Share this page
on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page7️⃣3️⃣ Akwai munafukai a cikin mutanen mu, jiya na sanar da cewa zan bibiyu mutanen Daula don na san shirin su, bayan na bibiye su suka shirya farmaka ta. Abun tambaya waye ya sanar da su shirina? Sannan bayan na kuɓuta daga hannunsu a an kai ma ni hari, sanann an samu nasarar harbina kuma ba mutanen Daula ba ne na waye da wannan aikin?" Yaja hoton kan mutum ya zagaye shi sannan ya saka alamar tambaya a wajen kan. "Dole na gano ko waye domin farautar rayuwa ta ake yi, kuma ba wanan ne karo na farko da aka farmake ni ba. Sai dai na baya na yi tunanin mutanen Daula ne. Domin na dawo kenan daga wajan gyaran takalmi da yammaci, kan hanyata ta komawa gida ne suka farmake ni suka saka ni a mota. Sai dai cikin ikon Allah lokacin jami'ana da zan ba wa wasu bayanai suna kusa sun hange ni suna tunanin yadda za su tinkare ni saboda ba su iso akan lokaci ba har na gaji da zaman jiran su na kama hanyar gida. Sai Allah ya sa akan idanun jami'an mu abun ya faru suka bi wadan can mutanen har suka kuɓutar da ni bisa umarnin oga. Sannan na gano Harbin da aka yi ma ni ba daga Daula ba ne bullet din bindigar ya fito ne daga weapon serial number DSS stock ." Jalaluddeen (Makaho) ya juya ga gefe a wani allon yana nazari yayin da Taj ya tsaya yana kallon sa na ƴan saknni kafin ya juya ya kalli allon dake manne a bangon ɗakin, alamar bayanai da hotuna ne ke yawo akai. Kamar ana sake gina abun da ya faru ne a baya. Shiru ya mamaye ɗakin. Makaho ya matse sandarsa a hannunsa , zuciyarsa na bugawa a hankali amma cikin karfi. Ya ji wani abu a cikin kansa yana faɗa ma sa cewa. Abun nan bai tsaya ga kwanton ɓauna kawai ba." "Ka ce an sanar da su?" Taj ya maimaita tambayar Jalaluddeen a hankali kamar yana auna kalmomin. Jalaluddeen ya haura tsayuwar sa. "Eh duk abun da na tura ma su sun san shi kafin lokaci." Taj ya yi shiru na dan lokaci sanan ya ja numfashi mai nauyi. "Wannan ba al'ada ba ce." Jalaluddeen ya matso kusa da teburin da ke tsakiyar ɗakin. Yana jin kowane motsin iska. "Na riga na fara zargin akwai mutum a cikin tsarin mu." Jalaluddeen ya faɗa cikin murya mai sanyi. "Amma yanzu na fahimci ba zargi ba ne gaskiya ne." Taj bai amsa nan take ba. Sai ya ɗan juyo da kansa amma idanunsa bai kalli Jalaluddeen kai tsaye ba ya ce . "Waye kake zargi?" Tambayar ta yi nauyi fiye da yadda aka furta ta. "Duk wanda ya san motsi na " Wannan amsa ta Jalaluddeen ta sa dakin ya kara yin shuru. A waje iska ke kaɗawa tana bugun window dake ɗakin kamar tana kokarin fadar wani sirri. Daidaita lokacin wayar Taj ta yi ƙara, sai ya duba. Sakon ya fito ne daga wani lamba da ba'ayi seve ba. *Ya fara tambaya sosai, ku hanzarta kafin ta gano komai* Taj ya kalli sakon sannan ya rufe wayar da sauri. Jalaluddeen ya ɗan ɗago kansa. "Me ya faru?" Ya tambayi Taj. Shiru ne ya biyo baya kafin Taj ya ce. "Babu komai." Amma muryarsa ba ta yi daidai da kalmomin sa ba. Jalaluddeen ya ɗan matso gaba zuciyarsa ta fara nauyi. "Ka san wani abu?" Jalaluddeen ya tambaya a hankali. " Taj ya ɗago kai da sauri. "Me kake nufi?" Gajeren murmushi Jalaluddeen ya yi, irin murmushin da ba na daɗi ba. "Na koyi abu daya a wanan aikin." Sai kuma ya yi shiru bai sake magana ba. Shiru ne ya biyo baya kafin Jalaluddeen ya ce . "Za ka iya tafiya gobe za ku dake binciken." Taj ya juya ya fara tafiya har ya kai bakin kofa ya ji Muryar Jalaluddeen na cewa. ",Duk wanda ya fi sani na a nan shi zan fara zargi." Taj ya dakata da tafiyar da yake yi, kuma bai juyo ba. "Ka fara makara." Daga haka ya fita kofar ga rufe . Taj ya tsaya shi kadai a dakin yana tunanin yadda abubuwa suka sauya ma sa. A hankali ya ce. "Ba Taj ba ne... To waye?" Jalaluddeen yana tsaye a tsakiyar ɗakin sandarsa a hannunsa, tana rawa kadan . Kalmomin Taj ke yi masa yawo a cikin kansa kamar yadda iska mara nutsuwa. "Ka fara makara." Wanann kalmar tafi yi ma sa nauyi. Ya ja wani dogon numfashi ya mayar da hankali sa kan sautin da ke kewaye da shi. Agogo na tick tick a bango iska na shigowa ta window, da nisan motoci a waje. Sai ya ji wani ƙaramin sauti, sai ya ji wani abu kamar an motsa takarda a hankali. Jalaluddeen (Makaho) ya tsaya cak baya ganin komai amma kununuwan sa sun fi komai aiki. A hankali ya juya kansa zuwa teburin da Taj ya bar shi. Babu kowa a wurin . Amma jin sa yana ce ma sa, akwai wani abu da bai kamata ya kasance a wurin ba. Ya taka a hankali yana bin tebur ɗin da hannu. Sai ya taɓa wa wani abu, Fili ne wani karamin na'ura mai sanyi a saman tebur. Jalaluddeen ya tsaya . "Wace irin waya ce wanan ,?" Ya yi tambayar duk da babu mai ba shi amsa. Ya sa hannu ya ɗauka . " Na'urar ba ta da kara amma ta ɗan yi zafi kaɗan alamar ta daɗe tana aiki. Nan take ya fahimci an saka ma sa na'urar saurare a in da yake bincike . Zuciyarsa ta buga da ƙarfi . "Wato hakan na nufin duk abun da nake yi ana saurarena." Ya jefar da na'urar ƙasa ya taka ta da ƙarfi wanda sai da na'urar ta fashe. Daga wajen ya ji karar tashin Mota ta bar wajen a guje. Jalaluddeen ya juya da sauri amma ba su nan. "Sun riga sun ji ni." A lokaci guda wsyarsa ta yi ƙara, wanan karon ba Taj ba ne, wace lamba ce da bai san me ita ba. Ya ɗaga kiran wayar ba tare da ya yi magana ba. Jin shiru ya sa shi nufar hanyar fita don ya fice . _Fahad_ Kofar gidan su Nadra horn ya yi maigadi ya wangale ma su gate suka shiga ciki. Parking space ya yi parking motar sannan ya fito, Fitowar sa ya yi daidai da bude labulen window da Sidra ta yi daga nan ta hangi Fahad yana buɗewa Nadra karfin motar ta fito. Sai da numfashinbta ya yi kamar zai zau dauke. Ganin wani kallo mai cike da shauƙin so da Fahad ke aika mata, ita ma sai murmushi take yi ma sa. Cikin takaici ta dunkule hannu ta daki bangon ɗakin wanda ya sa ta saki ƙara saboda zafin da ta ji. "Wallahi ba zan bari ku yi farin ciki ba sai na farraƙa ku. Ba yadda za'ayi ku yi farin ciki ku bar ni cikin bakin ciki wallahi ko sama da ƙasa za ta hade ba sai na raba ku da juna kuma alkawari na ne wannan." Tana faɗar haka ya saki labule ta koma ta hau gado ta kwanta. Knocking Nadra ta yi a kofar falon shiga babban falon gidan. . "Ammi dake kokarin zuwa bude kofar, tana budewa ta ga Nadra da Fahad a tsaye. Cike da farin ciki ta ce . "Ku ne a daren nan haka lafiya?" "Lafiya lau mun zo gaishe ku ne." "Bisimillah ki shiga ciki ma na. Suka shiga ciki suka gai da Ammi sanan Nadra ta nufi ɗakin Umma tana ƙwala na ta kira . Abba ne ya fito daga part ɗin sa yana ganin Fahad ya sa ya saki murmushi yana cewa . "Fahad kai ne a daren nan, ina fatan dai ba wata matsala ko?" "Babu komai Abba muna zaune lafiya." Nan ya gaida Abba cikin girmamawa sannan ya shida Umma da ta fito yanzu tare da Nasara. Ta marasa wajen Abba ta ce . "Abba." "Na'am ƴar Abba ya faɗa yana rike hannunta suka Zauna a tare. Sai ta yi saurin zama kasa. "Ina Aunty Sidra ce ban ga ta fito ba ko ba ta ji zuwa ga ba ne." Ta yi maganar tana nufar dakin su. "Ki duba tana dakin baƙi." Cewar Umma tana kalli. Nadra. "Me take yi dakin baƙi kuma ko tana da bako ne?" Ba wanda ya amsa ma ta ita kuma ta nufi ɗakin. Da sallama ta shiga sai ta hango ta kwance kan gado ta ya tana lulluɓe cikin bargo. Ƙarasawa ta yi kamar ta tayar da ita amma ta fasa cikin rashin jin dadi ta ce. "Allah sarki Aunty na so mu yi magana ta fahimta da ke ki fahimce ni ko za ki daina jin haushi na. Kuma ba ba ki da lafiya bai dace na tayar da ke ba. Ko ba haka ba na san idan kina barci ba ki son a tayar da ke. Zan tafi Allah ya huci zuciyarki ya kuma ba ki lafiya." Daga haka ta fice daga cikin ɗakin. Sidra na jin fitar ta ta tashi zaune tare da bin kofar da ta fita da harara. Ko da ta fita ta koma falo ta samu Ammi ta kawo wa Fahad tuwon aljanna da miyar ɗanyar kuɓewa sai ƙamshin man shanu miyar ke yi. "Ga girkin uwar gida ka ci na san kana son shi, Allah ya sa Amarya ba ta cika ma ka ciki ba." "Yauwa Ammi Allah ya bar ma na ke, kamar ko kin san ban yi girki na take away za mu siya dama.," Wani kallo Umma ta yi ma ta mai sannan ta ce. "Take away Nadra kika ce fa? Yaushe kika zama haka? Abinci da za ku ci ke da mijinki ya gagare ki ? Wanan ba tarbiyyar d na koyar da ke ba ne?" 'Oh Allah ta ya zan fahimtar da su ne? Xan ce ma su na kasa girki ne saboda damuwar Aunty Sidra ko xan ce na kasa girki ne dan saboda jarabar Yaya Fahad ?' Tana tsaka fa tunanin ne ta ji Muryar Fahad na cewa . "Ba haka ba ne, ni ne na ce ta huta yau kawai na yi ma na take away, akin na ma ta hawa ita kadai a gidan nan." "Wanan ba dalili ba ne Fahadz kada ka yi kokarin kare ta. Aikin da Nadra ta saba da shi a gidan nan ai bai kai aikin gidan ka yawa ba, kawai dai lalacin da ba ta da shi a baya ne take so yanzu ta koya " Cewar Ammi tana kallon Nasara. Umma za ta yi magana Abba ya ce. "Ku bar ta haka nan in sha Allah ba za ta sake ba." Kallon Nadra ya yi yana cewa . "Ƴar gidan Abba kada ki sake bari mijinki ya tafi siyen abinci gidan abinci bayan kina da ran ki da lafiyar ki ba tare da wani baban uzuri ba." "To Abba in sha Allah." Tashi Abba ya yi yana cewa "Zan ɗan fita kika kafin na dawo kun tafi, Allah ya ma ku albarka sai da safe." Daga haka ya fice suna ma sa sallama. Umma ta tashi ta ba su wuri su ci abinci. "Ammi ma ta ce ina zuwa ." Barin wajen ta yi Fahad yana kallon yadda Nadra ta kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka . "Kukan me za ki yi, daga magana kin daki baki kina fadar zance waye ya san ba ki yi girki ba? Ke kika faɗa da bakin ki." Ya yi maganar yana ƴar dariya. Sanann wanke hannu ya fara cin tuwon. "Ki yi hakuri mu ci kin ji Nadfah. Ko take away kike so na siya ma ki a hanya?" Kai ta girgiza alamar a'a. "Okay to kaza fa za ki ci?" "Ba zan ci ba." Ta saka hannu suka fara cin tuwon a tare. _Jalaluddeen_ Bayan ya fito daga ɓoyayyen gidansa yana tsaye a ƙofar gidan ya ɗan tsaya yana sauraren bugun zuciyarsa. Murmushi kadan ya yi yana kara matse sandarsa dake hannusa. kai tsaye hanyar gida ya koma. Don ya san zuwa yanzu Ma'eesha za ta iya ɗaga hankalin ta. Ya san da ya zo da wayarsa ta yake waya da ita da tuni ta kira shi. Yana tafiya maganar Taj kawai ke aunawa a ƙwakwalwarsa da kuma na'urar saurare da ya gani a ɗakin. "Ka fara makara" *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page7️⃣4️⃣ Bayan ya fito daga ɓoyayyen gidansa yana tsaye a kofar gidan ya ɗan tsaya yana sauraren bugun zuciyarsa. Murmushi kaɗan ya yi yana kara matse sandarsa dake hannusa. Kai tsaye hanyar gida ya koma dan ya san zuwa yanzu Ma'eesha za ta iya ɗaga hankalin ta l. Ya san da ya zo da wayarsa ta yake waya da ita tuni ta kira shi. Yana tafiya maganar Taj kawai yake aunawa a ƙwakwalwarsa da kuma na'urar saurare da ya gani a ɗakin. "Ka fara makara.!" Mai keke nape ya tare ya sanar da shi unguwar da zai kai shi. Har bakin layin su ya kai shi sanan ya ce ya dakata a nan zai sauka. Yana sauka kenan sai ya tambaye shi kuɗin sa, ɗari biyar ya ce ma sa kuɗin sa. Take ya zare dubu daya a cikin aljihun wandonsa ya mika ma sa. Yana mika ma sa ya kama hanya, mai nape ya ciro ɗari biyar da niyyar ba shi canji amma sai ya ga ya fara tafiya. "Mallam ga canjin ka!" Alama ya yi masa da hannu alamar baya son canjin. "Ikon Allah ga mutum Makaho har da sandar jagoransa amma ya bar canji haka kamar wani mai kudi?" Ya ja kekensa ya bar wajan yana sake mamakin wanan makahon. Cikin nutsuwa yake tafiya har ya karasa kofar gidan. Ya sa hannu ya tura kofar fale-fale bakinsa dauke da sallama. Da sauri Ma'eesha ta fito daga ɗaki yana sakin ɓoyayyen ajiyar zuciya. "Wa'alaika salam warahmatullah." Ta amsa tana murmushi. "Sannu da dawowa Mijina." Ta kama hannunsa ta taimaka ma sa ya zauna a saman tabarma . Sai sannu take jera ma sa kamar mai ciwo. Tashi ta yi ta kawo masa breakfast,kunun gyada ce ta yi sai ƙosai da ta soya. Kasancewar yanzu ta daina yin abinci kala-kala ko akwai saboda canjin rayuwa da ta samu kanta a ciki. Sai da ya sha kunun gyaɗar da ƙosai ya ƙoshi kuma ya ji dadin kunun sosai ba kadan ba. Bayan ta kwashe kayan tta dawo ta zauna gefen sa . "Mijina." "Na'am matata." "Ina fatan dai lafiya da na ga an isar da sallar ina ka dawo ba har gari ya waye lokacin da ka saba dawowa ya yi ba ka dawo ba, haƙiƙa hankali na ya tashi a lokacin musamman da na kira wayar ka na ji ga a kashe. Hankali na ta sake tashi kada a yi amfani da makantar ka a cutar da kai, ka san mutane idan suka ga mutum Makaho ne ba wuya za'a cuce shi ." "Kar ki damu ba abin da zai same ni in sha Allah. Na gode da nuna ƙauna da kulawa. Allah ya bar mu tare." "Amin ya rabbil izzati." _Fahad_ Bayan sun kammala cin abinci ne Nadra ta kwashe kayan ta je kitchen ta wanke su. Sannan ta shiga ta yi wa su Umma da Ammi sallama . Har ta kai bakin ƙofar fita daga dakin Ammi dai ta kira ta. Dawowa ta yi ta ce . "Ga ni Ammi." Wani leda ta miƙa ma ta tana cewa. "Karbi wanan kayan mata ne na gyaran zamantakewar aure. Ina so ki sha su. Wasu haka nan za ki sha ki yar da robar, wasu da madara za ki sha su . Duka dai an rubuta su za ki gani sai ki dinga amfani da su. "Kai Ammi dan Allah ki bar su ko wadanda Gwaggo Laraba ta ba ni ban gama sha ba, sanan kin kara ma ni wasu." "Eh nata daban nawa daban don haka karbi ki je ki yi ta sha ki zama ƴar gatan mijinta." Ba musu ta karba ta rike zuwa falo Ammi na bin ta a bayan ta suka tarar da Umma na yi ma sa sallama. Har wajen motat Ammi ta raka su in da Fahad ya ba ta kudi ma su yawa. Cike da murna ta koma cikin gidan bayan ta ga wucewar motarsu daga cikin gidan. _Sidra_ Bayan fitar Nadra sai ta tashi daga likimon da ta yi kamar mai barci . Wayarta ta ɗauka tana kuka ta sanar wa Sady babu abun da ya faru. Sady baby ta yi farin ciki kuma ta yi bakin ciki. Farinciki shi ne jin Nam da wata ɗaya za'a aurar da Sidra kuma ga ƙauyensu, bakinciki kuma shi ne jin yadda zaman Fahad da Nadra ya yi daidai suke zaman aure cikin soyayya da juna. "Daina kuka ƙawata, don Allah ya isa haka ki kwantar da hankalinki akwai wani Mallami da zan kai ki wajen sa aikinsa yana ci sosai, idan muka je kika sanar da shi matsalar ki to ki ɗauka bukatar ki ta biya kawai. Aikinsa kamar yankan wuƙa ne." "Ni fa Wallahi ban yarda da bokayen nan ba maƙaryata ne, karya suke yi mafi yawan maganar su." "Ke ba boka ba ne shi fa Mallam ne, ki kwantar da hankalinki bukatar ki ta mallakar Fahad za ta biya ki sa wannan a ranki." "Kai gaskiya hankali na bai kwanta da zuwa wajen boka ba Wallahi." "Wallahi ba boka ba ne gobe ki zo mu je za ki tabbatar da abun da nake faɗa ma ki ." ",Shi kenan zan zo duk da ban san yadda zan fito daga gidan ba. Abba ya tsaurara ma ni, idan ba damuwa ke ki je a madadina ma na." "In ji waye ya faɗa ma ki cewa zan iya zuwa a madadin ki, ai ke za ki je da kanki ya ganki, idan ya so daga baya zan dinga zuwa ina karɓo ma ki magani ko ba ki je ba. Yanzu ki yi dabara ki bar gidan nan gobe in sha Allah." Shiru ta yi tare da nazari kafin ta ce. "Zan duba yiwuwar hakan." Sallama suka yi ta katse kiran wayar tana tunanin hanyar da za ta bar gidan nan. *Bayan kwana biyu* _Nasreen_ Tana zaune ita da saurayin ta a wani tsadadden gidan cin abinci. Suna tattaunawa kan maganar auren su. Kamar an ce ta daga kai ta kalli kofar shigowa. Jalaluddeen ta gani tare da wani mutum wanda zai iya haifar ta. Dukkansu sanye suke cikin shigan Suit baƙaƙe. Sun zo sun zauna a wasu kujeru biyu da ke gefe ɗaya. Shi mutumin yana sanye da bakin glass a idanunsa yayin da Jalaluddeen bai saka glass ba. Kallon saurayin nata ta yi a dan firgice ta ce. "Sai anjima za mu yi waya ina sauri zan je wani wajen." Kafin ya yi magana har ta bar wajen ta fita da sauri. Mamaki ya kama shi amm ba wanda zai tambaya, don haka ya biya kudin abincin ya fice. Dama daga ita har shi kowa da motarsa ya zo suka hadu a wajan . Gudu Nasreen ke yi kamar za ta tashi sama, burin ta kwai ta isa gidan Ma'eesha. Tafiyar da za ta dauke ta Mintuna ashirin da biyar ta isa a mintuna goma sha biyar. Ko sallama ba ta yi ba ta shiga ƙwalawa Ma'eesha kira . "Ƙawata!" Da sauri Ma'eesha ta fito waje tana tambayar Nasreen lafiya. Ba ta tsaya bayani ba illa iyaka ta janyo hannun Ma'eesha tana cewa. "Zo mu je da sauri ba lokaci." Ganin yadda take jan hannun ta ne ya saka ta fisge hannunta tana cewa. "Anya kanki daya kuwa ?" "Idan muka je za ki gani." "Ba inda zan je ba tare da izinin mijina ba." "To wajan shi mijin ne za mu je." "Wai me ke damunki ne haka?" "Yau zan nuna ma ki asalin waye mijinki, za ki yarda cewa mutumin da na kawo ma ki photo na ce shi ne mijin ki amma kika ƙaryata ni to yau za ki tabbatar wanan shi ne mijin ki. Ba Lokaci mu je." _Mamy_ Zuwa yanzu ta rame ta fige ta fita a hayyacin ta sosai ba kadan ba. Don ko barcin kirki ba ta iya yi. Da zaran ta kwanta daddare to za ta kasa barci ne sai mafarkai barkatai da take yi a duk lokacin da barci ya yi nasarar ɗaukarta. Gefe guda kuma ga matsalar dake tsakanin ta da Laila. Din kullum sake rasa abubuwa suke yi a gidan. Ga shi ta rasa ta ina matsalar take . Ba ta zargin ƴaƴanta amma sai dai masu aikin gidan su take zargi. Ranar da ta dinga bala'i akan sai an fitar da kayan da aka ɗaukar ma ta . Haka ta dinga binciken ɗakin masu aiki amma ba ta samu komai ba. Abubuwa sun yi ma ta zafi ga shi bokan da yake ma ta aiki ya nemi maƙudan kudade a wajen ta saboda aikin da ya yi yana neman warware wa. Ya umarci da ta bayar da kuɗaɗen don ya sabunta aikinsa. Da kyar ta iya shawo kan Sidra ta yarda da cewa za ta bi ta su tafi gobe. _Alhaji Daula_ Zaune yake a tangamemen falonsa da waya kare a kunnensa yana magana. A tsaye bayansa kuma wasu murɗaɗɗun maza ne guda biyu. Sai da ya kammala wayarsa sanann ya juyo ya kalle su. "Yanzu yaushe contenar za su iso ne?" Ɗaya daga cikin su ya ce. "Yau da misalin ƙarfe biyu na dare za su iso ta jirgin ruwa." Jinjina kai ya yi kafin ta gyara zamansa ya ce. "To da zaran sun iso a raba makaman ga waɗan da suke jira kamar yadda aka saba. Sannan ku kasance cikin shiri saboda wanan Intelligence officer ya sa idanun su akan harkokin mu. Ku bi komai a sananu saboda yana da basira fiye da tunanin ku, na ji labarin waye Jalaluddeen sai kun yi taka tsantsan. "Na so mu ga bayansa kamar yadda muka yi wa sauran jami'an da suka nemi shiga gonar mu, amma shi mun gagara sanin sa sai daga baya." Cewar daya daga cikin yaran Daula. "Ka san shi yana da matuƙar lissafi ya ɓoye kansa wanda ba mu san shirin sa ba sai dai ya yi nisa a binciken da yake yi. Ya matukar iya basaja Yallaɓai yana da abubuwan da ya sani akan mu." Jinjina kai ɗaula ya yi sannan ya ce. "Ranar da kuka ritsa shi ai kasa kashe shi kuka yi, wai a ce duk yawan ku mutum ɗaya ya gagare ku har ya tsere ba mu sani ba, taron mara sa amfani kawai." Ya yi maganar cikin takaici. "Ka yi hakuri yallaɓal za mu shirya ma sa gadar zare zai faɗa." "Haka kullum kuke cewa, ku ne ma su shirya gadar zare karshe shi ba zai faɗa ba ku ne za ku fada ciki.." Ya yi maganar yana amsa wayar da aka kira shi. _Ma'eesha_ Kallon Nasreen take yi da maɗaukakin mamaki . "Ban gane mijina ba ina kika gan shi, ko dai can wajen gyaran takamin da yake zama ya yi?" Dariyar rainin hankali ta yi kafin ta ce. "Ko ma sai ina ne za ki ga ashirin waye mijinki ki san da waye kike zaune ." "Na san da wanda nake zaune Khalifa ne mijina dan asalin garin Maiduguri ko ina da wani mijin ne bayan shi." Sanin cewa duk yadda ta yi kokarin fahimtar da Ma'eesha ba za ta fahimta ba ne ta saka bin ta a hankali ta yadda za ba za ta bijire ma ta ba. "To amma ba jimawa na kira wayarsa ba ta shiga ." "Eh idan mun je can za ki gan shi kuma za ki ga abun mamaki ." Hijabi ta saka suka fita in da ta rufe gidan da makulli sannan ya shiga motarta da niyyar za ta kai ta wajen mijinta. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page7️⃣5️⃣ Hijab ta saka suka fita in da t rufe gidan da makulli sannan ta shiga motarta da niyyar za ta kai ta wajen mijinta. _Makaho_ Yana zaune a tsadadden gidan cin abincin shi da ogan sa Assistant Director Sulaiman don bai yarda ya je ɓoyayyen gidan nasa sa ogansa ba, don a halin yanzu kowa abun zargi ne a wajansa. "Ka ce Harbin da aka yi ma ka ba daga mutanen Daula ya fito ba?" Jinjina kai ya yi yana kallon Ogan nasa kafin ya ce . "Ƙwarai kuwa ba daga mutanen Daula ba ne, ɗaya daga cikin mutanen mu ne suka harbe ni bullet din bindigar ya fito ne daga weapon serial number na DSS stock." Mamaki ne bayyane a fuskar ogan nasa kafin ya ce "To yanzu waye kake zargi?" "A halin yanzu kowa abun zargi ne a wajena musamman wannan da suka san shiri na.

Chapter 42 of 49