kai wa Abayas da hijab ɗin, ta na tuƙinta hankali kwance motar ta kashe kanta ba tare da tasan dalili ba.
Sakkowa ta yi ga ranar da ake tsalawa, mai mugun zafi, duk ya yi mata yawa.
Wayarta ce ta fara ringing, dubawa ta yi ta ga Abbih ke kiranta cikin muryarta mai sanyi da kamala, ta ce '' tohh lafiya? , yau kuma.''
Cikin muryarsa mai amo ya ce ''Hello, kina ina?. ''Na ɗan ta fi delivering kayane.'' ''Where?."
''Lamido crescent.'' ''in kin kai kije rijiyar zaki ana neman ki.'' '' da fatan dai lafiya.'' ''in kin je kya gani.'' ƙit ya katse wayar.
'' murmushi kawai ta yi ta na ƙara jinjina al' amarin Nabil ɗin.
Titin tsit ya ke babu napep ɗin da ke gilmawa, ko ina shiru.
Hydar da ke tsaye tare da Amir da ya fito raka sa ya ga wata mata ta ɗan yi backing na su duk da abaya ce a jikinta.
''Amir ne ya ce is like that lady overthere is searching for help.'' ''ni fa na fita harkar mata a yanzu, za ka iya zuwa ka gane ma kan ka idan hakan ne.''
''Dude Dan Allah zo muje we won't be local a sanadin haka please, kalli bayan ta da kyau wallahi uwa ce ta haife mu.''
''OKAY.''
Daga haka su ka nufi Ammi dake tsaye ta na duba ko Allah zai sa ta samu number mechanic a wayarta.
''Assalamualaikum, good noon Maa.'' Amir ya faɗa, Juyowa ta yi tare da faɗin'' Noon My dear.''
Ɗago kansa ya yi shi ma ya gaidata.
Sannan su ka tambaye ta mai ya sami motar.
''Wallahi Son I don't Actually know, kawai motar ta tsaya, ban ma san ya zan yi da shi ba .''
''Hydar ɗan zo ka duba tun da kai ne ke hawa lexus.''
A hankali ya ta ko tare da buɗe gaban motar ya ɗan yi taɓe-taɓensa sannan ya ce ta shi ga ta kunna, a ta ke motar ta kunnu.
Murmushi ta yi tare da faɗin ''Thank you Son, What's your name?.'' ta faɗa tare da nuna Hydar, '' Am Aliyu buh ana kirana da Hydar.'' ya yi maganar ba tare da ya kalli fuskarta ba, dan haka kawai nauyinta ya ke ji.
'And you?." Ta nuna Amir. ''Am Umar Maa.'' '' Ku duka babana ne kenan motar ta ta buɗe tare da ɗaukan dubu goma, ta bawa Aliyu dubu biyar, shima Amir ɗin dubu biyar.
''toh ga shi ku sa yi chewing gum.'' ''murmushi Aliyu ya yi ban da Umar da ya fara dariya ya ce Maami no need, we are very grateful.'' ''chicken change right?, lemme add more.''
''Noo Mom wallahi, Alhamdulillah, kawai dai we are now men not boys, that's why.''
Da ƙyar ta samu su ka amshi kuɗin, sannan ta shige motarta ta ɗauki hanyar delivery ɗinta.
Shima Aliyu ya ɗauki hanyar gidansu five kee ɗinsa a hannunsa (za ta yi maka rana 🌚😂).
Bayan ta yi delivery ɗin gidan Neneh ta kama hanya amma, yanayin unguwar ya canza.
Ko da Aliyu ya koma bai fi minti talatin ba Mami ta aike sa siyan fruits, Dan sun ƙare a fridge.
A hanyarsa na fita da ga unguwar su ka yi clashing da wata mota zuge glass ɗin ya yi ahankali itama ta zuge nata. ''Murmushi Ammi ta yi tare da faɗin "You again son?, you live arround here?." ''Yes Maa, ina wuni." "An wuni lafiya." Su ka ɗan gaisa sannan kowa ya yi hanyar sa, dan shi rumfar Shehu zai je siyan fruits.
A hankali ta ke gangara motar na ta akan titin da ke malale da kwalta, saboda gidan Nenehn ya ɗan shige mata duhu.
A side ɗin right hand ɗinta ta ga Aliyu shuwa Arabi's mansion, hakan ya ba ta dama da dalilin karkatar da hancin motar ta ta danna horn a cikin gidan.
Mai gadi ne ya buɗe, tare da tambayarta wa ta zo gani, sai da ta ba shi amsa, sannan ya barta ta shiga cikin gidan.
A hankali ta yi parking tare da futowa cikin shigarta na Abaya, ta nufi in da ta fi tunanin entrance ne, shigarta kam ya yi dai-dai, da fitowar hajja daga kitchen dan yau Salimah ba lafiya,.kuma slay queen na bacci.
" Duniya kenan, ƴar ɗakina ta yadda ni, toh yanzu ke miye riba, wallahi kin bani kunya har wannan mai fuska kamar jan ƙosai ya samu raba ni da ke wallahi kin ji kunya, ki tsaya anan na kawo miki ruwa, ƴar daɗi miji, maganar da zan miki second ɗaya ma wallahi ta yi yawa, Allah na tuba an gaya mana miji, har ya gama dai ƙuruciyyar sa bai min kishiyya ba." Neneh ta faɗa ta na kama kujerar falon, ta zauna akansa.
Durƙusawa Ikimat ta yi har ƙasa ta gaida Nenehn, sai da ta amsa sannan ta shigo ta zauna a ƙasa.
"Bara na kawo miki ruwa ƴar albarka, mai shiga tsakaninmu sai Allah, ko Maimu ba ta iya ba."
" Neneh da kanki za ki kawo min ruwa? Ina Liya, ina ƴan aikin?."
Har ta tafi ta dawo ta zauna.
"Liyana ko masifa da kata'i, ai ƙarar ta zan ba ku daman, bata gaida ni, in ban da zagi, da cin mutuncina a gidan nan da ta iya.
Akwai ranar da ta sa aka tsinko mata tsamagiyya wai za ta zane ni fa in gayamiki, nikam nace,hoho hoho idan ƴaƴan Ikimat ba su ji kaina ba wa zai ji kaina."
"Ita Liyanar?."
"Zan miki ƙaryane?."
"A'a Neneh."
" Ta shi kije kiyi girkin ma na fasa."
Ta shi ta yi ta shiga, kitchen ɗin da ya ke a goge sai sanyin tiles ya ke fitar da ƙamshin kayan ƙamshi, dan Neneh na son su sosai.
Cikin minti talatin ta gama haɗa cous-cous da ya sha goat meat, sai ƙamshi ya ke.
Ba su jima da cin abincin ba, Neneh ta fara sanar da ita an yiwa Liyanar miji, da kuma abin da Abbhi ya ce.
"Toh Neneh Allah ya tabbatar da Alkhairi."
"Amin."
Har Ammi ta tafi Liyana ba ta ta shi ba itama kuma ba ta tambaye ta ɗin ba.
Sai da aka kusan kiran magriba sannan ta tashi ta nufi bathroom ta yi wanka tare da saka kayan bacci, sai da ta sha maganin mura sannan ta koma baccin ya ƙara ɗaukanta.
Washegari da safe ma ba ta wani kula Neneh ba dan ba ta jin daɗin jikin na ta tun jiya, ga shi Abbin ya na ta magana akan ta yi haƙuri ta rasa ma da uwar mai za ta haƙura.
A kwana a tashi asarar mai rai hausawa kan faɗa, yau aka sa ranar Liyana da Hydar wan da gaba ɗaya a gidan Nenehn aka saka nan da sati huɗu biki.
Kuma har yanzu ba'a sanar da Liyana bikin ba, kuma har yau sai dai su haɗu da Sultan a gidan Lily ko kuma joint tun da ba school.
Yau dai kam kamar kullum shigarta na palazzo trousers da long sleeve shirt ne a jikinta sai hula black color da slippers ɗinta baƙi, car key ɗin motarta ƙirar Kia Picanto ta ɗauka tare da ɗaukan Atm card ɗinta, ta cilla mint chewing gum ɗinta a baki, ko da ta fito ba ta tarar da Neneh ba, dan haka wucewa ta yi kitchen ta ɗan ɗauki bottle water ta sha rabi sannan ta nufi hanyar motarta, ta ajiye tare da tada motar, mai gadi ya buɗe mata ta cilla motar titi, tare da sakin waƙan _Asake, terminator._
Ta na bin waƙar ta na gyaɗa kai har ta ƙaraso kasuwar kwari, dai-dai wani ƙaton shopping plaza na atamfofi da abayoyi , mai suna _LIYANA PASSION CO._ ta tsayar da motar ta, tare da futowa ta nufi cikin wurin da zamu iya kiransa da kasuwa, dan babu abinda babu a ciki na kayan da mata ke sawa ajikinsu.
A hankali ta sauko tare da shiga cikin babban boutique ɗin, Abbhi da ke tsaye ya na magana da receptionist akan duk wanda ya zo nemansa in dai ba Liyana ba ce ace baya nan ya na companyn atamfarsa.
A hankali ta tako tare da rufe masa idanu.
Murmushi ya yi sosai sannan ya ce "Day maker."
A hankali ta sake masa ido sannan su ka ƙarasa office ɗin sa.
Zama ya yi a CEO chair ɗinsa mai juya mutane, tare da faɗin " Sweet heart, The reason why I called you here is that......"
Kasa ƙarasawa ya yi dan bai ma san ya ya zai fara ma ta bayani ba , kuma this is the only way out for him, Dan Jiddah ya rantse idan ba'a yi auren ba babu su babu shi, ita kuma Neneh ya biya ta nonon ta da ya sha.
He has no choice than ya yi hakan, shi ya rasa mai ya musu da suka ɗauki zafi hakan.
"Abbhi just say it, kar ka ji komai okay, you're my own father, na san ba ka son ɓacin raina buh just say it."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin " Liya Jiddah ya zaɓa miki miji." Ya ƙarasa maganar tare da runtse idanunsa, wani kalar bugawa zuciyarta ya yi, arazane ta ce " Sultan fa...........
Sorry da bana update kwana biyu yau da zafi na na taho 🥹💎
Rashin data ne ke sa ni rashin update, ga ciwon wuya amma kuna raina habibties 😌🥰
THANK YOU FOR READING 💜
To everyone who took the time to read The Regret, you’ve just held a piece of my heart in your hands.
Kuna daga cikin dalilin da yasa zan ci gaba da rubutu.
See you in the next chapter of our journey.
With love,
Pending Amarya 🦋
> Pending Amarya's book corner Extraordinary everyday 🦋
> Share for more pages in sharing ɗinku ya yi yawa zan ƙara typing da yawa.
Pending Amarya as usual 🦋 🫠
I really love you readers 💎
> Pending Amarya's book corner Extraordinary Everyday
> Mondays to Fridays from 8am to 12am follow for more 🎊🫂📚> PENDING AMARYA'S BOOK CORNER EXTRAORDINARY EVERYDAY POSTING LINK 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbAyucH7j6g0IDCpPi2V
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.💪
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
The Noble Writters ✊
Dedication is our strong
THE REGRET 🙆
when love meets temptation who survives?
The Regret Mallakar pending amarya ce ban yarda a sauya min labari ba ta ko wani siga, idan hakan ko ta faru kotu ne zai rabani da ke!!!!
Pending Amarya ni ce satellite ina haska su kamar ring light 😂😂💔
Mallakar Pending Amarya ce_
NDA DUBDO🦚
My Maiduguri ppl
THIS PAGE IS DEDICATED TO PRETTY SK ✅🎊
THANKS YOU DEAR ✅
Zan so kije da ni🫂 Babyn bae ai kinsan dani🤗
Baby na you promise say that you no go leave me kar ki yada ni 🤌🙌
Baby zuciyata zo gata 😩 zan kula da ke likeee ƴar auta, so nake kin zamto min mata zo masoyiya 🤧 Soo tell her ta ko taka a hankali 🥴💔🦧🥀🫵
🦚💎
LONG CHAPTER ✍️
_PENDING AMARYA _
Page 21
Ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin " Liya Jiddah ya zaɓa miki miji." Ya ƙarasa maganar tare da runtse idanunsa, wani kalar bugawa zuciyarta ya yi, arazane ta ce " Sultan fa...........
''Sultan kuma?, which Sultan Liya?."
'' Saurayina mana wanda na ke baka waya sometimes ku gaisa, that fair guy da kake gani a status ɗina, ka ke tambayata akansa.'' ta ƙarasa maganar ta na gunjin kuka.
Kenan abin da Nenehn ke faɗa gaskiya ne da ɗan gidan Alhaji Kyari ta haɗa ta. Ashe yau ita da Neneh sai kotun ƙoli ta ji su.
'' Sorry princess, ni ban taɓa kawowa is your boyfriend ba, ni à tunanina is just a normal friend ,
Buh I'm really sorry. Find a place in your heart ki yafe min, please.''
Ta fi minti biyar ta na kukan ba ta daina ba, ta na kukan kuma still ta na taunar chewing gum ɗinta.
A hankali ya ce ''tashi muje ki sha ice cream, Allah ya huci zuciya mai muhimmanci.''
A hankali ya ke jan hannunta har suka fito wajen, motarsa ƙirar Benz, wacca ya saba hawa, ya buɗe mata gaban motar sannan ya ja hannunta ya zaunar da ita.
Shima motar ya shiga tare da bawa motar wuta ya bar boutique ɗin gaba ɗaya.
A hanya ma ba ta fasa kukan ba, dan kuka ta ke har da majina.
A hankali Abbihn ke satar kallonta, sannan ya cigaba da tuƙi har suka ƙarasa babban eatry.
Sauka ya yi daga cikin motar wanda sai da ya yi da ƙyar sannan itama ta sauko.
Ya riƙe mata hannu, su ka shigo eatry ɗin.
Zama suka yi a wani ɗan ƙaramin parlour da nan ko wani VIP ke zama sannan ya yiwa waitress alamar ta kawo musu menu.
Sai da ya zaɓa sannan ya zaɓarwa Liya dan ita, kan ta na ƙasa ta na aikin kuka.
Ɓangaren Hydar kam tun ranar da aka mai magana, ya daina shiga sabgar kowa a gidan, ko Sultana ya daina sakarwa fuska rayuwarsa kaɗai ya ke yi.
Ko last week da aka sa rana, babu wanda ya yi wa magana ballantana a kai sa gaba.
Yau dai kam ba ya wani jin daɗin jikinsa, ɗan wani kalar kasala ya ke ji.
Mami ce ta shigo ɗakin na shi a hankali, ta shiga tashin sa daga barcin, da ya ke faking ya na yi.
''Shirya za ka kaini unguwa.'' Mami ta faɗa tare da tsare shi da manyan idanunta.
''Buh Mami bacci na ke yi, kuma akwai drivers a gidan.''
''Ni kuma na ce kai za ka kaini, ko da magana.''
Bai ƙara cewa komai ba ya tashi tare da zira slippers ɗinsa ya yi hanyar dressing room.
Cire kayansa ya yi ya saka bathrobe, ko da ya fito bai tarar da Mami ba.
Sai da ya tara warm water a jacuzzi, ya yi wankansa sosai, sannan ya fito haɗe da shiryawa cikin kaftan white color, da black cover shoe, sai Rolex Explorer ll da ya manna a tsintsiyar hannunsa, tare da manna hularsa a gashinsa da ya ke a gyare.
Sannan ya feshe jikinsa da turarensa na Armani Georgia haɗe da Valentino.
Wanda ko bai fesa ba ƙamshinsa na nan.
A hankali ya ɗauki wayoyinsa tare da fita daga ɗakin gaba ɗaya.
Ko da ya fito daga ɓangaren sa, ɓangaren Mamin sa ya nufa, haɗe da yin sallama.
Babu kowa a parlourn sai TV da ke ta aiki, a hankali ya zauna a ɗaya daga cikin tsadaddun royal cushions ɗin, sannan ya fara danne -dannensa a waya.
Saukowa ya ji ana yi daga stairs bai duba wanda ke saukowa ba ya cigaba da chatting ɗinsa da ya ke yi.
''Aliyu tun da aka maka maganar na yi maka mata ka ƙullaci kowa a zuciya?, C'mon amshi jakar nan daga hannuna.''
Mami da saukowa ta kenan ta faɗi hakan.
Beyi magana ba ya amshi jakar na ta da kuma mukullin motar ta, ya fita daga gidan zuwa cikin mota.
Mami da ta ci ado cikin wani dakakken less ɗinkin bubu gown, ziconic chain ko kuma nace set ɗin ziconic na wuyanta da kunnanta da kuma hannyenta which means earrings da bangles.
Ta nufi motar ta ƙirar Prado black color, ta shige bayan motar ta zauna.
Motar ya cilla titi sannan a hankali ya ce ''Mami ina za'a je.?."
''Kwari market.'' ta ba shi amsa a taƙaice
Ta hanya mai nisa ya bi saboda kawai ya yi shatale -tale da ita.
A wani babban eatry ya tsaya tare da parker motar sannan ya ɗan kalli Mami ya ce ''Lemme get some water.''
''Be fast.''
''Okay Maa.''
Daga haka ya fito daga cikin motar ya ƙarasa cikin eatry ɗin.
Ko da ya shiga ciki receptionist da ta ke kuma a matsayin cashier ya sama.
Ya ba da ordern ruwa wanda a take a ka kawo masa ruwan ya bada Atm card ɗinsa a ka zari kuɗin.
Juyowan da zai yi, ya yi ido huɗu da ita, wani babban mutum na mata kiss a gaban goshi amma bayan mutumin kaɗai yake gani.
Ɗauke kansa ya yi daga dubansa agaresa, dan tabbas wannan bad luck ce a wurinsa, haɗuwa da ita tashin hankali ne.
Liyana kam kallo ɗaya ta masa tare da kama hannun Abbhi ta na wasa da shi.
Fita ya yi daga eatry ɗin da ya ke dana sanin shigowansa.
Sannan ya yi hanyar wajen da yayi parking motar Mami.
Shiga motar ya yi tare da sauke nannauyen ajiyar zuciya, tare da yiwa motar key.
'' siyan ruwa ne ka yi kusan hour ɗaya a ciki bayan wurin sai da pure water da muka bari, duk juye juyen da za ka yi sai ka kaini kasuwar nan na faɗa maka abin da ba ka sani ba.''
Shi dai duk yadda za ta jima ta na mai faɗa ba zai tanka ba.
A ƙofar Mudassir and brothers ya faka motar, sannan ya buɗe mata motar ta sauko ya bita zuwa ciki, ba ta wani yi siyayya da yawa ba su ka fito, ta shige motar suka bar wurin.
Liyana kam da ƙyar Abbhi ya lallaɓa ta ta fara cin abincin dan daman da shi ta ce za ta yi break fast.
Tari ta fara sosai tun da ta ga shigowarsa, wanda da ƙyar Abbhi ya samu ya tsayar da tarin tare da mata peck a goshi.
Hannunsa ta riƙe tare da faɗin ''Abbhii, kana nufin zan bar Sultan? Amma da ka yi convincing ɗin su Neneh ka gaya musu ina da wanda na ke so ai.'' ta faɗa wani gutun hawaye na sake fita daga cikin idanunta.
''I wish zan iya miki hakan, buh Neneh ta ce in har na sake ɗago maganar nan na biyata nononta da na sha.''
Ajiyar zuciya ta sauke tare da faɗin '' you know I always wants the best for you? , Soo na amince, amma kar sultan ya ce yaudararsa na yi, i can't take that.''
Ta faɗa ta na ƙara rushewa da wani kukan.
''Okay Liyana, don't waste your tears babyn Abbhi, okay.''
Gyaɗa kai kawai ta yi tare da faɗin ''Abbhii amfeeling cold, can you take me home.''
''Sure.''
Daga haka ya biya bills tare da ɗaukanta kamar baby ya wuce da ita cikin motar.
Koda Aliyu ya mayar da Mami gida, tisa shi ta yi a gaba, tare da faɗin ''Kaga yau ɗinnan ba zai wuce ba ka je gidan Neneh ganin Fatima ba, mutum zuciya kamar fir'auna, you better ka saki fuskar ka, ka aikata abin da nake gayamaka, am I clear?." ''Yes Maa.''
Daga haka ya kwashi wayoyinsa ya yi ɓangarensa.
Ko da ya isa ɓangaren nasa, Amir ya kira a waya, dan he can't go that house da sunan zance ya zo.
Ba'a wani jima ba Amir ya iso cikin shigarsa na ƙananun kaya da suka amshi jikinsa.
''Man mai sa ka kira ni ?."
''Amir Mami wai na je gidansu yarinyar da zasu aura min.''
''Toh kaje mana.''
''kai dai ba ka taɓa kawo shawara mai ɓillewa, ta ya zanje, na ce mata mai?."
''Abin da ake faɗa mana.''
''You're not serious, ina maganar way out for me, Kai kana min maganar banza.'' ya ƙarasa maganar ya na sakin tsaki.
''Man kira min Sultana abeg, ta kawo min abinci, am starving.''
Ko kallonsa Aliyu be yi ba balle ya sa ran answer.
''Toh ai shikenan it's already four o'clock is better ka shirya, kaje wurin your future wife, wa ya ga matar Aliyu da ciki after 9 months za'a je labour room.''
Ya yi maganar ya na sakin wani tijararren dariya.
Ta shi Aliyu ya yi ya bar mai ɗakin tare da barin gidan gaba ɗaya.
Duk da bai sauya shigarsa ba, ya nufi gidan da ke opposite da su tare da ƙwanƙwasa musu ƙofar.
A hankali Uzaifa mai gadi ya buɗe masa ƙofar.
''Alhaji sannu da zuwa.''
Ɗaga mai hannu kawai ya yi tare da wucewa cikin gidan tare da yin sallama.
Neneh da ke zaune cikin shigarta na kullum, ta ɗago kanta ta na mai kai duba wurin da ta ji sallaman Aliyu.
''Aah mai sunan Rafiƙ kai ne yau a gidan nawa.''
Be yi magana ba ya ne mi wuri ya zauna aka ɗaya daga cikin kujerun parlourn.
Cikin Muryarsa mai amo ya ce ''Neneh.''......
Sorry da bana update kwana biyu yau da zafi na na taho 🥹💎
THANK YOU FOR READING 💜
To everyone who took the time to read The Regret, you’ve just held a piece of my heart in your hands.
Kuna daga cikin dalilin da yasa zan ci gaba da rubutu.
See you in the next chapter of our journey.
With love,
Pending Amarya 🦋
> Pending Amarya's book corner Extraordinary everyday 🦋
> Share for more pages in sharing ɗinku ya yi yawa zan ƙara typing da yawa.
Pending Amarya as usual 🦋 🫠
I really love you readers 💎
> Pending Amarya's book corner Extraordinary Everyday
> Mondays to Fridays from 8am to 12am follow for more 🎊🫂📚> PENDING AMARYA'S BOOK CORNER EXTRAORDINARY EVERYDAY POSTING LINK 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbAyucH7j6g0IDCpPi2V
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.💪
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
The Noble Writters ✊
Dedication is our strong
THE REGRET 🙆
when love meets temptation who survives?
The Regret Mallakar pending amarya ce ban yarda a sauya min labari ba ta ko wani siga, idan hakan ko ta faru kotu ne zai rabani da ke!!!!
Pending Amarya ni ce satellite ina haska su kamar ring light 😂😂💔
Mallakar Pending Amarya ce_
NDA DUBDO🦚
My Maiduguri ppl
THIS PAGE IS DEDICATED TO MY FUTURE HUSBAND 😪
YOU'RE THE BEST DUK DA BAN SANKA BA😪😂😂😭
ALLAH YA HAƊA NI DA KAI 😌
_ If days was a love song and I told you to be with me until we gone old could you wait, would you stay_ 😪😭
🦚💎
CHAPTER TEN 😍
_PENDING AMARYA _
Page 22
Duk da bai sauya shigarsa ba, ya nufi gidan da ke opposite da su tare da ƙwanƙwasa musu ƙofar.
A hankali Uzaifa mai gadi ya buɗe masa ƙofar.
''Alhaji sannu da zuwa.''
Ɗaga mai hannu kawai ya yi tare da wucewa cikin gidan tare da yin sallama.
Neneh da ke zaune cikin shigarta na kullum, ta ɗago kanta ta na mai kai dubanta wurin da ta ji sallaman Aliyun.
''Aah mai sunan Rafiƙ kai ne yau a gidan nawa.''
Beyi magana ba ya nemi wuri ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun parlourn.
Cikin Muryarsa mai amo ya ce ''Neneh.'' ɗago kanta Neneh ta yi tare da kallonsa ta ce ''Lafiya ka ke kirana haka kamar ɗan maye?."
Tsaki ya ja sannan ya kalleta ya ce " ina wannan yarinyar?."
"Wadda ka bani ajiya."
Saita muryar shi ya yi sannan ya ce " toh sai anjima."
Bai jira cewar Neneh ba ya tashi ya bar gidan dan wani kalan zazzaɓi ke neman rufesa.
Ko da ya ƙarasa gida bai bi ta kan kowannensu ba flat ɗinsa ya shige tare da kwanciyyarsa.
Ɓangaren Liyana kuwa, tun da Abbhi ya dawo da ita gida kuka kawai take tun dawowarta, kallon pictures ɗinsu da Sultan kawai take tana kuka, Neneh ta zo ta mata magana har ta gaji sai dai ta ɗago ta dallawa Nenehn harara sannan ta kuma ɗauke kanta.
Ta yi kuka ta godewa Allahnta, ta kira Sultan amma fushi ya ke da ita yaƙi ya ɗaga for almost two weeks yanzu.
She has no choice than to give up ɗin da ta faɗawa Abbhin.
Komai ya cakuɗe mata.
Ta kira Lilian ita ma wayanta is not reachable, ta kira Ilham kuma network ba ya bari ta ji.
Haka ta fawwalawa Allah komai, first in history da ta ɗauki Kur'ani ta karanta saboda samun sassauci, because in dai karatu za ta yi sai dai ta karanta na ƙwaƙwalwanta bai fi aya ɗaya ba ta cigaba da jin waƙoƙinta.
Haka rayuwarta ta cigaba amma tsiwar nan na nan.
Amma ba ta cika fita ba kullum ta na gida sai dai fa ta yi suna sosai a Instagram kowa ya san ƴar gidan Nabil ( Liya bae).
Kullum shi ma Abbhi ya na gidan bai cika fita aiki ba sai ya tabbatar ta ci ta ƙoshi ta na walwala sannan zai tafi office.
Bikin Liyana saura two weeks, next week za'a kawo lefenta which is idan biki ya rage one week, kuma suna ta tsara events sosai da ƙawayenta, kuma sun shirya da Sultan amma ba ta gaya masa bikin ba.
Yau dai kam she's in a good mood sosai, dan kallo ɗaya za ka mata ka ga hakan tattare da ita, ga wani gyaran jiki da ake mata, dan wata mata Mamin Hydar ta ɗauko all the way from Ethiopia, sai kuma Neneh ta ɗauko ta nan gida Maiduguri.
Wani kalan tsantsi fatar ta ta yi ga wani shegen ƙyalli
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 31