Share this page
ya mirde mata haka ta daure tasake yunkurin mikewa,, Wani Marin yasake watsa mata ta sake zubewa a kasa wallahi ni kuwa zanga waye ubanki a gurin nan zanga wazai tsaya miki da har kike batun muddin kina raye ya fada yana huci tamkar zaki gabadaya muninsa ya kuma bayyana kananun idanun nan sun kankaci saboda masifa ,damko gashin kanta ya sakeyi ya dagota yajata har gadon yasanya hannunshi yakaima ta mugun naushi a ciki Wanda yasanyata sumewa Bayan ta fasa uban kara wacce tayi dai dai da shigowar harira gidan saida gabanta ya fadi da sauri ta kashe motar ta nufo cikin gidan,, Dariya yayi yana shafa uban tumbinsa yana fadin karfin maza yakare daganan ashe, nan take yashiga shafata tareda cire mata kayan jikinta babu tausayi balle imani baiji sanda ta sanya key ba siganinta yayi cikin dakin tana sallati da karfi Wanda yasnyashi dagowa da sauri rai a matukar baci yana mata kallon maiya kawoki ke kuma,, Bakinta na rawa da hannun ta ta nuna masa kasan maryam din inda jiki keta zuba harya fara bata bed din,kallon wurin yayi da sauri ya mike a gadon yana zazzare idanu,, Da gudu ta karaso inda maryam din take ta kamo kanta tana jijjiga ta tana kiran sunata shiru babu alamun numfashi rai vace ta dagotana kallon alhajin ta soma fadin mai kayi haka Alhaji kashe ta zakayi Bayan inbata yadda ba akwai hanyoyi da dama dazaka ni cikin ruwan sanyin amma kake kokarin kashe ta dole akira doctoh Tina domin ciki ne da ita,, Ciki ,ciki kuma lallai ma mayar iskar yarinyar nan wallahi kuwa ayau din nan zaa cire shi,, Bude idanu sosai harira tayi a kansa ranta a bace tace a matsayinka nawa zaka cire mata ciki Bayan wanna azabar da wulakancin dakayi mata bakada wannan *karfin iko* wallahi mudai damuke yan iskan naka zaka iya yin wannan hukuncin akanmu amma ba a kan.. Duka yakaimata a baki babu shiri ta hadiyar sauran maganar dake bakinta ta sanya kuka tana kara rungume maryam jikinta,, Wallahi karki bari raina ya baci bazaki sameni da kyauba ke bakome bace bace karya wulakantacce a wuri na a yau din nan wallahi zan iya bada jininki ga kungiya,ya fada yana nuna ta da dan yatsa a harzuke,, Saida ya bude kofar dakin kafin ya juya a dakile yace ki sanya mata kaya Tina na nan zuwa zanga uban daya tsaya muku keda ita masu jinin tsiya shegu ya buga kofar da karfi ya fice,, Da sauri harirata sauko daga kan gado tayi dakinta da gudu ta dauko mata sabuwar atampa doguwar Riga tareda pad ta dawo ta gyara ta ta sake maida kanta akan cinyar ta gayabada ta kasa nutsauwa duk wani kullin maryam dake zuciyarta saitaji babu shi sai tsantsan tausayinta rungumeta ta sake yi a jikinta tana hawaye a hankali tace Allah ya tashi kafadarki sis jin sautin takalman yasanya ta ajiye kan maryam din kan gado tai maza ta koma chan kan mirrow ta zauna tareda daidaita kanta,, Alhajine ya bude kofar tareda doctor Tina hannun ta rike da yar jakar aikinta sannu tayi musu Kasai ta kauda kanta yayinda Alhaji yayiwa doctor tina nuni da maryam dake kwance yana fadin ki fara yimata kwajin ciki idan shine ki gauggauta shire shi yanzu,, Angama Alhaji "ta fada tana Karasawa inda maryam din take,, Alhaji na fita doctor Tina ta shiga aikinta inda harira ta taimaka mata da kyar suka samu numfashinta ya dawo normal kafin tashiga duddubata inda ta dibe jininta a syringe ta ajiye gefe saanan ta daure wa maryam din Karin ruwa,, Ganin tana kokarin tafiya ya sanya harira dakatar da ita da tamabayar ina zataje kuma,, Saida ta gyara zaman glass dinta kafin taje dole akwada jinin dana dinba lab zanje yanzu zan dawo nanda one hour,, D sauri harirar ta mike ta karaso inda take tana fadin amma kamata yayi ki fara tsaida jinin nan datake zubarwa ko,,, Nooo ta fada tana girgiza kai bamu bukatar hakan domin indai zubarwa zaayi gwara abarta kawai,, Amma baki ganin wani Abu zai iya samunta kafin ki dawo kar jini ya balle mata fa don Allah ki daureki fara yimata wata dabarar fitar da ciki aiba wahala bane doctor Tina a wurinki,, Allura ta hada cikin sauri tayima saanan ta zuba cikin drip din ta fice,, Ajiyar zuciya harira ta sauke tana addua Allah yasanya jinin ya tsaya haka kar cikin ya fita,,zama tayi kusa da ita tareda zuba mata idanu cikin tausayawa wazata nema ne yanzu ya taimaka mata tasan muddin takira yansanda itazata kwana ciki domin suma yan sandan mutanen sune hakama baban ta tasan ba kaunar su maryam yake ba tun asalin shi ga gida cike da masu tsaro,,oh Allah ka kubutar da baiwar nan taka,, *********** Da fara'aarta ta shigo bakinta dauke da sallama rike take da mug Wanda ta hada shaye dayaji kayan kamshi,, Fuska a sake ummi ta amsa mata tareda mikewa daga kwanciyar datayi,, sannu antyn ta,, Yawwa ummin maryam ya jikin naki?anty hafsa ta tambaya,, Wane jiki kuma ko kawazuci dai kawai duktabi ta daga hankalin mu yarinya nachan makale da mijinta,,abba yayi saurin fada yana murmushi,, Waro idanu waje anty hafsat tayi tana dariya tace lallai kam ya kamata kibarmin yarinya ta huta gaskiya bandake da abunki ki kirata mana hankalinki saiya kwanta ai,, Waye nidin ummi ta fada tana girgiza kai Allah ya kyauta kawai dai kwana biyu bana mafarkai masu dadi akanta ne shiyasa,, Saida ta zauna gefen ta akan gadon ta mika mata mug din kafin tace Allah ya kyauta insha Allah ma tana lafiya tunda kikaji shiru indai ba son jin labarin sabon miji ko kishiya kike son jiba ta karashe cikin wasa,, Dariya sukai gaba dayansu yayinda UMMI nata ya zamto na yake domin zuciyar ta ta gaza kwanciya da samar mata natsuwa akan lafiyar maryam daure wa kawai takeyi musamman yadda su abba suka damu akan ta,, ******************* Tunda suka shigo da kyar mommyn ta tilasta masa yadan tsakuri abinci Wanda yakejinsa tamkar madaci fresh milk kawai ya dauka yayi musu saida safe ya wuce sashen sa,, Tunda yajiga yake kan system dinsa gabadaya bayanan inda Alhaji yake yakebi yana bincikawa so yake yarigasu isa kafin suje,da kyar ta hanyar abokinsa Mahmud jb wani maaikacin hukumar bincike ne na CID,ya Khalil ya yi masa bayanin komai inda basu runtsa ba saida suga bincike gabadaya bayanan guest house dinsa guda hudun dake garin Abuja ,sun sami bayanan gida guda uku dayane suka rasa bayanan a kansa na rigester komai inda hankalinsu yafi kwanciya da tabbacin gidan ne Maryam take,, Adaren suka yi shirinsu tareda taimakon wasu da Muhammad ya hada su a cikin aikin zasu fita karfe hudu da rabi na dare,, Sai misalin goma da yan mintuna suka shigo gidan tun kallon daya da mom tayi mata jikinta yayi sanyi zuciyarta ta shiga bugawa tabbas tasan babu lafiya sai dai ganin dad kwance da drip daure a hannun sa ya sanya hankalinta kwanciya tana hamdalla dama asirinta ya tonu ba,, A tsorace ta karasa gurin dad ta zauna gefen gadon tana tsura masa idanu ya rame sosai kamar ba dad dinta ba bacci yakeyi sai dai yana yin yadda yake numfashi zai tabbatar maka da jin jikinsa, ta Dade zaune kafin ta mike tabi Bayan mom zuwa dakinta,, Hankalinta ya dada tashi ganin mom din ta hada kai da hannu ta kuka yarda hand bag dinta tayi ta karaso da sauri tarungume mom tana fadin menene mom wani abune yasamu dad don Allah ki daina Ku ka pls ta karashe itama tana kukan,, Dagoda fuska mom tayi tareda tsare safina da idanu na wasu dakiku kafin ta kauda kanta tana Jan majina ,murya na rawa ta soma fadin safina mai kika dauki rayuwar nan ne ,,menene cikin duniyar nan ne safina dabazaki nutsu ki kama bautar ubangiji ki ba ki duba halin dakika jefamu safina mun rasa yayyanki a lokacin damuke tsananin bukatar su Allah yazo ya bamuke tabbas munada hannu cikin tabarbarewar tarbiyyarki amma tunda har nace miki kiyi hakuri kikai kukanki ga mahallincin ki inhar sun zalinceki da sannu Allah zaibi miki hakkin ki balle babu Wanda yazalunceki cikinsu maryam dauke take da nuna biyu haka kema kigayamin ina zakukai rabon nan in kika dage ehee? Tunda mom ta fara magana safina ke zunburar baki tana fadin dama akan haka suke daga hankali haka,azahiri kuwa cewa tayi mom ai bazaki taba ganewa ba ni kadai nasan halin danake ciki zama da wanchan dan is..kasa Karasawa tayi batasan dalilin hakan ba kuma sai tayi kasa da kanta ta mike da sauri ta fice daga dakin,, Dakinta ta nufa ta shige toilet ta sakar ma kanta shower kozata samu nutsuwa,, Koda ta fito babu kayanta a dakin dole tasanya hijab ta fita rai baci tana fadan komai an kwashewa mutum tamkar mutuwa yayi mtsss taja dogon tsaki,, Bangaren da ya Habib yake ta nufa anci SAA yaudai tayi sallama😳kafin ta jiga tsaya wa yayi chak da goge jikin sa dayakeyi da towel baki budi yake kallon ta for de first tym kenan in history rayuwar ta da yaji tayi sallmaa kafin ta shiga dakin,, Kauda kanta tayi tana tamke fuskar ganin sa da dan boxers kawai ta wuce shi tajanyo akwatinta ta bude ta dauki kayan bacci ta juya ta wuce shi zata fita da da sauri ya sanya hannu yariko hijab dinta Wanda yasanyata tsayawa chak batareda tajiyo ba,, ganin batada niyyar motsawa koyin tsiwar yasanyashi matsawa kusa da ita ya jige jikinta tareda yaye mata hijab din jikinta ya rungumeta ta Bayan yana wasa da hancinsa akan wuyanta sai ina kuma matar Habib,, Kasa amsawa tayi sai jikinta dayayi mugun saki dama haka yakeso janye jikin sa yayi yajata kan bed inda yashiga romance dinta itama yanzu bata hanashi dukda dai idanu kawai take zuba masa yayi ya gama ,, Rungume take jikin sa a hankali ya ce alhamdulillah munsami sunayen wadanda suke da hannu cikin lamarin nan na kama maryam,, Zumbur ta mike tana zaro idanu waje inda gabadaya jikinta ya dauki tsuma sai gumi ke yanko mata ta ko ina, Sosai bugun zuciyar sata ta Shiva bugawa cikin sauri sauri yana karanto inna lillahi wainna ilaihir rajiun cikin zuciyar shi tabbas koda safina batayi magana yagano tanada hannu cikin maganar nan,, Dagowa yayi ya dogari hannu sa da pillow ya tallafe kumatunsa saida ya daidaita kansa kafin yace lafiya ke kuma daga magana madadin kiyi murna sai kika rikice tamakar ke kika kamata ????,,, *mrs noour*✍🏻 [7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* 🔱🔱🔱🔱🔱 Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com Wattpad me @pheeymarrh *HIKMAAH writers association* Edited by👉🏻 *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sis👉🏻 *Maman Sultan*😘 بسم الله الرحمن الرحيم 🅿➖6⃣5⃣ Kauda kai tayi gefe ta hadiya miyau da kyar da kyar ta iya aro jarumta ta kimtse fuska cikin in ina take fadin maizasa kayi mun zanchen ta meye abun farin ciki dajin hakan da har zan tayaku murya,tana gama fadar haka ta sauka daga kan bed din ta dauki towel dinta ta shige toilet wata irin nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tana dafe kirji anya kuwa anya kuwa asirina bai tonu ba kuwa,,wata irin murdawa cikin ta yayi Wanda har saida ya kaita ga zaman a gefen bathtub tana dafe kirji tunowa da tayi da waye ya khalil,, Ohh ni safina anya kuwa bazanyi nadamar aikatan abunda nayiba kuwa tabbas nasan zan fuskanci matsala babba idan sunana ya fito cikin lamarin nan,, Hannu ta sanya ta share zufar dake keto mata daga saman goshinta da kyar ta iya watsa ruwa jikinta tayi wankan tsarki ta fito jikinta a sanyaya ta dawo ta leka fuskar ya Habib bacci yake ga dukkan alamu don ta jima a toilet din wayar ta ta dauka ta koma chan palor dakin ta shiga neman layin Alhaji saidai abunda bata sani ba shine idon ya Habib biyu duk wani motsi nata akan idonsa daukar wayar da tayi saiya dad'a tabbatar masa da lallai akwai kamshin gaskiya cikin maganar hajiya ladi ,inna lillahi wa inna ilaihir rajiuun ya shiga fadi yana rintse idanu sa,, Ana kiran sallar magrib doctor Tina ta dawo inda ta shigo dakin ta tadda maryam din kwance ta sake dudduba ta kafin ta fice daga dakin ta kulle don key din yana ta waje ne wayar Alhaji ta kira inda yace ta karasa parlonsa,, Result din Maryam ta mika masa inda yanuna ta dauke da juna,, girgiza kansa yayi yana hura hanci ya mika ma doctor Tina takardar yace kije ki cire shi yanzu karta kwana dashi koda zata rasa ranta kuwa zan nuna mata karshen taurin kai,, Amsa tayi tana fadin angama yallabai,, ta mike ta fice daga dakin ta koma zuwa dakin,, Koda ta koma tana nan yadda ta barta bacci take ,magunguna ta fito dadu ta hada allurai guda biyu masu karfi Wanda ta saba aiki dasu saanan ta karasa gadon ta sake dubata jikin yayi sauki sosai saidai jinin dake zuba ya bata ta sosi pad din tayi jagab har bedsheets din ya baci dole ta ajiye syringe din ta koma dakin Alhaji inda ta bukaci harira ta taimaka mata su gyara ta wata asirtacciyar ajiyar zuciya ta sauke dama neman dalilin dazai kaita dakin ta keyi kozata ita hana doctor Tina yin wannan allurar,,amma sai taki mikewa don gudun kar a dagota saida ya Alhaji ya daka mata tsawa kafin ta mike tana yatsina baki adole bataso,, Saida ta tsaya a parlon ta dauki cup ta tsiyayi ruwa a dispenser marar sanyi kafin tabi Bayan doctor Tina inda ta tarar da ita harta cire mata drip din tana kokarin cire mata kayan jikinta ta,, sanya hannu suka gyara ta cikin kayanta dai ta sake bada atampa doguwar Riga suka sanya mata harira Gamawar su yayi daidai da farkawan maryam din gaba dayan jikinta yayi mata nauyi ko yatsan hannun ta ta kasa dagawa idanunta Kansu jitakeyi tamkar ta kwana cikin hayaki da kyar take iya kyafta idanun,, Da sauri harira tace yawwa kinga ta farka ma bari ta fara shan koda tea ne don gaskiya yau throughout babu abunda tasanya acikinta ga zubar jini,, Bataso hakan ba amma ganin hariran ba kanwar lasa bace dole ta amsa da toh aranta tana mamakin yadda take nuna damuwar ta akan wanna yarinyar Bayan sun saba aikin akoyaushe ita da kanta take kai yaran mutane har office dinta a zubar musu da ciki,, Batafi minti shida ba ta dawo da cup a hannu ta tana fadin sorry pls gashi ki bata don Alhaji na jira na ta mika mata sai da bata bari ta rike ba ta sakar mata cup din a jikinta da sauri suka matsa baya inna lillahi sorry doctor Tina wallahi ban lura ba ina sauri in fita ne yi hakuri pls,, Ta fara kuluwa da abunda harira takeyi mata amma babu yadda ta iya ta amsa da its okay kawai ta juya ta nufi bathroom,, Cikin gaggawa harira ta dauko allurar da ta hada ta siyaye kusan duka tabar kadan inda ta zuko ruwan data tsiyayo ta cike dai dai yadda ta gani tayi maza ta maida ta ajiye,, Ta dauki kusan five mins kafin ta fito daga toilet din tana fitowa ta dauki allurar tayi maryam din ta tattara kayanta tace ki hada mata wani tea din bari inga Alhaji,, Da sauri itama tace aa bazan yi jiraba wannan aikin kine kya iya zama keda yazamar dole tai maza ta fice tana hura hanci tareda Jan tsaki,,said a ta bar parlon ta haura sama kafin tanema gefe daya tana sauke ajiyar zuciya alhamdulillah lillahi shirin farko yatafi dai dai Allah kabani ikon kubutar da maryam daga gidan nan zuwa gobe,, Allurar bacci ta sake yimata ta nemi wuri ta zauna saida taga bacci ya dauketa kafin ta fito ta wuce itama gurin Alhaji,,🥺 Komai yayi daidai zuwa anjima cikin zai fita doctor Tina ta Sanar da alhaji,,tare suka fita da alhajin don yau bazai kwana gidan ba shirinsa ya gama rushuwa na kasancewa da maryam dole ya bar gidan ya wuce gidansa gaba dayan kiran safina yana kallo babu damar dauka dole ya kashe wayar baki dayan ta saboda amaryar sa batada dama yanzu nan saiya kwashi kashin shi a hannu dukda dai tunanin sa dauka yakeyi kozata tambayi yadda suka yi da maryam ne,, Jin wayar akashe ya Dada tada hankalinta na shiga uku ni safina zuciya ta ta fada tsoron hukuncin dazan fuskata,,dole ta dawo ta kwanta jiki a sabule tana kullawa da warwara akan abunda ya kamata ta farayi,, Duk yadda yaso ya daure kasawa yayi ya mike zaune ya kunna wutar dakin inda tayi saurin juyowa tana kallonshi shima idanun kawai ya zuba mata wadanda suka yi jajur tamkar na mai ciwo,, Mai yasa safina kika zabi wannan rayuwar ne ? maiyasa kike kokarin jefa iyayenki dani kaina cikin tashin hankali da damuwa? Mai kika dauki rayuwar duniyar nan ne safina ki gayamuni ke kika sanya a dauke maryam?ya fada rai a bace,, girgiza kai kawai takeyi tunda yasoma magana tana hawaye ta kasa furta masa ko kalma daya babu tsiwar nan balle rashin mutuncin hakan ya tabbatar masa da lallai ita dince domin yafi kowa sanin halinta,, Answer me safina kice ko bake baceeeh?ya fada cikin hargagi tamakar zai shake ta,,,, *pls kuyi hakuri da wanna baki nayi* *mrs noour ce*✍🏻 [7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *🐴🐴KARFIN IKO🐴🐴* 🔱🔱🔱🔱🔱 Written & story by *@PHEEYMARRH* Pheeymarrh@gmail.com Wattpad me @pheeymarrh *HIKMAAH writers association* Edited by👉🏻 *oum Zahara*😍 Dedicated 2my lil sis👉🏻 *Maman Sultan*😘 بسم الله الرحمن الرحيم *Mommyn zahra Allah yabada SAA ya bada kyakkyawan sakamako,mrs auwal🥰* 🅿➖6⃣6⃣ Kuka takeyi sosai ta kasa tanka masa dukda yadda taji tsawar har tsakar kanta sun kai kusan minti biyu a haka,inna lillahi wa inna ilaihir rajiun ya fada yana kauda kansa daga kallonta wasu zafafan hawaye ne suka shiga silalowa daga idanuwansa,, Mikewa yayi ya sauka daga gadon ya wuce toilet gaba daya hankali da nutsuwar da tunanin sa sun gushe daga jikinsa shawer ya sakar wa kansa yana tsaya abunda kawai yakejin zuciyar sa zata iya sanyaya kenan sai kash saima wasu mugayen sakonni data shiga gaya masa akan matakin daya kamata ya dauka a Daren nan ba sai gobe ba yakai kusan minti ashirin tsaye kafin yayi wankan tsarki ya dauro alwalar ya fito,inda take zaune nan ya barta tana ta faman aikin kuka har shesshekar nason taci karfin numfashinta kallo daya yayi mata ya kauda kansa saboda wani Abu daya ji yataso ta tokare masa a makoshi na kallonta dayayi tabbas bacin cikin dake jikin ta wallahi da babu abunda zai hanashi ya sawwake wa kansa wannan auren kaddarar na biyayya,, Jallabiya ya sanya ya wuce parlon chan gefe inda wurin praying mat dinsa take yashiga jero nafil filu domin kai kukansa ga mahaliccin sa,, Koda cikin duhu suke taji kallon dayayi mata binsa tayi da idanu harya fita kuka mai karfi ta sake kamar ranta zai fita sai yanzu tafara jin kunya da nadamar abunda ta aikata anya kuwa *karfin iko* da gatan datake takama dashi kuwa zasu kwace ta awannan karon nohhh ta fada da karfi tana danne saitin zuciyar data hasasho mata tunanin wannan maganar zata iya sanya dad dinta zuciyar sa ta buga ya mutu,, girgiza kai takeyi da karfi tana fadin daina min wannan tunanin pls banason rasaka dad Kaine gata na,rashin ka na dan lokaci yasanyani shiga wani hali balle rashi na har abada mikewa tayi da sauri ta dauko wayar ta ta shiga neman layin Alhaji akaro na ba adadi cikin kankanin lokaci dukta fita gayyacinta kallo daya zakayi mata kasan babu nutsuwa a tattare da ita saboda yadda take nacin kiran wayar da a kashe take gaba daya,, Jin karar wayarsa yaki kare wa ne ya sanyashi dayayi sallame ya mike yashiga dakin yana tunanin Allah yasa ba jikin dad bane domin waye zai tasheshi cikin tsohon Daren nan,, Wuceta yayi tana rike da waya tana aikin kira da kuka ya dauki wayar Wanda yayi dai dai da sake shigowar wani kiran ,, "" khaleel""ya fada yana kallon wayar cikin tunanin yayinda safina ta tsaya chak tana kallonsa cikin ta na murdawa sakamakon jin sunan yakhalil datayi ,, Cikin sauri yadaga kirjinsa na tsanan ta bugu assalamu alaikum ya fada tamkar mai tsoron yin magana,tsoro ne ya shige shi na daya yana tunanin kardai ya khalil sun tabbatar da hannu safina cikin maganar nan sai kuma tsoron jin labarin ko wani Abu ya sami maryam din ne,, Waalaikum salam ya amsa masa cikin yanayin daya kara sanyashi cikin damuwa,lafiya kuwa khalil cikin daren nan ko an samu wani labari ne Habib yayi karfin halin tamvaya,, Bayanin yadda bunciken nasu ya kansance yayi masa a takaice tare rokonsa akan yana bukatar sa suje nan da one hour wurin ya kirasa ne saboda bayason tada hankalin dad,, Ajiyar zuciya ya sauki mai karfi kafin ya amsa da toh shikenan inkazo ka kira ni kawai dama muna cikin case din no need inyi reporting zan kuma samu karin wasu mutum biyun ana,, OK hakan yayi ma na gode sainazo ya khalil ya fada tareda katse kiran,, Juyowa yayi zai wuce amma gabadaya tausayin ta ya hanashi ganin yadda ta rikice gaba daya(Allah sarki ya Habib masoyin gaskiya😭) Karasawa yayi kusa da ita yatsaya gaban ta dab da ita har suna jiyo hucin numfashin juna hannuwansa ya sanya yakamo hannayen ta duka biyun ya rike yana mata kallon cikin ido na wasu dakiku gaba daya tausayin ta ya gama rufe zuciyar sa wayar dake hannunta ya cire ya wurga ta kan gadon ya juya yasoma tafiya da ita tana biyedashi ta zuba masa idanu har kofar toilet ya kaita kafin yace ki shiga ki yi alwara kizo ki karasa raya sauran daren nan wajen kai kukanki ga Allah pls safina ki tsaya ki roki ubangijin ki gafara da yafeyar sa akan ayyukan kan ki,,yana gama fadar haka ya saketa yajuya da sauri ya wuce parlon yabude kofa ya fita,, Toshe bakinta tayi saboda wani sabon kukan daya taho mata mai karfi ta shiga toilet,, Ta dan jima a bayin tana kuka kafin ta dauro alwalar ta fito turus tayi ganin sa sanye da uniform dinsa tana zuba masa idanu,, Sai da ya dauki jakar Bayan sa Wanda kayan aikinsu ne bindigogi da wukake ne ya raya ta a Bayan sa'annan ya karasa inda take take yadafa kafadar ta yace kiyimun fatan dawowa lafiya safina a adduar ki kiyi mana fatan cin nasara zamu je gurin maryam,, Gaba daya tama rasa abunyi kukan ya fara ragimuwa don kansa saboda tsabar tension da damuwa murya na rawa tace Allah ya Baku Saar dawo da maryam lafiya ,Allah ya dawo daku lafiya kuma tana gama fadar haka ta wuce parlon tana sharar kwalla ita kanta tasani Allah bazai kyaleta hakan namba irin rayukan data bata irin mutanen data wulakanta irin cin zarafin datayiwa mutane irin mugun Sharron datake bibiyar maryam dashi dole ta koyawa kanta dauriya domin tasan wanna somin tabine ma sai an gurfanar dasu a kotu ma,,tana kallon sa harya fice ya rufo mata kofar,, Allah sarki rayuwa yanzu inya rasa ransa shima hakkinsa ya rataya a wuyana kenan duk a daliln Abu daya Wanda bai amfane ni da komai ba *karfin iko*,, A hankali take bude idanuwan tawadanda suka yi mata nauyi sosai tana sallati cikin zuciyarta sosai ta kejin ciwo a marar ta da kugunta ga hannun ta dake jin zugi yakema ta dau wasu mintuna a hakan kafin abubuwan dasuka faru suka shiga tariyo mata kara ta fasa da karfi tana rintse idanunta firgigit harira ta farka wacce ke kwance chan gefe kan gadon da sauri ta matsa kusa da ita ta rike mata hannun dake daure da drip tana tambayar lafiya ki nutsu karki cire wanna karin ruw.. wani irin kallo maryam ta watso mata Wanda ya sanya ta kasa karasa maganar,, Da kyar ta yunkura ta tashi zaune gabadaya marar ta jinta take a dunkule hannun ta tabi da kallo Wanda ke daure da karin ruwan babu bata lokaci ta sanya hannu ta cizge shi tayi jefa da igiyar tasa kafa ta ture dogon karfen da aka sagale drip din jiki kuka ta sanya da iyakacin karfin ta tayi nadamar zuwanta duniya yau lallai ta tabbatar itadin bata da rabon jin dadi a duniya mai ya sanya hakan ne,menayi mukune irin haka zaku wulakanta rayuwa ta data aure na?, mai yasa zaki nuna tausayinki gareni?, yanzu ko kuwa

Chapter 29 of 32