Share this page
sannan ya ďauki ďayar key ďin motarsa ķirar Zakir ya nufi H&k ventures. Liyana kam telegram ta hau tare da fara chatting dasu cousins ďinta inda har suke sakar da ita bikin Assultanah da Amir da kuma na Sultan da Ily da duk ba a sanar da su ba. Sai around ten o clock ya dawo gidan, a yadda ya bar gidan a hakan ya tarar da shi babu wani chanji da aka samu. Direct ďakinsa ya shiga da ledojin hannunsa, a kwance ya tarar da ita jikinta sanye da wasu kayan bacci masu ďan taushi da nauyi. Hannunta na riķe da remote Wanda da alamun kallo take. A hankali ya ķaraso inda take fuskarta a ďaure babu alamun rahama. Yaye bargon da take ciki yayi tare da tallab’o fuskarta Buh still ko kallonsa ba tayi ba. Bai mata magana ba shi ma ya ciro wani milky donut daga wani kwali mai kyau tare da wani yoghurt ya fara sha tare da donut dinsa . Tun ya na sha ta na ďauke kanta har ta fakaici idanunsa tare da warce Yili yoghurt ďin hannunsa tare da donut ďin tana mai ķyalķyalcewa da dariya. Kallonta kawai yayi Sannan ya juyar da kansa ya na mai canza tashar zuwa Spoti Tv. Wayarsa ce ta ďauki ring hakan ya sa shi kai dubansa kan bed sides inda ya ajiye wayoyin nasa. Ganin number dake kiransa ne ya sanyata saurin rarrafowa daga ķarshen gadon da take tare da ďaukan wayan da sauri. Da kallo ya bita sannan ya ci gaba da abin da yake. “Hello Papa, i won’t be coming back home today, saboda birthday party ďin zola, and bayan nan zamu je Maldives a can za ayi sauran party ďin.” Daga can b’angaren Marwa ta faďa ta na mai shafa lips scrub a leb’enta. Warce wayar Aliyu ya yi daga hannunta sannan ya fara magana a fusace “Duk inda kike you better come back to this house kafin jikin ki ya yi tsami, who’s Zola?.” Ya ķarashe maganar tare da tambayarta a zafafe. “Baddie Zola, Our friend back then, ko ka manta?, Izabela Lewandowska that Lady from Poland.” Tayi maganar trying to reminds him her. “And I said you should come back to this house na baki nan da minutes talatin or else ki zauna a nan har ki gama abin da ya kawo ki.” Ya na gama faďin hakan ya katse wayarsa ba tare da ya tsaya jin abin da zata faďa masa ba. Har ķarfe ďayan dare babu Marwa babu dalilinta, Liyana da taga ba zata iya ganin ķwaķwaf ba, ta samu waje ta baje a kan gadon wanda a take bacci ya kwasheta. A take ya kira Amir ya sanar da shi abin da yake faruwa inda ya basa go ahead da da zarar ta dawo ya ci ubanta ya ajiye ragowa, sannan Kar da ya ķara kiranta. Daga haka suka ďan tab’a hira inda Amir Ke sanar masa aurensa da Sultana har da na Sultan da Ilham. Ya yi mamaki sosai da jin hakan, dan shi dai ya san kusan kullum ya na waya da su Mami har da su Ammi da Sultana da ma Ilham ďin Buh none of them even try to do sub’utar baki su gaya musu. Ko da suka gama wayar bai koma bacci ba alwala yayi ya tada sallah . Ko da ya idar ďinma bai kwanta ba addua ya yi ta yi na neman tsari daga kowani sharri. Sai after sallar asuba sannan ya kwanta domin yau ba ya jin zai iya zuwa gym. +++++After A Week ++++++ Sun ci gaba da gudanar da rayuwarsu cikin aminci da ķaunar juna. Sannan har yau Marwa ba ta dawo gidan ba ita ma kuma ba ta tambayesa ba dan ita ba ta son zamanta daman a cikin gidan. Zaune suke a living room ya na tufke mata kanta dake tsife. A hankali Marwa ta turo ķofar parlourn jikinta sanye da checkered jacket da jeans trousers. Bata kalli inda suke zaune ba ta ci gaba da tafiyanta towards her room. cikin muryarsa mai amo Wanda ke jagula lissafinta ya ce “ Ki koma daga inda kika fito, there’s no way da za ki zauna min acikin gida, how dare you da zan kafa miki doka ki ķi bi kina zaman gidana.” Ya ķarashe maganar a hasale. “Buh ai na faďa maka birthday zanje, sannan naje inda zani dan haka wallahi babu inda zan je.” Ta ķarashe maganar tare da ďaukan ķaramin trolly ďin da za ta shigar da shi cikin ďakinta. “Ahh okay lalacewar naki har ya kai da zan miki magana ki ķi bi kenan abi?, toh wallahi sai kin bar min gidana.” “Lalacewar tawa kuma kaine sanadiyyar ta ai, kuma wallahi ban yafe ba, abin da kamin sai anyi ma y’ay’anka mark my words.” Marwa ta faďa tare da kokarin bangaje Aliyun. Jin kalmar Marwa na karshe ya sanyata sakin Wani kalar ķara tare da zubewa a wajen wani ruwa na bin ta ķafarta. Ķara ruďewa tayi dan ganin ruwan ya mugun tayar mata da hankali. A ruďe Marwa da Aliyun suka juyo zuwa wajen da take, kusan a tare shi da ita suka ķarasa wajen Liyanar. Doke hannunta da ta riķe mata ķugunta da shi liyana ta yi tare da Fashewa da kuka ta na mai miķowa Aliyu hannu. Baya ta yi kamar za ta faďi ya yi saurin ka mota tare da ďaukanta, ya na mai zaunar da ita a kan cushion. Wani kalar gumi ke keto mata, sam ta ma kasa masa magana. “Marwa get me some water.” Ya faďa a ďan razane. “Let’s take her to the hospital, she’s in pain.” Ta faďa a sanyaye dan Marwa duk rashin imaninta tana tsoron ace mutum ba shi da lafiya. “I’m not asking for your opinion, just get me what I asked for .” Ya faďa a ruďe. Wani bell ya danna wanda a cikin seconds talatin yan aikin gidan suka fara shigowa cikinsu har da wancan Chinese lady ďin dake gyara masa ďakinsa. Su kansu sun yi mamakin ganin Boss ya kira su , because daga sun gama aikinsu ba sa sake shigowa gidan dan su apartment dinsu a wajen main building din yake. Ya ma rasa mai zai yi, koda aka ďauko wayar nasa ma manta sunan da ya yi saving Doctor Zhu da shi ya yi. A zafafe ya ķara danna bell ďin jikinsu na rawa suka fice. Da sauri ya ďauki car key ďinsa tare da sunkutanta ya nufi bayan mota da ita. “ Wayyo Allah na Ammi nah ki taimaka ki yafe min, wallahi ba zan ķara ba Ya, Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, mutuwa zan yi , Summa sabila yassara, fa inna ma’al usri Yusrah, Ya Alih ka fadawa Ammi nah Abbhina Ilham dina su yafe min, na san mutuwa zan yi, kai ma ka yafe min.” Ta ķarashe maganar ta na damķan kujerar motar. A galabaice a ka ķarasa labour room da ita, hankalin Aliyu idan ya yi dubu toh ya tashi, dan ya kasa lissafin komai a brain dinsa. Doctor Zhu ce tazo da dan sauri ta shige cikin labour room ďin ba tare da ta jira jin abin da Hydar ďin zai fada ba. ••••••••••• Bai fito da wayoyinsa ba ballantana ya Kira gida a tashi da addua dan Allah na gani a lamarin Liyana ya sare ba kaďan ba. Har ķarfe shida na yamma babu wani labari game da Liyana labour kawai take. Idan banda sallah babu abin da ke tashinsa a wajen da yake. Ķarfe bakwai daidai na yamma ta sullub’o yaranta uku , wanda ko wannen su tazarar five minutes ne a tsakaninsu. “Congratulations Mr. Alih, Allah has blessed you with three beautiful little Queens of Jannah, Allah ya taya ku riķo, duk da fita kayi ka barmu, kai Romeo you can’t watch her in pain right?.” Doctor Zhu ta ķarasa maganar tare da zare hand gloves ďinta daga hannunta ta na mai ijiye su akan wani tray da cleaner ta zo wucewa da shi. “Alhamdulillah, Alhamdulillah ala kulli hal, Mrs Zhulaihat, kina da 5% share a H&K, thanks for saving her.” Ya ķarashe maganar kamar Wanda zai rungumeta. “Thanks I really appreciate, and then wa ni hanzari ba gudu ba, her womb is very weak kafin ta ďauki wani cikin za a dan ďau lokaci.” Ta yi maganar ta na mai ďan mayar da murmushin fuskarta. “Babu komai a hakan ma mun gode ma Allah.” Ya ķarashe maganar still murmushi a kan fuskarsa. “ Yeah, yanzu Ana gyarata da Babies ďinta, in the next hour za ka iya shiga, amma please a samo mata abin ci wanda za ta iya ci sosai, ba lallai ta iya cin Chinese food da ake badawa a hospital ďin nan ba.” Doctor Zhu ta faďa tare da barin wajen nasa. Da sauri ya fice daga hospital ďin tare da nufar hanyar gida. Ko da ya isa gidan ma direct kitchen ya nufa tare da ďaura ruwa a cikin wani electric flask, tare da kwaso madara da cocoa powder da wasu abubuwan da suka dace. Tare da ķara tilan kayan babies ďinsa, dan ya ķudiri cewa babu Wanda zasu gayawa ta haihu sai dai saukarsu jibi a Nigeria. ※※※※※※※※※ Gida Nigeria kam tun safiyar ranar da Liyanar za ta haihu Ammi gabanta ke ta faďuwa, ta kira numbersu ya fi sau dubu amma sam ba ta ďagawa daga ita har Aliyun. Amma Abbhi sai ya ce da ita kar ta damu dan jiya sun yi waya kuma ya ji ta garau. Haka dai ta ajiye maganar ta ci gaba da sabgoginta ba tare da ranta ya so ba. Shi ma kansa Abbhi ji yake kamar ba lafiya take ba, ji yake tamkar ya yi booking flight zuwa China ďin ko ya ji sanyin rashinta. Ga bikin Ilham da ya rage saura one month da two weeks, ya kamata ace ta na nan ďin. AFTER FIVE HOURS ❤️ Liyana ta samu kanta har ta fara breastfeeding yaran duk da ciwo da kirjinta suke mata. A hankali ya buďe ķofar ďakin tare da shigowa ya na mai zama a kusa da ita. D’aya ce a hannunta take bama nono sauran kuma suna kwance a baby cot. Kallon su ya yi sosai tare da faďin “ Wacce na bawa Fatima a cikinsu ma?, I’m confused kin san kamar su ďaya.” Ya ķarashe maganar ya na mai ďaukan wacce ke ďan motsi da bakinta. “Gata nan a hannu na, ko baccin da sauran ke yi ba ta yi ba, sai cin abinci kawai take.” Ta ķarashe maganar ķwalla na ďiga a idanunta dan ta gaji yau kaďai wallahi. “Keep her lemme thank you well , because ďazu bacci na idonki ba sosai kika ji ba.” Ya yi maganar tare da ďauke ta daga kan cinyarta ya na mai maida ta a cikin yan uwanta. “Haihuwa ba Abu bane mai sauķi ba Liyana, kin sadaukar da jikin ki lafiyar ki rayuwarki, just for me naga ya’ya’na a duniya, Allah ya miki albarka, Nagode miki sosai bisa haķuri da juriyar da kika yi da ni tun daga ranar da muka fara haďuwa dake, you were sturbborn back then, Buh honestly your sturbborness is one of a kind, and I always love it that way ko a lokacin, Allah ya yarda dake ya taya mu riķo, don’t worry about what Marwa is saying earlier, let’s focus on our daughters, shower them with the love they deserved, wallahi Fatima babu wadda nake so a duniya sama dake idan kika cire Mami, may we always be happy with the zab’in da iyayenmu suka mana, no devil shall come against our happiness, I can’t thank you enough Liya bae.” Ya ķarashe maganar ķwalla na zubo masa. Tallab’o fuskarsa ta yi tare da share hawayen da ya zubo masa, sannan suka shiga kallon juna. Ķurawa juna lips suka yi sannan suka shiga bawa juna Wani kalar French kiss mai tsayawa a rai. Buďe ķofar da a ka yi ne ya sanya su ture junan su da sauri dan har sun manta inda suke. Nurses biyu ne suka shigo sakamakon kukan da jarirai ke yi. Da sauri liyana ta ďauki ďaya ba tare da ta kalli nurses ďin ba ta cigaba da basu ďaya bayan ďaya. Washe garin ranar da sassafe aka sallame su, ko da ya mayar dasu gida kiran maids ďin gidan ya yi sannan ya fita daga gidan ya nufi office, hours dinsa biyu ya gama abin da zai yi a office din, daga nan ya wuce shopping mall ya yi wa yaransa siyayya masu mugun yawa da tsada dan tun yau zai bawa pilot ďin jet ďin Abbhu….. TTHE REGRET🦋🥰 PENDING AMARYA CE📓🦋 J🦋 A🦋 W🦋👊🏿 THE NOBLE WRITERS TEAM ✍🏻 PENDING AMARYA 60 Nayi adding pages 📄 enjoy 😊 Washe garin ranar da sassafe aka sallame su, ko da ya mayar dasu gida kiran maids ďin gidan ya yi sannan ya fita daga gidan ya nufi office, hours dinsa biyu ya gama abin da zai yi a office din, daga nan ya wuce shopping mall ya yi wa yaransa siyayya masu mugun yawa da tsada dan tun yau zai bawa pilot ďin jet ďin Abbhu. Zaune take kan kujerar dake ďakinta ta ķurawa yaran dake bacci cikin cot ďinsu hankalinsu kwance ido, sanye take cikin wani body hug da ta ďora masa summer abaya Wanda ya dace da shigar jikin nata. Wayarta dake ring din video call ta ďauka domin ďagawa amma gannin Wanda Ke kiran nata ne ya sanyata ajiye wayar tare da lumshe idanunta ganin Mami ce mai kiran nata. Turo ķofar ďakin nata a ka yi a hankali Wanda Jin an bude ķofar ya sanyata ďago kanta dan a tunaninta Hydar ne, amma sai ta ga sab’anin hakan domin Marwa ce cikin shigar wani abaya mara nauyi, hannunta ďauke da tray wanda ke nuna cewa abinci ne a ciki. D’aure fuskarta Liyana ta yi kamar ta ga maķiyarta, ķarasa shigowa Marwan ta yi ba tare da ta tankawa mugun kallon da Liya ke bin ta da shi ba, ta ķarasa shigowa tare da ajiye abincin a kan center table ďin dake falon. “Liya ga abincin nan za ki iya fara ci kafin ya yi sanyi, sannan dan Allah idan babu damuwa ina son yin magana dake.” Marwa ta faďa ta na mai tsare Liya da idanunta. “Za ki iya faďan abin da ke ranki tun da abincin ba dole bane sai na ci.” Ta yi maganar tare da ďaukan wayarta. Zama Marwa ta yi a kan kujerar kusa da Liyanar a hankali tare da dafa gwiwar Liyanar da ta yi crossing ķafarta da shi. Wani banzan kallo da Liya ta bita da shi ba ta san lokacin da ta cire hannunta a jikinta ba tare da fara magana a hankali. “Ki yi hakuri da duk wasu abubuwan dake faruwa a tsakanina da Aliyu like kalar maganan dana faffaďa har ya zama sanadin haihuwar ki, na san ba sona kike ba tun kafin mijinki ya sanar dake duk wasu abubuwan da suka faru a baya a tsakanina da shi, amma ina so ki sani komai muķaddari ne daga Ubangiji, ba wai kuma zan faďa miki hakan bane dan ina Jin tsoranki, sai dan kawai na fayyace miki da cewa a zamanin da suka wuce ne Aliyu ke gaba na ba yanzu ba, duk da ina son shi.” Marwa ta faďa tare da gyara zamanta. “ Ki yi sauri kiyi maganarki dan Allah kafin mijina ya shigo.” Liyana ta faďa a ďan faďace. “Okay lemme go straight to the point, Na san ya riga da ya faďa miki da cewa mun yi soyayya a baya da……” Ba ta ķarasa ba Liyana ta ce “har haihuwa kun yi.” Murmushin yaķe Marwa ta yi sannan ta ďago da fuskarta tare da faďin “Yeah mun haihu tare, and the funniest part is that har yanzu ina kan rufa masa asirin da shi ya zama sanadiyyar tarwatsewar rayuwata.” Marwa ta faďa tare da goge ďan guntun ķwallan da ya zo mata. Sosai jikin Liya ya yi sanyi sannan ta ďago a hankali tare da faďin “Mai ya tarwatsa rayuwar naki?.” “Yarda!, Yarda Liyana, na san kin ji last call da muka yi da Aliyu a kan wani birthday da naje, she’s my close friend a kaff China ko Aliyu shaida ne, da akwai ranar da ni da su muka je wani hotel dan kawai mu huta dan Aliyu ya Saba min da idan a ka ďan yi tafiya a hotel muke zuwa mu huta ba a gida ba, toh a ranar mun je wani presentation wanda har Aliyu ya kama mana ďaki, bayan mun fito ma ni ya bawa key, then sai na kawo Qawayena cikin ďakin domin mu ďan huta. Ko da muka huta ma ashe a cikinsu wata ta saka camera a ďakin. kusan shekara 7 ana threatening ďina a kan porns video ďin ni da Aliyu, suka gayyato min wani guy ya kwana da ni a can Nigeria shine ranar da Aliyu ya kama ni da shi. Ko da na bi shi can North Korea ďin ma ashe duk setup ne Qawayena suka ďana min. Wallahi Liyana a yanzu ina da wanda yake son aure na amma sun hanani, because since lokacin suka nuna min bukatansu na joining lesbianism , sannan suka ce idan ban yi joining ba sai sun yaďa video ďin. Ni na gaji da duniyar nan no body loves me.” Ta ķarashe maganar hawaye na fita a idanunta. “Ai kin ga hotel, ke mai ya kai ki yarda da ķawance?, ni da nake nan sai da na shiga university sannan na fara ķawance shi ma dan kawai Asha ruwan tsuntsaye ne tun da nayi aure ban cika kulata ba, dan wallahi Aliyu nan gani nan bari, gwamma ki goge hawayenki mu san yadda zamu b’ullowa lamarin.” Liyana ta iddashe maganar a tausashe. “Na barwa Allah komai zai yaķe min duk wani azzalumi dake cikin rayuwata, sannan zan faďawa Aliyun duk abin da ke faruwa domin fitar porn ďinnan dai dai yake da b’ata komai nasa, domin Aliyu babban mutum nè a faďin duniyar nan ba ki ďaya.” Marwa ta faďa tare da fara ķoķarin tashi a wajen. “Da ya fi muku.” in ji cewar Liyana tare da ďaukan wayarta. Har dare gaba ďaya Marwa ke ta ďawainiyya da ita, amma duk da haka a wajen ta gani take Marwa babu abin da ta mata na burgewa. Yaranta kam Ma shaa Allah, kamanninsu ďaya farare tal- tal da su. Sai dare sosai sannan ya samu dawowa. A zaune ya tarar da ita cikin shigarta na kayan bacci ta na gyangyaďi hannunta na riķe da daya daga cikin jariran da sai tsula kuka take. “Sorry Wifey na bar ki da raino, kawo ta na riķeta kiyi baccin ki.” Aliyu da shigowarsa ďakin nasu kenan ya yi maganar tare da ajiye key din motarsa a bed sides. “Ya Alih mai sunan Mami tun tuni take ta kuka har yanzu bata daina ba, ka taimaka min dan Allah Kar ta mutu.” Ta ķarashe maganar muryarta a karye. “Daga kuka sai mutuwa?, normally yara na hakan ai, it’s a normal thing.” Ya ķarashe maganar tare da amsar Khairat wadda suke kira da Alynerh daga hannunta…… Wayyo Allahna manage gobe zan kokarta nayi muyi mu gama a week dinnan sorry for the late post🦋🥹🤌🏻😭 THE REGRET 🦋👊🏿 Pending Amarya ce🦋😇 J🦋A🦋W🦋👊🏿 The Noble writers ✍🏻 🦋🙏 Pending Amarya 61🦋🦋🦋🦋 “Daga kuka sai mutuwa?, normally yara na hakan ai, it’s a normal thing.” Ya ķarashe maganar tare da amsar Khairat wadda suke kira da Alynerh daga hannunta. Manna yarinyar ya yi a ķirjinsa sannan ya tashi a hankali tare da fara zagaye ďakin da ita yana mai ďan jinjigata. Tsagaita kukan Alynerh ta yi wanda hakan ke tabbatar masa da cewa bacci ta fara. A hankali ya ajiye ta a cot ďinsu na ďakin, sannan ya sanya bargonsu ya lullub’eta da shi. “Ahh Done with this young lady, saura kuma Mamansu, ban san da wani drama ta zo min da shi ba, wannan da take cuno baki, anyways I’m ready for you.” Ya yi maganar ya na mai kwanciya a kan gadon nasu. “Babu wani drama, na gaji da rashin ďaga wayoyinsu Mami da ka sakani, yaushe zamu koma gida?.” Ta yi maganar a shagwab’e. “Tomorrow in shaa Allah, just be ready, bara na ďan watsa ruwa wallahi na gaji da yawa Liya.” Ya faďa tare da fara shiga changing room din dakin. “Idan ka fito please ina son maka magana if you didn’t mind?.” Ta faďa cikin tattausar murya. “Sure, anything for you my dear.” Daga haka ya shige changing daga nan kuma ya shige bathroom. Babu tunanin dake zuwar mata kai sai maganganun Marwa da tun rabuwarsu a ďazun yake mata yawo a brain. Cikin mintunan da basu haura 20 ba ya fito daga banďakin ķugunsa ďaure da towel. Dressing room nasu ya shiga tare da ďauko kayan baccinsa daga clothset, sannan ya dawo ya feshe jikinsa da turarukansa masu tsadar gaske, sannan ya ďaura da kayan baccinsa masu taushi tare da ďaukan sleeping mask ďinsa ya nufi kan gadon da shi. “Ife, gani na zo mai zamu tattauna.?” Ya ķarashe maganar tare da ďaura sleeping mask ďinsa a goshinsa. “Ya Alih is about Marwa.” Ta faďa a sanyaye. “Mai ya faru da ita Marwan?.” “Ya Alih wallahi yarinyar nan ta na ganin rayuwa, rayuwarta ya rushe da yawa a dalilinka, kuma Billah ta rasa ta ya zata b’illowa lamarin har ya yi tsamari.” Ta yi maganar ta na ďan kallon reaction ďinsa. “Mai ta faďa miki.” Ya faďa da ďan zafi. Bata yi ķasa a gwiwa ba ta sanar da shi komai dake faruwa. Sosai ya girgiza da Jin lamarin da ta kawo masa, amma still bai nuna damuwarsa ba ya sanya slippers ďinsa tare da barin ďakin. Bai zarce ko ina ba sai ďakin Marwa, a hankali ya buďe ķofar ďakin tare da shigowa a hankali. Zaune ya tarar da ita ta bawa ķofar ďakin baya idanunta na kan laptop ta na kallon pictures ďinsu na da. “Why Marwa!, mai sa ba ki faďa min ba why?.” Ya faďa a sanyaye, “ ba ka fahimce ni ba a lokacin, ko da ka same ni da shurem you walk out on me ba ka bar ni na maka bayani ba, I chatted you on Facebook, what’s app, Telegram, instagram, Imo, gaba ďaya block ďina kayi, and now it’s too late, kai ma ka san da hakan.” Ta faďa tare da goge hawayenta. “waye a cikinsu yake threatening ďinki?.” “It’s Zola, my best friend.” Ta faďa a sanyaye da disassar murya. “kina da pictures ďinta wanda faces d’inta suka fito sosai?.” “Yeah ga su nan.” Ta faďa tare da nuna masa screen din wayar nata. “Tura min shi a wayata, har da na ubanta idan kina da shi.” Daga haka ya fice daga cikin ďakin. Ko da ya fita a ďakin na ta ma bai zarce ko ina ba sai study room ďinsa, sai da ya ďau kusan awanni biyar sannan ya gama haďa pictures ďin da ta tura masa tare da yi mata forward ďinsu. Har an fara kiran sallar farko hakan ya sanya shi yin sallah sannan ya koma bacci. Liyana kam maganar komawarsu Nigeria ba ķaramin farinciki ya sanya ta ba. Tun safe Chinese maid ďin ta shigo tare da yiwa babies wanka, sannan ta haďawa Liyanar ruwan wanka da sauran kayan gargajia da suke hadawa wankan masu jego da shi. Sai a lokacin ya samu daman fitowa daga study room ďinsa, direct wanka ya yi shi ma tare da yin brush sannan ya shirya cikin wasu black suits wanda suka mugun yi masa kyau. Wani black Mecury chiffon yard ta saka wanda ďinkin ya zauna ďass ďass a jikinta suka mata kyau mara misaltuwa, high heels ta saka black color, sannan ta naďe kanta da mayafinta, tisa yaranta a gaba ta yi ta na kallon kyakkyawar fuskarsu. wacca ta fara zuwa duniya ita ce Fatima suna kiranta da Alya, then wadda ta ci sunan Ammi suna kiranta da Aida sai Alynerh wadda ta ci sunan Mami…… Gobe zamu cigaba besties 👯 😂🦋🤌🏻 Allah ya huci zuciyar masu imani 🥰🥺🫩🦋👊🏿😂😂 THE REGRET 🦋💖 Pending Amarya ce 🦋🎉 J🦋 A 🦋W🦋 THE NOBLE WRITERS TEAM 🦋👊🏿📓🖇️ Pending Amarya 62💖 This page is Dedicated to me Pending Amarya 💖 wacca ta fara zuwa duniya ita ce Fatima suna kiranta da Alya, then wadda ta ci sunan Ammi suna kiranta da Aida sai Alinerh wadda ta ci sunan Mami…… “Ta so mu tafi driver na jira around 3 na yamma zamu sauka

Chapter 28 of 31