ta yadda zata fara,kwanciya tayi kawai tana Jan abun rufa"ya jikin naki"taji muryar sa ya tambaya ,
"Da sauki,i n a kwaa na"" ta fada a d'arare ita kanta taji abun banbarakwai itace da gaisuwa balle shi Wanda har saida ya kalleta don tabbatar wa kafin ya amsa da lafiya lau ya kuma lumshe idanunsa yana fadin inama Kinyi nadamar kafin lokaci ya kure miki ,inama kin chanza halayenki tun a da ba yanzu ,inama kin sauya rayuwar ki a lokacin da kowa zaiyi farin ciki da hakan,,
Tana son yi masa tambayoyi amma ta kasa bakinta yayi mata nauyi musamman yadda ba sabawa tayiba indai bada dad ko mom ba sai meeena da wuya kaga tana maganar arziki da wani ,so take ta tambayi jikin dad dinta ,da kuma maryam amma ta kasa haka ta hakura ta lafe cikin mayafi tamakr bacci yake yi har gari ya waye sosai ,,
Alhamdulillah jikin harira itama ta samu lafiyahar mikewa tanayi sai dai Anyi mata Karin jini don ta jima tana zubar wa ,,
Hakama Alhaji shima ya samu lafiya an cire masa bullets din guda biyu yanana zagaye da jami'an tsaro ana jiran samun lafiyar sa a izakeyar sa zuwa koto,,
Yayinda duk wani bayani da bincike Anyi shi tsaf a cikin gidan Alhaji Bayan yaransa da aka kama wasu kuma sun mutu,,
Dad dai kai jikin sai addua domin har yanzu numfashinsa yaki dai dai ta jinisa yaki suka kuma π
*mrs noour*βπ»
[7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *π΄π΄KARFIN IKOπ΄π΄*
π±π±π±π±π±
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me @pheeymarrh
*HIKMAAH writers association*
Edited byππ» *oum Zahara*π
Dedicated 2my lil sisππ» *Maman Sultan*π
Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*naji dadin comments dinku sosai fans Allah ya bar kaunar*π₯°π₯°π₯°
*second t d last page*π₯΅
π
Ώβ6β£9β£
Dad dai kam jikin sai addua har yanzu numfashin sa yaki dawowa normal jininsa yaki sauka,,
Tashi tayi daga kwanciyar tana kallon inda yake, vacci yake yi da alamu mai nauyi ne don har charbin dake hannu sa ya fadi saukowa tayi ta isa gabansa , ta tsaya kallonsa takeyi cike da so da kauna sosai soyayyar sa tabi duk jinin jikinta,, kaunarsa tabima jinin da tsona da b'argon jikinta hannu ta sanya ta share hawayen tana tausayin kanta mai ya sanya ta kasa chanza ratuwar ta,,
maiyasa bata yi nadama ba tun tuni,,
mai yasanyi idanunta da zuciyarta kasa gane mata gaskiya sai yanzu da lokaci ya kure mata,,
hannu ta sanya ta shafa dan tayin cikin dake jikinta soai take jin kaunar shi Wanda batada tabbacin yadda zata kasance musu karshe gidan yari zata haifeshi karshe achan zai fara rayuwar shi kuka ne ya taho mata da karfi da sauri tafada toilet tasakeshi da iyakacin karfinta Bayan ta kunna pampo gudun kar ya Habib ya jiyota,,
Ta kai kusan minti asirin kafin ta lallashi zuciyarta tadaurayo fuskarta ta fito har lokacin bacci yake yi dukda a takure yake baiji dadin kwanciyar ba,, mayafin da ta rufa tadauko tarufe mata jiki da alamu bai samu rintsawa ba cikin dare duba da yake baccin,,
Bude kofar tayi tafita tasoma binciken dakin da dad din nata yake Bayan ta tambayi wani doctor sama tahaura tashiga dakin tana sallama a hankali,,
mom ce ta amsa mata ta nufi gadon dayake tana gaida mom da kuma tambayar jikin dad din,,
Amsa wa tayi da alhamdulillah yana ki jikin kema,,
Da sauki mom har yanzu bai farka ba ne ?safinar ta tambaya tana zama gefen gadon kadan,,
Eh mom ta bata amsa aidama lokacin farkawar sa batayi ba sai zuwa gobe ,,
Adduoe tayi masa sosai tana share hawaye mom na amsawa da ameen,,
Duk Wanda yaleko dakin sai ya saki murmushi saboda yadda suka kwanta kai da gani kasan akwai soyayya kauna hade da shakuwa mai karfi tsananin su sun jima suna bacci a haka musamman yadda kowa cikinsu ya rabu da bacci kwanakin baya,,
Sai kusan karfe uku suka farka maryam ce ta fara farkawa amma jin yadda ya kwakumeta jikin sa tamkar mai tsoron kada a sace ta ya sanya yin lakur itama tana tuna halin data shiga a kwanakin baya burinta daya kawai taji Allah yasa cikin jikinta nanan lafiya don har yanzu jinin bai daina zuba mata ba,,
Hannun sa taji ya dage rigar ta yana shafa cikinta zuwa mararta,rintse idanun ta tayi tana jinsa bata tanka masa ba tana Jan numfashi a hankali,,
""Ya lafiyar baby na ya fada cikin kunnenta,""
Kara rintse idanu ta tayi tamau batada takammamiyar amsar dazata bashi juyowa tayi da jikinta tana fuskantar shi tareda sake shigewa jikin sa kanta na bisa kirjinsa,
My hayat,ta kira sunan shi cikin muryar rada,
Bai amsa ba shima sai kiss dayayi mata bisa kanta,,
Lumshe idanu tayi kafin ta bude kamar maiyin rad'a tace ina harira ne da fatan tana lafi..
Knocking din da akayi ne ya sanya ta yin shiru da sauri ta mike ta zauna kokarin tashi takeyi amma ya rike mata hannu gam dukda hannun daaka harbeshi ne dole ta zauna tana gyara dan kwalenta,,
Amsawa yayi kafin aka shigo doctor ne hade da nurses guda biyu,,
Hannu ta sanya ta cire rukon dayayi mata shima baiyi musu ba ya sakar mata ta koma bakin gadon ta ta zauna ,hade fuskar yayi tamau tamkar Wanda uwarasa ta mutu har aka gama dubasu suka fita tasan kishi ne kawai kecin zuciyarshi tunda babu mayafi jikin ta Allah ya taimaka ma doctor ya bawa nurses allurar suka yi mata,,
Suna fita wayar sa ya dauka dake gefe akashe take tunda mommyn ta kawo masa kunnawa yayi ya shiga dialling number mommyn,,
"Hello mommyn pls ki aikomin da hijabs yanzunnna yana gama fadar haka ya kashe wayar batareda yajira jin ta bakinta ba ya rintse idanu sa kawai tamkar mai yin bacci,,
Idanun kawai ta zuba mashi tana kallonshi sometimes inyayi Abu har mamaki yake bata dukda yakan sauya kaso tamaanin bisa Dari insuna tare yakan rage miskilancin nan da shariya amma maganar kishi ko yaya sai ta ringa fama dashi kenan kafin ya sauko,,
Mommyn ma girgiza kai tayi kawai tana fadin son Allah ya shirye ka tasan tsiyar tashi ce mikewa tayi ta hau sama tabada sabbin hijjabs guda hudu akai musu don sai yamma zata koma tunda asibitin basu cika son masu zamaba sun fiso barin patient shi kadai saiko su inzasu lura damarar lafiya,,
Fitar ta babu dadewa yaji ana tashin sa da kyar ya iya bude idanun cikin bacci yana kallon mai tashin nasa doctor ne,,
Sannu yayi masa,kai kawai ya gyada yana kallon bed din tun kafin ya tambaya ya mike yana kallon dakin ,,ina patient din take don mun jima tsaye bata nan har toilet nurse din nan ta leka,,
Jimm yayi kafin ya tashi ya leka toilet din da kansa batanan hankalinsa yadan tashi amma bai nuna musu ba yace maibe tana wurin dady tane bari na duba ya fice da sauri zuwa upstairs,,
Sai da mom ta bashi izinin shigowar kafin ya shigo da sallama sannu yayi mata yana kallon safinar dake kusa dashi ajiyar zuciya ya sauke a boye yana sake gaida mom,,
Fuskar a sake ta amsa masa da tambayar ya kokari tana zuba masa godiya da addua,,
Fita tayi mom din waje tace bari taje gida ta dawo ,,adawo lafiya sukayi mata dukkanta,,
Sannu tace masa tana dukar da kai,,kitashi kije likita na jiran ki,,
turbune fuskar tayi hawaye na zubo mata a shagwabe tace wallahi ya Habib naji sauki don Allah kace asallame ni banason allurar nan haka pls,,sosai ya shagala da kallon ta yadda take yi tamakr wata karamar yarinya,,
Kara turbune fuskar tayi tana langabar da kai ita tuannain ta tsare gida yayi pls mana yaya ta sake fadar da karfi,,
Da sauri ya didaita kansa ya tamke fuskar yace maza tashi yanzu ki huce lafin raina ya baci,,
Ranta ya baci da tsawar dayayi mata itafa bata son tsawa da daga murya taski tayi a ranta ta mike ta fice badon taso ba sai don zuciyarta data tuno mata halin datake ciki, (mai hali bayafasa halinshi,),,
Shikansa yayi mamakin fitar tata maganar kawai yayi amma bai taba dauka zata bi umarninsa ba,,
Baifi minti talatin tsakani ba mai aiki ta kawo mata hijab din tareda baban foodbowl ta gaidashi ta ta tafi lokacin har bacci ya sake dauke maryam bai tada itama don ya lura tayi nisa kuma tana jin dadin bacci dukda ta lullube jikinta duka da marufi har kusan fuskarta ,toilet ya shiga ya samu ya watsa ruwa da dabarar yayo alwalar ,sallolin yayi kafin ya koma ya bude foodbowl din lafiyyan fruits salads yho ne maidan sanyi ,daukar plates yayi ya zuba da yawa ya sanya chokali fork yakoma kan gadon datake ya ajiye a gefe table din karfen dake kusa sa gadon ya matsa ya sanya hannun sa ya yaye rufar da tayi duka ,sake gyara kwanciya tayi tana hade kafafunta da jiki wuri daya,,
Ya firgita sosai da ganin staining din jini a rigar ta har ya shafi bed sheet din da sauro ya Waro idanun yana kurawa wurin ido nan take zuciyarta shi ta chanza salon bugawar ta hankalinta yayi matukar tashi jini kuma shidai a iya saninsa koda ba likita bane shi amma yana san tabbas mace mai ciki batajini haka koda akace wasu nayi ai shi ba itaba ganain tayi zubar jini haka ba lokacin period dinta ba koda suna kwance zai sameta kuwa ,amma baisani ba don bayason ya yarda da abunda zuciyar shi ke gaya mishi dole zaije wurin doctors din suyi masa bayani kuwa,,
Zucoyarsa babu dadi ya matsa kusa da fuskarta yana hura mata iska a idanun ta tareda Jan hancinta ahankali dama hakan yakanyi mata idai zai tada ita aikuwa saigashi tana bude idanun a hankali cikin bacci ganin sa yasata sake juyowa ta sanya hannu ta duka biyu ta zagayo da jiginsa ta shige tana gyara fuskar ta bacci zata koma,,
Dukda ransa a jagule yake sida yadan murmusa kadan hanninsa ya sanya marar ciwon ya cire rikon datayi masa kokarin maidawa takeyi ganin haka ya sanyashi dagata gabadaya zaune yana shafa fuskarta yaja dogon hancin nata da dan karfi yana dage mata girar,,
Dole ta bude idanu tamkar zata yi kuka itaba sallah zatayi ba ya barta saida ya tashe ta,,
Maza ki wanke baki kizu ya fada a takaice yana matsawa gefe ,,
Sauke kafufunta tayi kasa ta wuce toilet tayo brush ta fito don itama yunwar takeji sosai ta dawo kusa dashi tun kafin ta zauna ya miko mata hijab babu musu itama ta amsa ta sanya kafin ta zauna kusa da shi fruit salad din ya fara diba yana bata ahankali tana sha ,said a ta shanye shi Tass ya sake dado wani da sauro ta amsa tana girgiza masa kai alamun ta koshi,,tsare ta yayi da idanu alamun are usure deba ta somayi takai bakinsa tana dadin eh,shima yasha sosai don ya jimababu wani abun kirki a cikin sa,,
Ajiye plate din tayi a gefe ta dawo zata zauna da sauri ya matso da ita ta zauna cinyarsa,ya soma matsa mata hannun ta a hankali baki bani amsa taba ya babyna nayi kewar shi sosai ,,zame jikin sa yayi ya kwanto da kanta bisa kirjinsa murya cike da damuwa yace gayamun mai ya faru Bayan zuwan ki asibiti,,
Bakaramin fitgita tayiba dajin tambayar sa sosai kirjinta yashiga bugawa cikin sauri sauri mai zata gaya masa ita kuwa tace Alhaji yaso keta haddin tako kuwa mai,,
Ta Dade shiru tana nazarin abunda zata gaya masa har saida ya matse hannun nata da karfe dole ta gaya masa kamar yadda mommyn ta bata shawara saboda su yi hubbasan ganin an dauki baban mataki akan Alhaji zayyane masa abunda ya faru tayi saidai bata gaya masa artabun dasukayi da Alhaji ba kawai tace ganin sa ya shigo babu suturar arziki jikinsa ya sanya ta firgicin da nan take jini ya balle mata adaidai lokacin kuma harira ta shigo ta kawo mata dauki,,
Sun Dade shiru tana jiran maganar sa taji shiru dagowa tayi ta kalleshi da sauri ta mike zaune a tsorace ta rikice da ganin yadda fuskar sa ta koma sai fitar da mugun huci yakeyi tana ganin yadda zuciyarta shi ke bigawa da karfi tamakr zata fado kirjinsa ga hawaye dasuke kwaranyo masa wadanda ko baa gaya mata ba tasan masu matukar zafi da radadi ne ,,
Murya na rawa tace pls ya tana dafashi kasa Karasawa tayi saboda kallon daya Watson mata ,,
Daodai lokacin likota ya shigo sake duba su da sauri ta share hawayen daya farazubu mata,,
Kokarin duba hannun sa likita yakeyi amma ya dakatar dashi murya a kausahshe yace yanason sanin result din Maryam yanzu nan,shima likitan baiyi musu ba ya shiga dubamasa ganin matarsa ce nan take ya sanar masa abubuwan dake damunta harda zubewar ciki sallati yayi da karfi yana dafe kansa bayason jin karshe yanzu duk yadda yayi rayuwa shi kadai gida tamkar maye cikin daya kwallafa rai aknasa ya futa akan wadannan lallai safina nayi rantsuwa naki mamakin siyafi na kowa muni,,
Na kowa muni wallahi ya maimaita da kafi tana buge tray din silver dake aje da allurar da sryge gaba daya jikin sa ya dauka rawa shi kanshi likitan said a yayi danasanin fada masa balle maryam wacce tayi tsuru jikinta itama yana kadawa,,
Ina bukatar sallama yanzun nan ya fada yana mikewa cikin matukar fushi kokarin bashi baki da hakuri suka somayi amma ya dakatar dasu ta hanyar daga musu hannu NOW I said ya fada idanunsa sunyi jajur ,dole likitocin suka fita,zagaye yasoma yi a dakin ya Dade a haka kafin ya zauna bakin gadon tareda tallafe kansa daya soma barazanar tarwatse masa ga sutin kukanta dake Dada digunzuma zuciya shi tunawa dayayi da maganar likita na jini ta da yahau ya sanyashi sauke ajiyar zuciya mai karfe tareda cije labbansa na kasa huci mai zafe ya ke fitarwa tasowa yayi ya dawo inda take mai ya sanya kila fita ne daga asibitin Bayan na gargadeki da hakan eyeh ya tambayeta rai a hade ,,
Tabbas tayi kuskure ita kanta tasani amma yazatayi da kaddarar da Allah ya rubuto mata ,
Batada amsar da zata bashi saima sautin kukansa nata data Dada karawa Wanda yakara fusata shi wurge yayi da plate din da suka gama shan fruit salad yana juyawa hannun ta ya damko da karfi ya dauki wayar sa number driver ya kira ,
Tana dagawa yace yazo asibiti nan da minti uku kafin ya fito,,
Janta yayi suka fito daga dakin Wanda yayi dai dai da zuwa baban doctor din sai dai shima duk yadda yaso ya tsaida shi ki yayi dayaga zai Tara mai masu bada baki kawai saiyaja matarsa suka wuce ,,
Allah ya taimaka driver ya isa dai dai lokacin suna fitowa sai gumi yakeyi saboda tashin hankali duk zatonsa wani abune ya faru don bai taba samun haka ba daga wurin ya khalil din,,
Shima likitan wayar daddyn yakira ya sanar masa halin da ake ciki ,babu yadda zaiyi tinda harya fice daga asibitin yace zaije gidan yasameshi kawai,,
Tunda suka isa ya bude motar ya fito itama ya bude mata ya kawo hannun ta har parlon ya kaita kafin ya juya ya fice motar ya sake komawa yashiga tana kallonshi driver yaja suka fice daga gidan kuka ta saki da dan karfi tasan hakan zata faru dama,,
*mrs noour*βπ»
[7/11, 17:44] +234 816 822 9024: *π΄π΄KARFIN IKOπ΄π΄*
π±π±π±π±π±
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me @pheeymarrh
*HIKMAAH writers association*
Edited byππ» *oum Zahara*π
Dedicated 2my lil sisππ» *Maman Sultan*π
Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
π
Ώβ7β£0β£
πππππ
Kuka ta saki da karfi tasan hakan zata faru dama da kyar ta ja kafa zuwa cikin parlon ta kwanta nan kujera ta juya bayanta tana cigaba da kukan a hankali,,
ita kanta maganar zubewar cikin ta daki zuciyarta amma ya zatayi ne da kaddarar ubangiji,,
Ta dade kwance anan har akayi magrib dayake babu Wanda yasan da shigowar tata dukda tana parlon sai da mommyn ta fito tsaf cikin shirin ta na zuwa asibiti ta ganta kwance,,
Hankalinta ya tashe da sauri ta karasa inda take har lokacin bata daina zubar da hawaye ba cikin damuwa mommyn ta rungumeta tana share mata hawayen,
Sai da taga ta daina zubar da hawayen kafin ta tamvayeta ko lafiya ,nan ta gaya mata yadda suka yi ta karashe tana sake fashewa da wani kukan mommyn bana son yace zaidauki wani mataki akan safina nina yafe mata kodon saboda dad gashi kince bayada lafiya kowa bai wuce yin kuskure ba Ai mommyn,,
Ajiyar zuciya ta sauke da karfi tana gyara zama kafin ta kalli maryam din da kyau tace ai daukar mataki ya zama dole kuwa koda kin yafe mata muma mun yafe mata toh kuwa hukuma bazata kyaleta ba duba da yadda sunan ta yake cikin case din nan don haka sai hakuri damuwar ma itace na lafiyar son amma gyada kai tayi kafin ta dauki jakar ta dake gefe data fito da ita ta bude ta dauko wayar ta tashiga neman layin sa duka layinkan nasa kashe suke dole ta aje tareda kama hannun maryam din suka haura sama har dakin ta da kanta ta hada mata ruwan mai zafi tace tashiga ta gasa jikinta,,
Shima chan daddyn tunda likitan ya sanar dashi yake kiran layinsa amma a kashe yanachan wurin police station komai saida aka gabatar masa dashi da yaran Alhaji ya nemi kwararren lauyen su yasameshi a station din suka gama magana bayason bata wani lokaci inda washe gari zasu tattara su mika kara ga court dukda dai da sun dage akan sai Alhaji yasami suki hakan ne kaidar su kafin akai court amma dyake abun na masu dashi ne lauyansa nazuwan kuwa saida yasan yadda yayai suka amsa don ba kara min Abu bane sunema Alhaji su rasa a hospital din, tunda alhajin babu laifi ya farfado amma ciwo nanan bai warke ba,,
Dakin mommyn tayi zaman ta Bayan tayi wanka taci abinci,,
Sai dare ya dawo suna zaune a parlon sama dukkansu daddyn yana tambayar maryam din abunda ya faru ya shigo da sallama ciki ciki,,
Babu Wanda ya amsa mishi sai ma idanu da suka zuba mishi,kallo daya yayi musu ya kauda kansa yana dada tamke fuskar wucewa yayi kusa da mommyn ya zauna,
Sauke idanunta tayi kasa ganin yadda yaki ko kallon inda take,,
Sannu Ku da gida ya fada a takaice yana zamewa ya kwanta akan kujera tareda dafe kansa,,
Babu Wanda ya amsa mai still dai su mommyn idanun su na kanshi,,
Ganin bashida niyyar yin magana ya sanya daddyn rufe shi da fada,sosai ta inda yake shiga banan yake fita ba musamman akan barin asibitin da yayi da danyen ciwo,,
Rintse idanu wan sa kawai yayi batareda yace komai ba har yayi fadan ya gama,,
zama yayi yasoma bashi hakuri a sanyaye tareda cewa yanzu ma daga asibitin nake kullum zan dinga zuwayana gama fadar haka ya mike ya fice zuwa sashen shi baya son doguwar magana a yanzu duniyar tayi masa daci Hutu da kadaici kawai yake bukata ,,
Girgiza kai kawai suka yi mommyn na fadin Allah ya kyauta tashi kije ki kai masa abinci ta fada tana kallon maryam,,
Da kanta ta Shiga kitchen ta hada masa abinci tareda coffee ta nufi dakin sa at bedroom takai masa baya dakin sai dai tajiyo karar ruwa da alamu yana wanka ne,,
Ta Dade zaune a dakin kafin ya fito kallo daya yayi mata ya kauda kansa yawuce wurin mirrow ya ba kujerar ya zauna ,sannu tayi masa a sanyaye tana kallonsa,,
Bai amsa ba saima bude mansayayi kokarin shafawa yakeyi amma ya kasa tasowa tayi ta dauki man sai kawia ya mike ta wuce drawer,jallabiya ya dauka ya sanya da kyar tana tsaye tana kallonsa hawaye tab a idanunta yana gamawa ya haye gado ya juyamata baya tareda rufe jikin sa da lallausan bargon sa,,
Yana jiyo sanda ta soma kuka amma haka ya daure zuciyar sa yashare ta yafison sai sun amshi hukuncin su a hannu kafin ya kulata don bayason abunda zai sanya ta rinjaye shi akan ya kyale safinar,,
Sosai kukanta ke taba zuciyar shi amma yayi buris da ita ta Dade zaune akan stool din har bacci ya fara cin karfin ta ta sauka kasa kan carpet ta kwanta,,
Saida ya tabbatar da tayi nisa a baccin kafin ya saiko ya dauketa ya maida ta kan gadon,,
*after two weeks*
Sanye yake cikin suit blue black sun matukar amsar shi idanunsa sanye da eye glass zaune yake bakin gado yana aiki cikin system dinshi jefe jefe yana daukar mug ya karbi coffee ya aje,,
Yayinda maryam take chan gefe zaune bisa resting chair doguwa dake bedroom din ta zuba tagumi tana kallonsa a azahiri amma a badini kuwa tayi nisa wurin tunanin irin zaman dasukeyi da ya khalil din tunda abunnan ya faru Sam yadaina saurararta tarasa meye laifinta a wannan Abu daya faru dukda ba wulakanci yakeyi mata ba, amma silent dinshi yafi komai daga hankalinta sometimes ma ko kuka yaga tanayi zai rarrashe ta har tayi shiru batareda yace mata komai ba,,
Muryar sa taji a kanta yana fadin tashi muje,yana gama fadar haka ya wuce mikewa tayi tabi bayanshi jiki a sanyaye har motar yana tsaye ya bude mata murfin motar shiga tayi ya rufe saanan ya zagayo ya shiga dayan barayin driver ya jasu,,
Mutane ne dankam cikin babbar court din dake garin Abuja daga bangaren Alhaji ,zuwa nasu ya khalil yaune zaa fara sauraron kara kowanne baraye da kwararrun lauyoyinsa,,
Sosai aka fafata inda kuma cikin hukuncin ubangiji komai yazo da sauki saboda shaidar harira inda ta labarta komai data sani,,
Kusan awa biyu kafin aka dage shariaar zuwa wani sati tareda,,
Zaune take gefen dad din tana bashi kunun gyada a baki yana karba a hankali jikin nasa har yanzu sai a hankali yayinda mom da ya Habib ke zaune kan kujerun duniya daga gefe ,,
Knocking akayi dukkansu suka kallo kofar a lokaci daya kafin ya Habib ya amsa,mutane biyu ne kowannen su sanye da suit bakake wuyansu sakale da igiyar id dinsu,,
Saida suka gaidasu kafin sukace daga court sike takardar sammaci ce ga safina,,
Saida mug din hannun ta ya fadi saboda razana jikinta yayi sanyi kalau sai zufa tashiga keto mata yayinda dukkansu suka yi mutuwar tsaye aka rasa mai amsar takardar cikinsu dukda suna expecting hakan dad ne ya mika musu hannu ya amsa tareda yi musu godiya,,
Da kyar ya tattaro jarumtar sa ya karasa wurin dad din yana fadin kawo dad in karanta mugani,,daga masa hannu yayi yana warware takardar tsaf ya karance ta takardar ce akan tuhumarta daakeyi ana bukatar ta a court saboda amsa wasu tambayoyi,,
Idanu kawai ya zuba mata Bayan ya ida karantawa yayinda ita kuma tayi kasa da kanta tanakuka a hankali,,
Mom ma hawayen ne ya balle mata sai ya Habib din ne ya soma kwantar musu da hankali shima na dauriyar kawai yana tausayin dad sosai da halin da zai shiga domin ba karamin so yakeyiwa safina ba dauriyace dama kochan vaya,,
Sosai dad din yayi mata fada har ya kasa daure wa saida kwalla ta zubo masa,,
Bayan sati daya Anyi zaman koto inda batareda shan wahala ba safina ta amsa laifinta tareda su Alhaji tunda ga tarin hujjoji Wanda ya bayyanar da gaskiyar magana tayi kuka sosi inda alkali ya yanke mata hukunci shekaru bakwai gidan yare tareda taear kudi sosai ta fashe da kuka mai taba zuciya yan uwa nta harta da maryam din kuka take sosai,,
Hikunci kisa ga Alhaji Bayan yayi shekaru goma sha hudu gidan yaro tareda aiki mai tsananin saboda cases din NASA sunada yawa ,wasu yaran bashi juwa duk hukuncin kisa ne,
Hajiya ladi itama zaman gidan kaso ne har karshen rayuwar ta tareda horo mai tsanani,,
Haka aka fita dasu suna kuka sosai kowa na nadamar abunda ya aikata musamman safina wacce ko a mafarki bata taba tunanin irin wanna rayuwar zata risks taba sagashi abunda take ganin ita mai *karfin iko* ce dashi Allah ya nuna mata nashi *karfin iko* ne gaskiya,,
Jingina kanta tayi bisa kafadar sa tana kuka sosi yayinda tana jiyo sautin ajiyar zuciya dayyai hannun ya sanya ya rungomuta jikinsa tana tausayawa dad da safinar kanta ita da zaabi ta tata wallahi data yafe mata ita,,
Mom kuwa zube wa tayi awurin numfashi sama sama nan yan uwa suka rufar mata har sanya kafa daya a mota tagano mom din nata da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 31 Chapter of 32