Share this page
mike tareda rufe shi da bargo ta fito zuciyarta cike da tunani iri iri,, wannan wane irin tashi hankali ne kwana daya dubi yarona yadda ya koma lallai ya zama dole inyi wani abu addu'oe ta topa mishi kafin ta fito ,, a harabar gidan ta ci karo da safina tana ta zuba wa driver ruwan tijara yabata keys din mota zata fita,shi kuma ya hana saboda masu gidan basu bashi umarni ba musamman yadda ta dage a motar ya Khalil zata fita,, dakata wa mommyn tayi tareda kiran sunan ta rai bace,, Yi tayi Kamar bata ji kiran ba tana harare harare ta cigaba da abunda takeyi,, danne zuciyar ta tasake yin kiranta safinaah da d'an daga murya,,saida taja tsaki kafin ta karaso tana cin magani ita adole fushi take da mommyn,, fada tayi mata sosai kafin tace drive ya bata keys din ta wuce cikin gidan ranta matukar bace irin wannan yarinyar daddyn zai hada Khalil dinta aure da ina sam wlh bazai yuwuba ada tana ganin daga tafiyar shiya fi amma dole gobe Khalil ya daure su koma nja inyaso duk abunda zai faru sai dai ya faru,, Washe gari da asubahi bayan idar da sallar maryam bata zauna ba wanka tayi ta shirya saanan ta sauka kasa kitchen ta nufa ta daura musu abun Karya wa ma'aikatan nataya ta zuciyar ta cike da tunanin da shaukin ganin ya Khalil ko Yaya yake ohoo ita dai addua ta Allah ya bashi lafiya saidasuka kammala saanan ta umarce su dasu shirya kan dinning sama ta haura toilet din ta sake komawa ta kara yin wani wanka ta fito,, doguwar riga light yellow ta dauko mai Shege kyau ta saka ta yafa mayafin jikinta ta nufi mudubi mai kawai ta shafa tarda fesa turare ta koma ta kasa a lokacin kowa ya hallara a dining tun fitowarta idanun habib Ke kanta ya kasa dauke idanun sa har ta karaso cikin tafiyar ta tanutsuwa ta gaida kowa kafin taja kujerar ta zauna ruwan tea kawai ta sha ta mike ganin haka yasa mommyn cewa don Allah maryam ki shiryawa yayanki breakfast ki kai masa,, kirjinta ne ya fara bugawa cikn sauri da kai kawai ta amsa ta nufi kitchen din ta shiryamai akan babban tray ta bi ta Kofar baya ta fice,, cike da tsoro ta tura Kofar bakin ta dauke da sallama ta shiga har kana table ta ajiye yana Zaune parlon ya jingina bayansa da kujerar idanunsa a lumshe suke tamkar mai bacci,, a hankali ya bude idanuwansa ya ware su a kanta da sauri ta janye idanunta kasa tana wasa da flower dake gefen rigar ta murna na rawa ta furta ina kwana ya Khalil ya jikin,, Lumshe idanuwansa yayi kawai batareda ya amsa ba sai yanzu yaji wani irin sanyi a cikin zuciyar shi rashin jin muryar ta kawai ya nifa shi halin dayake ciki taya daddyn zai iya tunanin rabuwar su mike wa yayi a hankali duk da jikin shi babu karfi ya karaso inda take,, hannunsa yasa ya kama nata hannun ya zauna da ita tareda ci gaba da kallon idanun ta itama idanun ta zuba masa ya rame sosai wani irin soyayyar sa taji tana bin duk wata jijiya da bargo na jikinta da sauri ta kauda kanta gefe tareda mikewa ta nufi kan table din tea ta soma hada mishi tana tunanin cikin zuciyarta anya kuwa zata iya rabuwa da soyayyar ya Khalil cikin zuciyarta Kamar yadda ta kudurta,anya kuwa bazata fada cikin gararin dayafi wanda take ciki ba muddin ta rabu dashi amma ya zatayi dole ta daure tayi hakan koda kuwa zata rasa ranta ne da sauri ta dauke hawayen daya fitowa daga idanunta don kada ya gani,, cup din ta mika masa ya amsa tareda hannun ta wani irin yamma taji har cikin jininta da suri ta janye hannun ta ta wuce plate ta duka ta zuba masa farfesun hanta datayi masa wanda yasha kayan hadi sai zuba kamshi yake ta dawo ta dire gabansa da sauri ta juya ta nufi Kofar fita,,, maryam ya fada in husky voice dins sai da jikinta ya amsa baki daya ya Allah ta futa tana danne kirjinta why ya Khalil ka barni haka in fara koyawa kaina hakurin rashin ka mai yasa kake kokarin sake harkar min da soyayyar ka ta fada cikin zuciyar ta,, lumshe idanunta tayi saboda kamshin turaren sa takeji Kamar a cikin jikinta ya Ke hannunsa ya daura bisa kafadunta ya juyar da ita tana fuskantar sa ,, maiyasa zaki wuce maiyasa bakya tausayi na rashin jin muryar ki kawai ya jefa ni a wannan halin amma kike kokarin tafiya batareda mun kema wa kanmu mafita ba ,, janye hannuwansa tayi daga kafadarta ta matsa kadan cikin sanyin murya ta fara magana wannan shine daidai abunda nayi mai zamuyi ya Khalil ,mai mukeda ikon yi bayan yin biyayya ga iyayen mu muyi hakuri kawai da juna ya Khalil,... d sauri ya daura yatsan sa bisa labbanta murya a shake yace pls maryam duk abunda zamuyi muyi shi amma banda rabuwa bazan iya ba kanki na fara yiwa wata'ya mace murmushi, kanki na fara sanin meye so bana jin zuciyata zata iya rabuwa dake,,,, sallamar mommyn ce ta katse shi da sauri maryam ta janye jikinta gefe cike da kunya tana yiwa mommyn sannu ta wuce ta fita,,karasowa mommyn tayi tana fadin a da alama son yasamu magani mai kyau ya sarki ta fada cikin wasa tana dariya kasa kasa,, komawa yayi ya dauki cup din ya fara sha cikin natsuwa sunagasawa da mommyn,,, *Kano* Da sauri baffa yace Aa shatu godiya zaayi wa ubangiji daya kaddara haduwar mu muna raye fadin labarin bayan rabuwa kuwa sai an nutsu tukunna,, Surajo yace Hakane baffa yanzu zanje gurin likita kawai a shirya fitar dasu kasa mai tsarki kawai baffa inaga hakan zaifi,, Jinjina kai baffa yayi yace wannan ma gaskiya ne maza kaje nima nayi wannan tunanin,,mikewa yayi ya fice anan ummi take gaya musu suwaye malam garba da halima da irin taimako da sukayi mata ,,godiya sosai sukayi musu aka cigaba da hira batareda ummin ta fada musu b'atan yarta ba,, cikin kankani lokaci surajo ya gama komai ya shirya musu tafiyar gobe da yamma shima saboda ummi ne tunda bata da passport dayaso suyi asubanci such tafi ,, waya yaringa yiwa dangin yana sanar musu anga Yaya shatu wadanda da dama sai a lokacin suke tunowa dawata shatu kowa yayi murna harda wadanda basu Santa ba wadanda aka Haifa daga baya,,, ganin halin da inna take kara shiga yasa aka tura garzali kiran iliya baban harira wanda yabi alhaji sun fita da mai gari don Alhajin yayi masa alkawarin zai saya masa wata katuwar gona saanan shima babban danta ya tafi gurin malam ya fada masa halin da mahaifiyar su take ciki hankali tashe suka taho da malam din ,, duk da yake baban malami ne amma hankalinsa ba karamin tashi yayi ba da sauri ya fito yace yana zuwa dole zaije ya kawo magani tukunna,, a cikin gonar garbati ya samu iliya ya zaiyane masa halin daake cike game da inna wani irin kulle wa yaji cikinsa yayi hankalinsa yayi kololuwar tashi bai tsaya angama ba dole zuka taho a motar alhaji suka nufo gida shikenan tamu ta kare yake fadi a zuciyar sa,, magani wanda yasha kayan hadi na musulunci da addu'oe shi malam ya ringa watsa wa inna jikinta saanan ya bata tasha wani irin kara ta saki da karfi kafin ta suma da sauri malam ya fito ya cire gyallen daya rufe hancinsa don kuwa kwarin na neman kumbura mai nasa cikin saida ya huta saanan ya koma tareda iliya wanda ya shigo yanzu maganin malam ya kara watsa mata jikinta ya kwara mata a fuska don kuwa yakasa saka hannunsa ,, Ajiyar zuciya inna tayi kafin ta bide idanu Allah yasa ta daina kumburi saidai ruwan har yanzu yana bulbula a jikinta na tuba malam nabi Allah inna ta fada tana kuka na cuce kanwata na cuce shatu da yarta Ku yafe min na cutar daku,, da sauri iliya yace inna don Allah kiyi shiru haka har ki samu lafiya ya fadi zuciyarsa cike da tsoro kada inna ta fadi abunda suka aikata bayan mummunan gargadin da boka yayi musu,,, *Mrs noour ceโœ๐Ÿป๐Ÿ˜˜* [7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *๐Ÿด๐ŸดKARFIN IKO๐Ÿด๐Ÿด* ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited by๐Ÿ‘‰๐Ÿป *oum Zahara*๐Ÿ˜ Dedicated 2my lil sis๐Ÿ‘‰๐Ÿป *Maman Sultan*๐Ÿ˜˜ ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู… ๐Ÿ…ฟโž–3โƒฃ2โƒฃ Da sauri inna ta katse shi tana kuka cike da tashin hankali take fadin Ku nemo min shatu da mero innemi yafiyar su kafin na mutu kasan kuwa halin danake ciki iliya ta karasa tana tsare shi da idanu,, iliya ya fara hassala da maganganun inna bacin tasan yin hakan ba karamin mummunan tashin hankali bane garesu baki daya,, a hassale yace inna don girman Allah kiyi shiru asamu acigaba da maganin nan don Allah Ke kinfi kowa sanin abunda zai biyu baya in kika furta wani abu,,, Kuka ta fashe dashi cike da tashin hankali da nadamar abunda ta aikata,,subhanallahi malam ya fada a raunane ya shiga bata baki da kyar aka samu tayi shiru sai dai hawaye dake bin fuskar ta,,, magungunan ta malam ya hada tareda yi ma iliya bayanin yadda zaayi amfani dasu kafin ya mike tareda yi musu Allah kyauta ya wuce,, Sosai inna Ke jin jiki tayi nadamar abunda ta aikata dubi irin halin data jefa kanta ciki batada magana banda ta neman gafarar ummi amma iliya ya hana Sam datayi zancen sai ya tsorata ta akan cewa bala'in dazasu fuskanta sai yafi wannan don haka gwara ta shiru a cigaba da magani ,dole take hakura,, Shi kanshi abun yafara damun shi gashi koya kira wayar yarsa bata shiga balle ta alhaji,, Kulawa sosai ummin Ke samu daga yan uwanta tamkar kwai haka suke ririta ta,,washe gari da yamma karfe shida jirgin su ya daga zuwa kasa mai tsarki Makkah tul munawwara ,, Wanda yayi daidai da saukar su maryam garin abuja ,, wani irin farin ciki takeji tamkar anyi mata bishara da aljanna batada wani buri face naganin ummin ta haka ma safina zuciyar ta cike da zumudin ta dawo karshen zaman maryam cikin su ya kare dad'in dad'awa kuma za'a sa musu rana da ya Khalil,, Motar su safina suka shiga dad yaso tafiya da ita amma mommyn ta roki ya barta suyi sallama da ita zata kawo ta,,tank God safina ta fada tana watsa mata harara ta wuce cikin motar don bazata taba iya hada hanya da ita ba a cikin gidansu ba,,, itama maryam din tayi farin cikin jin hakan dukda ta alkawartawa ranta komai za'ayi mata na lokaci kadan ne zata danne,, motarsu suka hau suka wuce main family house dinsu wato gidan iyayen daddyn kenan,,, kankararren gida ne wanda saida ya tsorata maryam dama a nja mu akwai irin gidajen nan bude baki kawai tayi tana kallo tundaga gate har suka isa harabar ajiye motoci,,,saanan suka fito tareda nufar cikin gidan,,, Sunsha tarba ta arziki daga mutanen gidan Kamar yadda suka saba musamman wannan zuwan daakayi da ya Khalil wanda ya kasance mafi soyuwa ga ahalin yan gidan alhaji hamidu da hajiya Fatima tsofafin yan boko komai nasu a waye akeyinsa ,, Sai da suka ci suka sha kafin hajiya ta tambayi mommyn ko itace maryam din,, eh ta amsa tareda gyada kai,, Lallai masha Allah shine ki kuma dan karanbani daga ganin jar fata zaki manne masa to Sam bazai yuwuba halilu sai rikita inba ni ba ,,ta fada cikin wasa da raha ,,dariya sukai gaba dayan su maryam dukar da kanta tayi ,yayinda shi kuma yai biris Kamar baya dakin,, mommyn ma dariya tayi tace ai hajiya maryam ta fishi zama kalar turai ai saidai ya nuna mata miskilanci kawai,, nan ma dariyar sukai gaba daya su ganin yadda ya kara hade girar sama da kasa yana basar wa,, ai yannan ki rufa ma kanki asiri ki nemi wani mijin amma banda wannan miskilin kafi mahaukaci ban haushi,,,dariya sosai sukeyi maryam harda rike ciki shi kuwa shanyanyun idanunsa ya zuba mata inama zata dawwama cikin wannan farin cikin tare da shi dayafi kowa murna a duniya,,, mikewa yayi kawai batareda ya nuna yasan hirar da sukeyi ba,, sai bayan fitar sa mommyn ta samu ta zayyanewa hajiya halin daake ciki gameda auren da daddyn zai hada na Khalil da safina,,, jinjina kai hajiya tayi ranta bace tace haba wannan ma bamai yuwuba bane yaron har yana neman hallaka kansa amma shi ya rufe idanu yace lallai sai ita to wlh Sam bazaiyuba zasu dawo zasu tadda ni wlh dole abar yaron ya zabi matar da zai zauna da ita ehee๐Ÿ˜Ž Mommyn taji dadi sosai sai yanzu hankalinta ya fara kwanciya tasan hajiya indai har tasaka baki tofa Dole daddyn yabi umarninta,,, nan sukayi ta hira kafin kiran sallar isha'i kowa ya mike ya nufi dakinsa,, malam ne Zaune tareda dad da kanin shi sai daddyn da abokanasa guda biyu suna magana akan aure su safina,, harga Allah malam Sam baiyi wani naam da zancen ba Bawai sunada wani aibu bane jikar sa yake ji safina zama da ita ba kowa ba bayason abunda kaje ya dawo amma ba yadda ya iya dole aka yanke sadaki naira dubu Dari suka casks musu harda dorin naira dubu Dari biyar na gaisuwa aka tsaida wata biyu masu zuwa,,, saanan malam ya rufe taro da addua suka mike kowa cike da farin ciki nan su daddyn suka kama hanya don dare ya farayi duk da dama a jirgin zasu koma,,, duk yadda ya Khalil yaso haduwa da maryam taki ,gashi wayar ma taki kunna ta ,,saanan ta rufe kofa da key har ya gaji da zagaye ya dawo guriisu hajiya ya zauna dariya hajiya ta bushe mai dashi itada mommyn don suna lura da yadda yakeyi gashi sai wani hura hanci yakeyi yana bata rai ,, Kara tamke fuska yayi yace Ke wlh grandmaa in guji haduwar mu dake bana son saka ido ehee,, dariya suka sakeyi kafin tayi magana suka tsinkayo muryar daddyn yana sallama gaba daya suka amsa mai ya shigo shida alhaji fuskar su cike da fara'a kana ganinsu kasan suna cikin farin ciki,,, Tun kafin su zauna alhaji ya fara fadin toh hajiya Ke an kasa ki sai kiyi hakuri don yace ki yimai tsofa,yayi maganar cikin raha,,, itama cikin wasa tace ina Sam ai da tsohuwar Zuma ake magani ai zaka dade baka samu macen mai wayewar irin tawa ba,,, dariya sukai sosai wannan karon harda Khalil yace wah ni aini shiyasa na ajiye ki a gefe don gudun zuga ni matata bazata taba ci gaba da karatu ba gwara dai yar kauyen,,, nan ma dariyar sukai saanan daddyn ya tura wa hajiya kwalin sweet yace gashi nana nanda wata biyu an tsaida rana,,,, nan take ya Khalil yaji wani abu ya tokare masa a zuciyarsa sallati ya saki yana addu'oe kardai daddyn safina yake nufi inna lillahi wainna ilaihir raji'un abunda yake maimaita wa kenan yayinda mutuwar Zaune kawai tayi tana duban ya Khalil din wanda idanunsa Ke lumshe amma uwa daban ce tana hango tashin hankalin dayake ciki da kyar ta samu zuciyarta ta fara karanto mata Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun,,, Hajiya kuwa cikin mamaki take tambaye daddyn wace ce ne yarinyar ice ko maryam ce ,,,, da sauri shima daddyn yace a ah Sam wannan yar wajen ii ce nawa safina yarsa,,,, Aa yau naji aikin banza hajiya ta fada rai bace yanzu har kayi girman da zaka yanke hukuncin aure batareda izinin mu toh wlh Sam wannan maganar bamai yuwuba ce Sam zuciyata batayi naam da wannan maganar ba,,, hakuri ya shiga bata alhaji ma yasaka baki yana fadin addua yakamata ayiwa abun ba tashin hankali ba tunda magana ta kare an rigada an shigar da maganar gun manya kuma da izini na ya tafi tunda yaran suna so ai shikenan,,,, Tsalle tayi sosai ta rungume mom tana fadin am so happy mom burina ya kusa cika ,,da sauri mom tace yama cika zaki ce,,Hakane kam mom dama kinga maganar karatu ne sai gashi zanyi aure a us gaskiya mommyn ina cikin farin ciki sosai, ai hajiya kareema tayi kokari tabbas maganar malam ta tabbatar dole ki shirya kije ki gaida ta kinga duk wannan abun ta dalilin ta ya faru da saidai muga wancan shigeyar na wadaka cikin daular arziki ,, tabe baki tayi tace kinsan Allah mom har naji wani abu ya tsaya min araina dakika tunomin da wannan useless girl din na tsaneta mom gashi kin bari sun tafi tareda su,, Dariya mom tayi tace ai aikin gama ya gama saidai tabi wani kwararon wutsiyar rakumi tayiwa kasa nisa,, Hakane ne kam mom shiyasa nake sonki ,,, Ummi sunyi saukar dare sosai tunda munada tazarar awa biyu tsakanin mu amma dayake kasance taci gaba motar daukar marasa lafiya tana nan tana jiran su babu bata lokaci akayi asibiti dasu,,, Tun a daren aka fara musu gwaje gwaje da duba lafiyar su kusan kwana aakayi abu daya ,, Ummi kam hawan jini ne sai zuciyarta dake barazanar kamowa da ciwo amma alhaji anyi duk wani gwaji daya kamata amma baaga abunda Ke damunsa,,, *mrs noour ceโœ๐Ÿป๐Ÿ˜˜* [7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *๐Ÿด๐ŸดKARFIN IKO๐Ÿด๐Ÿด* ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited by๐Ÿ‘‰๐Ÿป *oum Zahara*๐Ÿ˜ Dedicated 2my lil sis๐Ÿ‘‰๐Ÿป *Maman Sultan*๐Ÿ˜˜ ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู… ๐Ÿ…ฟโž–3โƒฃ3โƒฃ mommyn ce zaune bisa gefen gado ta rungumo maryam ta gefen ta magana take mata cikin sanyi da kawantar da murya hade da lallashi,, ba karami tashin hankali maryam ta shiga ba dajin saka ranar auren ya Khalil,hawaye ne ya fara zirarowa daga fararen idanunta zuciyarta tayi mata daci sosai jitayi duniyar gaba daya ta fita ranta wani irin zafi da radadi takeji a kirjinta na kishinsa ,,shikenan ashe burinsu bazai cika ba,, da sauri mommyn ta shiga share mata hawayen cikin sigar lallashi ta suma bata baki abunda nake so dake maryam shine hakuri da addua a kullum nake baku shawara akan Ku maida hankali gayi kada ki sawa ranki in har wannan auren ya tabbata wai don asalinki ne Aa ki daukea a kaddara ce kawai kuma inhar kedin matarsa ce toh ina mai tabbatar miki da sai kin aure shi,,, da sauri ta shiga girgiza kai cikin muryar kuka tace mommyn na gode da kulawar ki amma wlh ba haka bane kawai ummi na nakeson ganin,, murmushi mommyn tayi wanda iyakacin sa lebba ta don tasan abunda yake damun ta amma bazata takura ta ba ita tayi alkawarin yi musu addua akoyaushe ,,,ajiyar zuciya tayi kafin tace shikenan babu komai ummi Ke dai kin kusa zuwa wurinta amma dole kiyi hakuri ki kara kwanaki don inason ganin wannan ummin nema ta karashe tana murmushi,, Sunkuyar da kanta kasa tayi mommyn ai zaki ganta harki gaji itama nasan zata so ganin ki,,, Hakane Allah ya rufa mana asiri Allah ya kaimu da rai da lafiya,,ameen maryam ta amsa sannan mommyn ta mike don kwanciya,, fitarta keda wuya wani marayan kuka ya kufce ma maryam tayi kuka har saida taji kanta ya fara mata ciwo saanan ta mike a lokacin kusan biyu na dare alwalar ta daure ta fara jero nafilfilu har kusan asubahi kafin ta jigina bayanta da makeken bed din dake dakin hawayen dai ya cigaba da zirya daga idanuwan yana diga a hijab dinta,,, a kullum sake jin haushin kanta takeji data biyewa zuciyarta ta afka cikin soyayyar wanda tasan ko a mafarki yafi karfin ta ,,maiyasa bata raba kanta dashiba tunda safina ta nuna soyayyar ta gareshi?kuka ta fashe da shi sosai daga hannuwanta sama tayi tana kuka take fadin ya Allah kayi mun zabe na alkhairi ,Allah ka cire mun son ya Khalil cikin zuciyata,, tana nan Zaune hae r aka kira sallah sannan ta mike ta gabatar da sallarta,,, Kai tsaye dakin hajiya ya Khalil ya nufa bayan dawowar su daga masallaci wanda yake jikin gidan samun hajiya yayi tana sallar dole ya kwanta kan kujerar dake dakinta,,alqur'an ya dauka ya shiga karantawa,, Saida ta idar tayi azkar dinta kafin ta jiyo da fuskarta ga kallon sa tana murmushi take fadin ango ka tashi lafiya,,, bai kulata ba saida yakai karshen ayan saanan ya rufe ya maida bayansa ya kwanta kan kujerar tareda lumshe idanunsa,, tabe baki tayi tace in iskancin miskilanci naka ne ya motsa toh wlh tun wuri ka tashi ka kama kanka yawwa ,,, Sake gyara kwanciyar sa yayi batareda yace mata komai ba,,ganin haka yasa taja tsaki tana nade praying mat tace haka dai zakaje kanayiwa yar mutane wannan halin Kaine zaka sha wuya ni kaga tafiyata gun mijina,,, Murmushi yayi wanda saida kyawawan fararen hakwaran sa suka bayyana mikewa yayi Zaune yana jijjiga kai tamkar mai jin tsoron magana yace lallai tsohuwar nan dama Ke har gurin miji kike zuwa yayi daidai,,, ehhe maizai hana da raina da lafiya ta auren soyayya ai baya tsufana ko injiku yan zamani balle mu,,, gimtse fuska yayi a dakile yace Hakane kam wannan ashe kunsan da hakan kuke shirin yimin auren dole ko very gud ,,yana gama fadar haka ya koma ya kwanta tareda lumshe idanunsa,,, nan take tausayin jikan nata ya kamata takowa tayi a sannu zuwa inda yake ta daga kansa daga kan kujerar ta zauna saanan ta maida kansa kan cinyar ta ta soma shafa sumar kansa wacce take kwance luf Kamar kan jarirai , saida taga ya sauke ajiyar zuciya saanan. ta fara magana a nutse tace abunda nakeson dakai Khalil hakuri ne kawai mahaifinka yana kaunar ka bazai taba yin abunda zai cutar da kaina ni kaina naso daukar mataki amma dole na hakura sakamakon rashin jin maganar da wuri,, Sanin kankane bazanyi abunda zai zubar da mutuncin muba duba da yadda mahaifinka sun rigada sun shigar da maganar ka,,kayi hakuri indai rabon ka ce zaka aureta ko bajima ko badade,, ka dai dage da addua Kamar yadda mahaifiyar ka ta umarceka sai kaga abun yazo da sauki,,, bude idanunsa yayi kadan saanan ya motsa baki a hankali yace ameen amma hajiya I can't live without her yana gama fadin haka ya mike ya fice Kofar dakinta ya tsaya ya murd'a jinta yayi a kulle,knocking ya shigayi a hankali sarai maryam tana jinshi amma tayi biris dashi duk kuwa da yadda zuciyarta ta d'okantu da son ganinsa da jin muryar sa tarigada tayiwa kanta alkawarin hakura dashi bazata taba bari su sake haduwa ba har ta koma gurin ummin ta,, don kansa daya gaji dole ya wuci sahensa zuciyarsa a dagule ya rasa yazaai bulluwa wannan abun batareda hadin kanta ba, *after one week* Ya habib ne sanye da dakkakiyar hy shadda getzner coffee color wancen tayi matukar dacewa dashi turare ya dauko ya feshe jikin shi dashi kana ganinsa kasan yana cikin farin cikin bana wani abu ba kuwa saina dokantuwa da son ganin maryam,, Tunda yaji labarin auren ya Khalil da safina ya sama ransa naima auren ta sai inda karfin shi ya kare babu gudu ba ja dabaya Insha Allah saiya mallaketa a matsayin mata a yau dinna zai gabatar mata da irin tarin kaunar dayake yi mata,, Ya Khalil ne ya tunkaro da motar sa cikin gida yana shiga ya fito tareda mikawa driver key din motar kai tsaye cikin gidan ya nufa so yake ya tarke maryam yau kimanin sati daya kenan rabon daya sanya ta a kwayar idanunsa,, aikuwa cikin ikon Allah yana shiga ya tadda ita Zaune a farlon ta zubawa makekiyar tv dake jikin bango idanu kai saika rantse kallon take sabanin haka ita ta tafi ga duniyar tunanin ya KKhalil,da sanun ta fara jiyo kamshin turaren sa ya mamaye parlon da sauri ta waigo tana duban inda ta Ke jiyo kamshin ido hudu sukai dashi yana tsaye ya kafe ta da idanunsa masu rikitarwa tsintar kanta tayi da kura masa idanun itama sanye yake cikin navy blue din suit wadanda sukai matukar dacewa da kirarsa said dai ya dan rame dayin duhu ,,, janye idanunta tayi don tunawa da yanzu ya zama Khalil din safina ba nata ba hawaye ya taro cikin idanuwanta da dauri tayi kasa da kanta tana kokarin maida su,, takowa yayi har kujerar datake zune gefen ta yanema ya zauna batareda ya dauke idanunsa daga kallon taba sanye take cikin shiga atampa pink mai ratsin yellow dinkin riga da skirt wanda sukai bala'in amsar ta ta daura dankawlin saman kanta kyau yaga tayi masa sosai fiye da a baya sai dai rama datayi ,, Ajiyar zuciya ya sauki a

Chapter 15 of 32