gaba daya gurin turawa ne babu wanda yakejin cin mutuncin da ake mata,,
Kafa handle din Kofar tayi zata bude taji arufe matsawa tayi ta Kawan kwasa gefen dayake,,
Saida yai kusan two mins kafin ya sauke glass din ya kafe ta da idanun sa masu matukar rikita yan mata,,
Da sauri ta sauke kanta kasa kirjinta ya shiga bugawa da cikin sauri haka ta daure cikin daburcewa tace em eh dama naga Kofar bayan a rufe ne,,
Jin shirun yayi yawa yasata dagowa taga mai yakeyi ido hudu sukai domin kuwa kallon ta kawai yake,girgiza kai yayi a zuciyar sa yace da sauran aiki a gaba na,
nuni yai mata da hannun shi alamun ta zaga gefen shi ta zauna,,
juyawa tai cikin zumburo baki tana guguni ita tagaji da wannan wulakanci nasu sai kace ita tace tana son zama dasu,, yana kallon ta, ta glass harta zagayo ta bude gaba sai da ta kauda fuska gefe kafin ta zauna cikin fushi,,
murmushi yayi wanda iyakarsa lebensa ya ja mota suka huce domin siyayyar ,,
inda sukaje da safina nan ya kaita domin nan dinne zaka iya samun kayan mutunci na musulmai,parking yayi ya bude itama ta bude suka fita baiyi mata magana ba sai nuni dayayi mata da hannu alamun muje ko,,
jerawa sukai tamkar mata da miji sai dai kowa fuskar sa babu fara'a yayinda duk inda suka bi kallon su akeyi tamkar larabawa cikin shigar su ta jallabiya,,
koda suka shiga ciki zaman yayi yace kije ki zabi abunda kike so,,,
zaro idanun tai waje tace ya Khalil ni kadai zani tai tambayar kamar zatayi kuka cike da shagwaba,,
Ido ya kura mata tayi matukar burgeshi a sanyaye yace why not ko ni nasan kayan mata ne eyeeh?
girgiza kai tayi ta waiga gabas da yamma taga wurin gaba daya turawa ne Inka dauke ita sai hada hadar su sukeyi Kamar suna gida hadiyar yawu tayi ta share zufar data Ke tsatsafo mata,,
kara matsowa kusa dashi tayi Kamar zatayi kuka tace muje gida kawai ya Khalil wlh bazan iya ba tsoro nakeji,,
dariya yayi sosai yadda takeyi Kamar wacce tayi sata sai zaro ido take jiki na rawa,,
tsayawa kawai tayi tana kallon shi cike da so da burgewa dama tana dariya haka bata taba gani ba sai yau amma ba karamin kyau yayi ba Kamar ya cigaba dayi,,
jitayi an rike mata hannu da sauri ta waigo ya Khalil ne lumshe mata idanu yai yace muje ko,tsikar jikinta gaba daya ya tashi wani irin abu takeji a dukkan sasan jikinta,,
Yana rike da hannunta kayan sawa sunkai set talatin ya diba ,cosmetic kala daban daban inner dinta wanda har saida taji kunya turaruka takalma da yan kunnaye ,kai kaya ne kala kala Kamar wanda zai hada lefe haka ya biya kudin ta ATM suka fito saanan ya saki hannun ta suka shiga ya tada mota,,
*Kano*
inna ce take ta rangada sallama a Kofar dakin hajiya ladi yayinda ita kuma take can kwance tana bacci,,
wata yarinya ce ta fito sanye da wando da riga karam sun dame mata jiki karamar yarinya ce don baza ta fi sha shida ba amma kana ganin ta kasan ta goge a bariki,,Sannun Ku tace ,,
jinjina kai inna tayi tace Yawwa sannu don Allah hajiyar bata nan ne?,,
yarinya tace tana ciki sai dai bacci takeyi amma bari in mata magana,wucewa tai ta shiga cikin dakin hajiya ladi,,
Bayan minti biyu sai gata sun fito tare tana muttsuke ido sannu inna kune tafe hajiya ladi tace tana kare ma harira kallo wancen ko kallon inda take batayi ba,,
inna tace wlh nice ai cha nayi bari muzo tun yanzu kisan da daowar tawa,,
toh bismillah inna Ku shigo,,shiga ciki sukai yayinda hajiya ladi ta ja budurwan nan waje tace Ke hafsi abunda nake so dake shine kisan yadda zaayi ki dauki yarinyar nan photo saboda a tura wa alhaji kinji ni ko,,
gyada kai tayi tace kada ki damu hajiya yanzu kuwa,kitchen ta wuce ita kuma hajiya ladi ta koma dakin suka kara gaisawa da inna wacce kita faman washe baki,,
Hafsi ce ta shigo hannun ta dauke da tray wanda aka dora lemuka na gwangawan da ruwan gora sai cup ta ajiye ta gaida inna sannan ta kalli harira tace don Allah zoki taimaka min mu dauko kuloli abinci,,
Mikewa harira tayi suka fita domin ita shigar hafsi ta burge ta sosai tana fatan ina ma itace haka aida taji dadi,,
ko da suka fita hafsi saida tasan yadda tayi ta dauke ta photo sannan suka dauko kulolin abincin suka kawo suka sake fita suka ba su inna waje ,,
nan suka tattaunawa akan aikin,,Hajia ladi tace Insha Allah cikin satin nan zan nemeki domin har na Samar mata aikin tun zuwanki ,sai dai kawai shirye shirye tafiya,,
washe baki inna tayi tace toh babu damuwa Allah yayi all barka ,nan ta zuna ta kwashe abinci kafin ta miki don tafiya ,,
a tsakar gida inna taga harira wacce har tazama yar gida,,har Kofar gida hajiya ladi ta rakasu ta basu dubu biyar suyi na mota nan inna ta shiga washe baki tace an gode sosai Allah shiyi albarka waini kuwa kinga har zan tafi ban tambayi mero ba,,,
Sai da gabanta yayanke ya buga nan ta daburce tace wlh kuwa em maryam ai tanan nan,ai tana nan lafiya dazu muka gama waya da uwar dakin nata har muka gaisa da ita,,,
inna tace toh Alhamdulillah haka ake so mu mun tafi sai kinzo,,,
Toh Ku gaida gida ta rufo Kofar gidan da sauri ta koma ta amshi wayar hafsi ta duba photos din tana jinjina kai gaskiya ba laifi wannan ma zan wanki alhaji daki ta shiga da sauri ta turawa alhaji photos din kafin ta kira,,
Tunda suka kama hanya harira Ke santin haduwar hafsi,tace gaskiya inna ki bani ko dubu daya ne nima ta rakani insiya kayan kwalliya irin na yan birni,,,
Da sauri inna tayi mata dakuwa tace kul kar na kara ji ina abun burgewa anan zaki waye dai amma ba irin nata ba ki samo min saurayi dan birni mai maiko wanda vake ba harni saina zama abun kwatance ,,
dariya tayi tace haka ne inna toh wai ina meron taje ne?
itama dariya innar tayi tace yaushe zan sani ance dai birni tarayya take,,kema in Allah ya yadda chan zaki samu domin akwai kudi garin nan sosai,,
cikin zakwadi tace da gaske inna aikuwa nima chan zani so nake nafi maryam haduwa,,
inna tace ki kwantar da hankalin ki aiko yanzu ma kin fita kyan gani kuma kinga ita kudin aikin ta na hannu na sai yadda nayi dashi yanda taje haka zata dawo Ke kuwa kudin naki ai gyara zaki sha yadda zamu samu gidan mai galmi mu huta muma,,dariya sukai dukkansu har,,
Alhaji yayi farin cikin ganin photos din yarinya ce karama bai taba mu amana da yarinya karama ba haka yace hajiya kada ki damu kina da tukwaici mai tsoka amma ya labarin maryam ne don ni har yanzu tana raina indai ban kasar da kwadayin na akan ta ba bazan samu natsuwa,,
Murmushi hajiya ladi tayi cike da duniyanci tace ai alhaji yadda ka samu tsuntsu daga sama gashasse haka za'a kawo maka maryam har gida duk da dai har yanzu babu wani labari game da ita,,
alhaji yace shikenan babu damuwa sai munyi waya zaki ga sako yanzu,,
amsawa tai da toh alhaji sai anjima ta aje wayar tana murmushi jin dadi dana mugun ta,,,
*us*
Wani wurin shakatawa ya kaita dake hade da mall din ya hadu sosai yasha ado ta koina walwale Ke haskawa , burger da vanilla shake ya siya musu suka samu kujerun suka zauna ya mika mata nata shima ya soma ci hankali kwace,,
ita kuwa shake din kawai ta dauka ta fara sha domin tasan bazata iya cin wannan abun ba sam ,,
sai da ya gama sanan ya dago ya kalleta da sauri ta kauda idon ta gefe ciki da kunyar kamata dayayi tana kare mai kallo,,
Muryar kasa yace mai kike buri a rayuwa yanzu wanda da zaki samu yanzu ya tabbatar,,
batareda wani tunani ba tace ummi na ita kadai nake burin sake gani bansan a wane hali take ba nan danan hawaye ta taru a idon ta,,
ita dai komai kuka takeyi mai ne,kura mata ido yayi yace hey my mad girl dago Ke kalle ni,,
dagowa tai ta kalle shi wani irin shock suka ji gaba dayan su da sauri ta janye idanunta bazata iya cigaba da kallon shiba idanunsa sunyi mata kwarjini da yawa,,
Murmushi kawai yayi ya miki ya e let's go,,
itama mikewa tayi suka wuce gurin mota suka wuce,
yana gama parking ta fito cikin sauri harda hadawa da dan gudun ta sai yanzu ta tuna da safina mai yasa take mantawa da kowa da komai na duniya matukar tana tareda Khalil bayan tasan yafi karfin ta palon babu kuwa don haka dakin mommyn ta wuce kawai samun ta tayi tana gyara kayan drower dinta don bata yadda kowa ya shirya mata saboda ajiyoyin datake yi a ciki duk da tasha gwada bawa yan aiki da farko amma saita ga an daukar mata wani abu, shiyasa takeyi da kanta,,
sallama tayi tashiga tana ma mommyn sannu da gida,,
murmushi mommyn tayi tace Yawwa sannu kun dawo
eh momy kawo in tayaki aikin,da sauri ta miki ta karba ta cigaba da shirya kayan,,
kayan da suka siyo aka shigo dasu Niki Niki aka dire nan mommyn ta shiga duba wa tana yabawa tace haba ko kefa yanzu naga kaya, sunyi miki kyau ko Ke kika zaba abinda kike so ko,,.
da sauri maryam tace eh hajiya sunyi Allah yasaka da alhairi Allah ya kara budi,,
Muryar Khalil suka ji daga bayan su yana cewa mommyn duka siyayyan nan ni nayi ta itada ta fara kuka wai tsoro,karasowa yai ya zauna kusa da mommyn yace na gaji mom kiyi mun tausa pls,,
dariya tayi tace haka ka iya son jiki matar ka tana da aiki ai sai mai hakuri da juriya inba haka ba toh nifa tawa bata kare ba,,
dariya sukai har maryam kafin tace momy bari inje inyi sallah ta fice,
tan fitowa daga toilets ta tadda kayan a tsakar daki saida tai sallah kafin ta fara duba kayan tana jerawa Allah sarki rayuwa yau nice da gata haka yanzu wadan nankayan duka nawa ne Allah sarki ummi na tana chan tareda inna batada mai kwantar mata da hankali babu kowa nata dazata kallah taji dadi tayi kuka sosai a ranar,
kwana ki nata wucewa yayinda soyayya mai karfi take kara shiga tsakanin Khalil da maryam duk da bai furta mata ba amma kullum da salon sakon dayake aika mata in sun hadu har safina ta kammala exams dinta wanda gobe ake saka ran dawowar ta ,,
Yayinda a *Kano* hajiya ladi taita turawa inna abun duniyar sananb tasa hafsi ta kulla kawance da harira tana chusa mata munanan halaye wanda saboda kwadayin abin duniyar ta ha ta kosa ta tafi aikin,
A *Kaduna* kuwa su dad ne da mom suketa shirin tafiya yayinda ya dau waya ya kira habib yana son ganin shi,
baa wani dauki lokaci ba sai gashi cikin shigar kakin sa na sojojin,,
gaida su yayi cikin girmama wa,
suka amsa saannan dad yace Habib dama safina ta kammala karatun ta ne zasuyi graduations shiyasa zamu tafi amma fa harda kai a matsayin ka na dan uwan ta na gama komai Jibi zamu wuce sai ka cigaba da shiri zan turo maka kudi inda abunda kake bukata saika siya ,,
duk da baiyi murna dajin dalilin kiran nasa ba amma ba yadda zaiyi dole ya washe fuska da faraa ya shiga godiya da Allah ya sanya alhairi a karatun safina ,,
dad yana amsawa da ameen yayinda mommyn keta cika tana batsewa wannan yaron mai yake son zamane ko kuwa asiri shida uwar shi suka fara wa dad dinne lallai aikuwa da sake dole saita tashi tsaye kafin yai musu muguwar illar,,,
*share*
*comments*
*mrs noour ce*βπ»π
[7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *π΄π΄KARFIN IKOπ΄π΄*
π±π±π±π±π±
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
*HIKMAAH writers association*
Edited byππ» *oum Zahara*π
Dedicated 2my lil sisππ» *Maman Sultan*π
Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*Addu'oe Ku da sakwanni Ku suna isowa gareni, ina matukar jin dadin samun hakan daga gareku,Allah ya bar kauna ya kuma biya mana bukatun mu na alhairi gaba daya*
*~Ameeeeen~*π€²π»
*_I really heart u all_*ππππ
π
Ώβ2β£0β£
Yana fita mom ta juyo ga dad cikin bacin rai tace wai mekake nufi ne da abunda kayi,eyeeh alhaji meye amfanin zuwan shi bayan kasan wanda zaaje domin ta bazatai murna dahakan ba,,
dad baiyi mamakin jin hakan ba amma shi yasan dalilin sa na yin hakan,amma a zahiri murmushi yayi mata tareda rungume ta jikinsa cikin sigar lallashi yace haba mom din baby meye aibun wanda zai tayaka farin ciki he is one of our family now meye sa zaki chanza lokaci daya daga yin magana,kuma tunda ita batada raayin hakan shima kuma bai taba nuna sha'awar sa ga yin hakan ba,ai inaga babu abun fushi da tada hankali ko,,
Juyo da ita yayi suna fuskantar juna yace don Allah ki cigaba da nuna mai so Kamar da,bakisan wane irin alhairi Ke tattare da shi a nan gama pls ki daure zuciyar ki,,
Gyada kai kawai tayi domin tasan komai zata fada dad bayadda zaiyi ba duba ga yadda yake kaunar sa feye da safinan kanta watarana sai dai kawai don yarsa ce,,
ajiyar zuciya tayi tace shikenan komai ya wuce amma pls kada ka yi masa wannan maganar ko da wasa domin bana so nafi so yakasance tana da dan uwan da zai rinka bata shawara ko bayan ba ranmu,,
Jinjina kai yayi wannan kam gaskiya ne kinyi tunani mai kyau ,Allah ya zaba mana abunda yafi alkhairi,,
ta amsa da ameen,,
Jiki a sanyaye Habib yai musu sallama ya tafi zuwa ga makwan cinsa wanda Ke cikin air force daki ne guda biyu da bayi ta waje kan katifar sa ya kwanta cike da tunanin mai yasa kowa ya damu da hadasu da safina bayan halin su kowanne ya banbanta dana juna,,ni kam ina adduar kada Allah ya tabbatar da faruwar hakan gareni,
yarinyar da kowa ta raina mishi bare shi da kullum maganar daya ce dad dinta ne ya taimaka mishi ya ceto shi daga talauchi da yanzu yana can yana fama da fatanya duk sanda ta gayamai maganar nan kwana yake cikin bacin rai amma shine su dad zasuna kokarin hadamu zaman aure ina bazai yuwuba,,
haka ya raba dare yana juyi da tunani tabbas tun farkon zuwansa gidan dad yake kaunar safina da sonta tun yana ganin zata sauya watarana inta mallaki hankalin kanta har ya daina saka ran hakan domin kuwa abun nata kullum gaba yake yi,,
yau daace zata sauya to kuwa tabbas da kansa zaiyi fighting da kowaye gurin neman auren ta amma agaskiya a yadda take baya jin zai iya auranta,,
ganin tunanin bazai fisshe shiba yasa shi tashi ya fito yai alwalar ,ya fara jero nafil fili har aka kira sallah yayi snaann ya mike ya saka kayan training dinsa ya fice,,
*Kano*
tun safe su inna keta shiri yau harira zata tafi Abuja aikatau,,
basu sanar da ummin ba itama kuma bata tanka musu ba don kuwa tun lokacin data yi mata maganar ya labarin maryam ya kamata ko a wayane aji yadda take ko tana lafiya,,
kafin takai karshen maganar inna ta rinka zuba ruwan jaraba kwana tayi tana habaici da zagin ummi tin daga lokacin kota gaida ta bata amsawa haka ba harira kallon arziki bai hada ta da ummin balle gaisuwa musamman yanzu da kanta ya fara wayewar take rawar kai,,
inna ce ta leko dakin tareda harira wacce tasha dankareren leshi yayi mata kyau sosai tasha kwalliya suka gaisa da inna,,
inna tayi gyaran muryar tana dariya tace toh matar baba mugun nufin da kika dauka a zuciyar ki game da ni saiki sauke shi gadai harira nan itama zata tafi sai ki gane banida niyyar cutarki ,,
taimako ne ake kokarin yi miki tunda tsiya da rashin arziki a jinin ki suke ai gwara su sufita su nemo na Kansu koda na katifa ne,,
don haka ga harira nan zata tafi inkin so saiki sami hajiya ta dawo miki da yarki amma kisani duk wani arziki da zaki gani sai dai kallo wlh eyeeh na gaya miki tun wuri ,,,
Suka fice zuwa gidan hajiya ladi,,
ummi najin fitar su itama tazari hijabin ta tabi bayansu domin ita batasan gidan hajiya ladi ba amma yau tana fatan Allah ya amshi adduar ta don kuwa tasha bin bayan inna don taga gidan amma kullum sai an samu matsala ko go slow ko tara motar hawa ko kuwa subi bayan wata motar daban,,,
tayi saa kuwa tana zuwa bakin titi suna hawa keke napep cikin ikon Allah itama ta samu tace yabi bayan motar chan akayi saa kuwa matashi ne ya rinka zuba gudu yana bin bayan motar su inna har Kofar gidan hajiya ladi inna suka saika suka shiga,,
itama fitowa tayi ta sallami mai adaidaita ta bi bayan su kusa da gidan wasu matasa ne su biyu Zaune suna hira kai tsaye ta tunkare su tayi musu sannu suka amsa da Yawwa ,,
tace don Allah gidan hajiya ladi nake neman ,,
daya yace ai ga gidan nan yai mata nuni da hannu gidan da su inna suka shiga ,,
jinjina kai tayi duk da tana shakkakr tambayar su gudun zargi amma haka ta daure tace naji ance yara take kaiwa aikatau ko tayi musu tambayar Kamar bata sani ba,,
dayan ne zai charaf yace wah hajiya ladi ai karuwanci kawai take kai yara kowa yasani a unguwar nan sau nawa anan ansha kawo yan sanda da raba dambe don dai tana da saurin gindi be kawai gurin manya,,
tunda ya fara maganar taji zuciyarta ta buga nan da nan kanta ya fara wani irin sarawa jiri taji yana diban ta da sauri ta dafe Katanga gurin tana sallati da karanta addu'oe,,
aikuwa kafin ta dawo daidai saiga wata falleliyar motar ta paker a Kofar gidan,,
dayan yace kingani da alama yarinya da suka jiga yanzu anzo daukar tane ai gaskiya hajiya ladi shedaniyar mace ce muna rokon Allah ya kawo mana karshenta ,,
dayan ya amsa da ameen,
godiya ummi tayi musu ta hau keken ta kama don komawa gida tasan tabbas inta tsaya tofa zata iya suma anan gurin,,
da kyar tayi iya Jan jiki ta shiga gida anan tsakar dakin ta zube tana maida numfashi da kayar koda batasan hawan jini ba amma tabbas tasan yau jinin ta yahau Allah sarki maraice Allah Kaine gatanmu narasa iyayen na tunda suka kawo ni babu labarin su wanda yazama mana gata shima Allah ka amshi abinka daga hannu sama tayi tana kuka tace ya Allah aduk inda yata take Allah ka kamata daukin ka kada ka bari wani abin cutarwa y cuceta,,
nayi kuskuri Allah ka gafarta min ka yafe min kada in samu sakamakon danake tunani,,
tabbas ni nakasance mai laifi babba gareki na bin umarnin wanin ka ya Allah ka yafe min ka cigaba da tsirar da maryam a duk inda take,,
zazzabi ne mai zafi ya rufeta nan ta shiga rawar sanyi da kyar ta iya Jan jiki ta koma kan dan gadon nasu ta rufe,,
cikin murna hajiya ladi ta tarbo su inna suka kaisa nan inna ta damke amanar ji karta wurin hajiya ladi ita kuma tace ta amsa ha hannu biyu Allah yataya su roko amma inna ki kwantar da hankalin ki gidan dazata zauna babu wani damuwa ko matsala Ke da kanki duk randa ta dawo bazaki gane ta ba,,
kudi ta dauko masu yawa ta damka ma inna tace gashi na wannan watan sun aiko dashi saiki fara amfani dashi,,
cikin hanzari tasa hannu biyu ta amsa tana washe baki tace toh madalla an gode tun yanzu juyawa tai ga harira tace toh kingani ko abunda nake gaya miki saiki dage kowanne irin abu aka sakaki kiyi shi bana son musu harira kinji ko,,
toh inna tace kada ki damu domin itama tana kwadayin wannan kudi Allah yasa ita za'a rinka bawa kudin ba inna ba tayi yadda taga dama,,
wai ni kuwa ya maganar mero ne naga watan har ya wuce shiru ne,,inna ta tambayi hajiya ladi,
Kyabe baki tayi domin ta riga ta shirya abunda zata gayawa inna gyara zama tayi ta matso kwallar tace ai inna maganar danake so inyi miki kenan ai lallai abunda kike fada gameda halin uwarta to bata yarba don kuwa iskanci iri iri take yi musu ga rashin son aiki har ta kai ga ta zagi babban dan masu gida yai mata duka shine fa ta hada kayan ta ta gudu don dama sunce yawan bin maza kawai takeyi agarin,,
Sallati inna ta saki da karfi tana sallalami lallai matar baba anyi mai kashin tsiya burin ta ya cika hankalinta ya kwanta ai duniyar ce indai yawona bariki be duk inda take zata dawo in duniyar tai mata juyin waina,,
ajiyar zuciya hajiya ladi tayi don ganin tasamu nasara cikin sauki nanta shiga kwantar ma da inna hankali duk inda take za'a ganta zata dawo da kanta,,
da sauri inna tace wa aitayi zaman ta nifa dama damuwa ta kudin watan bawai batan nata ba yanzu inta dawo mai zatayi mana ai tai zaman ta a chan kawai,,
mikewa tayi ta kulle kudin a gefen zaninta tayi musu sallama ta tafi cike da murnar harira itama tayi dacen gidan aiki(sai ince inna abi duniyar nan a sannu ),,
*US*
Aiki suketa yi sosai maryam da mommyn a kitchen din duk da akwai masu dafa abincin dayawa amma mommyn ta fison ta tsaya su shirya abincin harda ita ga baki dake shirin zuwa gobe suna ta hidima yi musu snack kala kala,,
saida suka gama aikin tsaf sannan mommyn tace maryam taje tayi wanka,
dakinta ta wuce ta fada toilet tayi wanka da sbulanta da shower gels masu kamshi gashin kanta ta wanke shi shima shampoos masu gyara gashi saida ta sulle kanta tsab saanan ta fito daure da tuwel ta yafa daya a kanta gaban sallar magrib ta farayi kafin ta zauna gaban mudubi so take tayi kwalliyar dazaki burge Khalil don yace mata zasu fita ganin gari kusan sati daya kenan kullum saiya kaita gurare daban daban yawan bude ido wata rana in suka fita tun safe sai dare musamman in mommyn bata nan,,
kwalliya tayi sosai duk da bawani iyawa tayi ba amma tayi kayu sosai mikewa tayi ta nufi draws skirt da riga ta dauko arebain rigar mai karamin hannun ce brown color da fari skirt dinma haka ya bude tun daga sama har kasa sai top light brown mai dogon hannu ta saka da takalmi high heels fari ta dauki gyalen ta nufi mudubi,,
masha Allah ta furta tana murmushi ita kanta tasan ta hadu babu ta inda Allah ya rageta a kyau da lafiya duk wanda yasanta a Kano to ba zai taba iya gane taba yadda tai bala'in fari fatarta ta murje hatta da nonuwa ta suke kananan yanzu sunyi dan cika sosai ga uban hips kullum Kamar kara budata akeyi kullum gyalen ta rolling kanta dashi ta feshe jikinta da turare saanan ta fita kai tsaye dakin mommyn ta shiga wanda yanzu ta riga da ta saba kai tsaye take komai agidan waya ta tarar da ita tanayi guri ta neman kan kujerar dake gefe ta kwanta ta tada kanta da pillow din kujerar,,
da alama da yan uwanta take yin wayar jin tana ta gaisawa da mutane yara da manya nan itama kewar ummi ta dameta Allah sarki ummi na Allah kasa tana lafiya hawayenta ta share dayake shirin zubo mata ,,
Mommyn ganin haka tayi sallama ta katse wayar cikin sauri ta taso Gurinta cikin muryar lallashi tace haba maryam meye abun kuka kinyi kyau zaki bata kwalliyar ki pls share hawayen nan bana son nakara ganin su,,
share wa tayi suka mike tare zuwa palon Khalil da daddyn suna dining Zaune sa suka karaso suka zauna ,,
tunda suka fito Khalil ya kafe ta da ido wow masha Allah ya furta a zuciyar shi suna hada ido ya kashe mata ido yana mata signa alamun tayi kyau meye sirri,,
dukar da kai tayi har suka gama cin abincin idon shi nakanta ita kuwa taki yarda su hada ido yayinda mommyn Ke lura dasu banda daddyn dabesan mai akeyi ba abincin sa kawai yake
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 32