Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ *Alhamdulillah na gode Allah da ya bani ikon rubuta wannan labarin da na daɗe ina son rubuta shi. Allah ya bani ikon rubuta abun da zai amfani al'umma.* *Ni ce ta ku dai marubuciyar nan da na saba faɗakar da ku da misaɗantar da ku, to yanzu ma na zo ma ku da sabon labari mai cike da sarƙakiya tuggu da makirci, wanda zai bar ku cikin shauƙi da zumuɗi. Ku dai ku biyo ni kun san dai ba taɓa ba ku kunya ba, wannan na daban ne mu je zuwa* Ɗanɗano Page0️⃣1️⃣ Tafiya yake yi cikin takunsa na natsuwa da kamala, Sandar dake da hannunsa yana dogarawa ne zai tabbatar ma ka da cewa makaho ne shi, kuma sandar ce jagoransa. Sai baƙin glass dake sanye a idanunsa wanda ya zauna a karan dogon hancinsa da ya dace da kyakkyawar fuskarsa. Fari ne dogo mai matsakaicin jiki, sai dai kallo ɗaya za ka yi wa kyakkyawar fuskarsa ka fahimci cewa shi ba mai yawan fara'a ba ne da sakin fuska. Yana da ƙirar jiki da cikar zati irin na cikakken ɗa namiji. Sanye yake da wani royal blue yadi mai sauƙin kuɗi wanda ake kira da yi shirunka maraya, daga ganin kayan jikinsa za ka san sun sha jiki sai dai da dukkan alamu saurayin mai tsafta ne don kayan fes suke babu datti duk da kasancewarsa makaho ne. Tafiya yake yi a cikin layin unguwar da ta kasance unguwa ce ta ma su hannu da shuni, tun daga ganin shimfiɗaɗiyar kwaltar da ta shiga cikin unguwar ta ko ina har zuwa ƙerarrun gidajen dake cikin unguwar. Unguwar ta kasance shiru ne ba hayaniya. Har ya iso daidai katafaren wani gida ya tsaya, shiru ya yi na tsawon mintuna biyu kafin ya yi knocking ɗin danƙareren gate ɗin dake gidan. Daga ciki ya ji muryar Musa mai gadi yana cewa. "Waye nan?" Don tun da ya ji ba'ayi horn ba ya san ko ma waye ba da mota ya zo ba talaka ne. Ƙarasawa ya yi don dama daga toilet ya fito yana surutu shi kaɗai. "Ko ma waye dole za ku haƙura ku koma, don ita matar kirkir dake da tausayin talakawa kuke zuwa rana ba ku yanzu Allah ya karɓi rayuwarta ba ta raye, wacce ta rage a gidan ko mutuwa za ku yi ba za ta lalle ku da gashi ba ballantana ta taimaka ma ku." Yana buɗe ƙofar ya ga wanda ke tsaye ya ce ya ce. "Mallam makaho ne?" Shiru ya ma sa bai yanka ma sa ba, sai ya sake cewa. "To daga yau sai dai ka daina zuwa don wacce kake zuwa domin ta take ba ka Allah ya larɓi rayuwarta, tsawon kwanaki hamsin kenan yau, kuma na san ka zo ta'aziyya , kuma ka zo bayan wata ɗaya da rasuwar . Ina mai ba ka shawara ka bar nan kafin waccen marar mutuncin ta fito ta ganka uwar ɗakinka ta rasu ka sani ko?" Gundura ya fara yi da maganar ta Mallam Musa sakamakon ba ya son magana ko hayaniya , ga shi Mallam Musa bai iya magana a hankali ba, cike da mishkilanci ya yamutse fuskarsa yana ƙokarin shiga cikin gidan. Da kallo Mallam Musa ya bishi yana cewa. "Sai shegen girman kai da mishkilanci, ga shi nakasashshe yanzu an koro ka ka fito." Mamy ce ta fito tana kallon Makaho tana washe baki tana cewa. "Ango ya iso daukar Amaryarsa kenan Alhamdulillah." Bai ce komai ba sai sake tsuke fuska da ya yi, yayin da Mallam Musa ya cika da mamaki to waye angon ba dai makahon nan ba. Tsuke bakinsa ya yi ya koma bakin aikinsa yayin da Mamy ke yi wa Makaho iso tana cewa. "Shigo sirikina." "Alhaji dake zaune a falo ya ɗago kai yana kallon Makaho dake shigowa tare da sallama. Yana mai amsa sallamar ta sa yana bashi izinin zama. Zama ya yi a kan lallaudan centre carpet dake tsakiyar falon "Ina wuni Daddy." "Lafiya lau Khalifa." Kallo ɗaya ya yi wa Mamy ya kau da kai kamar an masa dole ya ce . "Ina wuni Mamy?" "Lafiya lau angon Ma'eesaha." Ta amsa tana wani dariya na mugunta. Shiru falon ya yi tana jiran Dady ya yi magana sai ta ji shiru, gabadaya baya cikin tunanisa. "Alhaji" Shiru bai amsa ba sai da ta sake kiransa a karo na uku Sannan ya dawo tunanisa yana cewa. "Na'am." "Ga shi ya zo ɗaukar Amaryarsa da aka ce ya zo ya ɗauka, ka bar shi zaune." "To ai na kira ita Ma'eesha tana hanyar dawowa." "Okay, ka jira amaryar ta karasa sai ku tafi ta je lalle da kitso ne." Bai ce komai ba illa ya sunkuyar da kai ƙasa. _Ma'eesha_ Fitowarta kenan daga cikin shagon saloon tana sanye da rigar Abaya green colour, tana gyara mayafin abyarta hannunta rike da handbag ɗin ta da wayarta I phone 16 pro max. Wayarta ce ta fara ruri tana dubawa ta ga Inno ce me masu aiki. Ɗaga wa ta yi ta maƙala wayar a kunne tana maƙe kafaɗarta yadda wayar za ta zauna, ta zuge zip ɗin handbag ɗin ta ta ciro makullin motarta tana cewa. "Hello Inno ya aka yi ne?" Shiru Inno ta kasa magana don har ya nufi motarta ta bude Inno ba ta yi magana ba. Zama ta yi a driving seat sannan ta ce. "Inno lafiya kuwa." Cikin kuka ta ji muryar Inno na cewa. "Ma'eesha kada ku dawo gidan nan ki je wani wuri." Cikin faɗuwar gaba ta ce. "Me ya faru ne Inno?" Ta ji ta sake cewa. "Aure aka ɗaura ma ki yau da wannan makahon da ya taɓa ceton ran mahaifiyar ki har ta ke kyautata ma sa." Wani dariya Ma'eesha ta yi tare da cewa "No ba zai yiwu ba, kada ki dake Mani wannan wasar." Ta katse kiran wayar tana cewa. "Haba wane irin aure ba tare da an nemi amincewa ta ba, ko auren ne ma ai sai a ce na fito da wanda nake so amma ba za'a yi ma ni dole ba, ballantana s ce wani makaho wanda ko a mafarki bai isa ya zo mijina ba ballantana a zahiri?" Tsuke ta ja tare da yi wa motarta key ta bar harabar Saloon ɗin. Horn take dannawa har maigadi ya wangala ma ta gate ta shigar da motar tana mai yin yin parking a parking space. A hankali ta sako da fararen ƙafafuwanta da suka sha zanen kalli ja ba baƙi. Fitowarta yi hannunta rike da handbag ɗin ta da makullin motarta. Da sallama ta shiga falon gabanta na faɗuwa. Gabadaya suka amsa ma ya sallamar ta shiga ciki. Ganin makaho ya haifar ma ta da wata faɗuwar gabar da ba ta san dalili ba. Bayan ta gaida Dady da Mamy ta miƙe za ta nufi ciki ta ji Mamy na cewa. "Alhaji ka sanar da ita ta fito ta bi mijinta tun da ga shi nan zaune yana jira tun ɗazu. Mummunar faɗuwar gaba ce ta ziyarce ta, wanda har sai da ta saki handbag ɗin ta a ƙasa. "Ke Ma'eesha zo nan." A hankali ta take taku kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki ta zo gaban Dady ta zube. "An ɗaura auren ki da Khalifa makaho yau, ku tashi ki bi mijinki Allah ya ba ku zaman lafiya." Kallon Dady take yi kamar wata sokuwa ta ma rasa me za ta ce ma sa, don ganin abin take yi kamar wani alamara. "Da...Da...Da..." Ta ma rasa me za ta ce wani kalma za ta kama da za ta yi amfani da shi wajen yi wa Dady magana. Kafin ta samu ƙarfin zuciyar furta. "Dady wane laifi na aikata da ka hukunta ni ta wannan han?" Tsawar da ya daka mata ne ya saka ta firgita. "Tashi ki kwaso kayan sakawarki ki bi mijinki, idan kika sake yi Mani wata magana a nan sai na ba ki mamakin da ya fi wanda kike ciki?" "Ba da ke mahaifinki ke magana ba kina zaune?" Jiki ba ƙwari ta miƙe ta ɗauki handbag ɗin ta da makullin motarta ta nufi ɗakinta. Nan ta samu Inno mai masu aiki, tana ganin Inno ta fada jikinta ta rungume ta tana fashewa da matsanancin kuka." Ita ma Inno kuka take yi tana cewa. "Allah ya yana tare da ke Ma'eesha, shi ya sa na kira ki a waya na ce kada ki dawo gidan nan. Wannan kishiya mahaifiyarki ba ta tsoron Allah, so take kawai ta ga rayuwarli ta tagayyara shi ya sa ta saka mahaifinki ya aura maki makaho musaki wanda ba ya da cin yau balle na gobe, ta ya ya mace irinki da kika taso cikin gata da jin ɗadin more rayuwa za ki auri fakiri nakasashshe? Ita me ya saka ba ta saka ya auri ƴarta Agola ba, sai ke da gidan uban ki ne za'a yi ma ki wannan cin kashin?" Cikin kuka Ma'eesha ta ce. "Mamy ba ta so na ta tsane ta saka mahaifina dake son farin cikina yanzu ya juya mani baya ya tsane ni, duk da haka bai ishe ta ba sai da ta saka ya aurar da ni a inda ta san zan wahala me na yi ma ta ne, Da zuciya daya mahaifiyata ta kawo su gidan nan ita da yaranta suna cin arziki, karshe ta ci amana ta auri mijin aminiyarta suka ci gaba da zama duk da haka Mahaifiyata ba ta nuna ta ji zafin abinda ta yi ma ta na aure ma ta miji ba, ta zauna da ita da zuciya ɗaya, sai bayan ran mahaifiyata ne za ta ma ni haka sakayyarta ga Mahaifiyata kenan?" Kuka suke yi dukkansu, kamar daga sama suka ji an daka ma su tsawa. A firgice suke kallon ƙofar. Mamy ce tare da Autarta Laila. "Sannu muna munafuka kina hure ma ta kunne ko?" Cikin rawar jiki Inno take ba Mamy hakuri ta fita daga ɗakin. Ma'eesha ta kalle su da idanunta da suka yi ja ta kawar da kai ta cigaba da haɗa kayanta a cikin babban trolly tana kuka. "Hi Amaryar makaho ya kike?" Cewar Laila tana dariya. "Mamy idan ta tafi ɗakin nan zan dawo da zama don ya fi nawa girma, ko funiture ɗin ya fi nawa kyau." Mamy ta kalli ƴarta ta ce . "Kar ki damu Shalele sai yadda kike so za'ayi." Kallon Ma'eesha dake hada kaya ta yi ta ce. "Ba ke mai gidan uba ba? Har kina yi wa yarana gorin cewa su agololi ne ko? To yanzu ke da gidan uban ki ne na saka uban naki ya yi waje dake, su agolan da kike yi wa taƙama da gidan uba su ne za su yi iko da gidan, ke kuka sai ki je ki fara cin garin kwaki, don ko kayan Gara da kayan ɗaki na hana ayi ma ki su ki je can ku ƙarata. Kina hutawa anan sai dai masu aiki su gyara Maki ɗaki su wanke Maki toilet ayi maki wankin da guga, ki sa a girka Maki abinda ranki ke so yanzu duk ba wannan a gidan makaho." Laila da Mamy suka sake saka wata dariyar har suna tafawa kamar wasu kewaye. Wannan karon Ma'eesha kukanta ne ya ƙaru sosai kamar ranta zai fita, ita kadai ta san halin da take ciki a wannan yanayin. Bayan ta cika babban trolly ne ta ɗauki madaidaici ta zuba underwears ɗinta a ciki. Sannan ta dauki karamin cikinsu ta zuba kayan kwalliyarta da turarruka, sannan ta dauko set sarƙar zinarenta za ta saka Mamy ta ce ke dakata ba in da za ki je da wannan." Wani kallo Ma'eesha ta yi ma ta ta ce . "Na mahaifiyata ce ita ta bani kyautatarsa dole ne tafi da shi." Daidai lokacin Dady ya shigo yana cewa. "Me kike yi ne har yanzu?" Mamy ta yi saurin cewa. "Alhaji ka karbi sarƙar set ɗin Gold ɗin nan kafa ta tafi da shi a sace ka san dai darajarsa." "Ke Ma'eesha kawo ɗan akwatin nan." Ta mika masa kawai ta zuge zip ɗin, sannan ta bude wata drawer ta ɗauko 🏧 card ɗin ta na cire kuɗi. "Alhaji ka karbi ATM ɗin nan, su ma, ta tafi haka nan daga ita sai kayanta." Tana rufe baki ya karɓa Atm card ɗin kamar me jiran umarni.key ɗin motar dake saman handbag ɗin ta Mamy ta kalla ta ce. "Har da makullin motarta ma ka karba, don gidan da za ta zauna ba ƙofa ballantana a samu gate na shigar da motar, idan aka ajiye waje za'a sace." "Eh haka ne." Ya fada yana mika hannu. Ba musu Ma'eesha ta miƙa ma sa ya karɓa ya fice daga ɗakin. "Ai duk wani abu da na san zai Maki amfani ba zan bar ki da shi ba." Ta fada tana jan hannun Laila suka fice. Ɗayan trolly ɗin ta fara fitowa da shi ta ajiye falon ta koma ciki. "Kai makaho tashi ka dauki babbar akwatin kayanta ku tafi za ta fito da kananan." Tashi ya yi yana lalube har ya ji ya ci karo da akwati ya ja yana yi wa Dady godiya da sallama ya fita. Tana fitowa rike da dayan madaidaicin akwatin sai karami dake da kayan turarrukannta ta nufi hanyar fita ba tare da ta kallon Dady ba ballantana Mamy." Sakin baki Mamy ta yi tare da cewa. "Amarya ba sallama?" Ba ta yanka ma ta ba ta fice daga cikin falon. "Ikon Allah, ko irin sallama da iyaye a nemi tafiyarsu ba za ki yi ba kin fice ko, za ki zo gidan za ki ga wulakanci. Kasancewar tana bakin ƙofa ta ji komai ya saka ta ce. "Idan kin ga na zo gidan nan Mamy duk wulaƙancin da kika dama ki yi ma ni." Ta saka kai ta fice Mamy ta saki baki yayin da Dady ya sunkuyar da kai ya kasa kallon Ma'eesaha. "Ungo Laila ga kudin sadakinta nan dubu uku ki ɗauka ki kai ma ta hakkinta ne." Da sauri Laila ta ɗauki kudin ta fice tana dariyar mugunta. A harabar gidan ta gan su Yana gaba da babban trolly tana bin sa da kananan a baya. Daidai lokacin motar Jamil babban yaron Mamy Yayan Laila ya danno hancin motarsa cikin gidan. Ko parking ɗin kirki bai yi ba sakamakon ganin Ma'eesha na kuka, ga makaho na gaba da wata babban trolly wanda ya fi na hannun Ma'eesha girma, ga Laila na miƙa wa Ma'eesha kuɗi. "Subhanah Ma'eesha me ya same ki kuma ina zuwa da kaya?" Ba ta tanka ma sa ba ta yi gaba. kallon ƙanwarsa ya yi yana cewa. "Munafuka me kuka yi ma ta kuma yanzu?" "Aure Mamy ta saka aka yi ma ta da wancan makahon, shi ne ya zo ɗaukarta za su wuce, ga kudin sadakinta dubu uku ta ki amsa." "What?" Ya yi tambayar a firgice. Yana ƙarewa makaho kallo ganin yadin jikinsa ba ta wuce dubu ɗaya ba, kuka daga gani kayan ma sun ji jiki, ko takaman ƙafarsa ma na soso ne sai wata hular taɓa ni ka ji hadisi da ya saka. "Aure da wannan nakasashen?" Girgiza kai ya yi tare da cewa "Da sake!." Ya bi bayansu a guje yana kiran sunan Ma'eesha, har ya karasa inda suke tafiya ba ta kalle shi ba. Haka ya dinga bin su yana rokon Ma'eesha amma ba ta saurare shi ba, haka ya hakura ya bar ta ya dawo. Kamar zai tashi sama haka yake tafiya har ya isa gidan. Don yau ya kara jinjina makirci da rashin imani irin na mahaifiyarsa. *KADUNA* Da sanyin asuba ta fito daga cikin bathroom dake cikin ɗakinsu. Harara ta watsawa ƙanwarta dake zaune saman sallaya tana karatun Alkur'ani mai girma. Cije laɓɓanta ta yi cike da takaici ta yi tsuki. Bayan ta kai karshen surar da take karantawa ta kalli yayat tata ta ce. "Aunty Sidra lafiya kuwa?" Harara ta watsa ma ta tare da cewa. "Ban sani ba." "Allah ya huci zuciyarki." Ta faɗa tana mai ci gaba da karatunta, don in da sabo ta saba da halin yayar tata. Komawa toilet ta yi sakamakon jin wayar dake hannunta tana vibration Ɗagawa ta ji bayan ta rufe kofar toilet ɗin, sannan ta amsa kiran daga cikin wayar ta ji an ce. "Haba Sidra ki yi ki fito ma na kin ce na zo na ɗauke ki karfe biyar da rabi ga shi ba ki fito ba, ko na wuce za ki zo da motarki ce?" Cikin yin ƙasa da murya ta ce. "Ba haka ba ne Sadiya kin san ƙanwata Nasara tana zaune idan ta ga na fito da trolly za ta gane zan tafi wani waje ne, kin san kuma za ta iya sauro ta faɗa a gidan namu idan aka kama ni fa? Yanzu ki bani mintuna kaɗan zan tura ta wani wajen idan ta fita zan fito ba tare da motata ba don asirina zai iya tonuwa." Tana fadar haka ba ta jira jin me ƙawar za ta ce ma ta ba ta katse kiran wayar . Fitowa ta yi tana kallon Nadra dake karatun Alkur'ani ta kira sunanta. "Ke Nadra!" Nadra ba ta dakata da karatun Alkur'anin ba sai da ta kai aya ta ce. "Na'am Aunty Sidra." "Ki tashi ku je garden ki duba mani zobe na ya faɗi ina ganin lokacin da muke fira da Fahad jiya daddare." Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Aunty Sidra why not ki bari sai da safe, yanzu akwai sauran duhu gari bai gama wayewa ba, idan gari ya waye sai na fita na duba ma ki. Za'a fi gani ma idan ba duhu ai, amma yanzu ba lallai a gan..." Idan ba za ki je ba ne ki fada ma ni, ai ga wayarki nan ki kunna torchlight ku je ki duba ma ni." Ba tare da ta sake yin magana ba ta miƙe tsaye tana cewa. "Bari na je na duba ma ki." Fita ta yi daga ɗakin ba tare da ta cire dogon Hijabin dake jikinta ba, wmhannunta rike da wayarta tana cewa. "Allah ya huci zuciyar Amarya a gidan Yaa Fahad, ai bai kamata a ce yau za'a ɗaura ma ki aure kina faɗa ba." "Ke dai kika sani munafuka." Sai da ta tabbatar ta nufi Garden ɗin sannan ta janyo trolly ɗin ta daga cikin wardrobe, kasancewar dogon Hijabi har ƙasa ta saka ba's ganin ko me take ɗauke da shi. A hankali ta bude ƙofar ɗakin bayan ta rataya handbag ta saka wayarta ciki. Akwai mutane a falon wasu na kwance wasu na zaune, kasancewar bikin auren Sidra ake yi ƴan uwa da abokan arziki na nesa duk sun zo garin, ɗakin ɓakin ya yi ma su kadan wasu suka kwana a falon. Cikin sanɗa take tafiya wata ma ta dake zaune ta ce. "Ke wace ce nan ke sanɗa?" Sai da gaban Nadra ya faɗi sannan ta juyo ta ce. "Ina kwanaku?" "Oh Amaryar ce ashe, lafiya lau ya kike?" Suka hada baki wajen amsa gaisuwar, wata dattijuwa ta ce ni fa ba na banbance wace ce Sidra wace ce Nadra." Wata buduwar ta ce . "Wacce ta fara fitowa ta karasa ta durƙusa ta gaishe ku ita ce Nadra, wannan ta yanzu kuma ita ce Sidra wacce za'a ɗaura wa auren yau, ai suna da banbanci ita Amaryar Sidra ai fara ce, ita kuma Nadra baƙa ce." Ita dai ba ta bi ta kansu ba ta wucewarta waje. Sai wata buduwar ta ce "Ai wannan Amaryar ba ta da kirki wallahi, jiya da Nadra ta ce mu zo mu kwana a ɗakinsu tun da su biyu ne amma fir wanan Amaryar ta ce wai ga falo nan ai, Sidra ba ta da kirki." Suna ta firarsu har Nadra ta dawo ta yi ma su sannu ta shiga ɗaki. Sai dai ba ta ga Sidra ba a tunaninta tana toilet ne don haka ta koma ta zauna a saman sallayarta tana cewa. "Aunty Sidra ban ga komai ba wallahi." Ta cigaba da karatunta don hadda take yi ba da Alkur'ani take karatun ba. _Sidra_ Tana zuwa harabar gidan ba kowa maigadi dawowarsa daga masallaci kenan ya ga tana kokarin fita ya ce. "Amarya lafiya kuwa." Kamar ba za ta yi magana ba ta ce. "Zan ba kawata saƙo ne tana waje." "A dawo lafiya." Ya fada yana zama kan kujerarsa hannunsa rike da carbi. Tana ƙarasawa ta buɗe bayan motar ta saka jakar kayanta sannan ta zagaya ta zaune wajen me zaman banza. Ba tare da ɓata lokaci ba Sadiya ta yi wa motarta key suka bar layin. "Na daɗe ina jiran ki fa." "Wallahi Nadra ce nake ta so na ɗauke hankalinta kar ta ga fita ta da akwatin kaya ta tona ma ni asiri shirina ya lalace." Shiru Sady baby ta yi tana rage gudun motar tana rage gudun motar bayan sun bar layin. Kiran waya ne ya shigo wayar Sidra, ta ɗaga tana cewa. "Hellow Khadijah ya aka yi ne?" "Kina ina ne?" "Ya kike tambaya ta kamar ba ki san komai ba, amma ai na fada ma ki komai kasancewar ki ƙawata." "Sidra abun da kike ƙoƙarin aikatawa kuskure ne, za ki wulaƙanta iyayenki ne, bayan kin san sun tara jama'a ana shagalin biki yau za'a ɗaura auren ki a ce kin gudu ya kike so su yi da jama'ar da suka tara? Sannan ga shi Fahad ɗin da iyayesa su ma sun tara na su jama'ar sai su ji labarin matar da Ɗan su zai aura ta gudu zai ji shi Fahad ɗin." "Ke ba gudawa fa zan yi ba, da zaran na samu abinda na je nema zan dawo ne sai a sake saka ma na ranar ɗaurin auren zuwa gaba, don na san Fahad na masifar so na dole ya jira sai na dawo, iyayena kuma za su hakura ne kawai ba yadda za su yi da ni bayan na dawo, kin ga idan na ba su haƙuri ai za su karbe ni ko da sun yi fushi kuwa. kuma ba wani daɗewa zan yi ba me yiwuwa nan da watanni uku na dawo." Tana fadar haka ta katse wayar tare da kashe wayar gabɗaya. "Khadijah ƙawata ce tun da na fada ma ta plan ɗina ta saka ni gaba wai kar na aikata." "Da ma me zai kai ki faɗa wa wata idan b ke ba." Daga nan ba wanda ya sake magana a cikinsu. _Nadra_ Tana idar da karatun Alqur'ani

Chapter 1 of 49