ma su ai ko kallo wannan yarinyar ba ta ishe ni ba. Har yanzu na kara rabuwa da ita ne saboda mutuncin iyayenta amma ba wai don ina son ta ba. Yanzu abu guda na sani yanzu yake ɗan damuna daga jiya zuwa yau. Tun lokacin da mu'amalar aure ya shiga tsakani na da ita na ji na daina jin haushinta, yanzu tausayinta nake yi, ga shi tun da na zo ƙasar tunanin yarinyar ya ƙi barin zuciya ta har sai da na kalle ta na ji nutsuwa anya yarinyar nan ba mayya ba ce ta lashe ma ni kurwa a daren gabaɗaya tunanin ta nake yawan yi na kasa gane me ya sa."
Murmushi Mama ta yi mai cike da ma'anoni kafin ta ce.
"Wato saboda ba ka da kunya ni mahaifiyarka kake yi wa waɗan nan zantuka ko?"
Dariya ya yi ya ce .
"Mama yanzu fa ba zamanin baya muke ba, idan ban sani jiki na faɗa ma ki abun da ke raina ba da qa zan yi? "
"Hmm"
"Yauwa Daddy ya ce na kai yarinyar nan ta zaɓi motar da take so, tafiya ta kama ni ba tare da na shirya ba, don haka zan kira Aunty Rahama a waya su tafi tare da ita sai ta zabi wacce take so."
"Okay ba damuwa, amma sai zuwa gobe ko jibi idan jikinta ya kara warware wa."
Fira suka ɗan taɓa sannan suka yi sallama ya kashe kiran.
_Sidra_
Shirya wa ta yi cikin riga da siket na leshi, ɗinkin ya kama ta yayin da duk surar jikinta suka kasace a bayyane. Shirin mayafi ta rataya a gefen kafaɗarta. Tana rike da handbag ɗin ta da wayarta a hannunta.
Sai zuba ƙamshi take yi tana taku ɗai-ɗai da dogon takalmin ta ma su tsini, sai zuba ƙamshi take yi.
A haka ta fito zuwa falon, Mama ce tare da Inna suke zaune a falon.
Jin takun takalmi ya sa suka juya suna kallon gefen, a hankali take taku sautin takalmin na bada sautin ƙwas ƙwas ƙwas. Kayan jikinta Inna ta kalla ta taɓe baki tare da cewa.
"Gwada da Allah ya sa jikana bai auri wannan yarinyar ba. Wani hanin ga Allah baiwa ne, sai Allah ya bashi kamilalliyar yarinya mai kunya."
Mama dai ba ta ce komai ba har Sidra ta ƙaraso wajen.
"Barkan ku da hutawa."
Ta fada tana zama kan kujera. Mama ce ta amsa da .
"Yauwa kin fito ko?"
"Eh Mama."
"Okay bari na sanar wa direba ya kai k"
"No Mama na fi son na yi driving da kaina."
"Okay, bari na ba ki mukullin motata."
Mama ta tashi ta nufi ɗakinta don ɗaukowa Sidra Sidra mukullin motarta.
Daidai lokacin Aunty Rahama ta yi sallama ta shigo, tana rike da hannun Baby Zahrah.
"Wa'alaiki Salam warahmatullah. Ku ne a gidan yau ma saboda ba ku gaskiya da yawan fita ko?"
"Eh na zo gaida ƙanwata ce Rumaisa ta kira ni ta sanar da ni wai Nadra tana nan gidan kuma ba ta da lafiya. Na ce mun yi waya da Mama amma ba ta faɗa ma ni ba."
"Kai Rumaisa akwai gulma, Allah ya shirye ta."
Mama ta faɗa tana mikawa Sidra key din motarta.
Ta karba tana cewa.
"Aunty Rahama Ina wuni?"
"Lafiya lau Sidra kin zo duba ƙanwarki ce?"
"Uhmm"
Ta furta tana nufar kofar waje . Da kallo suka bi ta Inna ta ce.
"Wa ya faɗa ma ki duba kanwar ta zo?
"Nan Inna ta ba Aunty Rahama labarin korar da Mahaifin Sidra ya yi ma ta da yadda ta zo Babanku ya ce idan ya dawo zai kai ta ya ba wa Mahaifinsu haƙuri."
"Allah ya kyauta."
Aunty Rahama ta faɗa ta durkusa tana gaida Mama, sannan ta gaida Inna. Baby Zahrah ta zauna kan ƙafar kakarta.
"Ina Nadra take ne?"
Mama ta ba ta amsa da cewa.
"Tana can ɗakin Yayanku?"
"Can aka kai ta?"
Inna ta yi saurin cewa.
"Can dai jarababben ƙanin naki ya kai ta. Yarinyar da yake ta ikirarin baya so to tana can ya karɓi budircinta ya bar ta cikin wahala."
Murmushi kawai Sidra ta yi ba tare da ta ce komai ba.
_Nadra_
Tana zaune a bakin gado ta yi tagumi tana tunani, me ya sa har yanzu Aunty Sidra ba ta nemi in da take ba, me ya sa har yanzu ko wayarta ba ta kira ba.
Wayarta ta ɗauka ta lalubo lambar Aunty Sidra ta danna ma ta kira.
Daidai lokacin da Sidra ta shiga motar Mama tana shirin yi wa motar key kenan sai kira ya shigo wayarta.
Ganin Nadra ce sai da ta yi tsuki kafin ta ɗaga ta ce.
"Ya aka yi ne?"
"Assalamu alaikum."
Nadra ta yi mata sallama cikin sanyayyiyar muryarta.
"Aunty kina cikin gidan nan kuwa?"
"Idan ba na ciki akwai inda kika aike ni ne?"
"Allah ya ba ki haƙuri. Dama na ga shiru ne ban gan ki ba tun shekaranjiya."
"Me ya hana ki saukowa ƙasa?"
"Ba na da lafiya ne?"
"Me ya same ki?"
Shiru ta yi ta kasa cewa komai. Dariyar bakin ciki Sidra ta yi kafin ta ce.
"Wato na zo na gaishe ki ko hamshaƙiya mandiya farkar me gari."
Ƙwallar da ya cika ma ta idanun ne ya samu nasarar zubowa.
"Ya aka yi kika yi shiru munafuka maƙaryaciya maciya amana, kin yi zancen karya, kin yi alƙawari kin saɓa na yarda da ke kin ci amanar yardar da na yi ma ki. To ki sani wallahi wallahi wallahi ki sani ja da baya ga rago ba tsoro ba ne sake shirin faɗa ne. Don wanann abun ya shiga tsakanin ki da Fahad kar ki ɗauka na haƙura ina nan akan baka na dole ki tattara tsumman rayuwarki ki bani wajen da kike da zaman wuccin gadi."
*Maman Ihsan ce.*✍️
09065327995
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce✍️
*SADAUKARWA*
Wannan shafin sadaukarwa ne gare ki masoyiyar arziki AMMEY LAYLERH alkhairin Allah ya kai gare ki a duk in da kike. Allah ya bar zumunci masoyiya 🥰
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page4️⃣5️⃣
Ya aka yi kika yi shiru, munafuka maƙaryaciya maciya amana, kin yi zancen karya kin yi alƙawari kin saɓa, na yarda da ke kin ci amanar yardar da na yi ma ki. To ki sani ja da baya ga rago ba tsoro ba ne sake shirin faɗa ne. Don wanann abun ya shiga tsakanin ki da Fahad kar ki ɗauka na haƙura ina nan akan baka na dole ki tattara tsumman rayuwarki ki ba ni wajen da kike zaman wuccin gadi."
Cikin kuka Nadra ta ce.
Aunty Sidra don Allah ki saurare ni ba yadda kike tunani ba ne, wallahi na fi kowa bakin cikin wannan abun da ya faru , ba da..."
Salla rufe ma ni baki, da a baya ne idan kika fada Mani magana zan yarda, saboda na san ba kya yin ƙarya. Amma yanzu kin canza."
"Wallahi ba karya nake yi ma ki ba, ba da son raina hakan ta faru ba, ko da kika ce na je ɗakin Mama na kwanta can na nufa. Ina zuwa ne na tarar da shi a cikin ɗakin Mama. Shi ya ce wa Mama ta ba ni fruit na kai ma sa. Na ce wa Mama ɗakinta zan kwana ta hana ni wai sai gobe idan mijina ya tafi. Ta ba ni fruit na kai ma sa. Kai ma sa da na yi ne ya ba shi damar isar da manufarsa a kaina. Ba yadda zan yi na yi iya ƙoƙarina don ganin na ƙwaci kaina amma ya fi ƙarfina bai bani damar hakan ba."
Ta karasa maganar tana gunjin kuka. Cike da takaici Sidra ta ce.
"Ko ma dai mene ne Fahad nawa ne dole ki bar ma ni shi. Majiya da ba ta ranmin kanta sai wani ya gina sannan ta shige."
Tana faɗar haka ta katse kiran wayar tare da yi wa motar key ta bar gidan.
Cikin sanyin jikin Nadra ta ajiye wayar tana cigaba da rera kuka.
_Daddy_
Zaune yake a ɗakinsa ya saka hoton Mummy da Ma'eesha yana kallo. Ƙwalla ne suka cika ma sa idanunsa. Ya saka hannu ya goge .
Shi sam ya kasa gane dalilin da ya saka baya iya taɓuka komai a cikin gidansa. Baya da kataɓus sai abun da Mamy ta ce yake zartarwa. Ga shi rashin Matarsa uwargidansa da ba ta duniyar da kuma rashin tilon ƴarsa da ya mallaka a duniya ya aurar da ita ga musaki faƙiri yana ji yana gani amma ya kasa komai. A hankali ya bude baki ya furta sunan Ma'eesha.
"Ma'eesha. Ki yafe ma ni, ina ji a jikina ba daidai nake ba, kuma na san ban kyauta wa rayuwarki ba, na cutar da ke, na yi ƙoƙarin hana zuciya aikata hakan na kasa."
Sai ya fashe da kuka. Motsin shigowa ɗakin da ya ji ne ya sa shi yin shiru ya kasa magana.
Kansa a sunkuye ta shigo ɗakin, idanunta akansa ta na nazarin sa.
"Alhaji."
Ya kasa ɗago kai ya kalle ta.
Ta kira sunan a kausashe wanda hakan ya saka shi ya ɗago kai ya kalle ta da sauri.
"Yau ma keɓewa ka yi kana kuka ko?"
"A'a Hajiya ba kuka nake yi ba."
Taɓe baki ta yi kafin ta ce.
"Idan ma kukan kake yi wannan matsalar ka ce, ka je ka yi ta yi kai ne a damuwa. Yarinya tana gidan mijinta cikin kwanciyar hankali me ye za ka damu kanka?"
Idan ita da damu da kai ai da ta zo ko sau daya ne ta duba ka. Amma ita ma sai ta zaɓi zama da wannan Makahon mijinta akan ka, da ba don haka ba ai da ta zo nan gidan idan tana son ganinka. Amma duk ka yi bi ka damu da ita bayan ba ta damu da ka kai ba."
Ta karasa drawer da yake ajiye kuɗi ta ɗebi iya son ranta ba tare da ta ce ma sa komai ba ta fice. Da ido ya bi ta har ta fita daga cikin ɗakin.
Tana fita ta nufi ɗakin ƴar ta Laila, wacce yanzu ita ke cikin ɗakin Ma'eesha. Wanda ya zama mallakin ta a yanzu.
Tana kwance akan tangamemen gadon ta ɗora ƙafa daya kan ɗaya tana chatting.
Inno wacce a baya ita ce mai yi wa Ma'eesha aiki, kamar gyaran ɗaki wankin toilet wankin kayanta da abin da ba'a rasa ba.
Inno ta fito daga banɗaki bayan ta gama wankewa daidai lokacin da Mamy ta shigo cikin ɗakin.
"Hajiya na sake wankewa."
Yamutse fuska Laila ta yi tare da cewa.
"Wannan karon ma idan na shiga na ga bai ma ni ba Tanko zai ɓaci. Fita ki bar mun ɗaki."
Mamy ta raka ta da harara tana cewa.
"Munafuka ta yi ta sunkuyar da kai ƙasa."
Inno dai ba ta ce komai ba, tana takaicin yadda Laila sa'ar ƴar cikinta take wulakanta ta. Sau uku tana wanke banɗaki amma sai ta ce bai fita ba ta sake wankewa Ga shi haka za ta bar banɗakin da ƙazanta ko pad ta cire idan tana period nan take ajiye ma ta sai dai ita idan ta je wanke wa ta ɗauke. Ko period take yi nan za ta bar alama sannan ta kira Inno wai ta je ta gyara. Idan ko ta cire kaya nan za ta zubar da su ƙasa sai inno ta kwashe. Wanda lokacin da Ma'eesha take ɗakin ba za ka taba gane cewa tana period ba idan ya cire kaya sai dai ta ajiye a inda suka dace.
Mamy ta kalli Laila ta ce .
"Ga kudin na san dubu ɗari uku sun ishe ki ko?"
Kamar za ta yi kuka ta ce.
"Ni har yanzu na kasa samun gatan da Ma'eesha ta samu a cikin gidan nan. Ita lokacin da take nan ai miliyoyin kuɗaɗe ne a account ɗin ta sai dai tayi ta zara tana bukatar ta, ki duba ranar da aka aura ma ta makahon nan irin miliyoyin kuɗin da aka cire a account ɗin ta. Amma ni kullum idan ina bukatar sai dai na yi magana ki ɗebo dubu ɗari biyu ko uku ki ba ni."
Daga ƙafarta ta yi cikin sigar rarrashi ta ce
"Ki kwantar da hankalinki da sannu zan saka ke ma ya bude ma an ki account ya zuba ma ki kuɗaɗe. Yanzu na kasa gane kansa ne kullum ckikin ƙunci yake. Kuma kin san Ma'eesha tun tana karama suke tara ma ta kudin lokaci guda ba ne suka saka ma ta."
"To ina su gwala-gwalan nata da kika ce za ki kawo ma ni."
Cikin damuwa Mamy ta ce.
"Har yanzu na kasa gane in da ya ajiye gold din nan."
Cikin takaici Laila ta tashi ta figi kudin ta zuba a handbag ɗin ta ta fice daga dakin bayan ta ɗauki wayarta.
_Makaho_
Yana zaune a tabarma a barandar kofar ɗakinsu. Ma'eesha na zaune a gefen sa ta zuba ma sa idanu tana kallonsa. Ji ya yi a jikinsa ana kallonsa don haka ya ce.
"Wannan kallon fa ba mene ne?"
Murmushi ta yi mai sauti kafin ta ce.
"Idan ban kalli mijina ba waye zan je na kalla?"
Dariya ya yi kafin ya ce .
"Ba wanda za ki kalla sai ni kuwa, saboda ni ne na ki. Ni ma Allah ya nuna ma ni ranar da idona za su bude na kalli Matata farin ciki na."
"Amin ya Allah."
Ta faɗa tana murmushi, zuciyarta cike da farin ciki. Haka kawai take jin kanta cikin nishadi da farin ciki da walwala.
Ɗan yamutse fuska ta yi tana cije lips ɗin ta.
Tuna date ta yi ai yanzu ne lokacin period nata.
"Inna lullahj wa'inna ilaihi raji'un."
Shi ne kalmar da ta fada a cikin zuciyarta. Domin ita kadai ta san irin wahalar da take sha idan tana period. Don tana jin jiki sosai. Ga shi ko Naira biyar ba su da shi a cikin gidan nan, ballantana ta yi tunanin siyen magani da alluran da ake yi ma ta.
Sallama suka ji yaro ya yi daga ƙofar gidan. Sai suka amsa a tare yarin ya shigo.
"A bani gawayi na ɗari huɗu."
Cewar yaron yana miƙa ma ta ɗari huɗu ƴan ɗari biyu guda biyu. Daga gidan Mallam Liman yake kasancewar A'isha ta yi wa Ma'eesha tallar gawayin wajen mutanen gidansu.
Tana rike da mararta ta dafa su da hannu biyu. Ga yaron tsaye yana miƙa kuɗi. Ta kalle shi da idanunta da suka fara canza kala, kafin ta yi karfin halim cewa.
"Aje kudin nan ka je ka ɗauka a wancan kitchen ɗin."
Yaron ya ajiye ya nufi kitchen don ɗauko gawayin. Jin yadda ta yi magana ya sa Makaho cewa.
"Ma'eesha lafiya kike kuwa?"
Gudun ta tayar ma sa da hankali ya saka ta yin murmushi mai sauti ta ce .
"Ba komai kada ka damu."
Ta yi kokarin ganin murya ta ba ta yi raunin da zai gane ba .
Yaron yana sai anjimanku, Makaho ne ya iya amsa ma sa. Makaho ya ce.
"Kika ce idan anjima na ba ki labarin abun da ya faru bayan an sace ni ko? Yanzu zan ba ki labarin komai har zuwa dawowa ta."
Tana jije lips cike da ƙarfin hali da dauriya ta ce.
"Mu bari zuwa wani lokacin, yanzu bari na shiga na ɗan kwanta.
"Kamar ba ki da lafiya."
"Lafiya ga ƙalau."
"Na san sai ba kya barcin yamma, don ke ma kin san bai da alfanu."
Ba ta iya sake yin magana ba a daddafe ta shiga ɗakin ta zube kan katifa ta fara murƙususu tana hawaye.
_Sidra_
Tana fita direct unguwar su ƙawarta Khadijah ta zame. A ƙofar gidan ta dinga danna horn. Maigadi ya leko bayan ya ga ko waye ne sa sai ya buɗe ma ta gate ɗin gidan.
Bayan ta yi parking ne ta fito da sauri kasancewar ta san daidai wannan lokacin Mahaifiyar Khadijah ba ta gida ta je wajen aiki.
Haka ta faɗa cikin falon a guje tana kuka. Khadijah na kwance kan kujera tana chatting kallo daya ta yi ma ta ta ɗauke kai, ci gaba da abun da take yi ta yi ba tare da ta kula Sidra ba.
Ganin haka Sidra ta fisge wayar daga hannun Khadijah ta yi jifa da wayar saman ɗaya daga cikin kujerun da suke falon.
Murmushin takaici Khadijah ta yi kafin ta ce.
"Na san wannan ranar tana zuwa. Ranar da za ki zo kina yi ma ni kuka ba, irin haka na guje ma ki amma kika ƙi saurara ta kuma biye wa shawarar Sady baby. Ga shi yanzu ta kai ki ta baro. Gani kike yi kamar ita ce mai ƙaunarki, ko kiran ki na yi ba ki ɗaga wa, ranar da za ki gudu ba yadda ban yi da ke ba ko saboda mutuncin zuri'ar gidan ku da tozarta su da za ki yi. Amma kika ƙi saurara ta. Kin ɗauka za su jira ki ne sai kin dawo kafin a sake maganar daurin auren ko?"
Murmushin takaici ta yi kafin ta ce.
"Sai kuma kika yi saɓanin fahimta ya kasance aka aura ma sa ƙanwarki a madadin ki. Kuma na ji dadin hakan dama ita ce ta dace da shi."
"Lallai Khadijah yau na san cewa ba ki so na ba ki ƙaunata, abun har ya kai haka? Ni kike taya wa farin ciki.?"
"Da kin saurare ni hakan za ta faru ne?"
"Duk wannan ya isa, so nake yi ki ba ni shawarar da zai sa Fahad ya zama mijina."
"Wani kallon ba ki da hankali Khadijah ta yi ma ta kafin ta ce .
"Kin taɓa ganin in da aka haɗa ya da ƙanwa zaman kishi su auri namiji daya su zauna matsayin kishiyoyi? Mu fa musulmai ne ba maguzawa ba."
"Amma idan ya saki ƙanwa ko ta mutu zai iya auren yayarta ko?"
"Eh zai iya. Amma an fi yi idan ƴar uwa ce ta mutu zai iya auren ƴar uwarta, amma idan ya sake ta ne tana raye akwai kunya ki auri mijin ƙanwarki."
Wani kallo Sidra ta yi ma ta kafin ta ce.
"Kunya, gaba na ba shi ba baya ba. Kuma duk hanyar da zan sai na bi shi wajen ganin na mallaki Fahad kamar yadda na sa wa raina cewa nawa ne shi kaɗai har gaban abada."
"Hmmm Allah ya shirye ki."
Ba ta sake magana ba ɗauki wayarta ta kira lambar wayar ƙawarta Sady baby.
Bugu ɗaya ta daga tare da cewa.
"Ƙawata."
Sidra ba ta amsa ba ta ce.
"Kina ina ne?"
"Ina nan Kaduna."
"Okay gani nan zuwa."
"Allah ya sa lafiya don ni tsoron ki nake ji "
"Ki kwantar da hankalinki mafita za ki ba ni."
Tana gama fadar haka ta dauki handbag ɗin ta. Ko kallon Khadijah ba ta sake yi ba ta fice daga falon . Da kallo Khadijah ta bi ta tana yi ma ta addu'ar shiriya.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page4️⃣6️⃣
"Ki kwantar da hankalinki mafita za ki ba ni."
Tana gama fadar haka ta ɗauki handbag ɗin ta. Ko kallon Khadijah ba ta sake yi ba ta fice daga falon. Da kallo Khadijah ta bi ta tana yi ma ta addu'ar shiriya.
"Allah ya shirye ki Sidra. Da na ga kin shigo kina kuka na dauka nadama kika yi ashe ba haka ba. Dama mahaukaci ba zai taɓa warkewa ba sai dai ya ji sauƙi."
_Ma'eesha_
Tun da ta shiga ɗaki ta kwanta sakamakon canjin yanayin da ta ji ne ya sa Makaho shhga damuwa. Ya san ba haka take ba, duk da baya ganin ta amma ya san akwai abun da ke damunta, ko don yanayin maganar ta ma.
Hankalinsa ne ya ji ya tashi domin baya son damuwarta, kullum yana son ganin ta cikin walwala, kamar yadda itaa take kokarin ganin ta faranta ma sa rai. Kullun zuciyarta cikin bakin ciki da damuwa take amma ta kan ari murmushi ta yafa a saman fuskarta don ganin ta ɓiye bakin cikin da take ciki. Domin akwai ciwo a zuciyarta. Musamman kan mahaifinta. Wani tausayin ta da ƙaunarta ya ji ya ƙara ginuwa a zuciyarsa.
Ba kyawun fuska kawai namiji yake nema a soyayya ba. Akwai wasu abubuwa masu girma da suke gina zuciyarsa da kwanciyar hankalinsa. Idan mace ta fahimci waɗannan, zata iya rike soyayya cikin hikima.
Girmamawa
Girmamawa shi ne ginshikin zuciyar namiji. Namiji yana jin darajarsa ne ta yadda mace take mu’amala da shi, a gaban mutane da a ɓoye. Idan mace tana girmama shi, tana sauraron ra’ayinsa, tana kuma kula da mutuncinsa, hakan yana kara masa kwarin gwiwa da jin cewa yana da matsayi a rayuwarta.
Rashin girmamawa kuwa na iya kashe soyayya ko da akwai kauna.
Biyayya (cikin hikima da mutunta juna)
Biyayya ba bautar mutum ba ce, a’a fahimta ce da haɗin kai.
Namiji yana son mace da zata iya bin shawararsa, ta nuna yarda da jagorancinsa a wasu al’amura, musamman idan yana kokarin alheri a gare ta,
Idan mace tana ta gardama a kowane lokaci, hakan na iya kawo zuciyarsa tayi nesa da ita, amma idan tana nuna biyayya cikin hankali da mutunci, hakan yana gina zaman lafiya. Fahimta da goyon baya
rayuwar namiji tana cike da nauyi da ƙalubale. Yana bukatar mace da za ta fahimce shi, ta tsaya masa a lokacin wahala, ba wacce zata kara masa matsin lamba ba.Lokacin da ya gaji ko ya shiga damuwa, yana bukatar wanda zai kwantar masa da hankali, ya ji cewa ba shi kadai bane.
Goyon baya daga mace yana kara masa ƙarfi da kwarin gwiwa a rayuwa. Idan namiji ya samu girmamawa, biyayya cikin hikima, da kuma fahimta daga wacce yake so, zuciyarsa zata zauna lafiya, soyayyarsa kuma zata kara zurfi.
Soyayya tana dorewa ne idan bangarorin biyu suna bawa juna abin da zuciya ke bukata.
Sandarsa ya laluba ya tashi a hankali ya fara tafiya har ya ji ya taɓo kofar ɗakin. Da sallama a bakinsa ya yaye labulen ɗakin ya shiga.
Tana kwance akan katifarta ta dafe mararta tana karanta duk addu'ar da ta zo bakinta. Sosai idanunta ke tsiyayar da hawaye tana ambaton sunan Allah. Dama kowace mace akwai yanayin da period nata yake zuwa duk wata. Ita Ma'eesha takan yi fama da ciwon ƙasan cikinta kuma ciwon na ma ta tsanani.
Lokacin al’ada, mace na iya jin abubuwa daban-daban a jikinta da kuma zuciyarta saboda canjin hormones.
Da farko, yawanci ana jin ciwon ƙasan ciki (cramps), wanda wani lokaci yana iya zuwa har baya ko ƙafafu. Wasu matan ciwon nasu yana da sauƙi, wasu kuma yana iya zama mai tsanani.
Haka kuma ana yawan jin gajiya da kasala. Jiki yana iya yin nauyi, kuma mutum ya fi son hutawa ko kwanciya.
A bangaren yanayi kuwa, ana samun sauyin hali (mood swings). Wani lokaci mace na iya jin haushi, ko damuwa, ko kuma ta ji kuka ba tare da wani dalili mai ƙarfi ba.
Wasu kuma suna fama da ciwon kai ko ciwon jiki gaba ɗaya. Haka kuma ciki na iya kumbura (bloating), wanda ke sa a ji kamar ciki ya cika ko ya yi nauyi.
Akwai kuma sha’awar wasu abinci (cravings), musamman kayan zaki ko abinci na musamman, kuma wani lokaci yunwa na ƙaruwa.
Amma ya kamata a sani cewa ba duk mata suke jin abu iri ɗaya ba yana bambanta daga mutum zuwa mutum.
"Ma'eesha lafiya kike kuwa?"
Cije lips ɗin ta ta yi ta goge sun hawaye tana kokarin daidaita nutsuwarta da muryarta.
"Na'am ka shigo?"
Ta amsa cikin sanyin murya.
Lalubar katifar ya yi ya karasa kai ya lalubo hannunta.
"Me ke damun ki?"
" Ba komai barci zan yi."
"Amma kin san barci a irin wannan lokacin na yammaci ba kyau ko?"
Kuka ne ya ƙwace ma ta sai ta faɗa jikinsa tana sakin wani sabon kuka. Kwantar da kanta ta yi a faffaɗar ƙirjinsa tana ci gaba da kuka.
Shi kuma hankalinsa ya tashi zuciyarsa ta yi ma sa nauyi. Take idanunsa suka sauya zuwa ja.
_Nadra_
Tun bayan da ta gama waya da Sidra ta take riskar kuka. Kuka take yi sosai ta rasa me ke yi ma ta daɗi.
Daidai lokacin Aunty Rahama ta yi sallama ta shigo cikin ɗakin.
"Subhanallah, me ya samu ƙanwata ce take kuka haka?"
Sai a lokacin Nadra ta lura da ita ta yi saurin goge hawayenta.
Ƙarasawa ta yi ta zauna gefenta, sannan ta dafa kafaɗarta ta ce.
"Nadra."
Sunkuyar da kai ƙasa ta yi tare da cewa
"Ina wuni Aunty."
"Lafiya lau ya kike ya jikin?"
"Alhamdulillah."
Ta amsa cikin sanyin murya.
"Me ke damun ki ne kike ta kuka?"
"Ba komai."
"A'a akwai komai kam."
Shiru Nadra ta yi ba tare da ya sake yin magana ba.
Aunty Rahama ta kalle ta cike da ƙaunarta ta riko hannunta cikin nata cikin hikima ta ce .
"Ina son ki dauke ni kamar ƙawar ki."
Kallon ta Nadra ta yi cike da mamaki ta ce.
"Ke fa babba ce."
Dariya ta yi kafin ta ba ta amsa da cewa
"Ai ba sai sa'arki za ki yi ƙawance da ita ba, ko wacce
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 49