Share this page
dan sura mai kyau ɗin nan ji yayi kamar ya koma gida. Daman kuwa bai yi nisa da Gidansa ba ya yi parking motar tare da faɗin ''Ummi Amir ya ja ki i forgot something at home, gobe sai na zo wurin Abban.'' ''Is Okay Son je ka wurin matar ka duk da naga ta yi baƙin dare.'' Amir kam banda dariya babu abin da yake. Bai kula sa ba ya fice a motar tare da sosa ƙeyarsa, Amir ya dawo wajen mazaunin driver, sai da ya yi wa Amir kallon warning sannan ya wuce ya kama hanyar gidansa. Bayan Liyana ta dawo ma sa wa tayi Ily ta kashe gas sannan suka fara hira har da Salimah. Ƙamshin turarensa ne ya fara sanar da ita wanda zai iso wurin, hakan ya saka ta ɗan lumshe idanunta na y'an daƙiƙu tare da sauke su akan kyakkyawar fuskar sa. Wani kalar murmushi ne ya suɓuce mata wanda ba ta yi aune ba. Gaisuwan da yake amsawa ne ya dawo da ita daga duniyar da ta lula. Kallon wadda ya sanya aiki zaune ta na hira da ya'n uwanta yayi. Wani kallo ya watsa mata haɗe da faɗin ''Ina abin da na sanya ki?.'' Turo lips ɗinta ta yi tare da kai dubanta wurin da yake tsaye tare da faɗin ''Ai Ummin ta tafi.'' Sai da ya kalli fuskan ya'n falon sannan ya ce ''Biyo ni." ''Ina ɗin zan biyo ka?." Bai kulata ba ya cigaba da tafiyarsa. Kallon su Reedah ta yi tare da faɗin ''Wai ƙarfe nawa za ku tafi ne?." ''Anan za mu kwana.'' Rashidat ta faɗa ta na kallon fuskan ya'n uwanta. ''Cabɓ, tun da kuka zo ya ƙafe ku da idanuwa, wallahi ku taso ku kama hanyar zuwa gidan Abbhi, haka kawai, akwai fa aure tsakanin ku.'' ''Kaji Liyana da wani zance, Allah na tuba, gaskiya wannan maganar ta ki ta ɓata min rai ainun.'' Unaisah ta faɗi hakan tare da cire glasses ɗinta. ''Ai wallahi sai mun kwana, Ilham kunna mana TV abeg.'' Faridat ta faɗa haɗe da shingiɗewa akan kujerar parlourn. Tsaki ta ja tare da barin wurin. Tsaye yake a wajen corridor ɗin ɗakinsa tsawon minti biyar ya na ta jiranta, cikin muryarta da yake jinsa har brain ɗinsa ta ce ''Gani.'' ''Saboda iskanci kin wani shanya mutum kamar mai jiran zuwan sarki, ko kin fara hauka ne.'' ''Ni ka daina kira na mahaukaciya tun da ba a bola ka tsince ni ba.'' ''Are you talking to me.'' ''Allah ni ba da kai nake ba.'' ta faɗa tare da niyyar arcewa aguje. Fizgota ya yi tare da haɗe ta da jikin bango, hannunsa ɗaya ya dafa a bangon da'yan kuma ya na mai riƙe haɓarta da shi. Mutsu - mutsu ta shiga yi da bakinta da har lokacin lipstick ɗin bai goge ba. Tsirawa bakin ido ya yi tare da matsowa da fuskarsa gab da nata lumshe idanunta ta yi sosai ta na Allah Allah ya sa sumbatar ta zai yi. Hydar da mutsu - mutsun da take da bakinta ke ƙara birgesa hakan ya sa ya ƙara matso da face na sa. Hannunsa na tsakiya da kuma na ƙarshe ya haɗe tare da balle mata lips ɗin har sau biyu. Liyana dake tsammanin jin lips ɗinsa ne taji wani kalar azaba ba ta san time ɗin da ta buɗe ido ba ta ware su akansa haɗe da riƙe bakin nata. Ranƙwashi ya ƙara sakar mata haɗe da faɗin ''You're expecting me to kiss you right?, toh Allah ya tsare bakina.'' Liyana saboda zugin da bakinta ke yi har ta fara ƙwalla. Tsaki ya yi tare da faɗin ''Spoiled brat.'' sannan ya shige ɗakinsa haɗe da kulle ƙofar da ƙarfin tsiya. Fashewa ta yi da kuka haɗe da durƙushewa a wurin. Su Ily kam da suka gaji da zama tashi suka yi suka fita a gidan tare da tafiya gidan Ammi. Daga ƙarshe dai Liyana sai da ta kusa hour ɗaya a wajen ta na gunjin kuka, sai da ta ji alamun kamar zai buɗe ƙofa sannan ta shige corridor ɗin ɗakinta tare da shigewa ɗakin gaba ɗaya. Can ɓangaren Hydar hakan nan yake jin wani kalar mix feelings a tattare da yarinyar. He dislikes her habits, not her, amama wani ɓangare na zuciyarsa gaba ɗaya yake ƙinta. Safa da marwa ya shiga yi tsakanin falo da master room ɗinsa, shi haka kurum yake son ya yi punishing ɗinta. Ace matar da ya aura babu kalar club da gidan nanaye da ba ta sani ba. He always wants kamilalliyyar mace for his self, the one with Deen, ƙarshen zance kuma wacca idan ba Hijab ta saka ba she will feel that the whole world ita suke kallo. Saɓanin wannan da su Mami suka zaɓa masa, wadda ko da lingerie za ta iya zuwa duk wata duniya da ta ga dama ba tare da ta ji ko ɗar ba, ba ya jin ta iya karatun Alkur'ani mai girma, kullum cikin waƙa take kamar jiƙar Bob Marley. Idan ya ce an cuce sa a wannan haɗin bai yi ƙarya ba. Dubi mahaifiyyarta mutuniyyar arziƙi he can remember ranar da ta basu 5, 5k shi da Amir. Very cheerful giver, uwa uba hankali, shi ma Dad ɗinta is something similar with the girl. Wani kalar tsaki ya ja tare da shigewa toilet ya ɗauro alwala tare da gabatar da shafa'i da wuturi haɗe da kwanciyarsa amma still baccin is no where to be found tunanin Liyana ya masa kane - kane a rai. Ɓangaren Liyana kam tun da ta shiga ɗaki recalling ɗin haɗuwarsu da shi take tun lokacin da suke 100lvl. Da akwai ranar da suka fita da Ily da aurensu ya na jingine da jikin mota ta sheƙar da ruwa a jikinsa da gangan, and that day ma a maimakon ta ba shi haƙuri sai ma gwalo da ta masa tare da faɗa masa ta ga uban da ya tsaya masa. Haka tai ta tariyo duk wani abubuwan da ta ɗinga masa wanda sai da suka saka ta kuka. Duk da yanzu almost 2 Weeks da saninsa a matsayin mijinta, buh that guy is very dangerous, he can squeeze her a lokaci ɗaya a manta da babin ta ''Ya rabb have mercy upon me.'' Ta faɗa haɗe ƙanƙame jikinta, sannan a hankali ta shige toilet haɗe da yin wanka ta fito ɗaure da wani white towel. Drying ɗin gashinta ta yi tare da zira kayanka da take Sallah da shi, bayan ta idar da sallar ma sai da ta ɗan roƙawa kanta tsari sannan ta kwanta bacci dan gobe za ta fita school. Su Ilham kuwa tun da suka baro gidan Liya kowa ransa yake a ɓace, barimma Unaisah da Rashanda. Ammi dai tun ta na tambayar na su har ta daina, Rufaidhat kuwa daman ko gidan rasuwa ba ta je ba , a cewar ta da iyayenta suka mutu Ikimat ɗin ba ta zo ma ta ba. Ɓangaren gidan rasuwa kam bayan fitar Liyanar da Hydar Abbhi sai da ya tayar da maganar, haɗe da ƙoƙarin kiran police, amma da Jiddah ya tsawatar masa sai ya bawa police ɗin haƙuri haɗe da faɗa musu is a family issue. Mama Fatuh da Yusrah kan sun gama ƙullace - ƙullacensu sannan suka koma can gida Niger, Maraɗi inda acan Mama Fatuhn ke da aure. A taƙaice dai gidan ya watse daga Mama Maimu sai Mama Lantana mahaifiyarsu Mama Fatuh. Sai dai mu ce Allah ya jiƙan Ummaru da gafara. Washegari da sassafe kafin ta tashi har Salimah ta tanadar mata emergency ɗinta dan wani kalar ciwo da jikinta ke yi saboda aikin da ta sha jiya. Zaune take akan dinning table ta na cin milky donut ɗinta da strawberry hollandia ɗinta hankali kwance ta na ci ta na lumshe idanunta haɗe da chatting da Lily. Ƙamshin turarensa ne ya fara ziyartarta haɗe da dagule lissafinta ta dabarbarce lokaci ɗaya. Cikin shigarsa na gym ya shigo hannunsa ɗauke da bottle water da kuma hanky. Kallonsa ya kai wajen dinning ɗin take zaune cikin wani faux fur v neck jacket black color sai wani crystal jeens palazzo trousers shima black color kanta ɗaure da wannan ɗan kwalin nata na martar minista. Ƙafafunta sanye da wani classy crystal boots white color designers mai shegen kyau da tsada. Sai kuma wani gucci bag white color akan table ɗin dinning ɗin. Sai idanunta dake sanye da wani glasses mai form ɗin medical glasses Wanda ta saba sawa. Tun da ya shigo kanta yake a tsugunne, jin idanunsa na yawo akanta hakan ya sanya ta fara ɗagowa a hankali tare da sauke idanun ta akan nasa for the second time. A dabarce ta ce ''Goo.... Good.....mor.....ning.....Yaya Alih.'' ''Morning.'' ya amsa a taƙaice tare da shigewa cikin kitchen ɗin dake bayan ta. Wani sassanyar ajiyar zuciya ta sauke haɗe da shigewa kitchen ɗin itama dan ta ɗauki package ɗinta ta wuce school....... *Durrah Hydar.*✍️ "Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need." *THE REGRET* (Dana sani). ~PENDING AMARYA CE~ *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* *THE NOBLE WRITER'S TEAM*💎 This page is dedicated to you my favorite brother. Yaya Sa'id dinaa 💎 Allah ya shiga lamarin ka Alhajina.🦋🎊 Burin kowace y'a mace.👥🌕 May Allah's blessings always be with you Fav miii 👥 Iganya miii🫢💪 _ Pending Amarya 37_ Tun da ya shigo kanta yake a tsugunne, jin idanunsa na yawo akanta hakan ya sanya ta fara ɗagowa a hankali tare da sauke idanun ta akan nasa for the second time. A dabarce ta ce ''Goo.... Good.....mor.....ning.....Yaya Alih.'' ''Morning.'' ya amsa a taƙaice tare da shigewa cikin kitchen ɗin dake bayan ta. Wani sassanyar ajiyar zuciya ta sauke haɗe da shigewa kitchen ɗin itama dan ta ɗauki package ɗinta ta wuce school. ★_______________________★ Ko da ta shigo kitchen ɗin ya na tsaye a gaban coffee maker ya na ƙoƙarin juye coffee ɗin a cikin mug, a hankali ta iddasa shigowa haɗe da nufar kan kitchen island ɗin ta ɗauki abin da Salimah ta mata packaging, ''Where did you think za ki je by this time.'' ya ƙarashe maganar ya na mai juya milk a cikin coffee ɗin, kallonsa ta yi da kyau sannan kuma ta juya da niyyar ficewa daga kitchen ɗin. ''One step kika ƙara sai kin gane shayi ruwa ne.'' ''Toh ni dan Allah mai na maka?." Ta yi maganar kamar za ta fashe da kuka. ''Ba za ki fita daga gidannan da wannan kayan ba, find something better to wear, otherwise babu inda za kije.'' ''Amma ai a haka nake fita daga cikin gidan nan for almost 4-5 months, and besides wannan shigar nake tun ina gidanmu har a gidan kakanni na.'' ''Ba na magana biyu, find something else to put on, leave my presence.'' ''Yaya Alih.'' ''Ba ni da ƙanwa irinki.'' daga haka ya zo zai wuce ta gabanta, da sauri ta riƙe rigarsa tare da faɗin ''Pleaseee.'' ''Ƙyale min riga na ko na zuba miki ragowan abin da ke hannuna.'' ''Dan Allah ka yi haƙuri, ai kayan ma a lefe aka saka min wallahi.'' ''Cika min riga ta na wuce, wai yaushe ma na fara wasa dake to this extent.'' ''Allah ni ba zan cika maka rigar ba , You have to say yes, an.....'' Bai bar ta ta ƙarasa maganar ba ya watsa mata ragowan coffee ɗin ba ki ɗaya haɗe da sakar mata ranƙwashi a kai. Ba zato ba tsammani Liyana ta ji saukar coffee mai zafin gaske a fuskarta, a gigice ta saki ihu haɗe da riƙe fuskan na ta. ''You think that ba zan iya ba right?." Ya na faɗin hakan ya ja tsaki haɗe da ficewa a kitchen ɗin. School ɗin da bata je ba kenan. Da ƙyar ta lalubo hanya ta wanke fuskarta a sink ɗin dake kitchen, jacket ɗinta duk ya ɓace da coffee ɗin, ji ta yi kawai kuka ta zo mata babu zato babu tsammani kawai ta haura sama da gudu. Ɗauraye jikinta ta yi sannan ta ƙara saka wani polo shirt da kuma palazzo trousers, wani ƙaramin akwati mai kyau ta ɗauka tare da zuba kayanta aciki. Har ta gama loda kayan ta na ta hawayenta sai kuma ta koma a hankali ta zauna haɗe da fashewa da kuka ta na faɗin ''Ba abin ka je gida ba Ammi ta ce ba haka ba, ka kama hanya kaje gidan Neneh kuma gorin duniya ta haɗa ta yi maka shi.'' Goge hawayenta ta yi tare da ɗaukan wayarta ta na mai kiran Abbhi amma bai ɗaga ba. Cilli ta yi da wayar akan gadon bacci ɓarawo ya sace ta. Arround ƙarfe biyun rana Salimah ta shigo kawo mata lunch, ko kallonta ba ta yi ba ta shige toilet haɗe da yin alwala. Bayan ta gabatar da sallar ma kiran Abbhi ne ya shigo wayarta haka suka cigaba da hira har sai wajen uku sannan ta shige toilet ta yi wanka haɗe da alwala domin miƙa sallar Asr. Hakan nan ta tsinci kanta da yin shiru akan abin da Aliyu ya mata ya da safe. Bayan ƙarfe shida na yamma ta sauko cikin shigarta na boomb short da kuma wani polo da ta ɗan ɗage shi kunnen ta sanye da ear pods ta na jin waƙar _Ayra Starr_, kan ta ba ɗan kwali amma gashinta a tufke yake, sai wani lipstick mai kyau dake ƙyalli a leɓenta. Zaune yake akan kujerar parlourn ya na kallon tashar Spotlight ya na kallon wani wasan Madrid, sai tapping ya ke da hannu ya na faɗin ''Mbappe pass the ball.''duk da she's a fan of Madrid amma Allah, Allah take ƴan Liverpool su cinye wannan ball ɗin. Wani kalar dribbling M Salah ya kai wa Belingum da Mbappe ya yi wa passing ball ɗin wan da atake ƙwalon ya shige cikin ragar Madrid. Wani kalar tsaki Hydar ya ja ya na faɗin ''Ohh God, damn it, ci biyar at thesame time.'' dariyar da yake ji ana yi ne ƙasa- ƙasa ya sa shi juyawa ya na kallon side ɗin da yake jin dariyar na futowa, dan shi har ga Allah bai ga shigowarta ba. Haɗa idon da suka yi da shi ne ya sanya ta ƙwarewa ta fara tari sosai, nufuto ya fara yi hakan ya sa ta fara janye jikinta ta na matsawa baya. Daman tun da can a jogane yake zaune a falon tun cin farko da aka musu, Amir ya kira shi yake ta masa dariya. A zafafe ya ƙaraso wurin tare da faɗin ''You're laughing saboda an ci mu wasa right?." ''Noo wallahi am coughing ba dariya nake ba.'' ''Za ki gane kurenki ne yanzu.'' ''Dan Allah kayi haƙuri wallahi, fuskata kaɗan ya rage fatar wajen bai ɗaye ba dan zafi, please Yaya Alih.'' ''Stop calling me with that stupid name da kike ƙoƙarin kakaɓa min.'' Sosai Liyana ta tsorata da lamarin Hydar. Wani kalar ɓaci ransa ke ƙara yi, yadda take ba shi haƙuri at the same time take wani kalar murmushi, abin da ya tsani Sultana ta yi. Zuciya ce ta ɗibe shi hakan nan kawai ya zare belt ɗin jikinsa ya shiga lafta ma ta kamar an aiko shi. Dukanta kawai yake babu ji babu gani, Salimah da ta ji ihunta ta fito bawa Hydaar ɗin haƙuri, guda ɗaya da Ya shauɗa mata a baya ba ta san time ɗin da ta shige ɗakinta ba haɗe da saka key. Ga shi jikinta daman babu kayan arziƙi duk cinyarta sai da ya yi masa dukan lilis. ''Frog jump.'' ya faɗa a zafafe haɗe da cillar da belt ɗin hannunsa tare da shafa gemunsa. ''Ba ki ji abin da na faɗa bane!." Ya faɗa a tsawace. Ta na layi ta tashi haɗe da faɗin '' Ni ban san yadda ake frog jump ba.'' ta ƙarashe maganar tare da fashewa da kuka. ''Kin ga already Sallah ake kira, kafin na dawo daga masjid ki tabbatar kin fara frog jump ɗinnan, if not za ki ga the worst side of me.'' Ya ƙarashe maganar tare da yin ƙwafa ya wuce masallaci da kayan jikin nasa. Liyana cinyoyinta kawai take bi da kallo haɗe da yin da na sanin fitowar da ta yi, indai wannan ne aure wallahi da ba ta yi ba, sanin miji ko iftila'i'. Fashewa ta ƙarayi da kuka mai tsuma zuciya. Ƙarar buɗe ƙofar falon da ta ji ne ya sanyata tashi da sauri ta na sharɓar majina haɗe da yin frog jump ɗin. Shigowa ya ƙarasa yi cikin takunsa na ƙasaita haɗe da faɗin ''Make sure kin zagaye falon nan sau uku.'' A tunaninta ko wucewa sama zai yi sai ta ga ya ma jawo ragowan fresh milk ɗinsa ya na sha. Sai da ta zagaye falon sau biyu sannan ta ji ƙarar buɗe ƙofar ɗakin Salimah. ''Salimah ina za kije?." ''Yaya Hydar girki zan yi na ga dare ya fara yi.'' ''Je ki huta yau ita za ta yi girkin, You over there." Juyowa ta yi ta ƙafe shi da manyan idanunta. ''Ma za ki tashi ki shiga kitchen ki dafa min abatcha, Salimah akwai fresh cassava da na kawo yau a ina kika ajiye?." ''Store ɗin ajiye potatoes yaya.'' ''Mai kuma abatcha ɗin?." Ta faɗa ta na gwale idanunta. Bai ma bi ta kanta ba ya wuce ya fara tafiya towards kitchen ɗin. A hankali ta tashi dan ba ta son jikinta ya ƙara tsami hakan nan ta na ji ta na gani. A hankali ta shiga ɗingisawa tare da bin shi a baya har suka ƙaraso cikin kitchen ɗin. Bai zame ko ina ba sai store ɗin potatoes da doya, wasu manyan cassava's ya ɗebo guda uku tare da ajiye mata su akan kitchen island. ''Start.'' ''Wallahi ban san mai ne abatcha ba, please karka dake ni.'' ta faɗa haɗe da fashewa da kuka haɗe da matsar da kanta gefe ta na mai gaucewa marin da yake shirin kai mata. ''Shut up.'' shiru ta yi tare da faɗin ''Toh ya zan yi?." ''Ɓare rogon tukunna.'' A hankali ta shiga ɓarewa slight mistake idan ta yi kuwa sai ya ranƙwasheta ko ya ɓalle ta da harara. Wani bowl ne ya zame a hannunta, still ba ta damu ba ta cigaba da gurza cassava's ɗin. Ranƙwashi ya sakar mata hakan ya sa ta ce '' zan kwashe idan na gama.'' ''Who care's idan yaso ki fasa gaba ɗaya kayan kitchen ɗin in dai tiles ɗin ba zai samu karcewa ba am okay, c'mon do something fast.'' ''Yi nake faaa.'' ta faɗa hawaye na zubar ma ta, ta sa hannu ta goge. Haka ya yi ta monitoring ɗinta a kitchen ɗin har abatcha ɗin ya zama done, wani ɗan wood plate ta ɗauko ta zuba masa abatcha ɗin. Bayan ya ga ta juye acikin plate kamar yadda ya umarce ta, wucewa ya yi ya zauna akan kujerar dinning dake cikin kitchen. A hankali ta shiga jan ƙafar har ta tako zuwa wajen da yake, ajiye plate ɗin ta yi a hankali sannan ta fara ƙoƙarin barin wajen. ''Ina za kije?." ''Hutawa nake son yi kafin nayi sallah.'' ''A ina za ki huta ɗin?, not when I'm arround.'' ya yi maganar haɗe da kai spoon ɗin abincin bakinsa, da sauri ya furzar haɗe da faɗin ''haka nace kiyi?, ko kin haukace ne da za ki zabga uban gishiri acikin abinci haka?." ''I use the measurement da ka ba ni." Ta faɗa haɗe da ƙoƙarin buɗe baki za tayi kuka. ''Ko da wasa naji kin ɓare wannan bakin naki mai kama da na ɓeraye sai kin gane kurenki da daddaren nan.'' da sauri ta kame bakinta haɗe da gyaɗa kanta ta na ƙara waro idanunta akansa. ''Salimah!, Salimah." Ya na mai ƙwala ma Salimah kira, Salimah dake rakuɓe afalo tun ɗazu ta shigo haɗe da kallon Aliyun. ''Bayan waɗannan kayan kitchen ɗin da akwai wasu ne ko su kenan?." Salimah ba tayi tunanin komai ba ta ce ''Eh yaya akwai wasu a storage.'' ''kina wanke waɗan nan da waɗancan ne ko kuma ba kya wanke su?." ''way'anda ake amfani da su kullum, kullum ake wanke su, su kuma na cikin cabinet sai every month ending ake wanke wa, su kuma na store ɗin are still new.'' ''Okay nagane shiga ki kwaso min.'' har Salimah ta yi hanyar store ɗin da aka ajiye sauran kitchen utensils ɗin sannan Hydar ya ƙara faɗin ''Noo Salimah just leave it you can go, ba sai kin kwaso ba.'' ''Okay Sir.'' daga haka ta fice daga kitchen ɗin ta na tausayawa Aunty Liyana. (Liyana nima kin bani tausayi a swear 🤧😂🥹). Kallonsa kawai take babu ko ƙyaftawa, she can't believe this guy na juya ta fiye da yadda ya juya stearyn mota a rayuwarta. Muryarsa ce ta katse ta daga tunanin da ta tafi, ''Kina jira ne na kwaso miki kwanukan?." ''Mai zanyi da su toh?." ''A kaina za ki juye, je ki kwaso kwanukan ki wanke su yanzu ba sai gobe ba, sannan ba na son maimaita kaina, am I clear?." ''Yess.'' ta faɗa a raunane. ''Good.'' da ga haka ya fice daga kitchen ɗin domin ɗauko wayarsa da car key ɗinsa ya siyo fruits ya dawo. ''Mugu kawai azzalumi, kuma Allah sai ya saka min, darajar ka ɗaya wallahi ina sonka da gidan sai ya mana kaɗan wajen yaƙi.'' ta faɗa ta na sharɓe majinarta. Muryarta har ta fara dashewa, ta kusa mintuna goma ta na kwaso kayan amma still ba su ƙare ba. A lokacin har kusan ƙarfe goma na dare ta gota, wanke kwanukan ta fara yi amma tsantsi yake mata dan kusan plate uku sun fashe daga farawarta. Ganin ya yi kusan minti biyar da fita da motarsa ya sanya ta kwaso wasu daga cikin kwalayen warmers ɗin ta fara ƙoƙarin haurawa dasu saman ɗakinta. Ta na yi ta na waigen entrance ɗin falon a haka har ta kai kusan kwalaye shida dukkanninsu da warmers aciki. Ana bakwan ne taji shigowar motarsa cikin compound ɗin da gudu ta dawo domin komawa kitchen ɗin sai dai kashh ta na zuwa dai- dai tsakiyar falo, ya buɗe ƙofar ɗakin haɗe da ƙafeta da idanunsa masu rikitarwa..... *Durrah Hydar.*✍️ "Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need." Not edited 🤍🙏 *THE REGRET* (Dana sani). ~PENDING AMARYA CE~ *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* *THE NOBLE WRITER'S TEAM*💎 Pending Amarya 38 Ana bakwan ne taji shigowar motarsa cikin compound ɗin da gudu ta dawo domin komawa kitchen ɗin sai dai kashh ta na zuwa dai- dai tsakiyar falo, ya buɗe ƙofar ɗakin haɗe da ƙafeta da idanunsa masu rikitarwa..... ''What are you trying to do?." Ya tambaye ta da muryarsa mai amo. Cikin inda-inda ta fara magana ''Ai...... Ai....... Daman ba su kaɗai bane kayan kitchen ɗin nawa ba akwai wasu a ɗakina.'' ''Su kenan?." Ya ƙara jefo mata wani tambayar, ''Yee....yeeaah, i think gaba ɗaya na kwaso.'' ta ƙarasa maganar ta na sosa goshinta, da gumi ya ɗan ɓata, alamun dai rashin gaskiya. ''Kin gama wanke wanken?." Ya yi tambaye ta haɗe da matsowa sosai wajen da take, komawa baya ya yi kaɗan haɗe da kallon cikin idonsa ta ce ''A'a.'' Ƙarar saƙo ne ya shigo cikin wayarta dake yashe a ƙasar Turkish carpet ɗin falo, hakan yasa idanunsa sauka kan saƙon dake ɗauke da Instagram icon, da ya fito cikin jerin notifications. A hankali ya tako zuwa wurin da wayar take haɗe da ɗaukar wayar, wani kalar runtse idanunta ta yi haɗe da juyar da kanta gefe ta kalli ɗayan gefen, Allah Allah kawai take Allah ya sa ba Nifraz bane ba ya tura ma ta saƙon. ''Mufti menk has shared a reel.'' shi ne abin da ya gani rubuce akan fuskar wayar, cikin muryarsa mai daɗi ya ce ''Unlock the phone.'' ya yi maganar ya na mai ƙafeta da idanunsa. ''Buh that's my private life, mai za ka yi da wayata?." Ta faɗi maganar kamar za ta fashe da kuka. ''Don't let me repeat myself, I said unlock this phone!." Ya yi maganar a ɗan tsawace. Amsar wayar ta yi haɗe da buɗe masa wayar, daman kuma ba ta fita daga chat ɗinta da lily ba a IG ɗin, soo kawai scrolling ya yi tayi ya na komawa can bayan chats ɗin, yadda ka san ta fizge wayar daga hannunsa haka take ji, dan ko Ammi idan ta amshi wayarta ta na dubawa zuwa take ta haɗa ta da Abbhi ya ƙwato mata ballantana wannan hallittan. Cikin wata kaliyar shaƙaƙƙiyyar murya ya ce ''Get lost.'' ''To where?, ina zanje babu wayata, ko kai ka siya min, wadda aka samin ma alefe ba gane kanta nake ba, idan ma ka ɗauka ita ce just gimme my pho....'' ba ta ƙarashe maganar ba ya bata mari lafiyayye a fuska haɗe da nuna mata hanyar kitchen. Jiki a sanyaye ta bar wajen hawaye na zuba a fuskarta, bayan ta ƙarasa kitchen ɗin ma kuka kawai take haɗe da faɗin ''Ni anya wannan hanyar da Lily ta ce in bi ba barinsa zan yi ba, haka kawai a maida martani ayi ta saka jikina tsami, da yarinta na, za'a maida ni tsohuwa, ni dai Neneh sai da Allah ya ishe min.'' ta ƙarashe

Chapter 16 of 31