Share this page
na yi masu gargaɗin na fi karfin su Umma. Har sai da ta kai ta kawo ana shakkar tara ta da maganar so. Ba wanda yake so na yanzu duk na watsa su saboda Fahad. Umma ba zan ɓoye ma ki ba har yanzu ina son Fahad kuma zan iya aikata komai don na same shi. Don wallahi Umma sai Nadra ta bar mun gidana da mijina." "Subhanallah!" Hawaye ta goge tana huci. "Wai ke ba za ki taba canzawa ba! Ke a matsayin ki na musulma ba za ki yarda da ƙaddara ba.?" "Ƙaddara! Ai Umma da tuntuni ƙaddarar ta zo ta hana ni haɗuwa da Fahad, sai da muka haɗu sannan ta ce za ta raba mu, ƙaddarar ma haƙuri za ta yi ta bar ni da shi wallahi." Da mamaki Umma ke kallonta. "Anya kanki daya kuwa?" "Umma komai ta faru komai ya lalace an mai matakin da zan iya tunzura Allah wallahi. Ba zan sadaukar da mutunci..." Kasa ƙarasawa ta yi don kada Umma ta gane ta aikata wani abun. Umma mamaki take yi ta ɗauka Sidra ta yi sanyi ne, ashe halinta yana nan ba abun da ya sauya. "Kina ji na ko?" "Eh ina ji." "Wanda ya bar wani abu da zuciyarsa ke so saboda Allah, Alkah zai musanya masa da abin da ya fi alheri a duniya da lahira. Idan zuciyarki tana son wani abu, amma Allah ba ya so, sai ki danne son zuciyar, ki hana kanki, ka fifita umarnin Allah da na Annabin sa a kan son ranki, to Allah zai saka maki da abin da ya fi shi alheri. Zai cika zuciyarki da imani, ya ba ki farin ciki da kwanciyar hankali da albarka a tare da lafiya a jikinki. A lahira, kuma Allah zai ba ki lada mafi girma da daukaka, wato Aljanna. Wannan alƙawari ne tabbatacce, babu kokwanto a cikinsa. Duk wanda ya gwada hakan da zuciya mai tsarkakakkiyar niyya, zai ga tasirinsa a rayuwarsa. Ki tsarkake niyyarki saboda ALLAH kawai, za ki ga abin mamaki daga falalarsa. Amma wanda ya ji tsoron tsayuwa a gaban Ubangijinsa, kuma ya hana zuciyarsa bin son rai, to lalle Aljanna ita ce makomarsa. ALLAH Ya sa mu cikin waɗanda suke fifita yardarSa a kan son zuciyarsu, ya azurta mu da daidaito a duniya da rabauta a lahira." _Sady baby_ Sam ba ta lura da cewa akwai motar da take bin ta tun da ta bar wajen Mallam da Sidra ba. Har ta kawo Sidra gida yana bin ta har ya zagaya gaban gidan sannan ya bi Sady baby a baya. Tana shiga layin unguwar su kafin ya karasa gida ya sha gabanta da mota. Ba shiri ta taka burkin motar. Ya fito a fusace daga cikin motarsa sai huci yake yi. Sady baby tana fitowa daga motarta da niyyar yin tsiwa, amma ganin wanda ke gabanta da yanayin fuskarsa ta sa gabaɗaya gaɓɓan jikinta yin sanyi. Tas tas ta ji saukar maruka biyu a fuskarta wanda har ya da ta wuntsila ta faɗi ƙasa. Wani gishiri-gishiri ta ji a bakinta wanda hakan alama ce ta cewa bakinta ya fashe har ya fitar da jini. Kallon sa take yi sai numfashi yake yi kamar matashin ɓauna. "Ashe rashin imani ki har ya kai haka, anya ke mace ce kuwa ? Ina karin maganar da kuke yi cewa ciwon ƴa mace na ƴa mace ne?" "JB ni ka mara??" "An mare ki, wallahi ji nake ma kamar na kashe ki kowa ya huta da annoba." "Au ni ce ma annobar? Sakayyar da za ka yi ma ni kenan?" "Akan me za ki yi ma ni haka? Akan me za ki kawo ma ni mace verging bayan ba haka muka yi da ke ba. Cewa kika yi yarinyar nan ita ma ƴar hannu ce tana mu'amala da maza, wanan dalilin ya sa na amince na yi ma ki wannan aikin ashe ba haka ba ne, yarinyar nan cikakkiyar budurwa ce ba ta wani ɗa namiji da ya taɓa sanin ta sai ni. Akan me za ki lalata rayuwarta me ta yi ma ki haka da zafi?" Kafin ya yi wani magana wayarsa dake cikin aljihun wandonda ya yi ruri. Ya duba mai kiran wayar, ganin Yayansa ya yi tsuki sanan ya ɗaga. "Meye kuma?" "To mara mutunci ka zo yanzu ina son ganin ka." Muryar mahaifiyarsa ya ji saɓanin na Yayansa da ya yi zato." Kashe wayar kawai ya yi ba tare da ya amsa ma ta ba. Kallon Sady baby wacce bakinta har ya kumbura ya yi sannan ya fara magana cikin kakkausar murya. "Ki jira haɗurmu da ke." Daga haka ya shiga motarsa ya yi ma ta key, sai da ya buɗe Sady baby da ƙura sanan ya bar wajen . Kuka take son yi amma bakinta ya kumbura ya kasa motsa shi sai hawaye kawai take yi . Tashi ta yi daga faɗuwar da ta yi, ganin har an fara kallonta jama'a ma su wucewa. Da ƙyar ta iya jan motar tana hawaye tana jin zafin abun da JB ya yi ma ta. Sai dai ba ta yi mamaki ba, dan idan ta tuna waye shi idan ransa ya ɓaci. JB. Cikakken sunansa shi ne Jabeer cikakken sunan sa. Wani sangartaccen ɗan ma su kuɗi ne a garin Kaduna. Mahaifinsa hamshaƙin ɗan kasuwa ne da yake kasuwanci har a kasashen waje. Sunan mahaifinsa Alhaji Kamil sai mahaifiyarsa Hajiya Karima. Su biyu iyayensu suka haifa yana da Yaya namiji mai suna Munnir. Tun tasowar Jabeer mahaifinsa ya sangarta shi sosai, saboda son da yake yi ma sa. Ko mahaifiyarsa tana kokarin ganin ta ba shi tarbiyya mai kyau amma son da mahaifinsa ke ma sa yake ganin kamar tana takura na yaronsa. Har yake ganin ba ta son Jabeer kamar ba ita ta haife shi ba. Don ba wanda ya isa ya yi ma sa faɗa ballantana duka, sai abun da ya ga dama yake yi. Hatta Yayansa Munnir bai isa ya ma da faɗa ko wani abun ba take zai kai kara wajen Mahaifinsu wanda shi kuma zai yi wa Munnir faɗa ya goyi bayan Jabeer. Karshe mahaifin nasu ya dauke shi ya kai kasar waje ya yi karatu a can sai ya gana saboda takurar da ake yi ma sa. Don baya son a kira shi da Jabeer dai dai JB.Wanan tafiyar ta kara lalata tarbiyyarsa bai ma tsaya ya yi karatu ba sai shashanci da harkar neman mata. Dole ta sa mahaifiyarsa ta je ta dawo da shi don dole. Driving yake yi yana jin kukan Sidra na dukan dodon kunnensa. Bai taba nadamar abun da ya aikata ba sai wanan karon. Ko don bai taba mu'amala da cikakkiyar budurwa ba ne sai kanta ya san budurci. Don duk ƴan matan da ya yi mu'amala da su to sune suke kawo kansu har wajensa. Amma kanta ya yi wa mace dole ba tare da sanin budurwar ba ce . Abokin Sady baby ne shi JB tun da ta ji labarin yadda yake sakarwa mata kudi bai san zafinsu ba ya sa ta shiga rayuwarsa. Suka zama abokai, kuma yana sakar ma ta kuɗi sosaiz har motar da take hawa da gidan da take zaune shi ya ba ta su. Dalilin abun da ya haɗa su da Sidra kuwa roƙonsa ta yi ya taimaka ya yi ma ta abun da take so, don ce ma sa ta yi Sidra za ta raba sunna ita kuma tana son ta dakatar da ita, ya yi basaja a matsayin Mallam su raina ma ta hankali kada ta je wajan wanda zai raba auren da gaske. Ta tsara abun da zai faɗa wa Sidra. Da ƙyar ya yarda akan cewa zai yi , ta samo gida da komai ta tsara ta kawo shi gidan sannan ta kira Sidra akan ta zo su tafi. _Ma'eesha_ Tana kwance saman gadonta bayan barcin ya sake ta sai kuma ciwon kai ya ma ta sauki shi ma. Ta bude idanunta da suka yi ma ta nauyi. Saman ɗakin ta fara kallo sannan ta kalli kofar ɗakin. Ganin ƙofar ɗakin a rufe ya sa ta lumshe idanunta . Daidai lokacin da Nurse ta shigo cikin ɗakin. "Assalamu alaikum kin tashi?" "Wace'alaiki salam warahmatullah." "Wace'alaiki salam warahmatullah." "Ƙanwsta kin tashi." "Na tashi sannu da ƙoƙari da ni." "Wani kokari? Ai wanda ya kawo ki yanzu ya ba mu dubi ɗari ya ce duk abun da kike bukata a siya ma ki ga kuɗin nan a hannuna, ko na ba ki ki rike a hannunki?" Shiru ta yi tana kallon kuɗin bandir ɗin dubu ɗaya ne ta fito da shi daga cikin handbag din ta. Sannan ta ɗauko wani dubu ɗarin ta ce . "Wannan kuma nawa ne ya ba ni kyauta. Gaskiya yana da kirki ya kike da shi ne." Ta yi maganar tana janyo kujera ta zauna tana farin cikin kuɗin . "Me da me kike bukata a siya ma ki?" "Ba na bukatar komai. Amma ki ciro dubu talatin ki ba Ni zan yi wani abun da shi." "Okay ." Ta yi maganar tana ciwo kuɗin, ga kirga dubu talatin fa sannan ta mika ma ta ." "Na gode ." Ƙadan pillow ta saka kudin sannan ta kwanta daidai lokacin da ya shigo da sallama. Ciki-ciki ta amsa yayin da Muryar Nurse din ga ya cika dakin ta amsa tana washe baki. "Barka da shigowa Yallaɓai." "Barka." Buɗe idanunta ta yi tana kallon yadda yake ta kowa cikin ɗakin cikin takunsa na ƙasaita. Tana tuna yadda yake dogara sanda yana tafiya kamar nakasashshe. Yanzu ga shi yadda yake tafiya irin na lafiyayyun maza. Ba abun da ke ma ta zafi kamar idan ta tuna wai ranar juma'a ɗaurin aurensa. Juyar da kanta ta yi ganin hawaye na shirin zubo ma ta. Bari na ba ku wuri Yallaɓai ." Da sauri Ma'eesha ta rike ma ta hannu tana girgiza kai Ammar a'a . Ganin haka ya sa ya ce . Ta zauna ba damuwa, duk da ba haka ya so ba. Ya so ya yi magana da ita sosai . "Ba wata matsala ko?" "Ba komai sir, yanzu za'a kawo na ta abinci ta ci sai na ba ta magungunan ta." "To ba damuwa bari na je masallaci daga nan akai wanda zan je na gani, amma nan fa awa daya in sha Allah zan dawo . Ki kula da ita sosai ." "In sha Allah, a dawo lafiya." Daga haka ya nufi kofar fita, bayan ya bude kofar sai da ya juyo ya kalle ta sannan ya fice . Yana fita ta nufi bathroom ta ɗauro alwala ta fito. Sallar azahar ta gabatar. Ganin Nurse din na cewa za ta kawo ma ta abinci ya sa ta ce ma ya ta bari zuwa anjima. Don ita ta san me ta shirya . "Aunty akwai nisa nan da kasuwa?" "Ba sosai ba nisan." "To don Allah ina son ki siyo ma ni wani hijabi ne." "Ba damuwa wani kala." "Fari nake so." "To bari na je na dawo, dama na tashi aiki wanda ya kawo ku ne ya ce na zauna na kula da ke ya biya ni." Daga haka ta fita . Wanda hakan ya ba Ma'eesha damar tashi daga saman sallayar da ta idar da sallah. Takalmi ta saka ta karasa wajan gadon ta cire kuɗin da ta amsa dubu talatin ta fice daga cikin dakin da sauri. Tana addu'a Allah ya sa kada ta hadu da Dr ko Jalaluddeen. Haka take tafiya kanta a ƙasa kada wani ya ganta ya gane ta. Cikin ikon Allah har ta fito daga asibitin ba wanda ya gane ta. Tana fita cikin asibitin ta rasa ina za ta je. Don ba ta da wajan zuwa, ba za ta iya komawa gidan aurenta ba. A fahimtar ta Jalaluddeen baya son ta, dole aka yi ma sa aka aura ma sa ita ba tare da yana so ba. Kuma bai ki tayin Dady da Mamy ba. Shi ya sa ya ajiye ta tsawon watanni da suka yi babu abu dayya da ya yi ma ta wanda za ta ce yana son ta. Bai nuna ma ta alamar so ba ko kaɗan, shi ya sa rayuwar aurensu ya daga banban da rayuwar auratayya da ta saba gani. Ashe yana nan yana neman macen da zai aura ita kuma ya mayar da ita banza. Kodayake ba laifinsa ba ne, an na shi ita a arhar banza bai sha wahala ba ya same ta, babu lefe babu kuɗin gaisuwa ko baiko dai kuɗin sadakin da aka ce ya bayar da dubu uku, wanda ko kaza ce za'a aura ma sa ta fi karfin dubu uku a yanzu ballantana mutum. Kuka ne ya ƙwace ma ta ta saka bayan hannunta ta goge. 'Tabbas ba in da zan tafi a halin yanzu, ban isa na je gidan Mahaifina ba. Haka kuma ba zan iya komawa gidan mijina ba. Don na tsane shi fiye da kowa da komai a halin yanzu. Ba na da kowa ban san inda dangin mahaifina suke ba na tafi wajensu na huta da wajan rayuwar. Na tsani zaman garin nan dole na tafi ko ma ina ne, barin garin nan ya zama ma ni dole ko zan sami sassauci.' Ta yi nisa cikin tafiyar da take yi ashe har ta kai titi ba ta sani ba. Kai tsaye ta hau saman titi ba tare da sanin ina take jefa ƙafa ba. Ihun jama'a ta kuma ƙarar taka birki da ta ji ne ya sa ta dawo cikin hayyacinta. Sai dai kafin ta yi wani yunƙuri har motar ta ɗan ture ta ta fadi ƙasa. Rintse isanunta ta yi gabanta na tsananta faɗuwa. " Ke wata irin mahaukaciya ce za ki hau titi kai tsaye? Yanzu da wani abu ya faru fa?" Cewar Captain Kabeer yana kallonta a fusace. Barrister Haidar ne ya fito daga cikin motar cike da kulawa yake kallonta . "Sannu baiwar Allah ba ki ji ciwo ba ko?" Ɗago da dara-daran idanunta da suka canza launi zuwa ja ta kalle shi. Sai da zuciyarsa ta harba da ƙarfi sakamakon kallon fuskarta. Cikin sanyin murya ta ce. "Ku yi haƙuri don Allah, ba na cikin nutsuwata ne. Amma Allah ya kare ba abun da ya same ni." Da ƙyar ta iya jijina ma ta kai, tashi tayi ta kalli tsaddadiyar motar da ta kusan kaɗe ta. Cike da takaici Kabeer fara magana . "Dan Allah ka zo mu tafi Yaya, ana jiran mu fa, nan da gudan marayun ma akwai tazara." Bai tanka ma sa ba ya shiga motar ya tayar suka bar wajen. Don har an fara cunkoson ababen hawa. Ma'eesha kam mai nape ta tare ta ce ya kai ta tashar mota. "Wace tasha za mu je Hajiya?" "Kowace tasha da ake hawa mota zuwa garuruwa." "To bisimillah shigo mu tafi." Shiga cikin nape ɗin ta yi ya dauki hanyar kai ta tashar mota kamar yadda ta buƙata. Barrister Haidar bayan sun bar wajan suka nufi hanyar gidan marayun da aka sanar da su cewa su je mahaifinsu na hanyar shi da Sanata Zuwan su ya yi daidai da zuwan su sanata da mahaifinsu. Kusan a tare motocin nasu suka shiga cikin gidan marayun . In da aka tarbe su cikin girmamawa kasancewar an ga sanata a tare da su. Har office din shugaban aka je tare de Maude. Nan aka yi ma sa tambayoyi ya bayar da amsa da ranar da aka kai yarinyar da kayan dake jikinta da komai sai da ya bayar . Babu ɓata lokaci aka fara bincike don wanda ke kan kujerar a yanzu ba shi ba ne a lokacin da aka kawo ta. Don wancan shi wancan ma ya rasu wani ne yanzu da ke kai. Da ƙyar aka gano file din da bayanai kamar yadda Maude ya faɗa. Sai dai komai da tsari suke yi hatta ranar da aka dauke ta da wanda ya dauke ta yana cikin file ɗin. "Waye shi wanda ya dauke ta?" Yana daya daga cikin masu tallafawa marayun gidan nan dansa ya aura wa ita." Cewar shi shugaban. "Amma yanzu baya ƙasar nan yana jinya a kasar Egypt tsawon lokaci. Shi da matarsa , Amma shi Ɗan sa yana garin nan na san gidansa." "Ba damuwa mu tafi gidan Ɗan nasa." Motoci uku ne suka haɗu na sanata biyu da kuma na Haidar da suka zo da shi daga Katsina. Kai tsaye suka kama hanyar zuwa gidan Alhaji Ibrahim Khalil. _Nadra_ Kallon Farida da take yi ma ta wani kallon tsana ta yi na wasu sakanni sanan ta dauke kai. Tana ganin rashin dacewar abun da ta yi na shigo ma su gida kai tsaye ba izinin har cikin falo. "Farida!' "Na'am Yaya Fahad." Ta faɗa a shagwabe. "Wani irin dabbanci ne za ki shigo ma ni gida kai tsaye ba neman izini." Kuka ta saka ma sa ba tare da ta ce komai ba. "Nadra dai barin wajen ta yi ta ba su waje, don ta ga kallon da take yi ma ta. Dama ta san ba ƙaunarta take yi ba, kuma ta ji labarin ita ma son Fahad take yi shi ya sa take zaune a gidan tsawon shekaru sa saboda shi. Tana ganin Nadra na barin wajen ta fara magana . "Yaya Fahad yanzu shi ne za ka dinga yi ma ni faɗa a gaban matarka ko?" "Wani dalili zai saka ki shigo ma na gida kai tsaye Babu izini." "Yanzu dan zan shiga gidan ka sai na nemi izinin. Ai da yanzu Ni ce a gidan da ba don wanan..." "Ya isa!" Ya dakatar da ita don ya san halinta yanzu za ta iya cin mutunci ga Nadra. "Kuma ina nan akan baka na sai ka aure ni." "Kawai ba, ki ɗebo kayanki ki zo ki zabi daki daya mu zauna matsayin mata da miji kin ji ko?" Jin maganar banza da ya faɗa ma ta ne ya sa ta kau da kai tana magana kasa-kasa. "Da sannu za ka shiga hannuna Wallahi." "Me kika ce?" "A'a ba da kai nake yi ba." Wayarta ce ta yi ringing. "Hallo Mumsy ga shi." Tun da ya ji ta ce Mumsy ya san ƙanwar mahaifiyarsa ce wato mahaifiyar Farida. Tun da aka yi aurensa da Nadra bai yi magana da ita a waya ba. Don ko ya kira ta ba ta ɗagawa tana fushi da shi saboda bai auri ƴar uwarsa ba ya fita waje ya auri bare. Farida ta mika masa wayar, ya karba ya kara a kunnensa. "Assalamu alaikum." "Wa'alaika salam." "Ina wuni Mama." "Lafiya ya kake ?" "Alhamdulillah." "Dama ƙanwarka ce Farida za ta je karatu America tun da auren bai yiwu ba ta koma makaranta. To sai na ga tun da kana da gida a America sai ta zauna a gidanka hankalina zai fi kwanciya. Ba na son. Ta zauna in da ba wanda zai tsawatar ma ta ko da ta yi ba daidai ba. Amma na san za ka kula da ita ta yi karatu yadda ya kamata ." Shiru ya yi yana nazari kafin ya ce . "To ba damuwa Mama." "Yaushe za ka koma ?" "Sai next week." "To tafiyar za ta yi ma ku daidai kenan. Sai ku tafi tare ." "Allah ya kai mu." Sallama suka ya mika ma Farida wayar ya haura sama. Farida na ganin ya haura ta yi kasa da murya ta ce . "Mama ya ya haura sama." "To yanzu sauran aikin ya rage na ki, ba sai na koya ma ki ba, idan ya so wanan karon ma ki tsaya shashanci kada ki yi amfani da damarki akansa." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page8️⃣5️⃣ *End of book 1. Last free pages* *To yanzu sauran aikin ya rage naki, ba sai na koya maki ba, idan ya so wannan karon ma ki tsaya shashanci kada ki yi amfani da damarki." "Mama ba zan yi sake ba, dama ai saboda muna gida ɗaya ne ga mahaifiyarsa ga mahaifinsa, Sanan kuma ka ƙanwarsa Rumaisa hakan ya sa na nake ɗaga kafa ba na iya yin wani abun. Sannan kuma shi Fahad ɗin yakan share ni kamar bai gane me nake nufi ba. Sai da na fito na nuna ma sa irin son sa nake yi ma sa ne yake cewa wai Sidra zai aura. Mama sai da na yi kamar na bar gidan na dai daure na zauna, har aka fasa auren bayan gudun Sidra na saka rai zai aure ni shi ne matsiyatan iyayennta suka sura ma sa ƙanwar. Wallahi wanan karon Mama ba zan saurara ba ko kaɗan. Dama ba idan kowa akan mu idan mun tafi American daga ni sai shi wallahi idan har ban ja ra'ayinsa zuwa gare ni ba na daina amsa sunam mace." Sautin saukowa ta ji daga sama ya sa ta yi wa mahaifiyarta ta kashe kiran wayar . Nadra ce ta karaso wajen ta kalle ta da murmushi a fuskarta . "Aunty Farida ina wuni?" Banza ta yi da ita tana danne-danne a waya tana taunar cingam a bakinta. A takaice tunanin Nadra ta ɗauka ba ta ji ba ne, don haka ta sake gaishe ta a karo na biyu. "Mtswww" Tsukin sa ta yi ne ya tabbatar ma ta da cewa ta ji ta Msawar. E b za ga yi ba. Don haka sai ta juya ta koma sama. Da harara ta bi ta kafin ta ce. "Wallahi sai na yi maganinki sai zama da Fahad ya gagare ki." Ta faɗa da karfi don ta ji ta. Kuma ta yi nasara, domin maganar ya shiga kunnen Nadra. Murmushi kawai ta yi. Dama ta zo ne ta kawo ma ta abin sha da abinci. Amma tun da ta ga take-takenta ta san ba shan komai za ta yi idan ga ba ta ba. Don haka ta shige ɗaki ta yi kwanciyarta. Don dama daiurewa kawai take yi ciwon kai ke damunta. _Jalaluddeen_ Yana shigowa ɗakin ya ga Nurse din da ta bari ta kula da Ma'eesha hankalinta a tase. Kallo ɗaya ya yi ma ta ya gane tashin hankali da take ciki. "Me ya faru?" "Yallaɓai wallahi ashe dabara ta yi ma ni tana son fita ne." "Ban gane be meke faruwa ?" "Cewa ta yi na ba ta dubu talatin cikin kuɗin da ka bayar. Sanan ya ce na je kasuwa na siyo ma ta hijabi. Ko da na dawo daga kasuwar ban ganta ba. Ba ta cikin toilet na zagaye gabaɗaya asibitin nan ba ta ciki. Na sanar wa Doctor shi ne da ya yi bincike ya gano da ƙafarta ta fita bayan fitar da na yi." Bai iya cewa komai ba ya juya ya fita daga cikin ɗakin. Wajen Doctor ya je don neman karin Bayan. Doctor ya nuna ma sa yanda ta fita ta hanyar CCTV camera da ya duba. Isso Jalaluddeen ya zaba wa computer yana kallon yadda take tafiya kanta a sunkuye alamar rashin gaskiya. Godiya ya yi ma sa sanan ya fito ya nufo inda ake parking motoci in da yanar yaronsa na jiransa. Gefen wajen me zaman banza ya zauna sannan direban ya ja motar suka bar wajen. Gidan da yake zaune tare da Ma'eesha ne ya umarci direba ya kai shi. Ko da direba ya yi parking kofar gidan Jalaluddeen ya fito ya shiga cikin gidan. Ba kowa gidan kamar yadda ya bar shi. Sai wayar Ma'eesha dake ajiye a tsakiyar ɗakin. Komai yana zaune a mazauninsa kasancewar ta mace mai tsafta. Wayarta ya durƙusa ya ɗauka, sanan ya karewa ɗakin kallo na wasu daƙiƙu sannan ya fito cikin sanyin jiki. Ya san ba za ta dawo gidan ba kasancewar tana fushi da shi. Har ta yi furucin saki da ta tsani ganinsa a rayuwar ta fiye da kowa. Hakan ya za na ma sa alamun cewa ba za ta zo inda yake ba. Sai dai to ina za ta tafi?" Abun da ya tsaya ma sa a rai kenan. Mutum ɗaya ce ta faɗo ma sa a rai wato Nasreen. Don haka ya fita da sauri ya bude murfin motar wajan zaman direba. Alamar ya fito ya yi ma sa da hannu. Ba musu ya fito. Jalaluddeen ya zauna mazaunin direba ya yi wa motar key suka bar wajen. Waɗanda da suka ga shigar da fitar sa mutane biyu suka bi motar da kallon mamaki. Kai tsaye ya ɗauki hanyar gidan su Nasreen yana sarrafa motar cikin ƙwarewa. Yaronsa dake zaune a gefesa yana son ya yi maganar cewa uban gidansa ya rage gudu amma ganin fuskarsa kawai ya ba shi tsoro, ya kasa yi ma sa magana. Domin yanayin da ya ga fuskarsa yanayi ne da tun da yake bai taɓa ganinsa ciki ba. A kofar gidan ya yi parking ya fito daga cikin motar. Ƙaramr door din gidan ya yi knocking. Maigadin gidan ya leƙo ya kalli Jalaluddeen ya kalli

Chapter 48 of 49