Share this page
ma ai sakarcin ka ne ya saka ka bari ya gan ka, kai ba ka san yadda za ka iya takunka ba?" "Yarinyar dai maƙura ce a wajen kyau, sai ka ce aljana ce ita?" Da sauri ta kalle shi ta kuma kalli hoton dake wayar ta zuba wa fuskar Ma'eesha idanu tana kallon kyakkyawar fuskarta wacce kyawun yarinyar sai da ya firgita ta. Ta kalli hannunsu dake sakale cikin na juna, shi yana sanye da baƙin glass ita kuma tana sanye da doguwar rigar Abaya. Tsuki ta ja kafin ta ce. "Kuma ba ka tunanin cewa ita yarinyar abokinyar aikinsa ce?" "Madam ba na tunanin abokinyar aikinsa ce domin a tarihi Jalaluddeen baya aiki da kowa, shi kadai yake aikinsa duk hatsari aikin kuwa." "To ka ce a wani gida yake zaune da yarinyar ko?" "Ƙwarai kuwa." "To me ya sa wanann karon bai kama hotel ba?" "Madam a farko a hotel yake zaune daga baya ne ya daina kwana a hotel yake kwana a gidan shi da yarinyar." Kallon mamaki take yi ma sa kafin ta ce . "Kana nufin a gida ɗaya yake kwana da yarinyar?" Ƙwarai kuwa Madam sai kin ga gidan, gida ne na ƙasƙantu miskinai, kai wannan ma ba zan kira shi da gida ba sai sai akulki ko kango. Don wallahi ko gidan da kike kiwon karnuka ya fi wanan gidan sau dubu." "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Yaushe Jalaluddeen ya zama haka? Rabon da ya kira ni a waya ma na mance kuma ko na kira shi baya shiga. Amma na san inda zan bi na san komai." Ta yi maganar tana haurawa upstairs, ba dadewa ta fito riga da handbag da mayafinta, da hannu ta yi wa Jimoh alamar su tafi. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 5️⃣2️⃣ Ta yi mahada tana haurawa upstairs ba daɗewa ta fito riƙe da handbag ɗin da mayafinta, hannu ta yi wa Jimoh alamar su tafi. Suna fita ta rufe ƙofar direbanta na ganinta ya taso da sauri, ta ɗaga ma sa hannu cike da izza, dole ya koma. Jimoh na bin ta a baya ta nufi wata tsadaddiya mota ta nufa yana bin ta a baya, key din motar ta mika ma sa ya karba ya bude ma ta bayan motar ta shhga ta zauna. Zagayawa ya yi mazaunin direba ya shiga ya yi wa motar key, horn ya yi maigadi ya wangale ma sa gate suka bar gidan. _Fahad_ Yana fita daga part ɗin Mama part ɗin Baba ya nufa, saboda ya san shi kadai ne idan ya yi ma sa Maganar komawarsu gidansu zai ce su tafi ba tare da Mama ta yi gardama ba. Don ya lura yanzu Mama so take ta hana ma sa matarsa. Da sallama ya shiga falon Baba, cikin sa'a kuwa ba kowa sai shi kaɗai yana duba wasu documents. Baba ya amsa ma sa sallamar yana cewa. "Ambassador kai ne ?" "Eh Baba." Ya zauna saman Centre carpet ya yi shiru. Ganin shirun da ya yi ne ya sa Baba fahimtar akwai magana a tare da shi. Tattara hankalinsa wuri ɗaya ya yi ya ce. "Kamar akwai magana a bakinka ko?" Ɗan sunkuyar da kai ya yi kafin ya ce. "Dama ina son mu koma gidanmu ne?" "To In ban da abun ka wanan ai ba wani abu ba ne, ka ɗauki matarka kawai ku tafi ma na." "Am dama dai Mama ce na ga kamar ba za ta amince ba." "Kan wani dalili za ta hana ka ɗaukar matarka?" Wayarsa ya dauka ya lalubo lambar wayar Mama ya danna ma ta kira. Bugu biyu ta ɗaga tana yi ma sa sallama. "Assalamu alaikum." "Wa'alaiki Salam, ki zo part ɗina ina son ganinki." "To Alhaji." Ta kashe kiran wayar tana kallon Aunty Rahama da Inna da suke firar kallon da Fahad ke bin Nadra da shi suna dariya. "Bari na je Alhaji na jira na." Tana faɗar haka ta mike don zuwa amsa kiran wayar Baba. Koda shiga falon Baba ta tarar da shi da Fahad ne a falon. Tun da ta shigo kansa yake a ƙasa ba ta kawo cewa shi ne ya zo da Baba da wata maganar ba. Zama ta yi kan kujerar da Baba yake zaune, kujera mai zaman mutum uku ne. "Barka da hutawa Alhaji." "Yauwa Barka dai ya gidan?" "Alhamdulillah." Shiru ne ya biyo baya kafin ya katse shirun da cewa. "Yaushe Fahad da matarsa za su koma gidansu ne, tun da ya dawo ai zamanta ya kare a nan sai ta koma ɗakin mijinta ko?" Kallon Fahad Mama ta yi ta gane cewa shi ya kawo wa mahaifinsa zancen. "Au har ka kasa jurewa ka kawo ƙarata ne tun yanzu? Ashe ba za ka iya jure wa ba, da wuri haka?" "To wane dalilin zai sa ki hana ma sa matarsa ma?" "Alhaji idan na ba ka labarin abun da yaron nan ya yi wa yarinyar nan za ka goyi bayana. Ni na yanke shawarar ma gara ya sake ta kawai tun da ba son ta yake yi ba." "Subhanallah me ya kawo wanan zancen kuma? Ba na son na sake jin makamancin wannan zancen, Fahad ko da wasa idan ka saki Nadra za ka hadu da mummunan ɓacin raina." "Alhaji ka tsaya ka saurare ni ina da dalilin da ya sa na ce ya sake ta. Aure ibada ne amma idan da cuta barinsa halal ne." "Wacce hujja kike da ita da za ki ce ya saki matarsa." Murmushin takaici ta yi kafin ta ce. "Hujjoji ma nake da su ba hujja ba. Hujjata ta ɗaya yaron nan da bakinsa ya ce baya son yariyar nan zai sake ta, na biyu na sanar da kai abinda ya yi ma ta a ranar da ta kwana a ɗakinsa, sannan ya saka ƙafa ya bar ta cikin halin jinya bai taɓa kiran wayarta ya tambaye ta jikinta ba. Kuma bai taɓa kiran wani ya tamabaye ya jikinta ba, tsawon watannin da ya yi a can mulkin nuna waya bai taɓa tamabayar ta ba. Sai yanzu da ya dawo ya ce ta bi shi saboda zalunci to ba za'ayi wannan da ni ba, ba zai iya yi ma ta adalci ko tausaya ma ta ba." Shiru falon ya ɗauka na tsawon mintuna biyu kafin Baba ya ce. "Fahad ba ka kyauta ba gaskiya, ba'a haka, ai ko dabba ce ka siyo ai ka dinga duba lafiyar ta, idan ba ka nan dole ka nemo mai kula da ita ballantana bil'adama. Ta ya za ka wofantar da yarinyar da aka ba ka amana? Ban tsammaci haka daga gare ka ba." Sai a lokacin ya daga kansa yana cewa. "Baba don Allah ku yi hakuri, ba yadda ake tunani ba ne, duk da ban kira ya kuma ban tamabaye kowa ita ba amma ina kula da ita duk wani motsi nata akan idanuna take yin sa, ina kallonta, kuma na tabbatar tana cikin ƙoshin lafiya. Gabadaya hankalina yana kanta tun da na bar ƙasar nan." Shiru suka yi suna sauraron sa kafin Baba ya ce. "Ka faɗa ma ni gaskiya meye ra'ayin ka akan wannan yarinyar ? Ba na son a takura wa kowa a cikin ku, shin za ka iya zama da ita a matsayin matar aurenka kuma ka kyautata ma ta da yi ma ta adalci ba cuta ba cutarwa? Shin kana son ta ?" "Baba ban sani ba ko son ta nake yi yanzu, na dai san a baya da aka aura ma ni ita ni kan ji haushi da takaici ko ganinta ba na son yi, a duk lokacin da na ganta sai na ji raina ya ɓacj na dinga jin haushin Sidra. Saboda ita ce ta ja faruwar komai. Amma daga baya ɗan zaman da na yi da Nadra na fahimci ta fi Nadra nagartar da kowane namiji yake buƙata daga wajen ƴa mace. Domin ta fi Sidra hankali da nutsuwa, tarbiyya, haƙuri juriya da hangen nesa, kuma tana aiki da ilimin ta na Addini. Waɗan nan ɗabi'un nata da na fahimta ya sa na daina jin haushin da nake ji na aura ma ni ita, kuma na san duk namijin da ya samu mace mai ɗabi'un nan da na lissafa tabbas ya zaɓawa ƴaƴansa uwa tagari. Na san cewa a baya da nake soyayya da Sidra i na duba hasken fata da ƙyale-kyale ne amma yanzu na fahimci ba shi nake bukata ba, nagartacciyar mace wacce za ta yi yarda waɗan da suka isa da ita su yi ma ta tsawa ta bi umarnin iyayenta ko mijinta nake buƙata. Ba ma mance huɗubar Mahaifinsu lokacin da Sidra ta gudu bayan mahaifinsu ya ba ni Nadra a madadinta sai yake sanar da ni cewa. Ya san ya yi ma ni sakayya da wacce zan ci jin dadin zama da ita, idan da Nadra nake so ba zai taɓa ba ni Sidra a madadinta ba, amma tun da Sidra ce to ya ba ni Nadra ba zan taɓa nadamar aurenta ba, domin ya san cewa zan fi jin dadin zama da ita akan Sidra. Kuma na zauna na yi tunani na ga cewa idan har Sidra na girmama iyayenta ba za ta taɓa guduwa a ranar aurenta ba, hakan na nuna rashin ɗa'a da biyayya ce ga iyaye. Amma ita Nadra duk da tana da wanda yake so kuma sun tabbatar za ta yi biyayya ga umarnin su sun isa da ita ya sa suka aurar da ita ba tare da amincewar ta ba. Wanda ko da aka sanar da ita ba ta bijire ma su ba ta yi ma su biyayya ta zauna da wanda suka zaɓa ma ta. To ire-iren waɗannan tunanin na yi na ji na daina jin haushin aurenta kuma ɗabi'un yarinyar suka burge ni. A yanzu ban sani ba ko ina son ta amma kuma na san cewa zan iya zaman aure da ita ta zama uwar ƴaƴana in sha Allah na ɗauki ƙaddarar da Allah ya rubuto ma ni cewa ita ce matata ba Sidra ba." Hannu Mama ta ɗaga tana godewa Allah da ya amshi addu'ar ta cikin gaggawa, kullum addu'ar ta Allah ya karkato da hankalin Fahad kan matarsa. Murmushi Baba ya yi ya ce . "To Hajiya za'a iya ba shi matarsa?" "In sha Allah, yanzu ma kuwa don sai yanzu hankalina ya kwanta." _Makaho_ Bayan sun yi sallama da Ma'eesha yana ta tafiya akan hanya har ya iso bakin titi. Kai tsaye ya nufi wajen da yake zama yana yin aikinsa na gyaran takalmi. Zaman sa na jimawa sai ga wasu motoci sun fito daga layin da ke tsallaken da su makaho ke sana'a. Motoci ne guda biyu ɗayar irin na ɗaukar kaya ne amma bayanta a rufe yake. Ɗayan kuma motar ce baƙa ce mai tinted glass ba'a ganin wanda ke ciki . Tun da motocin nan suka fito ya zuba ma su idanu ta cikin glass wanda ba wanda zai ce ga abun da yake kallo. Direban motor kaya ce ta tsaya daidai in suke ya yi parking, wanda hakan ya sa bakar motar dake bin motar a baya ita ma ta tsaya. Direban babban motar ya fito yana cewar. "Mallam gyaran mun takalmin nan yanzu sauri nake yi." Ya yi maganar yana miƙa wa makaho takalmin. Ganin makaho yana ɗan lalube ne ya sa ya ce . "Kai ba ka gani ne?" Mai yalon dake kusa da makaho ya ce. "Eh baya gani makaho ne amma ya iya aiki sosai." Zai yi magana kenan sai wanda ke cikin bakin motar ya fito yana cewa. "Wani irin sakarcin ne wanan za ka tsayar da mu akan titi bayan ka san ba mu da lokaci ko?" "To ya kake so na yi so kake idan mun sauka na fara tafiya ba takalmi ga shi daji za mu je idan ƙaya na taka fa me za ka ce?" "Ba abun da zan yi amma ka sani idan har ka bari kolayen nan suka fito kai ne a cikin hatsari da ka ɓata ma na lokaci, nawa ne takalmi da ba za ka siye sabo ba?" "Kolayen ai duk an siye su sai mun tafi za su zo ta Wajan sannan kuma idan zan siye takalmi ai ba nan zan samu ba sai na je wani wajen da za mu ɓata lokaci." Wayar direban motor kaya ce ta yi ringing, ya dauka yana cewa. "Afuwa oga kaya za su isa cikin aminci ba matsala, dama wani Kolo ne yake son ba mu matsala amma yanzu shi ma an siye shi ya shigo daga ciki." Daga nan ya katse kiran wayar yana cewa. "Wai har yanzu Makahon nan bai gama gyaran takalmi ba ne?" Daidai lokacin ne Makaho ya Miko ma sa takalminsa ya karba yana dubawa. "Ikon Allah Makaho mai basira, lallai idan mun dawo zan neme ja muna da takalmin da muka tara sun tsinke." Ɗari biyar ya ba makaho ya karba yana cewa . "Nawa ne nan?" "Ɗari biyar ce." "Ba na da canji?" "Bai ma san yana yi ba tuni ya shiga motar ya yi ma ta key." Mai siyar da Yalo ne yake cewa . "Rabon ka ce." Kallon mai Yalo ya yi kafin ya ce. "Ina zuwa zan je na dawo." "To Allah ya tsare." Barin kayan aikinsa ya yi a wajen ya tafi da sandarsa. Can nesa da wajen ya tsaya sai ga wani mai nape ya zo ya tsaya a gabansa. Shiga yayi suka bar wajan. Kai tsaye wani hotel suka nufa in da Makaho ya fito ya bar mai nape din zaune ciki yana jiransa, don ko sandarsa bai ɗauka ba a cikin keke nape ɗin ya bar shi. Cikin hotel ɗin ya shiga ba tare da ya yi wa kowa magana ba, sama ya haura sama. Ɗaya daga cikin ɗakunan ya sa key ya buɗe ya shiga ciki. Kayan jikinsa ya fara ragewa sannan ya shiga bathroom don yin wanka. Almost 30 minutes ya ɗauka yana sakarwa kansa shower 🚿, kafin ya gama wanka ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa da wani karami yana goge ruwan kansa. Man shafawa mai sanyin ƙamshi ya shafa har ya ɗauki turare zai shafa sai ya yi wani tunani ya fasa shafawa ya ajiye. Ƙananan kaya ya saka wando three quarter fari ya saka da farar riga. Gudun A.C ya ƙure sannan ya hau saman lafiyayyen gadon ya kwanta, ba jimawa barci me daɗi ya yi awon gaba da shi kasancewar daren jiya bai yi barci ba kwana ya yi yana yi wa Ma'eesha fifita. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page5️⃣3️⃣ Ƙananan kaya ya saka wando three quarter fari ya saka da farar riga . Gudun A.C ya ƙure sannan ya hau saman lafiyayyen gadon ya kwanta. Ba jimawa barci me daɗi ya yi awon gaba da shi, kasancewar daren jiya bai yi bari ba kwana ya yi yana yi wa Ma'eesha fifita. Sai da lokacin sallar azahar ya yi sannan ya farka, ya yi awa huɗu yana barci. Bathroom ya sake faɗawa ya yi brush da toothpaste ya yi wanka ya fito ya shirya cikin jallabiya fara. Fita ya yi don zuwa masallacin da ke cikin hotel ɗin. Har zuwa lokacin mai nape ɗin da ya kawo shi yana nan yana zaman jiran fitowarsa. Sai dai a lokacin mai nape ɗin ya gama cin abinci a cikin takeaway yana shan ruwa. Sai da aka idar da sallar sanann ya koma cikin hotel ɗin. System ɗin sa ya ɗauka yana shigar da wasu bayanai. Manyan wayoyinsa da ke ajiye a saman table ya ɗauki daya ya kunna. Wata lamba ya lalubo ya kara a kunne, bugu daya aka ɗaga. "Hello sai yau ka ga damar a same ka a waya kenan." Murmushi mai sauti ya ba yi wanda ya ba fito har ta cikin wayar. Kafin ya ce. "Ina hotel a ɗakin da ka sani." Daga haka ya katse kiran wayar kafin ya ɗauki ɗayar tsadaddiyar wayarsa ƙirar Samsung Galaxy Z fold 5 farashin wayar ya kai miliyan biyu da dubu ɗari shida. Irin wayar da ake lanƙwasawa ce ta koma ƙarama idaaka buɗe ta kara girma. shiga what's up ya yi yana duba tarin saƙonnin da suka shigo ma sa, na wasu ya buɗe, na wasu bai bude ba. Har zai aje wayar sai ya shiga bude saƙon da ya ga messages nata ya fi na kowa yawa. YASMEEN shi ne sunan da ya furta kuma sunan ne a jikin wayar da ya yi Seve da shi. "Messages ne barkatai wasu photon ta ne kawai tana hawaye, wani kuma emoji ne na kuka, wasu kuma voice message ne tana nuna damuwa na rashin ji daga gare shi ba kira ba saƙo. Messages na karshe da ta tura ba ta yi magana ba sai rera ma sa kuka kawai take yi. Bai ma ta reply ba ya kashe wayar ya ajiye kawai. System ɗin sa ya sake ɗauka ya shigar da wasu bayanai. Daidai lokacin aka fara knocking ƙofar. Tashi ya yi ya je ya bude kofar . Tashi yayi ta bude kofar nan ya ga Abokinsa da ya kira ya sanar ma sa yana hotel ɗin. "Khalid." Ya fada a saman leɓensa. Murmushi Khalid ya yi yana cewa yau dai ga ni ga *Senior intelligence officer*. "Dama ba ka gani na ne?" "Yanzu kam wa ke ganinka ai sai sai wanda kake tare da su." Wayarsa ce ƙarama wacce Ma'eesha ta siya ma sa ta soma ruri a cikin aljihun kayan da ya cire na wanda ya zo da su. Kallon kayan Khalid yake yi daidai lokacin da ya ga Khalifa ya ɗauki wayar, sannan ya duba ya san mutum ɗaya ce za ta kira shi a wayar. "Nurul ƙalb" Sunan da ya fito kenan don da wannan suna Ma'eesha ta yi Seve number ta da shi a wayar. "Assalamu alaikum." Daga can ɓangaren ta sa da wa'alaika Salam. "Mijina ya kake?" "Lafiya nake matata." "Ma sha Allah, ga abincinka na ajye ma ka don Allah ka dawo ka ci kada ka zauna da yunwa ka ce sai yamma." Murmushi mai sauti ya yi kafin ya ce. "Kada ki damu ni ba na jin yunwa." Nan dai da ƙyar ya shawo kanta ta hakura akan idan ya dawo da yamma sai ya ci. _Nadra_ Tana zaune a falo a falon Mama sai ga Sidra ta shigo ta same ta. "Ƙanwata kina zaune ne ke kaɗai?" "Eh, sannu da shigowa Aunty Sidra." "Yauwa sannu." Zama ta yi a gefenta tana ma ta murmushin yaƙe. "Sai ga Fahad ya dawo ko?" "Eh Aunty." "Kin yi magana da shi ne?" "Eh cewa yayi wai na tattara kayana mu koma gidansa." Sai da gaban Sidra ya fadi amma sai ta dake ba ta nuna tashin hankalin take ciki ba "To ke me kika ce ma sa?" "Cewa na yi ba zan koma ba, don Mama ma ta goyi bayana ta ce ba zan koma ba." "Da kyau, yanzu ya alƙawarin da kika ɗaukar ma ni?" "Aunty Sidra ai ban ɗaukar ma ki alkawarin komai ba." Wani kallo ta yi ma ta kafin ta ce. "Lokacin da na ce ma ki ina son Masoyina har yanzu ke da kanki kika ce ba son sa kike yi ba biyayya kika yi wa iyayen mu, na ce ki taimaka ma ni ya sake ki ya aure ni ni ma zan taimaka ma ki don ki auri Ya Sayyadin da kike so?" Jinjina kai Nadra ta yi kafin ya ce. "Eh tabbas mun yi haka, amma da kike ce ma ni wai sai na yi ma sa rashin mutunci da fitsara na dinga wulakanta shi sanann na dinga waya da tsohon saurayina dole zai sake ni a lokacin na ce ma ki ba zan iya aikata abu ɗaya da kike so na aikata ba. Ba don ko komai ba ke kanki shaida ce ko kare ne ba zan iya wulakanta shi ba, ballantana Ɗan Adam, ko kin manta cewa da duk wulakancin da kike yi wa ma'aikatan gidanmu da zaginsu da kike yi har ki ɗaga hannu ki mari mutanen da a haife sun haife ki me nake yi a lokacin. Kuka fa nake yi. Da a ce zan iya aikata hakan da a kan Waɗanda kike aikata wa zan yi. Ya kamata ki yi amfani da ilimin da Allah ya ba ki wajen tuna cewa Yaya Fahad mijina ne yi ma sa biyayya wajibi ne saɓa ma sa tamkar na saɓawa umarnin Allah ne. Tabbas na yi iya taimakon da zan yi ma ki wajen ganin ya sake ni ya aure ki, tun kafin wani abu ya shiga tsakanin mu na roƙe shi da Allah cewa tun da ba so na yake yi ba ke ni ma ba son sa nake yi ba ya taimaka ya sake ni ya aure ki tun da kin dawo kuma kina son sa shi ma yana son ki ya aure ki. A lokacin yake sanar da ni cewa zai sake ni amma ko ya sake ni ba zai taɓa auren ki ba, tun da har kika iya guduwa a ranar aurenki da shi. Tun a lokacin ya cire ki daga rayuwarsa, idan har ya nemi abu bai samu a lokacin da ya so ba ya fitar da abun kenan daga cikin rayuwarsa. Shi idan ya juya wa abu baya taɓa waiwayarsa har gaban abada." "Ƙarye ne , ƙarya ne wallahi.Fahad nawa ne ni kaɗai, kuma sai na raba ki da shi na aure shi." ",Zan yi farin ciki da haka, fatan nasara." Nadra ta faɗa tana murmushi. Daidai lokacin Mama ta shigo da sallama. Ganin yadda suka yi cirko-cirko ya sa ta kalli Sidra da ta tsuke fuska ta ce. "Lafiya kuwa?" "Lafiya lau Mama." Ta faɗa tana aro murmushi ta yafa a kan fuskarta. Ba dai gamsuwa Mama ta yi ba, amma sai ta bar zancen tana cewa. "Shiga bedroom ki tattara kayanki ki zo ki bi mijinki ko kuma gidanku." Daga Sidra har Nadra sai da ƙirjinsu ya buga a tare. Ganin yadda ta kwaɓe fuska ne ya sa. Mama tsuke fuska don kar ta kawo ma ta wasa. "Mama don Allah ki bar ni a nan." "Okay to je ki roƙi Babanku shi ya zartar da hukunci ba ni ba." Hawaye ya fara yi ma ta sintiri akan fuska tana cewa. "Shikenan na shiga uku ni Nadra." Janyo ta Mama ta yi ta zaunar da ita a gefenta, sannan ta riko hannunta cikin nata, cikin sigar rarrashi ta ce. "Meye abun tashin hankali kuma ƴata, ina ce da can ai kike zaune da shi kafin kuka dawo nan?" "To ai lokacin..." Sai ta yi shiru ta kasa cewa komai. Murmushi kawai Mama ta yi don ta san dalilin Nadra yanzu. "Kar ki damu ba komai in sha Allah, komai ya wuce da yardar Allah. Idan ya yi ma ki wani abu da ba daidai ba, ko abin da kika san ba ki so to ki yi sauri ki ɗauki wayata ki danna ma ni kira, za ki ga hukuncin da zan ɗauka." Mama ta lura da Sidra ta ga rashin jin daɗin da ta shiga yanzu -yanzu. Kuma ta fahimci har yanzu tana son Fahad ba ta fitar da shi daga cikin rayuwarta ba, duk kuwa da Kasancewar yanzu yana auren ƙanwarta ce. "Mu je ta taya ki tattara kayan yamma ta yi." Ta yi maganar tana jan hannun Nadra. "Yi zamanki Mama bari ba taya ta tattara kayan." Aunty Rahama ta yi maganar tana shigo wa hannunta riƙe cikin na Baby Zahrah. "Dama ba ki tafi gida ba?" "Eh na je kaeɓowa Nadra saƙo ne dama ." Ta yi maganar tana jan hannun suka nufi bedroom ɗin Mama. Sidra kam ficewa ta yi daga cikin ɗakin ba tare da ta yi wa kowa magana ba. Murmushi kawai Mama ta yi ta girgiza kai. Aunty Rahama na taya ta shirya kaya tana sake ba ta shawarwari. Hatta kayan gyaran jiki ta fito da su a cikin handbag ɗin ta ta saka ma ta cikin wata ƙaramar jaka. Sannan ta ciro wani ƙaramin roba da ke da wani hadin ta bude murfin goran ta ce. "Karɓi ki sha." Girgiza kai kawai ta yi alamar a'a. Amma ganin ba wasa a fuskar Aunty Rahama ya sa ta karɓa ta shanye. Sauran kayan duk ta yi ma ta bayanin yadda za ta yi amfani da su. Bayan sun ja akwatunan zuwa falo ne ma su aikin gidan suka kwashe su suka fita da su bisa umarnin Mama. Direban Fahad ya jera akwatunan a bayan mota. Fahad ya nufi part ɗin sa dan ɗaukar wasu abubuwan bukatar. Tsarabr da ya kawo ma su daga America ya sanar wa Rumaisa ta fito da su tare da bayanan na kowa. Part ɗin Baba ya nufa in da Mama ma ta ja hannun Nadra suka nufi part ɗin. Nan Baba ya yi masu nasiha sosai Nadra na kuka tana jinjina kai. Shi

Chapter 31 of 49