An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
๏ปฟ[7/11, 17:42] +234 816 822 9024: *๐ด๐ดKARFIN IKO ๐ด๐ด*
*๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ*
Written &story by *@PHEEYMARRH*
pheeymarrh@gmail.com
*HIKMAAH writers association*
Edit by๐๐ป *OUM ZAHRA*๐
DEDICATED 2 MY LIL SISTER๐๐ป *Maman Sultan*๐
ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ุงูุฑุญูู
.
Ya Allah yadda kabani ikon fara wanna novel maisuna *KARFIN IKO* lfy,Allah ka bani ikon gamawa lfy,Allah ya bamu ikon yin amfani da abubuwan fadakarwa dake ciki ,(ameen)..
๐
ฟโ0โฃ1โฃ
Zaune take bisa daya daga cikin kujerun dining din tana yin breakfast, tauna abincin takeyi Kamar bataso amma duk da haka gani take sauri takeyi yayinda takara dago idon ta ta kalli agogon bango da keta aiki,karo babu adadi ta kara Jan wani dogon tsakin mtsww,,
Yaya akayi ni baby meya faru tun dazu kike faman jera tsaki ,Momyn ta ta tambayi ta,,
Saidai ta kara yin wani tsakin tareda harara Kamar Wanda takeyi domin shi yana kusa da ita, kafin tace momy ki duba kiga time 2mins to eight, amma har yanzu wanna dan rainin hankalin bai zoba, i don't know who he think he is, tsaki ta kara ja tana fadin wahalalle ,dan talakawa kawai sai girman kan tsiya Kamar shidin wanine, wlh in.....
Ya isa haka,, momyn ta katse ta ,tana cigaba da fadin Kinga baby dama kin rufa bakin ki before daddyn ki ya ji,,kinsan indai akan HABIB ne yanzu zakuyi fada, nasan duk inda yake he's on his way here saboda haka pls calm down kigama break fast ki dauko bags dinki before he come,,.
Zunburo baki tayi cike da shagwaba Kamar yar yarinya ta ture plate din dake gabanta ta miki tana bubbuga kafa ta nufi step tana mita ,ai dama indai wanna dan talakawa ne baya laifi awurinku saini kuma saina rama wlh ,,.
Murmushi momy tayi tace baby rigima kullum dai Kamar jaririya haka take jin kanta ,Allah ya shiryar mana Ke,,.
Tana step din karshe ta ga daddyn ta ya fito daga part dinshin da gudu ta karasa ta fada jikinshi morning dadna na furta a hankali fuskarta ciki da fara'a Kamar back ita Ke fushi ba,,
Morning baby na kin tashi lafiya ,,
Fyn dad ,,
Ya shirye 2 kin kammala ko coz kada yazo yana jiran ki,,.
gimtse fuskarta tayi tareda janye jikinta daga daddyn tace tun dazu fa nake jiranshi daddyn har yanzu bai zoba kuma na gama duk shirina tun dazu,,.
Assalam alaikum ,muryarsa mai dadin da taushi ta karad'e parlor din,
Juyowa sukayi yayinda daddy ya saketa ya nufi inda yake yana amsa sallamar, ita kuma kallo ta kare mai sanye yake da kakin sa na sojojin Wanda yai masa matukar kyau tareda kara mai kwarjini ,, tsaki ta kara yi tana fadin ko don yaga yana da kyau ne yake wannan jin kan ohho๐คท๐ปโโ,aikin banza ta wuce dakinta ,yayinda ta barsu suna gaisawa da su momy.
Koda ta shiga dakinta kwanciyar ta tayi domin ta gama shirinta amma bazata sauka ba sai ta bata mai lokaci Kamar yadda yasata jiranshi,,,..
Har kasan 45 mins bata sauko ba har suka gama maganar da ta shafi aikin su , daddy ne ya duba agogon bango ya juya ya kalli mommyn dake danna wayarta, yace duba yarinyar nan har yanzu ta fito mana ya na jiranta kuma tace ta gama shiryawa amma ta shige daki tayi zamanta,,.
Tana kokarin mikewa lami ta kawo ma Habib abun motsa baki, tace lami maza kije ki duba baby daddy na jiranta su tafi,,
Amsa wa tai da toh tareda juyawa ta nufi dakin zuciyar ta na bugawa saboda tsoron cin mutuncin ta ,,ilai kuwa tana knocking ta shiga tareda sallama tun kafin ta karasa ta jefo mata tambaya ,lfy na kira ne na hana ki shiga min daki ba tareda na bukaci ganin,,
Yi hakuri anty daddy Ke kiranki, ,
Mikewa tayi ta dauki wayarta kawai ta juya tana fadin ki biyoni da wadannan ,..
Koda ta fito parlor bata iske su daddyn ba kai tsaye waje tanufa wurin parking lot Wanda motoci ne kusan guda bakwai kala daban2 masu tsadar gaske ,kusa da daddyn ta karasa ta rungume shi ,haka ma mommyn har tana hawaye na rabuwa da iyayen ta haka ta juya tahau daya daga cikin motocin ta zauna gidan baya yayinda Habib yake gaba gefen driver ya ja suka fice da gudu tana dagawa iyayenta hannu , Safina kenan Wanda iyayenta ki kiranta da baby,,,.
*Kano state*
Kofar nassarawa..
Mero,mero wai ja'irar yarinyar nan INA kika shige ne kina juna , inna ta keta faman mita yaye labulan dakin tayi Wanda ya soshe har baka ganin zanen jiki, kyakkyawan ruko kamai zai iya yagewa ,saidai a wanke yake babu wani digon datti dake jikin shi, zaro ido tayi waje Kamar wacce tayi gamo ta karkace kai cike da fitina ta soma fadin ,,kinga matar baba ki fita idona tun kafin in miki mugun aike ,Yaya zaki tasa yarinya a gaba kina kitsa mata mugayen halayya irin taki ta gado wlh kekam kinyi asara babu abunda zama da Ke yakare mu dashi bamda bakin ciki da m...
Inna don Allah kiyi hakuri sallama mukeyi maryam ta furta muryarta a shake alamun taci kuka har ta gaji idanun nan nata sunyi jazur Kamar basuda digon haske a cikin su,,,
Amshi nan inna tayo mata dakuwa tana fadin zaki fito kokuwa saina iskoki na Zane miki jikin ki ja'irar yarinya ai kin rigada kin gama gadon mugun hali irin na uwar ki, ki tashi ki shige muje ana jiranki tun dazu ,fusge hannu maryam tayi da karfi daga jikin mahaifiyar ta wacce kanta Ke kasa tana cigaba da goge kwallar dake ta zuba daga idanunta ,
tana ji tana gani haka inna ta tasa keyar maryam suka bar gidan tana jin sautin kukan ta daya karu, daga hannuwan ta tayi tana addu,'a ya Allah kasan halin da muke ciki Allah ka nuna *karfin IKO* ka akan wadannan bayin naka ka tsare mun maryam a duk inda zataje, fashewa tayi da kuka sosai tana tunanin halin rayuwa, duniyar kenan....,..
More cumments more typing
*Mrs noour ce* โ๐ป
[7/11, 17:42] +234 816 822 9024: *๐ด๐ดKARFIN IKO๐ด๐ด*
๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
*HIKMAAH writers association*
Edited by๐๐ป *oum Zahara*๐
Dedicated 2my lil sis๐๐ป *Maman Sultan*๐
ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
๐
ฟโ0โฃ2โฃ
Jan hannun ta takeyi tana zabga sauri tana mita so kike ki dauko mugun hali irin na matar baba wacce auranta banda masifa babu abunda ya haifar mana Ke ba saurayiba baki da Wanda zai tsaya miki kin dage sai karatun zamani ,kuma karatun zamanin nan naga ubanki ma har ya koma ga mahalincin shi ko zo in karshe bai saniba ,saike zaki dage akan Abu daya dan gadon duk kun tsiya tashi agun karatun zamani Wanda bazai yi miki amfani komai ba, toh wlh mun saka kafar wando daya nida Ke dole kije aikatau ,abunda kika samu ki dawo gida kiyi auranki...,
d'ago wa tai a razani tana duban innar wacce bata fasa mitar datake yiba,a raunane tace aure kuma inna shekara ta nawa dahar zanyi aure Kamar ina Kay....,,
amshi nan inna tayi mata dakuwa Wanda yayi daidai isar su bakin titi,adaidaita inna ta tare suka hau ,
tafiyar minti ashirin sukayi Wanda babu abunda maryam takeyi sai share hawaye da tunanin makomar rayuwar ta ,wai itace inna Zata kai aikatau saboda talauci ko dai saboda son zuciyar koko saboda *karfin IKO* ...,
Sallamar mai adaidaita tayi tareda daukar yar jakar kayan maryam ,in kin gama tunanin kya biyoni dake gidan ba boyayyen bane gareki,
sauka tayi tareda bin bayan inna bawani tafiya sukai mai nisaba suka iso Kofar gidan, tura Kofar inna tayi suka shiga soron gidan kafin tsakar gida inna tai sallama,
Saidai tayi sau hudu kafin matar ta fito tana amsawa ,amin wa'alaikum salam lale inna Ku karaso Ku shiga
Dan madai2 cin gida ne mai dauke da dakuna uku da bayi a waje da kitchen dakuna ruwa ta kawo musu ,tukunna ta zauna suka gaisa ,
Inna ta dora dacewa toh gatanan marainiya ce a rike amana zan dinga bulluwa bayan kwana biyu don jin lafiyarta, Hajiya ladi tayi murmushi wanda ita kadai tasan nufin shi tace kar ki damu inna Insha Allah in maryam ta dawo bazaki ganita ba ai garin Hutu ne da jin dadi yadda jikar nan taki take tubar kallah ai bazaki gane taba ai Abuja ta wuce yadda kike tunanin,...,
Dagowa maryam tai arazane tana ware manyan idanun ta tana kallansu ,Abuja kuma can za'a kaita tun daga Kano babu kowa nata ,kuka takeyi kasa2 tana hadiyar zuciya wai yaushe inna tazama haka inna mai sonta da kaunarta bayan tasan illolil dake tattare da aikatau shine za'a turata har wani garima can uwa d....,
Merooh..., firgigit ta dago fuskarta sakamakon kiran inna ya katse ta daga tunanin data Ke ,toh mero na nizan koma don Allah kiyi biyayya nasan kina da saidai kwana biyu da uwar ki keson bataki amma tunda Allah yasa nayi wa tufka hanci shikenan ,zan rinka zuwa akai 2 Hajiya na kira awaya ina jin lafiyarki kinji..
daga kai kawai maryam tayi fuskarta sharkaf da hawaye haka tana kallo aka kunsa ma inna kudi masu tarin yawa ta nade su a gefen zanen ta suka fita suna kara tattaunawa,..
Bayan Hajiya ladi ta dawo daga rakiyar inna abinci tasa aka kawo ma maryam shinkafa da miya harda nama kusan yanka biyar da rovar sobo da ruwa na gora ,,tana ganin abincin hawaye tafara sosai tana tina ummin ta tasan tana chan yau ko kwayar hatsi bazata iya kaiwa bakin ta ba haka ta tasa abincin a gaba tana kukan tausayawa rayuwar dazata shiga awani gari ,
A haka Hajiya ladi tazo ta taradda da ita Aa maryam Yaya Baki ci abincin ba kika sa Ababa kina kuka ki kwantar da hankalin ki su chan babu takura ina gaya miki zaki ji dadin zama sosai agarin nan maza ki gama anjima zamu kama hanya ,tashi kije wanchan dakin ga yan uwanki Chan da zamu tafi tare,
a sanyaye ta miki ta dauki abincin ta fita dakin ta shiga da sallama suka amsa mata yammata ne kamarta su uku suna chin abinci suna hira hankalin su kwance Kamar bada iyayen su aka rabasu ba,
gaishe sutayi tanemi gefe daya ta zauna ta zuba uban tagumi cike da dumuwa tana kallon abincin takasa kai ko loma daya bakinta ,har sauran yammatan suka gama suka fice daga dakin sa anan ta dan tsakali abinci ko loma uku batayi ba ta ajiye ta dauki ruwa tasha sosai sa anan ta masa jiki. Bango ta jingina ta cigaba da aikin tunanin,
Baifi thirty mins ba daya daga cikin yammatan tace ta fito su tafi,daukar yar jakar kayanta tayi ta fito jiki a sanyaye suka fito Kofar gidan saida Hajiya ladi ta garkame katon kwado a gate din sa anan ta umarce su da su shiga baya,ita kuma ta zauna gefen driver, driver ya ja suka kama hanya kowa na farin ciki yayinda maryam ta jingina jikinta gefen kofa tana share hawaye jefi2 domin taga alamar yammata murna sukayi Kamar zasu aikin hajji ,shin basuda iyaye ne dabasa kukan rabuwa dasu kanta ta chusa tsakanin cinyoyin ta kuka ta fashe dashi mai karfi ta toshe bakinta da hannu ta ,Allah sarki ummina an rabamu shikenan ummina zanyi wata rayuwa ta daban ,rayuwar da babu Ke aciki ,dawa zanyi rayuwa ummi kika bar inna ta badani saboda alkawarin ki da abba na wanda nasan inyana raye bazai bari haka ta faru dani ba ,Allah sarki abba na nayi rashin ka maiyasa kasa ummina daukar wannan alkawarin mai girma ne abba gashi yana neman ruguzamin rayuwa ta......
Karar wayar Hajiya ladi ce ta dawo da ita daga duniyar damuwar datake ciki ,hello Alhaji ranka ya dadi rayuwa sai da Ku in babu Ku rayuwa lami ce Alhajin Allah, ba tasan mai akace ba saidai taji Hajiya ladi ta rangada guda tareda shewa tace to ka kwantar da hankalin ka muna hanya nan da three hours zaka ganmu ,bataji mai yace ba ,Hajiya ladi tace kada ka damu kaidai kawai kayi mana tarba mai girma sai mun karaso ta kashe wayar tana cewa Alhaji kenan ai saika min gagarumar kyauta wacce baka taba yiwa kowa irinta ba kaidai jira zuwanmu tukun,ta maida wayar Jakarta.
Three hours later
Sun shigo garin Abuja maryam tagane sakamakon katon sign din daaka rubuta welcome to Abuja ,saida suka kara yin tafiya tukunna suka iso Area 2 taga anrubuta suka shiga jikin unguwar wanda gidajen suka iri daya ne awani gate ya tsaya tareda yin horn saida mai gadi ya leko ya gansu tukunna aka wangale masu Kofar gate din gidan kai tsaye gurin ajiye motoci ya nufa da alama driver yasata zuwa gidan,Hajiya ladi ce tafara fitowa saanan ta umarce su da su fito koda suka fito sai tace maryam ta tsaya anan bari ta fito yanzu ,haka suka shiga dukansu harda driver suka barta tsaye, batafi minti goma ba tafito tareda wata mata dagani itace matar gidan har kusa da maryam suka karaso tsugunawa tayi har kasa ta gaida hajiyar ,ta amsa tana kare mata kallo ganin haka maryam ta sadda kanta kasa,saida tayi kusan minti hudu tana kare mata kallo kafin ta jinjina kai ta kalle Hajiya ladi tace lallai Alhajin andace wanna kayan haka Hajiya toh karki manta dani ina jiran alert sukayi shewa tareda tafawa ,Hajiya ladi tace kibari sai munyi waya zaki ji komai muje ko maryam.....,,
# *shin wacce maryam*?
# *wane alkawarin ummi ta* *daukar wa abban ta*?
*comments*
*share*
*Mrs noour ce*โ๐ป
[7/11, 17:42] +234 816 822 9024: *๐ด๐ดKARFIN IKO๐ด๐ด*
๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
*HIKMAAH writers association*
Edited by๐๐ป *oum Zahara*๐
Dedicated 2my lil sis๐๐ป *Maman Sultan*๐
ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
*Masoya wannan novel ina mika sakon kwandunan da buhu buhun gaisuwa ta gareku, ina jin dadin comments dinku, Allah ya bar kauna๐ค๐ป*
๐
ฟโ0โฃ3โฃ
Muje maryam ko, wata motar Suka hau sabuwa dal gidan baya suka zauna,driver yaja suka bar gidan,suna barin unguwar Hajiya ladi ta gyara zaman ta fuskarta tana fuskantar maryam,mika hannunta tayi ta karba yar jakar kayan maryam din ta wurga ta bayan mota sa anan tajuyo ta ruko hannun ta,maryam Hajiya ladi ta kira ,dago wa tai ba tareda ta amsa ba ta zuba ma Hajiya ido kawai,
Maryam ina so ki nutso mgana zamuyi mai muhimmanci, maryam ki godewa Allah da yayo ki cikin mata masu sa'a, kinyi dace gidan da zaki zauna in har kinyi biyayya har karatun da kike so zaki cigaba ,sai kin wuce wa tsara Ke hatta da ummin taki ba lalle ta gane kiba duk Sandra kika dawo Nigeria ba...,
A razane maryam ta dago tana waro ido waje ,nan da nan kirjinta ya shiga bugawa da sauri2
Hajiya ba a kasan nan zan yi aiki ba dama Hajiya ,maryam tai tambayar muryar ta na rawa hawaye ya cika idon ta kiris take jira ta fara kuka,,
Murmushi Hajiya tayi ta dafa kafadar ta tace abinda yasa nace ki nutsu kinan tabbas ba a nan kasar zakiyi aiki ba amma fa babu wani Abu da zai sameki da nan da chan duk dayane Ke ina mai tabbatar miki da saikin yimin babbar kyauta,kar ki manta nagaya miki har karatun ki zaki cigaba da.....
Amma Hajiya mai yasa baki gayawa ummina da inna inda zaki kaini ba kika ce a Abuja zanyi aikin ,
hada hannuwan ta tayi wuri daya alamar roko fuskarta har ta jike sharkaf da hawaye muryarta na rawa tace Hajiya don girman Allah ki barni anan garin ma ya is a wlh zanyi kowa ne irin aiki matukar bai sabawa shari'a amma don Allah Hajiya kada ki kaini wata kasar daban wacce babu yare babu musulmai yan uwana wlh bazan iya zama ba haji.....kuka ne yaci karfinta ta rufe bakinta da rafin hannunta tasaki wani marayan kuka tana tuna halin daza tsinci kanta..
a fakaice Hajiya ladi ta harare a zuciyar ta tace wlh ko zaki hadiyi zuciyar ki ki mutu sai kinje gashi tun kafin Ku hadu ya bani wannan sabuwar motar inaga kunhadu amma a zahiri sai tayi murmushi takara ruko hannunta tace" haba maryam kar ki damu chan din bazaki suna gidan musulmai ne kuma hausawa tan uwanki ,kawai dai matar gidan ce batada lafiya shiyasa zaki zauna da yaran ta saboda hidimar gidan ,domin mai gida yace bayason aiki wadanda ba musulmai ba shiyasa yanzu haka yana airport yana jira tare zaku tafi..
Dammmm taji zuciyar ta ta bugawa nan danan cikin ta ya kulle ,jikinta ya fara rawa nan ta lula duniyar tunani ,kai anya Hajiya ladi ba cutar dani ztayi ba ummi na tasha gayamin duniyar nan mutane ba abun yarda bane kuma aini ba wai zaman kauye nayi ba da wayona ,gaskiya wannan maganar akwai wani abu da Hajiya Ke shirin aikatawa a kaina tabbas tafiyar nan ba alheri bace agareni, wani tunani tayi nan take jikin ta ya jike da zufa sharkaf babu inda baya rawa a jikin ta ,
tabbas ya zamar min dole innemo ma kaina mafita don wlh saidai akai ga wata tabbas na tuna da hirarsu SAKINA a islamiya itama fadima akan Hajiya ladi tabbas tana kai yara aikatau amma ance harda safarar yara sukayi kasa2 suna karuwanci sai yanzu tunani ya fado mat,..
Maryam, maryam tunanin mai kikeyi gamu mun karaso kin ganshi chanma yana jiran zuwanmu.
A firgice ta dago tan bazai ido taga ta ina zata ganshi,aikuwa chan ta hangoshi gefe daya da aka tanada don hurawa kallo ta karemai a yan sakwanni kirjinta ta cigaba da bugawa da karfi, sanye yake da kananan kaya riga da shirt fara wacce katon timbinsa ya cikata da wando jeans blue black, fuskarsa sanye da eye glasses bakikirin dashi ,ita tsoro ma yabata,wani yawu ta hadiye ,nan da nan ta rikice tafara kuka sosai ta na rokon Hajiya ,don Allah ki taimaka ki maida ni wurin ummina wlh ba inda zani Hajiya don Allah karki manta marainiya ce ni amanata aka baki karki ci amanar maraici haji...
Keeeeeeh dakata haka , Hajiya ladi ta daka mata tsawa,
shiru tayi yayinda hawayenta yaki tsayawa saima karuwa da yayi..
a tsawace Hajiya ta fara mata magana Yaya ina lallaba ki zaki kawo ma mutane maganar banza inace iyayen naki da Kansu suka kawo ki wurin bani na dauko kiba ,toh wlh ki shiga hankalin ki ki duba chan inma Alhajin kika kallah kawai to wadannan can mutane da kika gani duk securities dinsane ,idan kikayi kokarin yin wani hauka anan sai kin gane ba kida wayo ,gwarama ki nutso kiyi biyayya nagaya miki ,ki fito muje ta fada a tsawace....yayinda ta murda kofa ta fita ta barta Zaune .
Kallo maryam tabita dashi na tsana ita dama tunda suka hadu da ita taga irin kallon datake mata, taji Hajiya ladi bata mata ba ,ashe mugun abu na nan faruwa da ita, wani sabon kukan ne ya kufce mata da iyakacin karfinta tasake shi ta fara rerawa ,
Keeh dallah malama ki rufe min bakin ki kukan ki yana damuna ko ki sauka ko ki rufe min bakin ki....
tsiiit tayi ta hadiye kukan ,ita tama manta da driver a motar ,amma aiya lallashe ne a matsayin shi na dan uwanta musulmi tunda yanajin duk abunda suke fadi a motar ,amma zaice tayi shiru dukansu haka suke basuda imani,,wannan wace irin rayuwa ce , cikin lokaci kankani duniya ta juya mata baya , kukan takara saki a hankali ta dora dula hannayenta akan bakin ta,,
Bude Kofar taji anyi ,dagowa tayi da sauri tana duban taga waye ,Hajiya ce tare da Alhajin a tsaye yana kare mata kallo yana murmushi tareda lashe labbanshi Kamar wani tsohon maye, ita sai yanzu ta karema fuskarsa kallo taga yafi kyan gani a kusa kuma babane don zaikai shekara 59 koma yafi amma ya tsuke katon uban tunbi a kananan kaya,.......
*shin maryam zata tsira daga hannun su Hajiya ladi ko kuwa*?๐
*Yaya labarin Baby safina da Habib*?
*more comments*
*more typing*
*Mrs noour ceโ๐ป*
[7/11, 17:42] +234 816 822 9024: *๐ด๐ดKARFIN IKO๐ด๐ด*
๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ
Written & story by *@PHEEYMARRH*
Pheeymarrh@gmail.com
*HIKMAAH writers association*
Edited by๐๐ป *oum Zahara*๐
Dedicated 2my lil sis๐๐ป *Maman Sultan*๐
ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
๐
ฟโ0โฃ4โฃ
Kanta taji yayi mugun Sara mata ta fara karanta addu'oe a zuciyarta na neman tsari daga sharrin wadannan mutanen , ooh ni maryam Yaya zanyi haka zanbi mutanen nan suyi yadda suka ga dama da rayuwata, kai ina wlh bazan taba aikata abinda suke nufi dani ba inaa, wani irin karfi ne taji yazo mata ta bude baki way.....
taasss taji saukar mari a fuskarta wanda yasata tsuke bakinta daga niyyar ihun dataso yimusu ko Allah zaisa wani zaiji tausayinta ya maida ta gida, dafe gefen kumatun ta tayi tareda toshe bakinta da tafin hannunta , kuka takeyi kasa2 saboda azabar zafin marin datake ji...
Aa Hajiya karki kara taba lafiyar ta wannan kyakkyawar fuskar ba a bar ayi wasa da ita bace...
barta kawai Alhajin kana ganin niyyar tara mana mutane takeyi inba Allah yasa na dauki mataki ba da yanzu kila wurin nan ya cika da jama'a, ki futo nace ki biyomu Hajiya ta fada a tsawace,domin ji takeyi Kamar ta kamata tayita duka ta gama saka rai da samun dunbin kudi wurin Alhajin amma shegiyar yarinyar nan naso ta wargaza mata komai, wucewa tayi tana huce..
Sauka tayi tana Jan kafa da kyar saboda jirin datake ji ga yunwa dake damunta, dakyar take kallon gabanta sakamakon idanun ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 32