hassana riko hannun sa Wanda ya sanya shi juyowa a fusace dariya tashiga yimasa tana fadin yadai son lafiyar ka kuwa control u self baka ganin taron harda family safina ne pls ka wuce dakinka anjima ucan see her okay,,
Batareda jiran mai zaice ba ta shiga tafiya da hannun sa rike a nata alamun ya biyo ta babu yadda ya iya dole yabi bayanta,,
Anan parlon maryam tace abarta ta dinga kallon mutane daga kwace dole ummi ta zaunar da ita bisa kujera dukda ba wani Abu rakeji ba awai sai rashin karfin jiki,,
Mommyn ce ta karaso kusa da maryam din ta rungumeta ta gefe tana ta ba kanta zuwa wuya tareda tambayar ta Yaya jikin nata yanzu maiyake damunta,,
Murmushi tayi tace mommyn wallahi babu abunda yake damuna am alright,,
Mommyn hassana ce ta shigo dakin tana tambayr aa anty waiyaya baki fara ba ga baki sin hallara da alama tun dazu ina amaryar ne,,
Tsaki mommyn taja da karfi bari kidai Wai yarinyar nan marar tarbiya da mutunci itada uwarta sai Bayan mun dawo daga asibiti suke kirana Wai safina bata ma kasar tatafi us yin registration saidai muyi taron mu inta dawo Bayan daurin aure ayi tarewar,,
Whatt mommyn hassana ta fada tana zaro idanun waje anty da gaske kikeyi ko wasa ne tafiya kuma ta fada cike da tsannanin mamakin safina,,
Kauda fuskar mommyn tayi tace zan miki Karyane sakwan da suka aiko min kenan dazu,,
Sallati suka saka tareda ummi ni kuwa ko ajikina don nasan zata iya aikata abunda yafi ma haka indai safina ce,,
Mommyn mai kike fadane safina tabar kasar nan Bayan tasan da sharidin mu suka tsinkayi muryar ya Khalil a bayansu ransa a matukar bace,,
Shiru kowa yayi babu Wanda ya amsa masa,,
Jinjina kai yayi cike DQ bacin rai yawuce daga dakin,,
Toh yanzu ya zamuyi kenan anty ,,mommyn hassana ta fada jiki a sanyaye,,
yaya zamuyi kuwa mu samu mu sallami baki tukun wannan kuma so daddyn ya dawo naji yadda zaayi amma wallahi wallahi wallahi na rantse inhar Nina haifi Khalil vashi ba auren safina wallahi,,
Cikin dakiya da dauriya mommyn suka gabatar da Fulani day dinsu domin kuwa sosai maganar tafiyar safina Ke kona mata rai yayinda taron baiyi wani armashi ba tunda babu ango babu amarya,,
Sai gab da magarib su daddyn suka shigo tareda abba da hajiya sai alhaji Wanda dawowar su alhajin kenan daga Egypt wurin check up dinsa,,,
Parlon sama mommyn ta bude musu yake a gyare don saboda auren alhaji ya dawo bawai don ya gama abunda yakaisa ba,,
Saida sukayi sallar magrib suka ci abinci saman suka wuci masallaci sai Bayan insha I suka dawo tareda Khalil Wanda har yanzu fuskar nan tasa kamar Wanda akayita bishara da Shiva wuta ko alhajin duk yadda yaso yayi masa was an nashi na jika ki yayi tun a lokacin yasan akwai damuwa sosai,,
Shigarsu dakin hajiya tabi Bayan su rai bace itama don kuwa mommyn hassana ta rantafa mata duk halin da ake cikin harda kari akwai don ita Sam Dama batason wannan hadin,,
Nan hajiya ta kwashe yadda akayi tasanar da alhaji aikuwa ransa ya baci sosai yayinda daddyn yafi kowa bakin cikin da jin zancen nan shiya takura nasa dan badon Bayan sonshi ba amma shine zasuyi masa haka shiru yayi kawai yama rasa dawane baki zaiyi musu magana don yadda hajiya take wannan fadan yasan babu mai saurarar sa cikinsu,,
Abban maryam nama ya ringa basu baki akan a kira mahaifin yarinyar aji,,
Nan take alhaji yace maza daddyn ya fidda waya ya kira dad din safinar ,,
Aikuwa bugu daya biyu dad ya daga cike da faraa ya soma gaida daddyn shima yana amsawa,,
saida suka gama gaisawa saanan daddyn ya fada masa dalilin kiran nashi,,
Wani irin bugu zuciyar sa tayi Wanda saida ya dafe kirjinsa sallati yake daya Bayan daya hankalinsa a matikar tashe bai ce komai ba ya yanke kiran,,
Kallon mom yayi wacce Ke zaune tana cin abinci hankali kwace mai nake jine daga gidan su Khalil? ina safina ?
gaskiya ne abunda ake fada kokuwa ya kara shie yana daka mata tsawa,,
Ajiye chokalin hannun ta tayi ta na kallon sa shekekek tace eh hakan ne wani abin ya faru ne,,
Fidda hannu yayi ya dauketa da lafiyayyen mari abunka da tsohon soja saida ta kifa kasa gabadaya kanta jinshi tayi dimm ya daina aiki,,
Nuna ta yayi da yatsaa yace wallahi wallahi hajiya muddin yarinyar nan bata dawo gobe gidan nanba kafin daurin aure ba ki tabbatar da naki auren ma ya mutu,,
Yana gama fadar haka ya fice daga dakin zuciyar sa na bugawa da karfi wani irin zafi yakeji a kirjisa,,
Kai tsaye parking lots ya nufi tareda kiran driver ya shiga suka fice daga gidan,,
Sosai alhaji yake yiwa daddyn fada akan Yanke hukunci dayayi shi kadai Dama yaro bayaso hakama mahaifiyar sa toh gashinan tun kafin afara an fara saman Marsala,,
Shidai hakuri kawai yake baiwa alhaji,,
A haka dad din safina ya shigo jikinsa salube kallon daya zakayi masa kasan Bayan cikin nutsuwar,,
Hakuri ya shiga baiwa su alhaji akan bashida masaniya amma don Allah karsu damu gobe insha Allah da kanshi zai dawo da ita zaa kaita dakinta gobe komai dare amma don Allah suyi masa hakuri harda hawayen sa,,
*toh pa masoya maryam ya kuke gani*
*daga gobe ne,*,,,,π
*mrs noour*βπ»π
[7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *π΄π΄KARFIN IKOπ΄π΄*
π±π±π±π±π±
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
*HIKMAAH writers association*
Edited byππ» *oum Zahara*π
Dedicated 2my lil sisππ» *Maman Sultan*π
Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
π
Ώβ4β£9β£
Hakuri ya shiga baiwa su alhaji akan bashida masaniya amma don Allah karsu damu gobe insha Allah da kanshi zai dawo da ita zaakaita dakinta a goben komai dare kuwa,,
Amma don Allah suyi masa hakuri harda hawayen sa,,
Sosai abokin nasa ya tausaya masa wato daddyn musamman inya tuna yadda dad bashida burin daya wuce yaga ya aurar da safina musamman dayaga tasamu miji na gida tunda Khalil din ko babu aire mataayin yayan ta yake saboda abotar iyayen nasu sosai,,
Nan daddyn shima yasan ya baki suka baiwa alhaji hakuri amma fafur yaki yace Sam indai har gobe aka zo daura aure bata dawo kasar nan ba to wallahi aure an fasa shi angama kuma kenan,,
Haka dad ya mike yayi musu sallama saboda dare yayi jiki salube ya nufi motar sa Inda daddyn ya rako shi yana bashi karfin gwiwa da hakuri haka sukai sallama akan Allah ya zaba abunda yafi alhairi goben,,
Saida yayi hawaye a mota wannan wace irin jarabawa ce shi kuma tashi jarabawar kenan akan iyali ko yaushe burinshi yaga ya kyautata musu fiyeda kowa babu wani abu najin dadi da suka nema suka rasa amma sakayyar dazasu yi masa kenan,,
Kai tsaye sashen malam mahaifin sa ya nufa Inda koda ya koma gidan bayason ganin koda wulkawar mom ne balle ya dora idanun sa a kanta,,
Tun dayayi sallama ya shiga malam ya fuskanci akwai matsala damuwa sosai ta nuna karara bisa fuskar sa,,
Gaisawa sukai nan take sai hawaye dad ya Shiga zubar wa kamar karamin yaro,,
Malam bai nuna wata damuwa ba a fuskar sa sai dai har cikin zuciyar shi yana tausayawa dad ta bangaren iyali yana fuskantar wani hali dukda laifin gaba dayansa nashi yasha nunar masa amma bai ganewa sai gashi bai tashi ganewa ba saida lokaci ya kure masa,,
Nasiha sosai malam yayi masa taeda bashi shawar wari akan kula da tarbiyya da hakkin da Allah ya daura mai ya kamata ka gane wani abu abunda Ku masu kudin zamani ko ince yan boko baku gabewa shi gata da kuke gani ba shine yiwa 'ya'ya abunda suke so ba aa kula da hani da kuma lura da dukwani abu dayake alamtar rayuwar su na gaba shiyakamata kusa ido akai da tsawatar wa yanzu ka gayamin Ismail ribar mai kaci wurin gatata ta gashi tayi maka abunda ya nunawa duniya itadin bata dauke ka amatsayin mahaifi ba yau ga sakamakon abunda kullum nake yi maka nuni dashi kenan,,
Ya isheka nazari da hankali inkayi duba da yadda Ku nabaku taku tarbiyyar iya yawan Ku ban gajiya ba,,
Addua itace maganin da kuma babban toshe gurin gina turbar tarbiyyar yara,,
Toh amma tunda kunyi naku yadda ya kamata ta nuna maka tana da *karfin iko* akan kanta daku iyayen ta ,, toh nidin zan nuna muku nawa *karfin iko* inga Wanda zaija da hukunci na in ka fita ka turo min yaron nan habib,,
dole dad ya mike jiki salube gaba daya jikinsa da zuciyar su baya jin dadinsu yadda ya kamata amaawa yayi da toh malam zan turo shi ,Allah ya tashemu lafiya,,
Ameen malam ya amsa tareda sanya masa albarka kamar yadda ya saba kai kace baya cikin wani bacin rai,,(kira gareki yar uwa ya kamata duk wani laifi ko ita harzuka da yayanki zasu sanyaki ko su bata miki rai karki Gaza da yi musu addua domin itace takobin mumini Yaya tin suna kanana basuda wayon yiwa Kansu Ke kiyi musu saanan har girmansu kada ki gajiya akoda yaushe,,Allah kayiwa rayuwar yayan mu albarka kasa su zamto Yaya nagari masu amfanarwa ga daukacin alummar musulmiπ€²π»)
Koda yashiga cikin gidan dakin sa ya kulle kansa batareda ya nemi mom ba itama kuma dama da haushin sa a wuyanta itama batabi takansa ba gun yanuwanta ta kwanta wadanda babu wani cikinsu Wanda yake bata shawarar arziki saita tsiya,,
Washe*****gari*****
Kwaciyar ta tagyara kan cinyar ummi sosai take cikin tsananin farin ciki a yau hirar su suke tayaushe rabo hankalinsu kwance,,
Bayan kowa ya fayyacewa dan uwansa halin daya shiga bayan rabuwa sosoa kowa yayi ma kowa kuka cikinsu maryam taji mutuwar inna sosai nan tayi ta yimata addua tareda fadin nayafe miki inna Allah ya gafar tamiki,,
Saida gari ya fara haskawa sanan maryam da ummi suka mike domin fara hidimar biki maryam kitchen ta nufa kai tsaye yayinda ummi ta nufi dakin mommyn,,
Da sallama ummi ta shiga dakin mommyn,,
Saide hankalinta ya tashi ganin yar uwar tata tana kuka ,,Karasawa tayi kusa da ita ta zauna gefen gado ta dafa ta tareda soma share mata hawaye ,,
Lallashi tareda ban baki ta shiga yimata tasan duk bacin rai bawici akan bikin ya Khalil bane,,
Saida taga ta samu nutsuwar sosai sanan ta mike ta je kitchen da kanta ta hado mata lafiyayyen abun Kari ta kawo mata tursasa ta tayi har sai dataci abincin sosai saanan ta soma tamavyar ta maiyake faruwa ne mommyn maryam kike kokarin daurawa ranki wata damuwa,,
Share hawaye tayi cike da takaici ta soma maganar haba ummi ki duba irin wanna wulakanci da mutanen nan sukayi mana amma Wai daddyn Khalil ya nun min bani wani *karfin iko* akan dan dana Haifa saboda kawai inayi masa biyayya shine bamuda mutuncin dazai tuntubi raayin mu,,eyehh saboda Allah fa,,
Ajiyar zuciya ummi ta sauke tace wallahi ni na dauka wani abu ne ya faru ai hajiya addua ya kamata kiyi akan abunda zai zamana na alhairi bawai sanyawa ranki damuwa ba kuma maganar daddyn ai mijinki ne koda kinada *karfin iko* akan abunda kika Haifa baikai yanasa ba tunda dunkkan Ku karkashin *iko* sa kuke don haka addua kawai zakiyi tareda karfafawa dan nawa gwiwa har abun yazo ya wuce,,
Wallahi ummi ni har ga Allah bazan boye miki ba wallahi badon ganin idon ki ba harga Allah daya kenan ummi zuciyata tafi naam da tarbiyyar maryam musamman yadda yanzu asalin nata ya bayyana gata matsayin yace gareni akwai kuwa Wanda zaiso hakan fiye dani ,,
Dukda haka mommyn addua nan itace kadai maslaha garemu baki daya da yaran duka dai nakine kina iya zaba ma maryam miji duk Wanda yayi miki ni babu ruwana ciki,ummi ta karashe da wasa tana murmushi,,
Murmushi mommyn tayi tace ai zaku sani ne nan gaba wallahi nida yata zamu hade muku Kaine sai kun zama abun tausayi Allah yasa Khalil yayi gangancin amincewa da auren nan itama ta fada cikin wasa da dariya,,
Tare suka fito don tsayawa ga abunda zaa baiwa baki dukda maaikata sukayo haya tuni sun dade da fara aiki su a bayan gida,,
Tsaye take kitchen tana zuba kayan kamshin cikin tukunya wacce ta dora ruwan tea kamshin turarensa tajiyo Wanda ya tabbatar mata da yana kitchen din kasa waigowa tayi don tasan gabadayan idanunsa suna kanta ,,kokarin shiga store take ganin haka yasa shi maza ya shigo kitchen din ya sha gabanta ,,
Wani irin kallon yake jefanta dashi yayinda ita kuma dukta daburce wata irin kunyar sa takeji tadaban ayau g kirjinta fake tsananain bugs mata da karfi Wanda ta alakanta hakan dako kishin yau auren sane hakan yasanyata kauda kai gefe zat wuce,,
Hijab dinta ya rike da karfi Wanda ya sanyata tsayawa dole fuskar sa yakai saitin tata yace yaushe hearttee na tazama haka gaisuwar ma vazan samu ba ,,
Ina kwana ta fada a takaice batareda ta kalle shima ,,
Kara matsowa tayi kusa da kunnenta yace da kuwa nazo miki da labari ne mai dadi amma na fasa,,
Kara kauda fuskar tayi nana take ta turbune ta ta shiga gunguni labari ya wuci na aure kuma imba gulma ba ainasani, batasan tayi maganar har fili ba yaji,,
Murmushi yayi yace yawwa my hearttee shiyasa nake sonki saboda hakuri exactly maganar aure na ne amma bari sai an daura zamzo muyi maganar,,
Fisge hijab dinta tayi ta wuce store tareda bugo kofar hawayi ta shiga zubarwa kamar an bude tap gashi babu damar ta bude baki tayi dontasan zai ita jiyo ta ,,
Saida tayi kukanta ta koshi saanan ta fito ta juye ruwan dayake tafas a flask,,ta fice ranta bace batareda ta gama aikin ba don ranta a bace yake ,,
Manyan Manya mutane sun hadu ta ko ina domin daurin auren yan gata ya Kahlil da safina,,
*nagudu nayi baki sai anjima*ππ»ββπ€ͺ
*mrs noour*βπ»π
[7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *π΄π΄KARFIN IKOπ΄π΄*
π±π±π±π±π±
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
*HIKMAAH writers association*
Edited byππ» *oum Zahara*π
Dedicated 2my lil sisππ» *Maman Sultan*π
Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
π
Ώβ5β£0β£
Cike yake layin massallacin sosai da dankara dankaran manyan motoci dukda garin Abuja ne amma kai kana ganin yanayin motoci zaka gane tabbas yau daurin auren yan gata ne masu ji da naira,,
Daddyn da dad suna tsaye bakin masallaci suna gaisawa da masu isowa,,
yayinda su ya Khalil da abokan sa suke zaune cikin massalacin daga chan gefen layin karshe suna sauraron huduba jefa jifa suna masa tsiya irin na abokai shi kuma ya tamke fuska babu ko alamun farin ciki balle murmushi,,
Sosai yayi zurfi cikin tunanin maryam ganin abun yakeyi tamkar a film shi daddyn sa zaiyiwa auren dole duk irin kauna da soyayyar dayake nuna masa amma daddyn zai masa haka anya kuwa bazai sanya daddyn cikin jerin marasa kaunar farin cikin sa ba domin shi anasa tunanin duk Wanda yayi kokarin rabasa da maryam lallai yana cikin makiyansa,,
Amma wallahi alkawari ne ya dauka bazai hanata hakkin auren ta ba amma wallahi saitayi data sanin sanin ma balle ta aure shi,,musamman in bata janye maganar karatu ba toh wallahi shi zai iya yi mata komai ba,,
Yaseer ne ya jijjiga kafadar sa yace Yaya mutumina irin wannan tunanin haka anjima dai zaa wuce wurin saika mike mu gabatar da sallar a daura auren kowama ya huta ya fada cikin wasa da dariya kasa kasa,,
Kauda kansa yayi gefe ya kara cin magani saboda yadda yaji zuciyar shi ta buga masa da matsanancin karfi,murya a dakile yace kaida bazaka yi hankali ba a masallaci muke dai yana gama fadar haka ya miki shima domin gabatar da sallar,,
Mom ce chan cikin kuryar dakin dad suna waya da safina ta na gayamata abunda dad yayi mata jiya daya samu labarin bata na Wanda yakai ga har yanzu baya mata magana,,
Dariya safina tayi cike da jin dadi tace mom ai he deserved it ki duba abunda dad yayi mana saboda wannan useless girl din ai wallahi babu inda zan dawo saina gama gabatar da abunda ya kaini kuma dole su jirani indai an daura shikenan ai,,
Jinjina kai mom tayi tace kin kauta aikinyi tunanin mai kyau domin bazai yuwuba ka karar da lokacin da kuriciyar kaba gurin da namiji butulu ki duba irin abunda dad yayi min akan wannan tsinanninyar yarinyar,,
Toh Wai mom haka zaki zauna kina zuba idano bazakiyi maganin taba meye amfanin zamanta a duniya tunda tazama balai da masifa ko ina take sai ta lalata shi da bakin halinta,,
Kwafa mom tayi tareda Jan tsaki tace wallahi anjima da yamma zamuje wani wuri anyi mana kwarance kuma tabbas shi aikinsa yana yi sosai,,
Kai mom Wai maiyasa bazaki sa a harbe kanta ba zaki tsaya bata lokacin ki gurin zuwa irin wadannan places din ba nikam bani kaunar irin mutanen nan wallahi ta fada rai bace,,
Bakid hankali safina tashin farko mu zaa kama domin dai kinsan ni sarai halin dad dinki akan yarinyar nan,,
Duk da haka mommyn zaki iya yin wani abu dai kodayake koma menene sai yazamana mom pls ta mutu domin indai ba mutuwa tayi ba zata iya zama barazana ga aure na da ya Khalil kina ganin mom ko waya baiyi min ba,,,
Ki kwantar da hankali ki duk yadda mukayi inmun dawo zakiji we will talk later na bar baki mom ta fada tareda kashe wayar ta mike ta fice daga dakin,,
Kwance takebisa gado tayi matashi da pillow gaba daya jikinta a salube yake takasa kai kuda ruwan tea ne bakinta sai faman tsiyayar da hawaye take yi vanda kirjinta da yaki daidaituwa wajen bugunsa bugu yakeyi mata da karfi,,
Kara juyi tayi tareda share hawayen da suka silalo mata mai ya sanya kaddara da *karfin iko* zasu yiwa rayuwar su haka yanzu ya Khalil dinta ne zaiyi aure yau auren ma da wacce yasan ta tsaneta fiyeda kowa a duniya,,
Runtsi idanuwan ta tayi da karfi kanta na Sara mata kokarin take ta manta maganar biki cikin ranta amma ta kasa yakicewar musamman yadda take tino shekaran jiya yadda ya shirya musu engagement da irin soyayya da kauna tareda kulawa daya dunga nuna mata yanzu haka zai cigaba da nunawa safina ,,
Fashewa dayi da wani Sabin kukan Wanda yayi daidai da knocking din daakeyi a bakin kofar daki,,
Da sauri ta mike zauna tareda janyo dankwalin ta ta goge idanunta saanan ta mike jiki a sanyaye ta nufi kofar ta bude mommyn tagani tsaye hannun ta rike da tray,,
Da sauri maryam ta karba tana fadin kai mommyn da kanki,,
Cikin dakin ta ajiye akan bedside drower mommyn ta rufe kofar batareda ta tsaya sanya key kofar ba, saaana ta karaso ciki fuskarta babu walwala ko zama batayi ba sai data had a mata lafiyayyen tea saina ta zauna gefen gado ta rungumeta a gefen jikinta ta dago cup din dai dai bakinta Wanda ya sanya maryam soma kurbar ruwan tea dole ta nayi tana zubda hawaye Wanda duk yadda tayi kokarin hana su zubowa abin ya faskara,,
Saida ta shanye tasss saanan mommyn ta share mata zufa da hawayen dake zuba bisa kuncinta cikin muryar lallashi ta soma bata baki,,
Maiyasa ne maryam kike kokarin tayar da hankali ki Bayan kinsan doctor yayi umarni da ki cirewa ranki damuwa bana so pls kinji,,
gyada kai maryam tayi kawai,,
Addua dai bazan fasa yi miki tuni da itaba nasan kina kokarin to karki gaji ki cigaba da yi Allah bazai barki haka ba koba Khalil ba saikiga ya fito miki da Wanda yafi ya Khalil din komai,,
Da sauri maryam ta dago tana duban mommyn fuskarta cike da mamakin maganar mommyn,,
Bude idanu mommyn tayi itama tana tsareta dasu Wanda ya sanya maryam yin kasa danata idanun,,
zaki zauna hakane saboda jin dadin shi aina gaya masa wallahi muddin ya amince da auren nan yasanyaki cikin damuwa wallahi saina nema miki Wanda shi saiya kwanta ciwo inya ga auren Ku don haka inaso ki nuna masa kedin macace mai hankali da aji ki daure ki nuna masa tamkar bakisan yayi wani aure ba,,
Kwantar da kan maryam din akan cinyar ta tayi tana shafa mata gashin kanta tace maryam so nake don Allah daga yau banda gaisuwa ban yarda wata maganar ta sake hadaku dashiba kuma nida kaina zan sanya masa doka indai ba gaisuwa ba toh ban yadda da zuwansa gidan ba tunda shi baisan yancin kansa ba Wanda har ita safina tasan yancin kanta toh kuwa zasu sha ammaki na wallahi,,
Maza ki tashi kiyi wanka ina jiranki muje chan dakina kishirya bana son sake ganin digar hawayen nan naki abanza ki shiga jamaa ayi taro lafiya batareda kowa ya fahimci halin dakike ciki ba,,
Gyada kai maryam tayi tareda mikewa ta shige toilet,,itama mommyn mikewa tayi ta isa drawer dinta ta dauko mata kayan bikin ta aje bisa gado ta koma zaman jiran ta,,
Said a ta dauki kusan minti ashirin a toilet din tana tunanin shikenan yanzu anrigada an daura ma ya Khalil aure kukan ta tasha sosai kafin ta fara wanka jikinta a sanyaye tayi ta gama ta fito daure da towel iyaka gwiwa sai daya data dora bisa kanta don tsane gashin,,
Fitowar ta yayi daidai da shigowar shi dakin da gudu ya daga ta sama ya jiga jijjiu yawa da ita yana dariya yana kabbara allahu Akbar hearttee ,allahu Akbar hearttee,sosai yake juyi da ita a dakin ita kuwa gaba daya tarasa mai zatayi ga tsananin kunyar mommyn dake zaune tallafe da haba tana kallon ikon Allah toko yaron nan yasa mu tabin hankali ne,,
ganin yana neman tara musu mutane yasan ta daka matsa tsawa kaiii son kana cikin hankalin ka kuwa,,,
Chak ya tsaya ya juyo da dubansa ga Inda mommyn take shi wallahi harga Allah baisan ma tana dakinva ajuye maryam yayi a hankali sai kuma ya ruga da gudu ya fada jikin mommyn tareda rungumeta yana kokarin dagata sama ,,
Sallati ta saki da karfi ta make kansa da hannunta ,,,
Assshhh ya fada yana janye jikinsa tareda Sosa wurin kwabe fuskar yayi yace kai mommyn na mainayi haka,,,
Da kuwa tayi masa da hannu tace karbi nan shashasha kana hauka ne,,
Mommyn yau na haukace saboda murna mommyn yau inacikin tsan tsan farin ciki maryam tazama matata yana hawayen yake fadin hakan,,
Da sauri maryam da mommyn suka dago da idanuwansu ga kallon shi da tambayoyi cunkaus cikin zuciyar su ,,
Yes mommyn ya fada yana jinjina kai,,
Guda sukaji da karfi an nufo dakin mommyn hassana ce take ta faman yi cike da farin ciki tareda didde wacce harda rawar ta Inda mommyn hassana Ke taya ta suna fadin hamdu lillahi ,,,
Mommyn dai binsu da ido take yayinda maryam ta daskare agun jinta takeyi kamar baa duniyar nan take ba daga hannun ta tayi takai bakinta da iyakacin karfin ta ta ciji kanta Wanda said a yaji radadin har cikin kwakwalwar kanta,,
da sauri ta janye hannu tana runtsi idanu saboda zafi bude idanuwan ta tayi a hankali ta sauke su a gun dasuke murnace taga kowa yana yi cikin su musamman ya Khalil Wanda rabon dataga farin ciki akan fuskar sa irin haka harta manta lokacin,,
Muryar mommyn hassana ce ta katse mata tunanin datakeyi ta hanyar fadin yanzu mommyn wasan zai fara,,
yanzu zaa fara biki na dangi yayan gata ayyiyyuirriii,,
Ina amaryar takene Wai mommyn, mommyn hassana ta tambaya tana karewa dakin kallon,,
Wani wawan juyi maryam tayi ta koma toilet da gudu tana dariya ta danna key a kofar tolet din zaman tayi kan bathtub tana ajiyar zuciya maiyake faruwa haka ne da gaskine abunda kunnuwan ta Ke jiye mata ko kuwa mafarkin data saba yine,?
*mrs noour ce*βπ»π
[7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *π΄π΄KARFIN IKOπ΄π΄*
π±π±π±π±π±
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
*HIKMAAH writers association*
Edited byππ» *oum Zahara*π
Dedicated 2my lil sisππ» *Maman Sultan*π
Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
π
Ώβ5β£1β£
Nan take hawayen farin ciki suka shiga silalowa daga idanunwan ta hannun ta ta daga sama tanayi Allah godiya cikin zuciyar ta,,
Muryar mommyn taji tana tambayar ya akayi ne hakan ta faru,,
Cike da da farin ciki ya Khalil yace wallahi mommyn nidai muna Bayan saiji nayi an daura auren safina da Habib Wanda nan take kaina ya daure sai kuma nayi tunanin ko ankawo wani daurin auren ne daban banamu ba chan kuma sainaji ana fadin an daura auren Ibrahim Khalil tareda maryam abdullahi nan take gaba na ya yanke ya fadi ban gama mamakin ba saiga abban maryam da kanta har wurina inda muke zaune yakama hannun na muka yi gaba inda su malam da baffa da alhaji
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 32