Share this page
fadr haka ya sauke wayar tareda duban inda suke yace zanyi baki pls Kubani wuri yanzu sannan maganar bata mata rai dakikayi inkinso ki maidata ciki karewar so da nuna kulawa,, Mikewa mom tayi rai bace rike da kafadar safina suka fice dai dai step suka hadu da Habib yana kokarin haurawa wurin dad kallon banza su duka suka jefeshi dadhi yayinda ya dauke Kansas kamar bai ganiba yayiwa mom sannu batareda yajira amsar taba ya wuce ,, Dogon tsaki safina taja yayainda mom tayi kwafa taja safina zuwa dakin ta ,,, *mrs noour ce*โœ๐Ÿป๐Ÿ˜˜ [7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *๐Ÿด๐ŸดKARFIN IKO๐Ÿด๐Ÿด* ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited by๐Ÿ‘‰๐Ÿป *oum Zahara*๐Ÿ˜ Dedicated 2my lil sis๐Ÿ‘‰๐Ÿป *Maman Sultan*๐Ÿ˜˜ ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู… *ina godiya ga nuna kaunar Ku gareni Allah yabar zumunci,bazan manta da adduoe nku ga kanwata ba Allah yasa mu gama da duniya lafiya,Allah ka hada mu a jannatul Firdausi*๐Ÿคฒ๐Ÿป *~JUMM'AT KAREEM~* ๐Ÿ…ฟโž–4โƒฃ1โƒฃ Gefen gado ta zaunar da ita ta shiga rarrashinta tana nuna mata alfanon auren musamman yadda yanzu ya Khalil ya dada kama kasa yanzu haka hada hadar bude wani sabon company yake Wanda yake zai kasance na hadin gwiwa ne tareda wasu turawa,, Ajiyar zuciya safina ta sauki tace mom wallahi duek wadannan abubuwan nake dubawa da tuni na rabu da shege tunda har yanzu bana cikin zuciyar shi kince damun dawo zakisan abunyi gashi har yanzu shiru haka zanje yayita wulakantani gashi dan illimin dazanyi tutiya dashi kuna neman hanani,,ta karsshe tana matsar kwalla,, Murmushi mom tayi tace ki kqantar da hankali ki anjima idan an kawo kayan lefe hajiya karima zata zo batun makarantar kuwa saidai kiyi hakuri banda abunki inda arziki meye baya sawa da hanawa dole ki hakura muddin munason cin ribar daura auren nan,, Hakanan ta furta shikenan bawai don zuciyarta ta aminta ba don batajin zata iya hakura da karatunta ta tsaya matakin secondary ina bazai yuwuba wallahi ta furta a zuciyar ta amma a zahiri mikewa tayi tace mom bari na shirya inje gurin auntyn miemie din(wacce take mata gyara ne na aure) Cikin jin dadi mom tace da kinvkyauta kuwa,, Ba ita tasamu kantaba sai wajen karfe uku na yamma tun safe take tikar uban aiki dukda maaikantan dake cike da gidan amma mom tace ita zatayiwa baki yan kawo akwati abinci da drinks dama tun jiya ta yi sanacks kala kala,, Kai tsaye toilet ta fada ta sakarwa kanta shawa tareda dauro alwala ta fito,sallar ta fara gabatarwa wacce ta kufce mata tana istigfari na neman yafiya ga ubangiji saanan ta mike ta isa drawer atamapa ta dauko blue mai ratsi ja da yellow a jiki dinkin doguwar rigace mai biden kasa ta saka tayi matukar karvar jikinta ta feshe jikinta da turaruka cikin Wanda ya Khalil Ke kawo mata batareda bata lokaci ba ta fada gado ta kwanta nan take bacci yayi gaba da ita,, Hayaniyar ta dinga jiyowa Wanda yasata bude shanyayun idanuwanta a hankali Waro su tayi tareda mikewa zaune babu shiri ya Khalil ta furta yana tsaye sanye da shadda maroon color wacce tasha aikin hannu tayi matukae karbar jikinta yana tsaye jingine da kofa yana ta doka mata murmushi nan nasa mai mayukar kayi da tsada da sauri ta sauko da kafafuwanta kasa ta diro gaban sa jikinta nadan rawa take dadin ya Khalil mai kakeyi anan pls ka fita kafin wani ya ganka kafin ta rufe baki ta jiyo muryoyin su safina na kokarin haurowa sama da gudu ta jiyo ta fada taoilet tareda danna sakata jikinta sai rawa yake yi adduoe take kar Allah yasa safina ta tarad da ya Khalil a dakin,, Jin shiru hwr tsahon minti goma yasata sakin ajiyar zuciya a hankali tana hamdalla,, Wanko fuskar ta kawai tayi ta futo ta kimtsa kanta saboda zuwan period dinta kasa ta nufa da sauri tasan yanzu yan kawo kayan sin tafi,, Turus taja ta tsaya yayinda taji meena na sakin guda mai kafi nan take kibiyar kishi ta soki kirjinta kasa daga kafarta tayi taja ta tsaya daganan gaba daya duniyar taji kamar an daura mata akan kirjita duk yadda take tunanin bazata damuba amma ina abin saitaga ya wuce haka domin kukane Ke kokarin kufce mata da sauri tabi ta bayan manyan kujerun dake palon tafice chan karsgen garden din gidan ta nufa cikin flowers din dake zagaye da katangar gidan ta boye kanta ta saki kuka mai cin rai babu abunda idanunwan ta Ke hango mata banda tarin uban akwatian dake parlon ita ba akwatin yake damunta ba zuciyar ta ce ta karaya da shikenan ta rasa ya Khalil duk yadda yake kokarin kwantar mata da hankali Ashe duk dadin baki ne tunda gashi hardashi akazo kawo kayan auren ma,, Kamshin turarensa take ji kamar a jikinta da sauri ta dago da idanunwa wadabda suka rine saboda kuka ido hudu sukayi dashi fuskar sa ahade babu alamun walwala ko farin ciki,, Maida kanta kasa tayi domin bata son ganin fuskar sa,,tsugunwa yayi gabanta tareda kama haba ya zuba mata idanuwa, sosai yakejin kukan nata har cikin ranshi shi kanshi yasan dole hakan zata kasance shiyasa ya kafe wa mommyn saiyazo,, ajiyar zuciya ya sauke mai karfi hannusa ya sa ya dago da fuskar ta wacce hawaye ya shiketa sharkaf lumshe mata idanu yayi tareda karyar da kansa gefe alamun tayi shiru,, Kauda kanta tayi daga barin kallon sa batason maganganin sa suyi tasiri a jikinta batason kalamansa suyi tasiri ga zuciyar ta batson sakonsa yayi tasiri ga idanunwanta gwara ta fawwalawa Allah lamarin ta ta hakura dashi kawai har abada,, Mikewa tayi batareda tace komai ba ta wuce shi yayinda shi kuma ya bita da idanu sosai yake tausayawa lamarunsu amma babu wani Abu dazaiyi Wanda ya wuce addua kuma kullum cikin yinta yake yana kuma ganin amfaninta domin kuwa akoda yaushe wutar kauna da soyayyar ta karuwa takeyi cikin ruhinsa da gangan jikinsa,, Mikewa yayi jiki babu kwari yana amsa wayar momy,, *misra* Sosai yan uwa sunyi murnar ganin mijin shatu Wanda suke ganin karfin addua ce dasuka sanya yi agaba ba dare ba rana,, Abban maryam yaso su taho gida Nigeria saboda Neman maryam amma ummi take tace suyi hakuri kawai su cigaba da addua Allah ya tsareta a duk inda take amma subari suyi aikin hajj sai sutafi gaba daya,, Dole haka abba ya hakuri din vayason abunda zai bata ran ummi a yanzu kuma yayi alkawarin daina tilasata akan abunda batayi niyya ba gudun haihuwar da marwr ido,, dukda ummi itama dairiya kawai takeyi amma gaba daya zuciyar ta tana ga son ganin UAR tata maryam,, Sun koma zaman auren su lafiya sosai yake ririta ta kamar sabuwar amarya Allah yasa yayi dace da matar sa hafsat batada damuwa tana amfani da illimin ta yadda ya kamata ta nuna kawaici sukayi zaman su lafiya har iyayenta saida sukazo har masar sukayi abban maryam murnar ganin matarsa da fatan ganin yarsa kuma,, Ba karamin bacin rai ya shiga ba da tsannin mamakin hali irin na inna yayar mahaifiyar sa uwa daya uba daya ta ringa nuna masa kiyayya irin haka mai muni,, Shima ya gaya mata abunda ya faru bayan rabuwar su,, Sunyi aikin hajji lafiya zuwa jibi suke saka ran komawa gida Nigeria,, *Kano* Izuwa wannan lokacin inna ta gama galabaita da ciwo Wanda yaki ci yaki cinyewa kullum kara tsananta yake a koda yaushe cikin Neman gafara Allah take da mutane wadanda ta zalunta gashi harira tunda ta sanya kafa ta gudu bata kara ganin taba yan uwa duk sun gujeta yaynta ma daurewa kawai sukeyi wurin bata abinci Wanda sakyar take iya kaishi bakinta,, Ga illiya kuwa tunda yasa mu hannun sa ya fita daga Wuhan inna yayi asubancin cikin dare yabar garin har yau bai kara waiwayar Suva sai yau,, Cikin dare inna na kwace cikin zafin ciwo tayi kukan tayi nadamar yadda ta bata rayuwar ta a banza ga yadda sakamakon ta ya kasance tana tsaka da wannan kukan daya zame mata jiki ta rinka jiyo motsi kasa kunne tayi tana sauraro tareda tunanin waye wannan kuma tasan babu mai kasadar shigowa inda take inba yayen taba suma kan dole ne inzasu bata abinci ko magani,, *mrs noour*โœ๐Ÿป *๐Ÿด๐ŸดKARFIN IKO๐Ÿด๐Ÿด* ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited by๐Ÿ‘‰๐Ÿป *oum Zahara*๐Ÿ˜ Dedicated 2my lil sis๐Ÿ‘‰๐Ÿป *Maman Sultan*๐Ÿ˜˜ ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู… *masu korafin ummi ta Dade a hospital kuyi hakuri dolece tasa hakan abunda nakeso Ku gane ummi fa faduwa tayi kasa sakamakon jin mummunan zance paralyzed a abun wasa bane kuma shi taso yasamu ummi,,* ~Mrs noour loves u all๐Ÿ˜˜~ ๐Ÿ…ฟโž–4โƒฃ2โƒฃ Kai tsaye a nijar suka sauka domin kememe didde taki yadda su wuce Kano tace sai gida nijarโ˜บ Sun Sabo tarba sosai ko ina daga yan uwa sai zuwa sukeyi ganin shatu da yanzu ta zama ummi sosai yan uwa sunyi farin cikin ganita kowa sai nan nan yake da ita,, Ita kuwa sai kuka koyaushe inta ganta cikin yan uwa tana tuna maryam ko awane hali take oho Allah kadai yasan daidai shiyasa taso su wuce Kano kai tsaye,, Sosai yan uwa da baffa suka mike tsaye wurin yin addua ga maryam ba dare babu rana Allah ya tsare ta duk Inda take ya bayyanar da uta cikin koshin lafiyar ta,, Kwanan su hudu suka yi shirin tafiya kano,, sai gamma Li's suka iso cikin kauyen saye cikin da kewar garin abba yake bin ko ina da kallo babu wani sauyi da aka samu sosai a garin,, Sanye suke cikin shiga ta alfarma suna hakimce a bayan mota driver na Jan motar har kofar gida su inna ta tsaya suka bude suka fito gari ya fara duhu saboda shigowar magrib ba kowa ne ya nae abba ba balle kuma ummi kai tsaye cikin gidan suka nufa inda tun shigowar su suke jiyo kukan inna sosai jikin su yayi danyi dukkan su saida kirjinsu yabuga mamakin jiyo kukan inna suke yi ba komai ne yake daga hankalinta ba balle takaita ga zubda hawaye hartayi kuka mai sauti irin haka ba,, Sallama sukayi su karasa cikin gidan kai tsaye sashen innaer suka nufa sai dai tun kafin su karasa wani irin mugun doyi ya bugi hancin su Wanda har saida hartar cikinsu ta kada da sauri su ka kalli juna cikin mamakin,, Abba ne yafara yin gama amma saiyaja ya tsaya ganin baban garbati tsaye bakin kofar inna ya rufe hancin sa da babban zani,, fada take yiwa inna sosai yayinda ita kuma Ke rokar sa Allah maaiki ya tausaya mata ya kwana tare da ita illiya nason kashe ta,, ganin abun baba dauki yasa abba yiwa ummi nuni da kai alamar ta taho su jiga tare sukai karasa suna sake maimata sallmar cikin sanyin jiki,, Da sauri baban garbati ya juyo yana zare idanu waje cikin mamakin lafiya maiyakawo wadanda yan birni haka cikin gidan su ,, hannu abba ya muka mai sukayi musabaha Yaya baka gane niba audu ne,audun inna, Waro idanu ya karayi waje cike da tsananin mamaki yace audu audun inna dama kana raye Kaine rungume shi yayai cike da tsantsar farin ciki nan take hawayen farin ciki ya shiga zirarowa daga idanuwansu,, Inna kuwa kuka ta fashe dashi da karfi tana fadin hamdu lillah Allah nayi maka godiya zuciyar ta na karfafata akan ummi zata yafe mata musamman idan taga yadda sharrin ta yakoma mata,๐Ÿค” Zare jikinsa yayi tareda tambayar ina inna Yaya,, Dukar da kansa yayi cike da damuwa yayi masa nuni da cikin dakin,Wanda kafin yakai ga daga kafa yajiyo muryar ta tana fadin gani nan audu ka daure ka kara so don Allah ka yafe min ta fadi tana kuka mai cike da tsantsar nadama,, Hannun ummi ya riko suka shiga kuka sosai inna keyi tana neman yafeyarsu dama hausawa sunce inzaka gina ramin mugunta ka gina shi dai dai kanka yau gashi tagani imba zama dasukayi da ummi tun tana yarinya ba da ko Qur'an aka dafa mata bazata taba yadda ita dince ba,, Audu kam yayi kuka kasa maganar sukayi baki dayansu ummi najin zafin abunda suka kullawa maryam gashi babu wani gamsasshin bayani daya nuna sunsan inda take mikewa kawai ummi tayi ta fita saboda kukan daya kufce mata mai karfi,, yayinda abba ya hadu mai biyu ga zafin rashin yarsa ga kashe masa uwa datayi,, Shikuwa mai zaiyiwa inna a rayuwa mai yayi mata haka irin wannan mugun nufi haka muryarsa a raunane yace babu komai inna mun yafe miki yana gama fadar haka ya mike ya nufi kofar fita,, ganin haka yasata kiransa da sauri tsayawa yayi chak batareda ya juyo ba domin harga Allah baya kaunar kallon kwayar idanun ta ,, Cikin muryar kuka tace don Allah ka roki shatu tayi min gafara ta yafe min,, babu komai inna shatu ma ta yafe miki Allah ya yafe mana baki daya yasa kai ya fice,, anan cikin gidan ya tadda ummi sai aikin kuka take matan gidan sunata kokarin bata baki,,zama yayi shima tareda tambayar abunda ya samu inna,, aikuwa nan take suka warware mai duk abunda suka sani nagame da ciwon nata yanzu ma haka roko take akan wani ya kwana da ita saboda sau biyu kenan illiya na kokarin karasa ta Allah bai bashi SAA ba ana ganinsa,,shi kuma baban garbati yace Sam babu Wanda zai kwana cikin dakin kar wani ciwo ya kama mutum saboda war in dake fita jikinta,, Mikewa ummi tayi tana yi musu saida safe ta fice daga gidan, Shima ganin haka yasa abban binta duk yadda yaso ya shawo kanta ki tayi tace Sam bazai kwana tareda inna ba wallahi shiyasa ta mike ta fice daga gidan tun wuri kafin yayi alkawarin kwanan,, dole babu yadda zaiyi ya hakuri yayi sallama da yan gidan akan gobe zasu dawo,, domin yayi alkawarin babu wani Abu dazai karayin kuskuren yadda ya yi yabata mata rai,, Sosai jikinta Ke rawa takasa koda motsi saboda tsoro ga ciwo duk a zaton ta aljanun data saba gani ne yau ma suka dawo amma ga mamakin ta zuwa jimawa kadan saiga illiga a gabanta fuskar sa lullebe yana karasowa gabanta ya cire mayafin daya rufe fuskar sa sosai ta tsorata ganin yanayin fuskar sa,, Cikin kausashiyar murya yace na gayamiki dama zan dawo inna kuma dawowata bazatayi miki kyau ba yana fadin haka yana tunkarota gadan gadan da sharbiyar wukar sa,, Babu inda baya rawa jikinta dukda ta dade tana adduar Allah ya dauki ranta musamman data samu damar rokar ummi gafara amma kuma mutuwa ba wasa ba,,baki na kyarma ta shiga fadin illiya kayi min rai karka manta ni din mahaifiyar kace,, Dariya ya bushe da ita yace Ke kikasan wannan kin aikata mummunan laifin daya take Wanda nayi,, Katse shi da fadin amma yanzu wannan Abu daya faru gareni har ga kai bazai zamo mana znah ba,, Kya karasa bayanin a lahira da sauri ya daga wukar ya farde ta bisa wuyan ta saida yaga ta daina numfashi saannan ya juya cikin sauri ya fice daga dakin,, Saidai yana fita sukai karo da garbati Wanda kallo daya yayi masa jikinsa yabashi babu lafiya musamman ma dayasan kawun nasa illiya an koreshi daga kauyen nasu,, da sauri ya nufi dakin inna yana haska yar tocilan dinsa aikuwa nan yayi ido biyu da gawarta yashe a kasa jini na malala kasa nan take ya fasa ihu yana kururuwar neman taimako,, Kan kace meye mutane gida gaba daya kowa ya fito a gigice kowa yayi arba da ita sai sallati da sallami,, Iya nema sun nemi illiya amma ina yariga da falle yabar kyauyen dama tareda layar sa yake,, Sosai zance ya bugi abba yaso taimaka ma inna iya karfinsa Ashe Allah bazai nufa ba yayinda ummi koa jikinta saidai tausayin bawa kawai saboda karbar hukuncin kabari tuna wannan ne yasata yafewa inna,, Nan aka daure akayi mata wanka tareda sallah aka kaita gidan ta na gaskiya(saimuce inna masu irin halinki Allah yabasu ikon gyarawa ummi data baro a asibiti gudun dawainiya da ita saigashi ita ce tafara mutuwa batareda tayi tunanin ba tana tsaka da shuka mugun nufi,Allah masa mu gama da duniya lafiya ka tare mana imanin nu *ameen*) Sai bayan sadakar bakawi sukayi niyyar tafiya Kano wurin hajiya ladi,, *************** Babu irin shege shegen malaman da mom batayi ba Abu ya ci tura ya Khalil ya kafe kan bakansa babu karatu babu aikin gidansa,, Ba karamin tashin hankali safina ta shiga ba ita dakeson iko da daukaka da kuma mulki taya zata taka duk Wanda takeso musamman yadda kawayenta dasukayi karatu tare sukai ta zugata ta bada mata haka zata zauna babu class secondary level sai dai haihuwa nan da gud four years kin tashi aiki kuma abune mai sauki ya nemo miki mai illimin ya aura,,sosai maganar Ke daga mata hankali,, Shirye shirye sosai ya kankama daga kowanne bangaren sosai mom Ke Gyara yarta ta yar gata soyayya babu kasar da basu zaga ba komai sai sun fitar dashi daban sosai dad ya saki kudi sosai suke hidimar su,, Yayinda mommyn itama babu laifi dukda taso auren ya Khalil da maryam amma ya zatayi dole ta saki take shiri sosai musamman dayake ya Khalil ne dan farko kuma na karshe haka ma maganin kariya iri iri koyaushe cikin bashi take,, Ga uban gayyar kuwa babu wani shiri da yakeyi ko kayan akwatin babu tsinke nasa a cikin,ya fada yayi baki kallo daya zakayi masa kasan bashida nutsuwa da walwala kullum fuskar nan tasa murtuk ga bakin space da ya koma sanyawa idanunsa kamar wani jamin'in tsaro,, Mikewa yayi daga kwancen dayake ya fada toilet ya watsa ruwa ya fito jallabiya fara khal kawai ya sanya tareda tree quarter aciki turaruka yafeshe jikinsa dasu ya zari key din motsrsa ya fice,, Tiki yakeyi sannu a hankali hankali sa gaba daya yana ga tunanin maryam taki bari su hadu tunda aka kawo lefe gashi biki yau sauran kwana hudu gaba daya yarasa mai yake yimasa dadi,,horn yayi a kofar gate din ,, da sauri maigadi ya wangale masa kofa yashigar da motar har wurin parking,,ya dade zaune cikin motar batareda sanin makamar yiba kusan minti ashirin kafin ya kashe motar ya fito cikin gidan ya nufa kai tsaye yana fatan samun ganin gimbiyar tasa da farko,, *Mrs noourโœ๐Ÿป* [7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *๐Ÿด๐ŸดKARFIN IKO๐Ÿด๐Ÿด* ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ”ฑ Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com *HIKMAAH writers association* Edited by๐Ÿ‘‰๐Ÿป *oum Zahara*๐Ÿ˜ Dedicated 2my lil sis๐Ÿ‘‰๐Ÿป *Maman Sultan*๐Ÿ˜˜ ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู… ๐Ÿ…ฟโž–4โƒฃ3โƒฃ Horn din daake yi masa da karfi ya sanya sa tsayawa da kyar ya cire kai ya juyo yana duban mai zabga masa horn haka ga mamakin sa yaseer ne duk a zatonsa safina ce keyi masa,, daga masa hannu kawai yayi batareda ya maida martanin murmushin da yaseer din keyi masa ba,,parking yayi shima ya fito ya nufo sa hannu ya mika masa amma yaseer sai ya Watson masa harara yace lalle mutumina abun naka har yayi tsauri haka to karike gaisuwar ka ba wurinka na zoba,, damm yaji kirjinsa ya buga masa mai yaseer Ke nufi badai wurin maryam yake zuwa ba impossible ya furta a zuciyar sa wacce ta chanza salon bugun nata cikin sauri sauri,, da sauri ya Khalil ya riko hannun sa ganin yana kokarin tusa kai cikin gidan shima juyiwa yayi cike da mamakin yana duban ya Khalil din,,dage masa gira ya alamun tambayar lafiya,, da kyar ya budi baki murya chunkushe yace yaseer naga alamar bakada hankali ne gidan mutane kake kokarin fadawa haka batareda neman izini ba... Injiwa yace maka baa bane izni ba yaseer din ya fadi yana tsare sa da idanunsa,, kauda kansa yayi gefe batareda yace komai ba, ganin haka yasa yaseer cewa malam ka barni inje inga masoyiyata tunda kai muginta ta hanaka yimin hanyar ta har number ta kasaka blacklist ko toh ta Allah bataka ba,,janye hannun sa yayi ya tura kofar ya shige ciki,, ya bar ya Khalil wurin tsaye Wanda tunda yaji abunda yaseer din ya fadi yaji kamar an sauke masa aradu takai gaba daya jikinsa ya mutu murus ya kasa koda daga yatsan sane banda wani irin sarawa da kansa yakeyi kamar zai tsage gida biyu,, ya Khalil, ya Khalil firgigit ya dago kansa yana duban ta wani irin bakin ciki ne ya kara turnuke masa cike jiyake da dama dayasa an kama masa ita harsai ya auri maryam yasa afito da ita amma ina bayajin zai iya aikata wani mugun nufi akan kowa,, karasowa tayi kusa dashi tana zuba murmushi cike da yauki da salo tana fadin yanzu ya yaseer yace ya bar min kai a waje shiyasa nace bari inje inshigo da kai,, Kara tamke fuskar sa yayi ya janye jikinsa daga gareta yayi gaba ciki cike yake fadin bari in gaisa da mom tukun na,, Bin Bayan sa tayi itama ranta yadan sosu bata kaunar wani yanuna mata girman sa ko isa bata ganin zata jure wannan halin na ya Khalil amma kwafa tayi tana jinjina kai a fili ta furta babu komai nesa ta kusa zuwa ai da sannu zanyi maganin Ku ni safina,, a falon ta tadda ya Khalil din hakince bisa kujera suna gaisawa da mom sai cin magani yakeyi yayinda mom kuwa sai washe baki takeyi a dole ga siriki yazo Karasawa tayi ta zauna kusa da shi suka cigaba da hira su hankali kwace duk da safina ta na lura dashi hankalinsa gaba daya baya Kansu jifa jifa yana dagowa ya dubi steps ko zai ganta,, Mikewar mom tayi tashiga cika ganin haka yasa yaseer rasowa ya tsugunna gaban safina yana washe baki yace da girman kujerar ki hajiya ina mutuniyar tawa don nifa na kosa inyi tozali da ita kar zuciyata ta buga,, Murmushi tayi cike da jin dadi yadda yayi mata inama ace hakan ya Khalil yake datafi kowacce mace sa a aduniya amma babu komai ,bude baki tayi tace karka samu damuwa tunda nayi maka alkawari ai kamar ka sameta ka gama,, fadada murmushinsa yayi yace yawwa damuwa kinsamu kyauta taban mamakin wacce ko wanna saurayin naki bai taba yi miki irinta ba,, ranta ya soso dajin abunda yaseer yafada amma babu yadda zatayi dole ta daga wayar landline tasa mai aiki kiran maryam din,, adduoe kawai ya Khalil yake jerowa cikin zuciyar sa domin neman take ta buga ta tarwatse bakin cike ya gama mamaye masa zuciya tsanar safina ta kara samun babban mazauni a zuciyar ta tasaan da irin son dayakewa maryam amma take kokarin hadata da wani ,wanin ma yaseer da yasan shi akan naci akan abu gaba dayan idanuwansa sun chanza launi sunyi jajair jijiyuyin kansa sun fito sunyi rudu rudu kallon hanya kawai yakeyi yaga taina zata bullo,, Aikuwa saigata ta sauko cikin tafiyar nan tata ta nutsuwa da sanyi sanye take cikin shadda black color dinkin doguwar Riga tasha aiki tundaga saman har kasa bata daura dankwalin ba akanta sai mayafi kawai data dora bisa kanta saosai tayi balain kyau Wanda har saida safina ta bayyana kishin ta karara ta hanyar Jan dogon tsaki tareda fadin useleess girl kawai ta kauda kanta,, Su kuwa dukkansu da yaseer din da ogan gabadaya idanuwa suka zuba mata harta kara so kanta na kasa koda wasa bata dago idnunta ba musamman datake jiyo kamshin turaren ya Khalil Wanda ya doke na kowa kamshin da sanyin dadi,, ****** *Kano* da salllama ummi tashiga gidan su halima sada tajira aka bata umarnin cigowa sannan ta shiga sannu tayi mata tana mata kallon sani amma kuma bata gane inda tasan taba ganin haka yasa ummin fadada murmushi ta tace halima ummin maryam ce fa a zaburce ta mike tana Waro idanun tace ummi kece kuwa da gaske tana kama hannun ummin,, dariya tayi sosai tace haba halima saikace bakeba na dauka ko shekara Dari zanyi bama tare zaki ganeni balle dudu du banfi watanni ba,, Jinjina kai halima tayi bakinta yakasa rufuwa tace wallahi dadai zan iya ceawa haka amma banda yanzu Ke kinga yanda kika koma kuwa ummin maryam kinyi kiba kinyi kyau kinzama wata babbar hajiya,, Sosai suka gaisawa ummi tayi masu godiya sosai akan dawainiyar dasukayi da ita a baya sannan ta gabatar mata dalilin zuwansu akan maryam din ,, Jinjina kai halima tayi tace wallahi kuwa ummi wannan shiyakamata mumaida hankali akai bari in kira malam a waya nan take takira mijinta ta shaida masa zuwan su ummi harda abba sosai shima yayi murna yace gashinan bisa hanya ,, Saanan ta Gyara zama sosai ta na fuskantar ummi tace tabbas maryam tana cikin koshin lafiya kwanakin baya ance tazo amma lokacin bana gidan naje kauye to kinsan abin yara madadin ko number waya su amsa ina haka tazo ta koma amma dai

Chapter 19 of 32