Share this page
suke anan ne suke gayamin,, Sun yanke wannan hukunci ne a nasu zaman dasukayi inda shi malam din wato kakan safina ya yanke wanna hukunci suma kuma sukayi naam da hakan sakamakon samun gamshahsen bayani dayayi daga bakin ya Habib inda ya sanar wa malam soyayyar mu da maryam,, Wallahi mommyn ban tsaya gamaji ba tunda na tabbatar ni din suke nufi kawai na juyo da gudu na hau motor din yiwa hearttee na albishir Ke kuma kin wani hana ya karashe yana tamke fuskar,, Doka mommyn takai masa ya goce suna dariya tace lalli son amma aini ya kamata ka fara sanar wa saboda hankalina yafi naku tashi,, Zaro idanunsa yayi waje yace mommyn a ina kinsan kuwa yadda nakeji kuwa,, Doka ta kara kaimasa tana fadin tashi ka fita ,fita wallahi daga gidan nan ko in saba maka,, Da sauri ya fice su didde sukabi Bayan sa suna masa tsiya ,, Sujudun shukri mommyn tayi cike da tsantsar murna da farin ciki ta mike ta karasa bakin kofar toilet din tana fadin maza ki fito ki sameni a dakina yanzun zama bai gannmu ba,,, Kan ubancen me kake shirin fadamin ne me kunnuwa na suke shirin jiyemin mom ta fada a matukar harzuke tamkar zata daki dad din ,,, Abinda dai suka jiye miki daga farko su zasu cigaba da jiye miki har karshen rayuwar ki sakamakon bijire min da kunyar ta dani dakukayi malam ya yanke hukunci Wanda nima yayi min daidai hakan auren safina da Habib aka daura inanan inajiran duk wani rashin mutunci da zakuyi keda ita,, Kan uban chan ai wallahi alhaji inka isa Shegiya bake wanna dan iskan yaron matsiyace gantallale mai yake dashi dama burinsa kenan yaga yadda zaiyi ya mallake maka dukiya to kuwa gashi burinsa ya cika ta hanyar auren yata ,, Gyara tsayuwa tayi tana zazzare idanun cike da masifa da rashin mutunci ta nuna dad da yatsa tace wallahi wallahi saidai yayi baban kuskuren a rayuwar sa ni din nan daka Ke gani waje na kasani bakasan cikina ba da sannu zanyi maganin Ku,, Wanna kuma matsalar ki ce amma hukuncin malam babu maija dashi wallahi zan ita sallama ta dake kanki akan maganar malam wallahi,, Tsaki taja da karfi tana hura hanci tace zancen banza zancen wofi ai dukkanku munafukai ne babu wani malam daya yanke hukunci banda iya munafuncin ka to wallahi koda malam dinne wallahi bai isa bayayi kadan walla..... Kau taji ya yanke ta da lafiyyen mari Wanda yayi matukar gigutar da ita murya a kausashe yace ki fice mun daga dakin nan ko kuwa kiji abunda kunnuwan ki bazasu taba mafarkin son jiye miki ba ya mike ya fice daga dakin ransa a matukar bace,, Kuka ta fashe dashi da karfi tana fadin wallahi kayi kadan dad din safina daidai yau duk abunda zai faru ya faru amma wallahi bazan zauna a cutar da yata ba Habib ,Habib fa wallahi bazai yuwuba ne wannan Sam ,, Fuuu ta fice tana kuka ta ratsa mutane ta nufi dakinta wayar ta dauka tareda dialling number safina sai da ta gama karanta ta yanke baa dauka ba ,,bata hakura ba sake bugawa tayi amma shiru ,, Tsaki taja tana fadin yar banzar yarinyar mai kunne tsiya ko ina tashiga tabar wayar Ohio,,sai datayi mata missed calls biyar ana shidan ta dauka cike da farin cikin take fadin hello mom na ,, Ina kika Shiga kika bar waya nata faman ringing mom ta jefo mata tamvayar rai bace,, calm down mom ina parlon ne nida friends dina muna party din mu na celebration din bikin na mana,, don Allah rufe min baki daga nan shashasha kawai wawiya to kima daina domin kuwa Khalil yarigada ya zama na maryam Ke kuwa kinzama ta Habib,, Whaattt ,,safina ta fada cikin karaji mom pls don lose my gud mo... Ke mom ta daka mata tsawa kibar duk abunda kikeyi kidawo zama bai ganmu ba an daura auren ki da Habib da Habib nake fada miki da Habib safina kuka ne kufcewa mom Wanda ya sanya kanwar mamanta amsar wayar,, Hello safina kina jina.. yawwa momy don Allah kada ki fadamin abunda mom take fada gaskiya ne pls momy,, Dakata safina abunda muke bukatar daga gareki shine ki bar duk abunda kikeyi ki dawo kasar nan yau komai dare amma kam tabbas maganar gaskiya ce kin tabbata matar Habib,, Kara ta buga da iyakacin karfinta ta saki wayar kasa tana ihu da kuka da sauri friends din nata suka shigo dakin wadanda dukkansu turawa ne babu musulmi kodaya cikinsu,, Rirrike ta suka shigayi suna bata hakuri fusgewa tayi ta fice daga dakin da gudu ta nufi inda suke celebration din nasu ta shiga watsi tareda faffasa kayan dake gurin tana ihu da kuka da iyakacin karfin duk iya yadda sukayi duhana ta abun ya faskara said a tayiwa dakin rugugu saina ta koma cikin dakinta da gudu ta janyo handbag dinta ta dauka visa ta da wayoyi da laps dinta tana fadin wallahi maryam nice ajalinki ni zakuyiwa haka lalli ya Khalil ,,wallahi bazanyi zaman aure da Habib ba wallahi dad bazan yiba bazan yi ba,,ta hada kudaden ta duka ta dauka key din motarta Dana gidan ta baiwa daya daga cikin kawayenta ta fice daga gidan tana kuka,,(ni kuwa ina๐Ÿคช) Jin shiru yasanyata bude kofar ta fito tunanin ta kowa ya fice sai dai tana fitowa taji an rungumeta ta baya ,ta tsorata sosai da farko saidai jin kamshin turaren sa ya sanya ajiyar zuciya ta Shiga kokarin kwatar kanta amma ta kasa saboda ta baya yake rungume da ita,, Pls ka barni insaka kaya kar wani ya shigo fa ta fada a shagwabe,, Murya cikin rada Wanda yakai fuskar sa daidai wuyanta yace maiyasa kike korar mijin ki bayan murna nazo tayaki da yanzu safina tayi miki kwace mommyn fa tace dazu har kin kwanta ciwo,, Zumburo baki tayi gaba nace lafiya ta kalau kuma bani zaka taya murna ba kaje chan gurin matar ka kataya ta murna,, Juyo ta yayi gaba suna facing din juna yace shiyasa nazo ai tunda Allah ya ceceki na zama angon,, Kasa tayi da kanta saboda irin kallon dayake binta dashi Wanda yake sanyata jin tsikar jikinta na tashi,, Hannu ya kai saman gashinta Wanda har ya fara bushewa ya Shiga shafawa a hankali idanunsa kur akan ta jinsa yake yi wani iri,, Kokarin janye jikinta take amma ya rike ta gam a kirjinsa gaba daya ta rikice jikinta sai rawa yakeyi yayinda shikuwa yayi tamakr baigani yana cigaba da bullo mata da sabon salo ta hanyar kai fuskar sa ga gashin kanta yana sunsuna yana Jan numfashi da kyar,, Knocking sukaji daga bakin kofar Wanda ya sanya maryam kafafuwanta suka Shiga rawa sosai hawayen ta soma zubarwa ahankali cikin rawar murya tace pls ya Khalil mommyn ce,, Janye ta yayi daga jikinsa yana sauke nannauyar ajiyar zuciya gabadaya jikinsa yayi sanyi idanuwansa har sun chanza launi,, Hijab dinta ta dauka da sauri ta zura ta bude kofar da sauri,,kallo daya mommyn tayi masa tasan akwai wani abu tora kanta tayi cikin dakin saigashi zaune bakin gado,, Waro idanu waje mommyn tayi tace maiye hakane Khalil yake damunka bana son irin wanna abun fa wallahi kayi wasa ba zata tare yau ka shiga hanaklin ka,, Ke kuma wuce muje tasa keyar maryam tay suka bar dakin mommyn na mitar wanna zakewan da yakeyi ai dole saita Gyara yarta wallahi,, Shikuwa kwanciyar yayi kan gadon yana shakar kamshin ta ,tareda yin hamdalla ga ubangiji daya mallaka mai ita,,, Chan kuryar dakinta suka Shiga da didde sai dariya su ummi keyi wacce tace itadai yar kallo ce tareda didde suka shiga toilet wani irin hadi ne na zallar madara sabuwar tatsa Wanda yasha hadin gyara diddde ta durje mata jiki said a yayi minti talatin kafin mommyn ta miko musu wani ruwa a bocket Wanda na hadin turare ne mai matukar kamshin da Gyara fata shima akayi mata wankan dashi har cikin gashin kanta sanan ta daura wani sabon Zane ta fito bakin gado mommyn tace ta zauna ta miki mata wata hadin madarar shanu da zafin sa tace maza ta kurbe,,sai da ta shanye tas Allah ma ya taimaketa hadin babu wani magani mai daci a ciki wani irin tirare suka kunna tayi turaren sa gaba daya jikinta harta gama saanan mommyn ta dauka mata wani dankararren leshi dark blue da ratsin baki da yellow ta sanya dinkin riga da zani Wanda yayi matukar yimata kyau abunka ga fari,, Duk iya nacin mommyn hassana akan kwalliya mommyn hanawa tayi tace bata cika son kwalliyar nan ba yarta ta na da natural kyauwunta dole suka hakura inda ta sanya awarwaro da enkunne da sarka kalar blue da mayafi milk color da takalmi ta feshe ta da turaruka sosai,, *mrs noour*โœ๐Ÿป๐Ÿ˜˜ [7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *๐Ÿด๐ŸดKARFIN IKO๐Ÿด๐Ÿด* ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited by๐Ÿ‘‰๐Ÿป *oum Zahara*๐Ÿ˜ Dedicated 2my lil sis๐Ÿ‘‰๐Ÿป *Maman Sultan*๐Ÿ˜˜ ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู… *gaisuwa da fatan alhairi Gareku yan karfin iko fans group,,da duk daukacin masoya Allah ya bar kauna mai dorewa ,,Allah ya biya mana bukatun mu,,ameen๐Ÿคฒ๐Ÿป*๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜ ๐Ÿ…ฟโž–5โƒฃ2โƒฃ Sosai biki ya koma na dangi yayinda maryam ta gyare ta manta da ciwo farin ciki kuwa har saida ta zubar da hawaye bata taba dauka a rayuwar tana da sauran gatan nan ba saigashi lokaci daya Allah ya amsa mata adduoe data dade ta nayi,, Anci ansha anyi waazi mai ratsa zukatan muminai saan aka shiga daukat pics Wanda harda ya Khalil din shima yasha ado da bugaggiyar rantsatsiyar shadda blue sai bayan magrib aka gama walimar,, Inda bayan sallar isha alhaji ya kira taron family dazasuyi,, Har cikin bedroom yaseer ya biyo Khalil yana masa tsiya yayi masa kwace ashe shiyasa yake cika yana batsewa inya gansu tare shikenan na hakura amma nan gaba zaka wahala ka sake,, Murmushi yayi shima kadan yace ai saidai kar a kuma dai amma kasan ni din daban ne kuma na nuna maka,, Haka sukai ta yi masa tsiya da sauran abokan dasuka zo kaishi dakin shi ,,shi kuma yayi kwanciyar sa kan kujera yaki ko motsawa yace babu Wanda zai bishi gidanshi indai ba gulma ba domin shi matarshi batada kawa don haka ya hutasshesu zai siya bakin matar sa da kansa,, dariya sukai sosai suka shiga yi masa tsiya har akayi isha saanan sukayi masa sallama suka tafi,, Gaba dayansu sun hallara a babban parlon alhaji akan meeting din da zasu gabatar,, Sosai abba ya bude taron da addua kamar yadda alhajin ya umarta [7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *๐Ÿด๐ŸดKARFIN IKO๐Ÿด๐Ÿด* ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited by๐Ÿ‘‰๐Ÿป *oum Zahara*๐Ÿ˜ Dedicated 2my lil sis๐Ÿ‘‰๐Ÿป *Maman Sultan*๐Ÿ˜˜ ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู… ๐Ÿ…ฟโž–5โƒฃ4โƒฃ Kauda kansa yayi tamkar baiji taba saina mikewa da yayi ya nufi drawer ta kwallin wayar daya bata ya dauka ya koma bakin gadon ya zauna,, Zaro wayar yayi daga kwalin tananan kamar yadda ya bata a kashe da alamu bata taba amfani da ita ba,, Mikewa yayi ya isa inda take zaune kan stool gaban mirror, dukawa yayi ya rungume ta sosai da jikinsa ta baya,,yana sauke ajiyar zuciya a hankali,,hannun sa ya sanya ya amshe turaren dake hannun ta tana fesawa ya ajiye kan mirror din,, Hearttee fita zamuyi bana son wannan kwalliyar haka pls ya fada cikin kunnuwanta cikin sanyin murya kamar mai rada,,wayar ya ajiye sanya mata cikin hannun ta ya hada yana murza hannun sannu a hankali yana Jan numfashi da kayar,, Nan take jikinta ya fara rawa yayinda shukuwa wani irin shauki yakeji yana ziyartar gaba daya ilahirin gabobin jikinsa laushin hannayenta tareda wannan daddadan kamshin dake fita a ko ina na jikinta suna matukar daga masa hankali,, Sunsunar gashin kanta ya shiga yi yana kara matse ta a jikinsa kokarin janye jikinta takeyi ta hanyar motsu mutsu da jikinta Wanda ya matse ta tsam ya hanata janye jikinta daga gareshi juyo da ita yayi batareda bata lokaci ba ya shiga kissing dinta ta wuya har zuwa bakinta Wanda ya sanya ta nan take ta shiga zubda hawayen ,, Ganin abun nasa babu sauki ya sanya ta tattaro sauran karfin daya rage mata ta tura shi ta matsa gefetana sauke ajiyar zuciye tareda shafa lips dinta saboda zafin dasuka fara yi mata,, Murya na rawa ta futaYa Khalil na shirya fa mommyn na... daga mata hannu yayi alamun baya bukatar ji,,lumshe idanunsa yayi yana fadin oh my gosh yarinyar nan sonta zai iya illata ni da ban aureki ba tabbas nasan narasa rayuwa ta,, Sosai yakejin bacin ran yadda maryam din take hana masa kanta bayan tafi kowa sanin shi mijinta ne bata tsoron fushinsa Sam yanzu sai na mommyn jinjina kai yayi da sannu zanyi maganin Ku,, Tamke fuskar yayi yamike yayi gaba harya bude kofar ya juyo yana kallonta yadda har yanzu ta kasa nutsuwa kamar wacce zaa yanka jinkita har yanzu rawa yakeyi girgiza kai yayi kawai saana murya a shake yace umarni na baki da kifara amfani da wayar nan daga yau karki bari na kira baki dauka ba,, Gyada kai kawai tayi don tasan neman na fitina kawai yakeyi itadai burinta ya fice daga dakin kar mommyn ta biyo bayanta tabbas shiyasa dole mommyn Ke hadata kwana da didde in ba haka ba kuwa akwai matsala ,,gaba daya yanzu shi tsoransa ma takeji da irin wadannan salon daya shiga bullo mata dasu,, Babu irin rokon da ban baki da ya Khalil baiyi wa mommyn ba amma kememe ta zubawa idanunta tuka tace Sam wallahi bai isa ba ya hadawa yarta lefe ba a kasar nan har safina ta samu kimar a fitar kasar waje sai yanzu zai zo mata da maganar su fita ta hado kayan ta bazai yuwu ba wallahi,, Dama jiya na gama maganar kabi mommyn ka inzata koma Ku hado lefen Ku achan akawo mana eyeeh,, Dariya kowa yakeyi musu a dakin banda ummi wacce keta fadan babu wani barnar ta da kudinsa da zaiyi bayan irin hidimar dayake yi mata,, Dole haka ya mike ya fice daga dakin ransa a bace maiyasa mommyn keyi masa hakane duk yadda ya so ya ci burin wannan ranan ya samu ya kebe da matar sa amma shine mommyn ta bullo masa itama tanan babu komai aii,, Kwanciya yayi bisa daya daga cikin kujerun dakin na parlon sa yana Jan dogon tsaki bari daddyn ya dawo zanyi komai a kwana biyu kuma wallahi dole su barni na huta nima shiyasa Sam bazan zauna gidan nan ba,, Sai bayan sallar magrib suka isa garin bauchi kofar gidan malam motar ta parker,, a gajiye suka fito safina kuwa da kyar take iya daga kafa da ajiye wa saboda tsabar gajiya ga yunwa dake addabar bata take in komai tun dasuka taho ,,kallon gidajen dake unguwar tayi cike da kyama zuciyar ta na Dada zafafa da bakin cikin wanna gantallalan aure da dad yayi mata ,, Koda suka isa cikin gidan babu Wanda tayiwa koda kallon arziki ne balle na tsiya parlon malam ta shige tayi kwanciyar ta bisa doguwar kujerar dake dakin ,, Matar malam keta hidima dasu,sannu kawai Safina ta iya budar bakinta tace mata kamar ba kakar taba Wai donma gidan a gyare yake tsab dad ya gyarashi saidai ba wani kayan jin dadi ne a gidan ba don harta da ac malam kin yadda yayi a sanya masa saidai babu laifi don babu wani gida mai kyau gidan anan unguwar,, A kyamace tadauki ruwan ledar tasha takoma ta sake kwanciya harda juya baya don bata kaunar bude idanunta ta ga tuwon nan da su malam da Habib sukeci,dukda kamshin miyar ya cika mata hanci amma tsabar iya girman kai da dagawa ya hanata koda sake kallon kwanon,, Sai da suka gama cin abincin sukayi sallar isha ,saanan ya Habib yayi musu sallama,,koda yayi mata sallamar ko motsi batayi ba balle yasa ran zata kalli inda yake tana ta faman charts da meena tana sanar da ita halin datake ciki,, Juyawa yayi ya fice jiki a sanyaya yana tausayawa halin kuncin rayuwar dazai shiga zaman aure da safina ba abune mai sauki ba,,harya isa gida yana aiki saka da warwara matakan da zai dauka da zai sanya su samu zaman lafiya amma saiyaga ina wannan bazai yuwu ba gurin safinar,, Baifi minti ashirin da shiga gidan ba inna suka shigo gida da sallamar su Aisha Ke ta zabga gida har suka shigo cikin gidan yayinda Hauwa suka dafe yayan nasu suna murna ganin sa,, Shima dariyar yakeyi yana musu sannu da zuwa da kansa ya debo wa innar tasa ruwa suka sha saanna aka gaisa tana tambayar Yaya amarya,, Ya amsa da tana nan lafiya gidan malam tana gaidaku,,inna yamai jiki,, Maijiki da sauki yau kam alhamdulillah shiyasa muka taho kar abarka kai kadai tana gaidaka itama innani,, Wuri su Aisha suka basu inda suka tattauna gurin da safina zata zauna,, Jim inna tayi kafin daga bisani tace ai inaga daka Ke neman gurin zama a cikin gari gwara a gyara maka naka dakin wancan filin lambun sai a hade ayi wani babban dakin ko da bayi ne inyaso madafi saitayi hakuri ta fito na tsakar gidan namu,, Jinjina kai yayi yace tabbas inna nima nayi wanna tunanin Saidai ina gudun abunda kaje ya dawo inna bakisan wacece safina ba tunbaya ina kokarin fahimtar dake wallahi inna bazan juri tace zata ci ma wani nawa zarafi ba ko wulakantashi balle kuma ke wan... Aa dakata habibu indai tanice banida wata damuwa da sannu kuma komai yayi farko zaiyi karshe ka ringa tunawa da hakan ko shin kasan albarkar da ubangiji ya boye cikin auren Ku Wanda sai kun zauna zakuci ribar shi,,wallahi ni bani da wata damuwa kaidai din zaa baiwa baki da kwarin gwiwa kuma kuma insha Allah albarka ce zata biyo baya,, Ajiyar zuciyar ya sauke da karfi yana fadin Allah yasa hakan mama,, Ameen Allah yayi muku albarka ya azurta da zuria dayyiba,, Mikewa yayi kawai ya fice zuwa dakin sa kallo daya zakayi masa kasan baya cikin farin ciki,, Kin komawa yayi cikin gidan gaba daya sai dare dayaji shugiwar motar su alhaji ,saanan ya mike cike da azama ya nufi dakin baibi ta cikin parlon ba saiya zagaya ta bayan dakin sa don bata bukatar ganin kowa musamman maryam din Wanda a yanzu ya kasa danne hakurin sa a kanta koyaushe ganinta daga masa hankali yakeyi,, Sai dai kash yana isa ya Tatar da mommyn a dakin sunata hira dolensa ya zauna yana cin magani ya gaidasu ya kawar da kansa,, Ganin batada niyyar tashi yasanya shi mikewa yayi musu saida safe ya wuce dakin gimbiyar sai dai kash itama tun kafin ya isa ya dinga jiyo muryar didde suna hirar su hankali kwace wani irin bakin ciki yaji ya kara ziyartar zuciyar shi juyaa yayi ya koma dakinsa,, Wannan wace irin rayuwa ce mutum da matar shi ana yimasa iko ni nataba jin haka tsaki yayi ya sake yin juye tareda rungumar pillow lumshe idanun sa yayi yana sauke ajiyar zuciyar I wish she's here yafada cikin zuciyar sa amma lokaci yana zuwa Zaku sha mamakin na idan har hakuri na ya kare,, haka ya kwana juyi dayayi niyyar kiran wayar ta saiya fasa vayason daga hankalinsa amma kuma zuciyar sa na bukatar jin muryar ta don samun nutsuwarta,, Bayan idar da sallar ta basu koma bacci ba kitchen ta nufa inda suka shiga hada break fast sai karfe takwas da minti goma suka gama Wanda harda abincin bakin dazasuyi daida ta hadashi ta zuba cikin warmers saanna ta wuce dakinta inda didde ta shiga Gyara ta kamar yadda suka saba sai wurin karfe Tara saana duka fito ta bata hadin safen ta sha kafin ta fita da sauri maryam ta sanya key cikin kofar ta don tasan zai iya ritsa ta kamar yadda ya saba,,saida ta sanya kayan ta afin ta bude kofar gaban mudubi ta koma ta shiga taje gashin kanta gaba dayanta ta chanza cikin kwana biyu tayi matukar kyau da haske ga santsi da sulbi daya biyekan fatar ta har gashin kanta shiyasa akoda yaushe bakinta bazai gajiba wurin yiwa ubangiji godiya ba,, Da sallama ya shiga cikin gidan bayan sun gama gaisawa da malam,,saida aka bashi izini kafin ya shiga cikin dakin dauke da sallama a bakinsa matar malam ta amsa tana washe baki maraba lale da ango dukawa yayi har kasa ya gaidata tana amsa wa cikin sakin sakin fuskar tareda tambayar inna,,suna lafiya tana gaidaku,, Mikewa tayi ta fice daga dakin tabasu guri,ganin haka ya sanya shi kallonta sanye take da kayan bacci masu matukar kyau da laushi gashin kanta yasha Gyara Wanda ta daure shi da rebom kalarkayan light blue,,mikewa yayi ya isa inda take ya zauna kujerar dake kusa da ita ya zauna shiru kawai batareda yayi mata maganar ba kamar yadda yayi niyya yayinda ita kuwa ko kallon arziki bai isheta ba tana ta karatun novel dinta har malam ya shigo sanan ya ajiye tana kauda fuskar ,, Gyaran murya yayi yace toh safina ba mijin kinan anjima da dare zaa kaiki gidansa don dazu yazomin da maganar abarki sai ya Gyara gida sinaga babu amfanin hakan tunda zaman aureni zaikai ki bawai zaman kyale kyale ba saboda haka zakiyi hakuri abunda yakeda shi zuwa nan gaba saiya Gyara miki,, Toh malam ta masa fuskar babu yabo ba fallasa a zuciyar ta kuwa cewa tayi anzo wajen dama haka nake jiran zaka gane shayi ruwane darajar malam kake ci dama ,, Zaune take aparlon ta kurawa TV udanu kamar da gaske kallon take gaba daya hankali ta yanaga jiran shigowar shi tundata shirya take zaune amma shiru babu alamun sa gashi har su mommyn sun fito mikewa tayi jiki sanyaye ita ma suka tafi rakiyar su har bakin mota mommyn hassana na kara jaddada mata abubuwan data gaya mata harta shige motar suka tafi so take ta tamvayi ya Khalil din amma wazata tambaya tasan dashi mommyn tace zasu tafi amma gashi ko breakfast baiyi ba ya wuce kenan,, Wunin nan haka tayi shi babu walwala gar sai da yamma zuwansu anty hafsat matar babanta da iyayen ta sunzo Allah sanya alheri biki ,, kafin ta dan sake yayinda ita kuma sai janta a jikinta,, Sai a lokacin tasamu kebewa da iyayen ta har abba yake gaya mata abunda ya faru bayan rabuwar su tunda illiya ya zagaya masa layer nan gaba daya yaji duniyar ta chanza masa baya mantawa a lokacin harta da illiya gasa ganeshi yayi nuni yayi masa da hanta daya nufi ta Karya sake waigowa garin Kano aikuwa tunda na miki hanya babu musu nake tafiya kwana na biyu chur ina abu daya saidai inda na samu inci in wani ya tausaya min,,a kwana na biyun ne na iso garin jos daidai camp dinsu na bitar alhazai a lokacin na hadu da baban hafsat ya tsaidani cikin hukuncin ubangiji banyi masa musu ba ya ganeni amma ni kuma Sam bangane Shiva yayi ta kokarin tunanin kwana biyar dasuka wuce na kawo masa dollars da sarkar white gold da sunan chanji,, Ganin bani cikin hankalina ya sanya shi lafiya dani gidansa Wanda yake mazaunin garin yola ne kasuwanci me kaisa garin Kano ,, Iya zaman danayi Allah baisa na samu lafiya ba Sam na manta daku da rayuwar Ku gaba daya harna zamo dan gidan acikin gidan inda yarsa taci gasar kartun zata wuce kasar misra don cigaba a lokacin ne kuma mahaifinta ya hadamu aure inda akayi muka wuce chan da zama nima ya dorani a harkar tasu ta sai da gwal inda ni nake yo musu oder ana turawa Nigeria Saanan ya bani kudi na ya kara mun da wasu nin kin su ,cikin lokaci kankani Allah ya buda min sosai arziki ya bunkasa har lokacin da muka hadu da ummi take chan wannan shine abunda ya faru don haka maryam ki riketa da hannu biyu tamakr ummin ki Hafsa batada matsala Sam Ku zauna lafiya ,, Hawayen ta share tana murmushi tace insha Allah abba zan sauke ta tamkar ummi,, Yawwa Allah yayi miki albarka soasai yayi mata nasiha mai ratsa zuciyar databi mijinta fiyeda yadda ta taso taga ummi nayi duk wani abu na bacin rai ta gujeshi dayiwa mijinta ,,sosai ta sha kuka kamar kar su rabu jitakeyi inama gobe tabisu sutafi amma babu hali aure ya hana,, *mrs noour*โœ๐Ÿป๐Ÿ˜˜ [7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *๐Ÿด๐ŸดKARFIN IKO๐Ÿด๐Ÿด* ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ Written & story by *@PHEEYMARRH*

Chapter 23 of 32