yadda ta shaku da ita ga wata irin soyayya datake yimata jinta take Kamar yar uwarta ta jini,uwa uba uban gayyar wanda baisan da wannan tafiyar ba ya wuce sabon company dinsa tun before seven,,
Horn ya danna driver a Kofar makeken gate din gidan saida gate man din ya leko ta yar karamar kafa ya gani kafin ya wangale masu gate din kirjinta ya tsananta da bugu a rayuwa bata kaunar fitina da tashin hankali gashi daddyn ya kawota inda zata gamu dasu a wurin gimbiyar safina yar girman kai,,adduar neman kareya daga sharrin mutum ta shiga karantawa har driver ya yi parking a harabar gidan,,
Sawkowa yayi ya budewa daddyn da ita kofa da sauri ta fito ta jingina jikinta da motar tana bin katon gidan nasu da kallo wanda sojojin Ke zube koina suna aikin su na tsaro abunka ida babban retired soja waya daddyn yayiwa dad akan sun karaso yace su shigo ciki ba matsala,,
yana gaba tana binsa abaya har cikin main parlon gidan ana suka tadda yan gida dad da mom suna Zaune bisa manyan kujerun parlon yayinda safina Ke kan karyawa bisa dining da sauri ta taso ta rungume daddyn tana cewa morning papa,Yawwa yata kin tashi lafiya ,lafiya lau ta amsa da sauri maryam tace anty ina kwana,,harar a ta watsa mata tareda juyar da kai ta wuce ta cigaba da karyawa,,
Musabaha sukai da dad mom ma ta gaida daddyn ganin haka yasa itama karasawa ta rakube gefen kujerar ta shiga gaidasu amsawa dad yayi fuskarsa ciki da fara'a mom kuwa ba yabo ba fallasa,,
Nan ma'aikatan gidan suka gabatar musu da abun karyawa suka ce Alhamdulillah daga kanshi suka taso,bude baki dad yayi yace maza kije kai maryam dakin baki,,
Turbune fuska tayi a shagwabe tace dad karyawa bakeyi fa batareda ta jira amsar shima ta kwala wa mai aiki kira ta umarceta da kai maryam din dakin baki ta cigaba da kurban tea dinta hankali kwance,,
da sauri maryam ta muke rike da hand bag dinta tabi bayan yar aikin tana jinjina lamarin safina cikin zuciyarta lalle zata tadda wulakacin daya fi karfinta Allah ka bani ikon yin hakuri har in koma nima ga namu gidan,,
up stair's suka nufa a ciki dakin yake babban dakine mai dauke da katon gado dan Italy set dinsa sai kayan kallon daga gefe tareda tv stand sai Kofar bayi daga gefe shima babban toilet ne mai kyau da tsari sai dai ba Kamar nasu ya Khalil ba zama tayi gefen gadon wanda aka shimfida masa bed sheet mai matukar kyau da dakin tsab yake da alama wannan shirin dad ne yasa akayi shi,,
ihun safina ta rinka jiyowa daga kasa da alama wani abun farin cikin ne ya sameta,,Karar bude Kofar ne ya tsinkayar da ita daga tunanin datakeyi mai aiki ce tace alhaji yana kiran ta,,
Mikewa tayi jiki a sanyaye tabi bayan ta har parlon kallo daya tayi musu tagane suna cikin farin ciki son ya bayyanar karara bisa fuskarsu safina na jikin dad dinta bakinta ya kasa rufuwa,, sannu tayi musu muryarta a sanyaye,,,
Amsawa sukai duka fuska a sake abin mamakin harda safina,ba karamin mamaki maryam tayi ba wanda har yakasa boyuwa a fuskarta,,
gyaran murya daddyn yayi yace toh maryam da farko dai zaki dan kara hakuri dole bisa ga tsaikon dazaa samu game da tafiyar ki gida,,
batareda yaji ta bakinta ba yacigaba da fadin yar uwarki ce sunan ta yafito ta samu admission Chan Oxford uni don haka zuwa Jibi zata tafi tareda su hajiya daganan zasu wuce siyayyan kayan biki don haka inaga zaki kara dan zama ana kafin Allah ya dawo dasu lafiya,,
Dad ya jinjina kai yace tabbas Hakane maryam da fatan zaki kara hakuri ko,,
da sauri ta dago kanta daga duken datayi tace babu komai wlh daddyn duk yadda kukayi dayane nagode Allah yasaka da alkhairi Allah yasa ayi tafiyar a sa'a,,
Ameen suka amsa baki daya saanan dad suka fita,nan suka cigaba da budirin murnar su safina na lissafa irin abubuwan datake so,mikiwa maryam tayi jikinta ya dada yin sanyi sosai ta ja kafarta ta wuce dakinta jagwab ta fada gado gaba daya ranta a jagule yake ta rasa mai yake yi mata dadi,
Allah sarki rayuwa yanzu shikenan da gaske raba su zaayi ada na dauka yayan masu kudi sai abunda suke so akeyi sai gashi naga sabanin hakan koda yake nidin na kowa bace banida gata da kima da darajar dazasu baiwa dansu abunda yake so share hawayen ta tayi tareda mikewa ta fara shirya kayanta cikin wardrobe tunda babu batun tafiya,,
Sosai ya Khalil ya daga masu mommy hankali bayan dawowar sa daga aiki yayi juyin duniyar nana mommy ta fada masa inda maryam take taki amsa daya take bashi da shine yayi hakuri kawai ya karba kaddara da Allah ya aiko masa da ita,,
gurin hajiya ya koma nan ma amsa daya ce batamasan da tafiyar maryam din ba,haka su mommyn hassana suma din basu sani ba mommy husaina kuwa dariya tayi tace hakan yayi daidai wlh yanzu kaga ka Samar ma kanka natsuwa ga zabin Yaya,,
Ficewar yayi daga daki rai bace koda daddyn ya dawo ya tadda fitinar ya Khalil baiyi wani mamaki ba don yasan zaayi hakan saidai godiya dayayiwa ubangiji daya samu ya rabasu,,
Sallamu yayi Kofar dakin daddyn kansa duke kana ganinsa kasan baya cikin walwala da farin ciki Kamar da a kwanaki biyun dabai ganta ba har rama yayi kuma duk iya binciken sa bai samu inda take ba saboda tsattsauran sharadin da daddyn ya kafa ma mommyn kada ta fada masa inba haka ba abakin auren ta,,
Karasawa yayi kusa da mommyn sa ya zauna tareda jingina gefen jikinsa da nata,sannu kawai ya iya yimusu,,
batareda daddyn ya amsa ba ya soma yiwa ya Khalil magana muryarsa a kausashe toh akan maganar biki ne zaka shirya gobe kaida mommyn zuwa us saboda siyan kayan biki saboda ita safinar tanason yin wasu abubuwan na gameda karatun ta don haka kabar duk abunda kakeyi Ku wuce gobe,,
*kuyimin hakuri Aminiya ta babu lafiya ina barar adduar Ku Allah ya bata lafiya,,*
*Mrs noour ce*βπ»π’
[7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *π΄π΄KARFIN IKOπ΄π΄*
π±π±π±π±π±
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
*HIKMAAH writers association*
Edited byππ» *oum Zahara*π
Dedicated 2my lil sisππ» *Maman Sultan*π
Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*Kai buhari da alama dai ka kayar mana da atiku shikenan babu komai,πkaima ana tare*πππ
π
Ώβ3β£9β£
Bude idanunsa yayi a hankali ya sauke su kan fuskar daddyn tabbas alamu sun nuna a fuskar daddyn babu wasa a maganar,,dagowa yayi a hankali daga jikin mommyn murya cike da bacin rai yace a gaskiya daddyn zan iya zuwa siyayya ko ina nema amma wlh banda maganar karatu Ashe ba auren ta shirya ba kenan karatu ne a ranta toh gaskiya daddyn idan mommyn bata taba sanar maka ba ayau zan Sanar maka banida raayin wacce take son karatu fiyeda auren ta bakuma zatayi aiki a gida na ba wlh,,
sakin baki daddyn yayi kawai yana kallon sa cikeda mamaki da takaice duk tunaninsa akan maryam ne ya Khalil yau yake yi masa musu,,yayinda mommyn dukar da kanta kasa kawai tayi tana addua Allah ya kawo abin da sauki donta dauki alkawarin bazata saka baki cikin wannan maganar ba tunda daddyn ba dararjata yakeyi ba,,
Rai bace daddyn yace wallahi wannan ne baka isa ba ni zaka nunawa shekarun ka sun kai,tana wajan ka bullo kenan saboda wannan marar asalin ko to wallahi kayi kadan kasani yin magana biyu,yawwa,,
Juya kai ya Khalil yayi tareda dage kafada donshima ran nashi ya dagula sosai yace shikenan daddyn ai wannan mai sauki ne saita nemi wani mijin baniba wallahi don kuwa kotayi registration aka daura auren nan wallahi tabar karatun nan kenan ya mike rai bace zai fice,,
A fusace daddyn ya tsaida shi yana fadin wallahi muddin nina haifeka akan auren nan zaka gamu da ba daidaiba sai kaga bacin rai na wallahi ni zaka ki yiwa biyayya akan wata mai ake da tsintaccoyar mage,,
Cikin fusata ya Khalil ya juyo idanunsa run rune jajur jijiyoyin kansa sun yi ridu ridu yace ka fahimceni daddyn wallahi koba safina ba koni nayiwa kaina zabi babu maganar karatu ko aiki a gida na biyayya kuma daddyn maizasa bazan ki yi maka biyayya ba bayan baka taba nuna tausayawar kar ko soyayya ba abunda nakeso ba bakiyi tunanin halin da zan shiga ba burinka in aure safina ka farantawa iyayen ta bayan su kuma a koda yaushe zabinta yafi musu komai muhimmanci a rayuwa yana gama fadar haka ya fice yabar daddyn da baki bude,,
Mikewa mommyn tayi rai a jagule itama ta fice batareda ta kara kallon inda daddyn yake ba,,
Jinjina kai daddyn yayi rai a matukar bace yace wallahi saina baku mamaki keda shi,,
da kyar da taimakon Allah ya isa bangaren shi jiri yakeji sosai yayinda gefen kansa yakejin kamar zai tsage saboda azabaar sarawar dayake yi masa ,kwanciya yayi bisa tafkeken gadonta yayi ruf da cike dafe kamsa yayi tareda runtse idanunsa,,
Kusan minti ashirin yana haka kafin ya sauke a jiyar zuciya mai karfe wayar sa ya lalubo kasan pillow ya kunna kyakkyawan hoton ta ya bayyan Wanda tayi balain kyau murmushi yayi Wanda iyakacinsa labbansa yana tuna moments din daya dauketa hoton ana e gobe zaa saceta,,
Numberta ya fara kira dukda yasan ba lallai bane ya samu ilai kuwa har yanzu wayar kashe take,ya Allah ya furta yana ceje lips dinsa na kasa,,
Har kusan minti goma yana cigaba da nacin kiran lambarta Wanda amsa daya ake bashi is switch off,tsaki yayi tareda yin jefa da wayar gefe,ya rintse idanunsa tunanin ta kawai yake,,
Maiyasa daddyn zaiyi masa haka bayan ya samu tabbacin a wurin driver daddyn ne da kansa ya dauke maryam daga gidan yayi hakuri kuma amma yana son shiga hakkinsa ,,
a haka yakeson suyi zaman auren ita zata zama mijin sai abunda tace,,
Mikewa yayi rai a jagule cikin fusata tunowa dayayi week end suke ,ficewa yayi daga dakin kai tsaye bangaren alhaji ya nufa wato kakan sa,,
Murya a shake yayi sallama tareda kutsa kai ciki amsawa sukai gaba dayansu, karasawa yayi ya zauna bisa katuwar tautausan daddumar da ke shimfide a tsakar parlon,,kwanciya yayi a gefen hajiya yana fadin kaga tsofaffi masu ran karfe,,
Dariya hajiya tayi tace kwarai kuwa ba irin kaba ragon maza kullum kana jikin mutum kamar mage,,
Dariya sukai alhaji yaxe Atoh shiyasa nake baki shawara kullum karki kujeni kibi kyale kyale don da alamu wannan mijin naki rago ne,,
Murmushi kawai ya Khalil yayi yayinda sukaita tsokanar sa suna dariya ,nan yayi zaman sa har sai da aka kira sallar azaahar kana suka mike a toilet din alhajin ya dauro alwala ya fito suka wuce masallaci,,
Tare suka fito harda daddyn bayan idar da sallar,suka nufo gida Wanda kaidar alhaji ne baya fita ranar lahadi hakama daddyn muddin yana garo balle ya Khalil Wanda shi tsarinsa babu yawo alwaz inba aiki ba yana gida koda yaushe,,
Kai tsaye gurin cin abinci suka nufa kowa ya fara cin abunda ransa keso dukda rashin sakin fuskar daddyn ga ya Khalil hakan bai hana shi sakin jiki dashi ba kamar babu wani abunda yafaru tsakanin su,,
Hankali kwance suka gama cin abincin suka mike gaba daya suka koma falo suka zauna ana ya Khalil ya soma gaya wa alhaji matsalar sa da hujjojinsa wanda hakan ba karamin harzuka ran daddyn yayi ba,,
Jinjina kai daddyn yayi bayan gama sauraron abunda ya Khalil ya fadar,kafin yayi gyaran murya ya maida kallonsa ga daddyn yace Sam ban tsammaci hakan daga gareka ba wannan shiga hakki ne dukda wajibinka ka sanya masa ido cikin lamurransa gudun baci amma tunda yayi biyayya ba yin auren nan ya kamata ka bashi damarsa a matsayinsa na Wanda zai zauna da ita,,don haka tunda bashida raayi topa babu mai takura masa domin ko anyi bazaa samu wani alfano gayin hakan ba wannan umarni ne na baka da abi zabinsa dole kamar yadda ka hana taka matar yin karatun da aiki ni anawa gani gado yayi daga gareka,,
Saanan ta juya ba ya Khalil fada yayi masa sosai akan abunda yayi tareda bashi umarnin kada ya sake jin makamancin hakan ya faru musu da jayayyai da iyaye,,
gyada kai yayi tareda baiwa daddyn hakuri saanan yayiwa alhaji godiya ya mike ya fice,,
Sosai alhaji yayiwa daddyn fada akan lamuran yara,,shima godiya yayi tareda yiwa alhaji addua ya mike ya fice zuciyar shi na tafasa har Khalil dan cikinsa zai kai kararsa akan mace ,,
Zaro wayar sa yayi ya shiga Neman number dad cikin SAA tashiga a tsaitsaye suka gaisa saanan ya dora da fadin alhaji gobe in babu damuwa ko yarinyar nan zamu iya maidata gaban iyayen ta,,
Jim dad yayi na dan lokaci kafin yace babu matsala saikazo dukda har cikin ranshi yakejin kaunar maryam kuma shi Dama mutum ne Wanda yake haka baya wulakanta ko takurawa ga wani,,
Kai tsaye toliet dinsa ya shiga tareda sakarwa kansa shawer sosai ya dade a toilet din yana kalkale jikisan da moyukan da turarukan wanka kafin ya fito kan mirror ya dauke mansa ya shiga shafawa kafin ya wuce dakin kayansa saida ya bata lokaci kafin ya fito da wasu kananun kaya wando jeans ne Wanda ta tauke daga kafa baki tareda rigar sa fara sunyi matukar daceawa da yanayin kirar jikinsa turaruka ya fwshe jikinsa dashi ya debi wayoyinsa ya fice,,
Kai tsaye harabar parking ya nufa dalliyar motarsa ya hau ya fice daga gidan hankalinsa kwance yake driving dinsa yana bin karatun daya saunya cikin motar sa,,jefa jefa yana sakin murmushi,,
Horn yayi a kofar gate dinsu da Saudi maigadi ya wangale masa gate din ya kutsa hancin motarsa ciki har wurin parking,,
da sauri ya fito fuskar sa cike da murmushi Wanda ya kara fito da kyausa hannuwansa ya harde bisa kirjinsa tareda jingina da motar ya zuba mata idanunsa tafiya takeyi cikin nutsuawa ta sadda kanta kasa wani irin wutar so da kaunarta na kara ruruwa cikin zuciyar shi ,,
Jitayi ajikinta da alamu idanu suna kanta a hankali ta dago kanta tana share gumin daya tsarfo mata ido hudu sukai dashi ajiye ledar hannunta tayi tarda Mirza idanunta shidin take gani ba gizo bane wani irin sanyi taji gabadaya jikinta har tafin kafa ta ,,
Karasawa tayi cike da zumudi cikin zazakan muryar ta take fadin ya Khalil Kaine,,
Jinjina mata kansa yayi yace yes nine mana kina mamakin ne bayan kinsan duk Inda kike zuciyata na gareki zan nemo ki maiyasa lafiya babu sallama,,
Kasa tayi da kanta tana murmushi ina wuni ya Khalil ya mommyn dasu hajiya,,
Kura mata idanunsa yayi bataeda ya bata amsa ba har jkusan minti biyu kafin yayi ajiyar zuciya yace maiyasa bazaki fara tambayar yadda nayi kewar kiba eheem heartee,,
Kara kasa tayi da kanta ciki da jin kunya tace ka shigo ciki ya Khalil safina na ciki,,murmushi yayi Wanda harsaida dimple dins ya loba ya Gyara tsayuwa tareda fadin kamar kin sani kuwa wurinta nazo tadi tunda kin gujeni,,
*kasar masar*
Jikin UMMI yayi kyau sosai babu wata damuwa suna ska ran sallamar su cikin satin nan don alhaji shima yaji sauki sosai ,
Zaune suke suna fira ummin na basu labarin abubuwan da inna tayi musu a baya,,
Dukna jikinsu yayi sanyi sai jin kara sukai da karfi Wanda ba karamin faduwar gaba ya haddasa ma ummi ba dafe saitin zuciyarta tayi tana fadin inna lillahi wa inna ilaihir rajiun,,
Mikewa tayi da sauri zata fita gaba dayan hankalinta ya tashi dajin karar Wanda har yanzu baa daina ba,,da sauri sirajo ya taso ya rike ta gam yana kokarin maids ta hankailsa a tashi yayinda didde keta Gyara zanin gadon tana fadin yi maza ka dawo da ita nan ,,
Cikin daga murya ummi me fadin abban maryam wlh shine didde muryarsa najiyo yana ohun nan don't Allah bari naje nagani kada ku hanani zuwa yau induba ,,
Kafin sirajo yayi wata maganar saiji sukai an kwala kiran ummin cikin muryar Karaji yana fadin shatu ke dauke maryam a wurin nan ki duketa nace shatu shatu baki jina ne,,
Chak suka tsaya don jin abunda ake fada Wanda suma kunnuwansu yauvsun jiye musu,,,..
*mrs noour CE*βπ»π
[7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *π΄π΄KARFIN IKOπ΄π΄*
π±π±π±π±π±
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
*HIKMAAH writers association*
Edited byππ» *oum Zahara*π
Dedicated 2my lil sisππ» *Maman Sultan*π
Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
π
Ώβ4β£0β£
Fizge hannun ta tayi da karfi cikin sassarfa gudu gudu ta nufi inda take jiyo karan sai dai kash tana isa doctors na zuwa dakin kafin takaiga shiga sun rufo kofar,,
Juyawa tayi da sauri tajisha leken ta jikin glass windows din dake dakin ,duk yadda taso ganinsa abin yaci tura haka surajo ya janye ta a wurin sakamako allaurar bacci dasuka yiwa marar lafiyar yana yasamu bacci,,
Kalaman nutsuwa da kwantar da hankali ya shiga gaya mata har ta samu nutsuwa amma achan kasan zuciyarta ta kudira aniyar komawa don tasan miryar audu ta tabbas ko shekara dari zaayi bazata taba manta wa dashiba,,
aikuwa cikin dare misalin sha biyu didde tayi bacci UMMI ta mike cikin sanda ta murda kofa ta fice kai tsaye dakin dazu na nufa ta window tayi kokarin lekawa saidai kash labulayyen dakin duk a rufe suke komawa tayi bakin kofar jikinta sai bari yakeyi kar wani ya ganta abunka da kasar waje sai ayi mata wata fassarar,,
Takai kusan minti bakwai tsaye bakin kofar tana shawar warin shiga ko hakura damuwar ta daya kada ya kasance ba audu bane mai zata fadawa yan dakin in suka kamata,dukda zuciyarta na tabbatar mata da shi dinne a dakin,,
Mika hannu tayi a sanyaye ta murda handle din kofar a hankali kirjinta na cigaba da bugawa cikin sauri addua ta shiga jerowa cikin ranta sai dai mai tana bude kofar yana dago da idanunsa ga kallon kofar dafe kirji tayi tana zaro idanu waje nan take jikinta ya dauki tsuma bakinta na rawa tareda nuni da yatsan ta gareshi ta furta abban maryam kana raye dama,,
Mikewa yayi shima daga kwanciyar dayake bugun zuciyar shi na Dada karuwa sosai yake cikin matukar kaduwa da mamakin shin shatu ce anan da sauri matar dake tsaye kusa da shi tajiyo tana duban ummi fuskar ta kunshe da mamakin maiyakawo wannan nan dakin kuma ,,mamakinta ne ya katse lokacin dataji mijinta na furta shatu da gaske kece shatu,,
Kuka ne ya kwacewa ummi babu shiri tana gyada kai alamun tabbatar maida hakan don bakinta ya kasa furta komai mikewa yayi daga kwancen dayake dukda babu wani karfi jikin shi ya sauke kafafun sa daga gadon ya taku sannu a hankali zuwa gareta domin tabbatar was idanunsa,,
Fasawa jikinasa ummi tayi tana rushewa da wani matsananxin kukan Dama kana raye abban maryam kana raye ka kujemu kabar mu cikin gararin rayuwa mai mukayi maka maiyasa kayi mana haka,,
Shima hawayen yake sharewa cike da tausayawa rayuwar su Ashe Dama akwai lokacin dazai sake dora idanunsa akan na shatu ina yarsa take a hankali ya janyeta daga jikin shi bakinsa na rawa yake fadin ina uwata shatu ina maryam take mai kuka zoyi nandin,,
Sai a lokacin matar dake tsaye gefe ta gane inda zancen nasu ya nufa ta tausaya musu hawaye na bin kuncinta ta kara so tareda kama shatu ta janyeta tace ba yanzu yakamata kuyi wannan maganar ba godiya ya kamata kuyiwa ubangiji daya sake hadaku a lokacin dakuka yanke tsammani,,
Jinjina kai ummi kawai takeyi yayinda hawaye keta ambaliya akan fuskar ta kasa sakin hannunta yayi har bakin gadon ya zaunar da ita,,
**********
*Bayan wata daya*
Sosai ake kai ruwa rana akan karatun safina duk yadda ta daga hankali da takurawa su dad abin ya faskara yayinda ya Khalil ya shafawa idons toka kememe yaki hakura akan raayins sosai maganar Ke dagawa safina hankali Wanda duk anata haukan tana tunanin plan ne kawai ya hada don ya cimma burinshi na auren maryam,,
Sosai ta uzzura tareda kara takurawar ta ga maryam waccce tun bayan dawowar su safina daga siyayya dad ya kaita gidan su sai dai kash bata tarar da kowa gidan ba tayi kuka kamar ranta zai fita tunanin ina ummin ta take har gidan su malam garba ta shiga aka sanar mata tun ciwon da ummi tayi wasu suka tafi da ita da alama yan uwanta ne gashi halima bata nan taje gida kauyensu,,
Haka taxi kukanta suka jiyo tareda dad don yake barinta a gidan tunda yaji halin da ake ciki sosai ya tausaya mata haka ya dinga mata nasiha tareda kalamai masu kwantar da hankali harta saina kukan,,
inama ace yadda dad yake haka yayi Saar mata da ya musamman ma yar don mom watara takan daga mata kafa amma safina killum cin kashin da rashin mutuncin ta daduwa yake ko yaushe tana maimata gaya mata ta tsaneta foyeda kowa a duniyar nan,,
Haka suka koma ta cigaba da zama cikin kunci da takura inkaga dariyarta toh Habib yana gidan ne dukda shima safina baya barshi ba gurin rashin mutuncinta sai dai baya damuwa da lamuranta,,
Yayinda ya Khalil shima yana kokarin kwantar mata da hankali inyazo dukda haduwar tasu saida dabara don tunda yasan da zaman maryam yake yawan zuwa gidan da sunan gurin safina,,
Ayau biki sura sati uku safina ce kwace sakinta kan makeken gadonta tana amsa waya kallo daya zakayi mata kasan ranta abace yake yayinda maryam Ke tsugune bisa gwuiwuwinta tana mammatsa ma safina kafa sannu a hankali tana addua a ranta Allah yasa agama lafiya dukda tasan zaiyi wuya safina bats kirkiro wani abun ma ta lakkaba mata donta ci mata fuskar ba,,
Aikuwa ilai da sauri safina ta janye lafar ta daga hannun maryam din tana jefenta da wani mugin kallo mai cike da nuna tsantsar kiyayya tsaki taja sanna cikin harzuka tace Ke wace irin jaka ce dakikiya ne sau nawa zan gaya miki yadda zakuyi min ne bude idanuwanta tayi tana karyar da kai gefe tace ohoo Wato kinayi ne don ki nakasa min kafa ko burinki yacika ko,,ta fada tana tsare maryam din d ido,,
Girgiza kai tayi jikinta ya dauki rawa tace aa wallahi kiyi hakuri,,
Hakurin uwarki marar zuciya kawai toh wallahi bazan fasa gaya miki ba komai zakuyi sai dai ki mutu wallahi ya Khalil nawani ni kadai kisan wannan tsaki taja da karfi tareda suake lafafunta kan yatsun maryam ta murje da karfi ta wuce,,
sosai maryam taji zafin har cikin ranta sai dai tayowa Allah godiya daya kasance babu takalmi kafar safinar mikea tayi jiki a sanyaye tana share hawaye ta Dada Gyara mata dakin ta fice zuwa nata dakin,,
Cikin kuka ta fada dakin nasu batareda sallama ba kamar yadda ta saba jikin mom ta fada tana sakin kuka da iyakacin karfinta,,
Girgiza kai dad kawai yayi ya cigaba da kurbar ruwan shayensa yanzu lamarin safina ya fara damunsa sai yanzu yake ganin tsantsar laifinsa wurin tabarbarewar tarbiyyar ta,,
Yayinda mom hankalinta ya tashi nan ta dada rungumeta jikinta kamar zata maida ita ciki tace lafiya safina maiya farune,ko bakida lafiya ne ta jiro mata tambayar hankali a tashi,,
Cikin kuka safina ta soma maganar yanzu dad haka zaku bari karatuna danaci buri ya wuce ni maiyasa ne haka dad yanzu meena takirani suna gab da rufewa kaki saka baki dad wallahi ni gaskiya na fasa wannan auren ta a fada tana kallon dad din,,
Dagowa yayi da idanunsa rai a baci yace wallahi da hakan kikayi da tun farko yafi miki ai duk Wanda baya jin maganar manya to bazai ki ganiba ba safina India Khalil ne gaki gashi nan zabi ne nayi miki da dan uwanki Habib kika nuna rashin isata sai gashi naki zabin yana neman watsa miki kasa a ido ,,
Maida Kansas yayi ga TV ya cigaba da kallon sa hankali kwace dukda yadda zuciyarsa Ke masa daci tunda ya taba zagayawa garden din gidan ya tsinkayi hirar maryam din da ya Khalil maganar auren ta kara fita daga kanshi,donshi ba mutum ne mai son zuciya ba donma yaki samun goyon baya daga daddyn Khalil din da tuni a rushed maganar,,
Haba don Allah alhaji maiye kakeyi haka yarinyar tazo mana hankali tashe kai baka kwantar mata da hankali ba sai kayi kokarin tayar mata ,,
Banza yayi da ita tareda daga wayar sa dake ruri yana amsa sallamar fuskar sa cike d faraa sosai ya shiga yin murna yana fading alhamdulillah ,masha Allah, haka akeso Allah ya taimaka kasameni a falo, yana gama
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 32