Share this page
cikin falon suka amsa ma sa, sannu da zuwa suka yi ma sa dukansu. Ya amsa sannan ya zauna suka gaisa. Ummee da kanta ta jawo ma sa abun sha ya sha sannan ya yi gyaran murya. "Duk da ba na da lokaci ina kan hanya ne, sai dai sanin gobe ne Jalaluddeen zai tafi ya sa na zo." "Haka ne Yaya." "Cewar Ummee." "Don haka rashin sanin cewa idan ya dawo washegari za'a ɗaura ma su aure. Na ɗauka cewa sai ya kammala aikinsa zai dawo, to sai aka samu akasi ba yadda na yi tunani ba ne, don haka ya kuke gani." "Kawai a ɗaura ma su aure ya tafi da matarsa kowa ya huta!" Cewar Ummee tana kallon Yayan nata. "A'a ku bari a ji daga bakinsa duk yadda ya ce haka za'ayi. " Cewar Abbi yana kallon Jalaluddeen. "Son ya ke ce shin a ɗaura ma ka aure kana da ra'ayin tafiya da matarka ba za mu takura ma ka ba?" "Abbi ina neman alfarma a yi hakuri a bari na karasa aikin da na je yi idan na dawo sai a ɗaura auren ko da kuwa ranar da na dawo ne." _Nasreen_ Bayan an kai amarya gidanta ta samu isasshen natsuwa sun koma masaukin su sannan ta dauki waya ta kira lambar wayar Ma'eesha. Bugu biyi ta ɗauka cikin nitsatsiyar muryarta ta yi ma ta sallama. "Assalamu alaikum ƙawata." "Rike sallamar ki ina son ki saurare ni da kyau." Cikin mamaki Ma'eesha ta ce. "Ikon Allah sallama bushara ne da saƙon aminci, amincin shi ne ba ki so?" "Duk ba wanan ba, ina mijinki yana gida?" "A'a ya yi tafiya." Sai da Nasreen ta yi dariya sosai kafin ta ce . "Idan kika wayi gari wanda yake tare da ke kika yarda da shi kika ba shi amana ya ci amanarki ya yi ma ki karya fa?" "Ba sai kin tambaye ni ba, na tsani ƙarya na tsani yaudara na tsani mai aikata su ko ma waye! Ai ke ma kin sani ba na son ƙarya idan na kama mutum da wanan halayyar zan iya rabuwa da shi kin sani. Amma me ya sa kika yi ma ni wanann tambaya?" "Amsar yaba tare da ni ko ba faɗa ma ki ba za ki yarda ba dan idanun ki sun rufe, amma idan na zo na nuna ma ki video da photo hakan zai tabbatar ma ki da gaskiyan lamari, ki gode wa Allah da na je biki a Abuja don zuwan ki ne." Daga haka ta katse kiran wayar yayin da Ma'eesha ta bi wayar da kallo cikin rashin gane in da zancen nata ta dosa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page6️⃣7️⃣ Na tambaye ka wace ce ita ba ka sanar da ni ba, yanzu ka shirya faɗa ma ni ne?" Juyo wa ya yi ya kalle ta ya n da take ƙaraso wa cikin ɗakin. Zama ta yi gefensa ta dafa kafaɗar sa tana cewa. "Na ji an ce uwa tana iya karantar idanun ɗanta, tabbas na yarda da wanann domin kuwa tun ranar da ka iso garin nan na lura da hakan. Amma sai ka ce ma ni ba haka ba lokacin da na tambaye ka, har na yi ma ka maganar nan ka nuna ma ni cewa ba komai." Shiru ya yi ya dauke kansa daga duban mahaifiyar tasa don ta yaya zai iya sanar da ita cewa yana da mata bayan ba su suka sura ma sa ita ba ba su san da zancen ba. Tabbas wata zuciyar na ingiza shi akan cewa ya sanar da ita komai amma yana gudun abun da zai je ya dawo. Don haka a ƙasan ransa ya ji cewa gara ya bari idan ya kammala aikinsa da ya kai shi can garin ne sai ya dawo tare da Ma'eeha ya ajiye ta gidan Mom tare da gabatar da ita ya sanar da ita komai. Zuwa lokacin ita ma Ma'eesha zai fara sanar da ita ko shi waye kafin ya sanar da danginsa. Da wanan tunanin ya saki murmushi yana cewa. "Mom kin dawo?" "Na dawo ya kake ya mutanen gida?" "Suna lafiya lau Alhamdulillah." "Ma sha Allah. To meye labari ?" Ta faɗa tana zuba ma sa idanu . "Mom ba komai fa kamar yadda na ce, idan ma akwai zan sanar da ke idan lokaci ya yi?" Jingina kai ta yi tare da cewa . "Allah ya kawo lokacin na alkhairi." "Amin ya Allah." Shiru ne ya biyo baya kowa da abun da yake ransa, kafin ta katse shirun ta hanyar cewa. "Gobe ne tafiyar taka ko?" "In sha Allah." "To Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya ya kare ka a duk in da kake ya ba ka nasara." "Amin ya Allah Mom. Na so na a ce na ƙara kwana biyu saboda Sadik ya kai ni wajen dangin ki da ban san su ba mu ga juna da su. Musamman mutanen Katsina ya dace na gan su har da wanann rigimammiyar tsohuwar da nake jin labarin ta wajen Sadik. " Dariya ta yi tana cewa. "Mahaifiyar tawa ce rigimammiyar tsohuwar sau nawa ka ganta ?" "Na gan ta ai lokacin da kika taɓa samun accident din nan ta zo a lokacin har ta addabi jama'ar asibiti idan an ce ta yi shiru ta fara masifa." Dariya ya yi suka cigaba da fira har Saddiƙa ta yi sallama ta shigo ɗakin. "Wato Yaya ka shigo ko ka neme ni ko?" "Afuwa sis ya kike, ina Sadik." "Yanzu ya shigo ya ce bari ya yi wanka ya zo ya same ka. " "Ke kina gidan dama?" "Eh ina nan kawai dama na shiga ɗaki ne ina jiran shigowar Mom, da ba fito Dad ke sanar da ni kana ciki." Zama ta yi kan carpet tana cewa. "Zan iya zama ayi firar da ni?" "Eh za ki iya ma na, tun da gulma kike son ji." Dariya Jalal ya yi yana kallon yadda take tura ba ki. Zuwa can ta ce. "Yaya Jalal wai ka fasa auren Yasmeen yanzu sai ka dawo tafiya kuma, to me ya sa bayan ni da ita duk mun gama sanar da kowa zancen ga shi har kuka sai da ta yi." "Ai na san giulma ce ta kawo ki nan yanzu." "Mom na tambaye shi ne fa na ga ƴar uwata ƙawata na cikin damuwa na rashin auren da ya sa aka ɗaga, ya bar ƙawata cikin damuwa da zullumi." "Kar ki damu sis komai lokaci ne, idan Allah ya kawo ranar sai ku ga komai sai ya zama tarihi, na fi son na kammala abubuwan da na saka a gaba a halin yanzu." "To Yaya Jalal Allah ya taimaka ya yi jagoranci." "Amin ya Allah." Sadik ya shigo da sallama a bakinsa, suka amsa ma sa ya gaishe da Yaya Jalal kasancewar tare da Mom ya dawo aiki shi. Zama ya yi suka cigaba da fira cikin farin ciki da nishadi har karfe sha daya na dare ta yi ba su sani ba. Daidai lokacin Yusuf ya shigo ɗakin da shi da Dad. Bayan sun yi sallama sun shigo ne Jalal ya kalli Yusuf yana cewa. "Har ka dawo ne?" "Eh yanzu fa karfe goma sha daya na dare." Duk sun yi mamaki sosai ba kadan ba, don ba su yi zaton lokaci ya tafi har haka ba. Sallama Jalal ya yi ma su amma kafin nan sai da ya turawa Sadik kuɗin ma su yawa a account din sa ya ce ya yi siyayyan gida kayan abinci da kayan bukata. Godiya da sa albarka Mom da Dad suka yi ma sa sannan ya yi ma su sallama, har wajen motat Yusuf suka raka su, sai da suka bar gidan suka koma ciki, sai dai zuciyar Mom na ayyana ma ta akwai abun da Jalal ke ɓoyewa. Ko da suka koma gida Ummee da Abbee na zaune a falo suna sai Yasmeen da ke can gefe. Da sallama suka shigo yayin da Abbee ke cewa . "Yauwa ga su nan ƴan halak sun bayyana, hankalinki ya kwanta?" Kallon su Jalal ya yi yana cewa. "Ga Ummeenku ta damu ba ku dawo da wuri ba ga dare ya y,i har za ta kira ku na hana ta na ce dare ya yi na san duk in da kuke yanzu za ku dawo. Ya su Dad din da Mom." "Kowa na lafiya suna gaishe ku." Cewar Yusuf yana zama kan kujerar mai zaman mutum ɗaya. "Son ba wata matsala ko?" Ta yi maganar tana kallon Jalaluddeen. "Ba komai Ummeena, in sha Allah kuma tafiyar safe zan yi." "Ba damuwa Allah ya kai mu ya tsara mun kai a duk in da kake ." "Amin Ummeena." Abbee da Umme suka tashi suka shiga ciki yayin da Jalaluddeen ya tashi ya koma gefen Yasmeen ya zauna. "Meye matsalar ki." Shiru ta yi ma sa tana wasa da wayarta. "Ki yi hakuri na fahimce ki, ni ma nan da kika gani dole ta sa na ɗaga auren saboda na fi son idan na kammala aikina na dawo sai ayi auren hankali na ba zai rabu biyu ba. " Cikun karaya ta ce. "Na ga kamar gujewa auren kake yi ne." "Wa?" Ya faɗa yana fito fito da idanunsa. "Kai ma na Yaya Jalal." "Wane ni? Waye za'a ba sa zugegiyar mace kamar ki ya ce baya so.." Madadin ta sauko sai ta sake tunzura tana cewa. "Wato ba ka ni aka yi ba cewa ka yi kana so na ba ko? Na sani ba sai ka nanata ma ni ba na san kai ba ka ce kana so ka ba aka ba ka ni." "Ya Salam ba haka nake nufi ba, kada ki juya mun zance ki fahimce ni." Tashi ta yi tana kuka wanda ya san kukan baya rasa nasaba da burin da ta ci na auren wanda shi kuma ya ruguza shirin nata. Bedroom ɗin ta ta nufa tana kuka. Bin bayanta ya yi zuwa ƙofar bedroom ɗin nata, ya tura ya ji ta rufe da key ta ciki. Barin wajen ya yi Yusuf ya bi shi da kallo yana dariya, hararar sa ya yi ya wuce bedroom ɗin sa. Ita kuma jin bai yi ta knocking yana roƙon ta ta bude ma sa ƙofar ba ne ya saka ranta ya kara ɓaci. Yana shiga cikin bedroom ɗin sa ya ci karo da kiran wayar Ma'eesha na shigowa cikin wayarsa. Kiran ya bari ta katse sannan ya bi bayan kiran nata. "Assalamu alaikum warahmatullah." Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya amsa ma ta. "Wa'alaiki salam warahmatullah mar'atussaliha." Murmushi ta yi cike da nishadin jin muryarsa. "Na'am mijina ina wuni." "Lafiya lau Alhamdulillah ya karfin jikin?" "Na warke dama zazzaɓin rashin sanin halin da kake ciki ne tun da na ji muryarka na warke." Murmushi ya yi yana mai jin dadin kalamanta da suke kwantar ma sa da hankali. "Me kika shirya mun za ki tanadar ma ni gobe idan zan zo?" "Komai da na san kana so na tanadar ma ka shi ." "To godiya nake mar'atussaliha, Allah ya yi ma ki albarka ." Da Amin ta amsa ma sa , daga nan ta ce ma sa . "Bari na bar ka haka nan na san ba kudi ne da kasa ba ballantana ka saka kati a waya." "Waye ya ce ma ki ban da kudi ?" "Na san a yadda ka yi tafiyar nan ba ka da kudi ai. Ms ce ba?" "Kika ce me?' "Na ce ko za ka samu wanda ke da account number sai ka tur mami na saka kudin da Z ka karamar mota. Kasancewar da za ka tafi wata babbar motar kaya fa ka bi na san ka sha bakar wahala sosai to hakan ya sa na ce bari na tura ma ka kuɗin motar cikin kuɗin tallafin da muka samu." "A'a kada ki damu wanann karon ba babbar mota zan bi ba, ƙaramar mota zan bi na samu wadan da suka bani kudi na san za su ishe ni." "To shi kenan Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi, Allah ya dawo mun da kai lafiya ." "Amin ya Allah na gode sosai Allah ya ma ki albarka ." "Amin mijina." Sallama suka yi sannan ya katse kiran wayar yana tunanin idan ya tashi gobe yin da jirgi zai bi kuma ki awa daya ba zai cika a jirgi ba zai isa, don haka ya yanke shawarar zai sauka a hotel ɗin sai zuwa yamma ya isa gida gudun kada ta zarge shi. Da wannan tunanin ya kwana. _Nadra_ Bayan ya gama ayyukan gidan kamar yadda ta saba, ta share ko ina ta gyara, ya saura daura ɗakin Fahad wanda ta san yana kwance tama jira ya tashi. Kitchen ta shiga don haɗa ma su breakfast, nan da nan ta kammala ta je ta yi wanka. Riga da siket ta saka na atamfa wanda ya zauna ma ta ya yi ma ta kyau sosai a jiki. Ɗakimsa ta nufa ta ji saukar ruwa a bathroom, hakan ya tabbata ma ta fa yana wanka kenan. Ɗakin Sidra ta tafi ta tarar da ita har ta yi wanka ta shirya cikin ƙananan kaya riga da wando. "Ina kwana Aunty." "Lafiya lau." Ta amsa ma ta ba yabo ba fallasa. "An tashi lafiya ya jikin naki." "Da sauki Alhamdulillah." "Ma sha Allah, Allah ya kara ma ki lafiya.," "Amin ." "Dama na gama haɗa breakfast ne shi ne na zo na kira ki za ki fito ne ko na kawo ma ki naki a nan?" "A'a zan zo nan na ci tare da ke." "Okay to mu je. A tare suka fita har suka haura sama , a dinning area suka karasa in da Nadra ta ja ma ta kujera don ta zauna ." "Bisimillah ki zauna ina zuwa ." "Me zan zuba ma ki Aunty?" "Ke ma kin san na fi Shan tea da safe da soyayyan ƙwai da hankalin turawa." Murmushi ta yi ta fara hada ma ta tea ta haɗa ma ta komai da komai da take buƙata. "Bari na je na duba ko Yaya Fahad ya gama shirya wa." "Hmmm da alama dama can kina son Fahad munafurci ne ya sa kika nuna ba ki so ko, yayin da kika ma ni alkawarin cewa za ki rabu da Fahad ni kuma ya aure ni shi ne kika yi kane-kane , amma ku saurari abin da zai biyo baya daga ke har shi mayaudarin ." Daidai lokacin suka ji ƙarar buɗe kofa kamar mutum ba fitowa. Ƙamshin turarerensa ne ya fara iso wa gare su. Yana sanye cikin suit farar takaminsa baki da farin glass da yake sanye da shi. Sai da zuciyar Sidra ta buga amma kallo ɗaya yi ma ta ya dauke idanunsa daga kallon ta . Ganin hannunsa time da wasu file ne ya saka Nadra ta mike tsaye tana cewa . "Barka da fitowa Yaye Fahad." "Barka dai Nadfah." Ya faɗa yana rungumo ta jikinsa, kunya ce ta lulluɓe ta don ta tabbatar Aunty Sidra na kallon su. "Kokari. Zame jikinta ya yi yana ce w. "Bisimillah ka zo ka yi breakfast." ''ina sauri ne ana jira na yanzu n nan idan Na dawo zan ci." Jinjina kai tai ta yi tare da cewa a dawo lafiya. "Ba za ki raka ni ba.?'" Ya yi maganar yana nufar hanyar sauka yana kuma cewa . "Aunty Rahama za ta zo anjima ." Cikin farin ciki da jin dadi ta ce Allah ya kawo ta lafiya. Yana fita wayarsa ta fara ruri, Aunty Rahama ce take kiransa. Ya daga yayin da ya isa wajen motarsa. "Hello Aunty Barka da safiya." "Barka dai ya kake ya Nadra." "Muna lafiya duka." "Na ga message naka kana sanar da ni Sidra na gidanka, yanzu haka su Mama suka bar ta?" "Eh wallahi abun ya dame ni." "Ka kwantar da hankalinka ina nan zuwa wallahi yau sai ta bar gidan nan, sai dai ta koma gidan ubanta ko yanka naman jikinta zai yi sai dai ya yi. Kai kafin ma na zo ma sai na biya na sanar da iyayenta halin da ake ciki kuma na sanar da su yau sai ta bar gidanka." Cike da gamsuwa ya jinjina kai yana yi ma ta godiya, sallama suka yi ya katse kiran wayar ya shiga motarsa tare. Da yi wa motar key ya bar gidan. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page6️⃣8️⃣ Cike da gamsuwa ya jinjina kai yana yi ma ta godiya, sallama suka yi ya katse kiran wayar ya shiga motarsa tare da yi wa motar key ya bar gidan. Nadra kam zama ta yi suka fara yin breakfast. Bayan kamar mintuna ashirin suna zaune wajen sai ga text message ya shigo cikin wayar Nadra. Ganin sunan Fahad ya sa Sidra ta yi saurin ɗaukar wayar da sauri kafin Nadra ta ɗauki wayar. Bude messages ɗin ta yi ta fara karantawa kamar haka. *Hi my Nadfah ya kike? Am sorry na bar gida ba mu yi gaisuwar safe yadda ya kamata ba ana jira na ne shi ya sa. Ya gajiyan daren jiya na gode sosai zuma ta. Tabbas daren jiya kin jiyar da wanan majidaɗin daɗi mara misaltuwa thank you so much, I love you more than anything* Sidra na gama karantawa sai zuciyarta ke tafarfasa ta juya ta kalli Nadra ta ga ita ma kallon ta take yi. Don dama ta ji ba daɗi daukar ma ta wayar da ta yi. Don haka ta fara jifar Sidra da wani kallo mara misaltuwa. "Munafukar banza kawai ke sa muka yi za ki rabu ma ni da saurayi na amma kika yi shiru kika sakar ma sa jiki jiki har ya kika samu kansa ko?" "Aunty Sidra maganar gaskiya ya kamata ko hakura da Yaya Fahad tun da ba shi kadai ne namiji a wanann duniyar ba. Matar mutum kabarin sa, wata ba ta auren mijin wata hakazalika wani baya auren matar wani, aure nufin Allah ne shi. Ban taɓa tunanin zan zauna inuwar aure da Yaya Fahad ba, haka shi ma bai yi zaton ni ce zan zama matarsa ba, amma da Allah ya ƙaddara ba ga shi mun yi aure ba muna zaune lafiya ya yarda da ƙaddarar sa ya karɓe ni matsayin abokiyar rayuwarsa, ni ma haka na yarda da shi a matsayin abokin rayuwata. To ke me ya yasa ba za ki yarda da ƙaddara ba a matsayin ki ba musulma ki nemi zaɓin Allah. A gaskiya da ba na ƙaunar Yaya Fahad amma a halin yanzu ina jin sa har ƙasar raina, ban san yaushe ne na kamu da son sa ba amma tabbas na san yanzu ina son sa. Shi ma yana so na don haka ki haƙura ki fauwala wa Allah lamuranki zai taimake ki, don Yaya Fahad bakya gabansa ko ganin ki ba ya son yi, kamar yadda ya ce idan ya bar abu ya bar shi kenan har abada ba zai dake waiwayar sa ba to haka ne. Fata na Allah ya ba ki mijin da ya fi Yaya Fahad." Tana faɗar haka ta tashi da niyyar za ta bar wajen, ita ma Sidra ta yi saurin mikewa tare da cewa . "Ni kike faɗa wa wadan nan maganganun saboda na zo gidan aro?" "Aunty Sidra wannan gidan ba gidan aro ba ne gidana ne na har abada sai mutuwa ce z ga fitar da ni daga cikkin...." Kafin ta mai zancen maganar ta Sidra ta ɗaga hannu da niyyar kai wa Nadra mari. Cike da zafin nama Nasara ya yi saurin riƙe hannun Nadra salqfin ta ce . "Kada ki kuskura hannu ki taɓa jikina, domin yanzu ba da ba me. Kika mare Ni sai na rama wallahi sai dai mu yi kare Juni biri jini wallahi." Cike da mamaki take kallon Nadra domin ba wacce ta sani ba ne, ba wacce ta saba rayuwa da ita ba ne, domin da ita ce, ba wacce ta saba zagi har ta mare ta ba ce, sai dai yi kuka ta ba ta hakuri. Ba wacce ta saba ba ce. Yau wata ce take gani a gabanta ba waccen Nadra ba ce." Nadra ta tashi ta bar wajan dan ta fara gajiya da magana ɗaya da Yayan take yi ma ta. Kullum zuga ta take yi akan ta rabu da Fahad ta yi ma sa wulakanci ko zai yi zuciya ya sake ta. Ita kuma ba za ta iya ba gaskiya ba za ta iya ba domin saɓawa Allah ta sabawa Iyayenta don ta faranta wa Aunty Sidra ba. Saman gadonta ta faɗa tare da sakin kuka , gabaɗaya ta rasa yadda za ta yi da rayuwarta, ga shi lokaci guda ta kamu da soyayyar Fahad ba tare da ta shirya wa hakan ba. Ga Aunty Sidra ta ƙwallafa wa ranta dole sai da shi za ta rayu. _Aunty Rahama_ Bayan ta gama shirin ta na zuwa aiki yara shi an kai su school ne ta fito daga gidan. Driving take yi a motar cikin nutsuwa duk da ta makara da zuwa aiki amma da safen nan ne take da tabbacin cewa za ta samu Abba a gida. Tana isa ƙofar gidan ba ta yi horn ba ta fito daga cikin motar, knocking ƙaramar ƙofar ta yi nan da nan maigadi ya taso ya buɗe. "Barka da aiki Mallam." "Yauwa Hajiya ina kwana?" "Lafiya lau, Alhaji yana ciki kuwa ko ya fita?" "A'a yana ciki?" Ya yi maganar yana matsawa gefe don ba ta hanyar shiga. Ta shiga ciki har zuwa ƙofar falon za ta yi knocking kenan dai ga Abba ya bude kofar zai fito. Tana ganinsa ta durƙusa cikin girmamawa ta ce. "Ina kwana Abba.?" "Lafiya lau, Rahmatuko ?" "Eh Abba." "To suna ciki ki shiga ni za fita?" "Ai wajen ka na zo Abba." "To bisimillah shigo." Ya yi maganar yana komawa ciki Aunty Rahama ta bi bayansa. Da sallama suka shiga falon Umma da Ammi dake zaune a falon suka amsa. Aunty Rahama ta gaida kowa cikin girmamawa sannan ta zauna ta kalli Abba ta ce. "Da farko dai Abba ba maganar Sidra zan yi ma ka ba kasancewar ba ka son a yi zancen ta. Amma ina son sanar da kai ne matuƙar ba ka dawo da Sidra gidanka ba to haƙiƙa za ta kasance barazana ce ga rayuwar auren Nadra." Da sauri suka kalle ta cike da mamaki, Abba ya shiga tashin hankalin jin cewa rayuwar auren Nadra zai iya samun tangarɗa akan Sidra." "Meke faruwa?" Cewar Ammi tana kallon Rahama. "Sidra ta dage ba za ta zauna a gidan mahaifin mu ba sai gidan Nadra a halin yanzu a can gidan Nadra take zaune wanda na san zaman dole matsala za ta biyo baya." Nan ta ba su labarin abun da ya faru daga rashin lafiyar Sidra har zuwa komawar ta gidan Fahad. "Ta ina hakan za ta faru wallahi na tabbatar ba alkhairi ne zai kai Sidra gidan Nadra ba sai don ta kashe ma ta aure, dama tana jin baki cikin an aura wa Nadra Fahad. Abba kasa magana ya yi illa ya dauki wayarsa ya kira ƙanwarsa Laraba. Bugu biyu ta daga ya fara magana cikin ɓacin rai da takaici "Laraba ina son idan kin gama abun da kike yi ki tafi gidan Maimaina ku hadu ku je gidan Nadra ku dawo da Sidra gidana ƙafarta ƙafarku, tana can ta tare a gidanta." Daga haka ya katse kiran. Wayar, daidai lokacin Aunty Rahama ta yi ma su sallama ta tafi. Idanun Abba kawai za ka ƙalla ka san cewa ransa a ɓace yake . _Jalaudeen_ Fitowa ya yi daga cikin gida yayin da gabaɗaya mutanen gidan suka fito don yi ma sa rakiya.. Mota ɗaya za su tafi airport da ita, miyar Yusuf ce "Yusuf ya shiga mazaunin direba yayin da da Jalaluddeen ya zauna gefensa. Bayan motar kuwa Abbi da Ummee ne a baya sai Yasmeen da take zaune a gefen Ummee. A hankali suke tafiya yayin da Yusuf ke cewa. "Amma idan ka dawo wanan karon shi ne dawowar ka ta kammala aikin ko?" "In sha Allah, don na riga na gama haɗa bayanan da zan haɗa, kama su shi ne abun da ya rage, da kuwa wasu abokan harkar ta su da nake so na tabbatar." "Allah sarki bro kana kokari ma Allah ya bada nasara." "Amin ya Allah." "Umme da Abbi suka hada baki wajan amsa wa. Har suka isa airport fitar fitar aikin nasa suke yi. Bayan sun fito daga motar ne Yasmeen ta tsaya a gabansa tana ma da wani kallo mai wuyar fassara. Komawa ya yi gefe wanda gane abun da yake nufi ya sa ta bi shi ta tsaya a gabansa fuska ba walwala. Murmushi mai sauti ya saki kafin ya ce . "Yasmeen rigima ko gaishe ni fa ba ki yi ba." Shiru ta yi masa wanda ganin haka ya sa ya ce . "Okay." Yana kokarin barin wajen. Rigarsa ta rike tana girgiza kai. "Me zan yi ma ki bayan fushi

Chapter 39 of 49