Share this page
maganar rai a bace Kamar lokacin ne tayi mai laifin ,dukda har lokacin idanun shi alumshe suke, dafe kirji maryam tayi tana zaro idanun ta waje sallati ta fara a zuciyar ta wlh ita ta manta ma da wani aike dayayi mata tabbas tasan tayi laifi amma ai ba laifinta bane a matsayinta na bakuwa da bata San kan gidan ba,.. mommyn ce tai murmushi tace to son baka ganin bakuwa ce batasan kan gidan ba kada ka manta dazu suka zo fa,safina ce tai charaf ta amshe da cewa mommyn ba wani bakunta iskanci ne kawai irinnan ya'yan iska.., Aa safina mommyn ta katse ta dacewa koke ya aika yazakiyi tunda bakisan kan gidan ba tukunna,da sauri tace no mommyn tana harara maryam Kamar idanunta zasu fado kasa wlh mommyn jakanta ce kawai irin na 'ya'yan talaka kada ma ki soma hada ta dani bata tambaya ga maid nan dayawa cikin gidan nan useless girl kawai, mommyn ganin abun zaiyi yawa tace matso na. Yata dama dalilin tasa ni kiranki kuma dulkanku kubani hankalin Ku nan domin muji asalin nata, kara kasa tai da murya cikin rarrashi tace meye sunan ki ,"maryam "ta furta a hankali Kamar mai ciwon baki Yawwa maryam inaso ki nutso ki gayamin gaskiyar labarin ki kar kiyi min Karya domin bazamu shirya dake..karaf safina tace mommyn wadannan talakawa kina expecting something gud ne kuma ma yadda taga wannan daular kinsan Karya ce kawai zata fada don..pls keep quiet as she said Khalil ya furta don baya son musu wa mommyn shi ,aikuwa siiut tayi ta koma tana gyatsina saboda tana ganin ya bada ita gaban maryam,a jiyar zuciya mommyn ta sauke tace maryam bismillah ina jinki, sunkuyar da kai kasa tayi ta fara bada labarin ta Kamar haka *asalin maryam* Kama yadda mahaifiyata ta gayamin ita yar asalin garin Maiduguri ne cikin wani kauye bankon sada ta taso cikin gata sakamakon ita kadai ce a gurin iyayenta mahaifinta tun tana karam yar shekara biyu ya rasu amma surukanta suka rike ta suka aurawa yayashi ita dukda haka yayanshi ya rike su cikin kulawa yanaso mahaifiyata sama da yayan da ya haifa yana zuwa Kano kai dabbobi siyarwa a matsayinsu na fulanin kanuri a haka mahaifiyata ta girma ta kasance kyakkyawan gaske ce kowa yana sonta harda dan maigari wanda yakeda mata gashi da son mata mahaifiyata wacce ake kira da aisah suna ce mata shatu taki yarda ta saurari surajo dan maigari wani zuwa da mahifina yayi suka taho da wani musa daga cikin garin Kano zai sayi dabbobi anan ya hadu da yar yayan babanta suka kulla soyayya kuma bai samu matsala ba aka bashi ita lokacin bikin da za'a kaita Kano lokacin aka saka shatu a yan rakiyar amarya inda wannan zuwan yai sanadiyyan haduwan ta da babana abdullahi ana ce masa audu inda yakasance shima ba baya ba wajen kyau duk da shatu batai Naam ba amma audu ya kwanta mata arai saidai batason yin nesa da garin su Kamar yadda mari tayi haka suka rabu yanata mata naci har saida ta gaya masa garin su sanan ya kyaleta koda suka koma haka shatu ta shiga tunanin audu har tsawan wata biyu shiru harta fidda rai rannan kwatsam saiga baban ya shigo cikin hanzari yace shatu dauko shimfida da bako garemu ,koda ta fita saita ganshi taji dadi sosai amma koda ya gabatar da kudirinshi mahaifiyar shatu tace Sam yarta bazata yi nesa da yarta ba duk yadda baba yayi taki dole haka audu ya koma a haka bai hakura ba bayan sati biyu ya kara dawowa inda baba yace yabashi shatu ya turo kawai shima zaije birni zaiji asalin sa gurin musa ,babana yayi farin ciki sosai ya kama hanyar komawa cikin farin ciki kuma gashi shatu ma ta amince dashi saidai gab da zai fita kyauyen wasu samari dauke da sanduna suka rufe shi da duka sukai mai lilis ashe labarin yajewa surajo cewar anbada shatu shiyasa akayi mai wannan dukan nan suka bashi har yamma saida wasu suka dawo daga kiwo suka ganshi kwace kamar matacce suka dauko shi zuwa gidan mu inda wannan jinyar yasa baban daura auren shatu da audu batareda sanin kowa ba sai yan uwa ,amma halin mutum ina cikin yan uwa wani ya zaga ya gayawa surajo aikuwa wurin mahaifin shi yaje hankali tashe ya sanar dashi Karya da gaskiya ran maigari ya baci sosai ya zaayi dansa naso amma abaiwa wani daga waje haka yasa akayi kiran su gaba daya da baba da audu da shatu yai musu fata fata ya ce su tattara su barmai gari maza kafin safiya haka shatu na kuka da mamana suka rabu inda baban yace tabi mijinta tayi biyayya komai ake ciki zaizo Kano sai Susan yadda za ayi haka suka rabu inda ya kaita suka hau motar Kano da yan kullin kayanta don auren ba shiri amma duk da haka baba ya kulla kudi yaba audu ya aiya mata abun bukata haka suka isa tana kuka na rabuwa da iyayenta kuma lokacin shekarunta sha uku ne kawai ,wata motar suka hau ta kauyen sayee koda suka sauka haka suka taka a kafa suka karasa Kamar yadda babana yake addua haka ya tadda mahaifin shi shi kadai a waje bisa shimfida yana Jan cazbaha gaban sa suka karasa yadda taga ya tsuguna daga gefe ita ma tayi audu ya gaida shi itama shatu ,cike da tuhuma baban ya amsa yace audu dasa kake tafe ne haka Jim yayi kafin ya aro jarumta ya warware wa baban komai ,jinjina kai yayi ya fadada fuska shi da fara'a yace masha Allah to Allah yayi muku albarka Allah ya bada zuri'a mai albarka,dukkan su suka amsa a zuci saboda kunya ,maza Ku tashi Ku shiga ciki ,haka suka mike suka shiga dakin dake soron gidan ya bude yace ta shiga ta shiga ya sakayo Kofar yace bari ya shiga gurin inna... *Mrs noour ce✍🏻* 😍😘😘 [7/11, 17:42] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… *kyan alkawari cikawa, godiya dubu Fareeda yakub da kika nemo min Besty na Allah ya kara kauna*😍 _wannan page din naki ne_😘 πŸ…Ώβž–1⃣2⃣ Dauke da sallama ya shiga cikin gidan as usual inna na nan tsakar gidan ta kafa kujerar ta ta sa ido a wulakance ta dago take kallon shi karaswa yayi kusa da ita yace sannu inna mun sameku lfy,lfy ta amsa a dakile shiru ne ta biyo baya na wasu yan mintinan tunani audu yake yadda zai sanar da inna yayi aure yasan duk bayanin da zai mata ba zata taba yadda da shima amma ya zaiyi dole ya gayamata, audu daka tasa ni gaba in baka da abun fada kona mikowa ka tashi ka bani wuri shan iska na fito yi,koda yake wace tsiyar ma ka tsinana ma kanka bare mu mu saka rai ta karashe cikin isgilanci,maganar tayi mishi ciwo donshi yasan bai taba zuwa birni ya shigo gida hannu rabba na ba amma kullum maganar daya kenan, a jiyar zuciya ya sauke a hankali yace inna dama akwai maganar da nake son fada miki ne,juyar da keya tayi tace kunne keji tunda gani agaban ka,sanyaya muryar yayi yace inna dama maganar auren shatu ne,da sauri ta katse shi a hasale wai shin mai sunan baba shatun nan ita kadai ce ne a duniyar nan dame tafi sauran yan uwanka na cikin garin nan indai ba kwadayin gadon shanun kakeyi ba sun hana ka sai ka hakuri indai bada wata manufa kake neman ba,share gumi yayi wanda yake neman jika mai jiki yasan fadar wannan magana a gareshi tamkar ya debo ruwan dafa Kansu ne amma ya zaiyi ta zamar mai wajibi,a gajarce yace inna ai baban yariga da ya dauren auren shatu yanzu haka tana nan cikin gud..zaro idanun ta tayi waje Kamar wata mai tsohuwar mayta tareda dafa kirji domin maganar ta razanar da ita kwairai da gaske aure kace mai sunan baba,auren da ake daurawa, shidai kasa kawai yayi da kai bai tanka ba yana jiran hukunci ,ai ba zato sai ji yayi ta kurma ihu da garfen gaske tana kukan munafunci jama'a kuzo Ku taimaka Ku rufa min asiri mai sunan baba ya sato musu ya mun shiga uku da asirin fulani ,da sauri ya mike cikin kidima yayinda kan Kice kwabo matan duk sasan sun hallara da yayan su gaba daya suna tambayar mai ya faru,audu dai shiru yayi kawai zuciyar shi nayi masa kuna yayinda inna keta razgar ihun ta shiga uku ta lalace mai sunan baba ya jefo mana bala'in fulani cikin gida fuu ta kwasa cikin sauri aka bita gaba daya yan gida domin su basu gane kan zancen data keyi ba zauren gidan ta nufa kai tsaye dakin audu ta fada aikuwa ido hudu sukai da shatu wacce tai maza ta janye gyalen ta ta rufe fuskar ta sallati ta fara cikin kwazozo da da sauri ta fada cikin dakin ta yaye mayafin ta kare mata kallo jinjina kai tayi eh lallai mai sunan baba juyawa tai tsakar gidan Inda jama'an gida sukai cirko2 suna jiran bayani gurin inna domin duk tambayan duniyar nan sunyima audu amma ba amsa, tana shiga tace da wani yaron maza jeka ki malam waje tana haki ita wannan wane irin bala'in ne haka ,da gudu yaron ya shika Kofar gida ya kira malam wanda yake zaman jiran kiran don yasan hakan zata faru Mikewa yai tareda kama hannun yaron sukai cikin gida da sallama ya shiga hankali kwance dukda yadda yake hango fitina da rashin hankali a idon inna ganin shigowar sa yasa matan gidan kowacce wucewa domin dukkan su surukan shine, tun kafin ya karaso inna ta fara magana malam kanajin abunda mai sunan baba ya aikata kuwa toh wlh bazai yuwuba ya jawo mana fitinar fulani kowa ya sansu ba baya ba gurin mugun nufi,a uzu billahi malam ya furta da karfi don Allah laraba ki dinga ktautata harshen ki meya sa ako yaushe bakin ki baya fadin alkairi ne,,ey ai dama haka zakace malam ai anzo maganar wanda baya laifi gun ka dole kai uwa kai makarfiya ka hanani fadin gaskiya toh kuwa in Allah ya yadda bala'in daya debo kanku zasu sauke shi Ku kadai, inna ta fada cikin fada tana tada jijiyan wuya Kamar zata kashe mai rai,girgiza kai kawai malam yayi tareda cewa Allah ya shiryar da Ke kai audu maza ka taho da mai dakin naka yanzu,cikin sanyi jiki ya juya zuwa dakin yayinda malam ya budewa inna ido kafin ta nutsu koda suka isu vanda harara babu abunda take aika ma shatu wacce kyawunta ne kawai yafi komai kona mata zuciya haka malam yayi musu nasiha sosai yace shatu tayi biyayya ga inna domin audu bashi da uwar data wuce ta itama inna yayi mata nasiha data rike shatu tamkar diyar cikin ta domin bata da kowa sai su a duniyar nan yanzu tunda iyayen ta sunyi nesa da ita saanan ya Sallamu su audu suka mike ita kuwa budar bakin ta keda wuya sai cewa tayi in Allah ya yadda fitina da bala'in ka dauko wa kanka tunda kai aure batareda Sani na ba ai mun kulla kenan haka ta mike ta shige daki fuu ta bar malam Zaune , haka zaman shatu ya kasance cikin gidan cikin bakin ciki da ukuba domin tunda audu ya koma cikin Kano gun sana'ar shi inna ta daura karan tsananta ga shatu tun safe itace sharan cikin daki da tsakar gida wankin ban daki ,girki wanki duk itace babu damar wani ya tanka tunda duk surukanta ne a gidan kowa shakkakr ta yakeyi dama ma malam wataran inya shigo yaga shatu na aiki Kamar vaiwa ga yayan gida nana Zaune yakan yi magana, a haka wata rana lokacin ta shekara da aure ta jiyo muryar yara sunata oyoyo baba ,oyoyo baba ,ita dai tana tsakar gida tsugune tana wanke kwanuka yai sallama ya shigo dagowa tai ta amsa tunda ta hada ido da shi taji gijinta ya vuga ta rasa natsuwar ta haka kawai taji bai kwanta mata ba shi kuwa daskarewa yayi yanan mata kallon kurulla masha Allah ya furta yana jinjina kai Aa iliya ne muryar inna ta katse shi da sauri ya wayance da cewa nine inna iliyan ki ya dawo,washe baki tayi cikin farin ciki lalae maraba barka karaso ciki binta yayi suka shiga ciki yana waigen shatu wacce duk ta tsargu suna shiga ko zama baiyi ba yace inna ina kika samu kyakkyawan yarinya haka,nan da nan ta tsuke fuska tace wace din kenan kake magana,matsowa kusa yayi sosai don shi baima lura da sauyin fuskar inna ba yace gata can waje tana daurayar kayan kwanuka ,dakata ta katse shi cikin bacin rai bana son ina cikin nishadi kana sako min maganar shatu matar mai sunan baba ce ,zaro idanun iliya yayi yace inna shi audu ne ta auri wanda kyakkyawan yarinya haka yai tambayar cikin mamaki ,tabe baki tayi tace hmm bari kadai nan ta zayyana masa duk yadda akayi da yanda take azabtar da ita, amma wlh inna audu anyi tsinanne yanzu ina ya gano wannan ya haka na dauka ko ta makwabta ce ince inaso lalle audu koni duk yawona na duniyar nan banyi gamo da kyakkyawan haka ba kai inna lamarin audu fa saikin dage wlh ya fada rai bace domin a rayuwa inda wanda za'a bashi wuka ya kashe to bai wuce audu ba, cikin murmushi inna tace ai Alhamdulillah dama jiran zuwan ka nake Kaine kadai wanda za'a rufa a birni tare ,da sauri shatu ta miki jiki na rawa domin duk abunda suke fada tana jinsu yayinda inna ta manta da zaman shatu a gidan da sauri ta wuce dakinta zuciyar ta cike da tsoro halin inna, haka shatu ta kasance cikin rashin kwanciyar hankali yayinda iliya kullum nan Kofar dakinta ya koma shimfida don ya ringa kallonta kawai sai dai inta gaji ta sakayo kofa a haka har kusan wata biyu da zuwan iliya sanan audu ya dawo koda ya dawo haka ta iske shatu ra rame ta lalace amma haka ya kauda kai duk don a zauna lfy ,kwana biyu da dawowar shi da dare suna kwance tace ni kam in tambayeka ,tace eh maizai hana fada mana,sai da tayi Jim sanan tace wai inna kuwa ita ta haifeka , ajiyar zuciya ya sauke dama yasan zaayi haka, Sunan mahaifina malam Sani malami ne sosai ya auri mahaifiyata maryamlokacin gidan su ita da inna laraba kadai iyayensu suka Haifa amma sai Allah yayi ikon sa inna ta taso da rashin farin jini har mahaifiyata ta girma ita koma sai manema ta ko ina wannan ne dalilin kiyayyar da Ke tsakanin mahaifiyata da yayarta uwa daya uba daya kuma dadin dadawa itaahaifiyata ta biyo mamanta wacce ta kasance kyakkyawa ce ita kuwa inna mahaifinsu ta biyo wanda gaskiya ba wani kyau ne dashi ba haka akayi ta tsaida maneman mahaifiyata wai don inna ta samu miji amma shiru ko mutum daya haka har Allah ya fito da mahaifina wanda ya kasance malami ne sosai koda yaje neman auren mahaifiyata lokacin mahaifin su yaso ta tsaida auren saboda inna amma malam ya dage har yana jawo musu ayoyi ahaka har akasa ranar bikin su inda inna tayi kuka Kamar zata mutu ta kara dora tsana sosai akan mahaifiyata wanda duk sharrin shaida ne har akayi biki ranar ana murna amma ita tunda ta fita gidan bata dawo ba saida aka kai mahaifiyata gidan ta haka rayuwa tai ta tafiya har Allah ya bawa mahaifiyata cikina har lokacin inna dai babu maganar aure har ta shiga watan haihuwa inda aka tura inna zuwa gidan mahaifiyata ta zauna da ita har ta haihu ,cikin ikon Allah ta sauka lfy ta haifene iyayen sunyi farin ciki akai ta hidima da mahaifiyata sai abunda take so zaayi ko za'a ci haka dai inna ta daure har bayan suna inda naci suna abdullahi sunan mahaifinsu inna dalilin kena da ake kirana da mai sunan baba,gashi tana ganin irin kulawar da malam yake tiwa mahaifiyata haka dai rayuwa taita tafiya bayan shekara uku ta kara samun ciki mai wahalar wa inda nan ma inna ce tace zata zauna da ita haka har lokacin haihuwa tazo inda mahaifiyata kecin bakar wuta malam sai tupi ya Ke rubutawa haka har unguwar zuman tace vari taje gida ta dauko wani jiko a gidan inda kafin ta dawo sai kukan inna malam yaji koda ya leko mahaifiyata ta riga ta cika haka yai kuka Kamar me inda ka kaita gidanta na gaskiya ita da abunda Ke cikinta wanda bai riga ya fito duniyar ba ,bayan arbain shine iyayen su suka hada auren inna da mahaifina Wacce halin su ya vambata da na mahaifiya tasaboda inna batada hakuri ko kadan gason abun duniya haka akai zaman harta haifi yara hudu maza duka ,garba,ne babba yana da mata biyu da yara sai haruna shima matan shi biyu sai musa shima biyu sai iliya wanda yakeda mata daya kuma duk Kansu a gidan suke Zaune da mata da yara hak a nai zaman babu dadi gurin inna har na fara zuwa cikin birnin Kano sana'ar wannan kena,ajiyar zuciya ta sauke tace lallai inna amma abun sai addua, yace Hakane amma wannan karon na samu daki tare zamu tafi dake aikuwa shatu tayi murna itama zata huta gwara aikin inna amma matsalar iliya ita tafi damunta wanda yakeji Kamar ya turbutsae ta cikin dare, aikuwa washe gari ya samu malam da maganar inda yayi farin ciki sosai yace shima yana shirin yi mishi maganar toh kuma sai Allah yasa yasamu,sabanin inna da bakin ciki ya cika ta zuciyarta ta cika da hassada taita fada tana kumfar bakin baisa ba yakai shatu birni ma bayan ga sauran surukan gida suna Zaune cikin yanuwa amma zai ware ta don baya son zumunci da yan uwa haka dai yai ta bata hakuri amma fafur taki saida malam yai mata da gaske yace kota yarda ko kar ta yarda tafiya babu fashi ,aikuwa cikin kwana biyu suka tattara suka koma Kano dan gida ne mai kyau dan karami ne sosai daki buyu da bayi da kitchen a tsakar gida haka sukai zaman su cikin rufin asiri har ta samu tana zuwa wurin yar uwarta wacce ta sanar mata har yanzu bavansu ba'a San rugar daya koma ba tunda maigari ya koresu haka rayuwa taita tafiya inda bayan shekara biyu da komawarsu Kano Allah yayiwa malam rasuwa sunyi kuka sosai sunyi bakin cikin babban rashin nana musamman audu da shatu wanda shikadai ne yarage musu gatansu haka sukai hakuri bayan shekara shida lokacin aurensu shekara goma da auren su Allah yaba shatu cikina haka taita laulayi babana yana kula da ita sosai har ta shiga watan haihuwa haihuwa inda ranar suna Zaune tsakar gida da yamma sai sallamar inna sukaji dukkansu saida gaban su ya yanke ya fadi amma haka suka daure suka tarbeta cikin mutunci wannan shine zuwan da inna tayi taki komawa ta zauna musu taki tafiya har shatu ta haifeni inda babana ya koma saanar saida gwanjo kuma yana samu sosai nana inna ta hana su sakat kullum cikin fitina haka na taso cikin gata dukda kuma Allah ya hada jinina dana inna bata kyara ta saidai tayiwa ummi na harna kai shekara hudu akasa ni a wata makarantar kudi na fara zuwa da islamiya inna dawo wacce take hade da hadda ina da matukar kokari a fannin islamiyya wanda boko sai dai a hankali domin hankali na yafi karkata ga Islam din a haka iliya ya uzzuri babana akan yanaso shima ya fara zuwa gurin saida gwanjon Dole haka babana ya hakuri amma bayaso domin yasan fitina ce kawai zata kai iliya da hassada a haka suka fara zuwa bayan shekara biyu suna lallabawa da dadi da babu a haka wata rana babana ya dawo gidan cikin matukar farin ciki wanda har ya kasa boye wa a fuskar shi ummi na dai ta daure bata tambaye shi ba har dare sannan yake gaya mata Allah ya amshi adduar shi yau dinnan sun kwance dila ya tsinci wata sarka ta white gold nade biyu da wasu dollars a dunkule cikin aljihu wani wando aikuwa ummina tayi murna kuma ya tabbatar mata da ya tambayi wani yace akalla sarka nan zata kai million daya da dauri Alhamdulillah Lilah ummi na ta furta cikin farin ciki amma kafin ta rufe baki sai salatin inna sukaji nan ta rinka bala'in donme bai sanar da ita farko ba ko iliya dan uwan shi sai mace saboda ta mallake shi haka aka kwana ana abu daya inda babana yahana ummi tanka ma inna har saida iliya ya dawo suka shige daki Allah kadai yasan mai suka tattaunawa wanda yasa inna bata kara maganar ba bayan kwana biyu inna tace su shirya shida iliya suje ganin gida shidai baba baiyi naam da maganar ba amma bayadda zaiyi haka suka shirya da safe suka dauki hanya wannan tafiya ce sai labarin mutuwar shi aka zo wa ummi dashi wai sunyi hadari ko gawar shi baa gani ba iliya ma ya ji ciwo sosai inna ta shiga tashin hankali sosai babu abunda take tunawa sai hirarsu da baba a daren yake cewa tayi mishi alkawari ko bayan bashi komai inna zata yi mata ko akan maryam ne kada ta taba bijire mata tayi hakuri kada ta taba maida mata bacin ranta akan kowanne abu zata yi musu ita dai ummi ta amsa ne kawai amma bata dauka wasiyya ce ya bar mata ba ashe mutuwa zaiyi ,maryam ma tayi kuka dukda ba wani wayona kirki ne da ita ba haka ta taso cikin maraici yayinda duk abunda baba ya tara iliya ya karbe dukda fadan da yan uwansu sukai akan inna ta bar gidan amma taki tace ta gama zaman kauye dole saboda rashi ummi ta maida ni makarantar gwamnati wacce da kaya da ya sanar cikin gida take rike damu amma duk da haka kullum cikin judge take gun inna haka har Allah ya kawo su hajiya ladi cikin rayuwa ta suka kawo ni nan ,nan ta gaya musu yadda sukai da su hajiya ladi harta tsira, *cigaba* Mommyn Khalil tayi kuka ta tausaya wa maryam yayinda safina ko ajikinta bata ji tausayinta ba saima gyatsina takeyi wat a story tace tareda yin tsaki ta miki ta wuce sama yayinda Khalil shima ya miki yana cewa momy shikenan kinga mommyn kin samu Karin maid kenan da sauri mommyn da maryam suka dago suna kallon shi wanda yayi hanyar fita daga parlon,mommyn ce tace stop there son up to my room now ta fada rai bace yayinda maryam tai kasa da kai tana sharar hawaye,.. *mrs noour ce✍🏻* [7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”± Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited byπŸ‘‰πŸ» *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sisπŸ‘‰πŸ» *Maman Sultan*😘 Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ… *yeeeeeeh πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»baki sun tafi yau,*😜 *ga sorry nan na cika muku a kwanduna kowacce ta dauki daya tayi maneji amma dai pls kuyi hakuri nima kuna rai na alwaz &4 rever*😍😍😍😘 *mmn najwa sun tafi da Kansu*πŸ˜‚ πŸ…Ώβž–1⃣3⃣ Juyuwa yayi fuskar shi daure tamau ya wauce sama,yayinda momy tace maryam tashi kije kiyi wanka kizo kisame ni a dakin I tink akwai kayan da zasu miki before son ya kaiki asiyo wasu,, ajiyar zuciya ta sauke jin an anbaci Khalil ne zai kaita amma ya ta iya muryar kasa tace toh hajiya nagode, Allah ya saka da alhairi,, Ameen yata maza tashi kije,tare suka mike sukai hanyar step kowa yayi bangaren sa,, da sallama mommyn ta shiga yana kwance ya harde Kafafunshi ya dora bisa hannun resting chair haka hannuwan sa suma ya hardesu tareda rufe idanun sa Kamar mai bacci amma tunani yakeyi how can mommyn shi tayi kokarin zubar mishi da girma a gaban wannan mad girl din,, karasowa tayi kusa dashi ta daga kanshi

Chapter 5 of 32