Share this page
wuri ta zauna tana Satan kallon shi,, Safina ce ta shigo itama kusa da mom dinta ta zauna tana fadin washh am tired mom,,dafa kafadar ta mom tayi cike da kulawa tace ai dole ne baby kusa taro gashi kuma anjima zaku koma na class party,, yamutsa baki tayi tace anya mom zan iya zuwa kuwa kinga sai 7:30zaa fara bana son fita ni kadai da dare haka ta fada tana kallon mommyn,, Mom tace Aa baby ga yayanki nan Khalil ki shirya sai kuje tunda na yaune kawai kokuwa hajiya,,kwarai kuwa mommyn ta amsa dama bai kamata ta tafi ita kadai ba anjima sai su tafi tare,, Murmushi jin dadi sukayi safina na kashe ma mom ido alamun plan dinsu yayi,, Mikewa tayi cikin jin dadi tace bari inje in fara shiri mom ta wuce tareda matsowa maryam mugun kallo,, dauke kai tayi kawai don batason wani bacin ran kirjinta zafi yake yimata gaba daya hankalinta ya tasahi tana kallon Khalil ya mike shima yace mommyn bari in shirya nima ya wuce batreda ya kalli inda take ba,, hawaye taji yana shirin zubo mata kauda kai tayi tana kokarin maida kwallar don gudun kada su mommyn sugani,, bayan idar da sallar ta mikewa tayi duk zuciyarta babu dadi maiyasa Khalil zaice zai tafi tareda safina tabbas akwai abunda ta shirya amma babu komai share hawayen ta tayi ta mike da sauri jikin window ta isa tareda leka wa Khalil ta hango yasan gayu cikin kananan kaya wadanda sukayi matukar fito masa da kyawunsa, kusan minti uku saiga safeena cikin wata haddadiyar princess dress ash color tasha makeup sosai a fuskarta tana taku daidai ta shiga gaban motar suka fice,, Jingina kanta tayi sai hawaye Kamar an bude famfo dafe kirjinta tayi yadda yakeyi mata suya zamewa tayi ta zauna dabas akan tiles kuka ta fashe dashi da karfi ko tasamu taji sanyi a ranta ashe haka kishi yake ,mai Khalil yake nufi da hakan dayayi ,, knocking din Kofar ta taji anayi da saurin ra mike ta fada toilet ta wanko fuskarta ta fito ta bude wata maid ce tsaye ta gaisheta tareda fada mata mommyn na kira ,gyada kai kawai tayi ta juya cikin dakin ta kara gyara fuskarta saanan ta fito,, dakin mommyn ta nufa kai tsaye ta tura kofa tareda sallama murya a sanyaye ,,amsawa mommyn tayi tace tashigo ciki,, karasawa tayi kusa da mommyn wacce take Zaune gefen gado ta zauna a kasa tace gani mommyn,, ta lura da yanayin ta ya chanza batada walwale amma saita share tace dama meeting ne daddyn yace zaayi game dake don haka karki kwanta da wuri ,, Kirjinta ne ya buga nan da nan hawaye ya fara zuba daga idanunta cike da dakuwa tace mommyn lafiya somayi wani laifin ne bansani ba don Allah kuyi h.. da sauri mommyn ta katse ta ta hanyar cewa Aa ki kwanta da hankalin ki inaga akan maganar komawarki gidana,, ajiyar zuciya ta sauke tana hamdalla a ranta finally zata je taga ummin ta,,cike da farin ciki tace toh mommyn nagode Allah yasa Ku gama da duniya lafiya,,ameen mommyn ta amsa dashi,, Karfe tara daidai kowa ya hallara a dakin daddyn suna jiran jin dalilin kiran,, adduar daddyn ya bude taron dashi kafin dad din safina ya juya ga maryam tareda tambaye ta meye asalinta dakuna dalilin zuwan ta nan ,,nan ta warware musu komai game da rayuwar ta dad yayi matukar tausaya mata,, Cikin muryar lallashi ya shiga bata baki tareda yi mata nasiha mai ratsa jiki akan yin imani da gaddara mai kyau ko marar kyau saanan ya dora dacewa Insha Allah nan da kwana uku zamu koma tareda Ke sanan da kaina zan kaiki gida,, muryar ta na rawa ta shiga yi musu godiya tareda jero musu addu'oe,, Gyaran murya daddyn yayi yace saanan abu na gaba mun hada auren yaran nan safina da Khalil gaba daya zamu koma chan Nigeria ayi bikin, rasss taji kirjinta ya buga zuciyarta ta neman fashewa dafe kirjinta tayi tana karanta inna lillahi wainna ilaihir rajiun Allahumma ajirni fill musibati a aklifni khairan minha tayi ta maimaita wa aranta yayinda Khalil shima ya dago a razane yana kallon daddyn wanda ya hango fuskarsa cike da farin ciki maida dubansa yayi ga mommyn girgiza mai kai tayi alamun kada yayi magana kallon safina ya shiga yi cike da tsana hankalinsa yayi bala'in tashi jiyake Kamar mafarki yakeyi,, Ita kuwa safina murna tamkar tayi tsalle gaban su daddyn,, *Kano* Jikin ummin kullum dad'a rikice wa yakeyi sakamakon kin kwantar da hankalinta datayi gashi jinita ba karamin tashi yayi ba har yana son taba zuciyar ta mijin halima da ita kadai Ke dawainiyar jinyar ummi domin kuwa inna ta tafi gida wai bazata iya zama gidan ita kadai ba kuma batada karfin yin jinya,, *mrs noour ce*✍🏻😘 [7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… *gareki uwar gidan alhaji abu(hajiya salma)ina miki fatan alkhairi,Allah ya tsare mu daga sharrin makiya,ameeeeen*🀲🏻 *ina yinku sosai kuma Allah ya bar kauna ta har abada*😍😍😍 πŸ…Ώβž–2⃣7⃣ gaba daya hankalinsa yayi bala'in tashi shidin suke nufi kodai mafarki yakeyi dubansa yakai ga su daddyn hirar su suke cikin farin ciki waigawa yayi inda maryam Ke zauna yaga wayam batanan hannunsa yasa ya kama fatar hannunsa da karfin gaske saida yaji azabar har cikin kwanyar kanshi kafin yasaki tareda kara bin dakin da kallo tabbas ba mafarki yake wannan abu a zahiri ya faru,, Innalillahi ya rinka ambata jiyayi gaba daya duniyar na juya masa kansa yayi masa wani irin nauyi mikewa yai dakyar yana hada hanya ya fice daga parlon,, kai tsaye dakin maryam ya nufa hankalinsa kara tashi yayi yadda yaga irin kukan dat akeyi mai tsuma zuciyar mai sauraro jiki a sabule ya karaso gareta zama yayi gefen gadon datake kwance sunanta ya kira a sanyaya maryam for de fast time,, da sauri ta dago da shanyenyen idanunwanta wadandan suke rine jajir saboda kuka ido kawai ta zuba batreda ta amsa ba,, shima idanun ya zuba mata mai zaigaya mata wace kalma zaiyi amfani da ita don rarrashi shi kanshi dazai samu mai kwantar masa da hankali da yaji dadi,, Cike da damuwa yace maryam ki fahimce ni ban San da maganar nan ba Sam wlh don haka ki kwantar da hankalin ki ni zanyi maganin matsalar nan pls ki daina zubar da hawayen ki masu matukar daraja,, Murya cikin kuka ta katseshi tana fadin aini wlh ya Khalil nariga da na fahimce Ke daman chan zuciyata tayi gangaci da kuskure da kamowa da sonka alhali tasan wutsiyar rakumi tayiwa kasa nesa don haka ladaina bani hakuri banida wannan matsayin.....ta karasa tareda fashewa da wani sabon kuka,, Pls for god sake ki fahimce ni zuciyata Ke take kauna Ke nake burin kizamo uwar yayana yadda kikaji maganar nan haka nima naji hannun ta ya kamo tareda share mata hawayen da Susa kasa tsaiduwa cikin muryar kwantar da hankali yace don Allah ki bar zubar da hawayen nan haka zuciyata zata iya daure komai amma banda ganin ki cikin kunci da damuwa,, Pls ki bar kukan nan haka ko na samu karfin gwiwar tunkarar su mommyn akan maganar ki ,, gyada kai kawai tayi batreda tace komai ba,, mikewa yayi ya isa kan mirrow ya dauko wayar daya sai mata ya kunna saanan ya dawo kusa da ita ya ajiye wayar yace zamuyi waya anjima,,ya juya ya fice,, bayan shi tabi da kallo cike da tausayin kanta har ya fice kuka ne ya kufce mata mai karfi,, taya zaice ta kwantar da hankalinta bayan yariga da ya koya mata yadda zata soshi tarigada ta kaishi chan cikin zuciyarta ta rufe soyayyar sa kawai take gudana cikin jinin jikinta ta gama kwallafa rai akansa gashi an rabasu lokaci daya saboda itadin ba komai bace,, Sun nuna *karfin IKO* su akan su lallai safina tayi gaskiya data gaya mata tun farko kada tayi tsautsayi hada hanya daita ma balle gangancin yin soyayya da Khalil,, Inda ta dauki shawara ta ta tsaya a matsayinta na wacce aka taimaka wa da hakan bai faru ba,,kuka taci gaba dayi sosai har kanta ya fata Sara mata,, domin shima daure wa kawai yakeyi amma halin dayake ciki baya tsammani takai rabin sa shiga cikin tashin hankali da damuwa kai tsaye part dinsa ya nufa toilet ya shiga tareda sakar ma kansa shower yakai kusan minti talatin kafin ya fito dukda haka wani irin daci yakeji a zuciyar shi,, Kwanciya yayi kan gado tareda rintse idanunsa da karfi duniyar gaba daya yaji ta fice mai arai taya daddyn zaiyi masa haka maiyasa bai tambayi raayin sa ba ,, damm it ya fada da karfi tareda kaiwa pillow naushi shi za'a hada aure da safina ina bazai yuwuba mikewa yayi a fusace ya fice,, dariya taji daga bayan ta cikin sauri ta dago ido hudu sukai da safina da meena suna mata dariyar mugunta, kauda kanta tayi gefe don bata kaunar ganin safina a yanzu,, tabe baki safina tayi cike da isa da wulakanci ta furta useless girl kawai kin gama karuwancin naki ko kinga yadda lokaci daya na nuna miki *karfin IKO* na ko,, karasowa tayi kusa da ita cike da gadara ta furta tsuntsun daya ja ruwa ai dakin bi umarnina da bakiyi kuka yanzu ba kuma kisani kuka yanzu kika fara arayuwar ki saima kin goma wannan matsaiyacin gidan naku saanan zaki kara tabbatar da abunda nake gayamiki,, Meena ce ta matso tana fadin sofeey dama kin kyaleta jakar haka taji da damuwar datake damunta kallon safina tayi tana dariyar shakiyanci tace in banda abunki sofeey ai dolene tayi kuka tana tunanin ta gudu daga wahala ta samu daular irin wannan ta nuna dakin da hannunta saanan tace mai zai hana bazatayi kuka ba wani abuma sai dad ya maidata rubabben gidan su,, dariya suka tuntsere da ita tareda tafa hannun,, Frowning safina tayi da idanu tace kuma fa Hakane meena gaskiya ya kamata mu tafi ko tasamu kayan data samu dana satar ta kulle su guri daya a koma gidan tuwo da kuka dariya suka sake shekewa da ita suka fice,, Kifa kanta tayi kan pillow taeda fashewa da wani kukan sosai zuciyar ta Ke yimata zugi tabbas tayi kuskure dama irin ranar nan tana zuwa ako yaushe zuciyarta na kwa barta akan ta tsaya matsayinta amma ina saitayi biris da ita saboda tsannanin soyayya datakeyi Khalil din,, dakin mommyn ya nufa ya bude kofa tana Zaune gefen gado ta buga uban tagumi dagowa tayi tana kallonsa cike da tausayi da so karasowa yayi kusa da ita ya zauna batareda yace komai ba,,, Rungume shi tayi tana shafa sumar kanshi kusan minti goma kafin ta soma magana cikin muryar lallashi tace don Allah son ka kwantar da hankalin ki kada kasa damuwa aranka ya shafi lafiyar jikin ka duka duka kwana biyu kenan da fitowar ka asibiti nasan abunda Ke damun ka,, amma abunda nakeso dakai addua zakayi tayi kasan halin mahaifinka in kaina banyi farin ciki da wannan maganar ba Sam,, da sauri ya bude idanun sa cike da mamaki yace mommyn da gaske,, kwarai kuwa ta bashi amsa cikin karfafa gwiwa tace dole in tayaka son abunda kake so kuma saanan zanyi farin ciki da wacce zata cigaba da kula da kai kamar yadda nakeyi amma safina banajin zata iya yin hakan sam ,, don haka ka kwanrar da hankalinka zanyi wa daddyn magana anjima koda ace zai hadau ne bai kamata ya yanke hukunci batareda jin raayin muba,, OK mommyn na ya furta yana murmushi I love u mommyn Ure d best,,itama murmushi tayi tace I love u son,,ya dade a dakin yana bacci gyara masa kwanciya kawai tayi ta mike tareda rufe shi da blanket ta fice sashen daddyn cike da tausayin dan nata musamman ma maryam wacce takejin ta tamkar yarta ta cikin ta,, mom da dad na zauna a dakin da aka ware musu suna hira hankali kwance yayinda safina Ke tsakiyar su tana rungume da dad din ta gefe,, dad yace yanzu mun yanke shawarwar da mun koma Jibi aka kwana biyu zamu saka ranar biki kuma inaga bazai dau wani dogon lokaci ba tunda kin gama makaranta Kya cigaba a dakin ki,, murmushi mom tayi tace gaskiya ne wannan ko two month aka sa inaga ya isa,, cikin farin ciki safina tace yess mommyn haka yayi kinga na huta da fadan malam kuma karatun dole in cigaba dayi ,,burinta zai cika mom Oxford university piew zan shiga batareda problems ba ,, dariya sukai gaba daya kafin dad yace ai malam gaskiya ya fada kinga kin huta ga karatun ga aure cikin kwanciyar hankali sai kiyi abunki,, da Sallamu ta shiga dakin yana Zaune bisa kujerar yana danne danne bisa system dinsa amsawa yayi batareda ya dago ya kalleta ba ,, kusa dashi ta zauna tareda yi masa sannu ta zauna zaman jiran gamuwar shi,, Baifi minti goma ba ya rife kafin ya umarceta da ta hada mishi coffee,,mikewa tayi ta fice ta hado ta dora a karamin tray ta dawo ta ajiye gabanshi ,, Saida ya gama sha saanan tace ni kuwa inason muyi magana,, Juyowa yayi yana facing dinta yace OK da fatan lafiya dai ko,, Kai ta gyada ta ce lafiya akan maganar auren nan ne maiyasa alhaji a matsayinsu na family zaka yanke wannan hukunci in batareda jin raayin mu ba musamman son at least ko baka ji ta raayin na ba ka ji nasa ko yana da wacce yake son aura daban,, dakatah hajiya ya fada cikin fushi shi Khalil dinne ya gaya miki baya so kukuwa kece bakida interest akai na dauka wannan yar tamkar yarki ce Kamar yadda suka dauki son tamkar sansu beside Ke akan idon ki sau nawa nake yi masa maganar fitar da matar aure yace kuma babu inya samu zai fadi,,shin ya taba gaya miki ya samu matar aure ne,, ajiyar zuciya ta sauke a sanyaye tace kwarai kuwa yanada wacce yake so gatanan ni kaina zuciyata tafi kwanta wa daita maryam ce ta cikin gidannnan,,, Dakatah don Allah hajiya kada ki harzuka in yanzu nan ya fada rai bace da daga muryar yace yarinyar da bakida takamaimai sani akan asalinta kike maganar hada danki aure da ita zancen banza zancen wofi kenan inshi ba shida hankali kema saiki biye mai eyeeh,, toh alhaji gani nayi yarinyar nan ta fadi asalinta kuma ma in karya ta fada ai dama dole zaayi bincike kafin ayi maganar auren ko,, a naki tunanin kenan kinji ko niba mahaukaci bane dazan hada dana aure da ita ba kowacce kuwa balle ba komai bace ita din yanzu ki duba tashin hankalin damuka shiga akanta haka zaayi auren wasu chan na bibiyar rayuwarta duk sanda wani abu yasameta tamu ta ganmu toh ni Sam zuciyata bata aminta da wannan maganar ba ,,kuma banason kara jinta kinji na gaya miki,, *mrs noour ce*✍🏻😍 [7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… *~(SUBHANALLAHi WA BI HAMDIHEE)~*🀲🏻 *~(SUBHANALLAHIL ALEEYUL AZEEYM)~*🀲🏻 *~(JUMAAT KAREEM)~*😊 πŸ…Ώβž–2⃣8⃣ Kuma banason kara jin kinyi min magana akan ta na gaya miki ya fada rai bace tareda wucewa kan bed yayi kwanciyar sa,, dama ta tsammaci hakan daga gareshi bazai taba fahimtar ta ba ko kuwa Khalil din kanshi,ita damuwar ta kawai Khalil ne batason ganin shi cikin damuwa,mikewa tayi ta wuce kan bed din ta kwanta ta juya mishi baya,, murya a sanyaye tace alhaji ko dai dan itadin ba yar wani bace dai shiyasa baka son hadin da ita?ta fada batareda ta kalle shi ba,, a fusace yace wannan tamabayar Ke zaki bawa kanki amsar ta inkikayi la'akari da yadda na aure ki,,yana gama fadin haka ya mike ya fice daga dakin ransa a matukar bace,, jikinta ne yayi sanyi sosai tunowa datayi da yadda akayi auren ta da daddyn,, Asalin daddyn Mazauna garin Abuja ne iyayensa ba kananan masu kudi bane babansa shahararen dan siyasa ne babban tsohon dan majalisar kasa ne sun tara dukiya banda ta iyayen da suka tara musu sunan sa alhaji hamidu Muktar da matar sa hajiya Fatima iyayensu uku ne daddyn ne babban mai suna Muktar wanda yaci sunan kallansu sai kannensa mata yan biyu hassana da Usaina wadanda baa chanza musu suna ba sun taso cikin gata da daula sosai daddyn yayi karatunsa a kasar waje har ya kammala shima fannin siyasa dai ya maida hankali akai yana da mata nadiya wacce har lokacin bata haihu ba, yayinda hassana take babbar lauyace wacce tayi aure tana Zaune a Egypt da iyayenta biyu,minal da haidar sai Usaina wacce take babbar likita ce tana Zaune garin Abuja da mijinta iyayenta uku safwan da Fatima wacce suke kira da mimi sai Muhammad,, Haduwar su mommyn ya samo asalin ne lokacin da daddyn yasamu kujerar yan majalisun shima, sunje taro kasa da kasa wanda akayi a nijar akan ciwon yunwa daya addabi kasar Itadin ba yar kowa bace sanye take da kayan su na fulani tana kiwo da kaninta sukuwa su daddy suna bin wasu kauyikan suna bada taimako tunda ya ganta yaji ta shigar mishi rai,, yayi kokarin su tsaidata amma saita gudu dole yasa aka bita batareda tasaniba kafin su gama taron nan na kwana hudu saida yasan yadda yayi ta amince dashi har magana takai gurin iyayenta,,suma sun amince batareda shan wahala ba sai dai shi nashi iyayen suka ki fafur da kyar da suden goshi suka yarda banda matar sa wacce tana kan raayinta bazai hadata kishi da yar matsiyata ba,, hakurin duniya da lallashi taki har akayi auren wanda iyayen basu sai mata komai ba saboda rashi,,koda ta tare ganin irin kyauwuna yasa nadiya balle fitina har saida ya saketa tace tafison haka ita ba yar matsiyata bace zata samu wanda yafi daddyn a haka na samu zaman lafiya,, Shekarata biyu da yin aure na haifi ibraheem Khalil bayan shekara biyar na kara haifar ya mace mai suna zainab shekarar ta gama uku Allah yayi mata rasuwa tun daga nan kuma shiru,, bayan wasu shekaru bude yaita samuwa ikon Allah kuma sai Sam bansamu matsalar kyara ko tsangwama ba daga yan uwanshi harya zuwa wannan lokacin da Khalil ya kammala karatunsa na law wanda yazama shahararren lawyer ne sosai daddyn kuma yana rike da mukamin ambassador of us dake wakiltar nija kudi sun zauna musu sosai fiye da tunanin mai karatu,, Suna na Fatima ana kirana da faisam inada yayye maza biyu sirajo da manga(babba kenan) wadanda suna nan tareda iyalensu kowanne yanada Yaya sai ni sai kanina fetal(karami kenan) ,,mommyn kenan take tunani n asalinta kara juyawa tayi lallai tasan daddyn baya kyamar talaka tunda ya aure taya zauna da ita batareda tsangwama ba matsalar shi dayace shi wani irin baudadden mutum ne wanda inya kafe ya kafe kenan sai wani ikon Allah,, Mikewa tayi tabi bayanshi yana kwance kan kujerar zama tayi kusa da shi tareda sauta murya ta bashi hakuri,, Nan take zuciyar shi tayi sanyi yace ya hakura amma zancen maryam bayaso gyada kai tayi tace in Allah ya yarda baza'a sake ba,, Koda y koma daki ya kasa Zaune ya kasa tsaye yarasa mai yake yi mishi dadi,kallon agogon dakin yayi yaga karfe daya da rabi jawo wayar sa yayi ya shiga neman number maryam kiran duniya yayi taki dagawa har duk da haka bai hakura ba ya tura mata text ya sake kira shiru taki dagawa tsaki ya ja tareda dafe kanshi wanda yake Sara mishi Kamar zai tsage gida biyu toilet ya nufa ya dauro alwalar saidai kafin ya tada sallah wani mugun zazzabi ya rufe shi jikin shi sai rawa yake karkar haka ya lallaba ya haye gado tareda lullube wa da babban bargon,, dukkan kira dayayi mata tana kallon wayar ta ki dauka tacigaba da sallar datakeyi sai wurin uku da kwata kafin tayi addua ta mike ta hau gado ta rufe rabin jikinta ta blanket,, wayar ta jawo ta kunna ta duba missed calls 78 sai sako guda daya ta bude,, _"""zuciyata zata iya jure kowacce damuwa banda fushin ki,wanda zai iya zama barazanar ga zuciyata da rayuwa ta pls ki daga wayar I need to hear ur voice now_"" Wani iri sonsa taji yana ratsa zuciyarta kuka ta saki a hankali tana magana hakan yafi ya Khalil ,hakan danayi shine daidai na dauki alkawarin ba rinka har abada na barwa Allah zabina damachan tsautsayi ne da kaddara don nasan kafi karfina ,haka ta kwana kuka har aka kira sallar ta mike tayi kwanciya tayi akan sallayar,, A falo misalin karfe tara da rabi na safe kowa ya hallara a dining donyin break fast banda Khalil da maryam mommyn tayi kokarin aikawa kiransu daddyn ya hana yace aiba kananan yara bane duk abun ya damu mommyn haka dai ta daure har aka gama saanan su daddyn suka mike suka fice tareda dad din safina,, Safina na ganin fitar su ta ce mom ya maganar siyayyar kinga flight din safe zamu bi,, Mom tace babu damuwa anjima sai kuje zanyi wa yayan ki magana saiku tafi tare,,OK mom tafadi tareda mikewa ta haura sama kai tsaye dakin maryam ta nufa ta murda Kofar ta shiga tana kwance bisa sallaya tana bacci fuskarta harta kumbura saboda kuka,, tsaki taja ta karasa fringe din dake gefe ta bude juice ta dauko mai sanyi sosai ta bude ta shiga tsiya yawa maryam a kanta ,, a firgice ta tashi tana sallati safina ta gani tsaye da gorar a hannunta,ina kwana ta furta murya a sarke,, daga mata hannu sama tayi tana gyatsina alamun bata bukatan gaisuwan ,,sai da tagama shan kamshin kafin tace maza ki tashi ki fara hada mun kaya na yanzu nan ta wurga mata gorar a fuska ta fita daga dakin,, Murmushi takaici tayi tana girgiza kai ba komai lokaci ne ta fada a hankali hawaye na silalowa daga idanuwan ta,,toilet ta shiga tayi wanka ta fito Indian pakistan ta saka green color yayi mata kyau duk da fuskarta babu walwala kayan sun amsheta sosai ,, dakin mommyn ta fara zuwa da sallama ta shiga bata dakin ta kara yin sallama shiru ta juya da nufin fitowa nan sukayi karo da mommyn hankalinta tashe da sauri maryam ta matsa baya tana furta sannu bata amsa mata ba ta wuce cikin dakin da sauri ta dauki wayar ta number daddyn ta kira hankali tashe take gayamai Khalil ba lafiya sosai,, kirjinta ne ya buga da sauri da shiga karanta innalillahi wa inna ilaihir rajiun,jiri taji ya na neman yarda ita da sauri ta zauna gefe kujerar,, likita mommyn ta kira kafin ta juyo ganin yadda maryam tashiga wani hali nan take tausayin su yakamata kama hannunta batareda tace mata komai ba sashen Khalil suka nufa har bedroom yana kwance sai rawar sanyi yake Habib na kusa dashi yana goge masa towel akai wanda aka jika jika da ruwa,, *Kano* Jikin ummi kullum babu sauki gashi malam garba ba wani karfi ne dashi ba a ranar jikinta ya rikice sosai an rubuta musu allura da magunguna ya rasa yadda zaiyi kudi har dubu goma sha hudu,, Yayi rokon alfarmar abashi bashi zai kawo amma dayake government ne Sam suka hana saboda mutane sun sha guduwa da kudin su,,kujerar dake gurin ya zauna tareda zuba tagumi,halima ce ta karaso hankali tashe tace malam Yaya ka zauna haka ga likitan chan najira,, Fuska babu walwala yace ya zanyi ne halima wlh kudin magani wlh duk rokon nayi amma sun hana gashi wayar sani bata shiga(sani yaron sa ne wanda yake toka mota ne sana'ar shi) hankali tashe tace malam yanzu ya zamuyi,,ihu suka ji daga bayansu da sauri suka waiga ga kallon wurin nurses din gurin ne suketa murna da shewa alhaji yazo kowa sai murna yake a haka har ya shigo tareda wasu nurses suna binsa tareda wata mata a keken daukar marasa lafiya,, gaba daya nurses din sai kai gaisuwa sukeyi cike da girmama wa ,, girgiza kai malam yayi yace ki duba halima Ke gani yadda mutanen nan sukeyi domin a basu abun duniya amma ki duba yadda ga marasa lafiya nan kwance su taimaka sunki,, karaf maganar akan kunnen alhaji yace bawan Allah waye ba lafiya mai ake bukata ne,, da sauri malam yace Aa ba komai,, Alhajin yace Aa bawan Allah indai taimako

Chapter 13 of 32