Share this page
sunce tayi alkawarin zata kuma dawowa,, Hamdala ummi tayi Tared daga hannu tayi wa Allah godiya,, Nan sukaci suka sha har malam garba ya dawo nan suka yanke shawarar a fara neman yan sanda sutafi dash gidan hajiya ladi dole bazata rasa wani dan bayani ba akan India maryam din take ba,, Aikuwa kowa yayi naam da hakan kai tsaye police station suka nufa suka shigar da report abunka da masu gidan rana tunda yanzu abba shima ya wuce raini nan take yan sanda suka shigar aka basu motar daya da yansan da biyu hard a dpo din wurin ya bisu domin dubu Dari biyar cus abba ya ajiyae masa kan table ,, tun daga nesa suke hango dandazon mutane cike da kofar gidan har suka iso rigima ce akeyi sosai da hajiya ladi da wasu India zuwan yansnada ya sanya mutane darewa kowa yayi nesa yayinda hajiya ladi murna ta cika ta duk a zaton ta alhaji ne ya aiko mata su amma sitaga sabain haka hanin bakin fuskoki don itama kwata kwta bata gane ummi ba,, cin mutunci sosi yan sandan sukayi mata tareda iza keyarta cikin mota suka tafi da ita motarsu na gaba tasu ummi nabin su baya har station din suka shiga,, Ba karamin tsaorata hajiya ladi tayi ba tayi rantsuwar tayi rokon da magiyar amma sunki yarda da ita duka sosai tasha a wurin amma taki fadin gaskiya saida taga dpo yasaka an dauko electric shock sanna zuciyar ta karye tashiga rokon zata fade amma ina saida suka gwada mata sau daya na wanin sanna suka cire aikuwa taji muguwar azabar da tunda take a duniya bata taba jin irin taba har sums tayi,, Ruwa mai matukar sanyi suka sheka mata Wanda yasanta sauke sauke ajiyar zuciya mai karfi tareda bude idanunta,tada ta zaune sukayi nan aka sake tambayar ta aikuwa babu gardama ko musu ta zaiyane musu abunda tasani tace kuma tabbas har yanzu alhaji ya tambatar mata maryam tana cikin garin Abuja don har yanzu yana bibiyarta saidai kuma tana gidan wani baban retired janar na yan sanda shiyasa bai samu damar sato maryam dinba,, Nan take aka dauki duk wani bayani daya kamata gameda alhaji sanna aka tasa keyar ta zuwa cikin cell tana kuka tana rokar su ummi gafarar su yafe mata babu Wanda ya tausaya mata domin babu tausayi Sam ga masu irin halin hajiya ladi masu lalata tarbiya yayen mu mata a duniya,, nan dpo ya shige kwantar musu da hankali akan yanzu zai aika da report zuwa Abuja akan cigiyar ta saidai abun takaicin shine babu hoton maryam din dazaa bada saboda lokacin baya akwai karanci rashi Wanda basuda ways balle kuma har akai ga zuwa wurin photo,, Hakanan dai aka tattara bayanai akan kwatanxen ta suka turashi ta email dinsu na Abuja ko ina kuma suka tura kowanne gari kozaa dace ,, Sosai sukayi ma dpo godiya suka tafi masaukin su suka wuce zuwa gobe kuma zasu dawo,, ********** *Abuja* Gaidasu tayi kanta har lokacin yana kasa yaseer ne kawai yasamu damar amsawa murna ta cika shi da sauri yace aa gimbiya tashi daga kasa karkiyi kura dawo kusa dani,, d sauri safina tace karta kuskura ta fara wannan gangancin batada wannan hurumin saboda Kaine kawai na daga mata kafa amma kai kanka nayi maka warning akan ta ba abar yadda bace tsintacciyar mage ,, da sauri ya Khalil ya damke pillow dake kusa dashi domin jiyake in baiyi hakan ba zai iya rufeta da duk a Wanda zai iya zama matsala ga maryam din shiyasa yayi hakuri zuciyar sa sai azalzala take da bakin ciki musamman inya kai kallonsa ga yaseer Wanda keta faman wani rawar kai da jiki,, Ku fita kawai waje nima Ku barni da ango na mu zanta ,, Dagowa yayi yana duban maryam din wacce akayi SAA ita ma shidin take kallon wani mugun kallon ya Watson mata mai cike da kaukausan gargadi amma sitayi Boris dashi ta juyar da kanta gefe dukda kuwa yadda kallon nashi yayi mugun tasiri wajen sanya tsoro da sanyin jiki gareta amma yazatayi bazai yuwu tayi ta zama jiran shi Wanda tasan yariga da yayi mata nisa yafi karfin ta mikewa tayi tabi Bayan yaseer suka fice zuwa waje,, Ya ilahi ya furta murya kasa tareda dafe kansa mai yarinyar nan take nufi ne kodama yaseer din ya Dade yana zuwa ne,, Muryar safina ta katse shi tana fadin ya Khalil ya kaga zabina nayi kokarin ko kaga yadda suka dace kuwa sosai dey are masa for each other ,, saukar kyakkyawan lafiyayyan maruka taji bisa kuncinta Wanda saida ta fadi kasa daga kujerar,, Kallon sa take cike da mamakin da bakin ciki ni ka marar ya Khalil,, Muryar sa a kausahe yace na dade ina burin yimiki Wanda yafi haka ma ki daure wannan yazame miki na karshe domin nagaba bazai taba zuwan miki da suqki ba ya mike ya fice rai bace yazo ya huce su maryam din batareda ya kalli India suke ba domin yin hakan zai iya sanyawa zuciyar bugawa yayinda yaseer yake yimasa maganar amma ko kallon tsaiya bai ishe Shiva ya kunna mortar ya jata da gudu gaske yabar gidan,, Ba karamin tashi hankali maryam ta Shiga ba Wanda saida yaseer din ya fahimta gaba daya ta rasa natsuwar ta ganin irin gudun dayake yi bana natsuwa,,,, *mrs noour*✍🏻😘 [7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… πŸ…Ώβž–4⃣4⃣ Gaba daya hankalinta da nutsuwar basu ga yaseer Wanda Ke ta kokarin cusa kansa gareta Wanda har saida ya fuskanci hakan da kansa ya sallame ta batareda yaso hakan ba domin shi harga Allah gani yake yasamu matar aure ne babu damuwa,, Ko a hanyarsa tunanin abunda yafaru kawai yakeyi kodai dama Khalil yana son maryam ne don ga alamomi nan sun bayyna,, Dage kafadun sa sama yayi alamun ko a jikinsa tunda aure zakayi kai Baka isa kahanani auren ta ba wallahi wayar sa ya maida aljihu Wanda da yayi niyyar kiran Khalil ne din,,sai ya cigaba da tukin sa kawai hankali kwance tareda kudiran aniyar babu wani mahaluki dazai hanasa auren maryam din,, da taimakon Allah ya Khalil ya isa gida ko tsayawa kashe motar baiyi ba ya wuce cikin gidan sashinsa ya nufa rai a matukar bace idanunsa sunyi jajir kai tsaye wurin fringe ya nufa ya dauko ruwa mai matukar sanyi ya balle murfin tareda kafa kai saida ya shanye shi tass kana yayi jifa da goran,, Bedroom dinsa ya shige tareda fadawa gadonsa ya kwanta rike da kansa Wanda yakejinsa tamkar zai tsage masa gida biyu anya kuwa banyi kuskuren yarda da wannan auren ba kuwa? taya zan iya rabuwa da maryam kamar yadda daddyn yakeso? anya kuwa zuciyata zata iya cigaba da bugawa matukar na rasa maryam kuwa? Juyi tayi gefe ganin bashida amsar da zai iya baiwa zuciyar sa sosai yakejin daci zuciyar sa gaba dayan duniyar ta fice mishi arai,, tin kafin ta kara sa cikin parlon take jiyo kukan safina Wanda ba karamin tashin hankali ya kara haddasawa zuciyar taba adduoe ta shiga karantawa dontasan yau Allah kadai zai ceceta a gurin mom,, Sallama tayi cikin sanyin murya ta shiga kallon daya tayi musu ta kauda kanta kirjinta ya kara tsananta bugu kuka sosai ta hango safina nayi jikin mom ita kanta mom din a kallo daya tagano matukar bacin ran datake cikin,, saman step ta nufa cikin sauri gudun kada su ganta sai dai kash matakala biyu ta taka taji an damko wuyan rigarta tabaya tareda fincikota masa harsada ta buga kafar ta jikin karfin step din,, Sosai taji zafin amma hankalinta gaba daya yanaga safina wance Ke kumburi tana sauke huci kamar kububuwa,, Nuni tayi da kirjinta tasoma magana cikin matukar bacin rai Ke garkin yi isar da wani zai dora hannun sa a jiki na wallahi wallahi kinyi babban kuskure,, domin kuwa ni safina matukar ina numfashi saina daidaita ratuwar ki saikin yi nadamar zuwan ki duniya wallahi,, don Allah kiyi hakuri anty wallahi banida laifin.. Kyakyawan mari taji saukar shi a fuskar ta Wanda ya haddasa mata yin shiru ga ban hakurin datakeyi,,dafe gurin tayi hawaye masu zafi suka shiga silalowa bisa kuncinta,, kunnenta ta kama da karfi ta murdi tace zaki iya mantawa da komai amma banda wannan alkawarin danayi domin yin hakan zai iya zama barazana ga rayuwar ki jaka kawai tasa kafarta wacce Ke sanye da takalmi mai tsini ta taka ta da karfi ta wuce,, Sosai maryam tasaki kara da karfi saboda tsananin azabar dataji ta ziyarceta har cikin kwakwalwar kanta kuka sosai ta fashe dashi,, Dariyar mom tajiyo daga bayanta kafin tace waike tsintacciyar mage ko to wallahi baa gidana ake wannan barikin ba wallahi koda safina bata dauki mummunan mataki akan kiba nizan dauka wallahi don safina bata taba rasa wani abuba tun tasowarta don haka Ke baki isa ki hanata auren Khalil ba muzuba nudake,, tayi kwafa ta wuce saman ,, Kwaciya tayi gurin ta fashe da kuka mai mutakur daci da zafi Allah sarki maraici Wai akama tana da uwa kenan dukda kaddara ta rabasu amma tana saka ran ganinta nan gaba inaga batada iyaye Ashe da haka zata rayu cikin gararin rayuwa mai matukar wahala meye laifin na aciki Wanda bansan maiya faru? Umarni ta bani kuma nabi na fita gun yaseer din mai kuma sukeso dani anya kuwa bazan bar gidan nan ba inshiga duniya kuwa,, Ta dade gurin kafin ta yunkura da kyar ta miki da bin bango ta isa dakinta toilet tashiga ta taro ruwa mai zafi ta zuba dettol a ciki sanan ta fito gefen gado ta zauna ta yaye doguwar rigar ta sosai takejin zafi gurin harya kumbura yayi jajir da kyar ta daure ta gasa gurin ta shafa mai akai ta kwanta ,, Kwana tayi salloli da kuka tana rokon ubangiji ya bayyana mata ummin ta kota huta da wannan gararin rayuwar har saida tayi sallar asuba saanan ta bingere a gurin ta fara bacci,, Kwana yayi babu nutsuwa da kwanciyar hankali a gurin sa donyasan waye yaseer akan son abunda yakeson mallaka matukar da gaske yakeyi,, duk iya nacin mommyn Khalil yaki gayamata abunda Ke damunsa ko da safen daya shiga da kyar ya kurbi ruwan tea ya fice zuwa office fuskar nan tashi kallo daya zakayi masa ka gane yau babu kalau,, Sosai safina ta tada borin wallahi saita tafi us zata karbi admission tayi registration babu yadda mom batayi da itaba amma taki hakura ko gurin gyaran datake zuwa taki zuwa ,,dad kuwa ko kallon inda suke baiyi ba don ba karamin bacin rai halin safina yake haddasa masa musamman dayaji akan dalilin datake wannan haukan,, Sosai kukanta yake damunsa saboda matukar son datake yimata amma lokaci yayi dayakamata ya daina biye mata saboda gidan wani zataje ba lalle tasamu abunda take so achan dinba kamar yadda malam ya umarceshi,, Aikuwa ganin dad ya fita batareda yace mata komai ba ya kara harzuka ta sosai ta dinga kuka ta koma gurin mom ta fada jikinta tana cigaba da kuka tace wallahi mom tunda dad shima yanzu ya daina sona wallahi sainyai karatunan akan wancen dan iskan zanbar karatuna Bayan basona yakeyi ba mom ki duba abunda yayi min jiya akan waccen useless girl din,, tapping bayanta mom keyi tana bata hakuri amma kamar tunzura ta akeyi takiyin shiru dole mom ta dauki wayarta takira number aminyar ta hajiya kareema Ranki ya dade hajiya karema ta fada Bayan ta daga wayar,, hmmm ai bar hajiyar nan tukunna yar gidanki kice fa tsiyar tata ta motsa,,mom ta fada ,, toh babu damuwa ki kwantar da hankalin ki hajiya nagi akan hanyar zuwa Ku shirya munyi waya da malam yana jiran mu,, toh hajiya saikin karaso ta fada tareda kashe wayar,, da kyar ta lallaba safina ta shirya domin ita bawani tadda takeyi dawasu malamai ba amma mom din ta karfafa ta akan zasu samu biyan bukatar su insunje,, tafiya sosai sukayi a motar kamar zasu bar garin Abuja ta wani karamin kauye suka dauke hanyar sosai sukayi lafiya kafin su isa karamin gidanae mai dauke da dakuna biyu da bayi da kitchen ba wani gyara gare gidan ba,, a kyamace safina ta shiga gidan Wanda zama ma kan tabarmar saida mom ta nuna mata bacin rai kafin ta dan dangwala ta zauna tana yatsina ita duk wani Abu na talauci bata sonsa kyamar sa takeyi sosai balle irin wannan wurin,, Sosai yayi musu duba tareda yan tsafe tsafen sa kafin ya dago ya kurawa safina ido wacce keta danne danne bisa wayarta,, gyaran murya yayi kafin yace hajiya naga abunda kukazo dashi kuma bukatar Ku zata biya amma gaskiya sai anyi aiki sosai akan shi yaron don bangano zaman aure da safina ba dadai wancan yarinyar nake ganin,, natake safina ta ajiye wayar hannun ta tana zare idanun tareda kallon mom cike da mamaki,, hajiya kareema ta gyara zama tareda fadin yanzu malam yazanuyi kenan meye mafita don Allah a taimaka mana,, A gaskiya kunzo a kurarren lokaci amma zamu gwada mugani wani bakin kullin Leda ya dauko daga kasan tabarmar sa ya miko musu yace gashinan ayau tafara wanka dashi na kwana uku ne Ku tabbatar da zaizo gidan kafin tayi shi da kanshi in har tayi amfani da maganin daidai to ko da maryam aka daura mai aure saiya sake ta ,, Sosai sukayi masa godiya tareda ajiye masa kudi masu tsoka suka tafi gidan hajiya momi suka ssauke safina saboda gyara saanna suka wauce gida,, Da dare mom tasaka safina yin wankan maganin dole saman takira mommyn Khalil a ways ta shaida mata safina babu lafiya ga kawaye suna bukatar baiwa Khalil listdinsu dasuke bukata,, Mommyn tace babu komai zaizo insha Allah dama koda lafiyar ta kalau yaci ace yazo din donsu gabatar da abubuwan biki,, Maryam na daki batareda tasan abunda Ke faruwa ba tun jiya dasukayi mata cin mutunci takiyayi had a koda hanya ne dasu iyakarta gaisuwa sai dai da suka fitane tasamu ta shiga kitchen ta cika cikinta tazauna gurin yan aiki suka sha hirar su dataji karar motar su mom din tayi maza ta dauki drinks da snacks ta shige daki ta kulle kanta ,,, *Kano* iya dakuwa da wuya hajiya ladi tasha shi gaba day an kamannin ta sun sauya sosai ummi tayi naam da hakan sai dai tafison su maida hankali ga kama alhaji Wanda hakan abba shima yafiso,, to abunka da yan sandan mu na Nigeria sunki kememe akan Wai kama alhaji hakanan batareda wani kwakwaran shaida ba zai iya zamo musu Marsala musamman tadda suke kan kanfen din siyasar su za a danganta abun da kamar turene daga wani bangaren,,sai dai subari Bayan zaben ,, *mrs noour* [7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… *~godya gareku masoya ina matukar jin dadin comments dinku da duas dinku Allah ya bar kauna ya kuma biya mana bukatunmu na alkahiri baki day an mu~*🀲🏻😍 *gaisuwa gareku yan groups din* ~karfin ko fans~🀝🏻😍 ~ummu suhaill fans~😘 *Gareku wannan kyauntar*🎁🀝🏻 πŸ…Ώβž–4⃣5⃣ Jin haka yasa safina fadawa toilet tayi wanna da maganin dukda kyamar datake amma haka ta daure tayi ta fito kwalliya sosai tayi tayi matukar kyau musamman yadda gyaran da akeyiwa fatar ta ya kara haska ta,, babu yadda mommyn bata kada ba amma fafur ya Khalil yace bashida lafiya sai dai yayi aike ko kuma ta turo mai da kudi da abunda suke bukata ya aika musu,, dole mommyn ta kyaleshi don tasan duk akan maryam yake yin haka nasiha sosai tayi masa na yadda da kaddara tanayi tana shafa sumar kansa har saida taga suyi akan fuskar sa kafin ta mike ta fice,, sosai yaji karfin gwaiwa yazo masa ya kudiri aniyar yau insha Allah bazaiyi bacci ba kai cikin kwananki biyun nan ma zai raya sube wurin yin nafil filu da kai kukansa ga Allah yasan zai amsa masa adduar sa domin bayajin ajikin sa zai rasa Maryam,, Tun tana zauni tana jira har bacci ya kwashe ta anan saiji tayi ana bubbuga mata kafa firgigit ta bude idanuwan ta cike da bacci tana duban mom kara rufe idanun ta tayi zata koma,, Zumbur ta mike tana bude ido tareda duban agogo sha daya da rabi na dare zare idanu tayi tana kallon mom baki bude,, Harara mom ta watso mata tace wani irin shashanci ne wannan safina yaron nan baizoba amma har kika iya sakin baki kina bacci batareda kin sanar min ba ko,, turbune fuskar tayi cikin kunkuni tace kai mom Wai mekike sonayi ne zan janyo shine mom tunda yaki zuwa koda na gaya miki maizaki tunda bakin su daya da uwarshi,, Zama mom tayi kusa da ita batareda nuna wata damuwa ba akan yananyin da safina tayi mata magana ba tace wallahi tabbas safina kinyi gaskiya mantawa nayi bakin su daya da uwar sa ba kaunar auren nan sukeyi ba da daddyn sa nakira dayafi.,, Mikewa safina tayi tana cire kayan jikinta tace nidai nayi abunda kikace wallahi mom duk son aurensa danake in har bai karkato zuwa gareni ba wallahi bazan yi zaman two zero ba kuwa,, Jinjina kai mom tayi tace Allah ya kayuata ,Allah ya kaimu goben zamusan abunyi,, Washegari,,,,,,,,, biki saura kwana biyu baki na jiki sun fara zuwa musamman daga bangaren mommyn da mom sosai aka fara shirye shiryen biki daga kowanne bangare Wanda ayau ne kuma mom ta shirya mothers day dinta,, duk iya nacin su fafur ya Khalil yayi kememe yaki zuwa gidan tun safe da safina tayi wankan magani babu shi babu dalilin shi abin yayi matukar harzuka ranta mom sai aikin lallashi da ban baki takeyi kamr ba ita ce ta dage akan saita aure ya Khalil din ba,, Har cikin dakinta dad din safina ya shiga domin kai mata kayan biki,, Kallo daya yayi mata yasan tana cikin damuwa sosai ta rame sosai tayi fayau da ita sai uban gaske data kara kamar wata wacce take lalauyi ga idanunta nan sun kumbura sun kankanci tareda yin jajur,, Zama tayi kan kujerar dake gefe ya umarceta data zauna,, zama tayi akasa daga gefen gado tana facing dinshi kanta sunkuye tana wasa da kasan hijab dinta ,, sosai yayi mata nasiha da kaalamai na kwantar da hankali akan kaddara dukda shi tunaninsa ya dauka saboda rashin iyayenta da kuma tsangwamar iyalinsa take kuka,, Sosai tayi masa godiya da kayan daya bata,, wand kafin ta rufe baki yace karta kara yimasa godiya tunda shi mahaifinta ne abunda yakeso kawai shine taciga da hakuri da safina wata rana sai labari ya dauka zamansu tare zaisa safina ta chanza wasu daga cikin hallayan ta ko ba duka amma ina sai yaga abin kara gaba kawai yakeyi,, babu komai dad insha Allah zan cigaba dayin hakuri kuma itama bata chanza watarana dad mu dinga yi mata addua ne kawai,, Sallati sukaji da karfi akansu da sauri suka kai kallonsu ga ko far mom ce take zaro idanu waje taeda sallati tana tafa hannu,, Kafin suce wani Abu mom ta fashe da kuka tayi kan maryam da duka ta rufeta tana fadin wannan wace irin tsinanniyar yarince mayya karfa kawai kin gama da mijin yatakin samu riba shine kike tunanin komawa gurin nawa miji n wallahi yau saina karki,,.. taswa dad ya daka mata wacce ta sanyata dakatawa daga dukan maryam din,, Wani mugun kallo ta watsowa dad tace nizakayiwa birga irintaku ta sojoji wallahi kayi kadan alhaji bazaa dokeni a hanani kuka ba Sam wannan bazai yuwauba inba sharri ka shuka ba tayazaai kashigo har cikin dakin Wanda ba muharrmar kaba eyeeh tafadi rai bace tana tada jijiyoyin wuya,, Koda dad ya mike bai kallo ko inda mom takeba ya kama hannun maryam wacce Ke duke kasa tana kuka sosai kamar ranta zai fita,,tafiya yafarayi hannun sa rike Dana maryam din duka fita a sakin yayinda maryam keta razgar kuka kamar ranta zai fita ta fara gajiya da wannan rayuwar mai wahala addua take koyaushe roko take koyaushe amma gashi kullum Allah na kara jarrabanta da jarabawa kala kala dinga gwada karfin imanin ta,, biyo Bayan su mom tayi tana zazzaga tojara iri iri da rashin mutinci akan alhaji zaici amanar ta har palon kasa bata damu da bakin dasuka fara zuwa ba Wanda Allah yasa gaba daya daga bangaren ta suke,, Ganin ya nufi hanyar fita yasanyata kwarma wani iho tasha gaban dad murya dage cikin tashi hankali take fadin mai kake nufi ne alhaji mai kake shirin aikatawa ina zaka kai yar mutane toh wallahi indai ina raye babu inda zataje wato zaka kaita inda zakuci karenku ba babbaka ko to wallahi ta Allah taku... Sukar mari taji tass akan fuskar ta Wanda yayi sanadiyyar makalewar maganar datakeyi a makoshin ta kallon dad take cikeda mamakin da tsana wance da durar mata lokaci daya ,, Hannun sa ya daga tareda yin nuni gareta yace wallahi muddin baki shiga hankali kiba zan iya daukan mummunan mataki akanki ,tabbbas duba ga halin ki babu wani abin mamakin gameda halin yarki,, Ya juya ya fice safina ta taso da sauri tana kuka tarike mom dinta suka haura saman sosai yan uwan mom suka dinga tunzurasu tareda karfafawa safina take tayi registration dinta koda kuwa dad din baisani ba halin mazan kena gashinan dad ma dasukayi auren soyayya da mom din ki ya iya yimata haka akan wata inaga Ke keda dama Ke kadai kike sonsa,, Kai tsaye gidan su Khalil ya nufa da maryam da kansa ya kiranyo daddyn Khalil ta waya ya fito,, bayanin halin da ake ciki yayi masa savanna ya roki alfarmar varin maryam din anan zuwa bayan biki vayason maida maryam gida haka so yake yaga iyayenta suyi magana sosai don karatu yakeson tayi shiyasa dauki alkawarin rikon ta kuma insha Allah bazai yi kasa a gwaiwa ba,, Babu yadda daddyn ya iya haka ya hakura badan yaso ba yace babu komai ta shiga ciki Cikin sanyi jiki ta soma Jan kafa kashi kafar dama bata warke ba daga buhun da safina tayi mata ba ga kuma Karin na mom muryar ta a snyaye tayi sallama tareda shiga ciki,, Da sauri Momyn hanssana ta tasso ta rungume ta murna kamar ta hadiye ta hakama mommyn wacce Ke zaune tana ta zuba musu murmushi,, Karasawa da ita parlon tayi suka zauna a kasa dama duba kayayyaki suke wadanda zasuyi amfani dasu awaken mothers day,, girgiza kai mommyn tayi da sauri tana kin amsa gaisuwar maryam tace maza dawo kusa dani lafiyar ki kuwa maiyasameki kika rame haka ga wannan kumburi duk fuskar tamakar wacce tayi accident,,mommyn ta fada cike da damuwa sai a lokacin kowa ya lura da yanayin ta ,, tabe baki mommyn hassana tayi tace anty kin manta halinsu su safina ne ai wallahi naga rashin kyautawar Yaya wallahi Bacon nariga da natafi da wallahi Masan gidan ne ya ajeta da dakaina zanje indauketa mu tafi da ita,, Ita dai kasa kawai tayi da janta tana tausayawa rayuwar ta wannan watangaririya dame yayi kama tazama marainiya marar galihu da karfi da yaji duk sanadiyyan su hajiya ladi da inna wadanda suka nuna wa rayuwar *karfin iko* ,, Anya kuwa Zata iya yafe musu kuwa hawayene ya shiga silalowa daga idanunsa,, Rungumeta mommyn tayi ta shiga lallashin ta saida taga tabar zubda hawaye kana tasa aka kawo mata lafiyayyen abinci tareda ruwa da drinks masu sanyi ta sanyata gaba dole ta cinye shi kafin ta umarceta da maza ta hada ruwan wanka mai zafi ta Gaza jikinta tazo ta zabi kayan zuwa mother's day,, Sosai maryam taji dadi irin wannan kaunar da mommyn Ke nuna mata batasan damai zata saka mata ba dinba addua ba cike da kwarin gwuiwa ta wuce saman kanta tsaye zuciyar ta na matukar kwadayin son ganin ya Khalil ,,, *Mrs noour*✍🏻😘 [7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… πŸ…Ώβž–4⃣6⃣ Cikin sanyin jiki ta tura kofar ta bude ta shiga dakin yana nan yadda yake fes dashi sai kamshin turaren ta yakeyi cikin irin wayanda ya Khalil yake siyo mata,, toilet ta shiga ta tara ruwa mai zafi ta shiga ciki sosai ta gasa jikin ta saanan ta fito, ta shafe jikinta da mai saanan ta murza man zafi a ina yake mata ciwo kwanciya tayi bisa gado tana jin wata irin natsuwa da kwanciyar hankali wani irin far in ciki takeji sosai Wanda rabonta dayin irinsa tun

Chapter 20 of 32