Share this page
ne karka damu muje wurin marar lafiya ,, Mikewa yayi suka tafi tare har kusa da gadon ummi a lokacin ta farfado anyi mata allura amma kwata kwata bata hayyacinta juya ido kawai take,, Sannu yayi mata kafin ya zaro bandir din dubu daddai ya basu yace maza asiyo maganin,,sannu ya kara yimata Aa cike da mamaki ya kara matsowa kusa da ita ya kura mata idanu wannan ba didde bace kuwa? *mrs Noour*✍🏻😍😍😍 [7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… *~Masoya na bakina nima bazai taba gaji yawa ba dayi muku fatan alkhairi Kamar yadda kukemin,Allahu ya bar kauna~*🀲🏻 *~,ANA MUGUN TARE IRIN HAR PARADISE DINNAN😍😘~* πŸ…Ώβž–2⃣9⃣ Kura mata idanu yayi wannan ba didde bace kuwa sudai su halima kallon kawai sukeyi cike da mamaki,gab da ita ya matsa,,jinjina kai yayi cike da murna yace tabbas wannan shatun didde ce tunda ga didde nan muna tare,, Cike da farin ciki yace shatu malam ina kuka samu sam.. Ji yayi kansa yayi wani irin sarawa da karfi dafe kan yayi yana sallati da karfi saboda yadda yakejin wani abu na kwankwatsar jikinshi,,da sauri malam garba yayi kansa kafin ya rikeshi tuni ya zube a kasa yana sallati da karfi,, Malam garba hankalinsa yayi bala'in tashi duk ya gigice ya rasa mai zaiyi ne ma, fadi yake Ku taimaka min alhaji ka rufa mana asiri ka mike don Allah ,dayake dakin da mutane da yawa nan take wasu suka ruga kiran likita ,,yayinda wasu suka kamashi aka kwantar a wani gadon da ba Mara lafiya,, Halima sai kuka take tana mun shiga uku ina zamu saka kanmu ni halima daga taimako yayinda ummin jikin nata itama ya kara rikice wa sai fitar da numfashi take da kyar,, Wasu likitoci guda uku suka shigo da nurses har guda biyar nan take aka dora shi akayi emergency dashi nan take labarin ya cika asibiti ana cewa alhajin didde mayu sun kamashi,, hankalinsu malam garba ba karamin tashi yayi ba nan wasu sukace su gudu tun kafin akamasu don alhaji ba karamin mai kudi bane,,nan da nan halima ta yafa gyalen jikinta babu inda baya rawa tace malam don darajar ma'aiki ka tashi mu gudu mubar asibitin nan,, duk da yadda shima hankalinsa yake a tashe amma haka ya daure tareda aro jarumta ya daka mata tsawa nan take ta tsaya don har ta fara tafiya,dole ta juyo babu shiri,kafe ta yayi da ido kusan minti biyu kafin cikin sigar kwantar da hankali ya fara magana,, Shin halima ina ilimin ki yake da hankalin ki ki duba chan umman maryam cefa kwance rai a hannu Allah batada kowa saimu yanzu in muka barta bakiyi tunanin wane hali zata shiga ba eyeeh,,, Mutuwa kike tsoro kokuwa mai ya kamata bawa yaringa hakuri da lamurran duniya da kuma hakuri da kaddara mai kyau ko marar kyau wannan mu kuma itace jarrabawar mu sai muyi hakuri da ita har Allah ya bamu ikon cinyeta kuma gashi nan ganin idanun ki ga dukkan alamun yasan ummi ne abunda nakeso daga gareki shine addua ba kuma ga ummin ba harga alhaji domin samun lafiyar sa shine samun kwanciyar hankalin mu,, Jikinta yayi sanyi sosai tabbas Hakane malam ta fada murya a sanyaye sai a lokacin ta samu hawaye suka zubo mata sharewa tayi da sauri saanan tace malam ya kamata ka siyo magungunan tunda ansamu kudin,,jinjina kai yayi ya mike ya fice jiki a sanyaye zuciyarshi cike da zullumin abunda zai biyo baya,, A emergency room kuwa doctors uku ne kan alhaji wanda baya cikin hayyacin shi sai wani irin jijjiga yakeyi dukda an daure shi da gadon gudun kada ya fado amma haka gadon Ke girgiza da karfi,, Wasu nurses ne suka kaima didde tsegumin abunda Ke faruwa batareda la'akari da tsufan taba ga kuma ciwo aikuwa nan da nan ta rikice musu kuka wiwi ta shigo uku mai yasame shi,,ita dai lallai dole akaita taganshi a haka wani doctor ya shigo wanda dama shiyake dobata, ba karamin fada yayi musu ba kafin yafara kwanta mata da hankali amma Sam ta fututuke take ita dai dole akaita ta ganshi dole ya ce mata yana zuwa ya fice yabarta da wat nurse,, da kyar wani likita ya bi malam garba ya fara duba ummin tareda bata taimako gaggawa allurai da magungunan ya zuba a drip sa'anan yayi mata wasu a cinya kafin ta fara dawowa daidai,, Kusan awa daya ana fama kafin aka samu ya daina jijjigar amma numfashin sa yake daidaita dole suka kira meeting saanan aka kira dan uwanshi , hankalinsa ya tashi shima yace gashinan zuwa amma a tabbatar da an kama mutanen nan,, Yana sauke wayar gurin baffa ya nufa ya fada masa halin da ake cike duk da dai baa fada musu takamaimai abunda ya faru ba,,shima baffa hankalinsa ya tashi amma saiya danne ya shiga kwantar maida hankali yace maza ya je ya shirya musu tafiyar ta jirgi su wuce,, Ummi dai ta samu dawowa dadai saidai bata magana saidai kallo da ido wadanda suke fita da hawaye ta gefensu ,,halima nata kokarin kwantar mata da hankali saiga wata nurse ta zo kiran su,saida hantar cikin ta ta kad'a saboda tsoro malam yace gasunan zuwa,, bayan nurse din sukabi bayan yasa wata dake kusa da su ta lura da ummin har office din ta kaisu suna shiga da yan sanda suka farayin ido hudu,nan take fitsari ya jiga tsiyayo wa halima saboda tsoro,, *us* Kasa karasawa tayi inda yake sai hawaye take fitarwa masu kuna tana tausayawa halin dazasu shiga musamman ya Khalil gashi tun baaje koina ba harya fara ciwo saboda soyayyar ta ,, tana tsaye a wurin likita yazo kafin mommyn ta mike ta ruko hannun maryam suka fito zuwa parlon suka bar habib da doctor din nan ya shiga dubashi cikin kwarewa ,, Zaman su keda wuya safina ta shigo hankali tashe wuce su mommyn tayi batareda tayi musu ko sannu ba ganin ta nufi dakin Khalil kai tsaye yasa mommyn daka mata tsawa rai bace dole taja ta tsaya tareda waigowa itama rai bace,, Mommyn cikin bacin rai ta soma magana wai yaushe zakiyi hankali ne safina for god sake Zaune kika ganmu amma Ke isasshiya kanki tsaye zaki shiga toh doctor yana duba shi zaki iya komawa anjima Kya dawo tunda ba'a riga aka daura muku auren ba ,, harara mommyn tayi tareda Jan tsaki ta kauda kai gefe tace amma mommyn ita din wannan illetrate girl din daura musu auren akayi datazo gurin shi bayan ni yakamata afara gaya mawa ta karashe tareda watsa wa maryam mugun kallo,, get out now safina mommyn ta fada a matukar harzuke,,itama kuka ta fashe dashi ta futa fuu Kamar zata tashi sama,,dakin mom ta shiga tareda fadawa jikinta tana tsananta kuka ,hankalin Mom ya tashi ganin irin kuka da tilon yar tata takeyi mai yafaru?, waya saki kuka?,ta tambayeta hankali tashe , Cikin kuka ta gaya mata abunda ya faru,,lallai hajiya Fatima Khalil din ba lafiya takasa sanar dani danake cikin gidan saanan Ke dakike a matsayin matar sa kije ta kora ki amma ta iya neman matsaiyacin yarinyar nan ko wlh bazai yuwuba kiyi hakuri kinji da kaina zanyi mata magana,kinji ki daina zubar da hawayen ki abanza,, toh mom tace cike da shagwaba kuma fa mom ko ganinsa bata bari nayi ba ,,dad'a rungume ta mom tayi tace kiyi shiru kawai zanje yanzu da kaina kuma dole mu bisu a sannu har ayi auren nan da anyi ta isa ta je gidanku ta yi miki IKO ne ,, cike da fitsara safina tace Tabb ina ta isa mom ai nima haka nake tunanwa kawai nake kyaleta kiga yar iskar chan aiki nasaka ta shine ta tafi karuwanci dakin wai ita adole zata nuna min bariki,,kwafa tati rai bace,, aiki kwantar da hankalin ki safina na yau ne zuwa gobe muna nja kinga kuwa mun kusa rabuwa da kwallon mangwaro kowa ya huta,,bari inje gurin hajiyar kada taji shiru itama shegiyar zan korata yanzu Kamar yadda ta kore ki,, toh mom safina ta fada cike da jin dadi ta mike suka fita tare ta shige dakinta tayi kwanciyar ta hankali kwance yayinda mommyn ta wuce bangaren Khalil din,, fitar ta keda wuta motar su daddyn ta kunno kai cikin gidan,,, *mrs noour ce*✍🏻😘😘😘😘 [7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… πŸ…Ώβž–3⃣0⃣ Fitar ta keda wuya motar su daddyn ta kunno kai cikin gidan,saida ta jira suka gama parking saanan ta karasa suka gaisa hankalinta a tashe suka dunguma sashen Khalil ne a daidai lokacin likita y fito daga dubashi,, gaisawa sukai da doctor din wanda yake family doctor dinsu ne har daddyn zai shige dakin likitan ya tsaida shi da nufin yi masa magana dole ya dawo suka zauna tareda zuba ma likita ido don jin maiyake damun Khalil din,, Saida ya gama rubuce rubucensa kafin yace a gaskiya dole Ku ringa lura da lafiyar Khalil domin yana neman jawowa kansa babbar damuwa zakayi mamakin yadda sauyin bugun zuciyar sa ya chanza a irin wannan kankani lokacin saboda haka gaskiya Ku tsaya da lura sosai akan lamuransa don gano abunda Ke damunsa wanda yake barazanar taba zuciyar sa Ku magance shi tun wuri,, Insha Allah zaayi hakan daddyn ya fada fuska ba yabo ba fallasa,,mikewa doctor yayi yace zan dawo anjima don kara duba shi,,OK babu damuwa suka amsa mai tareda mikewa har waje daddyn ya raka shi saanan ya nufi bedroom din Khalil shida dad,, Hankalin maryam ba karamin tashi yayi ba jin halin da Khalil ya Ke ciki sai kuka take kasa kasa,, harara mom ta wurgo mata cikin tsawa tace keeh ,, da sauri maryam ta dago cike da tsoro tana waro idanu waje wadanda sukai jazur,, uban mai kikeyi anan fitsararriya marar tarbiyyyar kawai ai dama kina makale anan cikin manya,,mom ta fada a harzuke,, dakatar da ita mommyn tayi tace haba hajiya kiyi hakuri haka ni da kaina na kirata nan,, Charaf tace eh hajiya amma duk da haka dataga zuwan su alhaji ai ta ba mutane wuri bawai ta zauna tana rarrraba idanu Kamar na mujiya ba sallati ta saki tana tafa hannu,,jinjina kai tayi tace lalli hajiya ki duba wannan munafukar yarinyar yadda take kuka Kamar uwarta ce ta mutu wai shin a matsa yinki nawa ko wacce zai aura ta danne damuwarta tana chan tanayi masa adduar samun sauki Ke kina nan saboda goyon bariki shine zaki nuna mana duniyanci toh tashi maza ki bar dakin nan,, Da sauri maryam ta mike tareda fashewa da kuka mai karfi,, mommyn kuwa baki bude take kallon kokarin mom cikin bacin rai tace haba haba hajiya wannan fadan duk mai yakawo shi ne cha nake maryam tazama yar gidannnan Khalil a matsayin yayanta yake dole ta nuna damuwarta akan ciwon sa,, Murmushi mom tayi wanda iyakarsa lebenta tace haba hajiya sai kace kema bakisan halin talaka vane a zamanin nan sai kayi kokarin maidoshi inuwa dayaji dadinta tohfa ba shida wani buri banda yaga ya maida ka rana,, toh Allah ya kyauta mommyn ta fada a hassale ta mike ta shige dakin Khalil,, Kwafa tayi tareda Jan tsaki tace da sannu zaku gane hajiya wlh dole ayi abunda yata takeso ta mike itama ta shiga,, gado ta fada tareda sake kuka da iyakacin karfin ta ko ta samu taji sanyi a ranta,wannan wace irin rayuwa ce anya kuwa zan iya yafewa inna wannan halin gararin rayuwar data jifane ,,maiyasa ban nemi taimako wani ba,maiyasa kaddara zaki kawo ni nan,,da sauri tayi istigfari ta mike tareda daukar alqur'an dinta tashiga karan tawa har saida taji natsuwa ta saukar mata kafin ta aje gefen bedside,, tagumi ta zuba hannu bibbiyu Insha Allah ni maryam nayi alkawarin cire Khalil daga raina ,nayi alkawarin barinshi har abada koda kuwa zan tsinci kaina cikin ciwon dayafi nashi,,zan maida hankalina game karatu na zan nemi na kaina don rufa mana asiri ni da ummi na Allah sarki ummi na kuka ta sake fashewa dashi mai tsuma zuciya,, dariya safina ta tuntsere da ita wanda yayi sanadiyyan dagowar maryam daga kifa kan datayi,, A shakiyance tace kuka ,kuka ko yanzu kika fara baki ga komai bama tukunna ki jirayi komawar mu nja gobe a lokacin zakiyi nadamar zuwanki duniya keda uwarki,,, shawara daya nazo in baki shine ki kama kanki muna dira nja inba hakaba cike lebenta na kasa tayi tareda huro hanci sannan tace wlh ,wlh ,wlh nayi rantsuwa labarin karyar dakika shirya ma su mommyn har kika samu karbuwa wlh saina tabbatar dashi,, Innalillahi maryam tashiga ambata wa nan take jikinta ya jiga rawa,, ganin haka yasa safina yin dariyar mugunta tace kinsan zan iya domin inada wannan *karfin IKO* don haka ki dauka shawara ta ko kuma kiyi watsi da ita Kamar yadda kikayi da farko duk ruwanki ne useless kawai ta jaa tsaki ta fice harta kai bakin kofa ta juyo tareda daga murya a kausashe tace kuma aikin dana saki indai ba tsohon naki bane zai fito daga kabari yayi min ba saiki mike ki fara yinshi tun yanzu,,ta sa kai ta fice,, Kukan bakin cike ta fashe dashi wannan wace irin rayuwa ce wasu masu kudin suka daukar wa Kansu lalle ta godewa Allah dayasa baa karkashin su safina take ba Insha Allah tayiwa kanta wannan alkawarin suna sauka nja inta barsu ta rabu dasu kenan har abada Mike wa tayi ta nufi dakin safina Kamar ko yaushe kayan nata tayi watsi dasu ko ina da gayya donta kuntata mata tsugunawa tayi ta fara aikin hada kayan,,, *Kano* Shi kanshi malam garba ya tsorata sosai dauriya kawai yayi saboda halima don inya nuna tsoransa baisan yazatayi ba Durkushe kasa suka dukansu Kansu a kansa Kamar yadda daya daga cikin yan sanda ya sasu,, Cikin kausashiyar murya babban su dasuka zo dpo din yafa musu tambaya ,,wa ya turo Ku gurin alhaji,maiye hadin Ku dashi,, gaba dayansu sun rike ci an rasa wanda zaiyi magana har kusan minti dayan shiru ,tsawa ya kara daka musu wacce ta kadar musu da hantar cikin su kafin suyi magana wayarta tafara ringing,, dole ya dakatah tareda dauka saida yayi kusan minti biyar yana wayar kafin ya katse rai bace ba haka yaso ba yaso ace yasamu wasu masu numfashin a wannan case din yazaai baffa yace abar maganar saisun karaso,, amma dukda haka bazai bar case dinnan haka ba umarni ya bawa yaransa dasu tafi dasu har dakin da ummi take su sa musu ido kada su fito ko ina har saisu baffa sun iso,, keyar su aka tasa har dakin yayinda yan dakin gaba daya kowa ya yi ta kansa duka sun waste ba kowa sai ummin dake kwance tana bacci,, Cikin awa daya sai gasu a asibitin lokacin anata rikici da didde saita je gurin alhaji ko kuma a nuna mata mayun saitayi maganin su,, Ganin baffa yasa tayi shiru dole sai da suka shiga dakin alhaji suka dubashi kafin suka bu kaci ganin su malam garba har dakin dpo ya kaisu da kanshi a lokacin ummi tafarka tana jingine da pillow ta baya halima na bata ruwan koko,, Zuciyar su ta shiga bugawa da karfi daga idanun da didde zatayi sai akan shatu waro idanu tayi waje cike da tsoro da tashin hankali tad shatun didde,da sauri ummin ta d'ago kai ta kalliesu nan take itama taji kirjinta ya shiga bugawa da karfi,didde ta fada itama a figice duk da maganar bawani fitowa tayi ba nan take didde ta fadi wanwar da sauri surajo yayi kanta aka kamata kowa sai sallati yakeyi yayinda itama ummin suma tayi dole likitoci suka dukufa kansu,kara shiga tashin hankali su malam garba sukai wanda adaidaita lokacin inna dake chan gida tana kirga tarin uban kudin da harira tazo musu dashi,,ji tayi Kamar ana zare mata lakar jikinta tun daga kanta har zuwa yatsun kafarta kudin ta aje ta jingina bayanta da dan gadon karfen dake dakin Baayi minti daya ba sai ganin wani bakin mummunan kare tayi ya gilma tama bayinsa dauke da kan mutum jini na tsiyaya kara ta kwalla da karfi ta sume a wurin,, Kusan minti hamsin kafin aka samu suka farfado allurai bacci akayi musu kafin doctors din suka fito Kansu ya daure da wannan abun alajabin dayake faruwa,, Surajo ko ya kasa Zaune ya kasa tsaye ya kai ya kawo Kamar zuciyar shi Zata tsage ta fado don takaici hanashi daukan mataki da baffa yayi,, Da sauri yabi bayan doctors din har office Kamar yadda suka bukata,, kwantar musu hankali doctor ya fara yi dacewa babu komai zasu iya farfado wa ako yaushe cikin koshin lafiya saidai abunda yake daure mana kai shine dama sunada alaka ne da patient din dake dakin saboda da alamun ganin ta yake sanya su shiga wannan halin,, da sauri surajo yace ina doctor babu wani alaka kawai dai akwai wani mugun abun da suke aik... ya isa haka sirajo baffa ya katse shi cikin muryar dat tako ya fara magana muna godiya likita tabbas suna da alaka indai har sunan data ambata ya zamto itace saidai hankali ba kwance ba bane da tabbas din itace sai dai muyi fatan samun saukin su,, Allah ya kawo sauki doctor ya fada,,ameen suka amsa dashi tareda mikewa suka koma zaman jiran farkawar su,, Sai bayan kusan awa uku ummi ta farka ahankali ta bude idanuwanta halima na gefe ta buga tagumi tana share hawaye hankalinta a tashe,,halima ummi ta shiga kiran ta a hankali firgigit halima ta dawo daga duniyar tunanin datakeyi da sauri ta karasa gurin ummin wacce ta soma kuka da sauri halima ta rike mata hannu tana mata sannu Cikin muryar kuka ta soma magana didde nace nake gani halima ko kuwa zafin ciwo ne dama itayena suna raye halima,waro idanu halima tayi cike da mamaki tace ummin maryam mahaifiyar ki ce wannan matar ,, kafin ummi tayi magana sai suka ga anbude Kofar dakin didde ce gaba sai baffa silurajo na bayansu da sauri didde ta karasa ta rungume ummi itama rungumeta tayi kuka suka saka sosai kowa a dakin saida suka sashi kuka yayinda su halima Ke godewa Allah daya tsirar da su tabbas sai yanzu ta gano kamarsu daya da ummin da didde baffa ne yace halima ta janye su saboda jikin ummin kin rabu wa sukai didde ta manta da kunya ta fulani musamman da shatu wato ummi take babbar diyar ta shima surajo karasowa yayi ya rungume su yana kuka yana fadin dama didde bani kadai bane danki maiyasa baki taba sanar dani ba inada yar uwa eyeeh,, Ganin abun nasu yayi yawa yasa baffa rufe su da fada kafin daga baya ya dora da yi musu nasiha kana godiya yakamata suyi wa Allah ba kuka ba saanan ayi fatan samun sauki su,, Dole didde ta janye jikinta amma hannuwan su na makale dana juna,,a sanyaye ummi tace mai yasa didde baku taba wai wayata ba maiyasa kuka manata dani a rayuwar Ku didde? da sauri harira ta mike tana ihun kiran mutane gida cikin kankani lokaci yan gida suka shigo hankali tashe ganin inna yasa hankalinsu yayi bala'in tashi yadda taketa kumburi Kamar balloon kuwa ya tsorata an rasa wanda zai karasa kuringa yayinda ita kuma ta farka a gigice ihun kawai take da iyakacin karfinta kai bakace inna bace,, nan take kafar ta tadama ta fashe jissss kake jin kara na fita Kamar an huda kumburariyar ledar nono nan take ruwa ya fawa feta mai azabar doyi da yauki ihun take tana kururuwar ataimaka mata amma kowa ya kasa karaswa dayake babu yayanta sai matansu da ya'yan su harta harira Jakarta ta dauka tana ja baya a tsorace zata gudu haka ilahirin gabobin jikinta ya shiga fashewa yana fitar da ruwan tana kuma kara kumbura ruwan na fita wari ya addabi yan gida kowa dole ya fice aka dage labulan dakin nata sama suna tsakar gida cirko cirko kowa da abunda yake sakawa a haka yayanta suka shigo hankali tashe magana harta fara cika kauyen Makotan kuwa sun cika kewayen inna dan kam ana gulmarmaki,, Hankalinsu ba karamin tashi yayi ba koda suka shiga da gudu ba shiri suka fito suna ammai Kamar zasu amayar da kayan cikin su ita kuwa in azabar tai azabar saita suma ta kuma farfado wa da kanta tana ihun saboda wuya,, *sai ince Allah ya kyauta inna kin bara girbar abunda kika shika*😭 *us* tana cikin aikin safina ta fito daga toilet tana wake wake kallo daya maryam tayi mata ta dauke kanta ta cigaba da abunda takeyi wurin mirrow ta wuce tareda Jan stool ta zauna tayi kwalliya saanan ta mike ta karaso inda maryam take wacce take kokarin rufe trolley fusge zip din safina tayi ta bude trolley kayan ciki da maryam ta nunke ta watso kasa gaba daya tashiga dube dube saida ta gama warware ninkin gaba daya kafin tayi tsaki ta mike ta nufi drower tana fadin ashe bata ciki ma rigar,, doguwar riga ta dauko mai matukar tsada da kyau ta saka ta fice daga dakin ,,girgiza kai kawai maryam tayi abun ya mata ciwo amma babu komai akwai lokaci ta cigaba da aikin wanda ta dawo mata shi baya,,, *mrs noour ce✍🏻😘* [7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… *~gareku wannan page din yan groups din~* ❀ *mrs noour Hausa novels*😘 ❀ *karfin IKO fans group*😘 ❀ *oum Asghar group*😘 ❀ *~ANA MUGUN TΓƒRΓ‹~*❀ *maman waleed ban manta dake ba*😍 πŸ…Ώβž–3⃣1⃣ kai tsaye main parlon ta sauka gaba dayansu suna parlon banda mommyn wacce Ke wurin Khalil,, ba bu wanda ta gaida balle sannu saima turbune fuska datayi tace mom ni yanzu ya zanyi ya Khalil ba lafiya kuma inason zuwa shopping ta fada a shagwabe,, Jawo ta jiki mom tayi tana fadin kiyi hakuri baby sai dai ki hakuri tunda muma mun fasa fitar,,.. Aa dad ya katse momy ba'a yi haka ba tunda ta shirya ga yayanta nan habib saiya kaita,, b'ata rai sosai tayi tafara gunguni no dad banason fita dashi wlh gwara driver ko inyi driven din da kaina but pls dad banda wanchan I hat to see him,, Shima dad d'in b'ata rai yayi yace Aa yanzu kuwa zamuyi rigima dake maza ki wuce kuje yanzu nan mai marabar shi da ya Khalil ne,, Mikewa tayi Kamar zatayi kuka tasan halin dad sarai zaiyi mata komai amma ta rasa dalilin dayasa yake b'ata mata raiba akan habib tsaki ta ja da karfi wanda yayi matukar b'ata ran dad don dukkansu sunji ga kunya yadda tayi masa a gaban daddyn,, Hawaye ne Ke silalowa daga idanunsa cike da bacin rai yake fadin why mommyn maiyasa?maiyasa daddyn bazaiyi farin ciki da abunda nakeso ba wlh mommyn bazan iya rayuwa babu maryam ba zan jure rashin bayyanar da sonta amma banda cire sonta a zuciyata pls mommyn kiyi wani abu mana,, Itama hawayen ta share cike da tausayawa tace kayi hakuri son babu abunda zan iyayi akan maganar nan kasan halin mahaifinka sarai don haka nake baka hakurin cire maryam a ranka ka ajeta a matsayin yar uwanka, domin kuwa ikon Allah ne kawai zai hana daddyn ka fasa aiwatar da wannan kudirin nasu don haka nake baka shawara Ku dage da addua I promise u nima daga yau na dauki alkawarin taya ka da addua kaji son ta fada tana share masa hawayen,, lumshe idanunsa yayi kawai shi kadai yasan yadda yakejin son maryam a zuciyar shi mommyn kuwa tasan irin illar da sonta zaiyi masa muddin yayi kuskuren rabuwa da ita kuwa,,girgiza kai ya shigayi da karfi yana fadin I can't mommyn ,I can't wlh bazan iya ba pls mommyn i need to see her now,,, Ba karamin tashin hankali mommyn ta shiga ba sakamakon ganin yadda yakeyi dole ta koma rarrashi tareda kwantar masa da hankali akan indai matarsa ce ko ana muzuru ana shawo saiya aure ta amma don Allah ya cigaba da kai kukan shi ga ubangiji talikai ,, da kyar ta samu yasha maganin data jik'a mai cikin ikon ubangiji baifi minti uku ba bacci ya dauke shi,, Jiki a sanyaye ta

Chapter 14 of 32