fara da wando baki tree quarter ya feshe jikin shi da turare bai tsaya shafa mai ba ya duba agogon bangon dake manne a bango karfe goma da minti biyu na safe fita yai cikin sauri ya nufi cikin gidan palon kasa ba kowa don haka sai ya wuce sama dakin maryam bata nan har toilet ya yi knocking shiru,,
fitowa yayi ya nufi dakin safina duk da yasan bawani shiri tsakanin su yana budewa ya hango ta durkushe tana jera kayan cikin trolley jingina jikinsa yayi yana kallonta komai nata cikin natsuwa takeyin shi,,
karar bude kofar toilet ne tasa maryam waigowa yayinda Khalil yana ganin alamar zata waigo yai saurin maida kallon shi ga safina wacce ta fito daure da towel sai daya data yafa a kanta,,
wani abune taji ya taso tokare mata a kirji ganin kallon da Khalil yake yiwa safina wanda batasan da gayya yakeyi ba daukar da kanta tayi saboda wani irin daci taji a bakinta har zuwa makoshinta,kauda kai tayi ta cigaba da abunda takeyi,,
da sauri safina ta karaso kusa dashi tace sannu bro ya kake, gyada kai kawai tayi batareda yayi magana ba wanda yayi daidai da dagowar maryam taga yana ma safina murmushi nan take taji hawaye nason zubo mata muryar ta na rawa tace anty na gama bari in fara wankin,,
bata tsaya jin amsar ta ba ta kwashi kayan ta wuce ta gefen shi wanda har jikinta yana gogar nasa amma hakan yafi mata data tsaya yi masa maganar ya matsa kai tsaye dakinta ta wuce cikin toilet ta zuba kayan a bucket ta kunna tap sai a lokacin taji hawaye yafara tsiyaya daga idanun ta zama tai gefen Banff ta na kuka wanda ta rasa kona meye oho saida tayi ma ishi sanan ta miki ta fara wankin jin kamshin turaren sa takeyi Kamar a bayin da sauri ta dago sukai ido biyu murmushi kawai yayi ya shiga cikin bayin ya kama hannun bucket din ya sanya mata cikin hannun ta alamun ta dauka kenan rike wa tayi biyo ni kawai yace ya fita,,,
itama batareda bata lokaci ba tabi bayansa rike da bucket din fita yai daga bangaren ya zagaya baya inda wurin shakatawar gidan yake wanda maryam bata taba sanin da wurin a gidan ba bakaramin kyau wurin yai mata ba swimming poll ne an zagaye shi da flowers kala kala ga manya da kananun fitilu masu kayatarwa wata maid ya kira datake mopping din tiles din wurin nuni yai mata da bucket din hannun maryam da sauri ta karasa ta amsa,,
matsowa yai kusa da ita ya kamo hannun ta ya fara tafiya ita kuwa binshi kawai take yi Kamar wata makauniya,,
mikewa sukai sai taga wani ginin ne daban wanda yafi ainahin gidan kyau a zuciya ta tace maybe ko bangaren shi ne ,bayan dakin ya nufa da ita nan ma garden ne mai matukar kyau don shima harda pool dinshi saidai karami ne sai kujerar shan iska dake gefe zagaye dasu furanni ne kala kala masu matukar kyau,,
Zaunar da ita yai a daya daga cikin kujerun wurin shima ya zauna a wacce take fuskan tarta ya zuba mata idanun sa masu matukar kwarjini,,,
kasa tai da idanun ta tana wasa da yatsun hannun ta kirjinta sai bugawa yakeyi cikin sauri sauri,,
kusan minti ashirin shiru dukkansu sukai sai faman kallon ta yake yayinda ita kuwa tsoro ne ya gama cika ta kada yaje yayi mata wani abun domin 'ya'yan masu kudinnan sai ahankali ta sha jin labarin su kuma dama fada ce in har mace da namiji zasu kebe su biyu toh tabbas na ukun su shaidan ne nan da nan ta shiga karanto addu'oe a ranta na tsari,,
saurayinki bai San mai ake kira da rescue bane ya jefo mata tambayar
da sauri ta d'ago sukai ido hudu dashi wannan wace irin tambaya ce saurayi kuma ita dama ta gaya mai ko wani tana da saurayi ne kasa tai da kanta ganin yadda ya kafe ta da ido wanda tarasa kallon meye haka yake mata murguda baki tayi tana fadin dan miskilanci kawai ka tsare mutum batareda zaiyi maka wani abun ba domin ita burinta ya sallameta taje gurin aikin safina tasan halin ta sarai,,
murmushi ya wanda har kyawawan hakoransa suka bai yana ganin yadda taketa murguda baki da gunguni kasa kasa,,
meyasa ki kuka a toilet bayan lafiya lau kika bar dakin safina?ya kara jefo mata wata tambayar,,
mikewa tai da sauri tace ba komai ni zan wuce kaga aiki aka sani kumaa maganar ce ta tsaya mata a makoshin yayin data ga ya mike takowa tai a hankali ya iso gaban ta har tana jin saukar numfashin sa fidda dan karamin box yayi ya bude zube ne tagani mai bala'in kyau ya fiddo dashi kamo hannun ta yayi ya saka mata ya sunkuyo da fuskarshi daidai tata cikin rad'a yace wace mace kika taba gani babu zobe ki aje min gashi nan aro na baki,,
yana gama fadin haka ya juya ya wuce ya barta a tsaye Kamar wata wacce aka dasa a wurin,,
*Kano*
kira kusan biyar hajiya ladi tayiwa alhaji kafin ya dauka cikin bacci tace ina kwana yallabai an tashi lafiya,,
bai amsa ba sai tambaya daya jefo mata Yaya dai ladi kike neman damuna da safen nan ko an samu labarin maryam din ne,,
murmushi tayi irin nasu na yan duniya tace etoh kusan hakane domin kuwa kakar ta tazo dazu nan ta gaya mai yadda sukai da inna,ta dora da cewa kaga shikenan baka kashe kudin ka a banza ba yanzu saimu fanshe shi gurin kanwarta,,
dariya shima yayi yace lallai hajiya bakida dama indan Wanan ne kada ki damu sai dai ina fatan takai maryam kyau ko,,
da sauri tace kwarai kuwa alhaji kaidai sai zuwa Jibi za mu hadu ,nan sukai sallama,cikin jin dadi Allah ya amshi adduar ta dama taga samu taga rashi a gurin alhaji saboda batan maryam yanzu kuwa zata fanshe abunda yayi mata alkawari,,
kwanan inna biyu ta dawo tareda jikar ta harira wacce take 'ya ce ga danta iliya wanda tafi so da kauna haka ma ko a jikokin tafi kaunar harira wacce take yar shekara goma sha hudu kenan kyakkyawa ce itama ba laifi batada makusa saidai bazaa taba hada kyan su da maryam ba,,itama tayo gadon halin inna da danta iliya shiyasa itama tasu tazo daya da innar,,
Ummi na daki tajiyo sallamar inna sai da gabanta ya yanke ya buga nan tai kokarin fara karanto addua ta mike ta fita tsakar gidan lokacin inna tana ta kokarin bude Kofar dakin ta da sauri ummi ta karasa ta bude mata tana ta faman zuba musu sannu da hanya,,
koda ta bude baya ta matsa saida innar tayi yan tofa tofen ta a Kofar dakin sanan tai bismillah da karfi ta shiga tana cewa harira kiyi bismillah saboda tsaro don bansan mai zamu tarar ba tunda kullum kana dai Zaune ne da mutum amma bakasan meye a zuciyar shi ba,,
ita dai inna shiru tai bata tanka ba don inda Sabo ta saba komawa tai ta dauki Kofi ta debo musu ruwa ta kawo har gaban inna ta durkusa kasa ta gaida ta da tambayar mutanen gida
*kuyi hakuri da wannan bana jin dadi ne pls*π
*share*
*mrs noour ce*βπ»
[7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *π΄π΄KARFIN IKOπ΄π΄*
π±π±π±π±π±
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
*HIKMAAH writers association*
Edited byππ» *oum Zahara*π
Dedicated 2my lil sisππ» *Maman Sultan*π
Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
~*ina mai Baku hakuri Masoya da jina shiru da kukayi matsalar waya ce amma yanzu zamu cigaba Insha Allah without any matsala har saina kammala ina fatan haka, naka sakon nin Ku da masu kira na gode ana tareπ€π»always*~πππ
*_sakon gaisuwa ta gareku kuma_*
*momy paki*
*mum Khady*
*Maryam T baliya*
*karfin IKO fans novel*β€
*mrs noour Hausa novels*β€
*oum Asghar novels*β€
*da dukkan Masoya na ina muku fatan alkahiri Allah ya bar kauna*ππ
π
Ώβ1β£8β£
Gaida inna tayi da tambayar mutanen gida,lafiya lau suke ta bata amsa ba yabo ba fallasa,,
Ganin datayi harira batada niyyar gaida ta yasa tace nikuwa Kamar harira nake gani ko tana kallon hariran,,
kauda fuska tayi tana gyatsina tace nice sannu,,
Yawwa sannu ya mamar taki suna nan lafiya,,
kafin harira tai magana inna cikin fusata tace lafiya Kedai har kullum mugun halin ki bazai ragu ba kullum sai dai yayi gaba yo bacin haka taya wanda ya kwaso tafiya zaki tasa shi gaba kina mai surutai marasa amfani ko kuwa abincin ma na gidan dana saidai in roka,,
da sauri ummi ta mike tana cewa kiyi hakuri inna na dauka ko sai kunyi sallar ne cikin ta nufa harta zuba ta kawo gabansu ta aje inna na zuba ruwan jaraba,,
Ficewa tayi daga dakin tana fadin Allah ya kyauta amma wlh komai zai faru sai dai yafaru amma yata dole insan halin datake ciki a yau zuwa gobe dole inji muryar ta hakuri na yakare haka bazan bi cikar mutum ba insaba ma mahallici na ba tunda baganin kawai cin kikeyi ba,,
Koda suka gama cin abincin ko hutawa basuyi ba inna ta tasa harira gaba zuwa gidan hajiya ladi yayinda ummi na daki tana jin fitar su ajiyar zuciya tayi tace ayidai mugani in tusa zata hura wuta,,,
*US*
ta dade tsaye tana mamakin Khalil tana shakar kamshi turaren shi duk da ya bar wajen amma kamshin nanan Kamar anyi barin turaren a wurin,, ajiyar zuciya ta sauke ta koma kan kujerar ta zauna lumshe manyan idanun ta tayi takai hannunta kan hancinta tana shakar kamshin zube,,
ya Allah ta furta a hankali wani irin son shi taji yana ratsa ta ta kowanne bargo da tsokar jinin jikinta,,,
ta dade Zaune a gurin tana tunani kafin ta mike cike da farin ciki take tafiya wanda ta kasa boyuwa a fuskar ta saboda lallausan murmushin dake fuskar ta,,
dai dai garden din gidan ta hangi Khalil da safina suna Zaune kan kujerun shan iskar dake wurin,damm taji kirjinta ya buga wani irin kishi taji ya tirnike mata zuciya ji take Kamar an daura mata dutsen dala a kirjinta,idanunta suka kawo ruwa duk da batasan mai sukeyi ba kodai hirar soyayya suke ne da sauri ta shiga girgiza kai komawa tayi gefe ta rakube cikin flowers tana kuka maiya sameni ne nake kokarin manta matsayi na da chusa kaina a inda banida yancin yin hakan bayan safina tana da burin auren ka ta kuma gargadeni kai koda kuwa batai min warning ba yaci inma kaina domin banda wannan matsayin dago kai tayi takara kallon su,,,
safina sai faman murmushi take gani tayi ta tashi ta zagayo kusa dashi ta sunkuyar da kanta dai dai nashi,,,
da sauri ta kauda idon ta sakamakon jin datayi zuciyar ta zata buga kuka ne ya kwace mata tai saurin rufe bakin ta da hannunta,,
mayaudari kawai macuci dama ba sona yake ba shima safina yake so,,,
kuka takeyi sosai ta dade a wurin kafin ta tashi taje gurin tap ta wanke fuskarta ta nufi cikin gidan don sun riga da sun bar wurin,,
ta Kofar baya ta bi wacce ta Ke ta mike har zuwa kitchen har Palo,, don gujewa haduwa da kgalil, sai dai tayi rashin saa tana shiga mommyn ta hango ta ta kirawo ta suna Zaune a palon gaba dayan su,,
tafiya takeyi a nurse cikin hankali kanta a kasa saidai bugun zuciyarta daketa karuwa cikin sauri karasowa tai gefen mommyn ta zauna a kasa ta gaida mommyn da daddyn wanda sai yanzu ya ganta gani take Kamar yasan ta a wani wuri,,amsawa yayi dauke da murmushi kan fuskarshi ,,
mommyn tace wai ni maryam ina kayan da aka siyo miki ne kike ta fama da kayan nan ne,,
dagowa tai cikin mamaki tace mommyn wane kaya kuma,, Aa kayan da safina ta siyo miki mana ko basuyi miki bane mommyn ta kara tambayar ta,,
Dagowa tayi ta kai kallon ta ga safina wacce take ta faman aikin nata na kallon banza da harara,,
ita sai yanzu ta tuna da anfita siyo kaya domin ita harga Allah ta ma manta da wasu batun kaya daaka siyo toh koda ta tuna ina Wacece da zata tambaya ina yake Kamar da kudinta aka siyo,,,sadda kanta kasa kawai tayi batareda tace komai ba,,,
Juyawa mommyn tayi ga safina wacce take ta danne danne a wayarta Kamar bataji abunda akeyi ba,,
ina kayan maryam da kuka siyo kukuwa baa siyo bane mommyn ta tambayi safina,,,
A harzuke ta kai kallon ta ga maryam tace an siyo mana ita din wacece dani zan kawo mata ta watsa ma maryam harara wai mommyn mai ta dauki yarinyar nan ne komai ita ta fada a zuciyar ta mtssssw ta ja tsaki ta mike ta nufi sama kowa ya bita da kallo banda Khalil wanda ya Ke kwace kusa da daddyn ya lumshe idanunsa Kamar mai bacci,,
two mins sai gata ta dawo dauke da ledojin a hannun ta watso ma maryam su tayi a jikinta ta koma ta zauna tana jijjiga jiki Kamar zatayi damve,,
Allah ya shirye ki mommyn tace cikin bacin rai maida kallon ta tayiga maryam cikin kwantar da muryar tace bude kingani insunyi miki ,in basuyi ba dole kuwa zakije ki zaba da kanki,,
cikin natsuwa ta fara bude ledojin ta farko dogayen rigunan ne aciki duka basuyi ma mommyn kyau ba haka maryam ta bude kayan duka mommyn ta daddaga su cikin bacin rai tace son tana kallon shi,,
bude ido yayi a hankali yace mommyn na ,,,
pls inaso ka shirya kuje da maryam ta zabi abunda take so don ni gaba daya kayan nan basuyi min ba,,,
Kafin yace wani abu safina tai charaf tace mommyn duk ga drivers nan bayan kinsan zan koma makaranta ta fada cikin gunar rai Kamar zatai kuka maiyasa mommyn keson bata mata shirin ta ne ita da take son su tsaida maganar soyayya su kafin ta wuce,,,
kallonta kawai mommyn keyi cikeda mamaki lallai yarinyar nan tayi nisa a rashin kunya itama daure fuska tayi tace saboda haka nace and he will do exactly as I said beside Ke mai zai hanaki bin driver tunda Ke ba bakuwa garin bace,,
mikewa tai ta nufi sama tana kuka mommyn ta yi mata fada akan maryam lallai zata dauki mummunan mataki akan yarinyar nan,mai ake da taimako musamman ma na talaka ka dauko mutum a rana ya maida ka inuwa kallon kanta takeyi kan mudubi mai maryam tafini ne eyeeh wanda har kowa ya damu da ita haka ne wayar ta ta dauko ta dannan kiran mommyn,,,
*Kaduna*
Alhaji isma'il ii ne sanye cikin shadda fara kal wace aka yiwa dinki yar ciki da baban riga yana hakimce a bayan mota mom na kusa dashi itama tasha ado cikin lallausan leshi fari wanda akayi wa ado da zanen green kananan sunyi matukar kyau a gaban gefen driver Habib ne shima sanye yake cikin wani yadi sky blue mai tsada gaske wanda dad din ya bashi dinkin zamani akayi wa yadin sai yayi matukar yin kyau fuskar sa sanye da eye glass fari,, driver ya ja suka dauki hanyar garin Bauchi su domin amsa kiran malam,,
suna ta hira hankali kwace yayinda mom taki sakewa Habib fuska ko magana aka sako ta sai ta share dad yana lura da ita tunda yayi maganar Habib da safina mom ta dauki abun da zafi take nuna halin ko inkula ga Habib din wanda da ba haka yakeba,,
sai misalin karfe uku na rana suka isa Kofar gidan malam motar ta paker suka fito babban gidana wanda an gyarashi ya hadu ta ciki duk da dad yaso a rushe gidan a asake Sabo amma malam ya hana yace shi Sam ba duniyar yazo zama ba mai ya rage mai da kyar ya tadda akayi gyare gyare a cikin gidan amma duk da haka gidan ya fita daban da na sauran yan layi ,,,
kannen dad dinne maza dake Kofar gidan suka taso suka tarbo su cikin murna har zauren gidan inda malam Ke Zaune kafafunsa tankwashe yana karatun alqur'an wuri suka nema suka zauna saida yakai karshen aya sannan ya rufe ya d'ago yana dubansu fuskanshi dauke da murmushi da sauri dad ya fara mai sannu malam ya gaishe shi haka Habib sai mom ta amsa cike da farin ciki yace wa mom ta shiga ciki ta miki ta wuce yayinda Habib yace bari shirma ya shiga ciki su gaisa ya miki ya wuce malam ya maido da dubanshi ga dad wanda ya Dada matsowa kusa da malam din sosai suka kara gaisawa malam yace ina ja'irar jikar tawan sarki boko injin ko ta koma ne,,,
wlh malam ta koma kasan tana kokarin zana harabawa ne shiyasa bata samu zuwa nan dinba,,
murmushi malam yayi irin nasu na manya yace muda take mana tsiya inta zo ai gwara tai zaman ta cikin wasa irin na kaka da jika ya fada wanda dad din yasan ba wasan bane tunda bata kaunar zuwa bauchin yayi mata kauye ita bazata iya zama ba har ta kwana tun tana karamar ta haka yake fama bata taba zuwa gidan Hutu ba sai dai kafar shi kafar ta,,
dubansu malam tayi takira sunan sa cikin muryar wanda take nuni da magana mai muhimmanci yake son suyi,,,
shima dad din kara dukar da kai yayi cikin girmamawa ya amsa da naam malam,,
Sai da yayi gyaran muryar yace akan maganar yarinyar nan ce safina ganin maganar waya bazata yiyu ba shiyasa na kira ka nan ban yarda da cigaban karatun ta kasar waje ba face da auren ta in kuma karatun ne tasa a gaba to kuwa yazama lallai ta dawo gabanka tayi karatun anan amma fa lalli umarni nake baka bazata cigaba da karatun jami'a a kasar waje ba,,
ajiyar zuciya dad yayi daman yasan maganar kenan da malam zai yimai don dama ko lokacin dasuka barta a chan ba karamin fushi malam din ya nuna musu ba,
dagowa yai yace Insha Allah malam yadda kace haka zaayi,,
inbanda ja'irar yarinya ce ga yayan ta nan habibu da ba sai a hada su aure ba domin ina jiyewa abinda ka iya duwa ya dawo in har tanemi wanda yake irinta toh ina mai tabbatar muku a lokacin zakuyi nadamar gatan da kuke nuna mata,,,
da sauri Habib ya ja baya wanda yake kokarin fitowa daga cikin gidan waye malam yake nufi?
ni Habib din ko kuwa wani?
yake tambayar kansa cikin zuciyar shi,,,
dad yace wlh malam nima ina wannan tunanin saboda shi tasan halinta zai ita hakuri da ita a matsayin ta na yar uwar shi toh amma kuma sai dai tazo min da maganar Khalil nan daddy ya gaya misi komai game da safinan ,,
malam yace toh Alhamdulillah indai har sun shirya din shikenan babu laifi amma fa ni yaron nan Habibu yafi kwanta mun arai bana muku baki amma sangarcin safina zai kawo mata matsala babba a zaman auren ta matukar bata gyara halin ta ba,Allah ya shiryar da ita yayi muku albarka gaba dayan Ku ,,
dad ya amsa da ameen bari inshiga mu gaisa DA inna dad ya miki,,
da sauri Habib ya dai daita natsuwar shi ya fito shima yace malam zan karasa gurin inna,,,
toh toh madalla ka gaida min da ita,,malam ta amsa,,
Habib yace toh zasuji sai na dawo anjima,ya fice cikin rashi natsuwa,,
Haka ya shiga gida jiki salube da Sallamu ya shiga Hauwa na tsakar gidan da gudu ta kwaso ta rungume shi tana oyoyo inna tace ta fito itama cikin farin ciki tana cewa lale da sojojin yaki dariya sukai duka suka shiga ciki yana zauna kan dan gadon dake dakin tana furta wassh inna nagaji, Hauwa ce ta debo masa ruwa ta kawo mai ya amsa yasha suka gaisa da inna tana tambaye su alhaji yace tare muke yace yananan zuwa anjima Ku gaisa,
tace toh babu damuwa Allah ya kawo shi lafiya ya yar tawa ince ko tare duk kuka zo,,
nan da nan fuskar sa ta sauya wanda har inna ta lura da hakan yace Aa ta koma makaranta da hajiyar dai mukazo ,nan ya ci abinci suna taba hira duk da maganar malam tana damun shi,,
Koda alhaji yazo maganar dai daya ce dai ta aure alhaji yace ta kwantar da hankalin ta Insha Allah zaiyi amma ta cigaba da yiwa Habib din addua Allah ya kawo ta gari ,,
haka Habib sukai kwana biyu suka dawo duk baya cikin natsuwar shi fatan shi daya ne kada wannan maganar ta tambbata domin bazai taba iya zama da safina ba,,
*US*
maryam ce sanya da arebain gown milk color wance akayi wa ado da duwatsu jajaye tayi rolling kanta da gyalen rigar tayi matukar kyau wanda mommyn tasa ta dole tayi kwalliya dukda powder ce da kwalli sai wet lip amma tayi kyau sosai tana Zaune bayan mota ta dukar da kanta kasa tana wasa da zoben da Khalil ya sanya mata yayinda safina Ke gaban itama sanye cikin wando jeans black da too green mai dogon hannu ta yafa gyalen a kanta sai iyayi takeyi duk da yadda ta hango maryam tayi wani irin kyau kayan sun fito mata da sirri kyau nata ,,Khalil na gaba wanda yake ta cin magani tin rabuwar su a garden bai sake yi mata magana ba da alama miskilanci nashi ya motsa kenan,,,
*mrs noour ce*βπ»ππππππππ
[7/11, 17:43] +234 816 822 9024: *π΄π΄KARFIN IKOπ΄π΄*
π±π±π±π±π±
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
*HIKMAAH writers association*
Edited byππ» *oum Zahara*π
Dedicated 2my lil sisππ» *Maman Sultan*π
Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*Oum zahra Besty na ina matukar kaunar ki kema Allah ya barmu tare*π
*~my dear ukty MAMAN sultan I really heart u dear Allah ya kara hade kanmu(ameen)*π
π
Ώβ1β£9β£
suna tafe safina nata naman samun shiga shikuwa gaba daya hankalinsa yana gurin maryam wacce ta takure a baya,,
har suka isa railway station saanan ta dago kanta sakamakon kiran da safina tai mata ki fito ki kwashe min bags dinna,,
safina ta fada ciki da gadara tana mata kallon raini Kamar taga kashi,,
Fitowa maryam tayi ta bude boot din ta dauko travelling bags din guda biyu ta soma ja da kyar Kamar zata fadi saboda nauyi,,,
Juyowa tai da niyyar yi mai magana sai taji yace Allah ya ki yaye sai anjima fuskar nan tashi babu alamun rahma da sauki dole haka ta ja kafarta ta sauka cikin yanga da son jan hankali tace ya Khalil na amsa number ka wurin mommyn zamu rinka gaisawa,,
gyada kai kawai yayi domin yana jin zafin abunda take yiwa maryam amma yana daure wa ne kawai saboda shi ana shi tunanin Kamar kusan halin shi daya ne da safina ta wani bangaren yana so maryam ta saba kuma da alamun tana sabawa domin yana lura da ita yanzu ba komai safina keyi mata ba yasa ta zubar da hawaye,,,,
wucewa tai gwiwa salube ta bi bayan maryam wacce ba wani nisa tayi ba saboda nauyin jakar datake jaa,,
Wuceta tayi ta siya ticket sai da takai har wurin shiga sannan ta amsa jakar tace Keeh magana zan miki wacce zata amfane ki idan kin yi amfani da ita sabanin haka kuwa barazana ne ga rayuwar ki data uwar taki gaba daya ta fada cikin kausasa muryar ,,,
abunda nakeso dake ki fita harkar Khalil ya riga da yayi miki nisa, ki gane kedin ba kowa bace face talaka kaskantacciya marar galihu kidaina kokarin hada hanya dani domin zanyi komai domin Khalil don haka ki tsaya matsa yinki na yar tsuntuwa,,
a sanyaye maryam tace naji anty amma wlh babu komai tsakanin mu da ya khal...
yehyeh safina ta katseta tana daga hannu saman cikin bacin rai dakata Keeh useless girl nasan komai game da halin Ku na karuwai shiyasa nake ryimki gargadi bawai don tsoro ba kinsan na riga da nafi karfin yin takara tareda Ke ,,ki wuce ki bani guri,,
juyawa maryam tai tana kokarin maida hawayen dake kokarin zuba mata wannan cin mutunci da cin fuska yana dayawa Allah yasa ma
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 32