Share this page
shima duk cikin shirin kune?kuka take mai taba zuciyar mai sauraro Wanda ya sanya harira zubda hawaye ta sake rike mata hannun murya cikin tausayawa tace ki saurare ne pls ki samu nutsuwa kona minti biyu ne inyi miki bayani don Allah ba don niba ko don darajar abunda ke cikin ki,, Kallon cikin ta tashiga yi sai yanzu takejin kasanta yayi mata wani iri tamkar wacce ta kwana da pad a hankali ta zura hannun ta ta shafa gabanta ta fito da hannun kirjinta ya tsanan ta bugu daya ilahirin jikinta ya dauki rawa jini ,jini sosai ta firgice kadan ya rage ta suman zauna kallon harira takeyi tamkar itace alhajin tana son karin bayani akan hakan amma takasa tambayar domin batason kunnuwan ta sujiyo mata abunda zuciyar ta ke zargi,, Kusan minti uku tana kallon hannu batareda tace komai ba hakan ya sanya dole harira ta sauko da sauri ta dauko tissue a toilet da sauri ta shiga goge hannun da wurin da ta cizge drip din shima har lokacin jinin yake fitarwa,, Sai da ta share mata tass kafin ta soma magana murya a sanyaye tace ki surarane maryam cikin jikin ki yananan daram bai fita ba said ai tada hankalin dazakiyi ayanzu zai iya fiddashi kuma babu wani Abu da Alhaji yayi miki,, da sauri ta dago da idanunta tana kallon hariran kai ta gyada mata cikeda tabbatar wa tace kwarai kuwa nan ta gaya mata yadda akayi,, taji ciwon yadda Alhaji yayi mata ammm ta godiwa Allah da babu abunda ya shiga tsakanin su,, Komawa tayi ta jingina bayanta da fuskar gadon tana sauke ajiyar zuciya har lokacin hawayen na ta sharara daga idanunta basuda alaman tsayawa,, Dafa kafadar ta harira tayi tace ki kwantar da hankalin ki insha Allah bazaki kara kwana gidan nan ba zan San yadda zanyi,,gyada mata kai kawai maryam tayi batareda ta iya furta komai ba,,, Duk wani shiri sunyi shi inda Habib yaso dakatar da khalil amma yace Sam hakan ba zai wuyuba dole suka fito tare gaba daya su su bakwai din a motar daya suka zauna saboda dare ne sosai yawan motocin na iyakawo musu matsala inji Muhammad jb da sannu suke bin duk wani kwatance na gidan har suka kusa da inda arean gidan ya fara suka parker motar suka kashe suka dauki makaman su kowa yayi shirinsa yadda ya dace suka tunkari gidan cike da fatan samun nasara ,,,, *tummmhh*๐Ÿค”๐Ÿฅบ *mrs noour*โœ๐Ÿป [7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *๐Ÿด๐ŸดKARFIN IKO๐Ÿด๐Ÿด* ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com Wattpad me @pheeymarrh *HIKMAAH writers association* Edited by๐Ÿ‘‰๐Ÿป *oum Zahara*๐Ÿ˜ Dedicated 2my lil sis๐Ÿ‘‰๐Ÿป *Maman Sultan*๐Ÿ˜˜ ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู… ๐Ÿ…ฟโž–6โƒฃ7โƒฃ Babu laifi karo na farko kenan a tsahun rayuwar ta data tsaya cikin dare domin rokon ubangijin ta akan al'amuran ta,takuma samu nutsuwa sosai cikin zuciyarta zuwa ga gangar jikinta har saida aka tada sallah kafin ta kuma mik'ewa tayi raka'atanul fijr sannan tayi sallah ta dade zaune hannayenta na sama ta rok'on Allah yafiya kafin ta jingina da drower littafan karatun Habib, Har lokacin hawaye ne ke silalowa daga idanuwanta wadanda harsun kankance saboda kukan dataci tausayin makomar ratuwar ta takeji data abunda ke cikinta Dana iyayenta musamman dad dayaci burin inganta rayuwar ta su sami zuri'a yalwatacciya daga gareta sai gashi ta rushe duk wannan hade da gata da illimin da suka bata, hannun ta sanya ta share hawayen ta mike jiki a sanyaye ta bude kofar ta nufi sashen gidan zuciyar ta na bugawa cikin sauri sauri sama ta nufa kai tsaye dakin dad da sallama ta tura ta shiga bakin gadon ta zauna tazuba masa idanu tamkar bata taba ganin sa ba kwance yake har yanzu numfashin sa bai daidaita ba sai dai drip din dataga an cire kama hannu sa tayi ta rike tana kuka a hankali tabbas ta aikatan laifi mai girma Wanda karbar hukunci sa ya zame mata dole Allah ya baka lafiya dad ka yafe min dad ka yafe min nayi nadama wallahi dad nayi nadama hannu ta sanya ta toshe bakinta gudun kar ta tasheshi ta mike ta fice a dakin kukan yataho mata gabadaya Wanda take dannewa dakin ta ta nufa ta fada gado tana kuka sosai,, Da sallama ta shiga dakin hannun ta dauke da wasu kayan ta ajiye mata a gefen gadon kafin ta kamata ta mike da kyar don har lokacin marar ta tushe take jinta take a dunkule tamakr intayi nishi cikin zai fita har cikin toilet ta kaita ta hada mata ruwa da kanta cikin bathtub mai zafi sosai saboda bugun dataci gurin Alhaji saida ta kamata ta shiga kafin kafin ta ajiye mata towel ta fito,, Ajiyar zuciya ta sauke mai karfi tana tajin radadin zafi inda ta daku sai dai tana jin dadin yadda ruwan yake ratsa cikin tsoka da k'ashin jikinta,bata jima ba ta mike ta fito saboda yadda jini ya bata ruwan ,wani ta sake tarawa ta koma ta kara gasa jikinta da marar ta kafin ta daura towel din ta fito kayan ta amsa ta sanya tana mamakin yadda lokaci daya harira take nuna damuwa da tausayi akan ta sai faman zuba mata sannu takeyi zama tayi bakin gadon ta sanya hannu ta amshi mug din da harira take miko mata Wanda tea ne a cikinsa,kafa kai tayi ta sha kusan rabi kafin ta cire daga bakinta tana kallon harira"na gode da kulawar ki ,,mai yasa kike nuna tausayin ki agare ne a yanzu maryam tayi mata tambayen,, Matsowa tayi ta kama hannun ta tana murmushi tace saboda ni yar uwarki ce musulma kuma yar uwar ki mace saanan yar uwar ki ta jini kedai kiyita addua Allah ya kubutar damu daga nan yar uwa tana gama fadar haka ta mike ta nufi kofa,, Tasss,tasss sukaji kara mai karfi tamkar na bindiga Wanda ya hana maryam sake yi mata wata tambayar ta saki mug din hannun ta akasa tana rufe kunnuwanta da hannayenta Bayan ta rintse idanunta da karfi gaba daya jikinta ya dauki rawa da sauri harira ta dawo kusa da ita ta rungumeta tana fadin ki nutsu maryam kar tsoro ya sanya abunda ke cikin ki fita yaran Alhaji ne mun rigada mun saba da wanna halin dabbobin nasu wani kararsukaji Wanda ya tarwatsa window dake dakin yayinda gujeje yayi yawa a harabar gidan da sauri harira ta kamata suka duka kasa anya kuwa lafiya gidan nan,inna lillahi kawai maryam ke ambata cikin karkarwa gaba daya ta firgice saboda yadda karar yake ta yawaita,, Jan hannun ta tayi suka rarrafa suka bude kofar duk a rikice suke don itama dauriyar kawai takeyi tasan tabbas babu lafiya sama suka nufa ta shige da ita bangaren Alhaji inda tayi mamakin ganin dakin a bude amma dayake a tsorace suke bata tsaya bi takan haka ba mabuya suka bema chan kuryar dakin Bayan kuje ru suka sakada,, Gida fa ya koma filin yakin babu alamar Abu zai yi sauki saima kamar ji sukeyi ana Harbin har cikin parlon mikewa harira tayi da sauri maryam ta rike kafafunta tana kuka tana girgiza mata kai alamar karta fita,janye kafar ta tayi da karfi ta dauko wayarta datahango akan dan table din dake tsakanin kujerun parlon ta dawo da sauri ta jiga kira ita dai maryam kuka kawai takeyi tana neman agajin ubangijin ta a kwanakin nan addua mutiwar ta kawai take roko kozata huta amma sai gashi yanzu gaba dayan abun ya firgitata ya kidimata ga ciwon marar ta dake karuwa kowace dakika,, Police station harira ta kira cikin gaggawa tayi musu kwatancen gidan saukar harbi taji a kan kafadar ta Wanda ya sanya ta yarda waya tana fasa kara cikin wata irin azaba dabata taba jiba arayuwar ta sunkuyawa tayi da sauri tana dafe da kafadar kadan ya rage maryam bata dauke numfashi ba saboda gigta ganin yadda jini ya wanke jikin harira lokaci daya kuka take sosi ta dafe bakinta da hannu daya yayinda dayan kuma ta kwakume hannun hariran da iyakacin karfin ta, "Uban waye yabaki damar kiran yan sanda a cikin wannan gidan ban gaya miki doka bane babu Wanda yasan da zaman gidan nan lallai ki tabbatar da saina tarwatsa kanki matukar naji da sunanki a kawo farmakin nan" muryar Alhaji sukaji daga Bayan su yana maganar cikin karaji da Bacin rai"" Dukda arikice suke hakan mai hanasu mamakin ganin sa ba agidan, kallon sa kawai sukeyi a matukar tsorace karasowa yayi inda suke ya damke kafadun maryam da iyakacin karfin sa ya fizgota daga Bayan kujerar yana saita bindigar sa kanta wallahi indai wanna shegen mijin nakine saina kashe shi sanan kema in kashe ki shigiya mai jinin tsi... Karar harbi sukaji Wanda yasanyasu fasa kara duka su ukun kasa maryam tayi tana sallati da iyakacin karfin ta don jin harbi tayi tamakar a tsakar kanta akayi rarrafawa ta soma yi ta koma inda hariran take saiji tayi an riko kafarta ta bayan dagata sama gaba dayan taji anyi da sauri ta budi idanunwanta tana kallon fuskar sa nan take ta dauke numfashi,, Karar buga kofarta ne ya sanya mom fitowa ta nufi dakin ta tsaye tayi a kanta tana kallonta cikin tausayawa tabbas yarta ta jifa kanta ga babban ramin da zaiyi wuya wani ya iya fiddo ta ma balle ita kanta,tasan sunyi sakaci akan tsawatarwa safina intana da laifi kaso arbain su zasu dauki kashi sittin din cikin dari, hannu ta sanya ta dauke hawayen daya taru a gefen idanun ta zama tayi kusa da safina ta dago kafadar ta ta rungumeta a jikinta kuka sosai safina ta kara rushewa da shi da kyar ta iya fadin mom nayi nadama wallahi nayi nadama mom na cuci kaina mom ina zan saka kaina da abunda ke cikina ga halin da dad yake ciki tun bashida tabbas din ni na aikata haka inaga yasan tabbas din nice nayi mom mai zai faru dashi mo... ""Innalillahi wa inna ilaihir rajiun safina kikace kece"" muryar dad ta katse maganar safina da sauri suka waigo suka kallon sa a rikice kan suyi yunkurin yin wani Abu saigani sukai ya zube kasa wanwar da gudu zuga rugo zuwa inda yake suna kuka gaba dayansu suna jijjaga shi ganin hakan ba zai fisshesu ba ya sanya mom fita da gudu kasa ta kira securities din dad cikin gaggawa suka daukeshi akayi asibiti dashi safina na kankame dashi tana fadin kayafemun dad karka mutu ka barni cikin gararin rayuwa banida wani gata inba nakaba a duniya nan har suka isa asibitin baban dake Abuja manyan doctors suka karbeshi cikin gaggawa akayi emergency dashi inda safina ta zube a gurin itama sumammiya kara mom ta fasa tana rikota tana kwala kiran doctors su taimaka mata itama da sauri aka dauketa akayi emergency da ita sai dai ba dakin su daya da dad ba,, Hannu mom ta daura akai tana kuka tana fadin. Na shiga uku ni yau wane irin musibace haka take shirin fada mana ne haka inna lillahi wa inna ilaihir rajiun,,,, Tunda ya dawo sallar asuba yake jiran shigowar khalil su wuce Kano amma shiru gashi har shida tayi mommyn dake zaune kusa dashi tace ko a kirashi ne ko kuma wayarsa zaa nema,, Aa yace bari inkira wayar sa banason a tasheshi in ya samu bacci ne kina kallo tunda abunnan ya faru baya samun ishasshen hutuma balle bacci ki barshi zuwa bakwai sai a dubashi,, Toh kawai tace tana gyada kai itadai tasan lafiya bazata taba sanya khalil kin fitowa su tafi ba balle bacci ko ita jiya sai dai bacci barawo amma bawai na dadi ba kona gajiya kuma kiran sallar farko taji kwanciyar ta gunduri rayuwar ta balle shi da ruwan shayi ma ya kurba gagararsa take sai an tasashi gaba amma zatabi ta tashin ajiran bakwai din tayi,adduoe ta tacigaba dayi kamar yadda daddyn ke ta laziminsa,, Bakwai sauran minti goma kira ya shigo wayar daddyn inda ya ce toh kin gani gashi ta tashi da kansa wayar ya duba bakuwar number yagani dagawa yayi cikin sallama,, Bata tsaya amsa sallamar ba saima kuka data fashe dashi tana fadin sun mutu Alhaji kayi gaggawar zuwa daddyn safina da ita kanta ba lafiya, sallati yayi da karfi yana fadin kuna wane asibiti ne,nan ta gaya mishi ya katse Koran yana fadin ganinan zuwa yanzun insha Allah,, Tun kafin ya katse kiran mommyn ke tambayar maiya faru Alhaji lafiya kuwa maiya samu khalil din,, Ajiyar zuciya ya sauke da karfi kafin yace dad ne da safina suke asibiti babu lafiya,,bari inje kije ki tashe shi kawai ya shiryo yasameni a asibitin ya fada yana mikewa,, toh ta amsa dashi ta nufi sama tayi sallam yakai sau uku a bakin bedroom dinsa shiru dole ta shiga ciki ta dan tsorata ganin Bayan cike ta karasa bakin kofar toilet ta yi knocking nan ma shiru harsau uku hankalinta ya fara tashi ta bude toilet din bayyan gadayan partdinsa ta leka koina bayanan sai wayoyinsa da suke zube akan gado ina yajene son,, Harabar gidan ta nufa cikin gaggawa ta karasa inda daddyn yake harya driver ya tada mota ta tsaidasu tana fadin bayanan fa Alhaji Bayan ciki anya kuwa yana lafiya Alhaji bai kwana a gidan nan bane kokuwa,, Shima hankalin sa ya tashi amma saiya dake yace karki damu bari in karasa asibitin yanzu duk inda yake zan nemeshi,, Amma Alhaji bai dauki wayar sa ba kodaya fa kardai shima daukeshi akayi A... A uzu billahi hajiya meye nayi mawa wanna mummunanan tunanin Bayan tashin hankalin dake gabanmu don Allah kibar wanna pls yana nan lafiya maybe yarigani in gaba ne ki koma gida zan nemeshi yana gama fadar haka ta shige cikin motar driver yaja suka tafi gaba daya shikanshi tunanin sa yafara kwancewa addua kawai yakeyi cikin zuciyar shi,, Babu yadda ta iyadole ta koma ciki tana sharar kwalla wannan wace irin rayuwa ce haka wane irin tashin hankali ne yake bibiyarsu haka zubewa tayi kan kujera jagwab tana zuba tagumi da hannayenta biyu,, *mrs noour*โœ๐Ÿป [7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *๐Ÿด๐ŸดKARFIN IKO๐Ÿด๐Ÿด* ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com Wattpad me @pheeymarrh *HIKMAAH writers association* Edited by๐Ÿ‘‰๐Ÿป *oum Zahara*๐Ÿ˜ Dedicated 2my lil sis๐Ÿ‘‰๐Ÿป *Maman Sultan*๐Ÿ˜˜ ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู… ๐Ÿ…ฟโž–6โƒฃ8โƒฃ Tattaro karfin ta tayi ta mike jiri na dibarta ta nufi maryam hankalinta tashe tana kiran sunanta da karif,, Tallafota yayi a matukar rikice ya soma jijjiga ta yana girgiza kanta bindigar hannun sa ya yar a kasa ya rungumeta sosai jikin sa yana kiran sunanta da karfi ina babu alamun numfashi a tattare da ita,mu gaggauta kaita asibiti pls ga jini na zuba mata harira ta fada cikin rudiya kallon wurin yayi yaga jini ne sosai yake zubo mata juyawa yayi da sauri zai fita da ita saiji kake tasss ,tass Wanda ya sanyashi faduwa kasa tareda maryam din rintse idanu yayi da karfi saboda azabar radadin dayake ji yana bin dukkan sassan jikin sa harbi ne Alhaji yayi masa a gefen hannun sa Allah ya tsare lokacin dayayi saitin harbin tsakiyar cikinsa Habib ya shigo inda ya harbesa a hannun amma dayake shima yagama tsaida harbin saida yasameshi,, Da sauri suka karaso cikin dakin suka kama Alhaji yayinda Habib yayi saurin daga ya khalil Wanda tuni jini ya wanke masa rigarsa har wando shima ya baci kokarin dago maryam yake yi amma ya khalil yayi sauri rigasa kai hannu alamun ya barta kawai,, Dole ya matsa gefe da kanshi ya dauketa ya fice da gaggawa ,ya Habib ya riko harira suka kaisu mota Muhammad jb yajasu cikin matukar gudu suka bar gidan suna fita motocin yansanda dana sojiji suna shogowa wurin,, Da kansa suka sanya Alhaji a mota tareda sojoji guda biyu da yansanda guda biyu suka yi asibiti dashi inda suka tadda har an shiga dasu maryam emergency ana dubasu,, Waya ya nema ya kira layin daddyn ya sanar masa abunda ya faru habkalinsa yayi matukar tashi amma Habib ya kwantar masa da cewar zai samu sauki saboda baa wuri mai hadari ne akayi harbinba,Allah ya kyautar ganmunan zuwa sai dai shima dad gashinan a asibitin babu lafiya ka karaso kawai zan taho nan din,,toh daddyn kawai yace ya kashe kiran,, Number safina yashiga nema amma shiru sai ring takeyi baa dagaba ya kira yakai sau shida kafin ya hakura ya koma kofar emergency room din ya tsaya zuciyar sa fall ciki da damuwa wadannan abubuwan marasa dadi dasuke ta shigowa cikin rayuwar su,, An samu da kyar an shawo kan numfashinsa sai dai yakasa dawowo dai dai dole suka sanya masa oxygen tareda yi masa allurar bacci ta 48 hour ko zaa samu cigaba ,, Safina kam stress din data jifa kanta ne da damuwar hukuncinta ya sanya ta suman inda sun samu ta farfado itama dai drip din suka sanya mata tareda yi mata allurar bacci,, Sai da likitocin suka yi musu bayani kafin hankalinsu yadan kwanta mom tayi zuru zuru da ita ta rame saboda damuwa da kyar daddyn khalil ya sanya ta ta yadda ta kira gidansu tasan halin baban ta fada ne kawai zai yi mata yadada mata damuwa akan wacce take dukda tana tabbacin bama shima dayake dolenta tabbas zasu sha zagi da tsinuwa agari wurin jamaa in maganar nan ta watso wanda basuda ikon hana faruwar hakan,, Sallama daddyn yayi mata ya tafi Bayan ya shiga dakin safinar ya duba ta dad kam sun hana ganin sa sam kafin ya tafi don shima dauriyar kawai yakeyi hankalinsa yana ga kan dan nasa tilo saukin ma daya daya sanyashi nutsuwa ganin maryam din dakayi,, Gida ya fara zuwa ya tadda mommyn zaune a falo ta zabga uban tagumi da hannu biyu tana zirarar da hawaye,, girgiza kai kawai yayi ya karasa inda take sunan ta yashiga kira har sau biyu bata amsa ba saida ya dafe kafadar ta da dan karfi kafin ta juyo da sauri tana share hawayen sannu zuwa ta fada a sanyaye ta kauda kanta,, bai amsa ba yace tashi ki shirya muje asibiti yanzu,kallonsa tayi da sauri cikin mamaki ta bude baki zatayi masa magana ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu yasan abunda zata fada ya wuce sama ya kyaleta,, Dole ta mike itama rai bace tana mamakin wannan Abu babu maryam babu khalil amma shi ta asibiti ce ta dameshi Bayan tayi ta kiran wayar sa yaki dagawa,,hijab kawai ta dauka akan praying mat ta sanya ta fito a parlon ta tadda shi ya sanya kaya daga manya zuwa jallabiya gaba yayi ta bishi suka shiga mota baice mata kala ba har suka isa asibitin,, Shiya fara fitowa kafin ita hannun ta ya kamo ya rike yana jin tausayinta har cikin ransa yadda ta sanya kaunar maryam cikin zuciyarta ga kuma ya khalil tabbas yasan ba karamin tashin hankali zata shiga ba inta gansu shiyasanya ma bai tsaya yi mata wani bayani ba akan abunda yake faruwa,, Jigum suka tadda su ya Habib da Muhammad jb suna jira har lokacin shiru baa fito da kowa ba ,,gaida su suka yi ,suka amsa tareda tambayar Yaya jikin nasu,, Habib ne yayi musu bayanin halin da ake ciki aikuwa mommyn neman zubewa tayi a kasa tana sallati da karfi kamata dad yayi ya zaunar da ita tana faman kuka tamkar ance mata sun mutu,,da kyar ya lallashe tatadaina kukan ta soma yi musu addua,, Kusan minti talaltin da zaman su aka fito da maryam aka kaita wani dakin ,,da sauri mommyn da dad suka mike suka ni Bayan su hanasu shiga akayi aka rufo kofar Wanda ya sanya mommyn kara fashewa da kuka tana fadin na mai zagayawa ummi ne in wani Abu ya sameki Allah ya tashi kafadun ki, Bai tsaya rarrashin taba yabi Bayan doctor din zuwa office ya Dade zaune yana rubuce rubuce kafin ya gama ya dago yana kallonsa,, Yaya jikin ta pls doctor, dad ya tambaya cikin fargaba,, Saida ya sauke ajiyar zuciya kafin yace jikinta da sauki sai dai munyi kokarin muga ansamu tsaida jinin abun ya gagara duba da yadda kusan kaso hamsin da uku na cikin ya fita dole aka yi fitar dashi ya rigada ya lallace sai jininta da ya hau kadan sai gojewar kashi da tayi a hannu ta Wanda shima angyara shi ,,don haka dole zakuyi hakuri da ganinta sai zuwa gobe tana bukatar Hutu sosai,, godiya yayi masa kafin ya fito yaji jiwon zubewar cikin nan amma babu yadda suka iya da hukuncin ubangiji baiyi wa mommyn bayanin cikin ya zube ba kawai yace ta samu sauki zuwa gobe zaa iya ganinta kawai damuwa ce ,ta dan samu nutsuwa tana yiwa Allah godiya don ita tafinjin ta maryam din musamman yadda ba ita kadai bace,, Bayan kusan awa uku kafin aka fito dashi shima dakin aka kaishi kusa da nata Wanda dad dinne ya roki hakan saboda sanya matakan tsaro a wurin su,shima din baa bari suka ganshiba likitoci dai sun tabbatar musu da Anyi aiki cikin nasarar an cire bullet din bai kuma samu wani ciwo ba bayaga harbin shima zuwa gobe zasu iya ganinsa,, godiya suka yi musu sosai inda babu bata lokaci yan sanda suka kewaye asibitin da bangaren dasuke zuwa dakin ,sai alokacin ya Habib yayi musu sallama ya wuce,, Alhamdulillah dukkansu washegari sun farka cikin koshin lafiya inda ya khalil ya tubure shi fa saiyaje ganin matarsa dole babu shiri aka maidashi dakin datake mommyn da maryam suna zaune sai gani suka yi an shigo dashi mommyn kam sakar baki tayi kawai tana kallon ikon Allah yayinda maryam tayi kasa da kanta zuciyarta fall farin cikin ganin sa tun dazu take zuba idon ganin sa ta kuma kasa tambaya shi kuwa gogan yiyayi tamkar ma baisan da mommyn a wurin ba ya nufi maryam gadan gadan yana kare mata kallo cikin farin ciki kiss yayi mata a goshin ta yana Watson mata iskar a wurin babu yadda ta iya duk yadda ta kai ga kaucewa saida ta lumshe manyan idanunta yadda taji sakon har cikin jinin ta,, Sallati mommyn ta saka da dan karfi ta soma fadin wallahi son yanzun nan zan muttsuke hannun nan inga ta rashin kunyar ka ta fada da murmushi akan fuskarta,, Sai a lokacin maryam ta dago tana kare masa kallo hankalinta ya tashi sosai sai yanzu ta lura maiya same shi haka daure hannun yake da bandage tun daga kafadar sa hannun ya kumbura sosai,kasa tayi da kanta tana kokarin maida hawayenta zuciyarta harta chanza yananyin bugawar ta,, Murmushi yayi ya matsa kusa da ita yayi mata peck a goshinta kafin cikin sanyi murya yace son din naki mommyn zaki iya kuwa,, da kyar aka samu ya zauna kan gadon suka maida masa drip din sa hankalinsa gaba daya yana kanta musamman daya lura ta shiga damuwa ganin ciwon dayake jikin sa ,, Ganin Abu babu sauki dole mommyn ta mike tana fadin da alama dai bakuda bukatar zamana anan kwaye jinyar kanku nima bari inje gun nawa mijin ta fice taja musu kofa,, Kokarin mikewa yakeyi da sauri ta rigashi ta sauko zuwa gurinshi ta kama hannun sa ta rike sai a lokaci hawayen datake rikewa suka balle tamkar an bude famfo hannun sa ta daura bisa kumatunta tana lumshe idanu saida tayi two mins a haka kafin tasumbaci hannu ta kura masa idanu "maiya sameka haka my hayat"" ta fada cikin sanyin murya cikin kuka,, Rungumota yayi ya kwantar da ita gefen sa yana shafa bayanta bai bata amsa ba a haka har bacci ya daukesu duka suna makale da juna(ho khalil ba kunya a asibiti ma๐Ÿค”) Sanyi asubahi ya farkarda ita a hankali ta bude idanunta wadanda suka yi mata nauyi sosai tana jin dan radadi cikinsu har yanzu Wanda Bayan rasa nasaba da kukan dataci,,babu kowa a dakin agogon ta kalla dake jikin bango har Anyi sallar asuba,, Mikewa tayi a hankali ta nufi toilet alwala tayi ta fito babu hijab dole ta bude gyalenta na kai ta yafa Allah yasa yanada dan girma ta tada sallah jikinta a matukar sanyaye takeyi sallar,, idarwar ta yayi dai dai da shigowar sa dakin kallon ta yayi kafin ya kauda kansa yanemi wuri ya zauna a daya daga cikin kujerun dake dakin yashigaba da Jan chazbin shi idanunsa a rufe,, Kan gadon ta koma Bayan ta idar da sallar tana kallon ya Habib din magana takeson yi masa ta rasa

Chapter 30 of 32