riga ce jaa da duwatsu golden akayi mata kwalliya rigar ta hadu sosai ta tashi ta zura ta ta yafo gyalen ta rufe kirjin ta saboda bata da bra daya ce wanda tazo da ita kuma ta wanke ko mai bata shafa ba sai wet lips kawai ta saka a labbanta t fesa turare,,
hijab din sallar ta tadauka ta zumbula ta fita,,,
da safina ta fara cin karo tana nane kusa da Khalil tana tusa kai yayinda inaga zai iya ya amsa kokuma ya share ta yanayi yana latsa wayar shi,,,
ba karamin kyau taga safina tayi ba nan danan taji gwiwa ta tayi sanyi anya kuwa zata bisu shi kanshi wasu irin kananan kaya yasaka sunyi matukar yi masa kyau sai taga har yafi safina yin kyau kodan dama yafita kyan ne ,,,,
karasawa tayi gefen mommyn ta zauna a kasa tana musu sannu ,,,mommyn ta amsa da Yawwa har kin gama kenan ,,
gyada kai tayi tace eh nagama a sanyaye,,,
takai dubanta ga Khalil wanda yayi Kamar baiji shigowar mutum ba yanata latse latsen shi a wayar sa,,,,
tsakin safina ne ya fargar da ita ta juyo tana kallon ta harara take watso mata mai dauke da gargadi,,,
Kasa tai da kanta tace gaskiya bazani ba inna shiga cikin su zan raina kaina musamman yadda suke yan gari dubi yadda suka dace da juna Kamar mata da miji,,,,
jinginar da kanta tayi tunowa da dabara datayi ta dafe kanta ta kwantar a kan kujeran tana matsar kwallar,,
Khalil ne ya miki yana kallon mommyn yace bari mudawo mommyn inada aiki anjima ya wuce safina ma mikewa tayi ganin maryam ta ki mikewa yasa mommyn tambaya ta ko lafiya,,,
dama abunda take jira kenan ta kara langavewa Kamar zatayi kuka tace mommyn kai na yana min ciwo wlh,,,,
assha mommyn ta futa kai kuma yanzu ya zakuyi ko a fasa fitar ne ,,,,
da sauri ta shiga girgiza kai tace Aa mommyn suje kawai ai safina zata iya siyanmu abunda za'a siya din,,,
da sauri safina ta dawo cikin farin ciki wanda har ya kasa boyuwa ta ce mommyn tunda bata da lafiya ni zan siya mata kar ki damu ko anje da ita ba lalle ta iya daukan abunda ya dace ba ,,,,
mommyn de badan ranta yaso ba tace OK babu damuwa but pls inner wears da sleeping dress kada ki manta da su,,,,
gyada kai tayi cikin murna tace OK mommyn zan dauko mata ta juya tana watsa mata kallon daya fi miki zaman ta wuce,,,
taku take daidai tana yanga cikeda jin kai da isa ta karasa gurin parking ta bude gaba ta zauna tana ta zuba yauki sannu bro ta fada cikin Jan hankali tana fari da idanun Kamar ba yar secondary school ba,,
gyada kai kawai yayi batareda ya amsa ba ,itama bata damu ba burinta kawai Allah yasa plan dinta ya tafi daidai yadda suka tsara,,
ganin yaki tada motar yasa ta cewa muje kawai bro wai bazata iya fita da muba ,,mommyn kuma tace a kyaleta kada a takura mata ni sai in zaba mata duk abinda ya kamata,,,
Baice komai ba ya tada motar ya fege ta suka fita wani babban shopping mall ya kaita ya yi parking a inda aka tanada domin yi suka fito sai faman chusa kai takeyi tana bashi labarin makaranta ta yayinda shi kuma baya ce mata kala sai dai ya gyada kai kawai yana mamakin abunda yasa maryam bazata fita dasu ba ,,
kodai yar garin nan ce karya tayi ma mommyn don kada wani ya ganta amma zaibi diddigi har ya gane ita din wacece,,,,
tare suka shiga amma saiya neman guri daya ya zauna a daya daga cikin kujerun zaman wurin yace taje kawai ta dauka musu duk abunda yakamata,,,,
ba haka taso ba amma ba yadda ta iya tasan bata isa tasa shi binta ba dole ta kira daya daga cikin ma'aikatan wurin suka wuce,,,
saida ta gama daukar wa kanta abunda take bukata sunana ta duba wadanda panties da bra ta dauka mata sai ta je gurin Arabian gown ta dauka mata kalar biyar sai sleeping dress guda uku kuma duka saida ta duba wanda yake lower price saanan take daukan ma maryam din babu tarkacen komai ta juya suka sauka kasa wurin biyan kudi ,,,,
Khalil ya biya suka wuce aka biyosu da kayan har wurin mota saida ya bude suka zuba musu tukunna suka juya ,,,,
koda suka kama hanya sai cewa tayi bro pls ice cream nakeson shaa don Allah ta fada tana marairace fuska bai ce mata komai ba ya kwarya kwana suka nufi wurin ice cream,,,
tare suka fito ta zabi kalar wanda take so shi kuma soft drink kawai ya dauka suka zauna kan kujerun suna sha,,,
Dagowa tayi taa kare mai kallo gaskiya ya hadu Khalil ta ko ina ga tsantsar kyau ga kudi ga illimi ga aji duk da yadda kirjinta Ke bugawa haka ta danne tace bro kana da girlfriend ne ,,,,
shiru ne yabiya baya har ta cire ran zai amsa mata amma sai taji yace Aa akwai wani problem ne yai mata tambayar yana tsare ta da idanunsa masu firgita yan mata ,,,,
nan da nan ta shiga rudu girgiza kai tayi kirjinta na dukan uku uku kai anya zan iya kuwa gaskiya gwara inyi shiru Tnx god tunda bayada girlfriend komai zai zo da sauki sai dai su mommyn su hada su kawai domin tana da aji itama batason ajinta ya zube a banza,,
Maryam ganin sun fita yasata sarewa wanda har mommyn ta lura da hakan amma saita kyaleta tace taje daki tasha magani ta kwanta,,,
amma maryam tace Aa mommyn nasha ai kuma bana jin bacci tunda kince aiki zakiyi muje kitchen din sai in tayani ko jikina zai warware min,,
Murmushi mommyn kawai tayi dama tasan lafiyar ta kalau kawai bata son fitar ne ,mikewa mommyn tayi tace muje mufara,,
Haka suka gaba babu wani sakin fuska data samu gurin Khalil amma ita cike da farin ciki suka dawo hankalinta ya fara kwanciya burinta tayi waya da su mom kai yau har dad saita gayawa so take ta tabbatar wa maryam itadin ba komai bace ta fita *karfin IKO* akan komai,,,,
kuda suka isa su mommyn da maryam suna kitchen yayinda maryam ta zage tana ta gyaran gyada jitayi a jikinta ana kallon ta ga kamshin turaren sa ya cika kitchen din kasa dagowa tayi ta kalleshi yayinda shi kuma ya jingina da Kofar kitchen din ya harde hannayensa ya zuba mata idanu duk yadda akayi yarinyar nan bata da gaskiya amma kuma babu wani alama daya nuna hakan amma yasan yadda zai mata ,gyaran muryar yayi yadda zaraji
nanda nan jikinta ya fara karkarwa tana yi batareda natsuwa ba har ta fede hannunta,,,
*mrs noour ce*βπ»π
[7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *π΄π΄KARFIN IKOπ΄π΄*
π±π±π±π±π±
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
*HIKMAAH writers association*
Edited byππ» *oum Zahara*π
Dedicated 2my lil sisππ» *Maman Sultan*π
Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*~Gaskiya ne fans din karfin IKO ina yinku sosai comment dinku ,shawarwari Ku kullum suna karfafa min gwiwa,~*β€πππ
*my ukteey Allah ya kara lfy*π€²π»
π
Ώβ1β£6β£
Nan da nan jikinta ya fara karkarwa tana yi batareda natsuwa ba harta fede hannun ta kara ta saki cikin zafi da radadin ciwon,,,
da sauri mommyn ta fito daga store hannunta dauke da karamin ledan semo ganin maryam tayi rike da hannu jini nata diga ta runtse idanunta tana kuka,,,
ta kai kallonta kofa Khalil na tsaye ya kafe maryam da ido Kamar baisan mai ya faru da itaba,,,
ran mommyn ya baci amma bata shi take ba kama maryam tayi tana jero mata sannu ta nufi tap da ita ta wanke mata hannun ta daure da tissue har lokacin maryam bata daina zubar da hawaye ba,,,
aaahhh oh my god muryar safina ta sasu waigowa domin ihu tayi da karfi cikin firgice ,Khalil suka hango hannunsa sai zubar jini yakeyi yana tsaye Kamar baa jikin shi jinin Ke fita ba yayinda safina Ke rike da hannunsa ita bata bashi taimako ba amma tana rike da hannun hankalinta a tashe,,,
da sauri mommyn da maryam suka mike jiki na rawa suna rige rigen isa guri shi,,
ruwa maryam ta dauka a saman fridge dake gefe ta kama hannunsa ta shiga tsiyaya mai a wurin mommyn kuwa tambaya take garin Yaya son hakan ta faru yanzu na ganka lfy duk ta rikice,,,
fusge gorar safina tayi tana fadin useless girl kawai matsa ki bani guri kafin ki shafa mai wata cutar ta fada a tsawace domin ta harzuke da ganin irin kallon da Khalil yake wa maryam wadda batasan meye ma'anar shiba,,,
maryam janye jikin ta tayi gefe domin ita sai a lokacin ta lura da kallon da yake yi mata,,
mommyn ce ta dawo dauke da first aid box tace maza su fito falo ta gyara musu,,
Maryam ce ta fara fita jiki a sabule bata son ya cika dora idanuwan shi a kanta saboda yana haifar mata da mutuwar jiki da karuwar buhun heartbeat dinta saita rasa natsuwar ta da sukuni,amma babu halin hanashi hakan,,,
kamshin turaren sa ne ya fargar da ita tai saurin Juyowa yana kusa da ita Kamar zai hade musu jiki,
kai dubanta tayi ga safina wacce ke ta faman watso mata harara kasa tai da kanta tareda matsawa gefe kadan don gujewa zaginta domin tana jin zafin cin kashin datake yi mata a gaban kowa kuma a duk lokacin data so,,
mommyn ce tafara gyarawa maryam hannu don tissue din data nada mata ya jike wurin bawa Khalil taimakon gaggawa , kafin nan ta amsa hannun Khalil gurin safina wacce babu abunda ta iya yi sai kallon hannu tana zare idanu ,mommyn ta gyara mai ciwo ne sosai yaji wanda dukkansu sun tsorata musamman maryam da take ta tunanin garin ya hakan ta faru bayan yana gabanta lafiyar sa kalau yake tsaye,amma baa mamaki da hukuncin Allah ta furta a zuciyarta,,,
mommyn gama mai ta nade hannun saanan ta mikawa safina box din ta maida,,
amsa tayi badan ranta yaso ba domin tana ganin ya zaayi a aiketa bayan ga maryam nan,,taku baifi hudu tayi ba taga wata maid tazo wucewa ta mika mata tace takai ta ajiye,,
mommyn bata ji dadin abunda safina tayi ba domin Wanan ya kara tabbatar mata da rashin kunyar safina tayi nisa,,Ku tashi Ku wuce Ku kwanta Ku huta mommyn ta umarce su ni zan koma kitchen ta mike ta nufi kitchen,,,
Yana ganin shigewar mommyn ciki ya matso da kansa kusa da kunnen maryam har tana jin hucin numfashin sa a gefen fuskarta kirjinta tane ya tsananta bugu cikin sauri sauri amma duk da haka bata dago kanta ba domin hakan yafi mata feye da hada idanu dashi,,
a sanyaye ya furta next time haka ya kamata kiyi wannan yai mata nuni da ciwon da yaji ya kara kasa da muryar shi yace wannan shi ake kira da,,shiru yayi batareda ya karasa ba sai iska daya wuro mata a kunne ya mike ya fice,,
bayan sa tabi da idanun ya Allah mai yake faruwa da ni wai ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta mike,,
four eyes sukai da safina wacce ta kumbura Kamar tasha yis fuskarta har jaa takeyi saboda fushi ita wallahi har ga Allah khalil ya mantar da ita ga inda take,,
hannun da maryam ta yanke ta damke da karfi tareda fusgarta zuwa sama,,
wani irin zafi ne ya ziyar ceta wanda bata ji irin sa ba koda ta yanke amma saita toshe bakinta da dayane hannun domin bata son itama kowa ya sani tasan tayi mata laifi tunda ta gargadeta tun ba yau ba don haka duk hukuncin data yi mata daidai ne,,
*Kano gurin ummin*
Zaune take ta tasa kwanon abinci a gabanta wanda ko loma daya bata yiba sai tunanin data keyi anya kuwa batayi kuskuren bin umarnin inna ba?
mai zata cewa ubangijin ta idan wani abu ta samu maryam Mara kyau?
tun tafiyar maryam take sunturi gidan hajiya ladi bata dawo ba gashi batayi magana bama inna kullum cikin jifan ta take da sharrin balle kuma tayi,,
sallamar inna ce ta katse ta ta dawo daga tallar zogale ,,
amsawa ummi tayi tana mata sannu ya kasuwa,,
lau da kai gefe tayi tace mun gode Allah don yafi zaman banza irin naki koda shike zaman banza yafi dacewa dake domin bakida kashin arziki a tare dake ya,,
mikewa ummi tayi domin batason jin wani bacin ran akan nada kitchen ta nufa ta dauko kwanon abincin inna ta kai mata gabanta tareda durkusa wa ta aje,,
Juyawa tai ta koma inda take ta zauna ta dauki kwanon ta fara ci badon dadi ba a zuciyar ta tana fadin wannan wace irin rayuwa ce a dake ka a hana ka kuka,amma ba komai zan zuba musu ido inga gudun ruwansu,,
washe gari da sassafe inna ta yaye labulan Kofar ummi tace toh ni zan tafi gida sai zuwa Jibi zan dawo ga zogale nan ki rinka dafawa dan gidan hanne zai rinka kai min tallar shi,,
lokacin ummin nasan sallaya tana ta azkar mikewa tayi tana mata Allah ya ki yaye ya tsare har Kofar gida ta rakata sannan ta juyo,,,
gidan hajiya ladi inna ta fara zuwa ko zata samu na rage kudin mota,,ai kuwa tayi saa jiya suka dawo tareda alhaji da dad dare,, da sauri ta shiga bugun gidan ta dade tanayi kafin aka amsa da waye da sauri inna nace nice innar maryam,,,
kirjin hajiya ladi ne ya buga duk ta daburce da sauri jiki na rawa ta budewa inna Kofar batareda tayi shawarar abunda zata fada ma domin kare kanta,,,
washe baki sukai ma juna wanda kowanne su baikai zuciyar sa ba sannu da zuwa hajiya ladi ta furta wanda inda inna tana da lura kallo daya zataci mata tagane bata da gaskiya ,,,
shiga ciki sukai inna na fadin ai na dade ina buga Kofar nan shiru nace injin bacci kukeyi,,,
yake tayi tana fadin wlh kuwa nadan koma bacci ne zama sukai,suka gaisa,,
sannan inna ta fara tambayar wai ya yar jikar tawa chaa nai vari in biyo inji labarin ta don zanje gidane dauko wata jikar tawa ko itama za'a Samar mata aikin Kamar na mero,ta dada washe baki tace da fatan bata muku gardama ko,,,
da sauri hajiya ladi tace Aa ko daya ai maryam batada gaddama bakiga yadda takoma ba Kamar wata kazar agric ai tuni ta kwantar da hankalin ta ta kama aiki sosai ta fadi tana zare ido,,,
dariya inna tayi cike da jin dadi tace ai nasan mero da himma ba Kamar uwar ta ba,gyara zama tayi tai kasa da kai tace emm dama hajiya zance ne yaushe ne zanzo amsar kudin aikin nata,,
murmushi hajiya tayi tace kada ki damu wata na karewa da kaina zan kawo miki har gida inna ai an riga da an zama daya, a zuciyarta kuwa tsinewa inna takeyi domin jiya ma haka alhaji ya sauketa ko sisi bai ba taba sai rashin mutunci daya dinga yi mata bacin ma sun saba harka da saiya sa anyi mata cin mutunci,,
mikewa inna tayi tace bari inje hajiya zan dawo In na dauko jikar tawa ko za'a samo mata aikin,,
ba komai inna da fatan dai jikar taki budurwar ce ko domin sunfi karsashin yin aiki fiyeda zawarawa,,
da sauri inna tace wlh budurwar ce badi dai muke saka ran auren ta shiyasa nace tazo ko itama Zata samu na katifa,,
toh ba komai inna ki gaida gida ina nan ina jiran zuwan Ku kuma ba miki alkawari kafin Ku dawo na Samar mata gurin aiki Insha Allah,,
toh toh ba komai sai kin ganmu,,
raka tai har Kofar gida sanan ta rufo Kofar ta dawo cikin sauri cike da murna tasamu wata damar wayar ta ta dauka ta danna kiran alhaji,,,
*Kaduna*
Habib ne sanye da cikin kakinsa na sojojin wanda sukai matukar yi masa kyau Kamar don shi aka kirkiri uniform din tsugune yake gefen kujerar da dad din safina Ke kai mommyn na gefen shi,,
hakuri dad yake bawa Habib na rashin samun cos din da baiyi ba na Liberia wanda daya samu ba karamin rike kasa shima zaiyi ba,,
dad yace Habib rayuwar nan daka Ke gani komai zakayi kayishi cikin gaskiya zanzo hazakar ka da kokarin da juriya ace su suka kaika ga mataki na gaba bawai in yi kokarin danne wani in tada kai ba wanda wannan yawan ci shi yake faruwa a kasar mu kuma sannan komai daka gani mukaddari ne daga Allah sai dai muyi fatan Allah yasa hakan shi yafi alhairi,,
ameen abba Habib ya amsa duk da yaso yasamu wannan cos din amma ya zaiyi da abunda mai sama ya hukunta kuma yana sawa ranshi indai yana da rabo zai samu ko bajuma ko badade,,,
mom dinma addua tayiwa Habib saanan ta juya ga kallon ta gurin dad din tace dadin baby ni kuwa baby ta kira ka jiya kuwa,,,
murmushi yayi irin nasu na manya cike da kaunar yar tashi don tunowa dayayi da rigimar ta yace munyi waya kam jiya tana min maganar Khalil ko ,,,
dariya momy tayi tace wlh kuwa kullum maganar kenan na dai bata hakuri tunda gobe ne zata koma su fara exam in munzo za a tsaida magana daya ko kuwa,,,
Mikewa Habib ya yi yace bari in koma abba na gode Allah ya kara girma,,
cike da jin dadi dad yace toh son babu wata damuwa ko,da sauri Habib ya girgiza kai yace wlh babu abba sai dai maganar inna ta danayi maka magana,,
murmushi dad yayi yace kada ka damu zan samu muje kafin mu tafi gurin safina,godiya habib yamai ya juya ya fita,,
Mom murmushi tayi tace kai dai da son din nan naka baa jin kanku mai kuma ya faru,,
dad ne ya juyo tareda matsoda ita jikinshi y rungume ta ta gefe yace matsalar inna ce wai aure taatsa mai yayi shikuma ya fison ya samu cos din kafin auren shine yakeso insa baki,,
tabe baki mom tayi tace to ai alhaji ya kamata yayi din tunda ba dole bane sai yayi tunda Gashi bai samu ba basai yayi auren ba kawai,,,
ni kuwa wlh hajiya wani tunani nakeyi mai zai hana safina auren Habib hankalinta yafi kwanciya da natsuwar shi fiye da Khalil,,,
dakata dakata alhaji mom ta katse shi cike da bacin rai tace don Allah alhaji kada ka fara ma wlh domin bazai taba yuwuba mikewa tayi cikin bacin rai fuu ta wuce sama Yaya suna ganin samu alhaji zai fara maganar Habib lalle gaskiyar MAMAN ta ne datace bata son zaman yaron nan a gidan nan ashe kuwa dama duk abunda babba ya hango karamin bazai iya hango wa ba ,,
*US* *American*
har cikin dakin ta takaita ta watsar da ita a kasa tana hucii,kamar macijiya,,
da sauri maryam ta dago tace don Allah kiyi hakuri ba laifi na bane,
da sauri ta dafe kumatun ra ganin safina ta kawo mata mari Allah ya ki yaye ta sameta a kai kara safina ra saki cikin jin zafi domin bata yi zaton maryam zata goce ba taso tasamu fuskarta ta var mata tabo sai gashi ita tabige da jin zafi,,
yarfe hannuwan ta tashiga yi maryam kuwa sai faman sannu da bada hakuri take yi mata,,tana kuka
dagowa tai a fusace tace tashi ki fita amma kisani ban gama da Ke ba saina yi miki wulakanci feye da tunanin ki useless girl kawai,,,
da sauri maryam ta mike ta fita zuwa dakinta kulle kofa tai kwata kwata taki budewa koda dad din Khalil ya dawo kin sauka kasa tayi dukunkunewa tayi a blanket tace bata da lafiya a daki taci abinci bata son kara haduwa da Khalil saanan ga safina wacce zata iya kawo mata hari ako yaushe ranar kwana tayi kuka sai dagabaya ne ta ga kukan ba shida amfani ta mike toilet ta fada tai dauro alwalar ta shimfida sallaya ta kabbara sallah ,,
Har kusan karfe uku da rabi sanan ta jingina da gefen gado lokacin zuciyar ta ta sanyaya sosai sai a lokacin ta fara tunanin maganar da Khalil yai mata a kunne mai hakan take nufi ne mai yasa zai yanke kanshi don ta yanke,haka tai ta tunani har aka kira sallar ta mike tayi ta dura da azkar dinta anan ta zame ta kwanta,,,
safina kuwa bayan fitar maryam waya ta dauka ra kira mommyn ta gaya mata yadda sukayi,,jinjina kai mom tayi tareda gayawa safina itama yadda sukai da dad din tun kafin ta karasa safina tace what mom dad tasan abunda yake fada kuwa ni da habib yake tunanin hada wa dis is a joke wlh,,da sauri mom tace ki kwantar da hankalin ki ai nayi maganin abun nasan ba zai kara maganar ba tai ta kwantar wa safina hankali har ta samu natsuwa ta sauka kasa gurin daddyn khalil ,,
yayinda Khalil yana daki daya ar runtse ido maryam yake gani ya rasa dalili shidai bai son meye so ba bama zai taba son wannan mad girl din ba shida yake burin mace wayayyar domin bazai taba barin matashi tayi aiki ba ko wani ci gaba da karatu haka ya kwana yana abu daya ga hannunsa daya dameshi da zugi kwata kwata ya kasa bacci sai tunani ,,,,
*Ku biyo ni donjin yadda zata kasance*
*shin Khalil zai furta soyayya ga maryam*?
*kuna tunanin safina zata yadda ta auri Khalil da karatun secondary sannan babu cigaba*?
*Yaya maganar Habib domin mutum uku kenan sukai Naam da hadin da da safina*?
_kada Ku damu anjima wani page din na nan zuwa Insha Allah_π€π»πππ
*taku har kullum*
*mrs noour ce*βπ»
[7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *π΄π΄KARFIN IKOπ΄π΄*
π±π±π±π±π±
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
*HIKMAAH writers association*
Edited byππ» *oum Zahara*π
Dedicated 2my lil sisππ» *Maman Sultan*π
Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*yaa ayyuhal laziyna amanu kuu amfusakum wa ahlikum naran*
_jumaat Kareem_π§π»
π
Ώβ1β£7β£
Da kyar ya lallaba yayi alwalar asubahi ya fito anan daki yayi bai samu fita ba sunyi jamii Kamar yadda suka saba yi duk da a cikin gidan sukeyi,,
yana idar wa ya koma gado nan da nan bacci yai awon gaba dashi,,
Karar bugun kofa ne ya tada maryam daga baccin datake domin bugun bana lafiya bane da sauri ta mike ta nufi kofa duk da baccin dake idon ta budewa tayi nan da nan kirjinta ya bada damm ta hadiye miyun dabata shirya ba safina ce tsaye cikin kayan bacci purple color kanta babu dan kwali,,
da sauri maryam tace ina kwana anty,,
tabe baki tayi tana mata kallon banza kafin tace follow me ta wuce cikin tafiyar nan tata ta takama da ji da kai,,
itama batareda bata lokaci ba ta bi bayanta tana koda ta shiga ganin ta tayi Zaune gefen gado ta harde kafa tana girgiza kafa,,
gefe daya ta samu ta zauna tana bin dakin da kallo ganin kaya a waste gaba daya a baza su a jiyar zuciya tai a zuciyar ta tana cewa zan jure koma menene tunda ta dalilin ki na tsira don haka akullum ko maizaki yimin zan jure shi,,
Keeh safina ta kira sunan ta kayan nan zaki shirya min su a jaka na sannan ga wannan kayan inners dina ne ba kowa nake bama wankin ba don haka ki dauka kibi a sannu gurin wanke su domin kowanne pant daya dake nan yayi kudin abincin Ku na wata biyu,,kuma ki tabbatar da kunsa hand glove a hannun ki don gudun daukar cutar talauci dake tattare da Ke tashi maza ki fara before in sauko kasa komai ya zama ready,,,
toh maryam ta amsa mata a sanyaye tana fadin da sauki ai indai aiki ne ba cin mutuncin naki bane zakiyi mun ta furta hakan a ranta,,
tashi tayi ta kama aikin yayinda safina ta shige toilet,,
Khalil ne kwance a daki yana aikin tunanin maryam yana son kara ganin ta amma bayaso tasan da hakan,,
shawara ce ta fado mai cikin hanzari ya dauki wayar sa ya kira number mommyn wacce take dakin mijinta suna bacci har ta gama ring bata sani ba balle ta dauka,,
tsaki yai ya aje wayar gefe ya miki toilet ya fada yai wanka cikin dabara domin hannun na damun sa,,
koda ya fato kai tsaya wurin drawer yanufa , fito da riga armless
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 32