tsinci kansa cikin farin ciki. "Bismillah ka ci kada ya yi sanyi." "Ke kuka fa?" "Kada ka damu na riga na ci nawa naka ya rage." Shiru ya yi kamar mai yin wani nazari kafin ya ce. "Ina son yau na lallɓa na fita na san ko ba yawa dai zan ɗan samu. Akwai wasu canji a aljihun wata rigata ina ganin za su iya kai ɗari uku ki riƙe su duk da na san ba waya amma ba za ki rasa abun siye ba. Tun da ni ba na siyan komai ballanta na yi amfani da kuɗin." "Jinjina kai ta yi tare da cewa "To Allah ya sa ma su albarka." Da Amin ya amsa sannan Don haka iya guda uku ya ci ya ce ya ƙoshi, ta ce za ta rufe ma sa zuwa Anjima ya ce A'a. Ya ishe shi. Dole ta bar shi ita sai ta cinye sauran . Cewa ya yi zai zo ya shirya ya fita, ita ce ta hana shi ta ce sai ya gama warware wa bai kamata ya fita a haka ba. Ta ce masallaci kawai za ta iya barinsa ya tafi. _Farida_ Matsawa ta yi dab da Nadra tana kallon ta cikin idanu bayan ta gama ƙarewa ɗakin kallo. Wanda kallo ɗaya za ka yi ma sa ka san cewa iyayenta ma sun yi bajinta sun siya ma ta kaya ma su tsada kama daga furniture har komaib dake cikin ɗakin . Taɓe ba ki ta yi kafin ta ce. "Amarya ta ango." Nadra dai ba ta tanka ta ba, don tun da ta lura da mugun kallon da Farida ke ma ta ne ta gane ba arziki ya kawo ta ba. Idanun Farida ya sauka akan sabuwar wayar Nadra da Fahad ya siya ma ta. Zare idanu waje ta yi tana mamaki kafin ta ce. "Au har matsayinki ya kai ya siya ma ki wayar Samsung Galaxy S23 ultra wayar da kuɗin ta ya kai miliyan ɗaya da dubu dari biyu ko fi ma?" Baƙin ciki takaici ya ishe ta, wayar ta ɗauka tana dubawa, irin wannan wayar ita ce take mafarkin mallaka a yanzu. Burinta da samu wayar, sai dai ta yi mamaki yadda take tunanin Fahad ba haka ba, a baya da ta ji sanyi a ranta lokacin da ta ji an ce ba da ɗin ransa aka yi ma sa auren ba baya son yarinyar. Sai dai hankalinta ya tashi ne da su Rumaisa suka faɗa cewa Fahad ya yi karɓi budurcin Nadra har ta kasa tafiyar Sa bya ɗauke ta. A wannan lokacin ta ji guiwarta ya yi sanyi. Ta ji ta sare sai kuma yanzu da ta ga wayar nan da ya siyo ma ta . "Nadra kike ko wace ce oho dai, bari na ba ko wani labari. Ni sunana Farida kuma ni ƴa ce a wajan ƙanwar mahaifiyar Fahad. Kuma soyayya muke yi da shi, ke a taƙaice dai sabada mu yi kusanci da juna me ya je ya ɗauko ni daga wajan iyayena ya kawo ni gidansu don mu shaƙu da juna soyayyar mu ta yi karfi kuma..." Kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon tura ƙofar da aka yi aka shigo. Kallon su ya yi ɗaya bayan ɗaya kafin ya ce. "Lafiya kuwa?" Murmushi Farida ta yi ta ce. "Lafiya lau ina gabatar ma ta da kaina ne." "Why not ki bari ku tafi can gaban kowa sai ku yi gabatar wa an bar su zaune suna jira." Nadra dai ko kallonsa ba ta yi ba ta mike tsaye ta nufi hanyar fita sanye da hijabinta har ƙasa wanda suka dawo da shi daga yin register na sim card. Da sauri ya rike hannunta wanda sai da ta ji faɗuwar gaba. Kallon su Farida ta yi wacce ta ji kamar ya soka ma ta mashi ne a ƙahon zuciya. "Farida ki je muna zuwa." Kamar ta yi ta kurma ihu haka take ji, q fusace ta fita. Kallon Nadra ya yi ya ce. "Ke wai ba na faɗa ma mi kada ki sake sanya hijabin nan ba. Da muka dawo ne ban cire ba." Kai tsaye ya ce. "Cire Hijabin nan." Ba musu ta cire, doguwar riga ce a jikinta na atamafa ɗinkin ya zauna ma ta cif a jikinta, atamfar irin me aikin nan a jiki ce kuma ta ji Stone work. Sun ɗan kama ta amma na sosai ba, kallonta ya fara yi wanda cikar halittar ta ke ba shi mamaki a iya shekarunta. "Haka zan fita? Ban saba ba fa." "Daga yanzu dole ki saba." Mintuna biyu ba ba ki kada ki bari na dawo na tarar da ke a cikin ɗakin nan ba tare da kin fito ba." Yana gama fadar haka ya fita daga cikin ɗakin. Tana nan tsaye ta ga lokacin da ya ba ta ya kusa cika, kuma ya hana ta saka hijabi ba t da wani zaɓi dole ta fito Suna nan zaune suna fira suna yaba kyawun gidan Fahad, shi kuma idanunsa na kan ƙafa yana jiran ta fito kafin su yi ƙorafi. Ƙarar ƙofar ya sa suka juya suka kalle ta. "Ma sha Allah." Wasu daga cikin su suka faɗa. Don tabbas Nadra ba ta da makudan tana da kyau da kuma diri mai ƙyau sai dai a ce ma ta baƙa ce ita. Kanta a ƙasa cikin natsuwa da kunya take takun ta. Shi kansa ya kasa ɗaukeidanunsa daga kanta, domin shi kansa idan ya ganta ba hijabi sai ya yi ta kallonta saboda surar jikinta mai ɗaukar hankali ne. Durƙusa wa ta yi ƙasa ta fara gaiahe su suna amsawa. Ƴan matan da su Rumaisa suka gaiahe ta a matsayin ta na matar Yaya. Kitchen ta nufa ta buɗe fridge ta ɗebo bottle water da lemukan roba sai da ta ciki tire sannan ta kai ma su ta ajiye ma su. Sannan ta kawo ma su cincin da dubulan da Alkaki ya yawa . Kitchen ta koma tana tunanin me za ta sarrafa ma su mai sauki ne. Ta duba kitchen ɗin duka akwai komai na buƙata. Sanin spaghetti ya fi sauki ya sa ta fara ƙokarin girka ma su. Nam da nan kuwa ta fara ma su girki ɗin . Ƙamshin turarensa ya da ta juya bayan ta blending na kayan miya. "Me za ki yi anan?" "Girki zan yi ma su." "Ba bukatar sai kin yi ma su girki don a yadda kiken nan da ƙauyanci ba wani girkin da kika iya, ki zo ki kawo ma su kwamacalar da za ki saka a yi ta magana akai. Idan sun tafi ki girka iya cikinki ke kaɗai." Maganar ta yi ma ta zafi amma sai ta yi Murmushi ta ci gaba da aikinta. Ƙamshi har cikin falon wata daga cikin matan na cewa "Sai mun ci girkin amarya kafin mu tafi. Shi dai Fahad na mamakin taurin kai irin na Nadra yake yi, wato ba ta daina ba ta ci gama da yi kenan. Cikin ƙanƙanin lokaci ta dafa ma su jallop ɗin spaghetti da ya ji kayan lambu da bisashen kifi. Sai Pepe chiken don kan gas biyu ta yi amfani da su. Babban food flask ta zuba ciki ta kawo ma su . Sannan ya kawo ma su Pepe chiken. Ta ƙara kawo ma su ruwan sanyi da lemu, sai plates da forks ta kawo ma su suna ta yi ma ta godiya . Miumushi ta yi tana cewa. "Ba komai, ku yi hakuri don ban san da zuwan na ku da wuri ba." Rumaisa ce ta dinga zuba ma su taliyar da pepe chicken ɗin . Don ganin suna da yawa ya saka Nadra ba ta kai ma su dinning table ba. An zuba wa kowa Rumaisa ta kalli Fahad ta ce. "Yaya daga yanzu in dai Aunty Nadra na wuri Sai dai ta za ta zuba ma ka abinci." "Am okay." Ya faɗa ya tashi ya koma can gefe kan sofa yana danne-danne a wayarsa. Shi a ganinsa ba ta iya girki ba kwamacala ce kawai . Sai ya ji kowa na santin abincin. "Aunty Ashe haka kika iya girki mai daɗi?" Murmushi kawai ta yi don ba sabon abu ba ne don a yaba girkinta. Don ko gida duk ranar da ta yi girki sai an fi ɗokin cin girkin nata fiye da na Sidra. Farida ce kawai ba ta ci abincin ba ta koma gefe tana danne-danne a wayar ta. Bayan sun kammala Rumaisa da sauran ƴan matan suka gyara wajan suka yi wanke-wanke. Har lokacin Fahad bai ci komai ba, don ko breakfast na safe bai yi ba. Sai karfe shida suka bar gidan. Nadra ta ba ƴan matan turarurruka iyayen kuma ta ba su dubu hamsin 50k cikin kudin sadakinta da aka ba ta. Bayan fitar su Fahad ma ya bar gidan, ba shi ya dawo ba sai karfe goma na dare. Yunwa duk ta addabe shi, don ba wani abun da ke cikinsa in ban da biscuits da lemu. Ɗakinsa ya nufa kai tsaye, a gajiye ya rage kayan jikinsa ya shiga bathroom. Wanka ya yi ya fito sanye da rigar wanka. Bayan ya shafa turarrukansa ne ya sanya wando three-quarter Blue da farar singileti. Ji ya yi ba zai iya kwana bai ci abinci ba, ga shi ko da ya je gidan Mama daddare nan ya ce a kawo ma sa abinci cewa ta yi ya je matarsa ta ba shi. Shi kuma baya iya cin abincin restaurant daga na mahaifiyarsa sai sai kuma ya yi ta fama da kayan snacks. Bai da zabi dole ya nufi part ɗin Nadra don yunwar yake ji sosai. Da sallama ya shiga ɗakin nata, tana zaune kan sallaya sanye da hijabi tana karatun Alkur'ani. Karfe goma da mintuna arba'in lokacin, tana karanta suratul Maryam. Zama ya yi bakin gadon nata har ta kai karshen surar. Don dama ta kusan idar wa. Juyo wa ta yi ta kalle shi yana zaune abakin gadon. "Sannu da dawowa." Kai kawai ya jinjina ba tare da ya amsa ma ta ba. "Please ki nema mani abun da zan ci yinwa nake ji." "To me kake so na girka ma ka?" "Komai mai sauƙi dai da ba zai ɗauki lokaci ba." "Na dafa ma ka indomie ne don ya fi sauƙi." Bai tanka ma ta ba, tashi ta yi ta je ta ajiye Alqur'ani ba tare da ta cire hijabinta ba ta fita zuwa kitchen. Don ita ta saba da saka hijabinta mancewa ma take da wai ya hana ta. Daga nan zaune da yake ya ɗan kishingiɗa ya kwanta kan gadon, ƙafarsa na ƙasa yaba kallon saman ɗakin. Lumshe idanunsa ya yi cike da gajiya nan da nan barci ya ɗauke shi a nan saman gadonta. _Maeesha_ Da misalin karfe goma na dare ta gama shirin kwanciyarta. Tana sanye da rigar barci iya guiwarta.Makaho kuma ya fito daga wanka kenan. Hannunsa rike da sandarsa ɗayan hannunsa kuma rike da kayan da ya cire, ya saka jallabiya. Da alama a cikin banɗakin ya sauya kayan jikinsa. Da sallama ya shigo Cikin ɗakin. "Assalamu alaikum" "Wa'alaika Salam." Ta amsa tana mai zuba ma sa idanun kasancewar akwai hasken wutar lantarki nepa sun bar ma su wuta. Zama ta yi a saman katifar tana kallonsa "Akwai abun da kake bukata me yanzu?" Ta tambaye shi sakamakon barci da ke idanunta tana son ta kwanta. "Ba na buƙatar komai, Allah ya yi ma ko albarka." "Amin ya Allah." "Ka zo ka kwanta saman katifar." "Ke ina za ki kwanta idan na kwanta saman katifa?" "Zan kwana ni ma a katifar mu kwanta tare ai ba wani abu ba ne matarka ce ni fa ta sunnah to mene ne don nun kwanta a wajen ɗaya, na tausaya ma ka ne fa saboda ganin ba dadin kwanciya ƙasan kake ji ba, sannan kuma ba isasshen lafiya ce da kai ba. Idan na ce na bar ma ka katifar ni ma ba zan iya kwanciyar a ƙasa ba jikina ciwo zai yi, ka sani ba wai sai an sanar da kai ba ma'aurata muke to me ye dalilin ka da ba ka son ka raɓi jikina, ba wai ina son wani abu ya shiga tsakanina da kai ba ne don Mun kwana a shimfida ɗaya amma na duba dacewar hakan ne sakamakon ba mu da wajen kwana sai wannan kayifar don ko bargo ma da za ka ji taushi babu. Amma sai gudun haka kake yi, na saka ka ka kwana tare da ni ranar da ba ka da lafiya bayan na yi barci ka zame jikinka ka sauka ka bar ni me hakan ke nufi? Ba akan daidai nake ba kai ne kake kan daidai?" _Sidra_ Da misalin karfe takwas na dare motar da ta kawo ta ta faka a ƙofar gidan Mahaifinta. Sakamakon motar ta k lalace a hanya ya saka suka yi dare. Sallama ta yi wa mai motar yayin da ya fito ma ta da trolly ɗin ta tana jansa ta nufi bakin gate ɗin. Knocking take yi kafin maigadi ya ce . "Waye a wajen." Ba ta tanka ba har ya taso ya bude. Ganin ita ce ya sa ya bude baki cikin mamaki ya ce. "Hajiya Sidra Kece daga ina?" Ba ta duba darajar farin gemu da ya haife ta ba ta ce. "Daga gidanku." Baki ya sake yana kallonta don bai yi mamaki ba kadan ne daga rashin mutuncinta, Don har marinsa ta taɓa yi. *Mamman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page3️⃣1️⃣ Baki sake yake kallon ta don bai yi mamaki ba, kadan ne daga rashin mutuncinta, don har marinsa ta taɓa yi. Da idanu yake kallonta har ta ɓace wa ganinsa. A hankali ya fara tuna wata rana ta dawo daga unguwa tana danna horn ɗin mota tana jiran ya bude ma ta gate. Shi kuma ya zagaya banɗaki sai da ya gama uzirinsa ya fito da hanzari ya wangale ma ta gate ɗin gidan. A guje ta shigo da motar kamar za ta bi ta kan Baba maigadi da motar. Ita ce ke driving sai Nadra dake zaune wajen me zaman banza. A fusace Sidra ta fito daga cikin motar ko kashe motar ba ta yi ba, Nadra ce ta kashe motar ta zare key. Baba maigadin yana kallon Sidra ta nufo shi a fusace sai da ya tsorata. Cikin kwantar da murya ya ce. "Ki yi hakuri Hajiya ina banɗaki ne lokacin..." Kafin ya kai karshen zancen ta ɗauke shi da mari wanda sai da ya yi baya kamar zai fadi. Tsoro da firgici ne ya bayyana akan fuskar Nadra. Idanunta cike da ƙwallar tausayin tsohon ta ce. "Baba don Allah ka yi haƙuri na san ba ta kyauta ba ɓacin rai ne, ba ta iya sarrafa fushinta ne." Ta yi maganar tana ɗauko ma sa hularsa da ta fadi ƙasa.Kallon Nadra ya yi tare da cewa. "Allah ya yi ma ki albarka." Da Amin ta amsa sannan ta sake ba shi hakuri ta nufi cikin gidan wanda Sidra ta riga ta shiga. A falon ta tarar da Sidra ita kaɗai sai huci take yi. "Aunty Sidra sam ba ki kyauta ba, ta ya ya za ki dubi wannan dattijo da ya haife ki za ki iya ɗaga hannu ki mare shi?" "Na mare shi akan me zai bar ni cikin mota ina jiransa? Ba aiki yake yi ba albashi ake biyansa ?" "Amma wannan ba shi zai ba ki lasisin da za ki taka wanda yake ƙarƙashinki ba, domin ɗan Adam daraja ne da shi kuma..." "Shut up!" Ta sakawa Sidra tsawa tare da cewa. "Ki fita a sabga ta idan ba haka ba wallahi yanzu zan ma ki marin da ya fi wanda na masa." Tana fadar haka ta nufi ɗakinsu ita kuma Nadra ta nufi part ɗin Ummansu. Sauran ma'aikatan gidan da suke gefe suna kallon yadda Sidra ta faɗawa Baba maigadi magana su ma suka shiga taitayinsu don na Baba mai gadi ma sauki ne. "Ita kuma wanan daga ina kamar wata korarriya ta dawo a wanann daren?" Direba ne ya yi maganar, sai mai ba wa fulawa ruwa ya ce. "Ai ta yi wa kanta sagegeduwa don da yanzu ita ce a gidan miji cikin rufin asiri, amma yanzu ga shi ta dawo ta tarar da mijin da take so ya auri ƙanwarta." Nan dai suka dinga firan Sidra a tsakaninsu. _Abba_ Tsaye yake a ɗakin Umma yayin da Ammi ke ta fama da Umma akan ta ci abinci amma ta ƙi ci. Don tun lokacin da ta yi arba da wasikar da Sidra ta rubuta ta ajiye ta gudu. To daga nan ba ta sake lafiya ba, abinci ma sai na matsa ma ta take ci. Saboda tana cikin tashin hankali na rashin sanin halin da ƴarta take ciki, ba ta san hannun waye za ta faɗa ba, kuma ba ta san in da ya shiga ba, don ko anan haka kawai idan suka fita unguwa daga ita har Nadra to Umma ba ta taɓa samin nutsuwa da sukuni har sai ta ga sun dawo gida hankalinta yake kwanciya, amma yau ga shi an wayi gari ba ta san in da Sidra ta tafi ba ko sanin halin da take ciki ba. Abba ya kalli mahaifiyarsa da take ta fama da Umma ya ce. "Ammi ta sha maganin ta kuwa?" "Ina fa ta sha Abdallah wannan yarinyar taka wallahi mu dai ba ta taɓa yi ma na rana ba, Allah ya wadaran halin Sidra ga shi ta saka mahaifiyarta ta cikin halin jinya, me yiwuwa tana can hankalinta kwance. Tun da yarinyar nan take ba abun arzikin da ta taɓa yi ma na, akan me za ki damu da yar da ba ta damu da ke ba, idan ta damu dake za ta tafi wani wajen ta bar ki ne?" Duk a cikin jikokina Sidra ce ta fita Zakka wallahi da ina da dama da na..." Sallamar ta da turo ƙofar da ta yi ne ya saka sauran maganar Ammi maƙalewa. Tana kallon Sidra da maɗaukacin mamaki, a hankali ta ce . "Sidra!" Umma dake kwance tana fama da jinya ta buɗe idanunta tana ƙokarin tashi zaune. Abba ya haɗe fuska kamar zai yi Aman wuta yana ma ta kallon bakin ciki da takaici. Trolly ɗin hannunta ta sake ta ƙaraso gabansu tana kuka. Tana ƙoƙarin zubewa akan guiwar ta kenan cikin zafin nama da tafasar zuciya Abba ya saka ƙafa ya yi balla da ita wanda sai da kanta ya haɗu da bango Ya bugu, ta zube a wajan tana sakin Maryan kuka. "Tashi ki bar mani gida tun kafin zafin zuciya ta ɗebe ni na yi ahalinki." _Ma'eesha_ Har ta gama zancen da take yi makaho bai tanka ma ta ba. Ita mamaki ma yake ba ta, meye a ciki don sun kwanta a katifa ɗaya tana matarsa yana mijinta. Ba ta gama mamaki ba ta ga ya kwanta akan tabarmar ya shafa addu'o'i a jikinsa ya juya ma ta baya. Takaice ya ishe ta don sai yanzu take nadamar yi ma sa magana da ta yi akan su dinga kwanciya a katifa ɗaya, sai ya ɗauka ko tana bukatar kasancewa da shi ne a shimfiɗar ma'aurata wanda abu ne mawuyaci ne ga mace budurwa kuma Hausa Fulani. 'Ba zan sake yi ma sa magana akan ya zo su kwanta a katifar ba in sha Allah.' Daga haka ta kwanta tana ta mita cike da takaici har barci ya ɗauke ta. _Nadra_ Indomie ta dafa ma sa wanda ta yi wa haɗi sai ya ji kayan lambu su carrot da sauran su ta dafaffen ƙwai da naman kaza. Ta ɗora plate ɗin indomie a tire ta rufe da wani plate ta saka fork sannan ya saka bottle water me sanyi da kofi . Cikin natsuwa take tafiya a hankali ta nufi ɗakinta don ba ta ji motsin fitowar sa ba da alama har yanzu yana ciki kenan. Ko da ta shiga da sallama a bakinta, ba ta ji ya amsa ba don dama shi sai ya ga dama take magana idan bai ga dama ko kana ma sa magana ba zai tanka ma ta ba. Stool ta janyo ta ɗira tire ɗin a gabansa. Ga mamakinta sai ta ga ya yi barci. Kamar ta tayar da shi kuma sai ta fasa tayar da shi. Don ba ta san yanayinsa ba, ba kowa ke son idan yana barci a tayar da shi ba, don haka ta fasa tayar da shi. Tsaye take tana kallonsa ta rasa ya za a'a yi. Don haka ta fara ƙokarin shiga wanka don ita ma barci take son yi. Hijabin jiki ta ta cire ta ninke shi ta ajiye a saman sallayar. Bathroom ta nufa don yin wanka. Wanka ta yi da shower gel ɗin ta mai ƙamshi sannan ta zuba wani turaren da Gwaggo Laraba ta kawo ma ta ta ce ta dinga zuba wa a cikin ruwan wanka yana da kanshi mai dadi kuma yana kama jiki ya daɗe yana kamshi a jikin mutum. Towel ta ɗaura a kikinta wanda ya tsaya ma ta iya rabin cinyarta, sai ta fito sam ta mance da wai Fahad na cikin ɗakin. Gaban dressing mirror ta tsaya tana goge jikinta da wani ƙaramin towel tana goge ruwan jikinta. A hankali ya fara bude idanunsa a cikin barci da ya ɗauke na mintuna. Saman ɗakin ya kalla kafin ya tashi daga zaunen da yake a hankali ya sauke idanunsa akan ta. Tana tsaye ta gama goge jikinta. Idaninsa na sauka a kanta sai da ƙirjinsa ya buga da ƙarfi. Tun daga kan zara-zaran yatsun ƙafarta yake kallonta Yana sama da idanunsa har zuwa santala-santalan cinyoyinta da suke sheƙi ga alamar cikar hips ɗin ta a bayyane. Kallonta yake yi cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara. Man shafawarta take shafawa hankali kwance tana rera wakar larabci. Bayan ta shafa man a hannayen ta ne sai ta fara ƙokarin zame towel ɗin jikinta. Kamar an ce ta kalli madubin sai ta hango Fahad ya zuba ma ta rikitatun idanunsa yana kallonta. Da sauri ta mayar da towel ɗin da take ƙoƙarin kwancewa ta janyo hijabi da sauri ta zura ta rufe jikinta. Kau da kansa gefe ya yi cike da takaicin rashin kwancewar towel ɗin ba ta yi ba. Don baj taɓa ganin mace mai diri da ta jan hankalinsa ba kamar idan ta kalli Nadra ba hijabi a jikinta. Ko

Chapter 19 of 49