dai ta san cewa tana da sura mai jan hankali ne ya sa take rufe jikinta kullun cikin hijabi.
Tabbas yarinyar ta kusan ruɗar da shi, amma saboda mishkilancin irin nasa ya basar kamar bai kalle ta ba.
Fuska ba walwala ya kalle ta cikin tsare gida ya ce.
"Ina abincin?"
Kallon stool ɗin da ke gabansa ta yi tare da cewa .
"Ga shi nan, na ga kana barci ne na ajiye ma ka."
"Ina barcin zan ci da kina ajiye kika kama gabanki ?"
"Ka yi hakuri na ɗauka ba za ka so na tayar da kai ba ne."
"Okay."
Ya faɗa yana miƙe wa ya nufi kofar fita ya fice daga cikin ɗakin.
_Sidra_
Wani azababben zafi ne ta ji ya ratsa tana zaton kanta ma ya fashe.
Duhu ta fara gani ga wani jiri da take ji yana ɗibarta daga kwancen da take. Muryar Abba ta ji cikin kakkausan marya ya ce
"Ba na bukatar sake ganin ki a cikin gidan nan, ki tashi ki koma inda kika fito, ki je wajen da ya fiye ma ki nan."
Cikin kuka ta ce.
"Abba ka yi hakuri ka yafe ma ni wallahi sharrin shaidan ne."
Idan ba ki tashi kin fita ba sai na illata ki kuma na saka a yi waje da ke yanzu kuwa."
Sai a lokacin ta yi kokarin kiran sunan mahaifiyarta mai tausayin ta. Uwa mafi uba ko da Uba sarki ne."
"Umma ki taimaka ki saka baki Abba ya saurare ni."
"Ba abinda zan saurara ki tashi na ce.
Sai a lokacin ta ji sautin kukan mahaifiyarta, don kuka ne ya ƙwacewa Umma q wanann lokacin.
"Umma don Allah ku saurare ni, ki saka banki Abba ya sauko."
Kallon kakarta ta yi tana cewa.
"Ammi please ki saka banki ɗanki ne Abba yana ma ki biyayya kuma..."
Kafin ta rufe baki Ammi ta ce .
"Ko kashe ki zai yi ba zan ce komai ba mara mutunci kawai."
"Na ji ko ba za ku yafe ma ni ba don Allah ku daura ma ni aure da Fahad idan bai aure Ni ba zan iya rasa rayuwata."
Mamaki ne ya kama kowannen su domin kuwa da alama ba kukan nadamar abun da ta aikata take yi ba. Kuma babu nadama a tattare da ita, ba ta yi nadamar wuce wa ta bar iyayenta cikin tashin hankali ba, ba ta damu da halin da suka shiga ba a'a ita ta saurayin ta take yi ma.
Cikin takaice Ammi ta ce .
"Ai sai dai ki mutu domin Fahad yana can tare da matarsa Nadra."
Kuka ta sake mai haɗe da kururuwa Abba ya ja ta ƙeee taka ihu bai saurare ta ba sai da ya kai ta har baƙin gate bayan ya ce maigadi ya buɗe ma sa gate ya cilla ta waje. Sai ga Ammi ta cillo ma ta handbag ɗin ta da trolly sun rufe gate ɗin ta ciki.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page3️⃣2️⃣
Kuka ta sake mai haɗe kururuwa Abba ya ja ta ƙeee tana ihu bai saurare ta ba sai da ya kai ta har bakin gate, bayan ya ce wa Maigadi ya buge ma sa gate ya cilla ta waje. Sai ga Ammi ta cillo ma ta handbag ɗin ta da trolly sun rufe gate ɗin ta ciki.
Kuka sosai Sidra ke yi tana tuna ranar haɗuwar su ta farko da Fahad.
Ta fito daga cikin super market tana tsaye tana magana da wata ƙawarta da suka daɗe ba su haɗu ba sai yau da ta zo shopping. Sady baby ta kalli Sidra ta ce .
"Na gaji da zuwa gidanku tun da ke ba ki zuwa gidan mutane dai dai ayi ta zuwa gidanku Ni ma na kama kaina."
Sidra dake sanye cikin fitted gown na less ɗinkin ya zauna ma ta a jiki less ɗin dari ne da ratsin golding sai ƙaramin gyale golding colour da ta rataya a gefen kafaɗarta sai baƙin glass da ta saka a idanunta tana jingine a jikin motarta sai ta buɗe bayan motar ta saka ledar siyayyen da ta yi, kallon Sady baby ta yi ta ce.
"Ki yi haƙuri ƙawata wallahi Abba da Muna ba su bari muna yawon gidajen ƙawaye, Khadijah ƙawata kawai suke bari na je ita ma sai da dalili.
Wata galleliyar mota ƙirar Lexus ( Lc series higher trims) ce ta ƙaraso wajen kyawun motar da tsaruwarta ya saka hankalin wadanda ke wajen ya koma ga motar. Hatta Sidra da ke sanye da bakin glass idnsunta na kan motar, sai dai ba za ka taba gane me take kallo ba.
Murfin motar mamallakin motar ya buɗe, a hankali ya ziro fararen ƙafuwansa waje wanda yake sanye da takalmi kambas masu tsada ƙirar Gucci sneakers. Kafin ya fito yana sanye da tsadadden kaya na alfarma Tshirt mai tsada da wando jeans.
"Fahad Majidaɗi kenan, I like the guy."
Cewar Sady baby tana kallonsa.
Jin shaka ya saka Sidra cewa.
"Kin san shi ne?"
Ba ta amsa ma sa ba, don gabaɗaya hankalinta ya koma kan Fahad.
Cikin takunsa na ƙasaita yake taku har ya shiga super market.
Sai da ya shiga sannan Sidra ta ce .
"Waye wanan guy din?"
Sady baby ta ce .
"Sunansa Fahad Umar Majidaɗi. Shi Ambassador ne Yana wakiltar ƙasarsa ne a ƙasar America (united state) yana yawan zama a ƙasar America , yana aiki a matsayin hadin gwiwa tsakanin tsakanin Nigeria da America. Yana jagorantar harkokin diplomasiyaz yana ƙarfafa dangantakar ƙasar da yake wakilta, da kuma kulawa da al'amuran ƴan ƙasarsa da suke zaune a American yana Magance matsalolin siyasa da tattalin arziki tsakanin ƙasashen guda biyu."
Murmushi Sidra ta yi kafin ta ce .
"Yana ƙoƙari."
"Na taɓa nuna ma sa ina son sa ya yi rejecting ɗina."
Cewar Sady Baby cike da takaici
Murmushi Sidra ta yi wanda ita kadai ta san ma'anarsa . Sallama Sady baby ta yi ma ta ta shiga motarta ta bar wajan.
Sidra ta matsa jikin motar Fahad ta jingina tana jiran fitowarsa. Ba jimawa ya fito tare da wani ma'aikacin super market din ta riko ma sa kaya.
A bayan motar ya saka ma sa Fahad ya dunƙule kudi ya ba shi, zagayawa ya yi wajen direba sai ya ga Sidra ta jingina da mirgina motar tana waya, tana pretending kamar da gaske.
"Wallahi Umma na gaji sosai ga Direban bai dawo ba yamma ta yi ban san yadda zan yi ba ga shi ba na iya shiga abun hawa na kasuwa."
"Excuse me."
Ya faɗa kamar wanda aka yi wa dole.
Sai ta yi kamar ba ta ji ba, kamar za ta yi kuka take magana akan rashin abun hawa. Kafin ta katse wayar ta kalle shi ta yi Murmushi.
"Oh sorry."
Ta fada tana matsawa.
"Nevermind."
Ya ba ta amsa yana kokarin shiga motar.
"Oh Allah yanzu ya zan yi na koma gida."
Kin haka ya ce.
"Ki shiga na kai ki idan ba za ki damu ba."
"Toh na gode."
Ta fada tana mai zagayawa mazaunin direba ta shiga ta zauna.
Tsawon lokaci mintuna ba wanda ya yi magana kafin ta ce .
"Na gode fa."
Bai amsa ma ta ba yana driving ɗinsa.
"Da ana samun mutane irin ku marasa girman kai masu saukin kai ai da an gode."
Sai a lokacin ya kalle ta yana cewa.
"Ke ce mutum ta farko da ta ce ina da sauƙin kai wai ba na da girma kai, kowa cewa yake ina ji da kaina ke kika fita daban."
Dariya ta yi tana cewa .
"To ma sha Allah na zama ta daban a wajen ka."
Kwatance ta yi masa ya kai ta har ƙoafar gidansu. Za ta fice ta ce.
"Sai yanzu ta daban za ta sake ganinka."
"Duk sanda kike bukatar gani na in dai ina kasar za ki ganni."
Ya faɗa yana miƙa ma ta katinsa ta yi godiya, sai da ta jira wucewarsa ta shiga cikin gidan,.
Direban su ta ba key ɗin motarta ta sanar da shi in da zai je ya dauko motar sannan ta shiga ciki.
Tun daga nan ta ke kiran Fahad a waya suna gaisawa har wata rana ya zo ya bayyana ma ta yana son ta. Ranar kamar za ta zuba ruwa ƙasa ta sha , daga nan suka ƙulla soyayya cike da kulawar juna, in dai yana ƙasar yana yawan zuwa ko da bai daɗe ba.
A hankali Sidra ta share hawayenta bayan ta gama tunanin ranar da suka fara haɗuwa da Fahad tana dafe kanta inda ta bugu da dukan da Abba ya yi ma ta.
"Ba zai yiwa a raba ni da shi ba Fahad nawa ne dole ya saki Nadra ya aure ni."
Da ƙyar ta tashi ga dare ya yi ta nufi bakin titi kasancewar ba nisa da gidansu da gidan Gwaggo Maimuna. Tana ganinta ita ma ta kore ta don ta dauki zafi kamar yadda ƙaninta Abba ya dauki zafi.
Daga nan sai ta nufi gidan Gwaggo Laraba lokacin karfe goma sha ɗaya na dare.
Gwaggo Laraba ta yi ma ta faɗa sannan ta kira Abba ta ba shi haƙuri akan ya yi haƙuri. Kwancewar shi ne dama da Gwaggo Laraba ya yi ma ta fada ya ce idan ba ta kori Sidra ba ta bar gidan nan idan ba haka ba sai ta hadu da ɓacin ransa. Ba ta da wani zaɓi dole ya ce ya tafi.
A ranar Sidra ta ga tashin hankali sosai ba kaɗan ba.
Ƙarshe ta yanke shawarar zuwa gidan iyayen Fahad don ta nemi alafarmar Baban Fahad ya je ya roƙi Abba ko Allah zai sa ya hakura kasancewar yana jin kunyar Baban Fahad yana ganin ƙimarsa.
Ƙarfe ɗayan dare ta yi ba abun hawa ga shi dama ba da motarta ta tafi Abuja ba. Yanzu na ina take ta mota.
Ƙarfe ɗaya da kwata ta isa ƙokar gidan su Fahad a jikace sakamakon dogon tafiyar da ta yi .
_Makaho_
Bayan ya tabbatar da Ma'eesha ta yi barci don dama shi ma ba barci yake yi ba idanunsa biyu. Tashi zaune ya yi tare da lalubar sandarsa ya ji ya riko ta ya mike tsaye.
Hanyar ƙofar ya nufa yana lalube har ya buge sakatar ya fita daga cikin ɗakin.
Bayan ya ɗauro alwala ya zo ya fara sallolin nafila. Ba shi ya kwanta ba sai karfe uku na dare.
Yana zaune kan sallaya yana addu'o'i kafin ya shafa.
Kwanciyar sa ya yi wanda ba jimawa barci ya yi awon gaba da shi.
Kiran sallar asuba ya farkar da shi daga barcin da ya soma ɗaukarsa.
Fita ya yi daga ɗakin ya nufi banɗaki.
Wanka ya yi ya fito ya yi alwala sannan ya koma dakin.
Jin tsit sai saukar numfashinta ya tabbatar ma sa da cewa .
Har yanzu barci take yi ba ta farka ba.
Kayan jikinsa ya sauya zuwa wata jallabiya kafin ya nufi in da katifar da Ma'eesha ke kwance.
Pillow ya buga yana kiran sunanta.
"Ma'eesha."
A hankali ta bude ida wanda daka a lumshe suke kamar bairci.
"Na'am."
"Lokacin Sallah ya yi ni zan shiga Masallaci, ki tashi ki yi sallah.
,"toh"
Ta fada hana tashi daga zaunen da take.
Fita ya yi shi ma ya je masallaci yayin da ita kuma ta gabatar da sallar a gida.
_Fahad_
Bayan ya bar indomie da Nadra ta dafa ma sa ɗakinsa ya koma. Kwanciyar rud da ciki ya yi yana cije lips ɗin sa ba tsakiya.
Ba abinda ke ma sa yawo a kansa sai yadda ya ga Nadra ɗaure da towel.
Gabaɗaya abun ya tsaya masa a cikin kansa ya yi kane-kane ne.
Cike da takaici ya ce .
"Oh Fahad wai tunanin me kake yi haka ne, ba dai waccen ƴar karamar yarinyar je neman birkita masa ƙwaƙwal.
Da sallama ta turo kofar ɗakinsa ta shigo, bayan sallamar da ta dinga yi a bakin ƙofar falon
Yana jin sallamar amma bai bude idanunsa ba kuma bai tanka ba .
Tire ɗin ta ajiye wanda ta jera ma sa abincin akai .
"Ga abincin nan na kawo maka."
Kamar ba zai amsa ba kafin ya ce
"Okay thank you, sai da safe za ki iya tafiya."
"To Allah ya ba mu alkhair."
Har ta kai bakin ƙofar ta ji ya ce .
"Zo mana."
Yadda ya yi maganar sai da gabanta ya fadi, don haka ta juyo cikin sanyin jiki ta karasa wajensa.
"Ina za ki je?"
"Kai ka ce na tafi ."
"Okay kuma yanzu na ce ki dawo"
Shiru ne ya biyo baya kafin ya ce .
"A nan ɗakin za ki kwana."
Ya faɗa kamar ba shi ya yi maganar ba.
_Makaho_
Dawowarsa daga masallaci kenan ya yi sallama, Ma'eesha na zaune a barandar ƙofar ɗaki tana hada ma su abun breakfast a gas ta amsa sallamar da ya yi .
Cikin sanyin murya ta ce .
"Ina kwana?"
Ya amsa da lafiya lau ya aiki ya ƙoƙari ?"
"Alhamdulillah, ya karfin jiki?"
"Alhamdulillah."
Sallama suka ji yaro ya yi ya shigo.
Suka amsa ma sa ya ce
"Wai ana sallama da Ma'eesha."
Cikin mamaki ta ce.
"Waye ?"
Yaron ya ce .
"Wani ne ya zo da mota yana waje."
A tunanin ta Yaya Jamil ne, amma duk da haka yya ce.
"Ka je ka ce waye?"
Yaron ya fita ba jimawa ya dawo ya ce.
"Wai ya ce saurayinki ne Abdul ya dawo ."
Mamaki da al'ajabi ya kama ta ya aka yi ya san tana nan , shin ba ta yi blocking nasa ba kuma ta fada ma sa ta yi aure.
Tashi ya yi cikin ɓacin rai ta dauki hijabin ta ta saka ta lallai makaho ta ce.
"Ina zuwa don Alaihi minti biyu."
Daga haka ya nufi kofar gidan ta fice.
*Mamman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page3️⃣3️⃣
Daga haka ta nufi ƙofar gidan ta fice.
Wata baƙar motar ce ta hango a ƙofar gidan, tinted glass ne ba ta iya hango na cikin motar.
Amma shi yana ganinta ya bude murfin motar ya fito ya jingina da jikin motar yana kallonta da maɗaukacin mamaki a fuskarsa. Don ko da Ma'eesha ta faɗa ma sa a waya cewa ta yi aure bai yarda ba, sai da ya tambaye Nasreen ta faɗa ma sa gaskiya ne, daga nan ya matsa ma ta akan sai ta bashi address na Ma'eesha. Da farko ta hana ma sa sakamakon Ma'eesha ta yi ma ta gargaɗi akan haka wanda har da barazanar cewa idan ta sake ma ta zancen Abdul ko kuma ta ƙara ƙalubalantar auren za ta rabu da ita. Amma sai Abdul ya ruɗe Nasreen da maƙudan kuɗaɗe wanda ya sa ta ba shi address n gidan. A tunanin ta ba zai gane gidan ba saboda yanayin unguwar ta talakawa ne kuka gine-ginen gidajen ba wani tsari ne da su ba.
Fuska Ma'eesh ta ƙara tsuke wa kafin ta isa wajensa.
"Abdul meye haka, me ka zo yi a nan bayan na faɗa ma ka cewa ni yanzu matar wani ce, amma saboda rashin sanin darajar aure ya sa za ka zo kofar gidan matar aure ka ce a yi ma ta sallama ta fito?"
Gajeren murmushi ya yi kafin ya ce.
"Wai yanzu Ma'eesha Ibrahim Khalil ce ta dawo haka? Look at you, kin yi baƙi kin rame duk wanda ya san ki a baya idan ya ganki yanzu ya san kina cikin wahala. Wannan rayuwar ba ta dace da ke ba, ba za ki iya ba kuma ba ki saba ba. Don haka wannan musakin mijin naki kuma faƙiri ki sa ya sake ki ki zo mu je ki cika ma ni alkawarin aurena da kika yi. Zan ba ki jin dadi da kwanciyar hankali zan mayar da ke..."
"Ya isa haka Abdul!"
"Kina da baƙin da za ki hana ni na yi magana ne? Bayan a baya ina ma ki kallon mai gaskiya ashe ba haka kike ba, bayan kin yi alƙawari ki saɓa an ba ki amana kin yi ha'incin? Ko kin manta ke da kanki kika yi ma ni alkawarin aure? Ke fa kika ce da zaran na dawo daga ƙasar Canada na dawo Nigeria za ki tura ni wajan mahaifinki na gama da shi a yi zandan aure kawai sai da na kira ki a waya ki ce ma ni wai kin yi aure haka yarda da amana take, bayan kin yi ma ni alƙawarin aure ashe yaudara kika shirya, Ni ina can ina tsara mana rayuwar da za mu yi bayan auren mu idan na ɗauko kin mun bar Nigeria, ashe sha sha sha kika mayar da ni ko?"
Goge hawayen dake kan fuskarta ta yi kafin ta ce .
"Ni ban zamo daga cikin munafukai ba da suke ɗaukar alƙawari su saɓa ko kuma su yi karya ko su ci amana. Ban yi ko daya daga cikinsu ba."
"To idan ba ki yi ba me ya sa kika yi aure bayan kin yi ma ni alkawari?"
"Ni ma kaina ban san da zancen aurena ba kwatsam lokacin ɗaya ake shaida ma ni wai an ɗaura ma ni aure ba tare da sani na ko shawara da ni ba ballantana neman yarda ta. Ka ga ta ina nake da laifi akan hakan?"
"To na ji ba ki da laifi amma ai Nasreen ɗin ta fada Mani wanda kika aura musaki ne kuma faƙiri to me ya sa za ki yarda ki zauna da shi? Ai kin fi karfinsa nesa ba kusa ba, ai zaren ba kalar yadin ba ne. Kina da ikon da za ki saka ya sake ki ko ta ƙarfin arziki ko ta tsiya tsiya , bai isa ya yi jayayya da ke ba, idan kuma ba za ki iya saka wa ya sake ki ba ki bar ni da shi ina da hanyoyi da yawa da zan saka ya rabu da ke ko yana so ko baya so ki bar ni da shi."
Ɗaga ma sa hannu ta yi alamar dakatarwa kafin ta ce.
"Ba ruwanka da shi?"
"Da mamaki yake kallon ta kafin ya ce.
"Kar dai a ce wai son sa kike yi, kina nufin kina son makaho mabaraci ina fatan dai ba ki taɓa bari ya raɓi jikinki ba?"
A fusace t ce.
"Abdul!"
Sai da ya kalle ta da kyau bai amsa ba ya dauke kansa yana kallon gefe.
"Ka fita a sabga ta domin yanzu ni matar aure ce, kuma zaman aure nake yi na ibada har abada ba don na fito wata rana ba. Khalifa mijina ne har a aljanna in sha Allah, ina son mijina ba abinda zai saka na rabu da shi mutuwa kaɗai za ta raba ni da shi, idan ka sake zuwa ƙofar gidan nan wallahi sai na tafka ma ka rashin mutunci, don sai na sa yara sun dinga jifanka da duwatsu sun farfasa ma ka mota. Wanda bai san darajar aure ba.
Makirin murmushi ya saki kafin ya ce.
Kika ce ba abun da zai sa ki rabu da shi ba ko? Sai kuma kika ce mutuwa ce kaɗai za ta raba ki da shi to ai ko akwai abun da zai raba ki da shi ɗin domin kuwa mutuwar rigar kowa ce kuma mutuwar tana nan tana jiransa idan kin isa sai ki hana mutuwar zuwa gare shi. Kuma ki jira ni ina nan dawowa gare ki
Yana faɗar haka ya juya ya bude murfin motarsa sai dai kafin ya shiga ya juya ya kalle ta ya ce.
"Kalli yadda kika rame kika yi baƙi kika lalace ba wanda zai gan ki yanzu ya ce wai Ma'eesha Ibrahim Khalil ce ta dawo haka."
Yana gama faɗar haka ya shiga motarsa ya yi ma ta key ya bar ta nan tsaye. Hawaye duk sun gama wanke ma ta fuska.
Hanyar shiga gidan ta nufa ta shiga cikin sanyin jiki. In da ta bar makaho tsaye a nan ta same shi.
_Nadra_
Da mamaki da kuma fargaba take kallon Fahad, Majidaɗi jin ya ce wai a nan za ta kwana.
Tsaye take tana kallonsa yana cin abincin sa hankali kwance.
Duk yunwar da yake kira yana ji bai cinye rabin abincin ba.
"Ka ce anan zan kwana?"
"Eh ko kina da matsala ne?"
"Eh ina da ita."
"Okay meye matsalar?"
"Ba na iya barci tare da wani a kusa da ni."
Dariya ta so ba shi anan sai ya danne. Tsaye ya mike yana cewa .
"Amma ai ke sa Sidra ɗaki ɗaya kuke kwana ko?"
"To ai ita Yayata ce."
"To ni ma ai mijinki ne?"
Cike da yarinta ta ce.
"To ai kai ba wai mijina ba ne, ka ga ka ce wai za ka rabu da ni ya Sayyadi ya aure ni tun da ba ka sona shi kuma yana so na. "
"Idan kika sake kira mani sunan wannan mutumin ba?"
"To ka yi hakuri."
"Okay na ji zancen rabuwa da na ce ma ki za mu yi lokaci nake jira."
Kafin ta yi magana ma ya ce.
"Ki ɗauke kayan nan ki kai kitchen, ki dawo da shirin barci ina jiran ki"
Tura baki ta yi ta ɗauki kayan ta fice daga ɗakin
Tana ajiye kayan kitchen da sauri ta nufi ɗakinta ta saka key ta mirza ta ciki . Ita kaɗai take magana a zuciyarta.
'Tab ai na gane nufinsa wato ya ce baya so na kuma zai sake ni ne nan gaba na je na auri Ya Sayyadina. Amma shi ne zai ce na je na kwana ɗakinsa ya yi Mani wayau ya kwashe albarkatun jikina sannan ya sake ni lokacin da zama fanko sannan zai bar wa Ya Sayyadi fanko, to ta Allah ba taka ba, masoyina mai so na tsakani da Allah ne kadai zai samu budurcina ba kai...'
Maganar ce ta maƙale sakamakon jin ƙamshinsa da ta yi, gane gabanta ya faɗi ta juya ta kalli ƙofar.
Tsaye ta gansa yana ma ta wani kallo da ta kasa gane ko na mene ne.
Yana kallon ta yana kuma kokarin hana zuciyarsa shin da take so, don tabbas tun da ya lyalle ta ɗaure da towel gabɗaya kansa kwance a kanta. Matsanancin sha'awarta yake yi, sai dai yana kokarin hana kansa zuwa gare ta. Musamman da ya san cewa ba ya jin son ta a ransa, kuma idan har ya ya aikata wani abu da ita raina shi za ta yi, don kallon ƙaranar yarinya yake yi ma ta, a ganinsa raini ne zai ja wa kansa kuma yana ganin ya fi karfin haka nan a wajen ta yana ganin ba ta da ajin da zai haɗa jikinsa da nata.
Tsuki ya ja cike da takaici ya harare ta sannan ya fice daga ɗakin.
Ganin haka ya saka Nadra ta yi Murmushi tare da cewa.
"Alhamdulillah na ji dadin wannan girman kai da ji da kai da kake da shi. Ya gani yana so amma Jin kansa da mishkilanci ya hana shi ya nuna, hakan ya Mani kyau kai kuma ya yi ma ka muni."
Haka ta kwana zuciyarta fara tas.
_Sidra_
Karamar door din gate ɗin ta ƙwanƙwasa, security dake bakin gate ɗin gidan ya duba agogo ya ga karfe ɗayan dare.
Don haka daga cikin ya ce.
"Waye?"
Ta waje ta ce
"Ni ce."
"Kece wa?"
"Ni ce Sidra matar da Fahad na gidan nan zai aura."
"Tofa yallaɓai da ya yi aure abin sa."
"Eh ƙanwata ya aura."
"To ai ba nan ya zauna da ita ba ki je gidansa ma na."
"Wajen mahaifinsa na zo, ka ce ma sa wai Sidra Abdullahi Maitama ce ta zo wajensa."
"Gaskiya yanzu dare ya yi Alhaji na barci ba zai yiwu na tayar da shi ba."
"Don Allah ka taimake ni ka sanar da shi ba zan iya kwana a haka ba ga ni a waje wani abu zai iya samu na, ba ni da in da zan je."
Daidai lokacin ne wayar security ya yi ringing, ya duba ya ga maigidan ne, ya dauka cikin girmamawa ya ce .
"Barka da dare yallaɓai."
"Ka bude ma ta gate ta shigo ciki."
Abun da Alhaji ya faɗa kenan sanan ya lashe kiran wayar.
Dama lokacin Alhaji Umar Majidaɗi bai yi barci ba, ya gama duba wasu document kenan yana shirin kwanciya ya duba CCTV camera ya ga Sidra tana tsaye jikin gate ga trolly ɗin ta a gefenta tana magana da maigadi.
Duk da ba wai ya gane ko wace ce ba amma tabbas ya san cewa ya san fuskar yarinyar ya taɓa ganinta amma ba zai tuna ina ba ne ya san ta.
Bayan ya ba security damar shigowa da ita ne ya juya ya kalli kan gadonsa da Mama ke barci.
A hankali ya kira sunanta yana shafa fuskarta. Bude idanunta ta yi a kansa ta ce .
"Alhaji lafiya kuwa?"
"Ki je ki bude main door akwai yarinyar da ta zo yanzu, tana tare da trolly me yiwuwa daga wani gari take dare ya ma ta a hanya."
"Wace ce ita?"
"Ba zan iya tuna
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 49