Share this page
tana hawaye, da a baya ne kafin yau canji ko nawa ne idan ta siye abu ba ta karɓar canji sai dai ta bar wa mai kayan. Amma yau ita ce da karbar canjin Naira hamsin. Murmushi ta yi tana goge hawayenta ta ce. "Alhamdulillah ala kulli halin." Ta shiga gidan, sannan ta mai da ƙofar langa-langan ta rufe tare da saka sakata. Shiga gidan ta yi kasancewar ta fita da hasken fitilar wayarta, sai ta bar shi cikin duhu shi kadai a ɗakin. Ita a tunaninta tun da ba gani yake yi ba ai ba amfanin bar ma sa haske da za ta yi. Ta shafa ta same shi tsaye tana mamakin yanda ba ya gajiya da tsayuwa. Tana kallon ɗakin yanzu ina za su kwanta ne, ba tabarma ba katifa. Zaninta ta ɗauko guda biyu ta shimfiɗa ɗaya a in da take zaune, sannan ta ciro daya ta shimfiɗa ma sa a inda yake tsaye ta ce. "Ka zauna a nan." Kamar bai ji ta kuma ya ji ta ya san me take cewa . Coke din ta ciro tare da bread ɗin, ta ɗebi Biredin kaɗan sannan ta ɗebi rabin cike ɗin cikin robar ruwa da ta yi alwala da shi. Ta ajiye wanda ta ɗiba a gabanta sannan ta ajiye sauran da kuma ladar bread ɗin. Coke dake cikin goran ta ajiye ma sa da robar coke din da ta ɗiba ta bar ma sa sauran. "Ga bread nan da abun sha na ajiye ma ka." Shiru bai ce da ita komai ba, sake kallonta ta yi tana maimaita abun da ta faɗa, nan ma shiru bai amsa ba, don haka ta yi shiru tana kallon da da mamaki, har shi zai dinga ji da kansa waye shi? Murmushin takaici ta yi ta zauna a saman zanen da ta shimfiɗa. Da kyar take cin bread ɗin don ba ta taɓa cin irinsa ba, daure wa kawai take yi ba wai don dadi ba sai don yunwa. Haka ta cinye wanda ta ɗeba tare da coke ɗin, sannan ta janyo bottle wataer da ta siya guda biyu ta buɗe daya ta sha, sannan ta rufe ta ajiye . "Za ki iya kwana a nan ɗakin kuwa?" Wani kallo ta ma sa kafin ta ce. "To ya zan yi kana da gidan da ya fi wannan ne da za ka kai ni na kwana?" "Babu ni ma a masallaci nake kwana." Ba ta ce komai ba ta daga kai tana kallon rufin ɗakin. "Na kwanta a nan ne ko kuma na tafi masallaci da na saba kwana a ciki ne na kwanta?" "Wannan kuma ra'ayin ka ne." Shiru ya yi kafin ya ce . "Bai dace na bar ki ki kwana a nan ke kaɗai a cikin wannan gidan." "To idan ka kwana akwai abun da za ka yi mani ne? Ko za ka iya kare ni ne daga cutarwar wani abun?" "Saboda ina makaho ba na gani ko?" Da alama maganar ta soke sa a zuciya, bisa la'akari da yanayin amsar da ya ba ta ransa a ɓaci ko bai fada ba. Sandarsa ya ɗauka ya fice daga cikin ɗakin ya nufi hanyar fita ba ta ce komai ba. Tana ji ya fice daga cikin gidan. Sai anan take ta ji babu dad'i, ga wani tsoro da ta ji ya dirar ma ta lokaci guda. Ko ba komai idan tana jin motsin mutum kusa da ita ai ya fi da ta zauna ita kaɗai. Tsoron gidan ya kama ta ta mike zumbur ta fita daga cikin gidan ita ma tana cewa. "Wallahi ba zan iya kwana ni kaɗai ba." _Sidra_ Suna zaune a katafaren falon gidan, wanda kallo ɗaya za ka yi ma su ka gane wayayyun ƴan mata ne ma su ji da kansu. Wata daga cikin su ta kalli Sidra ta ce . "Yanzu ba za ki haƙura da wanann burin naki ki koma gida tun lokaci bai ƙure ma ki ba?" "Khadijah kenan, ai ba zan koma gida ba har sai burina ya cika." "Matsalarki kenan ki ce ke ba wanda zai fi ki sai dai ki fi kowa? Idan Allah bai yi za ki samu wanan ɗaukakar ba fa?" Murmushi Sidra ta yi kafin ta ce "Khadija duk abinda nake nema zan same shi , ban taɓa neman abu na rasa ba, Hakazalika wanann abun da na saka a gaba zan same shi in sha Allah." "Eh watakila ki samu wancan abu amma za ki iya rasa Fahad da kika ƙwallafa rai sai shi, kodayake yanzu ba ki son sa tun da kuka gudu a ranar aurenku." "Fahad nawa ne ni kaɗai ba wata mace da ta isa ta raɓe shi ban ga bayanta ba. Kuma ba wai don ba na son sa ba ne, sanin cewa yana masifar so na kuma na san zai jira ni na dawo ya sa na tafi ba tare da tunanin wata matsala ba, kuma iyaye na na san da zaran na dawo za su yafe mani don farin cikin gani na za su yi. Ke dai kawai Allah ya kai mu gobe mu bar garin nan na samu burina ya cika na samu ɗaukaka na dawo gida cike a alfahari." Ta yi maganar tana Murmushi. "Sady baby kin san na kashe wayata, ki ara mun taki wayar na kalli hoton masoyina Fahad." Mika ma ta wayar ta yi tana karba ta kunna Data ta shiga Instagram, shafin Fahad ta shiga in da ta dinga kallon kyawawan photonsa a shafinsa nasa na Instagram. Hoton da ya dora ta zuba wa idanu taba kallonsa. Sanye yake cikin tsadadden Suit baƙi a jikinsa, ya daura kafa ɗaya kan ɗaya, bakin hannunsa ɗaure tsadadden agogo. Ya yi kyau sosai, ba ta san lokacin da ta sumbaci wayar ba tana furta furta kalmar "I love you Fahad." Kafin ta rufe datar ta miƙa wa Sady wayarta. "Dole ki haukace akan son Fahad domin ya hadu iya haɗuwa ga kyau ga kuɗi ga gayu ai kowace mace za ta so shi." Wata ce ta faɗa a cikinsu Nam dai suka cigaba da firar su akan Fahad, ita kuma tana jin dadi yadda ake cewa saurayin ta ya haɗu. _Fahad_ Bayan ya yi parking motarsa ya fito daga cikin motar fuskarsa ta yi jajir. Gabɗaya jama'ar dake falon kasancewar duka dangi ne bare ba su fara shigowa ba. Muryar mahaifiyarsa ya ji tana cewa. "Fahad." Sai da ya ɗan tsaya kafin ya juyo duk suka kalle shi. Cikin tashin hankali Mama ta mike tsaye ta karasa inda yake tsaye ta dafa kafaɗunsa da hannayen ta biyu ta ce. "Daga gidan surukan naka kake?" Kai kawai ya jinjina ba tare da ya yi magana ba. "Me yake faruwa to?" "Sidra ta gudu yau ba wanda ya san in da ta je." "What! Ta gudu?" Gabadaya falon shiru ya ɗauka yayin Mama ke salati. Kalarsa ce ta ce "Dama ba ta son sa ne?" Ma ta ba ta amsa da cewa. "Wallahi tana masifar son sa, maybe ma son da take yi ma sa ya fi nasa yawa. Ban san dalilin haka ba. Ɓoyayyar ajiyar zuciya Farida ta sauke tana mai farin cikin jin amarya ta gudu. Ko ba komai yanzu dole ya aure ta. Mahaifiyar Faridan ce ta ce. "Ga irin ta nan ya je ya nemi aure gidan ƙananun mutane, ga dangi ana ta yi ma sa tallar ƴan uwansa ya nemi daya ya ce baya so. Ga Farida nan sabida son da take ma sa ta bar kowa nata ta zo ta tare a gidan nan sabida shi amma yake wulaƙanta ta. "Kalarsa ta ce ai kuwa dole ya aure ta." Daidai lokacin Baba ya fito daga part ɗin sa yana tambayar me ke faruwa. Mama ta ma sa bayani shi ma salati ya yi yana cewa. "Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi." Sai a je a kwaso kayan lefen da aka kai ma su ya ke ya siye uban kaya kamar wanda zai bude shago ko bai san zafin kudi ba. "Aunty kar ku je Please." Ya fada yana kallon ƙanwar mahaifiyarsa. "Saboda me?" "Sun bani hakuri sun ce na amince a maye mani gurbin ta da ƙanwarta Nadra." Wani kuka Farida ta saka wanda kowa sai da ya kalle ta, ta haura sama tana kuka. Baba ya ce. "Kai kana son ƙanwarta ɗin ne?" "Wallahi ni ma ban sani ba." Ƙanwarsa ta yi caraf ta ce. "Wallahi in dai Nadra ce ba ta da matsala, wallahi wacce kake so ita ce mai matsalar. Sai girman kai da izza ni dama wallahi ba da ɗin raina za ka yi auren..." Mugun kallon da ya yi mata ya saka ta ja baki ta yi shiru, ita kanta Mama ta ji dadin hakan, don ta san su sau uku suna zuwa gidan kuma ta fi yabawa da hankali da nutsuwar Sidra." "Yanzu aka amsa masu cewa za ka auri ƙanwarta?" Jinjina kai ya yi ba tare da ya yi magana ba, Baba ya ce "Allah ya sa hakan ya fi zama alkhairi, a cigaba da shirye-shiryen da ake yi. Daidai lokacin da kiranta shigo wayar Fahad, ganin abokinsa ne ya saka ya fita zuwa harabar gidan, motoci guda biyu ne suka shigo. Matasan samari ne ma su ji da kansu kimanin su takwas suka zo gidan. Jagora ya yi ma su zuwa part ɗin sa, ta kofar baya ba tare da sun shiga part falon ba aika shiga part ɗin nasa. Suna shiga ciki suka Zazzauna a falon yayin da shi ya shiga cikin bedroom ɗin sa. Ganin yanayinsa ya sa suka san cewa a kai matsala, ba wanda ya yi magana har ya fito fuska ba walwala yake yi ma su barka da zuwa. Musamman waɗanda ba a kasar nan suke ba daga wata ƙasar suka zo halartar bikin aurensa. "Man lafiya kuwa?" A jiyar zuciya ya sauke don ya san ba ɓoye ma su komai zai yi ba. "Sidra ta gudu yau da safe." Mamaki da kasuwa suka shiga, suna tambayar sa dalili. Nan ya ba su labarin komai da ya faru har ƙanwarta da iyayen suka ba shi a madadin ta. Nan aka shiga jajanta lamarin tare da kara ma sa ƙarfin guiwa akan auren Nadra, sannan suka bashi shawara ya cire damuwa ko saboda jama'a da za su zo daurin auren kada a fahimci wata matsala. Haka suka dinga ba shi kwarin gwiwa har ya ɗan saki ransa suka fara shirye-shiryen zuwa ɗaurin aure. _Nadra_ Lokacin da aka fito da ita daga ɗakin da aka shiga da ita sai da Gwaggo Laraba ta saki. baki tana kallonta. Ba karamin kyau ta yi ba baƙar fatarta ta kara sheƙi da ɗaukar idanu. Kudin aikinsu Goggo Laraba ta bayar suka wuce don har lokacin dire ba na jiran su. Suna bayan motar Nadra ta sake gwada kiran wayar Sidra. Har lokacin wayar a kashe. "Gwaggo har yanzu fa wayar Aunty Sidra ba ta shiga, wani irin wurin gyaran jiki ta tafi da za ta kashe waya?" Gwaggo Laraba dai ba ta ce ma ta komai ba, sai ta sake cewa. "Maybe ma tana gida ta dawo ko?" "Ba na tunanin ta dawo don wajan da nisa kuma ana dadewa kafin a gama. Yanzu mutane sun taru ba mu son a san cewa Amarya ba ta nan, don haka ke ce za ki saka kayanta a matsayin kece Amarya kafin ta dawo, kin ga ba kowa ke banbance sunan ku ba ko?" Cikin rashin fahimta ta ce . "Ni na kasa gane wannan al'amari ta ya zan shirya a matsayin ta bayan ba ni ba ce Amarya." "Eh saboda mutane za'a iya ayi ta tambayar amarya ba dadi a ce ba ta nan, kuma Ummanki da Abba su ne suka ce a yi haka ko ba za ki bi maganar su ba ne?" "Shi ke nan zan yi Allah ya dawo da ita lafiya." "Amin yarinyar kirki ." Daga haka suka ƙarasa gidan dake cike da jama'a, don rana ta yi gidan ya fara cika. Ta part ɗin Umma suka bi suka shiga bedroom ɗin ta. Duk da ta yi kwalliya amma akwai damuwa a tattare da ita. Nadra ta rike hanjun Umma ta ce "Umma ba ki da lafiya ko?" Shafar gefen fuskar Nadra ta yi tana Murmushi ta ce "Lafiya ta lau ki yi sauri ga mau kwalliya can tana jiran ki tun ɗazu ta zo." Za ta sake wata magana Umma ta rufe ma ta baki ta ce. "Sarkin magana je ki kar ki ɓata ma su lokaci." Haka ta fita cikin sanyin jiki Umma ta bi ta da kallo tana goge ƙwalla. _Makaho_ Yana zaune a barandar masallacin ya jingina da bangon masallacin ya daga kai sama. Kamar daga sama ya ji ƙamshin turarenta, lalubar sandarsa ya yi ya na cewa. "Ma'eesha ke ce?" "Eh ka taso mu tafi gida." Tausayinta ta kama shi amma duk da haka bai hana shi cewa ba. "To ni da nake Makaho ba na gani wani amfani zan yi ma ki, tun da ba zan iya kare ki daga cutarwar wani abun ba." Shiru ta yi don ita ma ta san dole ya ji ba dad'i. Tashi ya yi ya na rike da sandarsa ya yi gaba ba tare da ya ce komai ba, ita ma tana bisa a baya har suka shiga gidan ta mayar da kofar ta saka sakata ta rufe. *Mamman Ihsan ce*✍️ 09065357995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page0️⃣5️⃣ Shiru ta yi don ita ma ta sa dole ya ji ba daɗi .Tashi ya yi yana rike da sandarsa ya yi gaba ba tare da ya ce komai ba, ita ma tana bin shi a baya har suka shiga gidan ta mayar da ƙofar ta saka sakata. Da lalube ya shiga cikin ɗakin, in da yake tsaye ɗazu can ya je ya kara tsaya wa. Ta shiga tana rike da ƙaramar wayarta ta kunna torchlight. Wanka take so ta yi sai dai ba ta iya wanka da ruwan sanyi, ga shi ba ruwan zafi. Kayan jikinta ta cire ba ta damu da yana wajen ba saboda ta san makaho ne, towel ta daura ta nufi ƙofar fita. "Ina kuma za ki ke dare ne yanzu fa." Ba ta iya amsa ma sa ba sakamakon kukan da take yi na rayuwar da ta tsinci kanta a ciki. Sai dai kuka mara sauti take yi, idan ba wanda ya kalli idanunta ba to ba zai je tana kuka ba. Banɗakin ta nufa kasancewar akwai ruwa da makaho ya cika bokitin na karshe ta ajiye. Sai da ta rintse idanunta tana sakin ajiyar zuciya sannan ta iya yin wankan. Tana fitowa ta same shi tsaya a kusa da ƙofar banɗakin, ba ta yi ma sa magana ba shi ma bai yi ma ta magama ya fito rike da bokitin ya nufi bakin Rijiya zai ɗebo ruwa. Man shafar ta ta dauka bayan ta goge jikinta sannan ya shafa mai. Bayan ya shafa mai ta fesa turare na jiki wato body spray. Kayan barci ta saka riga da wando da wata hula mara nauyi ta saka. Tana kallon ɗakin ta rasa ta ina za ta kwanta, ga ba gado ba katifa ballantana tabarma. Tana tsaka da wannan tunanin sai ya shigo cikin ɗakin da sallama a bakinsa. Ta amsa ma sa ba tare da ta lalle shi ba. Yana shigowa daidai yana kawowa wajen shimfidar ta ta yi ma sa ta ce. "Ga zanin da na shimfida ma ka nan ka zauna akai ." Ba musu kuwa ya zauna ya tanƙware ƙafarsa, shiru dakin ya ɗauka ba wanda ya yi magana. Bayan ta gama tunani sai ta koma ta rufe kofar dakin ta saka sakata. Daidai lokacin nepa suka kawo wuta haske ya gauraye ɗakin gabaɗaya. Kallon bread da coke ɗin da ta ajiye ma sa ta yi ta ga bai taɓa ba. Taɓe baki ta yi sannan ta dauki karamin akwatin ta yi pilow da shi bayan ta kwanta. Sai ta ji ya yi ma ta girma da yawa wuyanta zai iya ciwo. Cire shi ta yi sannan ta yi pilow da hannunta ta kwanta. Lokacin karfe goma sha daya na dare ne. Wayarta ta soma ruri ta ga lambar ba ta ƙasar nan ba ne, kuma ta san waye, katse kiran wayar ta yi tare da gyara kwanciyarta da sam ba ta ji fadinsa ba." Sake kira aka yi har ya katse ba ta ɗaga ba, a karo na uku ne ta ambaci sunansa. "Oh Allah Abdul ban san me zan ce ma ka ba." Ta yi maganar tana goge ƙwallar tausayin kanta da take ji, take wani sabon kuka ya zo ma ta sai ta toshe bakinta tana yin sa a hankali. Messages ne ya shigo wayarta ta duba still shi ne. *Ina fatan jina cikin aminci farin cikina, na ga kina katse ma ni kira fatan ba wani laifin na aikata ba, Please ki amsa wayata ko hankalina zai kwanta.* Tana gama karantawa ta katse kiran wayar, gabaɗaya ta kashe wayar ta koma ta kwanta tana hawaye. Kamar sauro na jiran ta kwanta suka fara kai ma ta hari. Abinda bai taɓa faruwa da ita ba kenan, sauro su addababe ta haka. Ga cizon sauro ga kuma kukan sauro da suke yi ma ta a kunne. Tashi zaune ta yi ta saka kuka tana kara sakin kuka kamar karamar yarinya. "Ma'eesha lafiya." "Wallahi sauro suke damuna ba zan iya barci a haka ba." "Ayyah sorry, ba ni ɗankwalin kayan ki." Ba musu ta zuge zip ta ɗako ta mika ma sa, ya matso kusa da ita ya karɓa. "Ki manta to." Kwanciya ta yi kamar yadda ya ce, ya dinga kore ma ta sauro da ɗankwalin. Tana jin kamar yana ma ta fifita har ɓaci ya ɗan fara daukarta kuma ya hadu ma ta da gajiya. Haka makaho ya dinga yi wa Ma'eesha fifita har ta yi barci . Tun karfe sha daya har biyu na dare yana zaune yake kore ma ta sauro. A lokacin ta farka ta ga yadda ta bar shi haka yake yi ma ta fifita. Awa uku kenan yana abu ɗaya. Tausayinsa ya kama shi cikin tashin murya ta ce . "Ka kwanta ka yi barci na gode." "Ba za ki iya barci ba idan na daina ku yi barci kawai, dama ni ban saba yin barcin dare ba." Barcin ta cigaba da yi har aka yi kira sallar asuba. Sai a lokacin ya ajiye ɗankwalin ya mike tsaye daidai tana buɗe idanunta. "Da ido ta bishi ya fice daga dakin bayan ta dauki Sandarsa." Bayan kamar mintuna goma ya shiga da alama alwala ya yi, sai ya ce . "Zan tafi masallaci sai an yi sallah zan shigo." Kai kawai ta jingina kamar yana ganin ta, ita ma tashi ta yi ta nufi banɗaki don ɗauro alwala. _Nadra_ Tana shiga cikin ɗakin ta samu mai kwalliya na jiranta. Da sallama dauke a bakinta ta shiga in da ta samu ɗaiyar Gwaggo Laraba tare da mai kwalliya. Duk da kasancewar ita ba mai son kwalliya ba ce kamar Sidra. Amma yanzu kam ba ta isa ta ce ba ta son kwalliya ba. Hijabinta ta cire wani ni'imtacen ƙamshi na tashi daga jikinta. "Bari na yi sallah lokacin sallah ta yi ." Ba ta jira cewar kowa ba ta nufi bathroom don sauro alwala Sai da ta gabatar da sallar sannan ta dawo kan su. Zama ta yi dadai lokacin da wayarta ke ringing, ta duba ta ga Ya Sayyadinta ne ke kiran wayarta. Murmushi ta yi za ta ɗaga sai Gwaggo Laraba ta karbi wayar ta kashe ta gabaɗaya ta ce. "Ki tsaya a gama da sauri ba lokaci, kina gani gidan ya fara cika da jama'a ko?" Mai kwalliyar ta buɗe akwatin kayan kwalliyar ta dubi Nadra ta ga ba ita ba ce ta kira ta, hasalima wacce ta kira ta fara ce ita kuma wanann baƙa ce. Kallon Gwaggo Laraba ta yi ta ce . "Ko dai ba gidan ba ne?" "Nan ne kar ki damu wannan ce za'ayi wa wacce ta kira ki Sidra ce ita ce ƴar wannan." "Okay." Ta faɗa a takaice ta fara yin aikin da ta kawo ta yi. Nan ta tsantsara wa Sidra kwalliya wanda ya yiasifar yi ma ta kyau kamar ba ita ba. Sannan aka ɗauko ma ta kayan Sidra wanda dama shi za ta saka a lokacin. Sai dai an ɗan sake ba tela ya sake buɗa ma ta faɗin kayan kasancewar Nadra ta fi Sidra diri da cikar halitta. Karba ta yi ta shiru tare da taimakon mai kwalliyar ta shirya ta, ta yi ma ta ɗaurin Ɗankwali. Nan ƴan uwa suka dinga ɗaukarta photo, ita dai har lokacin ba ta saki jiki ta ba, ta rasa dalilin dai zai saka a ce saboda Sidra ba ta nan ta maye gurbin ta. Ga shi an ce ba yanzu za ta dawo ba, ita dai addu'ar ta Allah yasa kafin karfe huɗu ta dawo, don idan ba ta dawo ba to ita kam ba za ta iya maye gurbin ta a wajen Dinner party ba. Ta ya ya za ta fito ta tsaya tare da Fahad kai ba zai yiwu ba ma. Ita kadai take saƙa da warwara har ta ji ana cewa karfe biyu ya yi yanzu za'a daura aure. Tsintar kanta ta yi cikin faɗuwar gaba da tsoro. _Fahad_ Kwance yake a bayan motar ya jingine bayansa da jikin motar, sanyi A.C da ƙamshin turarensa ke tashi a cikin motar. Mukhatar da Aluyi sun saka shi a tsakiya, Kabir na zaune a gefen direba wajen me zaman banza Suna ba shi baki tare da kwantar ma sa da hankali, don sun san yana cikin damuwa. Har aka karasa kofar gidan surukan nasa bai buɗe idanunsa ba. Kowa ya fito ya bar sa a cikin motar. "Ko sai mun fito da kai ne?" Cewar Mukhtar yana kallonsa yana Murmushi. "Hana Majidaɗi ka saki ranka ma na sai ka ce wanda aka yi wa auren dole?" Harararaa Fahad ya yi tare da cewa . "To idan ba auren dole aka yi ma ni ba na soyayya ne?" Ya faɗa yana ziro fararen ƙafarsa wanda ke cikin takal ki ƙirar kamfanin Prada, takalmar baƙi ne. Yana sanye da farar shadda gezna wanda aka yi ma sa aiki da baƙin zare riga da wando har da babbar riga. Ya fito yana gyara zaman babban rigarsa. Kansa sanye da bakin hula, hannunsa ɗaure da tsadadden agogonsa na Rolex Day-Date 40 (president watch) wanda ya zauna a hannunsa kamar don shi aka yi . Duk wanda ya kalle shi zai gane shi ne angon domin ya sha banban da kowa a wajen. Zuwan su ba jimawa aka fara shirye-shiryen ɗaurin auren. Ɗaurin aure ne da ya tara manyan mutane na gida da waje. Manyan kusoshin gwamnati da da saraki da ma su mulki, har da shahararrun ƴan kasuwa . Mutane suna ta yi wa Fahad fatan alkhairi ana taya shi murna, sai dai ya yi kokarin ganin damuwar da yake ciki bai shafi walwalarsa ba. Yana nan zaune ba abinda yake yi sai tunanin Sidra sam ya kasa dalilin da ya sa ta aikata ma sa haka, duk ikirarin da take yi na tana son sa har za ta iya yin haka? Bai ankare sa an ɗaura ma sa auren ba sai da ya ji an dafa sa ana taya shi murna. Bayan an gama an tashi ana ta ma sa fatan alkhairi ana ɗaukar hotuna. Daga nan Baba ya ce wa Fahad su shiga shi da abokansa su su gaida surukansa Haka kuwa aka yi da shi da Mukhtar, Khabir da Aliyu suka shiga cikin gidan. Falon Abba wanda shigowar su kenan shi da ƴan uwansa da abokansa. Suka durƙusa suka gaishe su tare da yi ma su godiya da ba su ƴa da aka yi . Daga nan kuma suka nufi main falon gidan, suka ga jama'a mafi yawansu ƴan uwa ne. Tun da suka shiga gidan kansa a ƙasa yake har suka durƙusa suka gai da dangin Amaryar. Kasancewar ba kowa ya san angon ba, kuma duk wani abin rabo da za'a raba wanda yake da photon Sidra da Fahad ba'a raba ba don kada jama'a su gan shi tare da Sidra a photo a fahimci wani abu. "Ina angon yake?" Wata Dattijuwa ta tambaya, Haidar ya nuna ma sa Fahad da ya sunkuyar da kai tun da suka shigo. "Ma sha Allah kyakkyawan saurayi kuwa ta samu, Allah ya ba ku zaman lafiya mai ɗore wa da zuri'a ma su albarka. Yadda muka zo taron biki Allah ya sa nan da watanni tara mu zo taron suna." Amin aka amsa ana sake rangaɗa guɗa wanda Fahad yake jin samuwar har cikin kansa. Nan suka yi ma sa nasiha sosai sannan ya mike su ma abokan nasa suka mike, in da suka nufi part ɗin Umma. Har lokacin tana cikin bedroom ɗin ta ita da wasu ƙawayenta. Gwaggo Laraba dake falon ita da jama'a ce ta shigo don kiran Umma ta zo ga ango ba abokansa Gabadaya suka fito ita da ƙawayenta, angwayen suka gaishe su suka sa ita dai Ummar karfin hali take yi, hade ɗaya damuwar halin da Nadra z ga shiga ciki take

Chapter 4 of 49