Share this page
mahaifinta na raye nan take bacci yayi gaba da ita,, Koda mommyn taji shiru bayanta tabiyo amma saita tarad da ita tana bacci Karasawa ciki tayi ta rufeta da mayafi saida tayi Jimm na yan sakwanni tana kallonta cikeda da tausayawa da kauna kafin ta tofa mata addua ta futo karo mata kofar tayi kawai,, Sosai maryam take bacci ta hankali kwance batareda wata fargaba ba,, koda dad ya koma gida mom tana nan tana zuba balai musamman data ganshi ya dawo shi kadai nan hankalinta yasake tashi sosai da kyar yan uwanta suka lallasheta saboda mutane ta shirya lokaci na kurewa,, Itama uwar gayya sake jiki tayi ta zauna aka shiga shiryata kamar wata sarauniya jifa jifa tanayin kwafa ko murmushi kamar wata tababbiya ita kadai tasan plan din data shirya zata basu mamakin sunan safina kawai sukeji basu San ainahin wacece itaba da abunda zata iya aikatawa ba,, Har daki ta samu dad ta bashi hakuri akan abunda tayi masa da Wanda mom tayi,, ai kuwa bakaramin far in ciki yayi ba India yayi ta yi mata nasiha wacce Ke jiga ta kunne hagu tana fita ta dama kafin daga bisani ta tambayi dad din kudi zatayi shirin walimar ta gobe,, dayake yana cikin farin ciki nan take ya tura mata five million account dinta yace suyi duk abunda ya dace inbai isaba tayi masa magana zai kara mata basai ta tambayi ya Khalil ba,, godiya tayi masa tareda rungume shi cikin tsantsar farin ciki kafin tace dad bari inje mu cigaba da shiri,, Yawwa baby jeki Allah yayi miki albarka,, Ameen dad ta amsa ta fice tana fita daga sashen ta doka tsalle tareda fadin makarantar babu fadhi indai aka daura auren babu yadda zaiyi dani kuma tunda saura kwana biyu nasan ko bananan zasu daura inna dawo ayi tarewar,, da gudu ta fada dakin nata Wanda yake cike da kawayenta ana ta shirin zuwa mother s days signa tayi musu da ido tareda yi musu tubs alamun tasamu nasara shewa gaba dayansu sukayi suna tafawa meena haba yanzu naji yar gari da taya zaace kin fimu kokarin da son karatu ace saboda wani namiji ki hakura haba aini wallahi ban dauka ko a mafarkin zaki hakura ba wallahi,,yanzu zai tantance tsakanin ki da wannan jahilar,, Frowning safina tayi da ido kanta na Dada girma tace sosai ma kuwa dama ita kanta tasan bazata taba iya had a kanta dani ba koda wasa koda ban cigaba da karatu ba narigada nayi mata nisa,,, Cikin bacci taji kamar ana mata Susa a fuskar ta hannu ta sa tasosa gurin takara juyawa ta Gyara kwanciyar ta amma saitaji ana hura mata iska cikin nauyin bacci ta bude shanyayyun idanuwanta wadanda bacci yaci karfinsu,,ganisa tayi kusa da ita ya rankwafo fuskar sa daidai tata har tana iya jiyo saukar numfashinsa akan fuskar ta ,, Zumbur ta mirgina gefe tareda Jan blanket ta rufe kirjinta kwabe fuskar tayi kamar zatayi kuka a shagwabe tace kai Yaya mai yasa kake yimin haka,, Kura mata idanunsa yayi wadanda suke kara rikitar da ita dajin kwarjinin sa janye idanun ta tayi tana turo baki hade da gunguni,, Murmushi yayi ya Allah ka mallaka min yarinyar nan soyaya zai iya zama barazana ga rayuwa ta yayi maganar cikin zuciyar sa amma a zahiri sai ya mike tareda Gyara tsayuwa ya kauda kansa saanan yace kowa yana chan shirin zuwa mothers day dimu amma Ke kina nan kina bacci alamun u don't care for u,, Ba karamin bugu maganar tayi mata ba Wanda ya sanya idanunsa suka fara tara ruwa alamun kuka take shirin yi lalai ma wannan tana nan dare da rana kullum cikin bakin ciki da rashin walwala shine zai gaya mata haka zaka game kuwa,, Itama cikin dakiyatace mai zaihana Yaya Bayan zamu hadu da ya yaseer ya roke ni alfarman haka ai dole ma inje kodon mu hadu,, duk iya yadda yaso ya daure ya shanye maganar kasawa yayi Wanda bansan lokacin daya sanya hanninsa ya bugi bakinta taba,dukda ba wani karfi ya sanya ba amma taji zugi har cikin ranta nan take ta sanya kuka Wanda na shagwaba ne kawai ta na bubbuga kafa kan gadon Bayan tarike bakin nata,, Warning yakeson yi mata amma yalasa gabadaya saiya shagala da kallon ta yadda takeyi kamar wata yar yarinya abun ya burgeshi girgiza kai yayi kawai ya fice dagadakin,, Dariya tashiga yi kasa kasa tace zaka gane ai da ka dauka zan kyaleka in baki yasan abunda zai fada baisan maizaa mayar masa ba ,, Itama mikewa tayi ta sauka kasa falo gidan ya fara cika da baki da alamu yan iwan mommyn ne suka iso Karasawa tayi suka gaggaisa kowa sai Binta yakeyida kallo sani amma basu saunta ba nan ta shiga kitchen suka karasa hadawa baki abinci suka shirya shi bisa manayan trays suka dauko har parlon ta ajiye sai sannu sukeyi mata mommyn kuwa fada take ta yi mata data zauna ta huta itada babu lafiya amma ina taki zama ,, Sai laasar sannan kowa ya shirya don tafiya kowa ya hade cikin kure adaka da shiga ta alfarma kowa yayi wa maryam magana ganin bata shirya ba saitace zata taho daga Bayan mommyn ma bata takura mata ba don ko itace babu indazataje,, Ganin kowa ya watse ya sanya ta yin kwanciyar ta akan gado ta na nazari da tunanin gwagwarmayar rayuwa data sha a Bayan Wanda take fata Allah ya sanya tasamu farin ciki itama Wanda zai dore,, Kamshin turaren sa tajiyo da sauri ta waigo da kallon ta ga kofa tsaye yake kamar koyaushe yayi folding hannayensa bisa kirjinsa yana kallon ta fuskar nan tashi murtuk babu annuri,, Kauda kanta tayi gefe saboda wata kibiyar kishi dataji ta soki kirjinta sanye yake cikin shiga ta alfarma wani danyen bvoile yard ne milk color jikinsa kaidaga Kasan ba karamin kudi aka kashe gurin dinkin sa ba yasha hularsa kusan kalan aikin dake jikin bvoil din haka akayi mata design dinta hannun sa sanye da agogo silver yayi matukar haduwa kaida ganinsa kaga ango sosai yayi kyau,, Murmushi yayi Wanda iyakacinsa labbansa ya sauke folding din dayayi ya duka ya dauki Babar ledar daya shigo da ita ya shiga ciki,, zama yayi gefen gadon yana kallon fuskqrta yadda ta hade rai tamakar zataci babu abin saiya bashi dariya Wanda saida ya dara kadan aikuwa kara kuluwa tayi don juyowar ta tayi daidai da sanda yake dariyar nan take sai hawaye,, Mikewa yayi tareda ajiye mata ledar bisa gado tareda wata farar takarda yace zan wuce saina dawo kiyi min fatan alhairi,, Kara kauda kanta tayi don bataso ya fuskance tana zunda hawaye domin shi murya na rawa tace adawo lafiya,, Shima batareda nuna damuwa ba a zahiri yace yauwaaa hearrteee saina dawo yasa kai ya fice daga dakin batareda yasake kallon inda take ba,, Tashi tayi da gudu ta rufe kofar ta tareda sanya mata lock ta fashe da kuka Karasawa tayi gurin kayan daya ajiye mata tayi watsi dasu akasa batareda ta duba maiye aciki ba sida taci kukanta ta koshi sannan bacci ya dauke ta batareda ta shirya ba,, Sosai aka kawata hall din kowa ka gani cikin farin ciki yake sosai amarya tasha kyau ta hade cikin shigar wani rantsantsan cordless milk da heard brown tareda takalmi da pos duka brown tasha kwalliya da Gyara sosai gurin ya kayatar abunka da abin masu naira manyan mutane kama daga maza da mata dayan mata da samari saikaxe wani reception ya dauka mothers day din yan uwa ne kawai su mom suka tara saiyaga sabanin haka,, Angabatar da komai cikin tsari amarya sai wani cika takeyi da iyaye ita adole tasamu miji Wanda yakerewa saa sai shisshige masa takeyi yayinda shikuwa yaci magani ko murmushi sai in sun hada ido da mommyn sa tayi masa isharada idanu saanan yakeyi ,, Ana soma cin abinci ya zare kansa ya fice batareda ya sallami kowa ba domin ransa ya fara baci yadda yaseer yake damunsa da maganar maryam ita kuma safina na biye masa ,,, Cikin bacci taji alamun knocking da sauri ta mike dukda jikinta a sanyaye yake ta bude kofar yar aikin ce tareda wata mata ta basu hanya suka shiga ciki saida ta shiga toilet ta wanko fuskarta da bakinta saanan ta fitowani irin sanyin jiki tareda faduwar gaba yake damunta dukda a zatonta ko bacci datayi ne bayan laasar gashi har magrib ta kusa,, Zama tayi suka gaisa saann tace oga ne ya turo ta ta shirya ta,, Jimmy tayi tana tunanin wane oga kuma ganin haka ya sanya matar cewa oga khalil,, Lafiya zaa shirya ni take tamvaye a ranta sai a lokacin ta tuna da kayan daya ajiye mata mikewa tayi ta dauko ledar dayar tkarda daya ajiye mata,, Saida ta zauna saann ta warware takarda rubutu ne bawani maiyawa ba cikin tsari da kyautar tamakar Wanda yarubuta ta soma karantawa kamar haka,, *_salam haeartteee zuciyata da ruhi hade da jini da bargon jikina bazasu tava zamtowa masu amfanarwa ba inba taredake ba,,don Allah ki daure ki kiyaye kishi na da tarwatsa zuciya ta,,ki shirya domin zuwa namu dinner,_* _love u husby_ ba karamin farin ciki takarda tasanya taba gaba daya saitaji bata jin wata damuwa sosai take murmushi kamar wacce akayiwa bishara,, Nan take mai makeups tajiga aikinta cikin mintuna ashirin ta gama gyare mata fuskarta ta taimaka mata ta sanya kayan kalar bvoil yard dinsa saidai nata kamar coffee color ne sarka da takalimi da pos hade da bongules duka golden color ne harda heard din ba karamin haduwa tayi ba tamkar wata amarya,, Suna gamawa mai makeup din ta kira wayar sa ta shaida masa sun gama shriyawa saiyace ta fito da ita yana mota yana jira,, dohu ya fara yi sosai donma Allah yasa tana fashin sallar sai hasken many an fitilun dake harabar gidan tunda suka fito yake tasbihi da godiya ga ubangiji yana kara adduar Allah yaji kansa ya amsa masa adduar sa na mallaka r maryam din,, Kasa boye farin ciki sa yayi Wanda key din mortar ya mikowa mai makeup din yace ya bata kyauta kuma ta shirya zuwa ya musu na biki,, Aikuwa godiya ta dinga yi musu tareda adduoe Allah ya ciki musu burin su,,har saida taga bacewar su,, Ran mom da safina yayi matukar baci na tafiyar Khalil batareda angama ba Wato duk wahalar wankan magani datakeyi abanza kenan ko,, Haka aka tashi ransu bace donma ganin mommyn nansa ya sanya su yin shiru basu tanka ba,, *mrs noour*✍🏻😘 [7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… πŸ…Ώβž–4⃣7⃣ Tunda suka dauki hanya kanta na kasa tana wasa da zuben dayasanya mata yayinda shi kuma gaba dayan hankalin sa nagareta idanuwansa basa gajiya da kallonsa jinta yakeyi tamkar ya hade ta da jikin sa ,, Wani babban hotel suka shiga Wanda tundaga wajen gurin kawai ya isa mutum kallo musamman yadda aka kawata shi da manyan fitilu kowacce zagaye da flower wadanda Ke fidda wuta kala daban daban,, Harabar parking ya ajiye mortar saanan ya fito ya zagayo barayin datake ya bude mata tareda kama tsintsiyar hannu ta,ta fito binsa kawai takeyi cikeda mamakin ganin sunan ta da nashi anyi rubutu alamu engagement day,, Ai tsurewa tayi dasuka shiga ciki babu kowa a gurin sai manyan tables guda biyar daya a tsakiya hudun kuma suna zagaye dana tsakiya ankawata su da launin kwalliya iri daban daban,, Sai dai kwalliyar na tsakitan yafi kawatuwa Wanda yake dauke da kujeru biyu,, Karasawa yayi da ita kan kujerar ya zaunar da ita sai ga hasken ya mamaye dakin na katuwar TV nan take pics din su da nashi daban da nata daban da Wanda sukayi tare ya shiga bayyana ga waka dake tashi mai tausasa zuciyar masoya,, Ba karamin farin ciki da nishadi suka tsunci Kansu ciki ba drinks ne suka sha Wanda shi ya ringa bata abaki sai engagement ring daya gabatar mata Wanda itama batareda bata lokaci ko tunanin badakalar safina ba ta amshi tareda alkawarin duk wuya tana tare dashi ,, Pics sosai aka daukesu Wanda musamman ya yi order daga babban studio sai gurin 10pm suka bar wurin shikeda nishadi da walwala,kowanne su jiyake tamkar an daura musu auren ne yau,, Koda suka iso gida yan mother s day duk sun dawo nan take kirjinta ya shiga bugu saboda tsoro ita har ga Allah tama manta da wani maganar auren ya Khalil yanzu in aka tambaye ta mai zata fadawa mutane,, Gashi kirjinta sai tsananta bugu yakeyi Wanda tarasa daliln faruwar hakan Bayan tasan tana cikin farin ciki,, Murmushi yayi tareda kashe mata ido daya alamun tamabayar lafiya,, Kasa tayi da kanta tareda girgiza kanta tana maida masa martanin murmushi kasa kasa,, Kashe motar yayi ya fito ya zagayo bangarenta ya bude mata hannun ta dai ya sake kamawa dukda cike take da tsoro amma vazata iya yimasa musu ba bayan gidan ya nufa da ita cike da mamaki tajata tsaya tana zuba masa shanyanyyun idanunta masu magadisu acikinsu,, Pls ya Khalil inajin bacci ta fada a shagwabe kamar zatayi kuka,, Shima idanun ya kafe ta dasu murya cikin rada yace ai kokarin danake yi kenan wannan is my responsible from now on yana gama fadar haka yasake rike hannun ta cikin dakinshi suka nufa,, Nan take jikinta ya fara rawa maiyasa zai kawota dakinsa at dis time eleven ta kusa ga mamakin ta sai taga ya bi da ita ta baya matakala asuka hau saiga wata kofa ya bude ga mamakin ta saigata a corridor din dazai sadata da dakinta,, Sai a lokacin taji hankalinta ya kwanta wato dabara yayi mata kar wani ya ganta Allah sarki ya khalil,, har kofar daki ya rakata yayi mata saida safe Wanda ta juya zata wuce da sauri ya manna mata gudniyte kiss a gefen fuskarta ya wuce,, Ta Dade tsaye a gurin cike da mamakin da tsananin shaukinsa sosia ayau ya kara martabar soyayyar sa cikin zuciyar ta sha fa gurin tayi tana lumshe idanu ,I love u so much ya Khalil ta furta tana murmushi hade da rufe fuskar ta ,dakinta ta shige tareda yin jifa da heard din dake kanta ta fada gado ta Dade tana tunanin abubuwan da ya Khalil yau yayi mata inama yasa anyi musu video coverage,, Sai gurin sha biyu na dare ta daure ta tashi ta cire kayan tareda zura jallabiya ta fada toilet ta watso ruwa tareda dauro alwala ta fito sosai ta nutsu tara da kaskantar da kanta zuwa ga mahaliccin ta tayi nafil filu da addueo sosai sai da ta gabatar da sallah asuba tayi azkar dinta saanan ta haye gado ta kwata ,, Haka yakasance da ya Khalil shima yakai kusan daya na dare ya na juye da tunanin ta kafin ya mike shima ya jiga jero nasa nafil filun da adduoe,, Sai takwas saura na safe ta bude idanun ta toilet ta fada tago wanka ta fito drawer ta wuce kai tsaye ta dauko wani swiss less marar nauyi ruwan sararin samaniya mai kwalliyar baki zare ta sanya dinkin riga da zani ne single rigar tree quarter gown ce kayan sunyi matukar yi mata kyau gaban mudubi ta isa ta shafe jikinta da mai saanan ta feshe jikinta da turaren mai kamshi ko powder bata sanya ba sai dan lip balm data sanya kadan a labban ta ta fice cikin sauri,, tunda ta fito kirjinta ke bugawa da karfi tarasa daloli gaba daya karfin jikin datake ji saiya koma mata sanyi a haka ta karasa kitchen din ta gaida mommyn da sauran yan aikin nan ta shiga tayasu aikin har aka kammala suka shirya shi bisa tafkekiyar darduma wacce yawanci hakan sukeyi indai sunada baki dawuya ne ka ga sun zauna a dining,, Sannu mommyn tayiwa maryam tace maza ta shirya tazo siyi break fast ga kuma baki sunzo da dare jiya su gaisa,, amsawa tayi da toh mommyn harta wuce sai mommyn ta dakatar da ita Wanda ya sanyata dawowa tace gani mommyn,, Dafa kafadar ta sanan tace yau muna da Fulani day komai naki yana ready karfe daya na rana zamu fara saboda suna da dinner anjima da dare Wanda ita safinar ta shirya,, gyada kai tayi tace toh mommyn babu komai na gode Allah ya kara girma da budi,, Ameen mommyn ta amsa cikeda jin dadin adduar maryam din gareta ,, Juyawa tayi jiki sanyaye tana shirin hawa step ta tsinkayi wata murya tana fadin kai yaya shine baki taso niba na taimaka miki,, Da sauri ta waigo da kallon ta ga matar wacce take sanye da babban hijab har kasa bataga fuskar ta ba tabata baya wannan muryar tayi mata iri daya data ummin ta kanta daure ta wuce saman cike da son ganin wace mata ce wannan mai irin muryar ummin ta ,, Haka ta sake yin wanka jiki ta snyaye ga faduwar gabanta daya tsanan ta kayan ta tamaida saboda tasan aiki Fulani day zasu gabatar Bayan sun gama kari saidai hula ta sanya fara a kanta taajiye dankwalin kayan ta fito,, tun kafin ta karaso take jiyo hirarrrakin su na yan uwa ga kamshij turaren ya Khalil datake jiyo sa tun daga India take saida ta karanta adduoe kafin tayi shahada ta kara parlon sallama tayi cikin siririyar murya ta Wanda ba kowanne tajiyo abunda take fadin ba,, Zama tayi daga gefe ta daga murya sosai ta shiga gaidasu gaba daya aka jiyo gareta don amsa mata,, Murtsuke idanu ummi takeyi cikeda tsananin mamaki maryam ce bake gani kokuwa idanu nane keyi min gizo,, A matukar razane ta dago sukayi ido hudu da ummin ta gabadaya nan take ta rude murya na rawa tace ummi ,ummina kece ko kuwa idanu nane nan take sai hawaye ya shiga silalowa tamakar an bude fampo gayda kai kawai ummi keyi alamun tabbas itace din,, da gudu maryam ta mike taje ta fada jikinta tareda fashewa da matsanan cin kuka rungume ta sosai ummi tayi tana fadin maryam Ashe kina kusa dani shiyasa tun jiya Dana shigo garin nan kitjina ke tsanan ta buga min,, Itadai kuka kawai takeyi tana murmushi ga ummi ta kamkameta kam a jikinta tana fadin ummi na Ashe zan sake ganin ki ummi nayi kewar ki ummi karki sake bari na nikadai ummi da kadaicin ki,, Kowa kallon su yakeyi harda su daddyn dasuka shigo a lokacin cikeda tasananin mamakin faruwar hakan yayinda ya Khalil har da dan hawayen sa jiyake yafi kowa farin cike dama mommyn shatu mahaifiyar maryam ce wacce ta kasance yarinya ce ga kanin baban mommyn,, Ummi maiyasa kika barni cikin maraici maiyasa kika bar makiya sulkaci galalbar rabamu muna tsaka da tsananin jin radadin rashin mahaifina,, Saboda fuskar ta UMMI tayi tace komai kaddara ne maryam haka rabbin samawati ya kaddaro mana amma rashin mahaifi maryam bakiyi shiba Allah ta bayyanar mana dashi a lokacin da bamuda ikon ganinsa saida yardar sa ga mahaifin kichan maryam tashi keje gareshi yaji dumin jikin ki,, Kallon ummi takeyi baki bude cikeda mamaki ko wani Abu yasamu ummin natane taya zata ce abban ta yana raye Bayan sun San ya dade darasuwa,, ganin haka ya sanya mommyn kamata ta mike da ita ta kara har gabansu da daddyn da abban ta mika hannun ta gareshi,, Murna ne shock ne far in ciki ne gaba daya suka dirar mata lokaci daya Wanda yayi sanadiyyan duke numfashi ta nan take tatafi luuu zata fadi,, Hearrtttee ya Khalil ya furta da karfi tareda daka wani mugun tsalle ya tare ta,ta fada bisa jikin sa,, *muyi hakuri banida chaji naso yafi yaka amma Allah ya kaimu gobe lafiya* *Mrs noour*✍🏻😘 [7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… *Kai gaskiya nayi matukar farinciki da comments din jiya, masu Gyara na gode sosai tabbas nasan kuna biye dani cikin wannan novel,,Allah ya bar kauna*🀲🏻😘😘😘 *kuyi hakuri hakan ya faru ne da cutting din wani gurin danayi tun a page 45 nayi kokarin gyarawa amma saida aka samu matsala,, kuyi hakuri da kuskuren,*πŸ‘πŸ» *mrs noour Hausa novels kuna ina ne banji gyaran kuba lafiya*😭😭😭 πŸ…Ώβž–4⃣8⃣ Gaba daya ya rude sai jijjiga ta yakeyi ga riketa gam jikinsa ya hana kowa karbar ta sai maganganu yake zubuwa akan ta tashi karta bari wani Abu yasameta zai iya rasa ranshi shima harda hawayen sa,, Wata cikin yan uwan mommyn ce ta Ke kokarin duba maryam saboda maaikaciyar asibiti ce amma ya Khalil yaki bada dama,, Sai ma sungumar ta dayayi yana kokarin wuce su daddyn zai kaita hospital,, tsawa daddyn ya daka masa ganin abun nasa babu nutsuwa ciki,, Chak ya tsaya batareda ya juyo ba muryar sa a raunane yace daddyn kayi hakuri muje asibiti kawai bazan iya samun nutsuwar jiran doctor ba,yana gama fadar haka ya fice daga parlon kai tsaye mortar sa ya shigar da ita Wanda tuni mommyn hassana tayi saurin yin gaba ta bude masa ya kwantar da ita a baya,, Da sauri ya zagaya ya shige itama ta shiga suka tafi,, Dole daddyn ya dauko motar suka shiga da abba da ummin da mommyn suka ni Bayan su kowa hankali tashe musamman ummin wacce take ganin kamar murna zata koma ciki,, gudu yake sosai gaba daya rabin hanakalinn sa naga maryam addua kuwa babu irin wacce bai karanta taba donma mommyn hassana tana ta kokarin kwantar masa da hankalin, har suka isa asibiti,, Saida ya karasa da mortar sa har main entrance din asibitin batareda duba parking ba ya kasheta ya sungumeta suka yi cikin asibitin,, ganin yadda yakeyi ne yasa nan da nan doctors da nurses suka amshe tasuka fara bata taimakon cikin kware wa,, Basufi minti goma ba suka fito kowa yana sharce gumi ya Khalil na ganin su babu kunyar su daddyn wandanda karasowa su kenan,,yabi likita da tamabayar Yaya take hope tana lafiya babu abunda yasameta ko,, Murmushi doctor din tayi tareda dafa kafadar ya Khalil cikin muryar lallashi yace calm down my friend babu wani Abu dayake damunta zaka ita zuwa ka ganta ai baijira ya karasa maganar ba ya wuce shi da sauri kamar zai hada da gudu ya nufi dakin,, Girgiza kai kawai daddyn yayi cike da takaici kafin ya mika ma likita hannu sukayi musabaha bayani yayi musu akan babu wani abu daya sameta daman hakan yakan faru wasu lokacin bakin ciki wasu lokacin farin ciki sunyimata duk abunda yakamata tana bacci zuwa anjima zasu iya tafiya da ita saidai tana bukatar hutu sosai ,, Godiya suka yi doctor din kafin suka rufawa Khalil Bayan zaune yake bisa kijera Wanda ya matso da ita dap da gadonsa yana kallon ta cike da so da kauna ina ma ace tana matsayin matarsa lalai dataga gata da tattali fiye da kowacce ya mace a duniya,, dariya mommyn hassana tayi tace kaga dan gidana ko ka manta ba safina bace irin wannan rudewa haka,, Dariya akai gaba daya dakin,, Shikuwa saiya sha mur ya tamke fuskar sa sai yanzu ya tuna fa da abunda yayi Allah ya kada ya zamo sanadiyyan barin gidan maryam din kodayake banida damuwa tunda sis ditace dad has not da rights ya rabamu kuma yanzu,, ganin jikin nata da suki ya sanya su mommyn komawa saboda baki aka bar ummi da mommyn hassana sai gogan Wanda yaki yadda su hada ido da daddyn kwata kwata don karma yayi masa zancen lafiya,, Sai karfe biyu na rana tafara bude idanun ta a hankali harta ware su gaba daya akan ya Khalil sukai ido hudu da sauri ya matso da fuskar sa kuda da ita cike da kulawa yake yimata sannu,,rintse idanun ta tayi saboda kunyar su ummi ta gyada kai kawai,, Doctor aka kira ya kara duba ta ya basu sallama tareda jandada Hutu gareta,,ummi ta dagota ta rungumeta jikinta har mortar su,, ya Khalil yana gama da sauri ya bude musu bayan motarsuka zauna shikuma ya zagaya suka shiga gaba da mommyn hassana suka nufi gida,, Tun kafin su isa suke ganin manyan motoci Jere a layin saboda mommyn suna bukatar space cikin gidan don haka shima a wajen ya parker mortar tasa suka fito sai binsu yake kamar zai amshi maryam din daga rukon ummi,, tun shigowar su ake yimasa kirarin ango yayinda tsaffi sai wake sa sukeyi shidai Bayan ko murmushi balle suga murnar sa, ko gaisuwar saiya kauda fuskar yakeyi karma atsaida shi da wani zancen biki,, Kokarin ratsa parlon yakeyi ganin haka yasa mommyn

Chapter 21 of 32