Share this page
kayan arziki babu ajiki na yanzu Yaya zanyi in rama salloli na ni maryam,sai yanzu ta tuna bata da ko gyale gashi bata da kayan sawa ko daya πŸ€¦πŸ»β€β™€yanzu yazata yi,ko gurin safina zanine? kai gwara wurin momy amma mai zan cemata satoni akayi koko me ?ya Allah ka kawo min daukiπŸ˜’ *comments* *share* *mrs noour ce✍🏻 [7/11, 17:42] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… *sakon kwandunan da buhunnan gaisuwa gareku Masoya na Allah ya bar kauna ,ina yinku Kamar yadda kuke yina 😍😍😍😍😘❀❀❀* πŸ…Ώβž–1⃣0⃣ Ya Allah ka kawo min dauki ,fitowa tayi ta nufi dakin safina kirjinta sai dukan tara tara yake ta murda Kofar ta bude ,ajiyar zuciya ta sauke tana dafe kirjinta sakamakon ganin safina da tayi tana bacci karasawa tayi gefen gadon ta fara kiran ta a hankali cikin natsuwa anty,anty,anty,cike da bacci ta bude idanuwan ta ta ware su akan maryam bakin ciki yazo mata iya wuya ta kafe ta da ido taji dalilin tashinta ,cike da tsoro muryar na rawa tace dama don Allah anty hijab zaki aramin inyi sal.... taasss taji saukar mari a fuskarta da sauri maryam ta dafe kuncinta saboda radadin zafin da rake ji nan da nan ta fara zubda hawaye,wannan shine kadan daga cikin sakamakon da zaki samu wurin saba dokokin dana gindaya miki tsaki taja tana nuna mata kofa out of my room now,sim sim ta fice tana share hawaye ,dakin ta ta koma ta nemi bakin gado ta hada tagumi ta rasa me zatayi ,ace dan Adam hijab ma da zaayi sallah ya kasa taimaka wa ko domin lada ai ta danne zuciyarta lallai na yarda zama da safina babban tashin hankali ne agareni, knocking taji anayi daga bakin kofa da sauri ta miki tana zaton ko safina ce tai tunanin bata hijabin amma tana budewa sai taga wata dattijuwa a tsaye da alamun suma ma'aikatan gidan ne gaidata tayi ,maryam ma dai gaisheta tayi sannan tace dama hajiya ce tace aduba mata ko da wani abu da kuke da bukatar shi in kuma babu ga abun Karyawa chan a dining ko za'a kawo muku nan ne ,da sauri maryam ta girgiza kai tace Aa haba dai dama hijab nakeson inyi sallah kuma naga anty na bacci ko zan samu ,toh hajiya bari a kawo miki ta juya, maryam na nan tsaye har ta kawo mata hijab din ta amsa tana mata godiya , sallolin da ake binta tayi sannan ta fito da hijab din a jikin ta a parlon sama ta tadda momy da Khalil suna kallo momy na kan carpet a kasa yayinda Khalil yayi matashi da cinyar ta hannun shi rike da waya yana dan nawa nesa kadan dasu maryam ta zauna akasa ta gaida momy ,ta amsa tana Dada tambayan ta gajiyar hanya ta kai kallon ta ga Khalil wanda bai nuna tasan Allah yayi ruwan mutum a gurin ba ta gaidashi ,har ta cire ran zai amsa sai kuma raga ya sauke wayar hannunshi kura mata ido yayi wanda tasa dole ta sauke nata idon don bazata iya cigaba da kallon kwayar idon shiba gabanta yana tsananta faduwa ganin haka yasa momy tace maza ki tashi kije ki Karya in akwai abinda kike so sai ki sa a dafa miki ,toh maryam ta amsa ta tashi ta nufi parlon kasa wanda Ke dauke da dining area a gefe daban ta karasa ta zauna cup cup ta dauka ta tsiyaya ruwan tea ta hada ta dauki bread ta fara ci dukda yanzu eleven ta wuce amma bata bukatar cin wani abu mai nauyi tana ci tana tunanin ummin ta ko a wane hali take oho kila ma ta kwantar da hankalinta da tunanin ko tana gidan aiki ita kuwa gata a wata kasa da ko a mafarki bata taba mafarkin ta ba Allah kenan kasa cin abincin tayi tayi taguwa tana kallon bread din, chan taji kamshi ya isheta wannan wane irin kamshi ne ji tayi a jikin ta ana kallon ta aikuwa tana juyawa sukai ido hudu da Khalil da sauri ra sauke idonta don bazata ita ci gaba da kallon shiba saboda kallon da yake yimata ki hada min break fast ki kawo min yanzu nan ya fada a taikaice kamar wanda baida lebe don imba ma dakin daya Ke shiru ba babu yadda zaayi taji shi,ya juya ya fice,,πŸ€¦πŸ»β€β™€ya Allah maryam tace baya gani ni bakuwa ce nasan mai yake cine ya'yan masu kudin nan da iyayin tsiya,to waima ina nasan dakin shi nida zuwa na kenan ko yar aiki ai tana bukatar bayani,ajiye bread din hannun ta tayi mike ta hau sama gurin momy aikuwa tayi saa domin kuwa bata parlon Jim tayi tana tunanin yadda zatayi ga dai ma'aikatan gidan amma kuma ita turancin nasu ba irin nata bane me zatace musu tunanin dattijuwar dazu ya fado mata tace bari ta duba sai ta tambaye ta sake sauka kasa tayi bata parlon itama bin wata kofa tayi ta bude don taga ma'aikatan na yawan bin hanyar koda ta bude kofa uku tagani daya na kallo daya hagu ,daya dama,ta rasa ina zata bi kada ta bude dakin wani da bai kamata ta bude ba,kai wlh komawa dakina zanyi bazan fito bama balle ya sake gani na shi ya Sani πŸ€·πŸ»β€β™€ Kwanciyar ta tayi aikuwa ko minti biyu bata yiba bacci yayi awon gaba da ita... Khalil na daki yana jira tun yana kallon bakin kofa shima har baccin yayi gaba dashi , sai azabar ta miki ta shiga toiler ta rinka tabe2har Allah yasa ta kuna ruwan zafi tayi waka tara dauro alwalar azabar ta fito ta rada sallar, itama safina sai lokacin ta mike toilet ta shiga tai wanka ta dauro alwalar ta fito saida tayi shafe2nta tayi kwalliya sosai ta wuce wardrobe arebain gown ta dauko fara kal mai ratsin ja ra saka da skintight fari sanan ta dawo ta shimfida praying mat ta fara jero sallolin da ake binta na hanya tai azahar sannan ta miki gyalen ta daura akanta Kamar hula tayi matukar kyau abunta ,ta kalli kanta tai murmushi ita kanta tasan ta hadu tunowa da tayi da Khalil yasa ta lumshe ido ta dauko turare kala biyu masu kamshi da tsada ta feshi jikin ta dasu ,flat shoe ta saka ja ta fita domin zuwa yin break fast😊 *asalin su safina* mahaifinta wanda ake kira da alhaji isma'il ii dan asalin garin bauci haifeffe iyayen shi da kakanni iyayenshi suna da hali domin babanshi bada gona ya dogara ba yana hadawa da kasuwa sai da kayan saya kama daga na mata dana yara da maza duka yana da shaguna dayawa cikin kasuwannin garin shiyasa koda alhaji isma'il ii ya nuna son shi ga karatun zamani ya bashi karfin gwiwa yasaka shi har ya gama secondary sannan ya zana jarabawa a Kaduna na air force base cikin saa ya samu koda sukayi shekara daya suka gama training ya cigaba da karatu inda aka fara turashi Abuja anan ya hadu da mahaifiyar safina suka kulla soyayya sai dai iyayenta basu yadda ba saboda ita nata mahaifin dan siyasa ne ga kuma kudi yaso yabada yarsa inda zasu kulla zumuncin su na yan siyasa amma data dage dole ya hakura sukayi aure cikin rufin asiri duk da albashin nashi ba wani tawa ne dashi ba haka suka zauna shekara daya ta haifi danta namiji aka sa mishi Usman ,bayan shekara uku sai ta sake haihuwar abdullahi shima tsakanin shi da safina shekara uku ,bayan shekara biyu ta sake samun ciki ta haifi musa suna kiranshi da daddy wanda yaci sunan mahaifin alhaji isma'il ii ,a kwana atashi yana ta samun karin girman har aka mai transfer zuwa Kaduna ranar da zasu koma suka samu mummunan hadari wanda duka yayan suka rasu sai safina kadai bayan sunyi zaman asibiti sun fito suka koma gida shikenan dalilin sangarta safina da sukayi suka dauki soyayya duniyar suka dora akanta komai take so shi za ayi lokacin data gama primary dinta yayi daidai da lokacin da aka tura alhaji isma'il ii US yin wani cos shine suka koma chan da zama shekara su uku a chan aka kara mai transfer zuwa Malaysia lokacin zahra tana ss one kenan shine ya barta anan domin cigaba da makaranta tunda ta kusa gamawa amma ya maida ta ta kwana wato boarding sai dai suke mata Hutu ko ita tazo ,shekaran shi daya aka dawo dashi Kaduna gaba ki daya tareda babban mukami lokacin kudi har sun yi musu yawa safina ta samu abunda take so lafiyyan gidan sama ya kera musu cikin mallali gra ,shine zuwan da safina tayi wanda suka hadu da maryam wanda jarabawa kadai ya ragewa safina ta zana tayo gida ,,Wanan kena . *cigaba* bata samu kowa a palon ba don haka kai tsaye dining area ta nufa ta bubbude Warmer's din ta zuba abinda take so ta zauna kenan sai ga asabe tazo kwashe kayan sannu tai wa safina ta dago ta kare mata kallon taga ba wata bace da alama ma'aikatan gidan ne ta juya ta cigaba da shan shayin ta batareda ta amsa ba,koda ta gama sama ta koma dakinta ta dauko wayar ta ta kira daddyn ta, yana dauka a shagwabe ta fara magana daddy nifa bazan zauna da yarinyar nan ba gaskiya kuma ni gidan nan bai min b.. kai baby daddy ya katseta tunda nace kiyi hakuri zansa abunyi sai kiyi ko bari in kira Momyn taku sai musan yadda zaayi ko kuma ki sauka kasa ki bata wayar sai muyi magana don munyi waya da dadin Khalil din baya kasar ,OK ta fada cike da farin ciki ta mike ta fita parlon kasa ta sameta ta mika mata wayar dad na yace zaku yi magana, amsa momy tayi it kuma ta koma kan kujera two sitter ta kanta tareda mike kafa ta dauki remote ta chanza tashar da Momyn ki kallo daga MBC masr zuwa MBC 3, koda momy sukayi waya daddy ya gaya mata komai yadora dacewa ya gayawa mijinta komai wato dadin Khalil to yace baya kasar dalilin kenan da nace safina ta kawo miki muyi magana don Allah hajiya ki zaunar da yarinyar nan kiji meya matsalar ta sai a sanar min ko shi Alhajin ki gaya masa sai ya sanar dani domin asan yadda za'a bulluwa lamarin kinsan halin yar taki sai hakuri ta dage bata son zaman yarinyar anan,murmushi momy tayi tace ba komai alhaji nima tun zuwan su kallo daya nayi mata nasan cewa tana cikin damuwa amma duk yadda mukai zakiji yau dinnan Insha Allah, godiya dad yai mata ya kashe wayar, momy ma mikawa safina wayar tayi tareda cewa ta kira mata yarinyar da suka zo dazu ,Jim tayi sai kuma ko mai ta tuna sai ta kike ta hau matakalan step kenan taga daya daga cikin yan aikin gidan ta kirata ta tura ta kiran maryam din dama bata son ko kallonta ita kyama ma take bata,ta juya ta koma gurin momy babu kunya tace na tura a kira ta ,momy jinjina kai kawai tayi tana mamakin saka cin da su daddyn sukayi akan tarbiyyyar safina,Allah ya kyau ta. *Ku biyo ni don jin yadda zata kasan ce cikin tarihin maryam* *comments* *share* *mrs noour✍🏻* *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… *sakon kwandunan da buhunnan gaisuwa gareku Masoya na Allah ya bar kauna ,ina yinku Kamar yadda kuke yina 😍😍😍😍😘❀❀❀* πŸ…Ώβž–1⃣0⃣ Ya Allah ka kawo min dauki ,fitowa tayi ta nufi dakin safina kirjinta sai dukan tara tara yake ta murda Kofar ta bude ,ajiyar zuciya ta sauke tana dafe kirjinta sakamakon ganin safina da tayi tana bacci karasawa tayi gefen gadon ta fara kiran ta a hankali cikin natsuwa anty,anty,anty,cike da bacci ta bude idanuwan ta ta ware su akan maryam bakin ciki yazo mata iya wuya ta kafe ta da ido taji dalilin tashinta ,cike da tsoro muryar na rawa tace dama don Allah anty hijab zaki aramin inyi sal.... taasss taji saukar mari a fuskarta da sauri maryam ta dafe kuncinta saboda radadin zafin da rake ji nan da nan ta fara zubda hawaye,wannan shine kadan daga cikin sakamakon da zaki samu wurin saba dokokin dana gindaya miki tsaki taja tana nuna mata kofa out of my room now,sim sim ta fice tana share hawaye ,dakin ta ta koma ta nemi bakin gado ta hada tagumi ta rasa me zatayi ,ace dan Adam hijab ma da zaayi sallah ya kasa taimaka wa ko domin lada ai ta danne zuciyarta lallai na yarda zama da safina babban tashin hankali ne agareni, knocking taji anayi daga bakin kofa da sauri ta miki tana zaton ko safina ce tai tunanin bata hijabin amma tana budewa sai taga wata dattijuwa a tsaye da alamun suma ma'aikatan gidan ne gaidata tayi ,maryam ma dai gaisheta tayi sannan tace dama hajiya ce tace aduba mata ko da wani abu da kuke da bukatar shi in kuma babu ga abun Karyawa chan a dining ko za'a kawo muku nan ne ,da sauri maryam ta girgiza kai tace Aa haba dai dama hijab nakeson inyi sallah kuma naga anty na bacci ko zan samu ,toh hajiya bari a kawo miki ta juya, maryam na nan tsaye har ta kawo mata hijab din ta amsa tana mata godiya , sallolin da ake binta tayi sannan ta fito da hijab din a jikin ta a parlon sama ta tadda momy da Khalil suna kallo momy na kan carpet a kasa yayinda Khalil yayi matashi da cinyar ta hannun shi rike da waya yana dan nawa nesa kadan dasu maryam ta zauna akasa ta gaida momy ,ta amsa tana Dada tambayan ta gajiyar hanya ta kai kallon ta ga Khalil wanda bai nuna tasan Allah yayi ruwan mutum a gurin ba ta gaidashi ,har ta cire ran zai amsa sai kuma raga ya sauke wayar hannunshi kura mata ido yayi wanda tasa dole ta sauke nata idon don bazata iya cigaba da kallon kwayar idon shiba gabanta yana tsananta faduwa ganin haka yasa momy tace maza ki tashi kije ki Karya in akwai abinda kike so sai ki sa a dafa miki ,toh maryam ta amsa ta tashi ta nufi parlon kasa wanda Ke dauke da dining area a gefe daban ta karasa ta zauna cup [7/11, 17:42] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… *kuyi hakuri fans matsala ne yasa kuka jini shiru ,masu kira da masu bina PC nima ba haka naso ba,amma ina yinku sosai😍😍😘* *~jama'a cigiyar oum zahra duk wanda ya ganta zan bashi kyautan page na gaba~*😎 *_mmn najwa Allah ya bar kauna😘_*. *maman sultan kar ki damu gani na dawo da 🐴🐴na*😜 πŸ…Ώβž–1⃣1⃣ *Habib* Sai yamma misalin karfe biyar ya isa garin bauci a gajiye ya shiga cikin gidan bakin shi dauke da sallama, Inna na kwance ta jiyo muryar dan nata da sauri ta miki tana kokarin fitowa sukai kicibus da shi murmushi suka sakar wa juna kowanne na murnar ganin kowa,juyawa tai zata koma ciki da sauri Habib ya rungume ta tabaya yace kai inna kin dade fa baki ganni ba bazaki ji dumin jikin danki ba,janye hannuwan shi tayi tana murmushi tai gaba tana cewa ka shigo ciki ka huta tukunna ko,bin bayanta yayi ya shiga ciki akan tabarma dake shimfide a saman ledar dakin ya zauna ,ita ma kusa dashi ta zauna kan tabarmar , "Inna mun same Ku lfy,ya gidan ina su Hauwa ne ko Ke kadai ce a gidan ne?" murmushi tayi tace duka ni kadai tambayar toh muna lafiya kalau su Hauwa kuma sunje dinki saini kadai a gidan Yaya wajen aikin naka da wurin su alhaji, lfy lau inna duka suna lfy sunce a gaidaku ,ya bata amsa ,muna amsawa ya wajen yar tawa kuna jinta kuwa,nan da nan ya canza fuska ya ce lfy lau ta koma ma ai, Inna ta lura sarai da canjin fuskarsa amma saita basar tai Kamar bata gani ba tace to Allah ya taimaka bari a duba maka dan abunda zaka ci,gyada kai kawai yayi ita kuma ta fita, a plate din silver ta zuba mai lafiyyan yarasa da miyar ganye ta ajiye mashi ta juya gyara zama yayi sai gata ta dawo dauke da ruwan sha da roba daban murmushi yayi inna Allah ya bar mana Ke ya amsa ya wanke hannun shi a robar sannan yai bismillah ya fara ci cikin jin dadin girkin , saida ya cinye duka abinka da soja kuma dama shi baya wasa da cikin shi yai hamdalla yace inna Allah yai miki albarka dariya tai sosai tace ameen tareda kai amma nima kaina ina gab da fara hanaka abinci ace wannan yaro kullum akai maganar aure sau kace sai lokaci yayi to shi lokacin jiran ka zaiyi ne ,kai inna ya fada waike da zarar kin ganni sai maganar aure nasha gaya miki in lokaci na ... amshi nan inna tai mai dakuwa kayita jiran lokaci ga yar wajen babanka nan safina k.. dammm yaji zuciya shi ta buga waro idanun shi waje yayi yace inna wace safina nakeji , wacce kasani dai yar wajen babanka ta bashi amsa kai tsaye, da sauri ya katseta yana fadin what cikin d'aga murya nan da nan idanun sa suka kadai sukai jajir pls inna nazo ne in gaishe Ku don Allah kada ki kara furta min irin Wanan maganar don Allah inna sokoko tai kawai tana kallon shi hmmm ai shikenan kaje gidan mlm din zaka same shi ai,itama ta bashi amsa rai bace domin ita bataga wani aibu a maganar datayi ba,matsowa yai kusa da ita tareda cewa inna malam din yace wani abu ne yai mata tambayar dukda yadda kirjinshi Ke matsanan cin bugawa yana adduar Allah yasa kada yakasance hakan,rai bace inna tace ko daya sai dai nida nayi,ajiyar zuciya ya sauke da karfi yace Alhamdulillah don Allah inna abar maganar nan iya haka domin ba kisan Wacece safina ba,sai kai ta katse shi ,inna bari inje in gaida malam din kafin ya shiga masallaci ya katse zancen domin bukatar wani bacin ran a yanzu,Mikewa yai ganin batada niyyar amsa miki ya fice cikin sauri gudun kada ta sako wata maganar ko a hanya tunanin kawai yakeyi *asalin Habib* Haifeffen dan garin bauchi ne mahaifin shi Mohammad shima dan gauyen garin ne da mahaifiyar shi ,auren zumunci akai musu da innar Habib ,mahaifinshi Mohammed sana'ar saida koli yake bawani karfi ne dashi ba saidai rufin asiri inda suke Zaune babu nisa tsakanin su da gidan mahaifin safina dududu gida hudu ne tsakanin su kuma da sanayya tsakanin iyayen gashi abokin ne ga mahaifin safina shiyasa koyaushe suna tare indai yana gari sabanin mahaifin Habib da baiyi ko primary ba amma duk da haka jinin su ya hadu da mahaifin safina indai yazo gari gidan su Habib ne wurin zuwanshi haka ha aka haifi Habib sai bayan shekaru biyar sannan ta kara haihuwa mace Aisha sai Hauwa sai bilkisu daganan bata kara haihuwa ba wani lokaci da mahaifin safina yazo ganin gida alokacin mahaifin Habib yake sanar mai zaikai Habib makaranta allo karatu chan azare aiko ranshi ya baci yace Sam bazaa kaishi ba yaita mai fada da nuna mishi illar kaida karatun allo yanzu zamani ya chanza yace shiya dauki nauyin karatun Habib din harya gama secondary Insha Allah ,aiko dole haka ya hakura,a lokacin dama yana zuwa ta gwamnati yana aji hudu haka ya cigaba harya kammala secondary dinshin duk da kokarin da take dashi Allah baisa yaci jamb dinshin ba ganin haka mahaifin safina yasashi zana jarabawa a air force base cikin ikon Allah ya samu kuma yai nasara har ya gama duk da dai albashin ba wani yawa ne dashi ba amma yana rufa wa kanshi asiri lokacin daya dauki albashin shi na farko lokacin ya zo garin bauchi ya tadda mummunan labarin na rayuwar mahaifin shi sunsha kuka sosai har aka gama zama ya koma aikin shi kanwarsa aisha tayi aure a kauyen azare sai kannen sa su biyu suka rage wand shiya dauki nauyin karatun su dukda makaranta gwamnati ce ya kuma hada da saka su koyon sanan"ar dinki , Habib dogo ne baki wanda bakin ma kyau ya kara masa a matsayin sa na soja kyakkyawan gaske ne yana da kira irinta maza da suka amsa sunan su yana da hakuri da kauda kai sosai gashi da girmama na gaba dashi Habib kenan, *cigaba* kai tsaye ya karasa gurin malam wanda Ke tsugune yana alwalar magrib ,sai da ya idar sannan ya mika ma Habib buta yai alwalar suka wuce masallaci saida har aka yi isha'i kafin suka rankayo gidan malam din suka zauna bisa shimfida dake tsakar gidan suka fara gaisawa harda matan malam din anan yaci abinci na dare inda yaita kaucewa zancen aure hardai saida malam din ya kara sa zuciyar shi cikin wani hali sakamakon maganar safina da yayi mai ,murmushi kawai yayi wanda iyakacin shi labbanshi amma a zuciyar shi alkawarin yayi gobe zai bar garin da sassafe bazai iya zama ba kada karamar magana ta kasan ce babban ,haka ya samu ya bar gidan koda ya koma bai tsaya hira da inna Kamar yadda ya saba ba ya wuce dakin shi ya kwanta cike da tunani bacci yai gaba da shi ,washe gari karfe 7:00yace ma inna zai koma itama bata wani sake mishi Kamar da ba tai mai Allah ya ki yaye hanya ya ajiye mata yan kudin daya tara domin su ya tafi gwiwa a salube,... *Khalil , safina , maryam* yarinya Kamar ba gidan wani zata ba in ta hadu da wanda ba haka halin sa yake ba ya kenan zaayi zaman auren,sallamar Khalil ce ta katse mommyn daga tunanin halin safina da take dukansu suka waigo safina tace oh my gosh wannan gayen ya hadu fa karasuwa yayi yana tafiya Kamar mace cike da girman kai da jarumta sanye yake da suit light blue wanda sukai matukar yi masa kyau dogo ne sosai ha yafi Habib tsaho saidai kyau kowanne bazai nuna ma wani ba sai hasken fata da Khalil yafi Habib wanda shi yake rud'ar da kyawunshi,sumar kanshi kwance rake cike da gashi Kamar balarabe kuma ga gyara datake samu sosai sabanin Habib wanda bayada raayin tara gashi a kansa,sauke numfashi safina tayi a hankali cike da yanga da ji da kai tace welcome bro , hi kawai ya furta ya juya gurin mommyn shi ya jingina jikinta how was d day son ya office din mommyn ta tambayeshi cike da soyayya tana shafa sumar kanshi ,a hankali ya furta not bad amma dai am relly tired me kika aje min mom,kafin ta budi baki sallamar maryam ta katse su harara safina ta watso mata tana toshe hanci gefe murmushi mommyn tayi tace karaso nan 'yata ,nesa kadan da su ta zauna a kasa ta gaida mommyn ta amsa cikin sakin fuska ,ta juya ta gaida safina wacce tayi kamar batasan da ita akeyi ba tana kallon tv haka ta juya cike da tsoron wani wulakance daga Khalil muryar ta na rawa tace ina yuni as she expected shiru ne ya biyo baya sai da yai kusan minti biyu kafin ya budi baki yace Mommyn ina kika samu wannan mad girl din ya futa idanunshi a lumshe ya nuna maryam da yatsan shi,mommyn rasa abun cewa tai saboda kunyar wulakanci da sukai ma maryam,maryam kuwa bata San sanda hawaye ya gama wanke mata fuska ba sai ganin digar sa tayi a hijab dinta ya Allah wannan wace irin rayuwa ce daga mai useless sai kuma mad girl haka zan kasance cikin wulakance su Allah kai maji rokon bawansa ne ya Allah ina rokon ka ka gaggauta amsar addua ta in koma wurin ummina kukan zuci take mai kunar zuciya,maganar sa ce ta katse mata tunanin inda yake cewa can u imagine mommyn na aiki mad girl dinnan taki zuwa yai

Chapter 4 of 32