Share this page
motar da ya zo da shi ne ya gane ba ƙaramin mutum ba ne. Hannu Jalaluddeen ya ba shi suka yi masabaha. Sanan ya nemi da wajen Nasreen ya zo. "To Yallaɓai bari a sanar da ita zuwanka." Ya koma ciki ba jimawa ya dawo ya sanar da shi cewa tana nan zuwa. Ba jimawa ta fito ta zuba wa bayansa idanu. Kasancewar ya juya baya yana tsaye jikin motar, ya ɗan kwantar da kansa a saman motar. Duk da cewar ba ta san ko waye na amma ƙirar jikinsa kaɗai zai tabbatar ma ka da cewa tsayayyen namiji ne. "Assalamu alaikum." Ta yi ma sa sallama. Ya amsa yana juyowa suna fuskantar juna. Da mamaki take kallonsa yadda ya zo kai tsaya ba tare da ɓadda kama da yake yi yana raina wa ƙawarta hankali ba. "Lafiya me ka zo yi nan ƙofar gidan?" "Ƙawarki nazo nema, na san ba in da za ta zo da ya wuce nan." "Tofah! daɗi na da gobe saurin zuwa, an zo wajen kenan, ta ga hanya yau ta gane shayi ruwa ne. Tabbas hakan ya ma ni dadi da ta gane ko kai waye, Alhamdulillah ko ba komai yanzu za ta tabbatar da cewa ba karya nake yi ma ta ba gaskiya nake faɗa ma ta. Kai wanda take kallo kamar waliyi kai ne ka yi ma ta karya." Girgiza kai ta yi tana murmushi. "Sai dai na tausaya ma ku daga kai har ita ababen tausayi ne, yanzu na san tana can cikin damuwa da bakin ciki, yadda ta tsani ƙarya da yaudara da cin amana. Ga Jsji ta kama ka da aikin aikata ma ta su. Tabbas na san shawo kanta ba abu ba ne mai sauƙi. Amma ko ba komai na yi farin cikin gaskiya ta yi halinta kuma..." "Ya isa, idan kin san inda za ta iya zuwa bayan wajenki to ki faɗa ma ni." "Ban sani ba, ka je can ka neme ta, yadda ka saka ta cikin halin da take ciki sai ka nemo ta ka shawo kanta." "Idan har kin san tana cikin gidan nan ki fito ma Ni da ita, idan kuma ba haka ba, kika bari na tabbatar tana ciki wallahi sai kin yi nadamar ƙaryar da kika yi ma ni." "Oh Allah, me zai saka na yi ma ka karya? Kodayake duk abun da mutum yake yi sai ya ɗauka kowa ma shi..." Tsawa ya daka ma ta wanda sai da hantar cikinta ta kada. "A halin yanzu raina a ɓace yake kada ki tunzura ni. Ina matata na tambaye ki." "Wallahi ban san in da ta tafi ba." Ganin yadda ta tsorata da yanayin ta ya tabbatar ma sa da gaskiya ta faɗa. Don haka ya shiga motarsa ya yi ma ta key a guje ya bar ƙofar gidan. Tafiya kawai yake yi ba tare da ya san in da zai ganta ba. _Alhaji Sulaiman_ Horn motocin da sauke ciki suka yi a ƙofar gidan Daddy. Maigadi ne ya leƙo. Ganin manyan tsadaddun motocin da suka zo ƙofar gidan ne ya sa da sauri ya bude gate. Motocin suka fara shigowa cikin gidan . Daidai lokacin da Laila ta fito za ta je unguwa. Ganin irin motocin ya sa ta fadin . "Wow." Haidar da kabeer suka fara fitowa, ta zuba ma su idanunta ko ƙyaftawa ba ta yi. Alhaji Sulaiman da abokinsa Sanata suka fito tare, sai Maude da jikinsa ya yi sanyi, sai kuma daya ma'aikacin gidan marayun wanda ya biyo su. Barrister Haidar ne ya tura Maigadi a je a sanar da maigidan yana da baƙi. Daddy dake zaune da Mummy a falo sai kuma Jamil dake zaune a carpet. Maigadi ya shigo ya sanar da Daddy zuwan baƙin. Kafin Daddy ya yi magana har Mamy ta leka ta window. Ganin manyan motoci ne ya saka ta jijina kai tana yi wa maigadi magana. "Ka yi sauri ka shigo da su manyan mutane ne ba'a barin su a barin su haka." Zama ta yi tana jiran shigowar su. Da sallama suka shigo cikin falon, Daddy da Jamil suka miƙe suna yi ma sa sannu da zuwa . Suka shigo kasancewar set biyu ba kujera ne a falon don haka duk suka zauna akan kujera. Laila ma fasa fita ta yi ta shigo ciki din ganin abub da zai turewa buzu naɗi. Bayan an gaggaisa Mamy ga sa mai aiki ta kawo ma su ruwa da abun sha, sai ma'aikacin gidan marayun ya fara maganar abun dake tafe da su. Sannan ya gabatar da dangin Mummy ga su nan sun zo suna bukatar ganin ta ita da ƴaƴan da ta haifa. Gabaɗaya falon shiru ya yi kamar ruwa ya ci su. Daddy jikinsa ya gama yin sanyi. "Wato tabbas ni ce na auri ƴar uwarku kamar yadda kuka damu tabbaci hakan daga gidan marayun. Kuma mahaifina ya ɗauke ta ne bisa ƙa'ida. Muna zaune da ita har Allah ya albarkace mu da samun haihuwa, muka haifa ƴa mace mai suna Ma'eesha. Wanda a yanzu Ma'eesha tana da shekaru goma sha takwas zuwa sha tara. Kuma sai dai ina mai matukar ba ku hakuri ƴar uwarku ta rasu watanni huɗu da suka wuce." "Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un." Kalmar da suke furtawa kenan lokacin da suka ji labarin mutuwar. Jikinsu ya yi sanyi musamman Alhaji Sulaiman da ƴaƴansa. "To ina ƴar da ta haifa?" Nan ne kowa ya yi shiru don ba mai bakin ba da amsa a cikinsu. Sai da Alhaji Sulaiman ya sake tambaya a karo na biyu sannan cikin sanyin jiki Daddy ya ce "Ban san in da yake ba?" "What? Wanan ma ai zancen banza ne!" Kabir ya faɗa yana miƙewa tsaye. Ita kuma Laila da take tsaye ta bude baki cike da tsiwa ta ce. "Kamar ya zancen banza, nan ba wanda ya san inda take ku je can ke neme..." Kafin ta kai karshen zancen da take son faɗa ta ji saukar lafiyyaen mari wanda ya sa ta wuntsilawa ta faɗi, wani duhu take gani sannan da wani sautin shuu da take ji a kunnenta jin ta da ganinta ya ɗauke na wuccin gadi. Ƙaramar mara kunya, na sake jin kin yi magana a wajan nan." Gabaɗaya falon suka juya suka kalli Captain Kabeer wanda ya yi ma ta marin. "Mamy ina kike ba na ganin komai sai duhu." "Na shiga uku daga magana kake neman makantar mun da yarinya ka kashe ma ta kunne?" A hankali ganinta ya fara dawowa ta sauke isanunta akan Kabeer wanda ko shakka babu ta san cewa shi ne ya mare ta. Kuka take yi tana son ta yi wata maganar amma ta kasa. "Alhaji ka yi ma ni cikkaken bayanin komai domin mu san in da za mu ɓullowa bakin zare. Nan Daddy ya ba su labarin duk abin da ya faru bayan rasuwar mahaifiyar ma'eesha zuwa hukuncin da Mamy ta yanke na aurar da Ma'eesha ga makaho . Da yadda komai ya faru har zuwa ranar da makaho ya dauke ta suka bar gidan ba su sake saka su a idanu. "Wani unguwa suke zaune?" Cewar Alhaji Sulaiman da idanunsa suka kaɗa suka yi ja. "Ba wanda ya san unguwar da suke, ko shi kansa ba wanda ya san in da yake." "Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un." "Amma ka ɗauki ƴa ka ba shi, ba ka san shi ba ba ka san unguwar da yake ba? Dole na shigar da kara akan ku." "Wallahi ba llaifina ba ne, matata ta kawo shawara ni kuma duk da na ƙyamaci abun. A zuciyata amma na kasa hana ta. Duk hukuncin da ta yanke ba na iya cewa komai, duk da a zuciyata ina jin ba daidai ba ne amma ba ma iya cewa komai" "Wanan matsalarku ce idan muka shigar da kara akanku za ku nemo in da take." Mamy hankalinta ya tashi ta rikice . Shiru Falon ya ɗauka kowa ya kasa magana, yayin da ake yi wa Mummy kallon zargi. "Ko z mu iya ganin photon su?" "Eh za mu samu." Cewar jam'i ya nufi dakin da suke ajiye kayan ajiya. Don lokacin da Laila za ta koma ɗakin Ma'eesha fa zama duke kwashe kayan fa basu bukatar su. Suka kai can. Bayan Wai mijina dawo da photon dake manne a bangon ɗakin Ma'eesha.sai wani guda daya na Ma'eesha tana sanye da hijabi ranar da ta yi waliamar saukar Alqur'ani mai girms. Gabaɗaya suka zuba wa photon idanun. Barrister Haidar ya mike tsaye yana cewa. "Wallahi ita ce. Ita ce na gani ba kowa ba, ita ce wallahi na kusa kaɗewa da mota , har Kabeer na ma ta fadar ba ta da hankali ne. Ta ba mu hakuri ta tafi." "Da gaske kake faɗa? To ina kuka ganta kuma ina ta nufa a lokacin.?" "Wallahi ba mu sani ba, amma da dukkan alama tana cikin tashin hankali, yanayin ta ma ys nuns hakan, don idsnunta ma a kumbure suke." "Ko zu mu tafi, amma ku sani da ka amsa za ku amsa kira daga kai har matarka, duk in da kuka kai yarinyar nan sai kin fito da ita. Idan kuma ba haka ba sai kunyi nadamar mafi muni a rayuwarku." Daga haka suka fice daga gidan rai a ɓace.. _Ma'eesha_ Bayan mai nape ya sauke ta s tashar mota ne ta nufi cikin tashar. Wani ya ganta ya ce . "Tafiya za ki" "Eh." "Okay wani gari za ki je?" "Bauchi." "Okay to yanzu ga motar da ke kan layi ba ta cika ba za ki ɗan jira kaɗan." "Ba damuwa." "Bisimillah ga wuri ki zauna." Ya yi magana tana nuna ma ta wani benci dake gefe. Ƙarasawa ta yi ta zauna saman bencin. Kifa kanta a saman cinyarta ta yi tana kuka kasa-kasa. Abubuwa biyu ne suka taru suka cunkushe ma ta zuciya. Na ɗaya ƙwryar da ya yi ma ta na tsawon watanni ba tare da ya sanar da ita gaskiyar lamari ba. Na biyu kuma kishin auren da zai yi. Domin gani take yi ba sonta yake yi. A zaman da suka yi tare da juna. Domin a tunaninta ita ce take son sa amma ba shi ba. Bai ɗauke ta matar aure ba sai yanzu ne yake so ya auri wacce yske so. Sam ta kasa gane cewa yana gani tsawon watanni da suka yi a tare ba ta taɓa tunanin ba makaho ba ne. Sai yanzu wasu abubuwan suke zuwa ma ta akai. Ranar da ta cire kaya a gabansa jikinsa ya dinga rawa kamar mazari. Wanda ko da ta tambaye shi cewa ya yi baya da lafiya ne. Sha surar jikina ne ya kiɗima shi. Da kuma idan za ta cire kaya sai ya yi saurin fita ya bar ma ta ɗakin. Har wata rana ya ce ma ta ta daina cire kaya a gabansa duk da ba ya gani. Sannan ranar da aka yi ruwan sama tana wanka har ta shiga rawar sanyi ta tuɓe kayan jikinta. Ba ta ɗan yana ɗakin ba tana lalube ta ci karo da shi har ya rungume ta ya yi kissing nata. Ga abubuwa da yawa da ya kamata a ce ya zarge shi amma ba ta yi hakan ba. Kuka take yi kasa-kasa. _Haidar_ Yana rungume da photon Ma'eesha da na mahaifiyarta. "Ka san Allah ko Kabeer yarinyar nan ita na gani na kusan kaɗewa da mota." Captain Kabeer dake driving ya ce. "To me ya sa ka bari ta wuce?" "To wata hujja ne da ni da zan tare ta akan cewa ita muke nema? Duk da lokacin da na kalle ta sai da zuciya ta ta buga. Na ji wani abu a raina game da ita. Duk da cewar tana kama da Dada amma hakan ba yana nufin na ce lallai ita ba ce. Ya yi magana yana kallon ta sosai. Fara ce doguwa ba ta da ƙiba. Duban manyan idanunta ya yi har zuwa dogon hancinta da karamin bakinta. "Wallahi kamannin Dada ta ɗauka sai, wata kila ma tafi Fadar kyawu." _JB_ Horn yake dannawa ba kakkautawa wanda duk wanda yake gidan kama daga ƴan gidan zuwa ma'aikatan gidan kowa ya san cewa shi ne ya dawo . Hatta maƙotarsu idan suka ji wanan horn na rashin mutunci sun san shi ne. A guje maigadi ya wangale gate ɗin gidan dan kada ya ɓata lokaci JB ya tafka ma sa rashin mutunci kamar yadda ta saba. A guje ya shigo cikin gidan, bayan ya yi parking dai da ya kwashe mintuna goma a cikin motar bai fito ba. Ko da ya fito daga motar duk wanda ya kalle shi in dai ya san shi to ya san cewa yanayinsa ya canza da akwai abun da ke damunsa. Domin shigowarsa cikin gida ma kawai idan ka gani ka san cewa shi ne kaɗai ya fita Zakka a cikin gidansu. Tura kofar Falon ya yi ya shiga kai tsaye ba tare da ya kalli cikin falon ba ballanta ya ɗan su waye a ciki. Kai tsaye ɗakinsa ya nufa ya tura ƙofar ya shiga ciki. Mahaifiyarsa wacce suke kira da Mimi tana zaune a falon tana tattauna wata magana ita da Yayansa Munnir. Da kallo suka bi shi domin sun ga yanayinsa ya sauya jikinsa a sanyaye yake. "Kamar wani abu na damun Autana." Nima haka na gani Mimi. Allah dai ya sa ba wata maganar ya ɗauko ta dame shi ba." Cewar Munnir din cikin damuwa. "Amin ya Allah, wallahi duk lokacin da Jabeer ya bar gidan nan ba na da kwanciyar hankali har sai na ga dawowarsa. Ga shi baya jin maganar kowa mahaifinsa ya riga ya ɓata shi duk yadda na so gyara shi abun ya ci turaz sai na gyara can sai ka ga ya ɓalle ta nan." "Addu'a za ki cigaba da yi ma sa Allah ya shirya shi." "Addu'a kam ina nan ina ta yi ma ku." "Dare ya yi ya kamata ka je wajan matarka" "Okay bari na je na ji meke damunsa kafin na tafi." Ya tashi ya nufi ɗakin Jabeer, yana kwance ya yi ruf da ciki ba abun da ke ma sa yawo a kansa sai abun da ya aikata wa Sidra. Kukan ta ne ya ke ma da amsa kuwa a kunnenta, abu biyu ya tsaya ma sa rai . Na ɗaya bai taɓa mu'amala da cikakkiyar budurwa ba sai kanta. Na biyu kuma yadda ba da son ranta ba bisa tilas ta amince da hakan. Wanda shi dai dai mace ta kawo kanta da kanta wajansa, kuma ya san duk ƴan hannu ne sun saba, ita kuma fa? Me ya sa Sady baby ta yi masa ƙaryar ciwa ita ma ƴar hannu ce kada ya damu. Bai taɓa nadamar yin zina ba sai yau. kusan a tare Yaya Munnir da mai aikin girkinsu suka nufi ɗakin Jabeer. Ita mai aikin gidan ta jera abincinsa a faranti za ta je ta kai ma sa. Tana shiga da sallama bai amsa ba hakan bai dame ta ba ta saba. Tana kokarin ajiye abincin sanan table dake gaban sofa ya daka ma ta tsawa. "Uban waye ya ba ki iznin shigo min ɗaki?" "Ka yi hakuri abincinka na kawo ma ka." ."idan ba ki ɗauke shi kin fita ba sai na tafka ma ki rashin mutunci banza jaka kawai" Ta fita da sauri ta san shi idan ta tsaya jayayya zai iya kai ma ta duka. "Assalamu alaikum warahmatullah" Munnir ya yi sallama ya shiga. Bai amsa ba idanunsa a lumshe. "Meke damunka duk ka canza?" "Mallam dalla ka fitar mun daga ɗaki, bayan ka gama munafurcinka wajen Mimi ka haɗa ni da ita sanan ka zo kana tambaya ta, to ban sani ba!" Nurmushi Munnir ya yi yana kallon ƙanin nasa yana cewa. "Kai kullum maganarka ina baya ka a wajen Mimi, to ka sani ba abinda nake faɗa mara kyau a gare ka, ka canza halinka idan ba ka ga Mimi ta so ka fiye da kowa ba.". Tashi tsaye ya yi yana yi na da wani kallon banza kafin ya ce "Mallam fitar mun daga ɗakin munafu..." "Tas" ya ji saukar mari a kumatunsa. Rintse idanunsa ya yi ya san ba kowa zai mare shi ba face Mimi ce. "Wai me ya sa ba ka da mutunci ne?" "Da kin ƙyale shi Mimi yana da damuwa na lura da hakan." "Idan yana da damuwa sai ya sauke kan mutane? Tun yaushe mahaifinsa ya dawo kasar nan, yana dawowa shi ya fara tambaya. Ina ka je ne tun safe !?" Bai tanka ma ta ba kuma baya da niyyar yin maganar. Ta bude baki zata fara masifa Mahaifinsa ya shigo yana cewa . "My son Ina ka je ne tun safe wayarka ba ta shiga?" Ganin halin da suke ciki ne ya ce . "Me kuma aka yi ma sa waye ya ɓata ma sa rai? Amma kun san ba na son ɓacin ransa a gidan nan ko? Me ya sa za ki yi ma sa faɗa hakan yaro ai ɗan hakuri ne." Cike da takaici Mimi ta bar ɗakin. Munnir ya mara ma ta baya suka fice. _Jalaluddeen_ Yawo kawai yake yi da mota s garin Kaduna ba tare da ya san in da zai nufa ba. Gefen hanya ya yi parking ga yinwa dake ɗawainiya da shi, wanda rabon da ya ci abinci tun jiya da rana. Kifa kansa ya yi a sitiyarin motar yana tunanin ina ya kamata ya tafi neman ta . Yau kadai gare shi, gobe dole ya koma Abuja bisa umarnin iyayensa. Magana ya fara yi shi kadai kamar wani zararre. "Ina kika tafi Ma'eesha, kewa kwanciyar hankalina, idan kina kusa da ni zuciyata tana samun salama. Ina godiya da Allah ya haɗa rayuwata da taki. Kullum ina kara son ki fiye da jiya. Murmushinki yana sa ranar tawa ta yi haske. Ba kyawunki kadai nake so ba ina son zuciyarki da kyawun halayenki. Ko da mun samu saɓani baya rage irin son da nake yi ma ki. Kece Aminiyata matar da nake son na raba rayuwata da ita har karshe. Ina alfahari da ke, kuma zan cigaba da kula da ke gwargwadon iyawa ta. Na gode da haƙurin ki da kuma ƙaunar da kika nuna ma ni. Ina so na zama wanda zai goge ma ki hawayenki tun kafin su zubo.Ina kike Ma'eesha?" _Fahad_ Dawowarsa gida kenan ya zauna akan kujerar dake Falon sama. Wani karamin box ne a hannunsa ya ajiye gefensa. Fitowar Nadra kenan daga kitchen za ta shiga ɗakinta ta ji ya kira ta . "Nadfah." "Na'am yaushe ka ka dawo.?" Ta yi magana tana karasowa inda yake . " Zo ki zauna kusa da ni." "Lafiya wanan kallo haka kamar za ka cinye ni?" Ya janyo ta ya zaunar da ita saman cinyarsa. "Ina kallon ni'imar da Allah ya ma Ni ne, wani lokaci har mamaki nake yi, me na yi da na cancanci samun mace kamar ki?" Ta yi murmushi. "Yau dai kana nema wani abu a wurina." Dariya ya yi tare da cewa "Ba komai nake nema ba, ina so ne kawai kisan cewa ina son ki ko da ban faɗa kullum ba zuciyata kullum tana fadin haka." "Ni ma ina son ka." "Ki yi ma ni alkawarin idan wani abu ya dame ki ba zaki yi shiru ba, ni ne abokin rayuwarki." "Na yi ma ka alkawari." Ya sumbaci goshinta. Sanan ya dauko wani karamin box din nan da ya dawo da shi ya ba ta . Karba ta yi ta bude. Ɗan kunne da sarƙa ne na gold, har da warwaro da zobe. Zaro idsnunta ta yi sanan ta rungume shi tana cewa. " Allah ya ba ni ikon faranta ma ka rai kullun." "Amin ya Allah, Murmushin ki nake so na gani kowane rana." Murmushi ta yi. "Tare de Farida za mu je America." Take murmushin dake kan fuskarta ta gushe. "Ya dai ko akwai matsala ne?" Murmushin karfin hali ta kirkiro tana cewa "Ba komai Allah ya kai mu." "Amin ya Allah. Don Mama ta ce ba ta yarda na bar ki a ƙasar nan ba tare da ke ba umarni ne ta ba ni." _Mamy_ Gabaɗaya sai sintiri take yi a falon ta, sakamakon rashin ganin Ma'eesha. Don Jamil ya faɗa ma ta cewa ya je gidan bai samu Ma'eesha ba an ce ba gidan suka kwana ba daga ita har mijin nata. Dama ta ki faɗa ne don ba ta son Ma'eesha ta hadu da dangin mahaifiyar ta. Musamman da ta lura manyan mutane ne karshen wahalar Ma'eesha zai kare. Shi ne ta tura Jamil ya je ya duba ko Ma'eesha na gidan ya je ya dawo ba ta nan. Cikin tashin hankali ya Jamil ya shigo falon yana cewa. "Dangin Mahaifiyar Ma'eesha fa sun shigar da kara akan ke da Daddy, yanzu haka ana bukatarku a offishin ƴan sanda." "Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un na shiga uku na lalace, yanzu ina zan nemo makahon nan a kama shi ya fito ma su da ƴarsu." *To Alhamdulillah, nan na kawo karshen littafin MAKAHO NE book 1, kuma shi ne free pages, book 2 kuma paid book ne. Normal group ₦500 ne posting sai ɗaya a rana. VIP group kuma 1k ne, posting sai biyu a rana, da ya zama complete shi ma kudinsa 1k ne. Sai s tura kudin ta wannan account number 2242538358 sai s tura shaidar biya ta wanan account number. 09065327995* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 49 of 49