wace ce ba amma na san za ki gane ta ke, mu tafi tare."
Shiru Mama ta yi kafin ta sauko daga kan gadon ta saya hijabi suka fita shi kuma Bana yana sanye da jallabiya a jikinsa.
Bayan security ya ba wa Sidra damar shigowa ta shigo tana kalle-kallen don gidan ko ina fitilu ne.
Main door ta nufa tana tsaye tana shakkar yadda za ta buga ma su kofa, sai ta ga an bude kofar. Baba da Mama ta gani tsaye suna kallonta.
Durƙusawa ta yi tana kuka yayin da Mama ta ce.
"Sidra?"
Sai a lokacin Baba ya gane ta .
Cikin kuka ta ce.
"Baba dan Allah ka taimake ni Abba ya kore ni, ƴan uwansa na sun kore ni ba na da wajen zuwa, dan Allah ka taimake ni ka ba shi hakuri ya yafe ma ni na koma gida."
Shiru Baba ya yi kafin ya ce.
Yanzu ransa a ɓace yake akan abin da kika aikata , ba zai saurare kowa ba, don haka ki zauna a nan zuwa wani sati idan na dawo daga ƙasar Germany zan je na roƙe shi ya yafe ma ki."
"Na gode Baba Allah ya saka da alheri. "
"Amin ya Allah, gobe da safe zan bar kasar idan na dawo sai kin fada mani in da kika je da kuma dalilin da ya sa kika tafi kafin na je na roƙe shi."
Kallon Mama ya yi tare da cewa.
"Hajiya a kai ta ɗakin baƙi a ba ta abinci ta ci ta kwanta."
"To Alhaji "
Mama ta fada tana cewa Sidra.
"Tashi mu tafi."
Baba ya nufi part ɗin sa yayin da Mama ta yi wa Sidra jagora zuwa daya daga cikin ɗakunan da suke saukar baƙi.
Daki ne wanda aka komai da komai na buƙata gado wardrobe mirror T.V da fridge. Ga toilet a ciki.
Mama ta kalli Sidra ta ce.
"Nan za ki zauna, bari na kawo ma ki abinci."
Daga haka ta fita don zuwa kitchen, ruwan semovita ya rage a cikin kula kuma tuwon da zafi da da miyar egusi da ya ji nama da ganda.
Kawo wa Sidra ta yi sannan ya ce .
"Akwai ruwa da lemu a fridge, don dama an zuba komai saboda baƙi da suka wuce yau."
Godiya Sidra ta ya wa Mama sannan mama ta fita.
Dama yunwa take ji ta buɗe fridge ta dauki bottle water da lemu ta wanke hannu ta ci tuwo.
Bayan ta gama ne ta ajiye kayan q gefe ta shiga bathroom ta yi wanka. Ta fita ta sanya kayan barci ta kwanta.
*Washegari*
Bayan Nadra ta gama aikin gyaran gidan da ta saba yi ya rage ɗakin Fahad ya rage ta gyara.
Kitchen ta nufa don ɗora breakfast sai ta ji alamar tafiyar mutum.
Tana juyawa ta gan shi yana fitowa ɗakinsa hannunsa rike da waya yana cewa.
"Ka yi hakuri Baba na macen yau ne tafiyar ta ka, da na kawo ma ka ita ka ganta. Amma duk da haka akwai sauran lokaci bari mu zo yanzu sai ta gaishe ka kafin ka tafi."
Daga nan ya katse wayar ya karasa kitchen ɗin .
Yana tsaye bakin kofar kitchen ɗin ta juyo suka hada idanu ya kalle ta daga sama har ƙasa. Kuma lokacin ma hijabi ne a jikinta.
Durƙusawa ta yi ta gaishe shi cikin girmamawa.
Bai amsa ba ya basar da ita. Cigaba ta yi da kokarin wanke tukunya za ta kunna gas ya ce .
"Ki je ki shirya za mu je ki gaida Baba zai yi tafiya da safen nan."
"To."
Ta ce tana ajiye tukunyar ya fito ita ma ta bi bayansa.
Ɗakinsa ya nufa ita ma ta nufi ɗakinta.
Rigar Abaya ta saka kasancewar kayan lefen ba hijabi ko ɗaya, kasancewar Sidra ba ta saka hijabi.
Ita kuma hijabin da ta zo da shi dama guda ɗaya ne na jikinta da ta zo da shi. Don ko kayan gidan iyaye Sidra ba ta ɗauki hijabi ba.
Ganin babu hijab ya saka Nadra ba ta da wani zaɓi saka Abaya mai ruwan ƙasa ta yi rolling kanta da mayafin abayar.
Ba ta yi kwalliya ba powder kawai ta shafa sai lips glow ta yi kyau ta fito kamar baƙar balarabiya.
Handbag ɗin ta ta dauka ta saka wayarta a ciki da wasu ƴan kuɗaɗe cikin na sadakinta ne ta ɗauka.ta zo wajen ɗaukar takalma, sai dai duk takalmomin zaɓin Sidra ce don dogaye ne ma su tsini, wanda ita kuma Nadra ba ta iya tafiya da dogon takalmin ba.
Tana tsaye tana neman mafita ya shigo ɗakin, kallonta ya yi ganin ta shiga har handbag ta dauka ya ce.
"Me kike jira?"
"Takalmin da zan saka nake nema. Ƙarasowa ya yi ya kalli takalmomi da ke wajen da sun kai kala goma sha biyar ya ce.
Duk takalmin da suke nan ba wanda ya ya ma ki, sun yi amma suna da tsini ba zan iya tafiya da su ba."
Hannu ya saka ya ɗauki wani bakin takalma ya ajiye q gabanta.
"Ki koyi tafiya da su daga yau."
Za ta yi magana ya wurga ma ta wani kallo wanda ya saka dole ta yi shiru ta saka haka nan, tafiya ta fara yi kamar mai tausayin ƙasa.
Ya yi gaba tana binsa a baya suka fice .
Har ya suka fito ya rufe kofar gidan yana zaune cikin motar yana jiranta ta karaso tana tafiya kamar mai yanga.
Yana zaune a mazaunin direba ta shiga ta zauna gefensa.
Ba tare da wani ya yi magana cikin su ba ya yi wa motar key suka bar gidan.
*Mamman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page3️⃣4️⃣
Ba tare da wani ya yi magana cikinsu ba ya yi wa motar key suka bar gidan.
Driving yake yi cikin nutsuwa yana kallon hanya, har suka ƙarasa gidan bai ce uffan ba, haka ita ma ba ta ba har suka ƙarasa bakin tangamemen gate ɗin gidan.
Horn ya yi security ya zo ya wangale ma sa gate ɗin gidan, ya shiga ya yi parking lot.
Kusan a tare suka fito daga cikin motar, ma'aikatan gidan da suke nan suka fara gaishe su, Fahad ɗin kam bai amsa ba ita Nadra ce take amsawa cikin girmamawa kasancewar ta ga duk sun girme ta.
Tafiya take yi a hankali sakamakon takalmin da ba ta saba amfani da irin su ba.
Ƙararrawar ƙofar ta danna, sai ga ɗaya daga cikin masu aikin gidan ta zo ta buɗe ma su ƙofar.
Ganin Fahad da Nadra ya saka ta gane cewa ita ce Amaryarsa.
"Sannu da zuwa yallaɓai ."
Bai amsa ba sai kokarin shiga ciki yake yi, ganin bai amsa ba kuma dama sun saba da halinsa. Cikin sakin fuska ta gaida Nadra.
"Sannu da zuwa Aunty."
Murmushi Nadra ta sakar ma ta tare da cewa.
"Yauwa Barka da safiya ya kike?"
"Alhamdulillah."
Part ɗin Mama Fahad ya nufa. Ba kowa a falon Maman don haka ya nufi bedroom ɗin ta.
Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga. Cak ya tsaya yana rike da handle ɗin kofar sakamakon ganin Sidra tana gaisawa da Mama.
Take fuskarsa ya sauya kamar wanda zai yi aman wuta.
Take ya juya ya fice daga ɗakin.
Mama na ganin haka ta san cewa saboda ganin Sidra ne ya ɓata masa rai.
Don haka sai ta bi bayansa tana cewa Sidra tana zuwa .
Lokacin da ya fito Nadra na zaune a falon ita kaɗai.
Bai kalle ta ba ta nufi part ɗin Baba, da kallo ta bi shi tana mamaki mai ya canza yanayinsa lokaci ɗaya.
Mama na fitowa ta ga Nadra zaune a falo, murmushin jin daɗi ta sake tare da cewa.
"Daughter dama tare kuke?"
Murmushi Nadra ta yi tare da sauka daga kan kujerar cikin girmamawa ta gaida Mama. Ita ma ta amsa ma ta cike da farin ciki da jin daɗi..
Hannunta Mama ta riƙe sannan ta ce .
"Mu je ki gaida Babanku kafin ya wuce ko?"
Tashi Nadra ta yi Mama na rike da hannunta suka nufi part ɗin Baba.
Yana zaune a falo sakan kujerar yayin da Fahad ke zaune a kukerar dake fuskantar Baba sai Farida da Rumaisa da suka saka Baba a tsakiya kowa tana fadin abinda da zai dawo ma ta da shi.
Mama ta turo kofar ta shigo da sallama, Nasara ma sallama ta yi gabaɗaya .
"Ga Daughter ɗin ka ta zo gaishe ka."
Murmushi Baba ya yi tare da cewa.
"Ma sha Allah, Daughter ƙaraso mana ."
Cikin sanyin jiki take tafiya ta karasa gabansa ta durƙusa ta gaishe shi.
"Ina kwana Baba?"
"Lafiya lau ya kike?"
"Alhamdulillah."
Tashi daga ƙasa ki hau saman kujera, ba ki ga ƴan uwanki duka a sama suke zaune ba, ba ruwan mu fa ki zauna duk ɗaya ne."
Sai a lokacin ta kalli Fahad, Rumaisa, Farida da duka suke zaune a saman kujera, sai sai ita ba za ta iya ba, don haka ya zauna a kasa saman Centre carpet ta ce .
"A'a Baba nan ma ya yi."
Mama ma ta saka baki ko za ta hau sama ta ƙi yarda ta zauna a ƙasa. Lokaci guda ta sake shiga ran Mama da Baba.
Ruamisa ce ta kalli Nadra cike da tsokana ta ce.
"Matar Yaya ina wuni?"
Nadra ta kalle ta ta ce .
"Ina wuni Aunty Ruamisa?"
"Ba na ce ki daina ce ma ni Aunty ba ni ƙanwarki ce tun da ƙanwar mijin ki ce ni ai na zama ƙanwarki ka ajiye zancen na girme ki."
Murmushi kawai Nadra ta yi ta kalli Farida da ke ma ta kallon banza, ba tare da damuwa ba ta ce.
"Ina kwana?"
"Lafiya."
Ta amsa a daƙile.
Murmushi Mama ta yi ta ce ce kin gane kowa ko?"
Ta nuna Rumaisa ta ce.
"Wanan ita ce kanwar mijinki ita ke bin sa sunanta Rumaisa."
Sannan ta nuna Farida ta ce.
"Wannan kuma cousin sister ɗin mijinki ce ɗiyar ƙanwata ce sunan ta Farida, a nan gidan take zaune tare da mu."
Kai Nadra ta jinjina sannan ta ce.
"Na gane Mama."
"Mu je mu yi breakfast kafin ka rasa jirgi ko?"
"Haka ne, to Bismillanku."
Daga haka suka mike tsaye ban da Nadra, sai da Rumaisa ta ja hannunta suka fara tafiya a tare.
"Ki saki jikinki matar Yaya."
A dinning table suka hallara dukansu Baba ne ya yi magana ta ce.
"Ina Sidra ba ta tashi ba ne?"
Jin sunan Sidra sai da gaban Nadra ya faɗi, amma ba ta yi magana ba ta yi shiru.
Ma ce ta ce.
"Ta tashi har ta shigo ɗakina."
Kafin wani ya yi magana ne suka fara jin takun takalmi ƙwas ƙwas ƙwas. Gabaɗaya suka juya suna kallon mai zuwa.
Sidra ce sanye da sanye da doguwar riga English wear tana tafiya idnsunta na kan Fahad sam ba ta lura da Nadra ba.
Kallo ɗaya ya yi ma ta ya dauke kai tare da kau da kansa gefe yana tsuke fuska.
A zubure Nadra ta mike tsaye cike da jin daɗi ta nufi Sidra tana cewa.
"Aunty Sidra, kece? daga ina? Yaushe kika dawo kina lafiya?"
Ta karasa gare ta ta rungume ta ƙam a jikinta tana sakin kuka.
Murmushi Sidra ta sake wanda ya tsaya iya saman lips ɗin ta.
"Aunty ina kika je kika bar mu cikin tashin hankali, Umma har rashin lafiya ta yi."
Sidra dai ba t ce komai ba, ganin Nadra za ta sake jefo ma ta wata tambayar wanda kuma ba ta son ta amsa ma ta a gaban kowa ya saka ta ce .
"Zamu yi magana anjima, yanzu mu je mu yi breakfast."
Murmushi Nadra ta yi tana goge hawayan da ya wanke ma ta fuska. Garin cikin kawai take ciki sakamakon ganin ƴar uwar ta cikin ƙoshin lafiya.
Zama suka yi a saman kujera yayin da Nadra gabaɗaya hankalinta na kan Ƴarta.
Ita kuma Sidra idan ta ga alamar Nadra za ta yi ma ta magana sai ta girgiza ma ta kai alamar a'a. Sakamakon ba ta so ta jero ma ta wasu tambayoyin da ba za ta iya amsa ma ta su a gaban ahalin gidan Majidaɗi ba.
Babu abun da Fahad yake hangowa a cikin idanun Sidra sau sallar soyayyarsa. Shi kuma ya ɗaukar wa ransa alkawarin sai ya musguna ma ta ya cusa ma ta baƙin ciki
_Ma'eesha_
Ganin makaho tsaye yadda ta bar shi ne ya saka ta saka wa ranta cewar bai ji komai na maganar da suka yi da Abdul.
Kallonsa ta yi duk da lokacin da ta kalle shi sai da gabanta ya faɗi, sakamakon ganin fuskarsa cikin irin yanayin da ba ta taɓa ganinsa ba. Da ƙyar ta iya magana ta ce .
"Am dama kana nan tsaye ba ka zauna ba har yanzu."
Bai tanka ta ba kamar tana magana da dutse.
Ganin haka ta saka ta janyo hannunsa ta zaunar da shi a saman tabarma.
"Mijina lafiya kuwa na ga yanayinka ya sauya?"
Shiru bai ce uffan ba karshe ma tashi ya yi ya shiga ɗaki, sandarsa da yake dogarawa yana tafiya ta ƙalla tana sauke ajiyar zuciya.
Bin bayansa ta yi zuwa cikin dakin ta ga yana laluben jakar kayansa.
Ya ciro wasu kaya sannan ya zuge zip ɗin.
Gane wanke zai yi ya saka ta fita da sauri, ruwan zafi da za ta hada ma su tea da shi ta juye a bokiti ta sirka da ruwan sanyi ta kai ma sa banɗaki.
Ko da ya fito yana laluben bokiti sai ta ce.
"Ranka ya daɗe na kai ma ka ruwan banɗaki."
Bai ce komai ba ya nufi banɗakin da kayan da ya ciro a jaka.
Wani ruwan zafi da dafa tana kokarin hada ma su shayi da bread. Don yau babu ƙwai kuma ba ta da kuɗin siyen ƙwai dan kudin ta sun ƙare daga ita dai ɗari biyar da ya rage ma ta.
Ya fito daga wankan ya canza kaya wanda ya cire kuma ya zo zai ɗebi ruwa zai wanke ta yi saurin cewa.
"Ka bar shi zan wanke."
"Na gode amma zan yi da kaina."
"Ni kuma ba zan bari ka yi da kanka ba, ko ba ka so na samu lada da albarkar da ke tattare da yi wa miji wanki ne?"
Bai ce komai ba ya lalubi sandarsa ya shiga ɗaki daidaito lokacin da take haɗa tea.
Fitowa ya yi da kayan aikinsa na gyaran takalma zai fita.
Kallo ɗaya za ka yi wa fuskarsa ka karanci damuwa da yake ciki. Ganin ya nufi hanyar fita bai yi ma ta sallama kamar yadda ya saba ba ne ya saka ta ɗauki kofin tea da ledar bread ta nufi kofar fita ta bi bayansa da sauri.
Shan gabansa ta yi ta kafa ma sa kofin a baki tare da cewa.
"Bismillah ka sha ko kadan ne kada ka fita ba ka ci komai ba."
Kau da kansa gefe ya yi ya ce.
"Ina azumi."
"Azumi shi ne ba ka faɗa ma ni ba?"
"Na macen ne ki yi haƙuri."
"Ko na ɓsta ma ka rai ne ka gafarce ni tuba nake kaina bisa wuyana."
"Ba komai kada ki damu."
"To Allah ya tsare ma ni kai ya kare ma ni kai, Allah ya kusanta ka da halal ya nisanta ka da haram, Allah ya haɗa la da alkhairinsa ya nisanta ka da sharri dan albarkacin nabiyyun rahmati."
Haka kawai ta ji kaso hamsin na damuwar da yake ciki ya ragu, cikin murya mara amo ya ce .
"Na gode."
Daga nan ya fice daga gidan tana kallonsa lokaci ɗaya take murmushi kuma take kuka ta ce.
"Alhamdulillah ala kulli halin."
(A rayuwar aure ko soyayya, akwai abu guda da ya kamata mace ta gane:
Ko wani namiji yana da irin nasa hali Kuma yadda yake sonki, haka yake nuna fushinsa idan wani abu ya ɓata masa rai.Ba wai saboda baya sonki ba ne, a’a, saboda ya damu da ke sosai,Don haka ke dai ki fahimci irin namijin da kike tare da shi. Idan mijin kirki ne, zai yi fushi saboda yana son ki gyaru, ba don ya cutar da ke ba. Idan mai saurin ɓacin rai ne, ki gane cewa yana magana ne da zuciyarsa, ba wai yana ƙin ki bane, Idan mai shiru-shiru ne, fushinsa yakan zama nesa da magana, amma zuciyarsa tana cike da damuwa, Idan mai gaskiya da tsauri ne, yana fushi saboda ya san abin da ya dace da abin da bai dace ba.
Idan mai tausayi ne, fushinsa zai zo da nutsuwa, amma zai so ki gane kuskurenki ba tare da ya takura miki ba, a kowane hali, rarrashi na mace shi ne sirrin da ake so. mace ta sani, Ki saurari damuwarsa ba tare da tsawatarwa ba, Ki nuna masa kin gane abin da ya dame shi.
Ki yi magana cikin ladabi da natsuwa,Ki yi masa nasiha cikin taushi, ba da jayayya ba,Ki nuna masa kulawa, ko da da kananan abubuwa ne. Na Miji baya buƙatar mace cikakkiya.
Yana buƙatar mace mai fahimta.)
_Nadra_
Suna cin abinci amma ita kasa cin abincin kirki, zuciyarta fara tas ta ji ma ta ƙoshi, burinta ɗaya ta keɓe da Sidra ta ji me ya faru da ita.
Bayan sun kammala breakfast Baba ya kalli Nadra ya ce .
"Daughter ina fatan ba matsala ko?"
Kai ta sunkuyar tana Murmushin ta ce .
"Ba komai Baba."
"Ko akwai magana ne mu keɓe kafin ta tafi?"
"A'a Baba ba komai."
"To ba abinda yake ma ki da bakya so? Kada ku dubi idanunsa."
"Ba komai Baba."
Sai a lokacin Fahad ya ce .
"Baba ni ba za ka tambaye ni ba sai ita?"
Dariya Baba ya yi yana cewa.
"Ba zan tambaye ka ba, dan wannan baiwar Allah ba za ta ma ka laifin komai ba."
Gabaɗaya suka saka dariya ban da Sidra.
Baba ya kalli Nadra ta ce .
"Daughter zan ba ki gift na aure da na so washegarin auren na ba ki abubuwa suka saka na manta."
Kallon Fahad ya yi ya ce .
"Ka kai ta wajen Alhaji Murtala mai siyar da mitaoci ta zaɓi duk irin motar da take so ."
Gabaɗaya suka saka dariya suna taya ta godiya in ban da Sidra da take yin yaƙe (masomin kuka) Nadra ta rasa mai za ta ce sai hawaye, nan aka hau yi ma ya dariya. Sallama Baba ya yi masu ya wuce yayin da Fahad ya dauki jakar Baban suka fita tare dan yi ma sa rakiya.
Daga nan kowa ya watse Mama ta nufi part ɗin Baba dan ta gyara ma sa.
Ya rage saura Sidra, Nadra, Farida da Rumaisa.
Farida sai kallon banza take yi wa Nadra kafin ta mike ta nufi ɗakinta.
Sidra ta nufi ɗakin Mama don can ta bar wayarta sai ta shiga ɗakin dan ta dauki wayar. Ganin haka ya saka Nadra ta bi bayanta.
Bayan Sidra ta dauki wayar ne sai ga Nadra ta shigo . Kwallonta Sidra ta yi ta ce .
"Lafiya ?"
"Lafiya kau Aunty, dama wata tanabya zan ma ki."
Taɓe baki Sidra ta yi kafin ta ce.
"Ki ajiye tambayoyin ki Sai kin fara amsa ma ni nawa tambayoyin tukuna."
Gyara tsayuwar ta ta yi kafin ta ce.
"Yanzu Ashe ƙanwa na iya cin amanar Yayarta?"
Cikin rashin fahimta ta ce .
"Wace kanwa kike magana akai?"
Nuna ta da yatsarta ta yi kafin ta ce.
"Ke nake nufi maciya amana, yanzu ke da kanki za ki iya cin amanata?"
"Aunty Sidra ta ina na ci amanarki?"
"Wace ce matar Fahad a yanzu haka?"
"Ni ce amma wallahi sunan dai ina matarsa ce kawai."
Tsuki Sidra ta yi kafin ta ce.
"Ko da a ce ba na nan yadda kika san ina masifar son Fahad ko da kin ga za'a aura ma sa wata ke me tsaya ma ni ne, amma abun takaici ke ce da Kanki kika aure shi.
Hawaye ne ya wanke ma ta fuska ta ce .
"Wallahi ban san komai ba, ban san abun da ke faruwa ba a ranar auren, ban san cewa kin gudu ba, cewa aka yi kin tafi gyaran jiki, har aka daura aurena da Yaya Fahad ban san da ni aka daura ba, komai ɓoye ma ni aka yi, sai bayan da aka kammala komai dare ya yi ne ake sanar da ni komai. Ba na da wani zaɓi Aunty Sidra, ba zan iya jayayya da hukuncin iyayena ba kin sani, sanin haka ya saka Abba ya aurar da ni ba tare da shawara da ni ba. Kuma ba zaman aure na mata da miji muke yi ba sunan dai an yi auren..."
Shiru ta yi sakamakon ganin Fahad ya shigo ɗakin.
Nadra ta goge hawayenta ta ƙarasa gaban Fahad ta ce.
"Yauwa Yaya Fahad ka sanar da ita komai ka sanar da ita ban ci amanarta ba, ka sanar da ita ba wani abu da ya shiga tsakani na da kai, ai ko hannuna ba ka taɓa rike wa ba ko?"
Wani wulaƙantaccen kallo Fahad ya wurga wa Sidra, kafin ya dauke kai ya kalli Nadra ya saki wani mugun murmushi sannan ya ce.
"Haba sweet heart meye na damuwa akan abun da bai da mahimmanci? Ki daina ɓata ranki ko don ajiyar babyn da na ba ki."
Ya yi maganar yana shafa cikinta ya kashe ma ta idanun ɗaya.
Ba ta gama fita daga mamakin Fahad ba sai da ta ji saukar tattausan laɓɓanta akan pink lips ɗinta. Zaro idanu ta yi lokacin da ta ji bakinsa a cikin nata yana ma ta wani irin tsotsa kamar wanda ya samu sweet.
Sidra zare idanunta ta yi wanda ta fara ganin Fahad da Nadra bibbiyu yana kissing ɗin Nadra cike da ƙwarewa.
Kanta ta dafe da ta ji kamar yana barazanar tarwatse wa, cikin tashin hankali ta dafe bangon ɗakin yayin da wayar da ke hannunta ya suɓuce ya faɗi ƙasa.
*Naman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*SANARWA*
Wannan ƙirƙireren labari ne, ban rubuta ta ba shi dan wani ko wata ba, idan suka ko hali ya zo ɗaya to a gafarce ni arashi ne mai kashe auren wawa.
*SADAUKARWA*
wannan shafin sadaukarwa ne ga members na MAKAHO NE FAN GROUP, da kuma MAMAN IHSAN NOVEL GROUP ina matuƙar godiya da ƙauna fa kuma tarin addu'o'i da kuke yi ma ni na gode Sosa Allah ya bar ƙauna much love😘
page3️⃣5️⃣
Sidra zare idanunta ta yi wanda ta fara ganin Fahad da Nadra bibbiyu yana kissing ɗin Nadra cike da ƙwarewa.
Kanta ta dafe da ta ji kamar yana barazanar tarwatse wa, cikin tashin hankali ta dafe bangon ɗakin yayin da wayar dake hannunta ya suɓuce ya faɗi ƙasa.
Nadra ganin abun take yi kamar a mafarki ta fara ƙoƙarin raba bakinta da nasa amma dai ya riƙo ƙugunta ta manna da jikinsa ya zagaye ƙugun nata da hannu ɗaya ɗayan hannunsa kuma ya tallabo ƙeyarta da shi.
Sosai yake kissing ɗin bakinta ya ziira harshensa cikin bakinta yana ma tsotson harshenta a hankali, duk yadda Nadra ta so ƙwatar kanta ta kasa.
Fahad kam tsintar kansa ya yi a wani baƙon yanayi, take ya fara jin ƙafafunsa sun daina ɗaukarsa.
Daidai lokacin Sidra ta fice daga ɗakin tana tana jin kamar zuciyarta za ta tarwatse.
Yana jin ƙarar buga ƙofa alamar ta fita daga ɗakin ne ya saki zare bakinsa daga cikin na Nadra tare da sakin ta.
Idanunsa har sun fara canza launi zuwa ja.
Hawaye ne ya gani yana bin fuskar Nadra.
Bai kula ta ba ya nufi hanyar fita, har ya kai hannu zai bude handle ɗin kofar ta ji ya ce
"Idan har na sake jin kin yi wa Yayarki makamancin maganar da kika yi ma ta yanzu sai na ba ki mamaki. Ko da wasa kada ki sake nuna ma ta cewa ba rayuwar aure muke yi kamar kowace mata da miji ba. Akan me za ki faɗa ma ta irin zaman da muke yi ?"
Cikin kuka ta ce .
"Saboda tana son ka ta damu da auren da muka yi har tana ce Mani maciya amana kuma ba haka ba ne."
"To tun da ba haka ba ne meye na damuwa.?"
"Ta shiga wani hali saboda aurena da kai tana son ka kai ma kana son ta."
"Ba na ɗin ta kuma!"
Ya faɗa yana dakawa Nadra tsawa wanda yanda ta firgice.
"Kada na sake jin kin ce ina son ta, daga ranar da ta gudu a ranar aurena da ita na cire ta daga cikin rayuwata. Domin Fahad Majidaɗi idan ya bar abu ya bar shi kenan har abada. Ba na dake waiwayarsa, har gaban abada kada ki yi tunanin Fahad Majidaɗi idan har ya bar abu zai dawo ya dauke shi ba. Har gaban abada idan ba bar waje ko wani abu kada ki yi tunanin zai dawo gare shi a karo na biyu, idan har na riga na yi nisa ba na jin kiran kowa, ajina ya wuce da mace za ta bar ni a lokacin da ta ga dama Sannan ta yi tunanin idan ta dawo zan waiwaye
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 49