ba.
Sai wani crop top mai kyau milk color ƙafarta kuma sanye da slippers ɗin Gucci.
Kanta ba kitso tayi parking a tsakiya santala santalan cinyoyinta na ta sheƙi kamar kullum.
''Sannu da zuwa my Neneh.''
''Subhanallahi, Fatima ko fitina? , maza dallah je ki saka tufafi kin bar su lantana a buɗe haka?."
Ɗago kanta tayi a ta kai dubanta wurin Neneh, amma idonta bai sauka kan kowa ba sai wanda ke sanye cikin shigar manyan kaya kansa na sanye da hular nan ta zanna bukar............
"Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need."
*THE REGRET*
(Dana sani).
~PENDING AMARYA CE~
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.💪
*THE NOBLE WRITER'S TEAM*🐾🦚
_Our strength lies in Dedication_🤍
Am back to who I'm 🤝
A baya nayi sanya amma yanzu na ajiye son jiki agefe, akan kawo ƙarshen wani abu domin fara sabon abu.
Dan haka na kawo karshen sanyin jikina domin cimma nasarata.
Kafin na cimma nasarata sai na ajiye son jiki agefe.
Am Soo sorry everyone.
Pending Amarya as usual 🦋 But not like before 😌🥀🙌💎
_ Pending Amarya 31_
Parking ɗin mota Liyana taji a compound wanda a take ta saki spoon ɗin hannunta haɗe da arcewa da mugun gudu.
Salimah kawai da idanu ta bita.
''Assalamu alaikum jama'a.''
Muryar Neneh ta daki kunnen Liyana da saura ƙiris ta ƙarasa buɗe ɗakinta.
Juyowa ta kuma yi a million ta fara saukowa da gudu jikinta daman tun mini skirt ɗin yau da safe ne ba ta yi wani wankan ba.
Sai wani crop top mai kyau milk color ƙafarta kuma sanye da slippers ɗin Gucci.
Kanta ba kitso tayi parking a tsakiya santala santalan cinyoyinta na ta sheƙi kamar kullum.
''Sannu da zuwa my Neneh.''
''Subhanallahi, Fatima ko fitina? , maza dallah je ki saka tufafi kin bar su lantana a buɗe haka?."
Ɗago kanta tayi a ta kai dubanta wurin Neneh, amma idonta bai sauka kan kowa ba sai wanda ke sanye cikin shigar manyan kaya kansa na sanye da hular nan ta zanna bukar.......
Ta ma rasa mai ke mata daɗi, tana tsaye ta kasa gaba ta kasa baya.
Neneh dai neman wuri ta yi ta zauna tare da faɗin ''Mai kike wani gwaggwale ido kamar kin yi wa sarki ƙarya.''
Duba wurin da Sultan ke tsaye Neneh ta yi, ta ga babu alamar sa, kallon Liyana ta yi tare da ƙara faɗin ''Kin aike sa ne naga baya nan.''
Shiru Liyana ta yi sannan kuma cikin sassanyar muryarta ta ce ''waye shi Neneh?."
''Ke nifa ba tambaya nazo ki min ba, zuwa na yi na sanar miki Umaru ya mutu murus, yanzu daga wurin gaisuwa muke zanje kwaso kaya na na koma can ɗin, Ita kuma Maimu ƴar daɗi miji ta na can tana,suma ita ala dole mijinta ya mutu.''
''Innalillahi wa inna ilaihir rajiun!, Neneh kiji tsoron Allah.''
''Toh yo tsoron ki zanji, ku zubo min abin da ku ka dafa in ci,abinci ko wahala?, abicin gidan rasuwan duk yaji sai kace a gidan yarabawa, toh ina fama da gyanbon ciki ina Ajiddeh da cin fara da mai.''
Liyana ba ta tsaya jin shirmenta ba ta haura ɗakinta haɗe da sanya simple abaya mara kwalliya haɗe da himar sannan ta zira slippers tare da ɗaukan car key.
Ta sauko da ɗan gudunta.
''Ke dai Fatima ba ki da imani, a sanar dake mutuwa amma ko ɗigon hawaye babu balle kuka.''
''Dan kin sanar dani mutuwa sai na kama birgima a ƙasa tun da sunana Ruth?."
''Kar ki zagen.''
''Kyaji da shi kuma.''
Daga haka ta fice daga falon tare da faɗin. ''Salimah ki kula da gidan, ke kuma Neneh idan kin taho ki haɗo min da kayana.''
''Ba ni aka kawo miki yar aiki ba ai.''
Bayan fitar Liyanar kallon Salimah ta yi sannan ta ce ''Wai Salimah da ta tafi da izinin wa ta fita?."
''Neneh dai tare muke anan fa."
''Allah ya kyauta kowa dai fitsararre ne.''
Ko da Hydar yaje office ɗin Abbuhn ma tare suka je gidan rasuwar.
Sannan Abbuh ya ce masa ya kula da harkar komai na office ɗin tun da Sultan ke na Hydar ɗin.
Gidan ya yi maƙil da jama'a saboda Alhaji Umaru mai son jama'a ne sosai.
HYDAR bai iya zama gidan rasuwar ba saboda tausayi matan dake kuka ke basa, ga matarsa sai suma take tun da ya zo aka nufi hospital da ita, amma da rana zai dawo ɗaukan Abbuh.
Liyana kam gudu kawai take shararawa a titi har ta ƙarasa bachirawan, ko ina shiru a unguwar a hankali ta sauko daga motar idanunta duk ƙwalla babu wani alamar tsiwa a tattare da ita, a hankali ta tako har cikin gidan.
Ko ina maƙil yake da ƴan uwa da abokan arziki, kowa nata jimami Ammi na zaune kusa da Fatima yayarta da suke da uba ɗaya tare da ƴarta Yusrah, ƙarasawa tayi kusa da Ammin tare da faɗin ''Ammi ya haƙurin mu?."
''Da godiya.'' ta bata amsa a taƙaice.
''Ammi ina Ilham da Mama Maimu?."
''Ke wacce kaliyar sha³ ce da ba ki da hankali sannan kuma ba ki da tunani?, kina ganin halin da suke ciki za ki wani kama tambayar banza da wani wofi.'' inji cewar Yusrah dake zaune kusa da mahaifiyyarta y'ar gidan yayar Ammi ɗin her half cousin sister.
''Karki saki ki ƙara zagina tun da dai ba uwarki na tambaya ba!."
''Bara uba uwata kika zaga?!."
Kallonta Ammi tayi tare da faɗin ''Fatima kar na sake jin bakin ki anan.''
''Ba zan sake magana ba Ammi amma wallahi ta zagan sai na rama.''
Dariya Yusrah ta yi tare da faɗin '' banza kawai mara tarbiyya.''
''Da ni dake idan makaho ya shafa ya san mai tarbiyya da mara tarbiyyar ai, tsohuwar kilaki.''
''Ni kike kira da karuwa?."
Tashi Liyana ta yi haɗe da cire himar ɗinta sannan ta ce ''An kira ki ɗin, ki yi duk uban da za kiyi, ko zan daku ne?."
''Liyana I said ki daina cacar bakin nan ko?." Inji cewar Ammi.
''Ammi can't you see ita ta fara takalata ko uwar ta bata gani da zata hanata faɗe.''
Ammi bata ƙara kallonta ba ta cigaba da lazumin ta.
Yusrah ce ta kawo wa Liyana mari ita kuma ta sa hannu ta kare, kamar ba gidan rasuwa ba haka suka fara dambe a tsakaninsu kamar wasu karnuka.
Yusrah ce ta samu nasarar kama gashin Liyana hakan ya sa ta saki ƙara.
Sannan a hankali Liyana ta gartsa mata cizo, Mama Fatu ce ta zo ta fincike ƴar tata tare da faɗin ''Ke ba kida hankali da za ki biyewa wannan.'' ta faɗa haɗe da fincike Yusrah a hannun Liyana, tun da gaba ɗaya a bedroom na yaran gidan suke.
''Kar ki sake wallahi Mama Fatu ki ƙara zagina, karki ƙara cemin wannan.''
''Kull cire Maman nan kira ni Fatuh mara ɗaha kawai mai suffan shegu.''
''Suffar shegu kam kina ganin ƴar ki kinsan ta fi ni suffar shegu har da na shaiɗanu ba ki ɗaya, ki kalle ni daga sama har ƙasa ban yi ƙari da komai ita kuma ƴar ki fa?."
Ƙanƙance idanunta Mama Fatuh ta yi tare da faɗin ''Ke da aka aurar dake saboda kuɗi fa?.''
''Da kema za ki samu ki aurar da ɗiyarki saboda kuɗi da kin fi kowa murna.'' Liyana ta ƙarashe maganar da tsirawa Mama Fatuh ido.
''Ba dai aure ba?, mu zuba mu gani.''
''Shege ka fasa, in fitsari banza ce kaza ma ta yi mu gani, ƴa ta gama ruɓewa kin zo kina wage wawwaran bakin ki duk kin hanani sukunin."
''LIYAANAA!." Ammi ta faɗa da ƙarfi.
''Ammi ki ƙyale ni.'' ta faɗa haɗe da cuno baki.
''Ikimat a gaban ki ƴar ki ke zagina haka ba ki ce komai ba.'' ta faɗa tana kallon Ammi.
''Ahh wallahi da sauran tarbiyya ta ni bake na zaga ba, aatoh kar ki kaini inda Allah bai kaini ba.''
Jiddah ne da yaji hayaniya ya fara yawa har matan dake waje sun fara shelantawa a tsakaninsu, hakan ya sa shi shigowa cikin ɗakin tare da yiwa Liyanar magana ''Ya Zahra mai kuke yi haka?, ko kun manta wurin rasuwa ne nan ɗin?."
Sassauta muryarta ta yi haɗe da basa haƙuri.
''Toh kar akuma."
''In shaa Allah jiddah.''
Daga haka ya futa daga ɗakin.
Sai data fakaici idon Ammi da Mama Fatuh data ajiye kanta kamar ta Allah, daman Yusrah nada kumatu manya manyan nan, hakan ya sa ta kwaɓe mata fuska haɗe da faɗin ''Shegiyya.''
A fusace ta ɗago kanta saboda yadda masifa ke cinta wayarta ƙirar iphone fourteen promax ta cillawa Liyanar wanda hakan ya sa wayar ta fashe tare da yin blank.
''Wa ya gaya miki ana nufan ƴar gidan Nabil da sharri a wanye lafiya, U la la.'' ta ƙarashe maganar da gwalo da kuma dariya mai cin rai sannan ta fice daga ɗakin.
Ammi ta ma rasa bakin magana ta rasa ya zata yi da lamarin Liyana, ta san wace Mama Fatuh ta san mai za ta iya aikatawa ba ta ƙi ta lalata rayuwar Liya ba .
Tunani sun mata yawa akai berekete, ga mahaifiyyarsu bata farka ba har yanzu Neneh ma shiru bata dawo ba.
Gasu Fati ƙarama har yanzu daga kai order kayan sadakan uku basu dawo ba da ita da ƙanwar Mama Fatuh, Mansura ma bata iso ba ( Fati ƙarama ƙanwarta da suke uwa ɗaya uba ɗaya, su biyu mamansu ta haifa).
''Yaro bai san wuta ba sai ya taka.'' jiin kalmar da Mama Fatuhn ta furta shi ya dawo da ita daga dogon tunanin data lula.
Liyana kuwa ko da ta fito daga cikin ɗakin a compound ta yi zamanta tana ƙwalla dan yanzu wani kalar taƙaicin biye wa Yusrah take.
Ga wani tuna marigayi da ta yi, Idan ya na mata wasa tana masa shan ƙamshi idan yana kiranta matarsa ashe dai ba zasu gana ba.
Ta takura kanta wuri ɗaya tana kukanta.
Sallamar da aka yi ta amsa tare da ɗago kanta tana kallon Unaisa da ta janyo wani ɗan trolly fuskarta duk hawaye sakin trollyn tayi tare da rungume Liyanar ta na faɗin ''Papi is gone!.'' haka suka yi ta raira kukan sannan suka kai kayan nasu ɗakin jikoki dake gidan.
''Ina Mama Maimu?." Unaisah ta tambayi Liyanar.
''She fainted kusan sau biyu, because a hannunta wai ya mutu.''
''Allah sarki ya rabbi I need this kind of love.''
Tsaki kawai Liyana taja tare da faɗin ''Zo ki raka ni gidana dan Allah.''
''Awwn kaga masu gida.''
''Y'ar iccar kawai.''
''na kai ki?."
Duk da suna cikin jimami hakan bai hanasu murmusawa ba.
Daga nan suka tashi tare da ɗaukan wayarta da car key ɗinta suka yo waje.
Ko da suka isa ƙofar gidan ma Sultan ke tsaye da Ilham wacce ke sanye da hijaby lemon green da ya haska mata fata.
Kallo ɗaya ta yi musu sai taji ba zata iya tafiya ba hakan yasa ta bawa Unaisah car key ɗin haɗe da nufar wurin da suke tsaye.
Cikin takunta na slay queens in hijaby (😂😂🤧). Ta iso wurin da suke tare da faɗin ''Ilham mai kike a anan.''
''Yaya Liyana tambayarki yake fa, yawwa Yaya Sultan here she is, amma fa as I said she's married, na barku lafiya.''
Kallonta ya yi sosai haɗe da barin jinginar da ya yi wa motar ya dawo yana bawa gidan baya ita kuma ta jingina da motar tare da folding hannunta haɗe da kallon sa da kyau sannan ta ce '' faɗi mai ke tafe da kai am all ears.''
''Liyana how could you?....."
'' How Could I what?....huh.""
Ta faɗa tana hura iska a fingers ɗinta haɗe da ɗage girarta guda ɗaya.
" Got married without telling me?."
Murmushi ta yi mai sauti sannan kuma ta tsuke fuska kafin a hankali ta kuma faɗin ''As you be my papa?."
Ta ƙarashe maganar da murmushi akan fuskarta wanda hakan yayi dai - dai da fitowar Hydar tare da Abbuh saboda bayan yaje office ɗin ya dawo gidan rasuwar da rana saboda mayar da Abbuh wurin aiki.......
To be countinue tomorrow in shaa Allah!!. babu sanya al'amarin pending amarya yanzu 😩🤧🎊
"Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need."
*THE REGRET*
(Dana sani).
~PENDING AMARYA CE~
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.💪
*THE NOBLE WRITER'S TEAM*🐾🦚
_Our strength lies in Dedication_🤍
_ Pending Amarya 32_
Ta ƙarashe maganar da murmushi akan fuskarta wanda hakan yayi dai - dai da fitowar Hydar tare da Abbuh saboda bayan yaje office ɗin ya dawo gidan rasuwar da rana saboda mayar da Abbuh wurin aiki.......
Wani kalar kallo ya watsa mata sannan ya kalli Abbuhn da bai ma lura da wa'yanda ke tsaye ba suka wuce cikin motar nasa.
Hararan gefen ido ta wurga masa sannan ta cigaba da magana da Sultan ɗin dake ta faman yi mata magana, amma tasa kanta gefe guda tana wasa da zara-zaran fingers ɗinta.
''Ka gama?, nace ka gama?, ban hanya na wuce.''
Daga haka ta bi ta gefen sa haɗe da shigewa cikin jeep ɗinta.
Acikin motar ma kasa driving ta yi ta rasa mai ke mata daɗi kawai Unaisah ta bawa car key ɗin domin taja motar dan a halin yanzu babu abin da take tunawa kalar rayuwar ta da Sultan and she ended up marrying his elder brother.
''Ya subhanallah.'' ta faɗa a fili.
Sannan ta jinginar da kanta a jikin kujerar motar, kawai tunanin yadda suke soyayya take, the kisses, the hugs, yanzu ai da kunya ta buɗi ido ta ganshi a matsayin ƙanin wanda take aure.
*NOTE.*
_Ƴan mata masu sakarwa samari ragamar jikinsu ku bi a hankali because baku san ya ƙaddara zata kasance da ku ba._
Za ta ji nauyin zuwa gidan surikanta ma bama Sultan ɗin kaɗai ba, Allah yasa ma surutu irin na Sultan ɗin babu wanda ya faɗawa kalar haukan da take yi da shi.
Har Unaisah ta iso gidan bata sani ba sai da ta yi horn, sannan horn ɗin ya fargar da ita daga nisan tunanin da ta lula.
Ko ina na gidan tsaff Salima ta gama gyara ko ina dan yanzu har wajen 4 ta gauta.
Ƙamshin turare ya gauraye ko ina ga wani sanyi da ɗakin ya ɗauka.
Salimah na zaune cikin falon jikinta sanye da hijaby tana wayarta hankali kwance.
Shigowar Liyanar ne ya sa ta katse wayar tare da faɗin ''Aunty Liya sannu da zuwa.''
''Yawwa, mai kika girka?."
''Dambun jollof ne.''
''An bar miki kayan ki, dafa mana pasta kafin mu fito please.''
''Toh Aunty.''
Daga haka suka bar falon ita kuma Salimah ta shiga kitchen domin dafa musu pasta ɗin.
Shigarsu saman ma komai tsaf - tsaf da shi sai ƙamshi yake mai bada nutsuwa.
Sai a lokacin ta kunna wayarta haɗe da faɗawa Lily rasuwar da aka yi musu.
''Hello lily.''
''Bae what's app nah.''
''Wallahi normal.''
''Bae tun safe ake cigiyar ki a online, wai first in history ƴar Nabil tayi offline for 2 hours.''
''Wallahi My Grandpa just japa recent.''
''Jehooovaaaa, how comes wetin come happen?."
''Person no go die again?."
''Dalla bae am surprised ne ai ta ya Jiddah zai mutu haka?."
''Thunder go fire you, bastard."
''Ahh bae mai na yi kuma?."
''Ba Jiddah ba fa papi.''
sun daɗe suna hirar sannan ta katse wayar.
Kaya kusan kala goma ta ɗiba da hijjabai biyar sai slippers biyu, sai laptop da kuma charger da brush da soson wanka da sabulanta da kuma mayukanta na jiki.
''Wannan kayan fa hajiyata.'' Unaisah ta faɗa tana ƙafe Liyanar da eyes.
''Na gidan rasuwa ne mana.''
A daidai nan Salimah ta yi sallama haɗe da shigo da pasta ɗin daya ci crab fish da gasasshen kaji, sai ƙamshi yake.
''Ga abincin nan.''
''Godiya muke hajja Salimah.'' Liyanar ta faɗa tare da janyo plate ɗin.
Salimah bata ce komai ba ta fita daga ɗakin.
Abincin suke ci hankali kwance suna hirar su gwanin burgewa.
A haka har suka gama cin abincin sannan ta shiga toilet ta yi wanka haɗe da shiryawa cikin simple dress mara hayaniya.
Ta yi kyau sosai ga yamma ta yi dan an fara kiran magriba.
Key ɗin ta ɗauka haɗe da trolly ɗinta sannan ta fito parlourn Salima na zaune ta na kallo.
''Mai kike yi tun ɗazu haka a zaune ba ki shirya ba?."
''Aw!, wai Aunty da ni za ki tafi.''
''Malama ba zan tsaya dogon turanci ba, taho mu tafi.''
''Toh.''
Daga haka Salimah ta shiga ɗakin ta in less than two minutes ta fito da wani ɗan kit.
daga haka suka fita daga falon tare da nufar motar Liyanar.
Wani kalar gudu take shararawa wanda ba'a jima ba suka iso ƙofar gidansu Ammin dai-dai kiran sallar isha.
Gidan kowa dai shiru babu mai tankawa kowa Unaisah da Salimah ne suka kamo mata trolly ɗinta suka kawo mata shi har cikin ɗakin.
Sannan ita ma ta mara musu baya.
Yusrah ce zaune kan gadon dake ɗakin Sandy Rash da Classy Reeda na zaune kusa da ita duk suna hira sama- sama.
Shigowar Unaisah da Liyana ne ya sa su farinciki haɗe da baƙin ciki duk a lokaci ɗaya.
Sannan kuma suka fara hira.
ILY ce ta ƙaraso cikin ɗakin haɗe da ajiyewa kowa abincin sa sannan kuma ta zauna tare da ƙurawa Liyana ido.
''Aunty Liya ko ki neme ni.''
''Sannu Ikimat, ko nace sannu Nabil.''
Matsowa ta yi kusa da Liyanar ta ɗan dake ta sau uku a ƙirji tare da faɗin ''Blood.''
''Sai dai period ba blood ba.''
''Ke dai da bak'ar magana, ance ki je ki ɗauki abincin ki.''
''Wa ya dafa?.
''Mama Fatuh ce.''
''Ill!, never!."
''Mai kike nufi?."
''Ba zan ci ba wallahi.''
Yusrah da tun lokacin da Liya ta shigo take jin wani kalar baƙin ciki na lulluɓe ta ne ta ce ''za ki ci kaza kazanki.''
''Toh mai kike ci na baka ba falling down.'' Liya ta faɗa haɗe da murmusawa.
''Uwarki za'a kwaɗan ta min naci.''
''Ahh wallahi kin yi kala da mayu daman, ni nafi ƙarfin na yi dake sai dai nayi da uwarki, dan haka ki aiko min ita da ita zan yi.''
''Bara uba........''
To be countinue tomorrow in shaa Allah!!. babu sanya al'amarin pending amarya yanzu 😩🤧🎊
"Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need."
*THE REGRET*
(Dana sani).
~PENDING AMARYA CE~
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
*THE NOBLE WRITER'S TEAM*💎
This page is dedicated to UNAISAH (Miss chubie)💎🌕
Barka da jummah my lovely fans 👥🫂
•°•°• Pending Amarya ce 33 •°•°•
''Ahh wallahi kin yi kala da mayu daman, ni nafi ƙarfin na yi dake sai dai nayi da uwarki, dan haka ki aiko min ita da ita zan yi.''
"Bara uba......."
''Bara uba, dani kike?."
''Ba ki ji mai nace ba da uwarki nake.''
Kafin Yusrah ta ƙara wani maganar su Rashanda da Unaisah suka fara bada haƙuri da haka dai kowa ya yi shiru.
Sai tsaki dake tashi a ɗakin different types of sounds.
Hayaniyya ke ta tashi a tsakar gidan wanda ke nuna alamun wani ne ya ƙara zuwa a cikin dangin.
Kowa ya shirya cikin kayan baccinsa, banda Liya kaɗai dake zaune ta na aikin chatting da wata ƴar class ɗinsu ta secondary school da suka haɗu ta IG (Instagram).
Sai da ta ga 11 ta ɗan gauta sannan ta kama cire kayanta haɗe da ɗaura towel ɗinta domin ta ɗan watsa ruwa.
Cikin ƙanƙanin lokaci ta fito ɗaure da towel haɗe da goge jikinta tare da sanya kayan baccinta, haɗe shafe jikinta da turarenta na Almiski wanda ta saba shafawa.
Ko da ta kai dubanta kan gadon ma har kowa ya yi occupying wurin kwanciyyar, duk sun fara bacci amma ban da Unaisah da take latsa laptop ɗinta ta na haɗa wani rahoto da zata bayar a gobe.
''Toh ni à ina zan kwanta?." Ta faɗi hakan tare da kai dubanta zuwa wurin Yusrah data baje a kan gadon.
Unaisah ce ta gyara zaman glasses ɗinta sannan ta kalli Liyanar haɗe da faɗin ''Ki ce musu su gyara kwanciyyarsu because ni ina gamawa a ƙasa zan kwanta ke kuma naga you're not a fan of kwanciyar ƙasa.''
''Ba zan iya kwanciyya a ƙasa ba just tell this girl to shift for me, duk ta cinye wurin.''
''Ni fa Liya karki ce za ki yi faɗa da daddaren nan idan ma falo ne kije ki kwanta a coach ɗin palo ko ki kira mijinki ya zo ya ɗauke ki ki koma gidanki.''
''Babu wanda zan kira a ɗakin nan zan kwana no matter what wallahi.''
''Ai shikenan.'' daga haka ta cigaba da danna laptop ɗinta.
Fincike filon da Yusrar ke kwance ta yi wanda ba shiri ta tashi daga barcin, wanda hakan ya saka faɗa a tsakaninsu, Neneh ce ta shigo cikin ɗakin tare da mutan gidan, su Rashidat da Faridat duk sun tashi daga barcin, Ilham kuma daman a wurin su Ammi ta kwanta duk tare suke da su Nenehn.
''Mai ya faru haka da ba zaku bari muyi bacci ba shima Umaru ya samu salama a inda yake kwance eh?."
Yusrah ce ta doka wani ɗan banzan tsaki haɗe da hararar Nenehn.
''Ai ba dake nake ba cangali tsone, da jiƙata nake.''
Rashidat ce ta yi wiƙi - wiƙi da ido tana kallon Nenehn sannan kuma a hankali ta buɗi baki ta ce ''Neneh bacci muke hayaniyar su ce ta tashe mu.''
''Duk yadda aka yi Ikimat kin ci zabi da cikin ƴar nan, taho muje can ɗakin Maimun ki kwanta acan ki ƙyale wannan kayan wankin mana.''
Liyana ce ta kalli Nenehn haɗe da faɗin ''Wallahi Neneh babu inda zani, kuce mata ta matsa min na kwanta tun da ba na ubanta bane.''
Yusrah ce takalli mutanen ɗakin kafin kuma ta murmusa tare da faɗin ''A gaban ku dai take zagina kuna ji kuna gani ko?."
Ilham da tun ɗazu abin ke sosa mata rai ne ta fincike Liyanar daga ɗakin.
''Ily ki cika ni kafin na wanka miki mari.''
Ko kallonta Ily ba ta yi ba ta shigar da ita ɗakin nasu, sannan a hankali ta fara magana ''Wai ke ba za ki nutsu ba fisabilillahi, kullum akan ki Ammi ke kukawa, ki tsaya mana ki duba lamarin nan, ke idan ta miki magana ko ta tsokane ki ba za ki iya over looking ba kawai ki barta, dole sai kin shiga harkokin ta?, haka jiya da yamma Sultan na waje kuka yi ta dambe haka maƙota ke ta yayatawa, just ki barta please.''
Ta ƙarashe maganar haɗe da miƙa mata ruwan sanyi domin ta sha.
Nannauyen ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce ''Naji amma wallahi aka min sai na rama.''
Daga haka suka kwanta haɗe da yin bacci.
Washegari da safe ma ko kallonta bata yi ba kuma Mama Fatuhn ce ke raba abincin safen fankaso da kunu, bata bi kan abincin ba ta sa Salimah komawa can gidan ta yo mata girki ita da su Unaisah suka ci kafin ta tafi aiki.
Ko ina na gidan shiru dan Liya baccinta ta ɗinga shararawa.
A haka rayuwa ta cigaba kewar Alhaji Umaru na yaɗewa a zukatan su yayin da yau ake sadakar bakwai na marigayin.
Tun safiyar yau Jiddah da Abbhi ke zuwa gidan marayu da talakawa marasa ƙarfi ake ta rarraba musu kayan abinci haɗe da tallafawa masallatai.
Gidan ruwa da ake siyarwa da masu ga-ruwa ruwa sai da suka rarraba musu kuɗi sosai domin al'ummar musulmi su amfana a kuma raba musu shi kyauta.
Sosai suka kashe kuɗi akan sadakar bakwai ɗin yau.
Mama Maimu kuwa a hospital results sun nuna da cewa hawan jininta ne ya yi mugun tashi, domin sai yau ta farfaɗo.
Tun da ta farfaɗo ɗinma kuka kawai take Neneh na bata haƙuri, amma sai ya ɗan ƙara warware wa zata dawo gidan.
Mr Ali namu kuwa shima wurin bada nashi gudunmawa ba'a barshi baya ba dan sosai ya turawa Jiddah kuɗi a account ɗinsa.
Ga kullum Mami sai ta takurasa akan ya kawo mata Liyanar yanzu almost wata uku da auren basu zo ba in banda shi da yake sintiri, idan Sultana ta ce za taje kuma sai ya ce zai karya ta idan ta taka zuwa gidan.
Yau dai kam su Liyana sai ƙasa ƙasa ake da kai dan su Mami da Abbuh zasu zo gaisuwa har ma da Hydar ɗin.
Ita wani kalar kunya take har addu'a take Allah ya sa kar azo da Sultan.
Ammi ce keta bawa Salimah da Ily order su ɗan dafa abinci saboda baƙin da za'a ɗan yi.
A hakan dai har suka gama girkin.
Ƙarfe sha biyu dai-dai su Mami da Abbuh da Hydar da Assultanah suka hallaro.
Gidan da ɗan hayaniya amma ba sosai ba.
A haka har suka shigo cikin gidan, palon Umaru ɗin da ake tarban baƙi.
Basu wani jima ba Ammi da Neneh suka shigo haɗe da gaisawa dasu Mamin, shi dai tun da ya kalli Ammi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 31