Share this page
da karfi kusan minti biyu tanayi saiki taji yaja buri da karfi tareda yin Rivas ya kkoma chemist din bai bari ta fito ba ya shiga aka gyara mai hannun ya fito suka kama hanyar gida ,, Har suka isa bai kulata saida yayi parking saanan ya dubeta murya a kausashe yace get out pls,,tareda dafe gefen kansa,, Kallonsa tayi taga babu alamun sauki dole ta bude murfin motar ta fice jiki a sanyaye ta nufi cikin gidan tana wai ganshi,,, tana isa da mommyn ta fara cin karo sallati mommyn ta saki ta nufota cikin sauri tana tambaye lafiya maryam daga fita zaki d'ago fuska dauke haka da bandage Maiya sameki,, murmushi karfin hali tayi tace babu komai mommyn faduwa nayi shine ya Khalil ya kini asibiti aka duba min,, Ya Khalil mommyn ta maimaita ,shi ya Khalil din yaushe ya dawo anya ba wani abun yayi miki ba kuwa nasan halin zuciyar shi,, da sauri ta girgiza kai tana fadin haba dai mommyn bashi bane wlh,, Allah ya sauwwake mommyn ta fadi don bata yadda da zancen maryam ba maza kije kinsa magani ki kwanta kinji,, gyada kai kawai tayi ta wuce itama mommyn fita tayi ta nufi dakin ya Khalil din tun daga bakin Kofar dakin tasan babu lafiya komai ya tarwatsa shi ya lalata ,,tsallakewa tayi ta wuce bed room dinsa yana kwance akan bed din ya lumshe idanunsa hannunsa daya ya dafe kansa da sauri mommyn ta karasa inda yake ta kura masa idanu tasan babu lafiya babu mamaki yaga bakin maryam ne dafe kansa tayi taji zafi rau da kyar ya bude idanunsa ya kalleta wadanda sukayi jajur ,,kai tsaye drower maganin ta nufo ta duba saanan ta dauko mai guda biyu ta dauko ruwa ta dawo zama tayi ta dago kansa ta dora akan cinyar ta ta soma shafa masa gashin kansa saida taga ya danyi sanyi saanan ta balle maganin ta mika masa,, babu musu ya bude bakin ta zuba mai ta kafa mai ruwa ya sha saanan ta cigaba da shafa masa kansa har aka kira sallar magrib kafin tace son maza kayi alwalar tareda wanka kaje masallaci kuma ka tabbatar da ka roki ubangijinka bukatun ka domin shi kadai ne zai biya maka ,,gyada kai kawai yayi tareda mikewa ya shiga toilet ,, itama mikewa tayi ta fito tareda umartan masu aiki dasu gyara dakin nashi,, Kowanne su da damuwa ya kwana yayinda taketa jiran taji shigowar sa gurinta Kamar yadda ya sama koda kuwa bazata bude mai ba har ta gashi bacci yayi gaba da ita musamman yadda kanta Ke mata ciwo ,, Hakan ta kasance da Khalil din wanda fushi yayi da ita sosai koda suka hadu da safe ko kallon inda take baiyi ba duk da hankalinsa na kanta yana kallon ta a fakaice harya gama yayi masu mommyn sai anjima,, Jikinta yayi sanyi ta shiga damuwa sosai amma haka ta daure ake aikin d'a ita na tarba su mommy hassada da Husain's kannen daddyn ,, bayadda mommyn batayi da itada taje ta kwanta amma taki,, Sai karfe uku da rabi ya shigo tareda bakin ba laifi yadan sake fuska saidai babu wani walwala har a lokacin yaki kallon inda take,, Da sauri ta karasa itama aka tarbesu da ita mommyn hassana da sauri ta janyo ta jikinta tana amsawa don ya Khalil dan gidan tane ya gaya mata komai game da maryam , Haka suka karasa cikin parlon aka gaggaisa saanan ta shiga kawo musu abunda aka tanadar musu na abinci ,,, Da dare misalin karfe takwas yayi knocking a bakin Kofar ta da sauri ta kike ta bude Kofar tunanin ta mommyn hassada ce amma saitayi ido hudu da ya Khalil ,, kauda kansa yayi gefe tareda mika mata wata katuwar bakar Leda ya juya da sauri tace ya Khalil ,, Chak ya tsaya batareda ya juyo ba ,,cikin sanyi murya ta furta kayi hakuri don Allah ,, Juyowa yayi tareda tsareta da idanu zuciyar sa na mai zafi yakasa manta yadda ya gansu da habib murmushi yake kawai yayi ya juya cikin sarsarfa ya wuta ta tsaye,,, Kusan minti biyu tana tsaye tana bin inda ya wuce da kallo kafin ta juya ta rufo kafarta bakin gado ta zauna tareda bude kafar wata duniyar shadda ce dark blue anyi mata dinkin doguwar riga gaba dayanta tasha aiki tun daga sama har kasa ba karamin kyau kayan yayi mata ba ,,ajiye tayi ta cigaba da duba sauran kayan takalmi ne da jaka kirar de Vinnieo masu matukar tsada sai mayafin dukkansu kalar milk color sai wani dan kit din dankunne da sarka mai dauke da agogon da zoben harda bangles shima kalar fari ,,ajiye wa tayi ta dauko turaren ta bude ta ciro ana taga yar guntuwar takarda ta fado da sauri ta dauka tareda budewa tasowa karantawa Kamar haka _kiyi amfani da wadannan gobe_ Maimaita wa ta shiga yi tana bin rubutun da kallon yadda yayi kyau shidai komai nasa ni kyau ne da tsari zame wa tayi ta kwanta tareda rungume takarda a kirjinta ahaka bacci yayi gaba da ita,,, Sai bakwai da rabi ta farka kai katse toilet ta yi wanka ta fito bata tsaya shafa ba doguwar rigar ta ta zura ta daura hijab dinta akai ta fice kasa a dining ta tadda sun kowa yana Karya wa,,cikin ladabi ta shiga gaidasu daya bayan dayan kafin taja kujerar ta zauna ta soma Karya wa ruwan tea kawai ta hada tasha,, saanan ta mike itama tawuce don shiryawa ,, *mrs noour ce*✍🏻 [7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… *Masoya ina muku fatan alkhairi Kamar yadda kukeyi min akoda yaushe,Allahu ya bar kauna,*🀲🏻 *one love ana mugun tare😘* πŸ…Ώβž–3⃣6⃣ Toilet ta fada ta shiga sulle ji kinta da mayuka da turare na wanka kamar zata chanza fata burinta dai ko tasamu ya huce daga fushin dayake yi da ita ta dauki kusan twenty five mins kafin ta daurayo cikinta ta fito daure da towel a jikinta daya kuma ta yafa bisa kanta don tsane gashin kanta,, Murmushi tayi ganin mommyn hassana sannu tayi mata tana karasawa gurin ta,,amsawa tayi itama fuskarta cike da fara'a tace wannan wanka da fatan dai kin chanza fata ko,, dariya tayi kasa kasa tana sunne kanta saboda kunya da alamun mommyn hassana ta dade a dakin tana jiranta,, kinga ni dan gidana ne ya tasoni wai saina shirya maike don haka na taho cikin hanzari kada na bata ran yallabai ta fadi tana karasawa kan mirrow ,, Dariya sukayi gaba daya saanan mommyn hassana ta fara fitoda kayan kwalliyar kala kala cikin make up kit dinta,, sosai ta shiga tsarawa maryam kwalliya sosai Kamar wata amarya sun dau kusan forty five mins ana abu daya harta da kayan ita taimaka wa maryam din ta saka su cikin tsari duk da kunyar da maryam din keji hakan bai hana mommyn hassana tsayawa ta gyarata ba,, masha Allah tabarakallahu ahsaanal khalikeen godiya ta tabbata ga wanda ya kera wannan halittar mommyn hassana ta fada bayan gama yiwa maryam dauri mai step wanda ya zauna mata das a kanta kwantaccen kashin gaban kanta ya kara fito da kyawun daurin dukda har lokacin da tabon ciwon a kanta ,, ita kanta godiya kawai takeyi ubangiji daya halliceta don ta firgita da irin mugun kyawun da tayi gyalen ta dauka ta yafa a kanta amma sai mommyn ta hana,amsa tayi ta nad'e shi saanan ta yafa mata shi akan kafadar ta,, haka suka jero har falon inda su mommyn Ke zaman jiran su masha Allah kowa ya dinga fadi haka suka fito har gurin motocin su suka shiga sai wurin party,, *misra* yau ummi ta tashi da matsanan cin faduwar gaba wanda yafi na kullum ta rasa mai yake yi mata dadi tana kokarin yin addua amma Kamar kara karfin bugun zuciyar ta akeyi,, kallon didde tayi dake Zaune bisa kujerar karatun littafin mai tsarki takeyi waigawa tayi gefen ga surajo ne Zaune yana latse latse a wayar sa mikewa tayi ta zauna saanan murya a sanyaye tace ni kuwa sirajo ya jikin alhaji ne,, saida ya waigo ya kalleta saanan yayi murmushi yace da sauki fa yana samun lafiya sosai yanzu,, shiru ne ya biyo baya na wasu dakiku kafin tace ni kuwa wlh kaga na gaji da zaman nan don Allah ka rakani in dubashi,, kafin ya bada amsa didde tayi maza tace Aa Sam babu inda zaki fita kema ki gama samun saukin tukunna ma,, shiru ummi kawai tayi takoma ta jinginar da bayanta da pillow,, Kwanan sa uku baisan wanda yake kansa ba sai yanzu ya fara motsa idanunsa da sauri matarsa ta mike ta danna wani abu minti kadan saiga likita tareda wata nurse sun shigo,, bayanin abunda tagani tayiwa likitan tana nuna masa hannuna daya motsa, karasawa likitan yayi ya yimasa gwaje gwaje kafin ya dago ya yi rubutun bisa file din marar lafiya saanan yace zai iya farkawa akowane lokaci,, godiya tayiwa doctor din suka fice maida kallonta tayi garesa hawaye na silalowa daga idanunta,tasaka bayan hannunta ta share tana adduar Allah ya baiwa mijinta lafiya,, Karar wayar hannunta ce ta katse ta daga tunanin datakeyi jiki a sanyaye ta daga baba taga ya bayyanar jikin fuskar wayar da sauri ta dauka tana karasa dauke hawayen dake zubo mata sallama tayi cikin wayar muryar a sanyaye,amsawa akayi nan ta duka Kamar yana gabanta ta shiga gaidashi yana amsawa cikin girma na dattijon mai girma,,saanan ya daura da tambayar ya maijikin da sauki ta bashi don harya fara motsa hannunsa ta bashi amsa,, hamdalla yayi saanan yace Allah ya kara lafiya ki cigaba dayi masa addua ba zubda hawaye ba Kamar wani mamaci,, gyada kanta tayi cikin girma mawa ta amsa da toh baba Insha Allahu, Allah ya kara girma,ameen ya amsa da kafin ya mika ma mahaifiyarta suka gaisa tareda tambayar maijikin,,,addua sosai mama tayi masa ita ma tana amsawa da ameen,,da sauri ta katse kiran ganin mijin nata yana motsa hannunsa sosai,, mikewa tayi ta matsa gab dashi bakinsa taga yana motsawa a hankali Kamar yana son furta wani abu kunnanta takara bisa bakinsa amma bata tsinci wata kalma guda daya dayake fadi ba ganin haka yasa ta shiga yi masa addua tana tofa masa bisa fuskar sa,, A hankali duhun dayake ganin cikin idanunsa yaye haske tangaraw ya gani kafin daga bisani ya hango shatun sa na Zaune tsakar gidan su fuskar ta babu walwala ta zuba tagumi yayinda maryam Ke tsugune chan gefe tana wanke kwanikan abinci itama fuskar tata chunkushe take da bakin ciki da rashin walwala,,shigowar yayi cikin gidan yana sallama,shiru babu wanda ya amsa mishi yana kokarin karasowa garesu ne inna ta fito daga dakinta hannunta dauke da wata sharbebiar wuka sai kyalli takeyi tana mikowa juyawa yayi yaga wa take mikawa saiyaga iliya ne cikin hanzari ya karaso ya amsa ya nufi maryam da wukar wacce bata dago kanta ta lura da abunda akeyi ba,, ganin haka yasa shi zabura zai karasa amma yaji kafarsa tayi masa nauyi bisa dole ya shiga kwala kiran maryam da iya kacin karfin sa wanda ya kasance a zahiri ma ihun kiran sunan maryam din yake yi amma idanuwansa a runtse suke da sauri likitoci suka shigo suka sake yimasa allura bacci mai karfi nan take ko seconds hudu bai kara ba bacci yayi gaba dashi,, *Abuja* manyan motocin su sune suka Parker a harabar company inda suka tadda dankara dankara motoci masu rai da tsada a wurin ,,mommyn hassana ce ta duba tana fadin kinga mommyn har mun kusa yin latti fa da alama wasu har sun riga mu,, Murmushi mommyn tayi tana kokarin bude murfin motar tace ai dole kuwa a riga mu tunda kun tsaya kyale kyale ba,, dariya sukayi gaba dayansu tareda saukowa cikin tafiyar ta ta natsuwa da Jan hankali take takawa saika rantse wata yar sarki ce ga kayan yadda sukayi matukar kar barta hannunta rike dana mommyn hassana suka shiga cikin dakin taron,, gaba daya idanu ya dawo Kansu musamman ga maryam wacce ta kasance yarinya a cikinsu mommyn ga kyau ga natsuwa da diri uwa uba hankali kanta a duke yake taki dagowa dukda yadda zuciyarta Ke bugawa yadda idanun sukai mata cha ba mazan ba bamatan ba,, masha Allah yaseer ya fadi yana dad'a kare mata kallo, tsaki ya Khalil ya ja tareda cigaba da duba takardun dake gaban shi a sanyaye ya furta aikai dama nan kafi kauri,,dogon tsakin da safina taja ne wacce Ke Zaune gefen sa yasashi dagowa da sauri sai yanzu zuciyar sa ta buga kasa dauke idanunsa yayi a kanta,, zungurin kafarda shi yaseer yayi cikin ba'a yace ya akayi ne wanda ba shida kauri yana dariya cikeda shakiyanci,, kauda kansa yayi amma gaba dayan hankalinsa da tunanin sa suna kanta harsuka karaso gurinsu suka zauna,sake dago idanuwansa yayi masu matukar kwarjini ya zuba mata su da sauri ta janye nata idon tareda sunkuyar da kanta kasa,, yaseer ne ya matso kusa da kunne sa yace gaskiya mutumina nima yau nayi kamu na sami tawa matar,, dukar da kansa yayi a dakile yace aikai yau har hudu ma zaka hada ana indai matane,, Allah kuwa serious mutumina na samu tawa matar kuma da alama yar gida zaayi don tareda su mommyn suka shigo wannan karon bazanyi sanya ba Insha Allah saina riga ka aure,, *kuyi hakuri da wannan abubuwan sun sani gaba pls*😍 *MRS NOOUR ce✍🏻* [7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… *~Dis chappee goes to u my dear sahiba, I fell de same Wy u feel,I reealy heart u dear,ina tayaki addua ako dayaushe,,Allah ka zaba mana mai kyau,,~*🀲🏻 *_Love u much besty_*😘 πŸ…Ώβž–3⃣7⃣ Murtuke fuska yayi tareda kauda kai yana kallon fuskarta wacce take duke tsura mata idanu yayi kaunarta da soyayyarta na karabin duk wani sako da lungu jinin da bargon jikin shi lura yayi da alamun tana cikin rashin walwala, kai kallonsa yayi ga mutanen dake dakin taron kusan gaba dayan mazan dake gurin idanuwansu na kanta harta da abokan daddyn sa ,, wani abu ya taso ya tokare masa a zuciya saboda kishi musamman ga habib wanda ya koma kujerar kusa da ita tunda yana cikin kujerun family ,sai yanzu yaga wautarsa a fili na barinta zuwa gurin nan domin maryam abun so da kauna da burgewa ce ga kowa yasan kayan data saka ya bada go dummawa wurin kara hasken kyawunta ,dukda ita din ta kasance mai kyauce koda kuwa towel ne ta daura jikinta,, Haka aka gaddamar da bude sabon company na ya Khalil na sarrafa fatu ana cikin garin Abuja,anci ansha hankali kwace taron daya hada kososhei na Nigeria amma wanda ake wannan budirin dominsa gaba daya hankalinsa a tashe yake alokacin da safina take nan nan dashi lada wata tayi mata kwace shikuwa gaba dayan hankalinsa naga maryam ganin yadda idanun mutane sukai mata cha duk ta kasa sakewa ga yaseer daya saka shi gaba da maganar ta,, Hangota yayi ta nufi Kofar fita da sauri yacewa su yaseer yana zuwa ya Mara mata baya sai dai kash saida yayi dana sanin zuwanta gurin domin kuwa yana fita ya Hangota wani abokin daddy ya tsaida ita,, nan da nan kishi ya turnuke zuciyar sa gaba dayan idanunsa suka chanza launi duk wani farin ciki dayake ciki ya gushe karasawa yayi inda suke baiyi wata wata ba ya damke hannunta da karfi batareda ya saurari maganar da abokin daddyn nasa yakeyi ba ya shiga janta saboda rashin saurin tafiyar ta,, Kai tsayi wurin motarsa ya nifa da ita ya saka dayan hannunsa ya bude murfin motar tareda turata gidan gaba mai maza munin banza ,zaga yawa yayi ya bude ya shiga ita dai binsa take kawai da kallon idanuwanta sun cika taf da hawaye kiris take jira ta fara yinsa saida ya dau kusan minti hudu kafin ya dago idanuwansa masu matukar kwarjini ya watsa mata wani kallo mai cike da sako wanda ita kadai tasan mai yake nufi da wannan kallon,, Kasa tayi da kansa hawayen dake makale a idanunta ya fada silalowa bisa kyakkyawan fuskarta ,hannunsa yasa ya dago fuskar ta tareda tsare ta da idanu runtse idanuwan ta tayi da karfi bata son kallon nan dayake yi mata kwayar idanuwansa sunyi mata nauyi a yau,, kusan minti biyu kafin a sanyaye yace kalli cikin idanuwansa hearttee ki duba kwayar idanuwanan ko Allah zaisa ki fahimci irin tsantsan kaunar danake yi miki hearttee pls sonki da kaunar ki yana neman sakin ciwon zuciya saboda kishin ki pls kije gida kawai saina dawo zan nemeki,, dagowa tayi da fuskarta tareda zuba masa idanu tai rau rau ta kwafe fuska cike da shagwaba tace pls ya Khalil ka barni don Allah nima zuciyata bazata iya samun nutsuwa na matukar bana ganin ka musamman yadda safi,, kasa karasawa tayi saboda kunya ta sadda kanta kasa kawai,, Murmushi yayi wanda yakara fito da tsantsar kyawunsa har saida dimple dinsa suka luba yaji dadin maganar ta at least yasan yanzu shima tana kishinsa tanajin kadan daga cikin abunda yakeji nagame da kishinsa,, bude mufin motar yayi ya fito zagayawa yayi gefenta ya budemata ta fito fuskarta a duke saboda kunyar maganar datayi kama hannunta yayi suka koma har saida suka shiga tayi maza ta zare hannunta daga nasa da sauri ya kara kama hannun nata ya nufi gurin su mommy lokacin anata daukan pics ne da gaggaisa wa da mutane mika hannunsa tayi ya kamo hannun mommyn hassana wacce take tafaman doka musu murmushi ganin yadda sukai matukar dacewa da juna,hada hannunsu yayi saanan ya rankwafo saitin kunnen mommyn hassana yace ga amanar yarki nan pls momy idanu sunyi hawan akanta kada asa wa danki ciwon zuciya ,duka takai mai a kafadar ya goce sunata dariya tace angama my son,,saanan ya wuce gurinsu yaseer,, duk abunnan daya faru bisa idanun daddyn da dad din safina akayi wanda hakan ba karamin bata ran daddyn yayi ba musamman ganin ga iyayen safinan da ita kanta safinar a wurin amma babu komai nasan yadda zan bulluwa abun ya fada a zuciyar shi,, sai kusan gab da magrib aka gama yayinda daddyn Ke neman ya Khalil don ya dauki safina ya kaita gida shikuwa yana chan tareda gimbiyar tasa sun koma gud ahankali kwace suna Zaune bisa kujerun dake cikin garden din gidan suna fitar su irinta Masoya hankali kwance,, Koda su daddyn suka iso dasu ya fara yozali lokacin ya Khalil ya rakota Kofar parlon suka kara tsaya wa har saida suka iso wurin saanan maryam tayi saurin juyawa da gudu ta nufi dakinta yayinda shikuma ya fuske ya shiga yi musu Sannun suna amsawa banda daddyn dayayi gaba rai bace mommyn tabi bayansa shi kuma yawuce gurin mommyns din nashi har daki suka shiga,, Kowa ya zauna kan kujerar cike da gajiya suka shiga fira sai alokacin mommyn husaina ta soma yi masa magna fuskarta tamke yanzu kai son Yaya yayi maka zabi na gidan girma da arziki ga safina wayayyar yarinya mai zakayi da wannan ana raba ka kana tusa kanka ga wacce ko takaimai mai asalinta baka sani ba ni wlh kwata kwata wannan maryam din bata yimin ba ,,ta karashe tana tabe baki,, da sauri mommy hassana tace Aa husaina bana son wannan maganar kema kin goyi bayan Yaya kenan ba Kya duba dabiun safina sunsha banban dana maryam a wajen tarbiya ko,, da sauri itama tace eh haka Kikace dai amma ba yadda zaki hada gata da asalin su ko gata tana da burin zama wata a wataran ita kuwa fa inayin ko secondary dinnan bata gama ba,, And kuma waye yace miki ina da bukatar mace wayayya mai ilimi ,,ya Khalil ya fada rai bace shima ya mike ya fice daga dakin ,,, wannan kuma matsalar kace batamu na wlh dole ka auri safina son ita ta dace dakai ba kwashe kwashe ba,, Allah ya shirye ki husaina kidai fara yi masa adduar zabina alkhairi shiya fimiki da wannan zancen daki keyi mommyn hassana ta fada itama rai bace ta mike tabi bayan Khalil,, Sosai daddyn yake yiwa mommyn fada a daki ta inda yake shiga batanan yake fita ba taya zan saka doka ko ketare kida shi magana ta ta zama ta banza yanzu tun saka ranar auren sa kin tsaya kin tambaye shi shin ko ya leka inda safina take eyeh toh wlh Ku shiga hankalin Ku ni bazan zama mutumin banza ba bana magana in chanza ta in kuka ga Baayi wannan auren ba to tabbas yarce ta fasa da kanta amma badai kuba wlh,, Kayi hakuri alhaji za'a gyaran yaran yanzu ne ka haifesu baka haifi halin su ba amma wlh tun ranar na bashi shawara hakura da maganar maryam,, Wannan kuma Ke kika jiyo abunda nakeson dake maza kije ki sameta ta shirya komai nata yau yazamana shine karshen kwanan ta cikin gidannnan gobe Insha Allah da kaina zan mikata gidan alhaji isma'il ii shidin ya maidata gidansu ko kuma chan din zata zauna duka de yasan yadda zayi da ita tunda aji yarta yabamu kuma tunda mun dawo sai a maidata inda ta fito zaman ta anan din ba shida wani amfani,,, Hakuri dai kawai mommy Ke bashi har ya gama ya fice, girgiza kai tayi tana sauke ajiyar zuciya jiki a sanyaye ta mike ta nufi dakin maryam,, Sallama tayi ta bude dakin ta shiga da sauri maryam ta juyo wacce Ke Zaune kan praying mat tace sannu mommy ,, Yawwa Sannun maryam ya gajiya da sauri maryam tace lahira mommy wace gajiya kuma tana murmushi,, Gyara zama mommyn tayi cikin hikima ta soma yiwa maryam magana a nutse toh maryam damuwa dai ta kusa kwarewa yanzun nan daddyn yake yimin zance maida Ke gurin iyayen ki nasan suma hankalinsu nanan a tashe saboda rashin ki ki shirya gobe zai kaiki gidan su safina in kika kwana biyu zanzo sai mu maida Ke gida,, sasai maryam tayi farin ciki saidai a wani bangaren zuciyarta na tuna mata wata kila shikenan ita da ya Khalil hawaye taji ya taro a idanunta da sauri ta shiga kokarin maidasu kada mommy ta gani,, Sallama tayi mata tace zata turo mata asabe ta taya ta hada kayan gyada kai tayi tana murmushi tace na gode mommy Allah ya saka da alhairi,ameen mommy ta amsa dashi ra yimata saida safe ta fice,, jagwab takoma ta zauna kirjinta na bugawa sai alokacin tasamu damar fitar da hawayen da sauri ta goge idanunta jin sallamar asabe ta mike suka shiga hada kayanta jikinta sanyaye,, *Kano* Ba karamin wuya inna da iliya suke sha ba inda mutanen gari suka dage da lallai saidai a yanke hannuwan iliya daga wuyan innan tunda anyi kwalliya sun gansu babu wani ragowar tausayi kuma da kyar da gudin goshin aka samu hannun ya fita saida malam ya hada da kiran wasu malami na kusan da kauye kam su tukunna,, Aikuwa dawa Allah ya hada samari suka rufar was iliya da dukan katon wuka da kyar maigari ya samu suka gyaleshi bayan sun yimasa lilis aka kori mutanen dake gidan haa daya aka rufo Kofar , Sosai maigari da malam sukayi musau fada da waazi da ayoyin da hadi sai wannan kadai ya ishemu ezna Allah ya shiryen sai Ku maida hankali gayin istigfari da neman gafarar wanda da kuka zalunta wadanda kuka kashe kuwa wannan sai a lahira kuma, Saidai inna Ke kuka ciki da nadamar take fadin as tag firullah wa atubu ilai ka tana neman yafeya ga yan gidan tana fadin Ku nemo minsu mero da shatu in nemi gafarar su koda na mutu bamu gamu ba kunema min gafarar su,, *mrs noour ce*✍🏻😘 [7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… *I alwaz pray 4u my dear Didi maman afrah😘,Allah ya tsareki ya kareki daga sharrin makiya da zuri'a ki baki daya,*🀲🏻 *Allah ya tsone idon makiya daga kankiπŸ‘ŠπŸΏ Allah ya barki da Mr abubakar dinki har gaban abada,*🀲🏻😍😍😍 πŸ…Ώβž–3⃣8⃣ Washe gari da safe karfe 8:dadai daddyn ya tasa maryam a mota har gidan su safina batareda sanin ya Khalil dasu hajiya ba da mommy kawai ta samu tayi sallama a tsaitsaye sai kuka take ita kanta mommy saida ta koka saboda

Chapter 17 of 32