dakile yace mai yasa zaki guje ni a wannan lokacin maiyasa maryam sake tsareta yayi da mayatattun idanunsa,,shiru tayi batareda tace komai ba saima kara kasa datayi da kanta kallon dayake mata duk tajita a tsarge maiyasa shima bazai fahimce ta itama ta fada a zuciya ta ,,,
ganin bata da niyyar yin magana yasashi matsowa kusa da ita tareda ruko hannun ta Kamar zaiyi kuka yace pls talk to me now maiyasa zaki yanke wannan hukuncin kina tunanin hakan shine lafiyar mu ki duba yadda so yake wahalar damu mai yasa zakiyi mana wannan horon ne,,
Janye hannun ta tayi tana share hawayen dake silalowa daga fararen idanunta murya na rawa kama zatayi kuka tace maiyasa kake cewa ya Khalil aini a ganina wannan shine daidai maizai sa mu cigaba da kwadaitar da zuciyoyin mu da son abunda muka San bazata samuba ,,mikewa tayi tana fadin kayi hakuri ya Khalil kayi hakuri pls tana gama fadar haka ta ruga da gudu zuwa sama ta shige dakinta tareda saka key kuka ta shiga rerawa tana dafe da kirjinta,,,
*Kano*
ba karamin wahalar inna Ke sha ba tayi nadamar marar iyaka cikin kwanakin nan babu mai shiga dakin datake sai yayenta daya zamar wa dole suma Sunayi suna kyamar ta yayinda iliya yau kwanan sa uku bai leko inna ba dama shine mai bata magani yana kula da ita toh kwarin dayake shaka ya fara mai illah kullum kwana take da ciwon ciki ga amai sai yau yasamu ya shigo ya daure hancinsa da baban Zane don gudun waro don har yanzu ciwon bai daina fitar da ruwa ba ta rame sosai ta lalace Kamar ba inna ba,
tana ganin iliya ta rusheda kuka tana fadin iliya kaima gudu na kake ka guje ni kwana nawa kenan bayan kai kadai nake gani bake jin dadi,,
katse ta yayi a harzuke yace haba inna nagaji haka bazan hutaba so kike ayi haihuwan guzuma da kwance uwa kwance kinsan halin dana shiga sakamakon zaman danakeyi a dakin nan,,
sallati inna ta saki tareda fashewa da kuka mai karfi wanda ya jawo hankalin babban danta baban garbati dayazo wucewa,,
sashen inna ya nufa amma ganin takalman iliya yasashi juyawa da niyyar komawa saidai maganar inna ta dakatar dashi dole baya ya dawo tareda labewa ta jikin kauren dakin,,,
Muryar inna ya tsinkayo tana fadin iliya ni najefa ka a wane hali bayan bala'in daka kara min a nawa zunubin tin bayan kashe kanwata maryam ban sake samun kwanciyar hankali ba saida ka kaini gun boka da kanka wanda ya jefa mu a bala'in da muke cike inda ka hakura ai dabaka tsinci kanka a wannan halin ba Aa kwadayin abun duniya ya saka ka yi masa kurciya tareda alkaba'i iri iri da har zaka guje ni toh wlh ka jira naka lokacin,,
mikewa yayi a fusace ya shake wuyan inna nan ta shiga kakari tana neman taimako ganin haka yasa baban garbati fadowa dakin cikin sauri ya kama hannun iliya hankali tashe ya fara kokarin cirewa daga wuyan inna wacce idanunta har sin firfito waje amma Sam ya kasa sallati ya shiga yi yana neman taimako kan kace kwabo yan gida sun cika dakin ganin haka yasa iliya sauta rokon dayayi mata ya daga hannu da niyyar janye wa amma hannu yaki daukuwa daga wuyan inna wacce ta suma saboda wahal ,,
A lokacin ne kuma alhaji abdallah dake Zaune tareda matarsa suna hira yaji kansa ya shiga Sara masa nana da nan wani irin duhu ya ziyar ci idanunsa nan take ya fadi sumammam da sauri matar sa tayo kansa tana jijjiga shi tareda kiran sunan sa amma ina ko motsin bayayi da sauri ta mike tanufa waje da gudu ta kira masu aiki aka kama alhaji abdalla suka saka a mota zuwa asibiti,,,
Sosai ummi ke samun kulawa daga ma'aikatan asibiti zuwa ga yanuwan ta suma musamman surajo wanda ya kasance kani gareta sunyi kika sosai da tausayawa rayuwar datayi musamman batan maryam wacce sun baza cigiyar ta ta koina kama daga nja har kasashen waje gidan tv da radio da jaridu amma shiru,,
shima alhaji yana samun sauki wanda daga baya likitoci suka bada shawara yi masa addu'oe don suna tunanin sihri be akayi wanda yasashi faduwa farkon ganin sa da ummi,,
*mrs noour ce*โ๐ป๐
[7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *๐ด๐ดKARFIN IKO๐ด๐ด*
๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
*HIKMAAH writers association*
Edited by๐๐ป *oum Zahara*๐
Dedicated 2my lil sis๐๐ป *Maman Sultan*๐
ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
ุงูููู
ุจู ุงุตุจุญูุง ูุจู ุงู
ุณููุงุ ููู ูุญูุง ูุจู ูู
ูุชุ ูุงููู ุงููุดูุฑ....๐คฒ๐ป
๐
ฟโ3โฃ4โฃ
Wata irin mummunan faduwar gaba ce ta ziyar zuciyar ummin a lokacin da ake wucewa da alhaji abdallah a gadon marasa lafiya dafe kirji tayi tana sallati har saida didde ta jiyo ta da sauri ta mike ta karaso inda take hankali tashe zama tayi gefen gadon datake tana tambayar ummi lafiya kuwa,,
jiki a sanyaye ta gyada kai kawai batareda tace komai ba,,
Idanu didde ta kura mata don bata yadda da amsar data bata ba ga alamun nan sun nuna tashin hankali da fargabar datake ciki,,ajiyar zuciya didde ta sauke cike da damuwa ta soma kwantar wa da ummi hankali wanda duk daukan ta akan tunanin halin da maryam take ciki ne,,
Addua ta bata shawarar ta dage dayi duma suna taimaka mata kuma Insha Allah duk inda maryam take zata dawo cikin kashin lafiya,,,
murmushi ummi tayi rai jagule ta ce wlh didde a kullum cikin yiwa maryam addua neke akan Allah ya kareta ya bayyanar da ita cikin koshin lafiya dukda kuwa ban taba zargin maryam akan zata aikata wani mummunan abu ba,,sai dai inna yau faduwar gaban ta daban ce wlh yanzun nan naji gabana ya yanke ya fadi wucewa da marar lafiya da akayi yanzu,,,
Jimm didde tayi kafin tace Allah ya kyauta addua dai itace zamu dukufa yi ba dare ba rana,,
Da haka suka cigaba da hira wanda ummi gaba daya batada natsuwa amsawa kawai take da eh da Aa hardai ta gaji tacewa didde bacci zatayi,,
Sosai iliya yake cikin tashin hankali da dukkanin dukacin ahalin inna wace kiris ya rage ta sheka lahira,,sai zare idanu yakeyi gida ya cika makel da jama'a ba masaka tsinke,,,
da kyar malam ya samu hanyar shigowa saboda jamร a yan tsegumin kowa nason gane wa idanunsa abunda Ke faruwa,,yafi karfin awa hudu yana addu'oe da yan dabarun na malamai ya shafa wannan ya goga wanchan amma hannu yaki fita dole aka umarce iliya dasu fito waje da inna don gaskiya warin dayake fita jikinta yana neman yiwa malam illah dole danta Yakama aka fito da inna wancen ta rame ta jeme babu kyaun gani babban tashin hankalin shine wannan warin dake fita daga jikinta,,,
ganin yadda jama'a suka cika gida yasa inna fashewa da kuka mai karfe muryar cike da nadama take fadin ki yafemin yar uwata na cutar dake da danki zuriar ki ,ki yafemin ,,
maida kallon ta tayi ga danta babban wato baban garbati tace don Allah ka nemo min shatu da mero innemi gafarar su nasan hakkin su Ke dawainiyar dani don Allah ta karashe tana rushe wa da matsanan cin kuka,,
malam ne ya matso inda suke wanda har lokacin hannun iliya na wuyanta yace baiwar Allah ko wane irin laifi kika aikata har haka keke fuskantar wannan ukuba,,
Cikin kuka inna ta soma gayama su Kamar haka shekaru masu da suka wuce tun tasowa ta na tsani yadda kanwata tafini kyau dadin dadawa ga farin jini wannan yasamun kyashin ta har ya kaini ga hallaka ta da hannu na nasa na danne mata fuska da pillow bayan na tusa mata katon zani ta gaban ta duk dan kada ta haihu har Allah yasa ta mutu ita da abinda Ke cikinta Ku yafemin ta karashe tana kukan nadamar ,,
sallati da sallalami aka dauka gaba daya wurin wasu na fadin ai dole kema ki samu wannan hukunci wasu na fadin dama abar iliya ya kashe ta kowa sai Allah wadai yakeyi da wannan mugun hali na inna kanwarka uwa daya uba daya kasa hannu ka kashe ta jama'a daamai wannan yayi kama,,,
Saanan audu ba mutuwa yayi ba wlh nan iliya yai sauri katse inna jikin shi sharkaf da gumi ko ina jikinshi sai rawa yakeyi,,da fadin don Allah inna ki rufa mana asiri karki fada kinga yadda fadin naki ya jawo mana,,,
Aa malam ya dakatar dashi barta ta fada ko ta samu sassauci ,,,
A sanyaye cike da wahala tace ai barshi malam akwai masifar datafi wacce nake ciki ne tabbas malam audu ba mutuwa yayi ba,,wannan abu ya faru ne tun lokacin da iliya ya dawo gida ya tadda shatu a matsayin matar audu zuciyar shi ta darsu da bakin ciki da hassada nan ya shiga kulla yadda zai mallaketa,,
A lokacin naje wurin wani malami yayi min asiri akan dangin shatu akayi saa asirin ya kama domin kuwa tun kawota garin nan babu wanda yasake neman ta itama kuma batayi kokarin neman su ba aka sanya Mantuwa tsakanin ta da iyayen da dangin ta,,
Sannan a wata rana illiya yazo yasame ni da zance nima kuma lokacin zuciyata cike take da tsanar audu saina bashi guyon muka kama hanyar wurin boka dan tsinanniya wanda yake cikin wani mugun daki yana Chan saman tsaunika amma haka muka ketare muka hau har inda yake kuma wanne ne kaidar aikinsa mudin ka haye zuwa inda yake toh bukatar dakazo nema angama
Muna isa wurin hayaki ne gurin ga kayan tsafi nan iri iri nan boka ya bayyanar gabanmu jikinsa daure da dan bante babu kyau gane a tattare dashi nan take ya bata rai tareda nuna mana hanyar komawa cikin kakkausan murya mai firgitarwa yace Ku tashi Ku koma sai bayan kwana biyu bana aiki yau ,, da sauri muka tashi muka sauka jikin mu sanyaye na dauka iliya ya hakura,,Amma ganin wannan Wight gold da kudin amurka da audu ya tsinta yasani kara tsanar sa don bana kaunar ganin cigaban shi a rayuwa ,,
haka nabi iliya muka kara komawa wurin boka dan tsinanninya akan lamarin audu nan boka ya bushe da dariya mai tsoratarwa wanda saida na firgita haka iliya ya rike min hannu yana karfafani ,saida yayi dube dubenshi da surkulle kala kala kafin wani kare ya bayyanar a gabanmu baki kirin mummunan mai jajjaye idanu yana fito da harshen sa waje dariya boka ya sakeyi kafin ya nuna iliya yace ka samu kan mutum dan shekara talatin a gobe ka kawo wan nan Karen da sauri iliya ya amsa da toh boka jiki na rawa ,,tsawa ya daka mana muka tashi da sauri muka nufo gida bayada banyi da iliya ba ya hakura amma yaki haka ya nemo wani ya kashe washe gari muka sake komawa gurin boka da gawar wacce ya nade a buhu,,,
sosai yayi tsafe tsafen da gawar kafin ya nuna gawar ta bata saiga wata laya ta fado gaban boka ,nan yasa hannu ya dauka tareda mikawa iliya yace mashi nan kasan yadda zakayi ka zagaya layar nan sau uku a kansa kuma ka tabbatar yana cikin hayyacinsa toh muddin kayi haka inya tafi ya tafi kenan har abada yadda gawan nana ta bata bat babu mai sake ganin sa ,,
nan muka shiga murna nan na kwance bakin zani na na mikawa boka kunshin kudaden dake jikina gaba daya muka mike har mun fara tafiya ya tsaida mu cikin kakkausar muryarshi mai ban tsoro yace sharadi daya Ku guji ranar da haduwar zata hada shatu da wani nata komai ya biyo baya karku waiwayeni ,,,
godiya mukayi masa jiki na yayi sanyi amma haka iliya ya karfafa ni dacewa itada iyayenta basa garinnan kuma ba fita takeyi ba ba kowa datasni anan ,,
haka bayan kwanan uku da zuwanmu wurin boka na tursasa audu zuwa gida shida iliya wanda yayi sanadin da iliya yasamu aikata abinda boka ya umarce shi nan ta fashe da mugun kuka tana fadin Ku yafe mun Ku roki su suyafemin gaba daya jama'a suka shiga tsane musu tareda Allah wadai da masu irin halin su,matasa kuwa tasowa sukayi da nufin karasa su gaba daya amma malam ya hana da kayr suka hakura yace wannan ma sakayyar dasuka fara girba ta ishe su,,,
*Abuja*
cike da shawaga ta fado dakin batareda sallama ba, idanunta tap da hawaye ta fada jikin dad wanda Ke karatun jarida ,,a jiyewa yayi gefe tareda fadin hoh yar rigima menene kuma baby,,turo baki tayi saanan tace dad har yanzu ya Khalil yaki zuwa wurina kuma gashi bai taba zuwa ba tunda muka dawo koda na kira wayarsa baya dauka dad ta karashe tana hawaye ,,,
dafa kafadar ta dad yayi yace safina ki ringa hakuri duka duka yaushe muka dawo after all kinsa suna shirye shiryen bude masa sabon kanfaninsa kiyi hakuri Jibi sai muje walimar tare ko ,,gyada kai tayi cike da jin dadi tace Yawwa dad tankiiu ,,,murmushi yayi yace maza tashi ki kiramin momy kuje tare kuyi siyyayar abunda zaku bukata and don't forget komai ya zamana kin siya tareda yar uwar ki,,,
Frowning tayi da idanun tana turo baki gaba tace dad wace kuma yar uwanta ,,,maryam yabata amsa a taikaice wanda nan take ta bata rai sosai tace dad gaskita bazan iya ba and pls dad don't spoil my gud mood OK ta fada jike da rashin tarbiyyyar ,,
yaji zafin abunda tayi amma sai ya gagara tsawata mata harta fice daga dakin wanda kai tsaye dakin mom ta wuce rai bace ta turo Kofar kan gado ta fada tana Jan dogon tsaki harara ta watsowa asabe dake gyaran dakin da sauri asibe ta fice daga dakin ,,,
Mom na fitowa daga toilet ta gant kan gado ta hade rai sai harara takeyi Aa lafiya Ke kuma kedawa kuma ,mom ta tambayeta,,hawaye ta share saanan tace dad mana wai don Allah mom baiyasa bazaki saka dad ya maida wannan karuwar gidansu ba wlh mom kwata kwata hankalina yakasa kwanciya yana chan gida daya tareda ita,,,
zama mom tayi kusa da ita tace wlh nima ina wannan tunanin amma kiyi hakuri dai har jibin muje chan dinko ,,,
badan taso ba haka dole ta hakura ta mike ta fice,,,
Zaune suke a falo suna hira maryam ba gyara wa hajiya farcen ta yayinda mommyn Ke kusa dasu sunata hirar wacce yawan ci akan yadda bikin bude kamafin na Khalil ne maryam tana ji n dadin hirar suka tsinkayo sallama a parlon ,amsawa mommyn tayi kafin ta tambayi menene ,,daya daga cikin ma'aikatan gidan ne yace dama ana sallama ne da maryam inji habib,,,
kallon Kofar takeyi kanta daure wane habib kuma itada bata taba fita ba muryar mommyn ta tsinkaya tana fadin gata nan zuwa iso dashi dakin baki ,,toh hajiya ya amsa a ladabce ya wuce,,,
*Mrs noour ceโ๐ป*
[7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *๐ด๐ดKARFIN IKO๐ด๐ด*
๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
*HIKMAAH writers association*
Edited by๐๐ป *oum Zahara*๐
Dedicated 2my lil sis๐๐ป *Maman Sultan*๐
ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
*sakon gaisuwa gareke wannan page din naki ne*
*@aisha ahmad hamza*๐
*bazan manta dakeba nasan kinanan kina zare zare๐,*
*Mrs Mahmud sarki*๐คฃ *ana mugun tare one love*๐ค๐ป
๐
ฟโ3โฃ5โฃ
Da idanu mommyn tayi mata ishara data mike taje,,a sanyaye ta mike tareda duban agogon karfe biyar na yamma wani miyau ta hadiye tareda Jan kafarta a sanyaye tasan duk inda ya Khalil yake yana hanyar dawowa,dole ta sallami kowaye da sauri gudun fushin sa,,,
mayafin kanta ta ware sanye take da atamfa Holland mai ruwan dorawa da ratsin ja ja ajiki dinkin riga da zani ne single saidai yabi jikinta rigar tayi mata das ajikinta baata daura dan kwali ba sai gyalen data daura a kanta kawai ware shi tayi ta yafa a kanta ta nufi fita,,,
Hajiya ce ta tsaida ita tana fadin Ke kuwa don kauyanci a haka zaki fita zancen babu yar kwaskwaremar mu ta mata a fadi haka tana dariya dake hajiya batada damuwa ta dauketa itama tamkar ya Khalil haka take mata wasan,,
Sunje kai kasa maryam tayi cike da kunya ga mommyn a wurin ai dole tayi mata kara kuma ma ita ba sanin kowaye bane aa hajiya hakan ma yayi yanzu zan dawo ta fada tareda ficewar,,
tsaye yake jikin motar sa ya harde hannayensa a kirjinsa yayi mata kyau sosai cikin shigar shadda sa saidai ko kafar ya Khalil dinta bai kama ba,,
kura mata idanu yayi harta karaso cikin tafiyar ta tanutsuwa da kunya abunda kke kara birgishi da ita kenan,,sallama tayi masa cikin daddad'ar muryar taa ai sanyi,,saida ya sauke ajiyar zuciya sannan ya amsa mata tareda fadin barkkaa dai kanwata da fatan kina lafiya,,
lfy lau ta amsa a takaice tana wasa da gefen gyalenta,,
Mu shiga ciki ta furta mai a sanyaye tareda juyawa ta nufi dakin baki yana biye da ita koda suka shiga har an tanadar mai abun motsa baki akan table nan take jikinta ya kara yin sanyi irin yadda wadannan mutane suke nuna mata kauna Kamar yan uwanta na jini bai kamata tayi musu haka ba amma ya tayi dole tayi hakuri tunda bai sanar da ita zuwansa ba,,
sai dai ya zamar matta dole ta dakatar shi ido ba mudu na yasan kima,,
Zama tayi a two sitter yayinda ya zauna a wancen take facing dinta one sitter abin motsa baki ta gabatar mai tareda tsiyaya mai juice din abarba wanda yasha hadi ta mika masa,,
Saida ya shanye tas kafin. ya gyara zzama tareda kafeta da idanu cikin shakakkiyar muryar sa ya soma fadin a gaskiya maryam ina da muhimmiyar maganar danake son sanar dake wancen ta dade tana damuna tun farko dora kwayar idona akanki nake matukar kaunar ki amma rashin sanin inda zan nemiki yasani hakurewa raina amma akoda yaushe kina makale a raina,,
sai kuma gashi Allah ya kara hadamu a lokacin dabanyi tsammani ba tun daga nan bake addua Allah ya amsa min tawa addua ki zamu matata,,sai dai kash a lokacin danake kokarin bayyanar miki da wannan sakon na fahimce soyayya mai karfi tsakanin ki da Khalil don haka dole na danne tawa soyayyar bawai don na daina kaunar ki ba Aa saidai gudun shiga hakki,,
sai gashi kwatsam a lokacin danake kokarin cire ki a raina saina samu labarin auren Khalil da safina shiyasa nace nima banga ta zama ba dole in shigo fagen dama a dama dani ko Allah zai bani sa'ar samun nasara,,
Don haka mai Kikace ?
kara dukar da kanta kasa tayi tana duban agogon dake daure a hannun ta kirjinta sai bugawa yakeyi itadai burinta ya tafi before ya Khalil ya dawo sai addu'oe takeyi a aranta,,,
ganin shirun yayi yawa yasashi sauke ajiyar zuciya tareda murmusawa a sanyaye ya kira sunanta maryam,,
dagowa tayi ta dube sa da fararen idanunta wadanda suke tamkar madara ta amsa da naam,,
Shikenan karki damu zan baki lokaci zuwa Jibi in mun dawo kiyi shawara da fatan zanji kabari mai dadi,,
Murmushi tayi kasa kasa tace shi kenan ba komai Allah ya kaimu na gode,,
Mikewa yayi tareda fadin OK na gode sai kin jini itama mikewa tayi suka jero har farfajijar ajiye motoci kirjinta sai dad'a bugawa yakeyi cikin sauri Allah Allah take ya ja matarsa yabar gidan amma sainaga yaja ya tsaya tareda gyara tsayuwa ya zuba mata idanu,,,
Janye nata idanun tayi daga kallon sa cikin sanyin muryar ta tace ni bari in shiga gida sai anjima,,
ni kuwa da akwai maganar danake son yi dake akan case din alhaji bai jira jinta bakinta ba ya cigaba da fadin a gaskiya wannan mutumin shuumin mutumin ne gashi dan siyasa dole abi abun a sannu tareda hujjoji masu karfi don yanzu muna tunkarar sa zaice makiya ne daga wata jamiyyar sukayi masa ture don haka nakeson wasu bayanai a bakinki ,,,
jinjina kai tayi itama kullum tunanin ta kenan tasan yana nan yana bibiyar rayuwar ta inba kamashi akayi ba bazata taba samun kwanciyar hankali ba,,a sanyaye ta futa babu komai ina sauraron ka nan ta bashi dukkan nin nutsuwar ta da hankalinta wanda harta manta da zullumin dawowar ya Khalil,,
bude murfin matarsa yayi ya dauko yar jota tareda pen ya shiga yi mata tambayoyi itama tana bashi amsa iyakar abunda tasani sun dauki kusan minti ashirin kafin ya rufe jotan ya na Jinjina kai Insha Allah zamuyi nasara ya furta,Allah yasa ameen suka amsa gaba dayansu Karar horn din motar ya Khalil tajuyo wacce har ta kutsa kai cikin gidan ta nufo gurinsu donyin parking ,,
nan take jikinta ya soma rawa kirjinta na dukan uku uku har ya karaso yayi parking ya fito fuskar nan tasa murtuk babu alamun sauki kauda kai yayi zai wuce da sauri ya habib ya mika masa hannu yana fadin Sallamu alaikum babban yaya ,,daga masa hannu kawai yayi ya wuce su cikin sarsarfa kana ganinsa kasan ran maza ya baci ,,
Wani miyon wahala ta hadiye tana zare idanu jikinta har lokacin rawa yakeyi dukda abunda ya Khalil yayiwa ya habib bataji dadin saba amma takasa bude baki ta bashi hakuri don nauyin da bakin yayi mata ,,
ganin haka yasa ya habib b bude mota tareda fadin sai anjima nagode gyada kai kawai tayi tajuya ta wuce Karar fashewa abu sukaji da karfi daga sashen ya Khalil din jikin ta ya kara tsananta da rawa daga kafa tayi da niyyar tafiya ta takejin wani Karar fiye da na farko ,, da sauri ta karasa sahensa sai kuma taja ta tsaya ganin Kofar bude ,,
kusan seconds ashirin tana tsaye tana shawarwarin shiga kota koma,,jin Karar tayi yawani yasata afka wa dakin ba shiri dafe kirji tayi tana zare idanu gaba daya dakin yayi fata fata da komai duk wani kayan ado ya watsar dashi kasha duk ya fashe tangarayen dakin hannun sa dauke da babban enlargement din hotonta da sauri murya na rawa tace ya Khalil pls don Allah kadaina kar...
Makale wa maganar tayi a makoshin ta sakamakon wani irin mugun duba dayake binta da shi,,kasa tayi da kanta don bazata iya jure irin kallon dayake mata ba ,,
Get out now ya fada a fusashe tareda mata nuni da kofa,,
kallonsa kawai takeyi gaba daya ya rikice idanuwansa sun kada sunyi jajir ji ajiyoyin kansa sun fito rudu rudu kuka ta soma yi ganin haka yayo kanta a fusashe yana fadin out I said,,
ja da baya ta shiga yi tana girgiza kai kayi hakuri don allah ,,,saukar abu kawai taji a kanta dafe gun tayi da sauri tayi kasa da kanta tareda runtse idanunta cikin radadi da azabar zafin datake ji nan take jini ya balle ya fara fita har yana diga kasa duk da dannewar datayi,,
Kura masa manyan idanunta tayi kusan minti biyu hawaye yana bin fuskarta kafin ta juya ta fice naushi ya kaiwa stool din dake dakin da kafa ya bi bayanta cikin azama ,,,
koda ya cimmata na wani nisa tayi ba saboda rashin saurin tafiyar ta fusgo ta yayi cikin zafin nama ya soma Jan hannunta wurin matarsa ya nufa da ita gidan baya ya bude tareda jefa ta ciki ya zagaya ya bude gaba ya tada motar a guje suka bar gidan ,,,
Wani babban chemist yanufa da ita wanda tun da duk dauki hanya bai kalli inda take ba har suka isa ya tsaida motar ya fito ya zagyo ya bude inda take hannunsa yasanya ya janyo hannun ta da karfi ya fito da ita suka nufi ciki,,
Mace ce a wurin da sauri ta taso ta taryesu cikin tausayawa tana ma maryam sannu ta zaunar da ita ta soma gyara mata yana tsaye sai hucin yakeyi yaki kallon inda taje dukda har cikin ransa yakejin kukan datake yi amma yakasa danne kishinsa zuciyarsa tuno masa takeyi da lokacin datake tsaye da habib,,kudi ya debo batareda ya duba yawan suba ya ajiye ma ta da sauri tace yallabai your hand is bleeding let me..daga mata hannu yayi kawai alamun baya bukata ,ya wuce gaba da sauri maryam tabi bayanshi hannunta dauke da ledar magani daaka hada mata ,,
bude motar tayi tashiga tun kafin ta gama zama ya ja motar da sauri ta rufo Kofar tana kallon hannunsa yadda yake digar jini da sauri ta furta pls ya Khalil ka tsaya a duba maka hannun ka yana jini sosai ,,,
Banza yayi da ita saima kara gudun motar dayayi ganin haka yasata fashewa da kuka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 32