wannan I hate her dad harda hawayenta tashi tayi ki biyo ni da kaya na useless kawai,ta wuce ,,,.
Allah sarki maryam da sauri ta dauki hand bag dinta da traveling bag dinta har biyu ta na ja da kyar saboda nauyi ta bita wanda ita har ta fice,da kyar ta karasa saboda nauyi ga tsoron karsu hajiya ladi su hangeta,driver ne ya karaso ya amsa tareda bude boot ya saka a ciki ya rufe ita kuwa hakimar tana baya ta hakimce sai goge wayarta takeyi saboda maryam ta rikeπ€
Maryam ta kama handle din Kofar zata murda tashi ga baya...
Wani mugun kallon ta watso mata wanda saida hantar cikin ta ta kada da sauri ta saki ta koma gidan gaba jiki na rawa ita dai fatanta tasamu tabar airport dinnan ko ta samu kwanciyar hankali aikuwa abunda take gudu ya faru domin hajiya ladi ta hango mai kama da maryam saidai suturar dake jikinta wanda bata ganiba sakamakon tariga da ta zauna a motar driver ya jaa sun wuce,,,
ni kuwa alhaji sai na Ke ganin Kamar maryam ce a wanchan motar sai dai kuma naga babu dan kwalin a kan ta ,hajiya ladi take gayawa alhaji,
Murmushi yayi yace gwara da kika ce kama domin kinsan maryam bazata iya yawo farat daya babu dan kwali ba , kinsan ansha tafiya maybe tana wani abun ne a toilet din ba fitsari ba ki kara hakuri,,
toh alhaji mu koma daga can wurin kujerun mu jira,OK ya amsa suka wuce suka zauna zaman jiran gawar shanuπ
*_asalin alhaji_*
Alhaji yahaya asalin dan garin Zaria ne iyayen shi babu laifi suna da hali yayi karatun shi mai zurfi kafin daga baya ya koma harkar siyasa, ya rike mukamai da dama yanzu haka yana cikin yan majalisar na kasa,shine na Kaduna ,ya saba da Hulda da matan banza tun a makaranta kafin ya fara aiki,har yayi aure madadin abun yayi sauki saima gaba yakeyi tunda ya je garin Kano suka hadu da hajiya ladi wurin harkar taron su na siyasa tasu ta kulle ,ita Ke nemo mai yan mata masu budurci yana bata masu rayuwa yayinda wadanda taga zasu basu wahala yakan shirya tafiya wata kasa sai hajiya ladi tacewa iyayen yara aikatau zasu sai yayi yadda yake so da yarinya sannan ya dawo da ita wanda wannan dabi'a tace yafi yinta ne ga 'ya'yan talakawa dayasan zai ita nuna musu *Karfin iko"* shi koda sunyi tunanin kai kara,a haka wata rana ya hadu da maryam da yamma tana sanye cikin unifoarm dinta na islamiya riga da dogon hijab milk color da wando milk color shima,sunyi matukar yimata kyau tun daga lokacin yasha alwashin saiya nemeta kota halin Yaya ne kuma a lokacin akai saa hajiya ladi suna tare da alhaji a mota ,nan da nan ta sauka ta bi bayanta har makaranta ta kuma jira har aka tashi tasake bin bayanta har gida sannan ta gayawa alhaji tun daga nan suke shirya yadda zasuyi saboda yaje wurinta ta ki sauraran shi ,shiyasa suka bullu mata ta haka,wannan kenan,..
*cigaban*
Har 45mins shiru babu maryam babu duriyarta,hajiya ta miki tace bari alhaji in duba yarinyan nan ko takasa gane hanya ne,toh alhaji yace don shima ya gaji yanaso ya samu hutawa,wucewa tayi ciki ta duba toilet bata babu alamarta fitowa tai hankalinta yadan fara tashi ta fara duba wa tun tana sa rai har ta fara sarewa hankalinta yayi bala'in tashi ta koma wajen alhaji ta gaya mai bata ga maryam ba fa koina babu ita,what ya fada yana zaro idanun Kamar ya bata nan ?toh inbatan ina tayi?
toh alhaji ina zan Sani cha nake muna tare da kai anan,tai maganar hankali a tashe kai amma yarinyar nan ko tsinanniya wlh mai take nufi ne ko ta gudu ne ,?
da sauri ya mike yana girgiza kai yace Aa bazata faraba muje ciki in samu na tambaya,.
duk neman duniyar nan sunyi babu maryam babu wanda yaga alamarta suna bincike yarinya mai jallabiya alhali basusan maryam ta dade da yadda wannan jallabiyar ta chanza wasu.π
Kai na gaji da typing
*urs*
*mrs noourβπ»*
[7/11, 17:42] +234 816 822 9024: *π΄π΄KARFIN IKOπ΄π΄*
π±π±π±π±π±
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
*HIKMAAH writers association*
Edited byππ» *oum Zahara*π
Dedicated 2my lil sisππ» *Maman Sultan*π
Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*shawarwari,comments, soyayya da karfin gwiwa,da kauna, dukkan su suna isuwa gareni,wlh ina matukar jin dadi masoyana ,Allah ya bar kauna ta har abada,kai ina ππ»ππ»ππ» ππππππππ*
π
Ώβ0β£8β£
Ran su yayi matukar baci babu ma Kamar hajiya ladi na farko ga dukiyar da ta ci burin samu wurin alhaji ga inna da tayiwa alkawarin,shin ya zatayi da wannan yarinya mai kafiya,
toh alhaji ko gurin yan sanda zamu je ne?tai mai tambayar hankalinta baya jikinta,what ya fada yana zare ido kina hauka ne nan fa ba nja muke ba anan ba'a maganar kudi ko mukami ,freedom and Justice kawai in suka tambaya ki meye dalilin guduwar ta kina da amsa domin indai ba guduwa ba zamu ganta a ciki indai batane,kai amma wanna yarinya ta shammace mu ,duk burin dana ci akanta infara dandanar rumunta karshe haka zata hadu da wasu yan iska su samu a sama na kawo musu har gida,kwafa yai tareda daga waya zaiyi kira,,..
*Habib*
tunda suka dauki hanyar komawa Kaduna yake tunanin irin wulakanci da safina takeyi mai,ransa a bace yake idanun sa sunyi jajir zame bayansa yayi ya kwanta a kujerar meya kamata yayi anya kuwa bazai bar gidan dad ba abun yayi yawa duk kuwa da irin tarin hallaccin da yayi mai da irin gudunmawar da ya bashi har ya kawo iyanzu ,yarinya Kamar ba jini alhaji isma'il ii ba ,ina tausaya wa wanda zai aure ta ya zauna da ita,
bai San maiyasa ma yake damuwa da lamarin ta ba runtse idanun sa yayi yana sauke ajiyar zuciya fuskar maryam ce ta fado mishi ,yarinya mai natsuwa da kamala I wish safina ce haka,mtss yayi tsaki ya juyar da kanshi gefe me zai dameni da Chan jin ta dole watarana zata gyaru kota dadi ko akasin haka,haka ya wuni yana tunanin maryam wacce shigar ta itace tafi burgeshi yana son mace mai suturta jikin ta shigar jallabiyar tayi mata kyau musamman yadda tai rolling gyalen sannan ta kara yafa wani a kafadar ta mur murmushi yayi tareda kara rungumar pillow,zai so yasamu matar aure haka,a haka har bacci yai gaba da shi,...
washe gari da safe ya shirya domin zuwa duba innar sa da yake son yi ,sai da yabiya gidan alhaji isma'il ii mahaifin safina sukayi sallama,aikuwa sai da ya cika mishi boot dinshi da kayan abinci ya kai wa su inna , shi dai bai San mai zai cewa wannan bawan Allah ba sai dai adduar Allah ya shiryar mai da yarshi kawai,
*Sai ince Habib Allah ya tsare*,..
*ummi da inna*
Wunin ranar ummin cikin damuwa tayi yayinda duk tayi sallar adduar ta biyu ce Allah ya jikan mijinta ya kuma kare mata yarta,
yayinda inna ta wuni cikin farin ciki har tana hadawa da wake wake, ko da tai sallar isha dakin ummi ta nufa sallama tayi tareda yaye labulan dakin jimm tayi ta saki Baki sallati ta fara tace kai matar baba kinyi asara wlh bazan fasa gaya miki ba auren ki asara ne agareni da zuri'ar baki daya dole mugun abunda kikeyi kiji tsoron kar ya koma kanki wlh bacin mero jika tace da nai mata mugun baki, da sauri inna ta dago tana ma inna kallon mamakin halayya irin tata Kamar ba uwa ba,
karaswa inna tayi kusa da ummi wacce Ke kan sallaya a Zaune rike da cazbaha , daga muryar tayi cike da tsana tace matar baba ki tashi ki ida nufin ki akaina naga kiyayyar dakike nuna min ta fara tsauri...
kiyi hakuri inna in ranki ya bace ba nufi na kenan b...
kinga matar baba koda nufin ki kenan bakida yadda zakiyi da ni *karfin IKO* ne na nuna miki sai inga yadda zakiyi,ni na wuce makwabta in kin zuba gubar a abincin ki hada da shayin bera a ruwa ki hada ki kaimin kinga kin wuta,ficewar ta tayi tana mitar maganar har ta kai gidan da Zata ,gidan alhaji lawal makwabta ne dasu safina gida biyu ne tsakanin su,
ummi girgiza kai tayi ciki da bakin ciki zuciyar ta sai bugawa take da sauri2 daga hannun ta tayi sama tana hawaye ,tace ya Allah ka jarabeni da abubuwan da dama na dadi da rashin sa kuma nayi imani da farin ciki ,ya Allah ina rokon ka Allah ka tsare mun maryam a duk inda take Allah ka kareta kasa mata hakuri da juriya a duk yadda ta tsinci kanta a halin rayuwa jin dadi ko rashin sa, ya Allah kasa yadda ta fita lfy Allah kadawo min da ita gida lfy,ta shafa ta zame ta kwanta kan sallaya ita matsalar inna bata dame ta ba inda Sabo ta saba ,ai kuma ta rike alkawarin mijinta Insha Allah zata cigaba da hakuri har Allah ya kawo mata karshen abun,..
sallama tayi aka amsa tareda cewa a shigo,shiga tai suka gaisa da hajiya zainab ,sannan tai gyaran muryar tace don Allah yannan ki taimaka min Kamar yadda aka saba ki kira min wannan yaron ,murmushi hajiya zainab tayi ta dauki wayarta wacce Ke kusa da ita ta kira number tana fara ringing ta mika ma inna ta tashi ta fice ta bata wuri,..Sallamu alaikum akace ,inna ta amsa Waalaikummussalm dannan kananan lfy ko,
"Lfy lau inna ya mero"
Lfy lau toh komai ya kammala kayiwo shiru gobe kazo ka amshi kudinnan sun cika a samu a biya mutanen nan kudin su"
"toh inna Insha Allahu ina kan hanya gobe,"
toh madalla ka gaida min da matan da jikokin nawa ,Allah ya tashe mu lfy sauran magana sai kazo saboda wayar dai kasan ta aro ce"..
"Toh inna ameen sai nazo ya kashe wayar,"
murmushi tayi ta fita tabawa hajiya zainab wayar ta ta yi mata saida safe ta wuce gida cikin farin ciki haka ta kwanta hankali kwance yayinda ummi tai kwanan Zaune tana kai kukan ta ga mahallici ,π
koda gari ya waye shiri tayi da wuri tai ma ummi sallama ta tafi gida kanwarta dake cikin sheka ,ummi tayi mata adawo lfy ta fice batreda ta amsa adduar ba ,sai karfe goma iliya ya karaso ,suka shige cikin kuryar daki suka turo kofa,
Sai ince inna abi duniyar nan da saukiπ
*safina da maryam*
sun danyi nisa dad ya kara kiran safina yace zai turo mata address din abokin shi wanda yake Zaune a can su zauna b4 yasan yadda zasu bulluwa lamarin maryam,
OK dad amma how many are they kasan dad bana son...
kai baby dad ya katseta ki bi abinda nagaya miki kawai ga address dinnan I will talk to u later love u ,
rai abace tace OK love u more ta kashe wayar ,harara ta zabga ma maryam,yaya bazan tsani Hulda da talakawa ba bcoz of her dad zai yimun haka ,na tsani takura ya zan zauna da wasu kuma har tareda wannan useless of no gud din tsaki tajaa mtsss
Wlh matukar gidan baiyi mun ba bazan zauna b...Karar sako ne ya shigo,ta dauka ta duba ta karanta ta gayawa driver ,suka dauki hanya, tafiyar 27mins suka iso cikin unguwar wacce ake kira da Jamestown unguwar ta hadu iya haduwa ita kanta safina sai da ta zuba idanun tana kallon balle maryam wacce take ganin wadannan gidajen Kamar a aljanna haka har suka iso layin numbers din gidajen sukayi ta duba wa har suka iso gidan horn driver yayi gate ya wangale da kanshi toh garine duk camera har an gama shaida su tun a motar ,kai tsaye wurin parking lot ya karasa wanda an kawata shi iya haduwa maryam ta girgiza kai tace lalle duniyar nan ni konan aka barni ai lafiya,..
fitowa sukayi suka karasa cikin gidan inter suka dannan baifi minti daya ba aka bude wata baturiya ce cikin shigar yan aiki ta gaishe su safina ce ta amsa domin turancin nata bai kai nanba tace su biyo ta tayi musu ja gora ,binta sukayi safina ta yaba da tsarin gidan duk iya bude idonta saita ce bata taba ganin gida wanda yai mata kyau da burgewa irin wannan ba ,hmmm balle maryam da zare idanun takeyi kawai saboda tsabar rudewa tama kasa gane komai sai jefa kafa take kan carpet mai tsakanin taushi da laushi haka suka wuce parlor din suka bi wata yar doguwar corridor data raba har zuwa step din sama gefe kuma wani parlor ne mai masifar kyau suka shiga safina sai kallo take a ankare kada ace tayi kyauyanci yayinda maryam take kallon komai daidai daki daki tsakanin ta da Allah ,Ure highly welcome my dears suka ji wata muryar mai dadi ta furta a nutsa,kai kallon su wurin sukayi tareda karasa suka zagaya wuri kujerun inda hajiya take safina ta zauna tance ina ina kW...maganar ce ta makale mata a makoshin ta sakamakon arba da tayi da wani haddaden saurayi dayake kwance jikin hajiya tana shafa sumar kanshi ya Allah ta furta a zuciyarta.
bismillah Ku zauna,hajiya ta sake cewa,wanda safina tai maza ta daidaita kanta ta fara gaida hajiya ta amsa cikin sakin fuska tace kuyi hakuri son ya hana ni zuwa tarban Ku,no ba komai mommy safina tace tana hararar maryam wacce hankalinta ya tafi ga kallon katuwar burner datake aiki sai wasu irin launin wuta kala2take fitarwa ga ruwa yana ta tafarfasa daga cikin ta ta kasa wanda shine yake saka turaren yayi kamshi, Keeh safina tace da daga muryar ,maryam tai firgigit ta dawo daidai wanda wannan tsawar itace ta tada wannan surayin dayake kwance ya bude idanun cikin bacci wanda yayi daidai da kai idanun maryam gurin sukayi ido hudu Dammmm kirjin su suka buga wani irin abu sukaji tun daga kan su har yatsar kafansu .....
*comments*
*share*
*mrs noour ceβπ»*
ππππ
[7/11, 17:42] +234 816 822 9024: *π΄π΄KARFIN IKOπ΄π΄*
π±π±π±π±π±
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
*HIKMAAH writers association*
Edited byππ» *oum Zahara*π
Dedicated 2my lil sisππ» *Maman Sultan*π
Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*Masoya kuyi hakuri na jina shiru da kukayi wlh uzuri ne amma yau zamu cigaba, ina kaunar Ku sosai ,kuna raina kullum,Allah ya kara ππππ a tsakani ,ameeeeenπ*
π
Ώβ0β£9β£
*khalilullah, safina &maryam*
Shi yafara janye idanunsa daga kallon ta tareda hada rai ya kara gyara kwanciyar shi ya basu baya maryam kuwa ta saki baki da hanci tana kallon shi,yayinda safina Ke watso mata da Aiken muguwar harara wanda yaki isa gurin maryam din domin ta amsa sakon ta shiga hankalinta sai da zahra tasa tsinin takalmin ta ta buga mata kafa sa anan maryam ta dawo natsuwar ta, durkusa wa tayi har kasa tace "ina kwana hajiya" ta furta muryar ta asanyaye cikin jin kunya,domin ta lura da kallon da momy take yi mata duk da murmushi ne a kan fuskarta,"lfy lau ya kuke ,ya gajiyar hanya"momy ta amsa,..
"Lfy lau suka amsa zahra ta kara watsa mata wata hararar domin har yanzu maryam idanunta suna kan shi bata dauke su ba duk kuwa da zafin da takeji a inda zahra ta takata,
Pls khalilullah daga min cinya, naga abun naka babu sauki,ga baki munyi oyah,muryar momy ta katse shirun nasu,
kusan minti biyu sanan ya kara gyara kwanciyar shi tareda kara rungume cinyar Momyn saanan ahankali ya budi baki yace momy ki barni mana koba yan aikin bane me kuma zaki yi mus...
cike da π± haushi da mamaki take kallon shi banda maryam da ita maganar bata wani dameta ba tunda ita a ganinta ko yan aikin gidan sun fita gata ,sai dai duk da haka tasan wulakanci ne kawai yasashi yin wannan maganar ko don safina yayinda wanda yayi maganar ya maida idanunshi ya rufe Kamar bashi yayi ba,..
Murmushi momy tayi tace kaga bana son wannan halin naka kasan na gayama daddy yace yaran daddyn ka na Kaduna zasu zo nan ko,to ai sune suka karaso bari inje in kula dasu kafin ka tashi daga baccin oko tace tana leka fuskar shi,..
nanma kusan minti biyu sannan yace ya budi baki da kyar yace OK, amma su basusan gaisuwa ba ne ko,Aa khalilullah momy ta katse shi dinga kana bacci taya zasu gaida ka ai sun San kai yayan su ne in suka huta sai a gaisa gaba daya ko..
maryam ajiyar zuciya ta sauke a zuciyar ta tace lallai ina gamuwa da mutane marasa mutunci,Allah ka karamun juriya da dauriya
zama da mutanen nan ,ita kuwa safiya zuciyar ta tayi mata baki taji zafin abunda ya yimata gwara wannan useless girl din amma ita fa amma da sannu zai gane,..
momy ce ta dauke kanshi daga cinyar ta ta mike tace musu muje ko sai a lokacin suka dawo daga tunanin da sukeyi maryam tai maza tace mishi ina kwana tareda Mikewa ,yayinda safina tayi gaba domin wlh bazata bai dashi ba in gata ne itama tana takama dashi har suka bar wurin Khalil bai motsa ba ma balle tasaka ran ya amsa haka take tafiya Kamar ruwa ya cita hanyar step suka nufa suka babban falo suka tarar sai kamshi yake tashi mai kwantar da hankali momy tayi on din light dakin ya gauraye da haske ya Allah maryam ta furta da karfi wanda yasa su safina Juyowa kallon ta aikuwa ba baki ba har bacci maryam ta saki tana kallon wannan falo tsaki safina tayi, ta juya duk da itama tsarin da haduwar palon yayi mata komai na dakin farine da ratsin ash color,wucewa sukayi wata kofa a gefe suka shiga dan karamin corridor ne suka bi suka mike karafin parlor ne suka sake tarar wa shima ya hadu sai dai bai kai manyan ba mai dauke da dakuna daidai acikin shi guda uku kowanne dauke da bayi,momy tace to Gashinan Ku duba inda yayi muku kuyi wanka da sallar sai Ku sauko kuci abinci,toh suka amsa momy ta juya ta rufe musu kofa ta wuce,
safina ce tafara yin gaba ta bude daki daga gefen hagu ta shiga sai da ta kare mai kallo sannan ta fito da shiga na gefen dama shima sai da ta kare mai kallo sanan ta fito ta shiga dayan shima ta gama kallon shi duka dakunan basuda babban ci imba na color ba set din royal bed ne daidai kwanciyar mutum biyu mai matukar kyau an shimfida lafiyayya zanin gado wanda kalarsa daya da labulayen dakin kuma kowanne kan mirror din an sanya kayan amfani akai ,girgiza kai tayi ta koma na farko data fara dubawa ta shiga ,maryam dai tana tsaye tana kallon ta cikin mamakin lamarinta ganin ta shiga itama kada tayi laifi tai maza ta bita tura Kofar tayi bakinta dauke da sallama wacce ta karasa ta a zuciyar ta sakamakon mugun kallon da safina ta kafeta dashi , tsaye tayi ita bata shigo ba ita bata juya ba ganin haka yasa ran safina kara baci a fusace tace Keeh useless girl waike dabba ce hala nan ma saikin biyo don't u dare ki fara tunanin zan zauna daki daya dake ,ki wuce ki kwado min kayana da aka shigo dasu ki shirya min su a wardrobe kafin in fito daga toilet ta tashi ta shige toilet tana hararar ta ,I hate dis useless girl wlh dole daddna yasan yadda zaiyi da ita don bazan taba zama da ita ba wlh, tsaki tayi a bayin ta sakar ma kanta shawa,π€
taji zafin zagin da safina tayi mata amma ya zatayi dole tai mata biyayya ko ba komai ai ta taimaka mata da yanzu tana nan gurin su alhaji wanda Allah kadai ne tasan mai suka gudiri niyyar yi mata Allah ya amsa adduar' ta ya kubutar da ita ko yanzu ya zasuyi in suka nemeta suka rasa oho?π
*hajiya ladi &alhaji*
daya daga cikin yaran shi ya kira yace maza ya hado kan sauran suzo such same shi a hotel din daya saba sauka,amsa wa yayi sanan ya kashe wayar ,
muje hajiya ya yace rai abace suka wuce ko da suka isa anan suka tadda yaran nashi yan isakan duk sun hadu niko nace dama akwai yan daba ne har a usπ€...
koda ya shiga safa da marwa ya fara Kamar zai yi hauka shi yama rasa yadda akayi harta gudu Kamar zaiyi kuka yace wlh hajiya in har aka kawo min yarinyar nan wani ya fara sanin ta bani ba wlh saina kashe ta Ke ba ita kadai ba har dangin su gaba daya sai nasa an musu kisan kiyashi wlh nayi alkawarin nan,..
Ajiyar zuciya hajiya ladi tayi tareda cire tagumi tace alhaji ka kwantar da hankalin ka duk inda take zasu nemota sai musan hukumcin da za'a mata kuma Insha Allah lfy zasu ganta batareda ta bada kanta ga wani ba kada ka damu nasan masu hali dayawa irin na maryam ka je huta kaidai zamusan abinyi,
shidai yaji hajiya ladi ne kawai amma jikin shi yana bashi bazai kara ganinta nan kusa ba amma kwafa yayi ya juya wurin yaran wayar ya dauko ya shiga gallery ya fito da huton maryam ya mika ma babban su ya wuce daki zuciyar shi a dagule wlh wlh muddin yarinyar nan aka sameta sai na gana mata muguwar azaba in kuwa har ta bada kanta ga wani koda a tsautsayi ne wlh alkawari ne na dauka sai na wulakanta rayuwar ta kare ma saiya fita daraja ita da iyayen ta,...
hajiya ladi kuwa bakin ciki ya cika zuciyarta tayiwa maryam Allah ya isa yafi dubu tareda tsinuwa yanzu shikenan duk abunda alhaji yayi mata alkawari ya tashi a banza kenan?..
(Sai ince Allah yasa maryam tayi muku nisa kenan har abada,ameen)π
*khalilullah, maryam, safina*
juyawa tayi takoma palon ta dauko jaka daya ta kawo dakin safina ta bude jakar ta fara shiryawa a wardrobe tana jingina gata irin na maryam har ta gama kayan babu atamfa
Acikin sai kanan kaya riga da wando ko riga da skirt haka dayan akwatin shima duka Arabian gowns ne gaba daya different colors haka ta shirya sai kayan kayan shafe2n ta takalmanta duk ta shirya su,sai littafan ta wadanda ta rasa ina zata saka su har safina ta fito daga toilet daure da towel a kirjinta sai daya tana tsane gashin kanta as usual de hararar maryam tayi ta wuce gaban mudubi ta zauna ,zaman ta keda wuya ta hango littafanta bisa kan gado,Juyowa tayi rai abace kama zata shake maryam saboda tsana tace Wanan uban ki suke jira ko ni? ko zaki ce mun bakisan inda zaki ajiye su a fadin dakin nan ba ne ,da sauri maryam ta kwashe su wurin bedside ta kai ta jera su tsab sannan tace anty na gama,banza tayi da ita har saida ta gama shafe2ta sannan ta juyo tace ki saurare ni da kyau bana bukatar ki kina rabata batareda na nemeki ba sharadi na farko kenan,
Bana son kina bata useless bakinki wurin yimin magana batareda na bu ka ci hakan ba,na biyu kenan,saanan na tsani a shiga harka ta wannan nafi tsana a rayuwa ta Wanan ne na karshe in kinji kin huta da sannu zaki San ko ni Wacece banida bukatar sanin ko kedin mecece domin nasan tsiya ce kawai Ke tareda asalinki don haka ki fita ki wuce dakin ki ,hawaye ne kawai Ke bin fuskar maryam Allah sarki rayuwa duniya kenan saika shigeta zaka San mai rake ciki Mikewa tayi gwiwa a sanyaye ta mike har ta kama handle din Kofar ,safina ta dakatar da ita tana fadin darajar daddy yasa kika samu har kika samu da sauki a wurina bana taimako kuma bana bukatar a taimake ni saboda haka kiyiwa useless kwakwal war ki fada haukan da kikayi dazu kada ki kara yin shi a gabana da har za'a wulakantani saboda Ke tsaki taja ta mike a fusace tayi gurin wardrobe....
murdawa tayi ta bude ta fita dakin hannun dama shi ta shiga da sallama ta wuce bayi nan ma saida tayi kyauyancin duk bata San yadda ake amfani da kayan bayin ba Allah yasa tana dube 2 taga karamin pampo ta gefen toilet ta yi alwalar ta fito wurin mudubi ta wuce inna lillahi wa inna ilaihir rajiun ta furta tana waro ido waje ooh ni maryam haka nake dama ko
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 32