Share this page
ci,, Suna gama ci yace wa mommyn bari mu amso miki sakon,, da sauri momy ta d'ago zata tambaye shi wane aike tayimai dazai karbo da sauri ya kashe mata Ido yana nuna mata daddyn,, murmushi tayi tace sai kun dawo muna bukatar drinks saboda baki, gyada kai yayi yace OK mommyn see u,,ya fice cikin farin ciki,, maryam ma sallama tayiwa mommyn sai sun dawo,, yana Zaune cikin mota yana kallonta yadda take tafiya cikin natsuwa sai ka dauka yanga take yi yadda take tafiya Kamar tana tsoron taka kasa,, harta zagayo ta zauna gefen shi sannu tamai tamaida kanta kasa ,, Wurare dayawa sukaje kafin daga baya suka wuce wurin shan ice cream suka zauna a kan fararen kujerun dake gurin ,, Suna sha yana dan janta da hira dukda bawani iyawa yayi ba shiyasa yafi gane ya fita da ita shan iska kawai,, duk yadda ya aro jarumta ya gayamata yana sonta kasawa yayi haka suka gama zaman su sukayi gida sai uban siyayyan dayayi mata tayi murnar sosai da kulawar dayake nuna mata wacce tarasa ko saboda meye itadai harga Allah sonsa da kaunarsa sun riga sun bi jinin jikinta intana tareda shi takan manta matsayin ta yadda yake nuna mata kulawa amma duk sanda ta tuna da safina sai taji duniyar tayi mata zafi tasan indai safina na raye bazata taba bari ta auri ya Khalil ba ,, ajiyar zuciya tayi tareda yin juyi ta kara rungume pillow Allah ka zaba min abunda yafi alkhairi gareni,, *share* *comments* *mrs noour ce*✍🏻😘 [7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… *_Allahumma salli ala Muhammad,,_* *_ " wa ala ahli Muhammad_* *_Kama sallayta ala abraheem,,_* *_ "Allahumma bharikh ala Muhammad,,_* *_Wa ala ahli Muhammad,,_* *_barakta ala ibraheem ,,*_ *_waala ahli ibraheem,,_* *_fill alamiyna innaka hameeydun majeeyd" (ameen)🀲🏻_* _______________________________ ~*Hapy Jumm"at Al Mubarak*~😘 _______________________________ πŸ…Ώβž–2⃣1⃣ a lokacin da maryam Ke daki tana tunanin khalil shima haka ta kasance gareshi lallai ya yarda so da kaunar maryam ya riga ya zama jinin jikin shi,tabbas ta kasance ita din ce farin cikin rayuwar shi,, murmushi yai ya daga hannuwan shi sama yana yiwa Allah godiya da kuma ya nuna mai ranar da zai mallake ta a matsayin matarshi ,, Lallai zai nuna mata gata zai ririta ta Kamar kwai lumshe idanun sa yayi tabbas yau yana cikin farin ciki da Allah ya amshi adduar sa ya hada shi da wacce ya Ke buri da kwadayin aure,, sai dai bazai taba gaya mata ba har sai ya tabbatar da ita din Wacece meye asalinta ,shin labarin data gaya musu gaskiya ne duk da wani sashi na zuciyar shi yana tabbatar mishi da hakan ne gaskiya,amma gaskiya ya zamar mai dole yayi bincike domin baya fatan yayi mata biyu a rayuwar shi,, haka suka kwana kowa da tunanin junansu,, Yayinda mommyn suke kwance a daki ita daddyn a kan gado itama dai tunanin take Allah yasa Khalil ya auri maryam hankalinta da natsuwar ta ga biyayya suna burge ta musamman yadda kyale kyalen duniya basu dameta ba wanda duka wadannan halayan su Khalil din Ke burin samu daga matar da zai aura,, tarasa dalilin dayasa take kaunarta tun sanda ta daura idonta a kanta jinta takeyi tamkar yar uwar ta tajini ,, Allah ka amsa min addua ta,, Washe gari da safe maryam bayan tayi sallah azkar ta cigaba dayi har saida gare ya fara haske tukunn ta miki ta shiga toilet,, wanka tayi ta fito mai kawai ta shafa tareda feshe jikin ta da turare masu sanyin kamshi,, drawer ta nufa ta ciro riga da wando masu matukar kyau rigar pink ce wacce take har gwiwa daga sama ta matse yayinda ta bude daga west dinta,sai wandon shima pink ne legens ta daura gashinta da ribom pink ta daura hula a kai baka ta fita zuwa kitchen don fara aikin tarbar baki,, kayan ciki ta dauko a fridge ta fara aikin shi tana yi tana tunanin Yaya gamuwar such da safina zai kasance yadda yanzu Khalil baya nuna kunyar ya nuna mata kulawa a gaban kowa,, Tayi nisa da aikin Momyn ta shigo ta sameta tana blending cittar daza suyi dinja karasowa tayi kusa da ita ta dafa kafarda ta tace sannu maryam harkin fara aikin,, da sauri ta durkusa har kasa ta gaidata tace eh mommyn babu abunda nakeyi ne kuma gashi kince da wuri zasu zo shiyasa na fara,, har cikin ranta taji dadi tace ai kin kyauta kuwa Allah yayi miki albarka Allah ya kara so da kauna a tsakanin Ku,, Kasa tai dakai cikin jin kunya don tagane nufin mommyn ita da Khalil kenan ameen ta amsa a zuciyar ta,, sai da suka kammala hada drinks din sannan mommyn tace maza maryam ki kira min Khalil yanzu yazo,, sai da gaban ta ya buga amma haka ta daure ta mike tace toh mommyn ta fita tayi bangaren sa,, ta dade tsaye ta kasa shiga domin ita bata taba shiga dakin saba gaba daya jikinta rawa yake duk ta daburce da kyar ta iya daga hannunta tareda runtse ido sai kace yau zata fara ganin shi knocking takai hannu zatayi shi kuma yana bude Kofar a hankali sai saukar hannunta yaji akan kirjinshi wani irin shock sukaji a ilahirin sassan jikin su murmushi yayi yayinda ita kuma da sauri da bude idanun ta ganinsa tayi tsaye gaban ta sanye yake cikin suit dark blue hannun sa dauke da briefcase dinsa da alama yayi shirin office kenan,, murmushi ne dauke akan fuskarsa mai kayatarwa wanda yake dad'a bayyanar da kyawunsa,, itama murmushi tayi tareda sune kai kasa a sanyaye tace ina kwana kafin ya amsa tai maza ta sake cewa dama mommyn Ke kiran ka da sauri ta juya zata bar gurin,, shima cikin sauri ya ruko hannun ta dole ta tsaya chak batareda ta juyo ba,, Kusan minti biyu yana kare mata kallo ta baya,ajiyar zuciya ya sauke ya karaso kusa da ita tareda matsa mata hannun da karfi,, Kara ta saki a hankali ta runtse idanunta cike da shagwaba tace yaya da zafi fa,, Kusa da ita ya tsaya Kamar zai hade musu jiki guri daya wanda har kowa yana jiyo saukar numfashin junan su, dai dai saitin kunnanta ya sunkuyo yace ki a karan kanki bazaki iya zuwa gaida ni ba why,, duk ta daburce jikinta sai rawa yake babu komai tace wanda maganar iya labbanta kawai tayi ta,, matsowa yai baya kadan ganin yadda duk jikinta Ke rawa ya daga kafada yace shikenan shiyasa nake son safina kinga kullum saita zo ta gaida ni har daki,yana gama fadar haka ya juya ya wuce,, da sauri ta waro idanu waje cikin razanar da maganar dayayi zuciyar ta tashiga bugu da karfi nana da nan taji hawaye na shirin zubo mata,, safina ,safina kuma mai yake nufi da hakan ko dai Santa yake yi itama da sauri ta shiga girgiza kai, kai ina ni nasan ni yakeso wani bangaren na zuciyarta ya gaya mata yayin da wani sashen na zuciyar ta yake tina mata da cewa har yanzu bai furta miki Kalmar so ba don yana baki kula da nuna damuwa bashi bane so,, hawaye taji yana bin fuskarta da sauri ta sa hannu ta goge idanunta ne suka sauka akan zoben daya saka mata a hannunta tana tuno ranar,, Da sauri ta goge hawayenta ta daidaita ganta sanan tabi bayan shi koda ta shiga yana kitchen tareda mommyn sai tayi zaman ta a parlon kawai cike da damuwa makomar ta idan ya kasance tausayin ta kawai yake ba sonta ba,, Minti kadan mommyn ta fito daga kitchen din yayinda shi kuma ya nufi dining donyin break fast ko kallon inda take baiyi ba ,, mommyn ce ta miko mata karan din maltina tace tasaka a fringe sannan tayi maza ta shirya su amso dinkunan su kafin ya wuce office ,daddy ya fita da driver , dayan kuma ta aike su siyayya da mai aiki,, Amsa tayi ta nufi sama ta jera ta fringe sanan ta shiga daki gyalen fari ta dauka kawai ta fito yafa shi tayi akanta kai tsaye waje ta nufa tana cewa mommyn sai sun dawo,, kai tsaya gurin motar sa ta nufa ta bude gidan gaba ta zauna tareda sunkuyar da kanta kasa tana wasa da zoben hannun ta,, tada motar yai suka bar gidan har suka isa babu wanda yayiwa dan uwansa magana kowanne su da tunanin dayake yi har suka isa,, bude motar yai batareda yayi mata magana ba itama ganin haka ta fito suka nufi shagon,daidai Kofar ya juyo cikin shakakkiyar muryar sa yace ki jira ana,, ya wuce cikin shagon,, shagon turawa ne kusan dukkansu don kuwa bawai sun iya dinkin hausawan bane iyakacin su riga da skirt ko doguwar riga shima kusan zuban na turawa suke dinka wa ,sai dai kawai dan dole kakai,, gaisawa sukai sanan ya amsa dun kunan ya biya kafin ya fito,, inda take tsaye ya karasa ya mika mat ledojin guda biyu ya sake miko mata kudi wanda ya ciro daga wallet dinsa dollas ne yace gashi kiyi amfani dasu ki koma gida inada ayyuka a office ,, ya wuce ya shige motar sa ya barta da baki bude,, bata gama mamaki ba taga ya data mota da sauri ta daga hannu ta daya sama kafin tai magana tuni ya bar wurin,, kusan minti goma tana tsaye Kamar gunki ta kasa koda motsa yatsan tane tana nan tsaye taga wata mota baka ta paker a gaban ta ajiyar zuciya ta sauke mai karfi Alhamdulillah ta furta a zuciyar ta don a tunanin ta Khalil ne ya dawo,, bude Kofar motar akai mutum biyu suka fito bakaken fata ne sanye suke da bakaken kaya fuskar su sanye da bakin eye glass suka tsaya gabanta fuskar su a murtuke babu alamun rahama da annuri,, kauda kai tayi gefe don ganin ba Khalil bane sai dai ganin mutanen nan gabanta ya shiga faduwa ta rasa dalili durkusa wa tayi ta dauki ledojin ta mike ta fara tafiya cikin sanyin jiki tana hawaye ,, ko taku biyar batayi ba taji anyi dauke ta chak ihun tayi da karfi tareda zubar da ledojin hannunta jitayi an rufe mata baki tareda saka ta cikin mota,, Wani bature ne daya fito daga shagon yaga abunda ya faru da gudu ya bi motar yana ihun su tsaya amma ina sun figi motar cikin bala'in gudu,, dole haka ya hakura ya dawo yana tunanin Wacece wannan su waye kuma,, Yana Parker motar sa a company dinsu ya fito kai tsaye office dinsa ya nuna duk kuwa da yadda yakeji gabansa na faduwa babu wanda yaiwa magana da kai kawai ya rinka amsa musu gaisuwa da akeyi mai,, sectarian shi ta bude mai kofa tareda kaimai briefcase dinsa ciki, babban office ne wanda ya hadu sosai kujerar ya ja ya zauna tareda bude file din dake gaban sa ya fara duba wa,, kusan minti goma yana kan page daya baya fahimtar komai dayake ciki gaba daya hankalinsa da tunanin sa suna ga maryam,, tunani ya fara a zuciyar shi ko takai gida yanzu kai maybe tana hanya kuma, in kuma ta kasa gane hanya fa da sauri ya girgiza kanshi yace haba zata gane mana kusan kullum muna fita tare,, mikewa yayi ya nufi fringe ya ciro ruwan roba mai sanye ya kafa kai ya fara sha,, saida yasha kusan rabi kafin ya rufe ya ajiye saman fringe din komawa yai yazauna tareda duban agogo ,, wayar sa ya dauka ya kira mommyn koda ta dauka kafin yayi magana tariga shi da tambayar kun amso kuwa ko basu gama bane,, girgiza kai yayi Kamar yana gabanta kafin yace mommyn mun amso bata dawo bane,, Da sauri mommyn tace Aa bata dawowa am sure tana hanya yanzu sai da nayi maka magana kace zata iya a barta ta saba gashi ka fara daga hankali tun yanzu ba,, da sauri ya ce mommyn ki kirani inta dawo ya katse wayar kwanciya yai kan kujerar gaba daya ya rasa natsuwar shi jiyake babu lafiya amma yana kokarin kwantar da hankalinshi akan babu komai ,, kusan minti talatin yana zube kowanne motsawar agogon a idon sa wayarsa ya dauka he's sure by now tana gida number mommyn yayi dialling,, bugu daya ta dauka don itama hankalin ta atashe yaki tunda ya kira ta,, muryar cike da damuwa yace hello mommyn ta dawo kuwa,, har yanzu dai shiru son ko bata samu taxi bane ta bashi amsa don hankalinsa ya kwanta ,, Katse kiran yayi ya mike da sauri ya zari keys dinsa dake kan table ya fice cikin sauri zuciyar shi tana tsananta bugu,, motar sa ya shiga ya tada ita a gujee ya nufi shagon lokacin daya isa zuciyanshi tayi wani irin bugawa da karfi sakamakon ganin mutanen dayayi sun dan taru a Kofar shagon ga motar yan sanda nan dafe kirjinta yayi yana karanto addua Allah yasa lafiya ba wani abune ya samu maryam ba,, cikin hanzari ya fito ya karasa wurin yana dube dube bata gurin,matsawa yayi gurin wani ya tambayar nan ake gaya mai abunda ya faru,, Watt ya fada da karfi tareda ruko wuyan rigar mutuncin cikin tashin hankali yace an dau keta Kamar yaya ,kuna kallo baku hana ba,, da sauri yan sanda suka karaso tareda rikeshi da kyar aka banbare hannun sa a wuyan mutimin yan sanda suna tambaya lafiya,, *kano* Wanka hajiya ladi tasa harira ta sukeyi ta bata wata doguwar riga ta saka wacce ta matse ta sosai,,kwalliya tasa hafsi tayi mata sanan ta bata wani magani a Kofi wanda aka dama dama da madara tace ta shanye duka,tana gamawa ta miko mata guran tsumi babba tace ki rike wannan ki rinka sha a hankali, amsa tayi tana godiya saanan suka fita motar dake Kofar gidan suka shiga guest house din alhaji a kaisu har cikin gidan motar ta Parker suka fito murna ce ta cika harira ganin girman gidan dazata zauna aiki a zuciyar ta tace lallai zan ci dadi yadda nakeso ,, hajiya ladi ce gaba suna biye da ita a baya har cikin parlon gidan security dinsa suka tarar a ciki,da sauri dayan yace su biyo shi saman benan suka hau harira sai zare ido take cikin kauyanci tana gyasa gidan a zuciyarta zama sukai kan kujerun dake parlon sanan security ya wuce wani daki minti kadan sai gashi ya dawo tareda alhaji wanda Ke sanye da jallabiya ajikinsa wanda tunbi ya cikata fam Kamar zata yage a jikinsa,,, Kirari hajiya ladi ta shiga yi mai yayinda yaketa dariya yana kare ma harira kyau lallai yau zai sha shaaninsa yarinya ce danya karama haka,, hannu ya mika tareda daukar check book dinsa dake kan stool ya rubutawa hajiya ladi check din kudi har miliyan daya domin ta chamchanci hakan yayi mata alkawari akan maryam kuma bai cikaba saboda batan ta shiyasa yai mata wannan kyautar don a wannan karon akwai abunda yake so ya aiwatar akan harira banda biyun bukatar sa da zaiyi da ita,, cike da murna ta amsa tana zuba godiya nan ta ja harira suka fita tace toh harira ranar wanka baa bayan Jibi kinga dai kyautar kudin dana samu naira miliyan daya saboda kayoki nan gidan,, zaro idanu harira tayi waje tace hajiya miloyan,,duka Ke kadai Jinjina kai hajiya ladi tayi tace kwarai kuwa don haka ki daure duk abunda aka saki kiyi kiyima alhaji biyayya zaki samu sama da miliyan a gurinshi bamda kayan sawa na kece raini Ke in takaita miki zai iya baki kyautar motar sabuwa dal a ledar ta,, Cikin murna da son abun duniya harira tace don Allah hajiya aikuwa kada ki damu komai zai sani zan yi mai motar ta kara jinjina maganar,,, Kafin hajiya ladi ta bata amsa hafsi ta fito tace hajiya alhaji nakiran ki,, da sauri hajiya ladi ta ce toh tareda wucewa ciki gurin alhaji waya ta tarar dashi yanayi cikin farin ciki,, Sai da yagama wayar kafin yace hajiya ladi lallai na kasance mai saa burina ya kusa cika kinsan kuwa su banga sun ga maryam a USA,, Zumbur hajiya ladi ta mike cikin dafe kirji baki na rawa tace da gaske alhaji,, Dariya yayi wacce ta kara fito mai da munin sa yace wlh hajiya yanzu haka tana gurinsu yanzu nayi musu transfer kudi a yau dinnan su dawo da ita Nigeria,, cikin murna hajiya ladi lallai alhaji kayi daidai lallai kai din mai *karfin IKO* ne lallai shegiyar yarinyar nan mai takeyi a garin har yanzu,, Kedai hajiya bari ai yarinyar nan saina wulakanta ta fiye da yadda kike tunani sauki daya zata samu gurina idan bata baiwa wani kanta ba amma in har ya kasance aka samu akasin haka lallai saina wulakantata abunda take gudu na lokaci kadan saita dawwama da yinsa har karshen rayuwar ta sanan in wulakan tata da iyayen ta gaba daya wannan alkawari naneπŸ‘Ί *Kaduna* Kamar yadda dad ya shirya hakan ta kasance karfe 7:00 suna airport domin zuwa us, tareda Habib wanda ya hade cikin kanann kayansa wanda sukai matukar yi masa kyau ,, ba laifi mommyn ta saki jiki da shi sai dai Kamar da ba,, Duk da saida tasa dad yayi mata alkawari da sun isa a yau ba sai gobe ba zai yi ma daddyn Khalil maganar auren su da safina,,, *share* *comments* _more comment more typing eyeeh_πŸ˜— *mrs noour ce*✍🏻😍😘 [7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… *gaisuwa da ban hakuri gareku Masoya na ina muku fatan alhairi a ko da yaushe,love u all*😍😘 πŸ…Ώβž–2⃣2⃣ Gudu suke zuba wa sosai a motar sun saka maryam tsakiya,wacce take a matukar tsorace jikin ta gaba daya rawa yake sakamakon dora mata bindiga da daya yayi a kai,, kai tsaye gidan da suke zaba suka kaita wani daki suka hankad'a ta ciki suka rufo Kofar har da key suka wuce,, a gujee ta kwasa gurin Kofar tana bubbuga wa tana rokon suda don Allah Ku taimaka min Ku fitar da ni anan su waye Ku ,mai zakuyi min kuka take sosai tana buga Kofar da iyakacin karfin ta dayake karfin mace ne ko motsi Kofar batayi gashi ta daina jin motsin su,, zame wa tai a wurin ta hada kai da Kofar kuka ta saki da iyakacin karfin ta why why Khalil mai nayi maka haka kayi sanadiyyan kawo ni nan marainiya ce ni mai nayi muku mai yasa ba kwa tausaya wa marayu ne eyeeh buga Kofar tayi da karfi tana tambayar mai yasa ne eyeeh mai nayi ne pls karku cuce ni ,Allah ni gata na bani da kowa,, mikewa tai tsaye da sauri saboda wani tunani daya fado mata kar dai yan yankan Kaine suka kawota nan fitsari taji yana bin jikinta gaba daya ya dauki rawa har hakoran ta Kamar mai zazzabi matsawa tai can lungu ta takure a kasa tana kuka kasa kasa saanan tana adduar Allah ya kubutar da ita a zuciyar ta,, Suna ajeta suka fara hada kaya mutum biyu zasu tafi da ita yayinda banga ya tafi cire kudin da alhaji ya turo musu,, Da kayar yan sanda suka cire hannun Khalil a wuyan shi suna tambayar waye shi mai ya faru,dagowa yai da niyyar magana yai ido biyu da ledojin daya bata a yashe akasa,, wani abu yaji ya taso mai ya soke zuciyar shi dafe kirjin shi yayi nan da nan jiri ya fara dibar shi fusge hannun sa yayi ya fara tafiya zuwa gurin ledojin tsugunawa yai ya bude ledar tabbas kayan su mommyn ne daya ba maryam hawaye yaji ya fin fuskarshi durkushe wa yai akasa ya kuka a hankali yana fadi meya sameki my mad girl,waye ya dauke ki ,meya sa nayi miki haka,, mikewa yai da sauri ya karasa gurin yan sanda ya rike hannuwan daya yace pls Ku taimaka Ku nemo ta batasan ko ina ba pls laifi nane wlh laifin nane,gani sukai yana kokarin zube wa a kasa da sauri suka ruko shi,, kai tsaye suka saka shi cikin motar su ta yan sanda yayinda daya ya shiga ya tuka cikin sauri suka nufi hospital dashi, dayan kuma motar sa ya nufa wacce tsabar rudewa ko murfin motar bai rufe ba, ciki ya shiga ya fara bincike a ciki anan ya samu ID dinsa ya dauka nan da nan dayake kasar waje ne suka gano information akan sa ,, number gidan suka buga na landline suka sanar da mommyn wacce itama a tsorace take dama don jiki ta ya bata babu lafiya,, sallati ta saki da karfi tana kuka da gudu ta haura sama ta dauko mayafin ta suka fice da driver wanda ya dawo daga kai daddyn office sai a motar ta sanar dashi,shima hankalin sa ba karamin tashi yayi ba yace gashinan zuwa yanzu,, *Kano* dariya hajiya ladi tayi tace kayi dai dai alhaji irin Ku akeso, lallai zata gane taurin kan data nuna babbar masifa ce akanta kuma alhaji ina mai tabbatar maka da ko mai kayi daita babu yadda zaayi dakai yoh wa take dashi inba wanna shegiyar kakar tata ba,, Wacce inta nemi daga mana hankali zaka sa a murje ta Kamar karamin kwado,, jinjina kai yayi yace wannan haka ne shiyasa nake son harka dake, yanzu dai turo min kanwar in fara gyagije tsufana da ita tukun ,, Mikewa tai tana dariya tace gaskiya kama nima daga chan zamu wuce da hafsi,, gargadi da Jan kunne ta kara yimai harira yayinda ita kuma ta tabbatar mata da kar taji komai zatayi duk abunda aka sata,,sannan ta wuce cike da murna lalli zanso in kara ganin maryam ta fada a ranta,, Komawa palon harira tayi bayanan duk da a tsorace take haka ta bishi cikin bed room dinsa wanda haka hajiya ladi tace tayi,jikinta ne ya fara rawa ganin alhaji datayi daga shi sai dan karamin kajeran wando,, tasaka yai ya nufo gurinta tareda kama hannun ta tanason kwacewa amma tana tuna maganar da hajiya ladi tayi mata binshi tayi har gaban wardrobe din dakin yasaka mukulle ya bude kudi ne tagani reras an jira su Kamar kayan sawa,, waro ido tayi waje ganin uban yawan kudin tace alhaji wannan kudin gaskine ,, dariya yayi cike da duniyanci yace Kwarai kuwa ya mika hannu ya ciro bandir daya na dubu daya ya mika mata yana kashe mata ido,, Mika hannu tayi ta amsa tana dudduba wa tabbas kudin gaskine lallai hajiya ladi batai Karya ba,ganin haka yasa alhaji ya rungume ta jikin shi yana shinshinar wuyan ta yace zaki samu duk abunda kike so na duniyan nan indai kika bani hadin kai,, gyada kai kawai saboda bakinta yayi mata nauyi jin yadda takejin wani abu na mata yawo a jikinta,, Duk da ihu da rokon datake mai haka ya biya bukatar shi da ita wanda ba karamin shan bakar azaba tayi ba amma haka yayi ta lallashin ta dacewa na yau ne zafin kawai gobe kila da kanta zata zo gurin shi haka ta daure wuni yayi yana abu daya babu imani balle tausayi yana ganin kudinsa yake mora,,yayinda ta kuwa harira kudin data gani kawai Ke gilma mata a idanun ta,, cike da farin ciki inna tayi sallama cikin dan karamin gidan nasu taji shiru har kusan sau hudu,,tabe baki tayi tace anyi na banza nidai ba yadda zakiyi dani don na lura kwanakin nan tsanar taki tayi Kamari,, tana kokarin bude kofa ummin ta fito tanatayi bango a sanyaye tace inna sannu da zuwa wlh bana jin dadi ne,, Ayya inna ta fada ai na dauka ma mugun halin naki ne ya motsa,,ta fada tareda shigewar ta daki don yau ita cikin farin ciki take harira tayi dace kila ma ta samu miji a can,, Sannu inna maganar ummi ta katse mata tunanin data keyi,, Yawwa ta amsa a dakile tana kauda kai,, itama ummin kauda kai gefe tayi gefe domin ita ma yau ashirye take da komai zai faru sai dai ya faru amma dole su fito mata da yarta,, a sanyaye tace inna wai kuwa kin taba gaisawa da maryam a wayar tun bayan tafiyar ta Kamar yadda kika fada,, Cike da matukar mamaki inna ta juyo tana ma ummin wani irin duba don maganar tazo mata a bazata bata taba tunanin ummi zata iya mata maganar ba,, sallati ta saki da karfi tana tafa hannu nan da nan sai ga hawaye cike da bacin rai tafara magana matar baba lamarin naki har ya kai ga haka

Chapter 10 of 32