Share this page
banyi ma to nace banyi wayar da ita ba,, Cikin bacin rai tace inna kiyi hakuri tambaya ce kawai nayi a matsayin na mahaifiyar ta wacce Allah zai tsiyar ranar hisabi ,ya kuma tuhuma ni akan tarbiyyyar dana maryam wacce amsa kike da ita wacce zan bashi,, Ihun inna ta saki da karfi tana cewa na shiga uku ni laraba mai keke nufi dani shatu cha nake da izinin Ku mero ta tafi aikatau eyeeh,, Aa inna ummin ta katsae ta itama cikin fusata domin taga abun na inna babu kara gwara itama tayi mata in yaso dan nata dayake taimaka musu ya dena kawai,, Mikewa tsaye tayi duk da ciwon datake ji a jikin ta tace inna kar ki manta yarinyar nan marainiya ce mu kadai ne gatan ta mahaifin ta kafin ya rasu mu yabar wa amanar ta,, amma sai kika maida abun tamkar wani *karfin IKO* ne kike dashi akanmu ikon ki dai yasa maryam tafiya aikatau amma badai da yawo naba ,, Wai kuwa inna kin San matar nan kuwa karuwanci take kai yayan mutane kuwa da sunan aikatau?,, mamakin ta kasa boyuwa yayi don a tunanin ta ummi ta riga da taji batan maryam din Kamar yadda hajiya ladi ta gaya mata,, amma dayake yar tijara ce cike da borin kunya tace karuwanci ko mugun hali irin naki mai wuyar bari hankalin ki ya kwanta tunda kin bata umarni ta kuma bi data dauki tawa maganar da yanzu muna sakaran kudin wata cikin satin nan kuma indai yawon duniya ne Ke zata debo wa abin kunya bani ba,, A razane ummi ta waro idanu waje wadannan hayaawe suke tsiyaya daga cikin su tace me kike fada inna ban gane nufin kiba ina maryam din take ina na tura ta ,ta jero wa inna tamabayer alokaci daya,, zarzzare idanu ta shiga yi da dana sanin maganar data fada kafin tayi maganar suka ji sallamar makociyar su wanda babu wanda yaiya amsawa Acikin su har ta karaso tana tambayar lafiya,, Ummi bata saurare ta ba ta juya gurin inna tace ki fada kun inda kuka kaimin yata ni zan nemo ta duk inda take maye amfanin zaman dan akeyi dake marar riba sai tarin bakin ciki,, da sauri halima ta rike ummi tana bata hakuri lalle tasan inna takai ta makura shiyasa ita kanta tayi bakin cikin tafiyar maryam aikatau balle kuma ummi,, ganin halima na bawa ummi baki ya kara tinzura inna tace zaki sha mamaki na kuwa a zuciyar ta,, yayinda a fili cikin kukan munafunci ta gayawa halima abinda hajiya ladi ta gayama ta ta dora dacewa yanzu wannan yar maiye laifina anan,, Sallati ummi ta saka wanda bata kai ga karasa shiba ta fadi nan kasa numfashi sama sama,, *US* Ta fi awa uku a dakin kafin tana durkushe taci kuka har ta gaji idanunta wadanda suke fararen kal Kamar madara sun rine sunyi jazur saboda kuka yayinda kowacce addua tazo bakinta karan ta take kawai,, Chan taji motsin bude kofa kirjinta ya tsananta bugawa jikinta babu inda baya rawa,, daya daga cikin wadanda suka kawotane ya shigo hannun sa dauke da Leda fuskar nan babu alamun rahama,, dad'a kankame jikin ta tayi wuri daya tana tsananta addua,karasowa yayi har gaban ta ya aje mata ledojin gabanta,, Muryar a kausashe yace kici abinci ,ki saka kayan nan kafin minti goma saba magana ta tana daidai dana dora bindiga yayi akanta tareda jinjina kai ya mike ya fice tareda rufo Kofar da key,, Wani marayan kuka ta saki tareda jawo ledar lafiyayyan yourghout ne babban gora sai dayan take away din fried rice ce da neman kaji a sama duk da yunwa takeji amma haka ta rufe ta ajiye,, datar ledar kuma doguwar jallabiya ce baka da karamin gyalen,addua tayi ta zura jallabiyar akan kayanta batareda ta cire ba ta daura gyalen kanta,, tunawa datai da gargadim sa yasa tayi sauri jawo ledar abinci tayi addua ta fara ci tana kuka,, minti goma bai Dada akai ba ya dawo yace ta biyo shi,kasa mike wa tai gaba daya tsoro ya gama cika ta sai daya zaro bindiga sanan ta mike kuka take sosai mai tsuma zuciyar me sauraro amma dayake basuda imani babu wanda ya tausaya mata haka suka tasa Ke yarta kowa dauke da bindiga suka shiga mota suka bar gidan,, *mrs noour ce*โœ๐Ÿป๐Ÿ˜˜ [7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *๐Ÿด๐ŸดKARFIN IKO๐Ÿด๐Ÿด* ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited by๐Ÿ‘‰๐Ÿป *oum Zahara*๐Ÿ˜ Dedicated 2my lil sis๐Ÿ‘‰๐Ÿป *Maman Sultan*๐Ÿ˜˜ ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู… *~Masoya ina matukar da godiya gareku,sakon addu'oe Ku da shawarwari Ku suna sanya ni farin ciki,ina matukar godiya Allah ya bar kauna(ameeeeen)~* *love u soooo muccchh๐Ÿ˜š๐Ÿ˜* ๐Ÿ…ฟโž–2โƒฃ3โƒฃ lokacin da ta isa asibitin yayi daidai da fitowar likita daga emergency,mommyn tabi shi zuwa office Kamar yadda ya umarce ta,, dagowa yai daga rubuce rubucen dayake yi fuska sake ya soma mata bayani akan ta kwantar da hankalin ta bawani damuwa bane zai farka zuwa anjima,, godiya tayi tareda Mikewa wanda yayi daidai da karasowar daddyn cikin office hannu ya mikawa likitan suka gaisa sanaan ya kara yimai bayani,, godiya daddyn yayi kafin yace zamu iya ganin sa, likitan yace babu damuwa amma sai ankawo shi daki tukuna, sai dai yan sanda nason ganin wani nashi tun dazu,, OK babu damuwa daddyn yace duk atunanin sa ko accident ne Khalil din ya samu tunda mommyn batayi masa bayani ba,, kai tsaye gurin yan sandan suka nufa wadanda Ke Kofar emergency room din,hannu ya mika musu kafin yace shine mahaifin Khalil wannan kuma mahaifiyar shi,, anan yan sanda sukai musu tambayoyi inda mommyn ce Ke bada amsan abunda tasan ya faru ta kara da rokon su akan binciken maryam,, ganin hotunan ta suka bukata inda mommyn ta nuna musu suka dauka a waya,, dole daddyn ya bisu station Kamar yadda suka umarta akan case din gano inda maryam take,, yayinda mommyn ta zauna akan kujerar tareda buga tagumi tana tunanin ina maryam aka kaita ,waya dauketa ita da take adduar Allah yasa tazamo sirikar ka sai gashi wannan mugun abun ya faru,, daga hannu sama tayi tana rokon Allah daya tsare maryam aduk inda take,, Gudu suke sosai a motar basu tsaya ko ina ba sai national airport na USA,, waya banga yayi ma alhaji ya gaya mishi gasu a airport,, dariya yayi yace gud aikin Ku na kyau abunda nakeson da Ku kada Ku yadda ko Kafa daya ya raba tsakanin Ku zata iya guduwa ko bayi ne lalle Ku bita Ku sanya ido sosai a kanta ,, cike da girmama wa ya amsa toh angama oga ya kashe wayar,ita kuwa tana tsakiya a takure da jikinta tayi kukan harya daina fitowa sai dai hawaye kawai dake kwarara daga idanun ta,, bude Kofar sukai tareda fitowa dukkansu suka tasa ta a gaban bayan mugun warning din dasu kayi mata,, Shigar su yayi daidai da saukar jirgin su dad wanda su kuma nasu sai bayan awa daya zai tashi,, Chan baya suka zauna tareda umartan ta data zauna itama suka sanya ta a tsakiya,, *Kano* hamdalla inna tayi a zuciyar ta amma a zahiri sai sallati takeyi yayinda halima ta fita da gudu don neman taimako,, cikin ikon Allah tana fita sukai kicibus da maigidan ta wanda yake kokarin shigowa ciki, don suna jiyo abunda Ke faruwa saboda Katanga ce kawai ta rabasu juyawa tai suka koma tare hankali tashe, ganin halin da ummi Ke ciki yace kawai halima su kamata akaita asibiti bari ya fara fita ya samo mota kafin su fito,, dakin ummi halima ta shiga ta dauko hijabin ta tasanya mata suka kamata tareda inna wacce Ke ta adduar mutuwa ga ummi,, adaidaita ya samu suka shiga kai tsaye asibitin murtala na gwnati suka kaita aka amsheta zuwa emergency,, Kusan awa biyu likitoci na kanta kafin asamu numfashin ta ya dawo daidai sukai mata allura,, daki aka bata don hutawa sanan likita ya bukaci ganin yan uwan ta malam sani ne da inna suka bi bayan likitan yayinda halima ta wuce dakin da aka kwantar da ummi,, Sai da yagama rubuta a farar takarda kafin ya dago ya mikawa malam sani takarda yace wannan zaku siya yanzu ana bukatan su da gaggawa,, Amsa malam sani yayi yana godiya,ya dora da tambayar mai Ke damun ta yaya jikin nata yake,, gyara zama yayi akan kujerar yace agaskiya jinin ta ya hau sosai amma munyi kokarin bata duk wani taimako daya dace sai tests da zamuyi mata anjima,, Jinjina kai malam sani yayi tareda adduar Allah yabata lafiya ameen inna ta amsa da sauri tana matsar hawaye na karya,, *USA* Sai da suka jira aka gama binciken kayan su kafin suka fito su dad ne gaba yana rike da hannun mom yayinda Khalil Ke baya rike da trolleys yana ja suka shiga awt room din idanun sa akan maryam ya fara sauka wacce Ke takure a tsakiya bugun numfashin sa nan take ya chanza,, tsayawa yayi yana kara kallon ta tabbas itace zuciyar ce ta tabbatar mai ya zai manta wannan kyakkyawan innocent face din,,amma maiyasa kullum tana cikin damuwa ne ya tambayi zuciyar shi,, Kiran dad ne ya maido shi daga tunanin dayake yi da sauri ya karasa wurin su,, cike da damuwa dad yace yanzu daddyn Khalil mukayi waya yana asibiti so ga driver nan ka wuce chan gidan mu zamu karasa asibitin,, Jinjina kai Khalil din yayi cike da jimami yace Allah ya bashi lafiya ,suka amsa da ameen,tare suka fita dad suka hau texy yayinda Habib ya zuba kayan su a boot ya shiga motar,, har driver ya tada motar jin an kira masu tafiya yasa shi tunowa da maryam ,lallai ya kamata kayi mata magana at lists ko sunan ta kasani,murmushi yayi ya cewa driver ya jira shi tareda fitowa ya koma ciki wanda yayi daidai da mikewar su don tafiya,, tafiya take Kamar wacce Ke tsoron taka kasa jikinta ya riga yayi sanyi ta hakura ta gama tsinkewa da lamarin duniyar nan don ta rigada ta fahimci alhaji yasa aka kamata,, mai Khalil yake nufi dayi mata haka dama bason ta yakeyi ba ko kuwa shima yana Hulda da alhaji ne,, Assalam alaikum sallamar Habib ya katse mata tunanin datake ina tasan muryar nan da sauri ta waigo tana ware idanu waka wadanda sukai jazur,, kallon juna kawai suka cigaba dayi batareda sunyi magana ba yayinda su banga Ke cike da tsoro kardai wani ne yabiyo su,, gyara tsayuwa yayi tareda folding din hannuwan sa a kirji yace malamar ko bata jin Hausa ne yayi maganar da murmushi dauke a fuskar shi,, Ajiyar zuciya ta saki a hankali ta amsa mai sallamar,tai maganar wacce iya kacin ta lebban ta,, sai kuma hawaye ya biyo baya,, ganin haka yasa banga shi cewa hajiya ya kamata mu hanzarta yayi maganar cikin ladabi as if irin yarinyar ogan su ce,, kasa mutsawa tayi tana tunanin mai zatayi,,wace dabara gareta yanzu tana wani motsin suna tare da bindiga su,, juyawa kawai tayi taku daya ana biyu muryar Habib ya dakatar da ita yana cewa pls ki dan bani just two min's,, chak ta tsaya batareda ta juyo ba ,karasowa yayi kusa da ita ya bude Baki da niyyar yin manga sai suka ji ana sanawar jigiya da katon hotunan ta ta kowacce tv dake wurin,, daga kan dazata yi sai ta hotunan ta ne,ajiyar zuciya ta sauke da karfi ta juyo fuskarta dauke da murmushi ta bude muryar tace kalli chan,, sai a lokacin ya daga kai ya kalli tv wacce pic dinta ya cikata da sauri ya juyo don tabbatar da abunda ya gani sai yaga bata,, waige ya shiga yi sai yaga ana janta da karfin har suna kokarin fita,,da gudu ya kwasa shima cike da kware wa ya bi bayansu yana zaro bindiga sa wacce ya tsoka a bayan wandon sa,,, *kuyi hakuri banida chaji shiyasa na turo muku haka anjima ma cigaba*๐Ÿ™ *mrs noour ce*โœ๐Ÿป๐Ÿ˜ [7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *๐Ÿด๐ŸดKARFIN IKO๐Ÿด๐Ÿด* ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited by๐Ÿ‘‰๐Ÿป *oum Zahara*๐Ÿ˜ Dedicated 2my lil sis๐Ÿ‘‰๐Ÿป *Maman Sultan*๐Ÿ˜˜ ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู… ๐Ÿ…ฟโž–2โƒฃ4โƒฃ ganin Habib dauke da bindiga ya jawo hankulan securities dake wurin da sauri suka rufa musu baya,,wani irin mugun tsalle yaye sai gashi gaban banga wanda Ke Jan maryam Kamar jaka daga bindigar yayi tsakiyar goshin sa cikin shakakkiyar muryar sa yace Ure under arrest,, Ganin securities din wurin na karasowa yasa banga hankad'a maryam jikin habib ya fada mota suka jaa a guje,,, binsu yayi shima a gujee cike da kware wa ya shiga Harbin tayar motar sai dai kash babu wanda ya samu motar saboda mugun rukon da maryam tayi masa ya hana shi saitin da kyau,, securities din yayi ma bayani a gajarce cikin hanzari suka rufa musu baya,, Juyowa yayi yana kallon yadda ta cukwikuye shi jikinta sai rawa yake bindigar ya maida bayan wandon sa yasa hannuwan sa biyu akan kafadar ta ya dago da ita tareda tsira mata idanu cike da tausayawa,, heey calm down pls Ure safe now ya fada cikin Kamar me rad'a,, wani sabon kukan ne ya kufce mata wanda tasan na tsan tsan farin ciki ne kwantar da kanta tayi gefen kafarda shi yayinda shi kuma ya kara rungumar meta cikin shi domin gaba daya jikin ta yaki daidaita saboda razanar datayi na Karar harbin bindigar,, restaurant din dake cikin hotel din ya nufa da ita ruwa kawai ya siya suka fito saida ya isa har wurin motar dazai shiga saanan ya janye ta ajikinsa badan yaso ba jiyake inama su dawwama ahaka,, bude murfin gorar yayi tareda kai bakin gorar ga bakinta,,cikin nutsuuwa ta fara sha saida ta wuce rabi kafin ta janye bakinta tana ajiyar zuciya da karfi hannu ta saka ta dauke hawayen da suka ganagro mata bisa kuncin ta,, Yaya kike ji yanzu ya tambaye ta,, Alhamdulillah ta bashi amsa a sanyaye muryar ta na rawa har yanzu a tsorace take itadai burinta su bar wajen kawai,, shima lura da hakan yasashi cewa shiga mota muje sai mu sauke ki gida,, gyada kai tayi tareda jiga ciki ya rufe murfin motar shima ya zagaya ya shiga kusa da ita ya zauna a baya ,, driver ya tada mota suka bar wurin,, Sun danyi nisa ya juyo yana kallonta cike da tausayi yace inane gidan Ku,da sauri ta dago manyan idanuwan ta tana zare su gida kuma ta tambayeshi a sanyaye,, Wani irin abune yaji ya taso mai tun daga tsakiyar kansa har yatsan kafar sa,,wadannan idanuwan masu matukar kyau suna burgeshi musamman yadda Zara zarar gashin idanunta suka jike da hawaye sai suka kara yin baki tareda sheki kukan ma kyau yake kara mata,, murmushi yayi yace karki damu bari mu sauka inda zan sauka saboda nima zuwa na kenan anjima dole zamu police station don gano inda iyayen ki suke,, gyada kai kawai tayi tana murmushi hade da hawaye Allah sarki inama tana da gatan iyayen dabai ganta a halin datake ciki ba Allah sarki ummi kina ina ne ummina kin barni cikin gararin rayuwa na shiga rayuwa ta tashin hankali yanzu shikenan saboda bani da gata fita ma saidai na hakura babu randa zan ganki kenan ummi na kuka ne ya kwace mata da karfin takeyi dukda ta dora tafin hannun ta akan bakinta amma sautin kukan nata yana shiga kunnuwan habib,, Wanda yakejin kukan har cikin zuciyar shi,,baya son ganin mace na hawaye dukda yake soja hakan yana sashi cikin matukar damuwa musamman nata da yake sauraro yanzu har cikin zuciyar shi Kamar ana tsantsagan zuciyar tashi da kibiya,, Kasa daure wa yayi kawai saiya matsa kusa da ita tareda dora kanta bisa faffadar kafarda shi yasa hannu ya zagaya nisa tata kafadar ya bubbuga ta ahankali cikin sigar lallashi,, har suka iso tana kuka idanuwan a rufe saida yayi magana kafin ta bude su da kyar saboda zafin da sukeyi mata sakamakon kukan data yini yi fita yayi tareda miko mata hannun sa alamun ta kama,,mika hannun ta tayi takama ta fito tana kallon sa cike da kauna yayi mata taimako da harta mutu bazata taba mantawa dashiba inama ace dan uwanta ne na jini matsayin yayan ta yake uwa daya uba daya datafi kowacce yarinya gata aganin ta ,, Yayinda shima yake tunanin ina ma Allah ya mallaka mishi ita a matsayin matar shi ya dade yana adduar Allah ya hada shi da mace Kamar ta sai gashi Allah ya hada su yau amma bazaiyi gaggawa ba sai yasan meye hadin ta da wadancan tukunna Karar rufe murfin mota ne ya dawo dasu daga tunanin da sukeyi da sauri suka waiga don ganin waye,, kirjin maryam ne ya buga da karfi nan take jikinta ya fara rawa tamkar mazari sakamakon tozali da idanuwan ta sukayi da safina ,, muryar na rawa tace safina,, tayi mamakin ganin su tareda habib amma dayake yar girman kaice saita basar irin basa gabanta dinnan dukda ma'aikatan dake gurin kin kiran kowa tayi sai maryam cike da gadara irin gidan ubanta dinnan ko mijin ta tace kwaso mana kaya zuwa dakina yanzu nana ta fada tana watsa musu kallon banza ita da habib din wanda ya kauda kansa gefe shima yayi Kamar baisan da zuwan ta ba,, Saidai tunani yake yaakayi safiya tasan maryam haka itama abin ya daure mai kai amma yanzu ba lokacin tambayoyi bane saita huta tukunna,, Yayinda maryam ta kasa motsa koda yatsan tane saboda mamakin yadda akai ta dawo gidan su Khalil taso ace ta bar gidan nan kenan har abada koda kuwa soyayyar Khalil din zata zama barazanar ga rayuwar ta har saida Habib din ya matse hannun ta da karfi kafin tayi firgigit ta dawo tunanin ta sake daga idanu tayi tana kallon gidan tabbas gidan ne toh Maiya kawo habib din nan har yace gidan sune nan din,, gyada mata kai yayi da murmushi dauke akan fuskar sa cikin shakakkiyar muryarsa yace ki shiga ciki ki huta zamuyi magana anjima OK ya kafeta da idanu,, kasa tayi da kanta itama tana murmushi kasa kasa ta gyada mai kai domin wani irin nauyin sa takeji saboda irin kallon dayake yi mata,, Jan kafa tayi a hankali ta nufi kayan su safina zata dauka da sauri ya karaso ya ce barshi kawai zan dauka kije kawai ki huta,, Juyawa tayi tawuce cikin gidan jiki a sanyaye tana yiwa Allah godiya na kubutar da ita dayayi karo na biyu kenan saidai wani sashi na Zuciya ta tana mai bakin cikin sake dawowar ta gidan su Khalil,, koda ta shiga mommyn ta fara neman yan aiki suka sanar da ita tana asibiti Khalil ba lafiya,, samun kanta tayi da tambayar meyake damun shi cike da damuwa hankalin ta duk ya tashi, suka bata amsa da basu saniba mommyn dai tunda ta fita bata dawo ba,, gyada kai tayi ta juya zuwa dakin ta dukda haushinsa datake ji amma hakan bai hanata shiga cikin damuwa ba duk hankalinta saiya karkata gason ganin shi ,, bathroom ta shiga tareda sakar wa kanta shawa ta dade kafin ta samu natsuwa ta yo wanka tareda dauro alwalar ta fito,, jallabiya ta dauko ta zura tareda sanya hijab ta kabbara sallah,, Har daddyn ya dawo baa fito da Khalil ba sai bayan kusan awa daya aka fito dashi tareda kaishi dakin hutu suka mike tare din ganin shi yana kwance idanuwan sa rufe yana bacci hannun sa dauke da Karin ruwa,, Matsawa sukayi kusa dashi yayinda mommyn ta zauna gefen gadon tareda kamo dayan hannunsa ta damke danata sannu take faman yimishi Kamar idanunsa biyu hawaye na silalowa daga idanun ta ganin yadda ya koma cikin awanni yayi rama sosai koda yake baccin kasan hankalinsa baa kwance yake ba,, daddyn ne ya shiga bata baki har tayi shiru,, suna nan Zaune dad da mom din safina suka karaso cike da murna da jin dadin ganin juna suka rungume mommyn da mom hakama daddyn saida sukayi musabaha saanan suka rungume juna kafin aka gaisa da tambayar ya mai jiki,, sukace Alhamdulillah jikin da sauki,,zaman su Baifi da minti goma ba aka kira wayar daddyn daga police station suka sanar dashi an ganta saidai baa samu nasarar kama wadanda suka yi kidnapped dinta ba amma an dauki number motar su don haka suna bukatar su anjima a station din wanda ya ganta zai kawota anjima,, godiya daddyn ya shiga yi musu ya tabbatar musu da anjima zaizo ya kashe wayar,, Cike da farin ciki yake sanar musu anga maryam din,, Wanda yayi daidai da motsawar Khalil don jiyayi Kamar shi ake gayawa labarin ganin nata bude idanu ya somayi a hankali har ya waresu kan mommyn wacce tafi kusa dashi,, mika hannu tayi tana shafa sumar kanshi wacce Ke kwance lub lub mai matukar laushi da sheki tace sannu son Yaya kakeji,,, Kallo yabi dakin dashi kafin zuciyar shi ta tuno masa abunda ya faru,,a razane ya kike dukda jikinshi babu karfi wanda saida yabawa su mommyn tsoro da karfi yace mommyn maryam maryam ta bata saboda ne I have to go now mommyn zan nemota kafin wani abu ya faru da ita,, Dad ne ya matso kusa dashi ya dafeshi cikin kwantar da murya yace ka natsu son an riga an ganta tana nan lafiya kalau babu abunda ya faru da ita,, d'ago idanunsa yayi masu matukar kwarjini ya kafe dad dasu,,shima dad din jinjina kai yayi alamun tabbas Hakane ,, sai a lokacin ta dan samu natsuwa amma duk da haka burin sa ya daura idanunsa akan kwayar idanun ta komawa yayi ya kwanta ya lumshe idanun anya kuwa maryam zata yafemai abunda yayi mata kuwa,lalli koda ta yafe mai shi bazai yafe ma kansa ba,, I relly love u my mad girl murmushi yayi tunowa dayayi da ita,, da kyar su banga suka sha suna shiga ciki suka sanar da alhaji yadda akayi shima ya tsorata cikin tashin hankali yace suyi maza su chanza gurin zama kafin yasan abunyi ,, kwashe kayan da zasu bukata sukayi suka hau wata motar suka fice daga gidan,, koda ta idar ana wurin bacci gajiya ya dauke ta,, Ko rabin awa batayi ba taji saukar ruwan sanyi a fuskarta a zabure ta mike tareda kwala ihu dama mafarkin su banga takeyi sa gashi dan tsabar rashin imani safina ta tashe ta ta hanyar watsa mata ruwan sanyi,, kasa tayi da kanta rana duban jikinta hijab dinta ya jike dagowa da kanta tayi tana kallon safina wacce Ke tsaye tana watsa mata kallon banza ganin yadda ta karayin wani fresh da kyau jefa mata gorar tayi a fuska da sauri maryam ta dauke gorar saboda baa rufe take ba,, Keeh useless girl har kin samu guri kin manta da dokokin na how dare u dazan saki aiki kisaka yan aiki kuna saboda Ke karuwar banza ce bakisan ki shirya min kayana ba saina biyoki amma hanyar karuwanci babu wanda bakisani ba basai an nuna miki ba ko maza ki tashi kafin mu gama cin abinci ki tabbatar da kin gama gyara min kaya na ta watsa mata harara tareda Jan tsaki ta fice tana cewa komai yazo karshe ai tunda dad yazo kin kusa komawa kazamin gidan naku indaina ganin wannan fuskar taki,, Mikewa maryam tayi a hankali tana hawaye shikenan ta dawo kuma wani sabon tashin hankalin zai dad'u ohh ni Allah ka kawo wa rayuwa ta dauki ta fada a hankali saida ta chanza kaya kafin ta nufi dakin safina ta fara shirya mata kayan harda na kawar ta dasuka zo tare,, Ganin kwanciyar bazata yimai ba ya bude idanu tareda kafe su kan fuskar mommyn yana langabar da kai alamun yanason wani abu,, ganin haka yasa mommyn matsowa tace ya akayi son ko kana jin yunwa ne,,tayi tambayar cike da kulawa,,girgiza kai yayi a hankali kafin yace mommyn muje gida haka pls inason hutawa a gida,, kafin tayi magana dad yace Aa son kabari ka kwana tukunna ka kara samun sauki,, Watt ya fada a zuciyar shi ai inya kai gibe bai ga kwayar idanun maryam ba mutuwa zaiyi yanzu haka shi kadai yasan mai yake ji ajikinshi dama zuciyar shi,, da sauri yace noo dad dakin mommyn nakeson hutawa,,ya fada a shagwabe,, OK babu damuwa daddyn yace suka mike tareda dad suka fuce zuwa dakin doctor don neman sallama,, yana ganin haka ya mike shima ya zauna don kada doctor ma yace wani abu,, murmushi mommyn tayi wadda ta gane abunda yake son gani a gidan ita kanta tanason ganin maryam din don tabbatar da lafiyar ta,, tareda da likitan suka shigo inda yayi farin cikin ganin Khalil zaune Karin ruwan aka ciremai wanda ya kare ya sake dudduba shi kafin ya rubuta musu yace Yasu iya tafiya amma ya ki yaye saka muguwar damuwa lokaci daya a zuciya don ba karamin

Chapter 11 of 32