Share this page
illah yakeyi fa lafiyar zuciyar ba ,,, godiya su daddy sukayi mai suka fita su mommyn suka hau tata motar yayainda daddyn da dad da Khalil suka shiga ta daddyn suka nufi gida,, a falo suka zauna gaba dayan su yayinda Khalil Ke kwance kusa da mommyn yayi matashi da cinyar ta,, kara gaisawa sukayi kafin daddyn yasa akira habib su gaisa,,haka ma su safina wacce ta sanar dasu dawowar ta dukda taso zuwa asibiti dad ya ce ta hakura suna kan hanya,, maryam na cikin aiki yar aikin ta shigo baturiya ce sanye da uniform din yan aiki ta gaida maryam din itama ta amsa don yanzu ra fara gwanan cewa da turanci irin nasu,, sakon dad ta gayawa maryam yayinda maryam ta bata amsa da sun fita tun dazu itada kawar ta,, komawa yar aikin tayi ta sanar da su daddyn wanda yayi daidai da shigowar habib sanye da jallabiya jikinshi don shima bacci ya keyi na gajiyan,, Gefe ya neman ya tsuguna har kasa ya gaida su duka kafin ya karasa gurin Khalil yana mai sannu,,da kyar ya budi baki ya amsa,,fuska ba yabo ba fallasa,, Anan habib ya soma gaya musu yadda akayi ya ceci wata yarinya a airport har zuwan su gidan nan saidai yaga Kamar tasan gidan nan,, zumbur Khalil ya mike daga kwance dayake yana kallon habib a dakile yace kana nufin maryam ne u mean kace kai ka ceceta ,, Shima jinjina kai yayi batareda wani tunanin ba yace yes Ina tunanin hakan coz bansan sunan taba amma tana cikin gidan nan,, ai kafin ya rufe baki tuni Khalil ya mike Kamar wanda aka tsikara ya nufi sama gurin ta dukda zuciyar shi tana cikin zullumin yadda maryam zata dauke shi amma komai zatayi masa tayi ya cancanci tayi hakan shidai burin shi yasameta lafiya,, bata dakinta kai tsaye dakin safina ya nufa tsaye yayi bakin kofa tareda folding din hannuwan sa akan kirjinsa ya jingina kansa jikin kofa yana kallon ta cike da tsantsar so da kauna jin sonta yakeyi yana dad'a bin kowace gaba da jinin jikin shi bazan ita rayuwa babu keba Ke yafa da dan daga murya ,, Chak ta tsaya da abunda takeyi batareda ta jiyo ba sai a lokacin taji tasamu natsuwa don jiyo muryar shi datayi alamun yasamu sauki kenan bata San sadda ta sake lallausan murmushi ba tana kara sadda kanta kasa,, Ganin taki Juyowa yasashi takuwo a hankali zuwa gurinta yayinda duk daga kafarsa bugun zuciyar ta Ke daduwa,, tsugunawa yayi Kamar yadda tayi yana leken fuskarta wacce ta sunne ta kasa cikin jin kunya amsar rigar hannunta yayi tareda kamo hannuwanta duka dogayen kyawawan yatsun ta yake kallo harya tsaya akan yatsan da ya sanya mata zoben yake kallo sonta na dada ratsa shi murza zoben ya shiga yi a hankali yana kara tsareta da idanuwan sa wadanda Ke saukar mata da matsananciyar kasala,, Kara kasa tayi da kanata tana hawaye wanda ta rasa kona meya dukda tasan na tausayawa kanta ne da zuciyar ta tayi karan banin fadawa tarkon kaunar wanda tasan yafi karfinta gashi saboda son datake yimasa takasa nuna masa fushin ta ko kadan ne sabanin haka ma sai tsintar kanta tayi da farin cikin ganin shi lafiya,, ganin haka yasashi sakin hannun ta daya ya tallabo fuskarta suna fuskantar juna da sauri ta runtse idanun ta wadanda basu daina zubar da hawaye ba,, heey my mad girl ya fada cikin rada da Jan hankali ji tayi wani abu ya tsirgar mata gaba daya jikinta numfashin ta ya kara gudu cikin sauri,,pls ki bude idanun ki kada kiyi min rowar ganin su pls zuciyata such kadai take da muradin gani pls ya fada yana dada narkar da muryar Kamar zai hade musu jiki,, a hankali take bude idanunta har ta ware au akan sa kallon juna suka shiga yi kowa na ganin ramar kowa ita tafara janye idanun ta daga nasa don tayi kokari ma ahaka saboda wani irin kwarjini dasuke yi mata aduk lokacin data kalle shi,, Kafa kunnuwan sa yayi tareda langabar da kai gefe cike da nadama yace am Sowry my mad girl pls forgive me,, yamutsa baki tayi tana turo shi gaba itafa ta tsani wannan mad girl din dayake cemata,, sake langabar da kayi yayi yace plss,ki yafe min bazai kara faruwa hakan ba sai da hakan ta faru nasan bazan iya rayuwa babu Ke ba I love u,, da sauri ta dago fuskarta dauke da murmushi jin dadi finally ya furta mata abunda ta dade tana jira ashe shima yana sonta ba ita kadai take haukan taba,,, Plss Ki yafemin ya sake maimaita mata,,gyada kai kawai ta rinka yin din ta kasa magana,, murmushi yayi tareda cewa thank u do u relly love me too,,yayi tambaye yana kara tsare ta da idanu,, kasa tayi da kanta cikin jin kunya batason mai zatace ba amma tasan son datake yi masa yafi wanda yake yi mata,, Keeh taji tsawar da safina ta yimata a razane ta matsa baya tafara daukar kayan tana kokarin sawa a drower dikta daburce ganin haka yasa Khalil mikewa ya amshe kayan dake hannun ta tareda kamo sandar hannun ta ya jata zasu fita daidai gurin safina yace wannan shine karshe ki koyi sallama before ki shigowa mutane daki ya wuce yana jiwo hucinta suka fice ayayinda maryam gaba daya jikin ta rawa yakeyi har parlon kasa ya saukar da ita ganin su mommyn yasa tayi saurin janye hannun ta wanda babu wanda ya lura da hakan sai mom din safina,, kallo daya itama taji ta tsani maryam lallai ashe kyau tafi yarta shine zai zabi wulakanta mata ya bata tsaya amsa gaisuwa maryam dinba ta wuce sama fuu gurin yarta ,, Mommyn kuwa da sauri ta taso ta roko maryam zuwa jikinta tana tambaye lafiyar jikinta,, Tum kafin ta isa take jiyo kukan safina da sauri ta karasa dakin ta rungomet jikinta itama ganin mommyn yasata kara kukan karfin tana cewa mommyn I hate dis hate Khalil yace yana sonta mom kuyi wani abu Zan mutu wlh in har ya aure ta wlh zan kashe ta ko in kashe kaina da sauri mom ta rufe mata baki tana tapping din bayanta alamun tayi shiru amma ina Kamar kara tinzura ta akeyi sai fadar maganganun takeyi Kamar wata taba biya, Lallai ya kamata inyi wani abu a yau dinnan don nagano soyayya yarinyar na a idanun Khalil bazan taba barin hakan ta faru ba ga samu ga rashi ina bazai yiyo ba mom ta fada a zuciyar ta ,,, *urs* *Mrs noour ce*✍🏻😘 [7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… πŸ…Ώβž–2⃣5⃣ Ta dade tana lallashin ta kafin tayi shiru tareda yi mata kulawarin yau zuwa gobe zataji kyakkyawan labarin auren su kinji ko,, gyada kai safina tayi tana murmushi jin dadi tasan iyayenta zasuyi komai akanta don farin cikin ta,, Yawwa my dear maza Ku cigaba da shiru mom ta fada tana mikewa,, harta kusa bakin kofa safina ta dakatar da ita tana fadin mom maiyasa dad yazo da habib ne bayan kinsan bana kaunar ganin sa kwata kwata ko dazu daya ganni ko gaisheni baiyi ba saboda jin kan tsiya bayan shidin ba kowa bane yana cin arzikin na amma ban isa ya gaida ni ba,, Dawowa tayi ta zauna kusa da ita tana fuskantar ta alamun maganar mai muhimmanci ce in serious tone tace lallai kin tunar dani maganar da nake son yi miki,, abunda nake so dake kar ki yadda hakan ya tayar miki da hankali ki nuna bakisan da mutum wai shi habib aka zoba saboda na lura wannan tafiyar da biyu dad dinki ya shirya azo dashi,, zan yi waya da hajiya kareema anjima don naga alamun reshe na neman juyewa da mujiya dole mu dauki mataki cikin gaggawa,, saanan gobe kiyi shiri mai kyau kisan yadda zakiyi ki samu damar shiga zuciyar Khalil inyaso in son su suke saisu hada auren su kowama ya huta,, watt re u saying mom maryam batada darajar dazata auri habib mommyn kinaga daga taimako tanemi rabani da Khalil kiyi tunanin hadasu aure sai su yi mana mugun abu gwara kar kisoma wannan maganar pls mom ta fada cikin bacin rai,, Jinjina kai mommyn tayi tace tabbas Hakane safina kina da tunani don dan Adam sai Allah musamman talakawan nan sai kayi musu inuwa su suyi maka rana,, meena kanwarta dake kwace a gado ta dago da kanta tana kallansu tace mommyn gaskiya ta kamata asan abunyi don maza irin su Khalil wuya suke ga kyau ga ilimi ga kudi ta ko ina maganar gobe kuwa kubar komai ahannu na zamusan yadda za ayi da shi ya fada tarkon wata jahilar daban balle mu,, shikenan mom ta fada ni zan sauka anjima zamuyi maganar ta mike ta fice daga dakin ta koma palon ta tadda su sunata hira gwanin shaawa maryam na gefen mommyn hankalinta kwace,,komai ya kusa zuwa karshe Insha Allah ta fada a zuciyar ta,, Karfe tawas na dare kowa ya hadu a dininga don cin abinci banda habib da maryam wacce Ke dakin safina tana karasa aikin data sakata don har daki suka shiga da kanwarta meena sukai mata cin mutunci son ransu ,, safina na gefen Khalil sai kokarin son hira take dashi yayinda shi kuma hankalinsa nakan step yana duban hanya yaga ta inda maryam zata bullo,, Kowa na cin abinci banda shi har mommyn ta lura cike da kulawa ta dube ishi tace son Yaya ko bakacin abincin ne lafiyar ka kalau kuwa,, Yamutsa fuska yayi yace mommyn banajin dadi ne bari na je daki na kwanta ,, Allah ya sauwwake suka shiga yimasa cikin kulawa ya amsa da kai kawai ya wuce sashen shi,, kai tsaye bedroom dinsa ya shiga ya bude bedside drower ya dauko kwallin waya mai matukar tsada budewa yayi ya dauko sim ya saka ya kunna tareda saka number s dinshi ya maida wayar kwalin ta ya fice ta baya ya zagaya ya haura sama batareda kowa ya lura ba dakinta ya nufa kai tsaye kwace ya hango ta gefen gado da alqur'an a hannun ta irin mai uzu biyun nan tana karantawa,, kashe wutar dakin yayi ya kunna a lokaci daya dago kanta tayi don ganin waye hangoshi tayi tsaye sanye da jallabiya fara khal jikinsa tayi matukar yi masa kyau bata sanda ta sakar mai murmushi ba,, karasowa yayi kusa da ita ya tsuguna tareda kamo hannunta na dama wayar ya daura mata kan hannun ya mike a sanyaye yace kisa a chaji gobe zamuyi magana make sure u look prettier OK ya fada yana tsareta da mayun idanun nan nasa kasa tayi da kanta tana murmushi batareda tace komai ba,, Ficewar yayi daga dakin yana yi mata gud nyt,, dakai ta amsa kawai kallon wayar ta shiga yi budewa tayi tasaka chaji Kamar yadda ya umarce ta,, A dakin mommyn ce da daddyn kwance suna hira Juyowa yayi yace wani kuwa hajiya bai kamata kuwa yarinyar nan ta koma gurin iyayen ta don zaman haka baida amfani kinga abunda ya faru dai don haka dole akiyaye gaba,, Jimm mommyn tayi don tasan hakan dama saiya faru dole cikin kwantar da murya tace amma inga da an barta anan din saboda chan din babu wani tsaro gaskiya ina tausayawa halin dazata shiga in ta koma,, Cikin halin ko in kula yace ai wannan ba abun damuwa bane mun rigada mun shigar da report dinta yan sanda zasuyi komai kanta sunannan suna bincike kuma har Nigeria sun aika da case din saboda haka babu abin damuwa,, Shikenan mommyn ta amsa don tasan komai taza fada daddyn bazai jiba don wani irin baudadden mutum be itada take burin samun maryam a matsayin suruka yanzu meye mafita Haka ta kwana sake sake,, Yayinda mom itama ta tasa dad din safina da maganar auren,, duk yadda yaso ta fahimce shi ki tayi dole hakura yayi yace gobe Insha Allah zasuyi maganar,, Habib na kwace sai juyi yakeyi ya kasa bacci sai faman tunanin maryam yakeyi ya kamata maryam ta koma gida ko don suyi aure, after all daman zaman nan ya ishe shi yana son komawa Nigeria haka ya kwana ya na tunanin ta da mafarkin ta har cikin bacci,, Yana idar da sallar asuba ya jawo wayar sa dake jikin chaji ya shiga kiran maryam wacce yajita akashe Tana idar da sallah bayi ta fada ta tara ruwa maiyawa tareda zuba gels din wanka masu matukar kamshi ta shiga ciki ta dade tana sulle jikinta kafin ta sakar ma kanta shower ta dauro towel ta fito,, Kirjinta ne ya buga da karfi da hanzari ta juya zata koma bayin shima da sauri ya damko hannunta wata irin Juyowa tayi da suri ta yarfo masa kashin ganta a fuskar shi wanda yake jike da ruwa take tsigar jikansu ta tashi gaba daya,, Jikinta ya shiga rawa sosai idanu ya kura mata yana bin ji kinta da kallo kasa tayi da kanta tana gunguni da baki,, hannunsa Ya dago ya dauke mata gashin daya manne mata a fuska yana tsare ta da mayun idanun sa,, janye hannun ta tashiga yi cike da kunya tace pls kasake ni nasaka kaya tafada tana harar shi,, kara matse hannun yayi yana sakar mata murmushi wanda yake haifar mata da mutuwar jiki lokaci daya, wata babbar Leda ya miko mata ciki rad'a yace use dis pls,,ya juya ya fice daga dakin,, da sauri ta dan nawa Kofar key ajiyar zuciya ta sauke tana murmushi ya kamata in rinka sama kofata key su sun saba da zaman turai shiyasa baya jin wani abu in ya ganni ahaka,, Bude ledar tayi wani dankareren leshi ne dark blue mai matukar tsada anyi mishi dinkin riga da skirt mai matukar kyau,, Jinjina kai tayi tana mamakin ina Khalil ya samu kaya haka Kamar a Nigeria ajiyaewa tayi akan gado ta isa gaban mudubi tashi ga shafa kwalliya tayi simple wacce takara haska fuskarta sanan ta Saka kayan sunyi mata das ajikinta Kamar an gwada ta dauri tayi mai kayu ta dauko takalmi guda biyune da hill da flat,,flat din tasaka tareda daukar pos din da gyalen dukan su light blue ne ta fice kasa,, kowa ya shirya suna dining suna yin break fast karasawa tayi cikin natsuwa ta gaida kowa saanan ta jawo kujerar ta zauna ta soma Karya wa,,, Zamanta keda wuya Khalil ya shigo cikin shiga ta manyan kaya wata rantsatsiyar shadda ce jikin shi fara kal dinkin riga da wando na zamani rigar karama ce kayan sunsha aiki sosai ya dora hula akansa hannunsa daure da agogon na white gold sai sheki yakeyi karasawa yayi idonsa hakan maryam wacce ta sunkuyar da kanata bayan ta gama kallon sa,, gaida kowa yayi ya ja kujerar ya zauna yana fuskantar ta ya shiga Karya wa batareda ya kalleta ba har suka gama kowa ya mike suka fita harabar daake ajiye motoci suka shiga matan daban mazan daban don su safina sunyi gaba tun da safe don kayan da zasu sanya yana makarantar,,, *Kano* Kwanan ummi biyu a asibiti bata farfado na sai ana uku ta farka halima ce Ke zama da ita tunda inna tace girma ya kamata bazata iya jinya ba yayinda mijin halima shike ta dawainiyar dana asibiti,, koda ta fara dawowa tunanin ga kuka ta shiga yai sosai tana cewa inna kin cuce ni kin cuce rayuwar yata wannan wace irin kiyayyar ce mai mukayi miki haka eyeeh duk yadda halima tayi kokarin kwantar mata da hankali taki dole likitan yakara yi mata allura bacci don jikin harya fara rikice wa,, Cikin gaggawa alhaji yasa akayi masa visa shida harira wacce tazama yar gari da kanta take kai kanta gurin alhaji tunda ba karamin kudi yake kashe mata ba ,, India suka tafi sanan yasa malami suyi masa rokon Allah akan case din MARYAM ya mutu don kasar waje ba irin Nigeria bace babu sauki,, *Mrs noour ce*✍🏻😘 [7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… *Alhamdulillah alaa kullee haaleen, ina matukar jin dadin addu'oe Ku,comments dinku na karfafa min gwiwa,shawarwarin na kara min natsuwa akoda yaushe, Allah ya bar kauna,(ameeeeen)*😍😍 *Naf zage* ~ina jin dadin adduar ki akoyaushe🀝🏻~ ~Bazan manta daku ba~ *karfin IKO fans*😘 *mrs noour Hausa novels*😘 ~Allah ya bar kauna gashi har da maryam Acikin group dinπŸ˜„~ πŸ…Ώβž–2⃣6⃣ Lokacin da suka isa har anfara taron a babban hall din dake cikin makarantar wanda ya sha ado da flowers da decoration's kala kala gwanin shaawa,, da sauri suka karasa wuri ya cika da manyan mutane yawanci turawa ne sukafi yawa a wurin da fararen fata bakaken fatar kaden me agurin su Kansu kallo daya zakayi musu kasan wa sune masu fada aji a kasa,, Yan graduation suna chan saman stage wanda shima an kawata gurin sosai kowanne su sanye da jajaye da baki suit masu matukar kyau,, har gurin sits dinsu akai musu jagora bayan sun nuna card dinsu,, sits dinsu kowanne da sunan sa jiki saidai babu sit din maryam da habib domin safina bata bada sunan su ba,, ran mommyn ya baci don tasan dama zatayi hakan kuma har magana tayi ma safina akan maryam tunda anzama daya amma shine tai kunnen uwar shegu da ita,, Hakuri ta basu tace habib ya samo musu sit koda ta baya ne saisu zauna,,jiki a salube suka juya da sauri Khalil ya tsaida habib tareda nuna mai sit dinshi yace ya zauna kawai zai nemo musu kawai,,yayi hakan ne kawai don baya son habib ya zauna tareda maryam lura dayayi da irin kallon dayake binta dashi,, Shima kauda kai gefe yayi yace no ka barshi kawai ka zauna don shima so yake su kebe da maryam don ya gayamata abunda Ke damunshi game da sonta amma ya lura Khalil ya tsare gaba da baya,, mommy ce tasanya baki tace habib ya zauna kawai tunda shi bako ne don itama ta lura kishi ne kawai Ke damun Khalil,, baijira zaman shi ba kawai ya kama hannun maryam suka fice daga hall din gaba daya fuskarsa tamke lura dayayi idon mutane gaba daya yana kanta,, Safina dasuke kan stage tana kallo abunda ke faruwa ita da meena wacce itace tabada wannan shawara,, Nan take bakin ciki yacika zuciyar ta, Kamar tayi kuka don takaici,, Har wurin sport din makarantar ya kaita ya zaunar da ita kafin ya saki hannun ta ya juyar da kansa gefe,,fuskarsa babu fara'a ko kadan,, ganin haka yasata yin kasa da kanta tana tunanin maitayi kuma itada safina tanemi wulakanta ta bai bata baki ba sai shine zaiyi..... mai Ke tsakanin ki da waccan,,ya jefo mata tambayar datayi matukar daure mata kai,,kallonsa takeyi cikin mamaki dawa yake nufi,, Juyowa yayi a fusace yace kinsan shi kuma kin gane wa nake nufi saboda ya taimake ki that doesn't mean ya samu dama ko wani matsayin a zuciyar ki,, ko kowa dama chan soyayyar kukeyi ne,, Dagowa tayi da sauri tana girgiza kai a hankali idanunta har sun kawo ruwa kirin take jira ta fara kuka,, ganin haka yasashi matsowa kusa da ita murya a shake yace a rayuwa ta Ke kadai ce macen da nafa kauna cikin zuciyata Ke kadai nake burin bawa soyayyata zuciyata da kulawata, kullum burina bai wuce in aureki na in faranta miki in baki kulawa tamkar kwai,,ajiyar zuciya yayi tareda dago fuskarta wacce har hawaye yafara jikata hannu yasa yana share mata hawayen cikin sanyi yace dukkan wannan burin nawa bazai samu ba saikin bani hadin kai inada matukar kishi sosai saboda haka ki akiyaye kinji koya fada yana tsareta da idanunsa wadanda tamkar wani magadisu ne cikin su wanda yake matukar kara rura wutar kaunarsa a ranta,, kai kawai ta daga alamun toh dauke hannunsa yayi akan fuskarta tareda kamo hannunta yace u look so pretty yana murmushin nan nashi mai tsada domin inka dauke mommyn maryam ce kawai take samun haka,, murmushi itama tayi a sanyaye tace na gode da kayan domin sune masu kyan bani ba,,,da sauri ya daura yatsa a labban shi alamun tayi shiru,, cikin rada yace kedin kin kasance Zara garene komai kika sanya Ke kehaska su har cikin ranta takejin wani irin nishadi da farin ciki sai murmushi kasa kasa takeyi,, Kuma bana son godiya komai nayi miki u re my wife to be ya fada yana lalubo kwayar idanunta tareda aika mata da wani sako wanda ita kadai tasan irinsa kasa tayi da kanta kaunar sa na kara ratsa dukkan wani bargo da jinin jikinta,, murmushi yayu tareda matsawa baya kadan yace wayar dauko in nuna miki yadda zakiyi amfani da ita,, waro idanu waje tayi tareda bude baki yatsan hannunsa yasa ya dalle bakin yana dariya da sauri ta dafe bakin hararar wasa tayi mai tareda kauda kanta gefe,, Kusan awa hudu aka dauka a hall din kafin aka gama safina tasamu gift da yawa tarda number yabo don kuwa akwai kokari ta wannan fannin saidai arabi ne ko ohoo,hotunan aka soma yi safina hankalinta a tashe yake tana tunanin gida Khalil ya koma tareda maryam ne ko kuwa,,matsawa tayi kusa da mom Kamar zatayi kuka tace wai mom ina ya Khalil ne ko ya koma gida ne tareda shegiyar nan,, Da sauri mom tace shiii ta dora yatsan ta a baki alamun safina tayi shiru itama mom din abunda Ke damun ta kenan amma yanzu ba lokacin magana bane,, kafin magana ta tsinkayo muryar mommyn tana waya da Khalil din ta umarce shi dasu shigo donyin pic,, koda suka shigo maryam gefe ta koma tareda dafe kai duk yadda sukayi ta dauki pic din ki tayi tace kanta na ciwo dole mommyn tace a kyaleta dama ta kudurta komai zaace bazatayi na itama tanada mutunci gwara taringa yin nesa da safina,, Aikuwa abunda take so ya samu nan safina aka zake da daukar pics da Khalil kala kala duk da hankalinsa na kan maryam amma haka ya tsaya akayita dauka sai dai fuskar nan tashi a hade take musamman yadda yaga habib ya koma kusa da maryam yana mata magana,,, Sai kusan laasar suka dawo maryam kai tsaye dakinta ta wuce toilet ta fada wanka tayi ta dauro alwalar tana fitowa sallah ta farayi kafin ta yi shafa jallabiya fara khal ta saka wacce take hade da hula ta sanya tayi matukar yi mata kyau irin mai shape din nan ce ta bi jikinta tayi mata dass wayar ta dauka ta fice cikin sauri da niyyar zuwa gurin Khalil Kamar yadda ya umarceta,, tana daf da shiga sashen ta ci karo da habib kasa tayi da kanta cikin jin kunya tace ina wuni,, kina lafiya ya ciwon kan naki yayi sauki da alama ya fada yana kafe ta da ido,, Cike da kunya ta amsa da eh don tasan ya gane inda zata take ta zabga sauri,, ajiyar zuciya ya sauke kafin yace in bazaki damu ba ina son muyi magana ne,, tsoro ne ya cika ta don gudun kada Khalil yazo ya same ta dashi amma haka ta dake tace to bismillah,, gyara tsayuwa yayi kafin yace don Allah zan iya sanin ko Ke Wacece ina nufin labarin ki saboda abunda ya faru a airport har yanzu abun yana damuna ta yadda akai kina gidan nan hakan ya faru,, hawaye ne ya taru a idanunta don tunowa datayi da abunda ya faru da ita cikin natsuwa ta warware mai komai game da ita tareda yi masa godiya na taimako ta dayayi,,, hankie ya mika mata cike da tausaya wa ta mika hannu zata amsa saiga Khalil ya wuce su fuu cikin bacin rai batareda ya kalli inda suke ba,, da sauri ta mike jikinta na rawa tace nizan koma ,, gyada kai kawai yayi batareda yace komai ba yana kallonta har ta shige juyawa yayi ya koma daki cike da damuwa kwanciya yayi rigingine yana tunani shikenan duk burin daya dauka akan maryam komai ya wargeje tank god daban riga da na furta mata komai ba juyawa yayi tareda yin matashi da hannun kujerar duk da haka yayi alkawari duk wanda take kokarin lalata mata rayuwa zai nemoshi a duk inda yake tareda daukar mataki akan shi wannan kawai zaiyi mata tasamu farin ciki,, koda ta jiga parlon ta sameshi kwance akan kujerar mommyn na kusa dashi ya daura kansa akan cinyar ta idanuwansa a rufe tamkar mai bacci karasawa tayi tayi musu sannu ta kema

Chapter 12 of 32