Share this page
dasu kayi mata nauyi saboda kuka, Inda yake Zaune ,nan suka nufa duka suka zauna harda maryam din, abun motsa baki aka cika mata gabanta dashi wanda ita take ganin ko ruwa baza ta iya shaba domin batasan mai suka saka mata aciki ba, har kusan minti goma taki ko kallon kirki tayiwa kayan gabanta sai faman share hawaye takeyi wanda yaki tsayawa duk da azabar zafin da idanun suke mata Kamar an watsa mata garwashi a cikinsu saboda kuka,ita kuwa tayi nisa ne cikin karanta addu'oe da tunanin hanyar da Zata kubutar da kanta ,kai wannan rayuwa ina Allah ya dauki rayuwata inhuta , saurin tuba tayi tana karfafa ma kanta gwiwa tasan Allahu maji rokon bayinsa ne nasan Insha Allahu Allah zai kubutar da ita sai dai kawai ta dage da addu'oe..... Keeh " muryar Hajiya ladi ta katse ta , Ki saurare maryam da kyau kiduba wadannan mutanen dake zagaye da nan,tana mata nuni da securities din Alhajin , dagowa maryam tayi tana kare musu kallo sanye suke cikin bakaken suit bakake dasu majiya karfi ,kowanne idanunsa rufe suke da bakaken eye glasses babu alamun rahma a fuskarsu bare Susan wani abu tausayi , kiris suke jiran umarni su aiwatar sai hura hanci suke, kuut ta samu ta hadiya abunda ya tsaya mata a makoshin ta, tana zare idanun ta wadanda sun kankace saboda kuka,maida duban ta tayi gurin Hajiya da Ke murmushin mugun ta saboda gano tsoron da maryam ta shiga tasan bazata sha wahalar shawo kanta ba.. gyaran muryar Hajiya tayi tareda daure fuska tace " maryam ki dubesu da kyau wadannan dakike gani ba keba hatta wadanda Ke cikin nan Ke in takaice miki ko airport dinnan Alhaji yabasu umarni zasu iya tada shi gaba daya da duk wani wanda Ke ciki saboda haka ina mai baki shawara ki kama bakin ki kiyi biyayya ga alhaji shine zaman lafiyar ki dana iyayen ki.. dagowa tayi a razane tana waro idanun waje .. Kwarai kuwa maryam Hajiya ta jaddada mata domin idan kikayi kokarin guduwa kokuwa yin wani abu da har ya bata ran alhaji tofa koda kina ganin zaki iya tsira, alhaji bazai barki da rai ba harda iyayen naki suma zai iya sawa a hallaka su koda kuwa kasar zaki bari ,domin kin San duk wanda yakeda kudi ko mukami shiyake da *karfin IKO* yin komai kuma a ko ina akan talaka kuma babu wanda ya is a yai magana balle ki Sarai in kin tsira wani zai tsaya miki, nisawa tayi tareda kurban juice din dake a glass cup ,sa anan tace ," shawara nabaki in kinbi kin huta keda iyayen ki sabanin haka kuwa kinsan abunda zai biyo baya... Kuka take sosai mai hade da sauti Kamar zata shide ,kukane mai taba zuciyar duk wanda yake sauraro mai imani amma fa domin su Hajiya ladi da alhaji murna ce fal ciki da zuciyar su suna gani dole tayi hakuri ta je kuma tayi duk abunda aka umarce ta.... Hajiya don Allah ki gayamin aikatau zanyi a chan ko kuwa? maryam ta jefo ma Hajiya ladi tambayar da bata yi tsammani ba.. ➖➖➖➖➖➖➖ *Safina* tana hakimce a bayan mota sai cika takeyi tana batsewa tsaki taja mai karfi wanda tayi ne domin Habib ya ji haushi tasan ya tsani tsaki a rayuwar shi ,aikuwa tana kallon shi ta gefen ido ya wurgo mata wani mugun kallo ,amma tunawa da yayi da mahaifin ta yasashi lallashin kanshi kuma ma inda Sabo ya saba da rashin girmama nagaba da tijara da rashin mutuncinta Kamar ba diyar Alhaji isma'il ii ba ,ganin kada ya tsaya bata lokacin shi a tunanin yasa shi mika hannu ya kunna radio CD plate na kira'ar sudais yasaka ya rage muryar kadan dai dai sauraron shi,ya zame ya kwanta ta bayan sa jikin kujerar tareda kulle idanunshi yana bin sautin kira'ar cikin zuciyar shi... Safina na ganin haka sai ta jawo laptop dinta ta kunna music ta shiga ta bude wakokin ta kunna tareda kure motar da kara ,duk dan ta bata mai rai saboda bai zo da wuri ba harta gama shiryawa , murmushi tayi tareda bin wayar da karfi kama wacce take cikin club harda yar rawa takeyi daga Zaune,tasan bazaiyi shiru ba saiya tanka ,so take ta gaggaya mai magana so take tasan shidin ba dan gidan uban kowa bane,. Sai dai kassh batayi sa'a ba domin Habib yayi alkawarin Insha Allah ko kallon arziki bazai hada shi da ita ba balle na tsiya ,mika hannun shi yayi ya kashe karatun ya lalubo wayar shi a aljihu ya kunna karatun tareda saka earpiece ya cigaba da bin karatun shi hankali kwance..., Haka ta gaji ta kashe tana zagin shi cikin zuciyar ta . Two hours suka iso airport na Abuja.. ➖➖➖➖➖ *Maryam $ Safina* Hajiya ladi ta fara kuluwa da lamarin maryam ta nida baki da niyyar yin magana dangara2 motocin su safina guda 4 suka shigo airport din a guje , a kusa da inda suke suka Parker motocin su , murafen motocin guda biyu aka bude sojojine su hudu kowacce motar su takwas kenan suka tako har inda motor safina take suka zagaye ,daya ya bude mata murfin Kofar amma sai tayi Kamar bata gani ba ,har kusan 15mins tana latse2 a waya tana jira Habib ya bude mata ,wanda shi yariga da yawuce ciki da sauran soldiers din dake dahar motar , Saidai suka is a har ciki sa anan ya lura safina bata futo ba, dole haka ya koma shidai fatan shi ya rabuwa da ita lafiya b4 tai mai wani abun da bazai iya tolerating din shiba , Komawar shi tayi daidai da mikewar da Su Hajiya ladi sukayi domin zuwa siyayya da alhaji yabada tulin kudi ayi mata siyayya kaya ta chaza da wadanda zata tafi dasu,. Karasawa yayi ya bude wa safina Kofar sa anan ta fito tana yatsina ta wuce suka take mata baya,.. Bayan minti talatin aka fara kiran passenger's din us su shirya jirginsu zai tashi , Masu bin jirgin duk suka mike harda safina wacce Ke tafe cike da yanga da jin kai ,Habib kallo daya yayi mata ya watsar sanye take da pencil trouser blue da blue din top mai dogon hannu tayi rolling kanta da pink din karamin gyale, fuskarta tasha make-up wanda da dace da fuskarta kafarta sanye da takalmi hill pink color ta wuce,..shima ya juya domin fita nan suka ci karo da Maryam wacce kanta Ke kasa tana hawaye ,dagowa sukayi atare suka kalli juna nan take yaji kirjin shi ya buga dakyar yasamu ya iya hada kalmar"sorry ya furta a hankali wanda inba ka kalli labbasa ba bazakai tunanin yayi magana ba gyada kai kawai tayi ta share hawaye tabi bayan alhaji da yayi gaba tabar Habib a tsaye Kamar an dasa shi. *shin maryam zatayi biyayya ga alhaji ko kuwa*? *shin zasu iya kulla alaka da safina ko kuwa ta taimake ta* *shin Yaya Habib* *kubiyo ni domin jin yadda zata kasan ce* *comments* *share* *Mrs noour ce✍🏻* [7/11, 17:42] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* 🔱🔱🔱🔱🔱 Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited by👉🏻 *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sis👉🏻 *Maman Sultan*😘 *yan uwa masu comments ina matukar jin dadi Allah ya bar kauna ,*💃🏻💃🏻😍😍 بسم الله الرحمن الرحيم 🅿➖0⃣5⃣ Samun kansa yayi dason kara kallon ta,amma ya kasa sakamakon bugun da zuciyar shi takeyi yasa shi shiga wani hali,meke faruwa danine haka daga kallo daya?? yayi ma kanshi tambayar wacce bashi da mai bashi amsar ta, karfin hali yayi ya waigo da kansa a hankali yana duban hanya amma ina ko mai kama da ita bai hango ba, ajiyar zuciya yayi tareda gyada kafadar shi ya wuce ya fita , inda sauran soldiers din Ke jiran fitowar shi ,saida suka Sara mai sa anan daya ya bude mishi murfin motar ya shiga ,suma suka ja suka figi motar a gujee. Tafiya takeyi Kamar wacce kwai ya fashe wa a cikinta wanda har zuwa lokacin hawaye bai dai na zubowa daga idanun ta ba ,tunanin halin rayuwa takeyi shin ta hakura kenan da kafarta zata taka taje wata kasa kuma zuwan nan tasan bashi da nufin alhairi gareta ,ooh ya Allah ka kawo min agaji da taimako ,ya Allah zuwana garin nan nasan babu alhairi Allah ka kubutar dani .... ➖➖➖➖➖➖ *Ummi da Inna* Zuciyarta fal farin ciki ta rangada sallama ba tareda jiran amsa ba ta kutsa kai gidan ,kai tsaye dakin ummin maryam ta nufa ta yaye labulan tareda fadin " ina kike ne matar baba ,ki fito kiga alherin da yarki ta fara samu tun kafin taje"... Ummi najin inna tai maza ta share hawayenta ta fito daga uwar daki tana murmushi wanda iyakacin sa labbanta tace"Sannun da zuwa inna har kin dawo",.. ai har na dawo ne ko kuwa in koma ne kin so kada indawo da rai saboda mero taki ce.. Kiyi hakuri inna ba nufi na kenan ba ummi ta bata amsa ta kara da tambayar ya aka baro su,.. innalillahi wa inna alaihir raju'uun, inna ta rafka sallati ta na tafa hannuwa, wai matar baba yaushe lalacewar taki takai haka ne eyeeh ince ko akan ki aka fara haihuwa toh inkin manta da zaman muna karkara kin kama na birni ita dai kunya da kara abubuwa ne masu muhimmanci ga ya mace musamman uwa akan 'ya'yanta , mu ana mu zamanin ko wuka suruka tace ka kiko ta yanka d'a ,dole ki mika ki shige d'aka saboda alkunya amma dududu yarnan ko awa biyu batayi ba da barin gidan nan kina tambayar ina na kaita ko... Inna kiyi hakuri ba nufi na kenan ba. toh koma dai mai kike nufi mero dai tayi dace tayi saa duba kiga tarin arziki da suka baya tun kafin ta fara aikin nan ,eyeeh kwance habar zaninta takeyi tana cigaba da mitar yanzu dai kinga dubu hamsin ne cif ,ai mero kam yar albarka ce kinga ansamu na katifa da tukwane ,in kika karfafa mata gwiwa baifi tayi wata shida ba ta dawo kinga asiri yarufu sai aure tunda ga manema can a gida duk wanda aka hada ta dashi zaman su zasuyi, daram ai kinga asiri ya rufa ,,.. Ita dai inna shiru tayi kawai domin komai zata furta baza ta tsira wurin inna ba , indai fata na aduk inda mamana take Allahu ya tsare ta daga dukkan abun da zai zamo cutarwa gare ta , miko mata kudin inna tayi tace to ai sai ki irga ki gani kisa albarka domin bazan barsu wurin ki ba su lalace a banza domin Ke ko yar sana'ar nan ta mata kika fara sai ta rushe ,maza ki sa albarka in kaisu mabuya na adane su.. Aa inna ki adana kawai ai nagani Allah yasa albarka, Ameen inna ta amsa tareda wucewa dakinta,kai ta girgiza tace wannan rayuwa Allah kabamu ikon cinyeta lfy , duk inda kike mamana Insha Allahu albarkanmu zata riske ki,Allah zai kare ki sai kin zama abun alfahari ,farin cikin ki zai dawo fine da na baya ,share hawayenta tayi da gefen zaninta ta wuce dan madafin nasu don Samar ma inna abunda zataci don batajin zata iya kai komai bakinta..... ➖➖➖➖➖➖➖ *Maryam & Safina* Ooh Allah kyau gani gaban jirgin sama wai zan hau sai dai ba a hawan dadi ba haka Hajiya ladi ta rike ta gam Kamar za a kwace ta har suka shiga domin alhaji yana VIP saboda gudu zargi , kujerar su ta duba sannan ta ja maryam suka zauna ,kujerun uku 2 ne a Jere maryam tana jikin window yayinda Hajiya ladi Ke tsakiya ,safina na gefe rufe idanunta da bakin eye glasses tasaka earpiece a kunnanta tana jin sauraron waka,..toh fa maryam ta rude lokacin da taji injina jirgin sun fara aiki alamun zai tashi yanzu kankami jikinta tayi tareda runtse idanunta da karfi jikinta sai rawa yake ta na karanta duk addu'oen da ta San ta iya wanda Hajiya ladi banda harara babu abunda take aika mata dashi don kada ta bata kunya ,yayinda safina batasan wainar da ake tiyawa ba,.. Sai da suka fara landing a dubai after two hours suka kara hawa wani ,duk motsin da maryam zatayi a kan idon Hajiya ladi takeyi hatta da bayi saita bita don karta gudu har sai da taga jirginsu na us ya daga sannan hankalinta ya kwanta tasan ko cewa maryam tayi ta koma gida in sun sauka bazata iya ba ,murmushi cin nasara tayi ta zame tafara sharar baccin ta hankali kwance ,yayinda safina ta tashi domin zuwa bayi , minti goma tsakanin sai gata ta dawo earpiece dinta ta maida ta rage hasken bulb din ta kwanta , ita dai maryam binta tayi kawai da ido tana tunanin ita kuma wannan ita kadai take ne ? to ko ma dai ita zata nemi taimako wurinta ne saidai kuma tana tsoron kar su Hajiya ladi su gane ta ko dai ta je wurin sauran passengers din ta duba ko zata samu wanda zata kai kukan ta gareshi ne, ooh ya Allah ka kawo min mafita Allah sarki ummi na ko a wane hali take yau zata kwana ita daya babu abba ya rasu ya barmu gashi nima yau anrabamu ta karfi ba tareda kinsan ina ni keba ko a wane hali nake ciki ba ,wasu hawaye masu dumi ne suka fara gangarowa bisa fuskarta,ta shiga sharewa a hankali har kukan ta yafara fidda sauti sakamakon shirun dake cikin jirgin, Hey hello pls kukan ki yana damuna pls control u salf or u re in need of something ? girgiza mata kanta tayi tareda share hawayenta tana mamakin dama wannan bahaushiya ce ,sai a lokacin taji wani irin sanyi aranta wanda ta gaza gane ko na menene , hamdala tayi wa uban giji sai take ganin Kamar zata iya taimaka mata, amma datayi wani tunani saida cikinta ya murde tana rokon Allah yasa itama ba karuwanci ne zai kaita ba,toh inba shiba ne menene yarinya irin haka tayi wannan tafiya ita kadai kuma da alama ta saba zuwa,zuciyar ta ta tunasar da ita haka, tun tana tunanin har baccin barwo yai nasarar sace ta sai ajiyar zuciya take yi abun tausayi😭 *masoya maryam Ku bata shawara,shin ta nemi taimako safina ko kuwa ta yiwasu Hajiya ladi biyayya taga yadda Allah zaiyi da ita* *comments* *share* *mrs noour ce✍🏻* [7/11, 17:42] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* 🔱🔱🔱🔱🔱 Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited by👉🏻 *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sis👉🏻 *Maman Sultan*😘 بسم الله الرحمن الرحيم 🅿➖0⃣6⃣ a hankali take bude idanuwan ta saboda kumburi da zafin da suke mata,wani irin azabbenben firsari ne ya tashe ta waigawa gefen da Hajiya ladi take tayi sai taga bata nan ,ina taje kuma ko bayin tashi ga ne kokuwa gurin Alhajin taje ne take tambayar a zuciyar ta ,komawa tai kan kujerar ta kwanta tareda lumshe idanunta,har kusan minti goma,wani tunani ya fado mata a zuciyarta batareda tunanin komai ba tai maza ta miki da iyakacin karfinta duk da yunwar dake cinta , trolling dinta tai maza ta dako ta bude kaya ta dauka wanda sakamakon dan duhun wurin yasa banga kalarsu ba ,tai maza ta rufe tareda maida jakar mazau ninta da sauri ta tusa kayan kasan hammatar ta tai maza ta koma ta zauna daidai lokacin da Hajiya ladi ta dawo daga toilet. Aa lfy maryam ko yunwa kikeji ne ,? girgiza mata kai tayi tace bayi nakeson zuwa,sai da ta zauna sannan ta dannan wani wurin,daya daga ciki ma'aikatan jirgin ce tazo ,Hajiya ladi tace ta bita ta rakata, aikuwa har cikin bayin ta kaita tareda nuna mata yadda zatayi amfani da toilet din sannan ta juya , ajiyar zuciya maryam ta sauke da sauri ta fito da kayan da ta makale ta ajiye a gefe sannan ta cire jallabiyar dake jikinta , kayan ta dauko ta warware wasu riga da wando ne ash color masu matukar kyau wando pencil ne rigar kuma ta kaima ta har cinya amma babu hannu sai farar jacket a sama ,da sauri 2 ta saka kayan tareda maida jalabiyar ta akai sannan tai fitsarin ta gyara taga komai yayi dai2, ta fito ta koma wurin zamanta tana adduar Allahu ya sa tasamu damar tserewa daga gurin su alhaji da wannan dabarar datake tunanin yi ameen. Sai 6:45 daidai jirgin su yayi landing a America, safina na gaban su maryam suka ni layin kowa ya dauki kayansa sannan suka fito harabar airport din kowa ya kama gabanshi ,sai ga alhaji ya taho har inda suke yana murmushi cin nasara, ya dade yana burin son kasanciwa da maryam sai gashi yasameta cikin sauki ba Kamar yadda yayi tunani ba.. Kusa da maryam yatsaya Kamar zai hade musu jiki wuri daya ya sunkuyo da kanshi dai dai kunnanta tace gamu a America ya gajiyan hanya, yana kashe mata ido, wata muguwar harara ta watsa mai tareda han tsaki ta matsa daga kusa dashi,tana lahantar shi a zuciyar ta , murmushi ta sake yi wanda muni kawai yake karamai yace lokaci ne kadan komai zai wuce, Hajiya tai dariya tace kwarai kuwa ba boka ba malam,... Saida ta bari sun kusa fita kafin tace Hajiya firsari nake ji ,fitsari kuma Hajiya ladi ta maimaita ,ta gyada kai ,tace ai saiki bari sai mun is a hotel din kya... Aa hajiya barta taje tayi inta dawo saimu wuce tunda bawai sauri akeyi ba,alhaji ya fada, ai sai kiyi sauri muje kiyi,nan ma Alhajin yace Aa ki barta taje tayi tadawo ai nan ba Nigeria bace inta gudu ma zata dawo da kafar ta ko kin manta haseey ne., Dariya sukayi duka tace yazan manta da haseey shegiyar yarinya kafaffiya, Ita dai maryam juyawa tai da sauri ta ajiye musu Jakarta ta wuce toilet ta shiga da sauri tana adduar Allah ya bata nasara ,jikinta sai rawa yake ta cire jallabiyar jikinta ta cire dan kwalin kanta tarin uban gashin data daure da ribom ta saki ya bazo mata har bayanta ,taja gefa da gefe ya rufe mata kunnanta har gefen fuskarta ta dauko eye glasses ta saka ta kalli kanta a mudubi sai ta ganta Kamar dama yar nan kasar ce, ta diba ruwa ta wanke fuskarta tayi ajiyar zuciya tana sake kallon kanta tasan da wuya su ganta saidai ilahirin jikinta rawa yake ga rashin Sabo da suturar dake jikinta ga tsoron karsu kamata,... maryam ya kamata ki ajiye tsoro domin wannan ce hanya mafi sauki da zaki bi ki iya tsira in Allah ya amshi adduar ki ,daga baya Kya San abinyi zuciyarta ta karfafa ta , haka ta fito ta leko gabas da kudu da arewa sanan tai shahada ta fito ,gefen shuke2 take bi har ta samu tabi wata hanyar fitar Allah yasa da dan iliminta tana karanta komai da inda zakabi ,dai2 zata fita taji wata muryar na magana chak taja ta tsaya tana sauraro, wayyo dadin mun iso amma kaga driver bai zoba na tsani ya kasan ce ni zanyi jira ba shida ni ba wlh da... kiyi hakuri baby am sure by now yana kusa ,ki rinka hakuri da rayuwar nan let me call him okay,, k dad luv u much ta kashe wayar tsaki tayi tana duba agogon hannunta ta juyo da niyyar komawa ciki sukayi karo da safina, kiyi hakuri maryam ta furta a hankali, kallon wulakanci tai mata ta wuce ta daga waya "hello dad" Yawwa baby fito yana jira ", don Allah kiyi hakuri da mutane a kullum ina miki fada,wani talakan dakike rainawa yafi mai kudi.. don Allah ki taimaka min Kamar yadda Allah ya taimake ki muryar maryam ta katse mata wayar wanda take ta kuka ta hada hannuwan ta guri daya alamar roko, in taimakeki Kamar ya safina ta jefo mata tambayar tana mata kallon wulakanci,.. Allah sarki maryam ita kuwa bata damu da kallon data Ke mata ba ta kara matsowa kusa da ita tace don Allah baiwar Allah rayuwa ta tana cikin hadari Ke musulma ce shiyasa nazo gareki ki taimaka min don Allah ki fitar dani dag... Keeh dakata safina ta fada a harzuke saboda ina musulma sai akace dole ni zan taimake ki muna America ne nan ba nja ba kigane haka ta karashe tareda watsa mata harara.., batai zuciya ba dai ta durkusa har kasa jikinta sai rawa yake tasan yanzu kila su fara neman ta kuma ba nisa tayi ba tunda tana cikin airport din har yanzu tasan naimanta zaiyi musu sauki, kuka take yi sosai tace ki duba girman Allah don darajar ma'aiki ki taimaka min rayuwa ta tana cikin hadari.. Karar wayar safina ce ta katse mata magani ta duba ta ga dad dinta ne,wucewa tai ba tareda ta kalli inda maryam Ke tsugune ba sai da ta fita sannan ta daga wayar dad gani nafito, dakata baby ba wannan ba wacce naji tana rokon ki taimako da fatan lafiya ko, lafiya lau dad wata ce bans an taba gaskiya, Dad yace amma dai ina fatan kin taimaka mata domin dajin alamun yar uwarki ce musulma, waro idanun tayo waje tareda yin gyatsina sannan tace dad ban taimaka mata ba gaskiya haka kawai taje wurin yan sands ko kuma ma'aikatan cikin airport din ta kai...... Kai baby yanzu zamu bata dake maza koma kije kiji ko kuma ki bata wayar ni sai inji jikinta yana bani akwai wani abu tunda najiwo muryar ta ,maza baby koma yanzu... *comments* *share* *mrs noour ce✍🏻* [7/11, 17:42] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* 🔱🔱🔱🔱🔱 Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited by👉🏻 *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sis👉🏻 *Maman Sultan*😘 بسم الله الرحمن الرحيم *gaisuwata gareku yan group din* *umm Asghar novel* *zuwairat novels* *Beenafa Hausa novels* ~Allah ya bar kyauna~😍 _ina yinki MAMAN najwa irin har abadan nan😍_ 🅿➖0⃣7⃣ Juyawa tai rai abace Kamar zatayi kuka inda ta bar maryam nan ta sameta wacce tana durkushe tana razgar kuka Kamar ranta zai fita ta gama yanke shawarar komawa wurin su hajiya ladi duk yadda rayuwa tai da ita haka Allah yaso , Keeh useless girl safina ta kirata ciki da girman kai da rashin mutunci ,da sauri maryam ta dago kanta domin ta shaida muryar nan ilai kuwa safina ta gani a tsaye gabanta , kallon wulakanci tagama kare mata sannan ta dialling number dad dinta mika ma maryam wayar tayi rike my dad wants to talk wit u ta furta tana harararta, jiki na rawa maryam ta amsa duk da atsorace take kada taje garin nneman taimako ta jefa kanta cikin taskun dayafi wanda ta Ke ciki... "Sallamu alaikum" muryar dad ta katse ta daga tunanin data akeyi, "Wa alaikum salam" ta amsa, Yarinya lfy ,taimakon me kike bukata kar ki damu da halin baby ki gayamin Insha Allah inda hali za a taimaka,,,,, shiru tai tana tunanin mai zatace ta fadi gaskiya ko kuwa tai..... Kar ki damu nima uba ne yata gatanan ita kadai take rayuwa a garin nan sai makwabta ki gayamin yadda inna cuce ki Allah zai iya barin mun yata lafiya ,ki nutsu ki gayamun Ki dauke ni tamkar uba ne,haka ya kwantar da muryar ya rinka bata baki shi duk a tunanin shi tana son guduwa ne daga wurin iyayenta tunda ya zauna a kasar yasan halin 'yaran kasar nan sai a hankali,,, aikuwa maryam ta samu kwarin gwiwa nan da nan ta sanar mai komai tana ta kuka ,yayinda safina take ga fatan zabga mata harara da tsaki , Sallati yayi yana neman tsari da mutane marasa imani irin haka,inama yana kusa da ita da saiya dauka mummunan mataki a Kansu sai dai kash nesa bata maganin kusa gashi Allah ya bashi 'ya sai godiya kawai umartan ta tayi data bawa safina wayar, tashi tayi ta je har kusa da ita ta duka ta mika mata,sai da ta ciro farin handkerchief a wandon ta sannan ta sa ta amshi wayar a wulakance cike da kyama,hands free tasaka wayar domin bazata iya karata a kunnanta ba,tace "hello dadna" In serious tune yace baby umarni nake baki ki tafi da maryam wurin ki b4.... waaaat ta fada da daga muryar dad n.... I mean it ,u had me ya bata amsa rai a bace ki wuce yanzu nan kafin kiga bacin raina now.,, ooh my gosh wlh na tsani yarinyar nan ya zakayi min haka dad kasan na tsani wani yana rabata balle

Chapter 2 of 32