Pheeymarrh@gmail.com
*HIKMAAH writers association*
Edited byππ» *oum Zahara*π
Dedicated 2my lil sisππ» *Maman Sultan*π
Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
π
Ώβ5β£3β£
Gaba tayi tana kunkuni dukda zuciyar ta cike take da tsoron dad da mamakin abunda yayi mata Wanda bata taba ganin haka daga gareshi ba,,
Tura kofar tayi batareda sallama ba ta shiga tana neman gurin zaman,,daga kai malam yayi ya dubeta na tsawaon second shida kafin yace koma kiyi sallama ya mai da kansa ya cigaba da karatun sa,,
Jimm tayi bata da alamar motsawa saida ta hada idanun da dad din nata taga babu alamar sassauci saana ta juya ta koma ciki ciki tayi sallmar tana kumbura baki da fuskar,,
Dad kauda kai yayi cike da bakin ciki yayinda malam ya dago yana amsa mata da fara'arsa kamar babu wani bacin rai ataredashi jikita andawo kenan ko,,ya fada da wasa kamar yadda yasaba yi mata,,
Eh grandpa ya kake ta amsa fuskar ba yabo ba fallasa kamar ba grandpa din taba,,
Girgiza kai kawai malam yayi yace wa dad inason ganin kowa a cikin parlon nan gobe da safe bayan sallar asubahi kafin mu tafi,,
Toh malam Allah ya kaomu dad ya amsa ,,
Dubansa yakai ga safina yace maza jikata jeki hita duk wata maganar abarwa gobe in Allah ya kai mana rayuwar kinji dare yayi sosai,,
Mikewa tayi ta fice daga dakin batareda ta tanka malam dinba balle ta amsa koda adduar dayayi ne da ameen,,
Dukqr da kai dad yayi cike da nadama sosai yana bakin ciki da wadannan halaye na yarsa Wanda da sam basu taba bata ransa ba sai yanzu a lokacin da lokaci yarigada ya kure masa,,
Gyaran malam yayi yace maza tashi ka shiga ciki Allah ya tashe mu lafiya,Allah yayi muku albarka,,
Ameen dad ya amsa yamike ya fice zuwa dakin sa bata cikin dakin mom dama baiyi tsammanin ganin taba tunda fushi takeyi dashi balle yanzu daya aurawa safina Habib toilet ya shiga ya dauro alwala ya shiga jero nafilfilu tareda adduoe da malam yabashi yayi saida ya gama saanan ya kwanta,,
Rungume take jikin mom ta na kuka sosai yan uwa sai bata hakuri akeyi da Allah wadai da halin dad kanwar mom tace wallahi ni har mamakin abun yake bani abu kamar a mafarki taya kamar safina da gata da mutunci da kimarta zaa hadata da kurtu Wanda yake matsiyaci gaba da Bayan Wanda arzikinta yake ci ai gaskiya dad yayi baban kuskuren wallahi,,
Dagowa safina tayi murya cikin kuka tace barshi anty ai wallahi saiya gane shayi ba ruwa bane in yana tunanin yayi nasara ne toh wallahi ni safina saina karshi har lahira da bakin cikina zaiga Wanda zai zauna inuwa daya dashi wallahi,,
Mom dai ta kasa maganar sai hawayen bakin ciki kawai take sharewa ita baban bakin ciki ta kawai shine maryam yadd tayi nasara akansu ita nata kudurin yanaga maryam ne wallahi indai har tana numfashi saita wulakanta rayuwar takamar yadda rayuwa yarta wannan cin mutincin,,
Har daki ta raka maryam ta hadata da didde saboda su kwana tare saboda sanin halin maza musamman dan nata daya nuna damuwar kasancewa da matar,,
Aikuwa taji dadin kwanansu tare da kakarta kusan kwana sukai basuyi barci ba tana kara bata labarin dangi da yanuwa dakuma yan dabarun su na zaman aure Wanda kuma ta karu dasu sosai musamman yadda ita ba kawa garetaba ba amfani take da waya ba ba wani abu tasani ba nagameda zaman aure Wanda wannan tunanin ya sanya mommyn hana tarewar ta kamar yadda ta gaya mata dazu,,
Sai karfe shida da Rabi ta tashi toilet ta shiga ta wanke bakinta saanan ta fito hijab din sallar ta tazura ta fice daga dakin ta janyo wa didde kofar ganin batada alamar tashi kai tsaye dakin mommyn ta nufa kamar yadda ta umarce ta,,
Da sallama ta shiga inda mommyn Ke zaune ta nufa ta zauna akasa ta gaidata saanan ta gaida ummi cike da faraaa suka amsa mata tareda tambayar didde tasu,,,
Babu bata lokaci mommyn tasa mommyn hassana ta soma gyarata a cikin toilet tayi wankan aka durjeta da halawa tayi wankan turaruka saanan suka fito zazzafar madarar mommyn ta miko mata ta shabye ta tass dukda babu suger amma taji dadin ta yadda dumi ya ratsa ta tunda tsakar kanta har tafin kafarta,,
Foodflask mommyn ta miko mata tace maza ta cinye abunda Ke ciki duka,,ummi mikewa tayi tana dariya tace vari inje nima wurin dana wannan shiri haka gwara musan yadda zamu bullo muku,,
Dariya sukai gaba daya banda maryam data kara dukar da kai tana murmushi jin dadi akoyaushe bata gajiyawa dayi ubangiji godiya yadda ya gata tata lokaci daya batareda yarda ko taimako kowaba hawayen ta goge a hankali ta bude dankareriyar Kaza ce wavcce akayiwa farfesuda magunguna kala kala sai kamshin kayan yaji takeyi,,
Kuka take fedda sauti sa a hankali tana shissheka tana jikin mom dinta ita kanta jitakeyi da dama data taya yar tata kokawa amma batason karyar mata da gwiwa,,
Sosai malam yayi wa dad fada akan saken dayayi da sangarta safina wacce ita tarbiyya baayi mata haka,,
Saan an yayiwa safina da Habib fada sosai akan suji tsoron Allah kowa yarike hakkin da Allah ya dora mishi su zauna lafiya,,
Sosai Habib yayiwa su dad godiya dukda har cikin ransa baya farin ciki da wanna aure yasan siyar wa kansa tashin hankali yayi yana da tabbaci shikenan yayi ban kwana da farin cikin rayuwa domin kuwa ta zamemasa dole bazai iya wulakan tataba saboda darajar malam da dad koda mai zatayi masa,,
Ita kuwa safina tsine masa kawai takeyi da fatan mugun alkaba'i gareshi cikin zuciyar ta lokacin dayake godiya,,
Saanan a karshe malam yace maganar makarantar ya soketa a wanna lokaci ranemi izini gurin mijinta chan shima ba wannan shekarar ba sai dai ta gama in muna da rayuwa,,
A firgice ta dago tana sake sakin wani kukan da karfi grandpa na gama yin registration fa maiyasa bazan yi ba bayan bashi ne zaibiya ba maiyasa haka ne kuke son muzguna min,,
Tsawa dad ya daka mata tareda jefo mata dakuwa murya cike da bacin rai yace maza nakara jin musu daga gareki wallahi sainayi mugun saba miki maza ki tashi kiyi karasa dibar kayanki kibar min gida yanzu na gaji da rashin tarbiyyarki banyi musu da malam ba babu Wanda ya isa yayi musu dashi ,,
Kara fasa wani kukan tayi tamike da gudu ta fice daga dakin kan gado ta fada tana kuka kamar ranta zai fita ita ce dad dinta yakeyiwa haka duk gata da kima da dagawar tawai itace zata zauna zaman aure da Habib duk saboda waccan tsinanniyar maryam mikewa tayi ta shiga hada kayanta tana kudurtar mugayen kuduri a zuciyar ta gameda maryam din da Habib,,
Mom ce ta shigo itama idanun ta jazur da alamar taci kuka harta gaji kwantar wa da safina hankali ta shiga yi tareda karfafa mata gwiwa akan zata daukar mata mataki akansu duka,,
Suna maganar dad ya shigo daga bakin kofa ya tsaya murya a kausashe yace mikomin visa ki dukan su nan da ATM dinki duka,,
Sakin baki tayi tana zaro idanu waje Wai maiya samu dad dinta ne haka mai yake nufi,,
Mom ce tace Wallahi alhaji hakan kuma ba zata sabu ba ai wannan zalunci ne karara da nun kiyayya kake kokarin nunawa yarka akan wani bare chan banza tunda tace zata bishi meye kuma nayi mata wanna tsatsauran hukuncin,,
Murya a dakile yace wanna shine hukuncin dana yanke yimata a lokacin data wulakantani a idon duniya saboda gata da ikon dana bata akan rayuwar ta amma tayi watsi dasu saboda haka amsar hukunci yazamar mata dole,,
Neman kukan tayima tarasa zuciyar ta ta kekashi fushi da tsana suka kara mamaye zuciyar ta kai tsaye ta wuce bedside drawer ta bude ta Ciro masa harda keys din motocin ta ta yafa gyalen ta ta fice daga dakin,,
Baiyi mamakin ba datayi hakan saidai baitaba dauka safina zuciyar tata takai kekashewar dazata iyafushi da dukiya da jin dadi ba juyawa yayi ya fice batareda ya tanka daya daga cikin maganganun da mom Ke gasa masa ba ,yayi alkawarin gyaleta har baki su tafi da sannu itama zaiyi maganin ta,,
Malam ne gaban mota da driver,sai ya Habib da safina a bayan zasu kama hanyar bauchi dad yana tayi musu fatan alhairi da Allah ya tsare yayinda mom da ahlinta babu Wanda yako leko balle susanya musu albarka har suka fice daga gidan sai a lokacin safina ta samu damar fashewa da wani iron kuka mai karfi da cin rai,, babu Wanda yayi kokarin rarrashin ta har tayi tagaji bacci yayi gaba da ita dama ba saba tafiya dogowa tayi ba a mota sunsaba da jirgi duk inda zata tareda securities tana jin kai saigashi daliln wadanda take ganin tafisu ikon komai Allah yanuna mata nashi *karfin iko* lokaci kadan,,
Murya a shake yayi sallama ya tamke fuskar sa ko digon faraa babu ciki ciki ya gaida su mommyn yayinda maryam ko kallon inda take baiyi ba,, ganin haka ya sanyata ya gaidashi murya a sanyaye,,
Banza yayi da ita ya yi kwanviyar sa kusa da mommyn hassana yana tambayr ta yaushe zata tafi,,
Harara mommyn ta sakar mata tana mata fada ta ido kasa tayi da kanta idanun ta ya kawo ruwa ajiye kular tayi tamike ta fice daga dakin,,
Kara lau da kansa yayi yana dariya cikin zuciyar sa dama haka yakeso yanzu zai bita kuwa kallon mommyn yayi yace mommyn wai maiyasa kike son bata yarinyar nan ne da gata naga kina zakewa da yawa ni wallahi ba daukar mai aiki zanyi dama kin barta tacigaba da aikinta,,
Uwaka karbi nan mommyn ta fada rai bace bana son wulakanci fa son wallahi a wannan kuma naga ta inda ikon naka zai tabbata tashi ka fice mun yanzun nan a dakin kafin inci maka mutunci tunda ka shigo dakin nan dama nasan da wata tsiyar ka shigo,,
Mikewa yayi yana kara kauda fuskar ya fice daga dakin kamar gaske kai tsaye dakin maryam ya wuce ya murda kofa yayi saa a bude take kulle kofar yayi ya karasa ciki kokarin take ta sanya hijab saboda daga ita sai zani a kasa tana kokarin sanya riga ya shigo,,
Kallon ta yake hartasanya hijab din kafin ya taka sannu a hankali zuwa inda take tsaye sai zunburo baki takeyi hannu ya sanya ya zare hijab din daga kanta batareda ta tsammaci zaiyi mata haka ba,,
Da sauri ta sanya hannun ta takare kirjinta rungumota yayi gaba daya zuwa jikinsa yana shafa gashin kanta Wanda yake tashin wani irin kamshin mai matukar dadi,,
Bakinsa yakai dai dai kunnenta yace maiyasa jiya kika yadda kuka kwana da didde eyeeh bayan kinsan bazan iya bacci bangan kiba,,
Ita dai luf tayi jikinsa kirjinta sai dukan uku uku yake kar mommyn ta shigo,,
Shinshimar kan nata ya shiga yi ita kuma tana kokarin janye jikin ta daga nashi amma ta kasa,,
Maiyasa kika yarda mommyn ta hanaki tarewa pls ki taimaka kice mata bakison zaman nan,,na gaji gaskiya ana shiga hakki na ,,
Ture sa tayi da karfi ganin ya fara shafa mata kirjinta nan take ta shiga zubda hawayen rigarta ta dauka da sauri ta sanya,,
Zama yayi kan gadon yaka karema ta kallo idanuwansa harsun chanza launi mikewa yayi yace maza ki shirya mu fita yanzu nan,,
Zaro idanu tayi waje ina kuma zamu ya Khalil yanzu nan,,
*mrs noour*βπ»πππ
[7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *π΄π΄KARFIN IKOπ΄π΄*
π±π±π±π±π±
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad ----pheeymarrh
*HIKMAAH writers association*
Edited byππ» *oum Zahara*π
Dedicated 2my lil sisππ» *Maman Sultan*π
Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*_hakuri,hakuri shi zan cigaba da baku uzirin masu Yaya ga miji ga busy na yau da kullum,kucigaba da yimin uzuri ,,Allah kasa mu dace ameen,,_*ππ»
π
Ώβ5β£5β£
Sai karfe bakwai da Rabi aka fito da ita da yan rakiya matar malam da matar wan mahaifinta lubna cikin motar kanin dad duk don a faran ta mata dukda ba wani tazara da gidan,,
Tarba sosai suka samu daga wurin inna da kannen Habib sai murna sukeyi sun sami anty basu taba ganinta ba amma sunsan dad don koyaushe yazo garin saiya nemi inda suke,yayinda gimbiyar safina sai sakin tsaki takeyi takure take da sanya katon mayafin da malam y sanyata yi ta kosa su fice daga dakin ta cire shi ta huta shiyasa ta tsani harkar jahilci da duhun kai,,
.su kuwa su lubna duk kunya ta ishesu domin kowa najin tsakin datake saki babu shiri suka mike don kaita dakin dukda da sunso barinta dakin innar tunda itama kamar mahaifiya ce agareta koda bata auri Habib ba,,
Har kofar dakin Habib inna suka rakasu ta bude musu kofar matar malam ta umarce ta dayin sallama anci SAA kuma tayi sallamar saidai cikin zuciyar ta tun kafin su shiga take jiyo kamshin pentin dakin suna shiga aka Karasa da ita gefen katifar Habib wacce inna ta lailaye ta da zanin gado mai kyau ta feshe dakin da tirare ,,
Zuciyar ta ce ta buga da karfi har saida ta runtse idanun ta mainake jine haka ni safina yaye mayafin tayi a hankali ta shiga kallon dakin zuciyar ta na tafarfasa nan take hawaye ya cika idanunta wannan menene haka matar malam ta fada a zafafe idanuwanta sun kada sunyi jajir tsabar masifa da tashin hankali,,
Sororo sukayi gaba dayan su suna kallonta babu Wanda ya iya tanka mata ,,
Mikewa tayi a fusace tana nuna dakin da hannun ta hawaye na malala visa kuncin ta anty lubna ki gayamin menene wannan kardai muyi mafarki ko tunanain ni safina ce zanyi rayiwa a wannan dakin,tab dijan balai da masifa kenan wallahi anty lubna lalacewar tawa bata kai ga haka ba wallahi babu Wanda ya isa ya sanya ni zaman cikin wannan kejin,kejin ma kamar na beraye domin ko dakin kajin gidanmu ya ninka wannan sau uku,,
Matar malam ta budi baki da niyyar yin magana sukajiyo muryar mutane ana sallama da alama makota ne suka shigo karbar amarya,,
Figar gyalenta tayi ta fice daga dakin rai a bace da sauri anty lubna tabi bayanta tana ki ranta daidai kofar fita ta cimmata ta damko hannun ta da karfi,,
Lafiyar ki kuwa safina anty lubna ta fada cikin Bacin rai ganin safinar na kokarin tozartasu,,
Lafiya ta kalau anty lubna ki sakar min hannu wallahi nafi karfin zaman gidan nan saidai inyaso dad din ya tsinimun shiyake da asara amma wallahi koda zaman awa daya bazan iyayi ba a cikin wanna dan iskan kazamin gidan ba,,
Tana gama fadar hakan ta fuzge hannun ta ta fice da gudu zuwa gidan malam yayinda su matar malam kunya ta hanata koda daga yatasa ni balle ta samu ta motsa tabasu baki,,Aisha ce ta kama inna ta shigar da ita dakin ganin tana zubda hawaye tun a lokacin taji matar yayan nasu ta fice mata a rai yayinda makota kowa sai saka yake a ransa suna alla alla su fita don yada magana,,
Anty lubna ce ta karasa gurin matar malam ta kama hannun ta tana fadin kiyi hakuri tasayuwa batamu bace mukarasa mubasu hakuri kafin musan abunyi,,
Saida suka tabbatar da ta hakura inna kafin su baro gidan suna sallama a tsakar gidan suka tarar da ita kawo mustapha kanin dad ya nada mata duka sai kuka takeyi da itakacin karfinta amma bakinta bai mutu ba da fitsari rantsuwa takeyi koda zasu kasheta bazata zauna a wannan gidan ba,,
Nanma su anty lubna suka korawa kawo mustapha bayanin irin cin mutincin da tayi musu ta zuvar musu da daraja da kima da mutincin gidan nan tunda agaban jamaa ta dinga zuba rashin mutincin,,
Aikuwa gadan gadan ya nufeta zai dada jibgar ta daman chan shi dan zafine ba kaunar halayyar yakeyi ba tswwa malam ya daka masa akan ya kayaleta,,dakansa malam din ya kama hannun ta ya mikar da ita ya juya yace maza mustapha ka kiramin Habib yanzu a waya ya shige da ita dakin sa,,
Lafiyayyar fura ya dauko mata ya umarce ta da ta shanye ta nan ya shige bata baki da waazin da nuni ya dinga yimata akan ratuwa da rayuwar auren kanta tareda yimata alkawarin matukar tabi mijinta saita zamo abin alfahari ga iyayenta kuma dukkanin gatan ta zai dawo da Wanda yafishi ma da kyar yasamu ta aminci da maganar zaman saidai akan dan lokaci kawai shima dole hakan ya amince don yasan halin safina sarai da taurin kai indai don duka ne koda kuwa zasu kasheta bazata zauna ba,,
Bai dauki lokaci ba ya kara so gidan inda har labari yaje masa akan abunda safinar tayi haka ya daure ya nunawa malam tamkar baisani ba,fadan dai ya karayi musu sosai,saanna yace sutafi Allah ya ki yaye yayi musu albarka,,
Tunda suka fito harsuka isa gidan bata ko kallin inda yakeba yayinda suna zuwa kofar gidan ta sanya hannu ta to she hancin ta tana Jan tsaki ransa ya baci amma haka ya nuna baima San abunda takeyi ba,,har cikin dakin ya kaita tare da dire yan ledojin budar bakin daya siyo ya dauki na inna ya nufi dakin ta don kai mata,,
*don Allah kuyi hakuri fita ta kamani yanzu madadin shirun gwamma ba yawa*
*mrs noour ce*βπ»π
[7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *π΄π΄KARFIN IKOπ΄π΄*
π±π±π±π±π±
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad ----pheeymarrh
*HIKMAAH writers association*
Edited byππ» *oum Zahara*π
Dedicated 2my lil sisππ» *Maman Sultan*π
Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
π
Ώβ5β£6β£
Duk iya yadda takai da taurin rai saida zuciyar ta ta soma karaya amma saita dake ta hanyar karfafa zuciyar ta da fadin wannan zaman na lokaci ne ,tabbas dad bazan taba zama da wannan lalataccen ba wallahi hannun ta sanya ta share hawayen dake kwance bisa kuncinta wayarta ta kunna Tara ta wuce na dare tasan yanzu mom na tare da dad dole haka ta hakura da kiran datayi niyyar yi sake kare wa dakin kallon take yayinda bakin cikin da tsana tarda kyamar Habib da dduk wani talaka ya kara nunkuwa a cikin zuciyar ta,,mikewa tayi da sauri tunowa da wani Abu da tayi da hanzarinta ta rufe kofar tareda sanya sakata don kofar bamai key bace saanan ta dawo ta shiga neman layin meena aikuwa bugu daya ta dauka cike da dokin sonin yadda kawar tata take,,
Aikuwa nan safina ta kwashe yadda akayita gaya mata sallati da karfi meena ta saki tana zare idanu waje kamar safina tana gabanta ,kawata daki daya fa kikace kokuwa vaki dai zaga gidan kin gani bane dakyau,,
Dogon tsaki safina taja tareda tabe baki tace pls meena vanason Karin wani tashin hankalin akan Wanda nake ciki shawara kawai nake neman kari akan irin cin mutincin dazanyiwa wannan shegen,,ke meena kinga gidan kuwa gabadayansa girman sa baikai part dina ba don haka karki sake yimin maganar sa kuma ni koda yanada girman nariga da nafi karfin shi wallahi tunda maishi a kasana yake ci da dukiyata zaiyi,,
Ajiyar zuciya meena ta sauke tace hakane kawas amma yanzu ki kwantar da hankalin ki kisamu kiyi bacci gobe mayi maganar da fatan dai kin garkame kofar ki karya kawo miki farmaki cikin dare,,ta karashe tana dariya cikin tsokana ,,
Tsaki kawai safina tayi ta kashe wayar gaba daya ta mike kayan jikinta ta rage don malam yace sai da safe zaa kawo mata kayan ta,,
ledar da Habib din ya ajiye ta dauka ta bude kaji ne manya guda biyu kuma babu laifi sunada girma sai kamshin kayan yaji suke nan take ta soma ci tareda kora maltina wacce ya siyo itama guda uku,,said a taji ta koshi kafin ta tura ledar gefe ta mike ta dauki ruwan gorar ta je bakin window ta wanke hannun ta ta dawo ta kwantar da kanta bisa pillow ta na saka da warwarar yadda zaman nasu zai kasance da ya Habib din,,
Sai kusan sha daya da rabi ya fito daga dakin innarshi zuciyar shi cike da zullumin yadda zai kwana daki daya da ita,, yanason ya danne zuciyar shi ya karfafa ta don gudun fuskantar raini daga wurin safinar wannan itace shawarar da inna ta dinga bashi Wanda shima yayi naam da hakan,,
Duk iya bugun dazaiyi yayi amma shiru kakeji kamar babu mutum a dakin dukda yake bugun a hankali yakeyinsa don kada inna tajiyo bayason tashin hankalin ta tun daga yanzu ranar farko,,
Dole haka ya fice ya bar gidan ya nufi dakin abokin sa sani ya kwanta dayake sani shima bamai son magana bane baidamu dayasan dalilin sa na baro amaryar saba,,
Zaune take ta zuba uban tagumi hawaye na silalowa daga manyan fararen idanun ta tayi zurfi cikin tunanin ya Khalil abunda baitaba yimata ba kenan ko kafin ya furta soyayya gareta a kullum saiyasan yadda yayi ya ganta amma gashi yanzu tunda ya tafi baiko neme jin muryar ta ba a waya Bayan kullum tanaji yana kiransu mommyn kullum baitaba cewa a bata ba ko yaushe idanun ta nakan wayarta koxai kira amma shiru,,
Gashi gyaran da mommyn keyi mata yafara takurata da sanya ta jin kasala da shaawa,,da sauri ta dago tana share hawayen dake kan fuskar ta mommyn ce zaune kusa da ita ta dafa kafadar ta tareda zura mata idanun ,,
Maiya farune yata kike kuka,a akwai wani Abu da kike sone eyeeh ,,mommyn ta tambaya cike da kullawa,,
girgiza kai tayi a sanyaye batareda tace komai ba,shikenan tashi muje didde zasu tafi suna kasa ki sauko yanzu tana gama fadar haka ta mike ta fice tasan maiyake damun maryam din bai wuce fushin da ya Khalil yakeyi bane Wanda itama tana sane da hakan,,
Sai da ta darwayo fuskar ta a toilet saanan ta fito har mota suka rakasu tareda yi musu fatan Allah ya tsare ,saanan suka juyo a Palo suka zauna mommyn nata kokarin janta da hira yayinda take binta da eh aa kallo ,saida aka kira sallar saanan mommyn ta mike ta wuce don yin sallar itama maryam din dole ta mike ta wuce jikinta sanyaye sai dai tana bude kofar taji an janyota da karfi Wanda said a ta tsorata niyyar kwalla kara takeyi amma jin kamshin turaren sa ya sanya ta dagowa a razane tana dubansa ,,
daga mata kai yayi a hankali tareda lumshe mata idanunsa masu matukar kwarjini ,dafe kanta yayi da dayan hannun sa ya maida kanta bisa kirjinsa ,,ajiyar zuciya suka sauke da karfi kiwannen su najin kewar dan uwansa,,
tsugunne take gaban malam kanta a kasa kai kace fadan dayake yi mata yana shiga kunnuwanta sosai malam ya kara yimata nasiha tareda gargadi sosai akan ta kula da kanta da hakkin auren ta,,,
Godiya tayi masa sosai saanan yatafi tsaki taja tana fadin aikin banza ai wallahi kunma samu safina da sauki ba kamar tada ba wallahi zaman aure ne ba zanyi ba sai dai komai zaayi ayi rashin mutunci yanzu na fara ta na gama fadar haka ta shige cikin gidan ta na wake waken turawa ta wuce innar ta shige daki kai tsaye wurin drawer ta wuce ta dauko wata karamar top ja da rats in fari sai wando jeans black ta sanya Wanda yayi matukar matseta ta sanyasu tareda yin rolling kanta da bakin gyale karami Wanda iyakar sa wutanta ta dauki wsyoyin ta da pos dinta dake kan bedside drawer ta fice daga dakin ta kullo,haka ta wuce inna a tsakar gida da bataeda ko kallon inda takeba balle tasamu yimata sannu,,
Ran inna yasoma baci hakurinta yana gab da karewa yau kimanin kwana shida kenan tunda ya Habib ya koma us wurin cos dinsa safina ke fita cikin shiga ta radhin mutunci dukda bawani dadewa takeyi ba inta fita yawanci siyan abinci ne da tarkacen ciye ciye amma yanayin suturar tata ce dabatsyi ma tun ana gulmar a Bayan idon inna abin har yazamo har gida aka sami inna da maganar dole haka taje har gidan malam ta gaya masa amma saigashi abin takaicin batada ko minti goma baayi ba ta sake ficewa hakan yana nufin batada niyyar sauya hali kenan,,
Ga wulakanci ta rashin mutunci tunda yazo gidan gaisuwa bata taba hadata da mahaifiyar Habib ba ada inta aiko mata da abinci watso shi takeyi waje don haka ya sanya inna ta daina zuba mata gashi koyaushe gida cikin kide kide yake tunda ya Habib ya siya kayan kallo da sets din gado da carpet harda kayan abinci Wanda yasan sudin takeci amma tace tafi karfin dafa Abu da kanta wallahi dukda batasan ya Habib din kasar us yatafi ba ,har yanzu fushi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 32