tare da kiran jinnuh kala kala sannan ya fara magana cikin wani kalar yare.
Bayan mintuna biyar ya fara warware ƙyallen dake jikin ƙwan, sannan ya rufe ramin da yake a buɗe, bayan ƙyallen ma da akwai wani baƙin zare da jan zare dake tattare da jikin ƙwan, duk sai da yabi ya warware tare da wanke ƙwan acikin wani ruwa saboda wasu rubutu da suke jiki, na kulle ruhin Liyanar wani Ya'r tsana ya ƙara zarowa daga bayan sa tare da fara ciccizge allurorin dake jikinta sannan ya zare pad lock ɗin da aka kulle ya'r tsanar da shi.
''Yawwa an gama abin da ya dace, amma wani hanzari ba gudu ba, idan fa kika kwanta da aljanu babu ke babu haihuwa.'' ya na faɗin haka ya ci gaba da iza wutan sa akan wani allon ƙarfe ya na ɗiga wasu turaruka, wanda ke nufin auran wasu yake shirin farraƙawa. (Allah ka mana tsari da tsarewarka 🥹😭💔).
" Malam ban gane babu haihuwa ga wanda ya kwanta da aljanu ba.?" Inji cewar Rufy ta na zaro idanunta.
''Eh mana ko kin taɓa ganin kin yi ɓari tun lokacin da kika zo ɗaukar fansar ɗiyar ki da aka kashe, kin san dai ba na son ja in ja, ku ɓace min a wuri ko na mayar muku da cututtukan da na ciro dan kutumar ubanku, in banda ƙarfin Kur'ani da kuma tausayin yarinyar nan wa ya ce muku zan sake ta haka kawai, yanzu ana can ana ƙona Aljani Gujungu, ma za ku tafi kar ɓacin rai ya shafe ku Dan uban Babanku, shegu dangin iblis.'' Malam Barbushe ya yi maganar ya na wani kalar fari da idanunsa.
Da sauri suka fita daga shagon Rufaidhat na zagin Mama Fatuh ta na faɗin ''Wallahi Fatuh nima kin san wacece ni tun lokacin da nake soyayya da Nabil, kin san banda hali, kuma a juri zuwa rafi watarana sai na fasa komai wallahi.'' Rufaidhat ta faɗa ta na dallawa Mama Fatuh harara haɗe da dungure ma ta kai.
''Wallahi Rufaidhat kema kin san duk kilakancin ki sai dai ki biyo Fatuh, babu record ɗinmu da ban da su, dan haka ki bi ni à hankali, ko an gaya miki ban san ke kika kashe iyayenki ba, ko an gaya miki ban san wace uwarki ba Asabe Karuwar ya'n garuwa.'' Mama Fatuhn ta faɗa tare da shigewa cikin motar ta ita ma.
Wani hawaye ne ya silale ma Rufy, sannan a hankali ta shige cikin motar ta ita ma ta bar wajen jiki a saɓule.
><><><><>><><><
Tun da aka fara karatun take jin wani kalar Abu na sakin jikinta ji take kamar inda ta maƙale an sakar ma ta ƙofa ta fice daga wajen.
Motsa hannunta ta yi kaɗan tare da ɗan damƙe hannunsa jin kamar ana zare wasu abubuwan da aka daɗe da ajiyar su ajikinta.
Jin kamar an damƙe hannunsa ya sanya shi ɗago kansa a firgice tare da amsar Alkur'anin hannun Ilham ya fara karanta Suratul Baƙara da daddaɗan muryarsa mai sanya zuciya sanyi.
Ya yi kusan minti talatin ya na karatun sannan yaji ta yi wani kalar attishawa tare da buɗe idanunta, a firgice ya ɗago kansa sannan kuma a hankali ya ci gaba da karatun hawaye na sauka daga idanunsa.
Hannunta ta sanya a hancinta tare da zaro duk wani auduga cikin hancinta, banda Aliyu dake ɗakin kowannensu a tsure yake barimma Neneh da take ƙoƙarin jike jikinta da fitsarin da ya taho ma ta .
Sai da tayi attishawa sau uku sannan ta fara miƙewa a hankali, tsabar murna Aliyu bai san lokacin da ya ajiye Alkur'anin hannunsa ba ya rungume Ilham da har ta kusa suma tsabar firgici ba.
Da sauri ya saki Ilham tare da rungume Liyanar da kanta ke wani kalar sara ma ta.
Ita ma ƙanƙame shi ta yi jikinta na wani kalar rawa, sannan a hankali ta ce ''Yaya mai yake faruwa?, Neneh yaushe kika z.......'' ai ba ta ƙarasa maganar ba Nenehn ta arce da wani gudu kamar ba tsohuwa ba, ita ma Ily ta mara ma ta baya.
Mutanen falon na zazzaune suna ɗan hawaye da jimami suka ga afkowar Neneh da Ilham cikin falon.
Tambayar su ake mai ya faru amma sam ko wannensu ya kasa faɗar komai, da wani kalar acceleration Mami da Reedah suka fito daga ɗakin.
Hakan ya sanya sauran mutanen falon tsorata, Ammi da Abbhi ne suka fito daga cikin ɗakin Liyana jin ana ihu a cikin falon.
Hydar ne riƙe da Liyana suka fito har cikin falon, jikin Ammi na ɓari ta nufo wajen da Liyanar da ke tsaye fuskarta ya yi wani kalar fayau.
''Iki nah ina za ki je?." Nabil ya yi maganar tare da janyota jikinsa.
''Yaya Liyana nake gani ga ta can, dan Allah ka bar ni na ji ɗimin ya'ta.''
Shi sai a lokacin ya lura da Liyanar dake tsaye jikin Hydar ta na bin mutanen falon da ido.
Jiddah da Abbhu da Abbahn Amir da shi Amir da Sultan ne suka shigo cikin gidan daga amso makara da kuma linkafani, jin ihu, hakan ya sanya su hanzartawa kar a zo matan ne ke kururuwa akan gawar Liyanar.
Da sassarfa suka shigo cikin falon a daidai lokacin da Mami ta taɓa kafaɗar Liyanar tare da rungumeta tsam ajikinta, cikin shashsheƙar kuka Mamin ta ce ''Welcome back to life daughter.''
Ita dai Liyana bin kowa take da kallo kamar wawiya, haɗa idanunta da Sultan da Amir shi ya ƙara razana gidan, dan sosai Sultan mugun matsoraci ne.
Dan bai san lokacin da ya ɗane Amir ba shi ma kuma Amir ya na neman ta yadda zai cillar da Sultan ya yi waje.......🤣🤣🤣😂😂😂
Mu haɗe on Monday
Manage please 💎🥀
Mutuwa kan kawo canji⏩⏮️🤝
''Ya Ubangijina ka basu daman share."
Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟
Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 🤧🥱😂😂💔
*THE REGRET*
PENDING AMARYA CE ✍️
JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
The Noble Writers Team.
**Pending Amarya 53.**
What goes around comes around ⏩ ⏮️ ⏩
Every ending is a new beginning 💎🥀 even if the heart disagrees.✅🌕🤝🦋
🤍 🫧 🤧
Not edited 🌟💔🥹
****
Da sassarfa suka shigo cikin falon a daidai lokacin da Mami ta taɓa kafaɗar Liyanar tare da rungumeta tsam ajikinta, cikin shashsheƙar kuka Mamin ta ce ''Welcome back to life daughter.''
Ita dai Liyana bin kowa take da kallo kamar wawiya, haɗa idanunta da Sultan da Amir shi ya ƙara razana gidan, dan sosai Sultan mugun matsoraci ne.
Dan bai san lokacin da ya ɗane Amir ba shi ma kuma Amir ya na neman ta yadda zai cillar da Sultan ya yi waje.......🤣🤣🤣😂😂😂
Ita kanta Liyanar tsoron kanta take, a hankali Jiddah ya ƙaraso wajen da take tare da faɗin ''Ya Zahra, kina raye, Alhamdulillah.'' sannan ya kamo hannunta daga cikin na Mamin ya zaunar da ita a kan cushion ɗin dake falon.
Har su Sultan na niyyar ficewa daga cikin falon Jiddah ya ce da su su dawo.
Duk sanyin Acn falon sai da gumi ya keto ma Sultan da Amir, sannan suka zauna a hankali nesa da Liyanar da kuma shi kansa Hydar ɗin.
Neneh kam sam ta kasa zaune ta kasa tsaye kawai jira take taji tak ta fara ta kanta.
Ily da Reedah da sauran ya'mmatan na zazzaune amma ba kusa da su Jiddahn ba, a hankali Jiddah ya fara magana tare da faɗin ''Ba abin gudu bane dan min kalleta ta tashi, ina ilmin ku yake?, da za kuyi ta yin ihu a cikin dare kamar wasu ya'n karkara, wannan sam ba dacewa ba ce, ai abin farinciki ne ace wadda muke kukan kewarta ta dawo cikin ƙoshin lafiya, kuma duk wanda ya yiwa Zahra Mummunan abu zai koma kansa da yardar Allah, kowa ya nemi waje ya kwanta.'' Jiddahn ya idasa maganar tare da ɗaukan walking stick ɗinsa.
''Ni dai a wurin mu da safe ake wannan, wa zai nemi wuri ya kwanta a gidan nan, salon na ga wannan al'amarin a kaina ta na ƙoƙarin ja na mu tafi, nifa daman ta sha faɗa min ko ta mutu sai ta dawo ta ɗaukeni mun tafi tare, TOH maganar gaskiya ba da ni za'a yi kwanan gidan nan ba Rafiƙ, yawwa.'' Neneh ta ƙarashe maganar ta na satan kallon Liyana da ta ma ta ƙuriii da ido.
''Ajiddeh ba na magana biyu maza ku nemi waje ku kwanta wa'yanda zasu koma gidajensu kuma suyi saurin tafiya kafin ƙarfe 12 ta yi.'' daga haka ya wuce stairs.
Hydar ne ya ƙaraso wajen da Liyanar take tare da miƙa ma ta hannu, ganin yadda mutanen wajen ke ɗan tsoranta sai shi kaɗai da Maminsa hakan ya sanyata miƙa ma sa hannunta tare da manne ma sa ajiki.
Har wajen Ammi ya ƙarasa da ita, wanda a take Ammin ta rungumeta ta na wani kalar kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.
Da ƙyar ta saketa, ita dai Liyana sai ganin yadda Hydar ke fasin fasina da ita kawai yake, har wajen su Abbuh da Abbha duk sai da taje sannan suka nufo wajen Neneh, wanda in less than two seconds ta fara ƙoƙarin hayewa sama.
Reedah kam a daren nan sai da ta saki reel a Instagram da Video ɗin Liya da Hydar ɗin ta rubuta ''Alhamdulillah, she's still alive.''
Daman mutane jiran updates suke, haka Fans ɗin Liya da na Reedahn sukai ta hamdala, kowa na farincikin ganin Liyanar na hugging mutane.
After 2 days.
Da sassafe Hydar ya tashi dake a gidansu ya kwana Amir dake nace ma ɗakinsa idan zai kwana a gidansu yau kam a ɗakin Sultan ya kwana.
Duk wannan badaƙalar da aka yi sai jiya Assultanah ta ga news ɗin mutuwar Liyana na yawo a social media ba ta wani jira ba ta kama hanyar jirgi ta dawo gida ta na wani kalan kuka, ita ma Lily sai a lokacin ta ga news ɗin a Instagram wanda hankali a tashe ta tashi ta yi hanyar gidan Nenehn tun da compound ɗin ake nunawa a cikin video ɗin.
Salimah kam tun ranar da Hydar ya zo gidan gaba ɗaya ta rasa yadda za ta yi da rayuwarta, dan ta ji cewa Liyanar babu lafiya, sai ita ma a ɗazun ta ga cewa news na yawo ya'r Nabil is dead, hakan ya sanyata kulle ƙofar gidan ta nufo hanyar zuwa gidan Nenehn.
Kusa da Ammi Liya ta kwana ta na baccin ne kawai amma sam ba ta jin daɗinsa dan jinta take kamar a wajen da ta yi kusan sati a takure, dan sai anyi sadakan uku yadda Jiddah ya faɗa sannan kowa zai koma gidansa, tun da Liyanar ma lafiyarta ƙalau.
Bayan Ammi ta tasheta da Asuba sallarta ta yi tare da ƙoƙarin komawa bacci wanda sam Ammi ta haneta akan sai ta tsaya ta godema Allah da ya bata dama na biyu a rayuwa ta cike taskes ɗinta .
Da ƙyar ta yi addu'an sannan ta koma ta kwanta wanda sai a lokacin cikinta ya ɗan ɗago wanda da alamu dai yanzu ya ta so daga kwancen da aka sanya shi yin.
Sai a lokacin idanun Ammi ya sauka akan cikin dake jikinta sannan a hankali Ammin ta ce ''Kina zuwa awo or you're taking it un serious just like your life.'' Ammin ta ƙarashe maganar tare da ɗan taɓa cikin Liyanar.
Marairaice face ɗinta ta yi tare da faɗin ''Ammi please later bacci nake ji.'' ta ƙarashe maganar tare da ƙoƙarin kwantawa.
''za ki tashi ko sai kin gane rashin lafiyar da kika yi nafila ne.?" Ammi n ta faɗa rai a ɗan ɓace.
Fashewa ta yi da kuka tare da ɗan dire ƙafarta sannan ta ce ''Ammi please nah, ɗan ya na lafiya ko yanzu sai da ya buge ni manaa.'' ta yi maganar tare da share ƙwallarta.
''Alright magana ta ce ba za ki ji ba kenan har yau, tashi ki fice min daga ɗaki kafin na ɓata miki rai.''
Ammin ta yi magana cikin fushi.
''Ammi atleast ki tausaya min mana, yaushe nayi rashin lafiya na tashi, ko 48 hours ba'a yi ba amma gashi ana ƙoƙarin haɗa min wani.'' Liyana ta yi maganar haɗe da ɗan turo bakinta.
Yunƙurawa Ammin ta yi kamar za ta tashi dan ta ga sturbborness ɗinta ƙaruwa yake ba raguwa ba, hakan ya sanyata saurin ficewa daga cikin ɗakin dan sam ba ta jin wani alamun rashin lafiya a tattare da ita.
Bigewa ta yi da mutum a hanyar ta na ficewa daga corridor ɗin guest room ɗin sannan a hankali ta ja baya ta na ƙoƙarin komawa ɗakin Ammin.
Saurin jawota ya yi jikinsa tare da buɗe ƙofar da yake tunanin empty room ne ya yi saurin kulle ƙofar tare da jinginata da bayan ƙofar.
Ɓare baki ta yi kamar za ta yi ihu hakan ya sanya shi haɗe bakinsa da na ta ya fara sumbatar ta, zaro idanunta ta yi dan ganin Abbhinta ya fito daga toilet hannunsa riƙe da wani towel ya na goge jikinsa da shi.
Ƙara waro idanunta ta yi sanadiyar haɗa idanunta da ta yi eye ball to eye ball da Abbhinta da ya yi saurin juyawa ya koma toilet ɗin ɗakin.
Da dukkanin ƙarfinta ta haɗa tare da turesa, ƙara jawota ya yi jikinsa da sassarfa ya na mai rungumeta tsam jikinsa, buh he can't feel that comfort of hug, saboda tumbin da ya ɗan tokaresa.
Saurin waro idanunsa ya yi tare da yi ma ta pointing cikinta da ya turo gaba sosai.
Ita dai ba ta biye ma sa ba ta sanya kanta ta fice daga cikin ɗakin, dan har ga Allah ba ta son Abbhin ya ƙara tadda ta a wajensa.
Ya yi kusan minti biyar a wajen da ta bar shi sannan ya saki wani kalar murmushi wanda ya tsaya ma sa iya laɓɓansa tare da shafa gemunsa zuwa bayan wuyansa sannan ya bar cikin ɗakin shima.
Dan shi kansa bai san mai ya kawo shi gidan ba, he just feel like ba zai samu nutsuwa ba har sai ya ganta, ya ji ɗuminta.
Fitowarsa daga ɗakin ke da wuya ya kusa cin karo da Neneh da ke cikin shigarta na Lifaya , sai da ta firgita ganin Hydar ɗin a gabanta, sannan a hankali ta dalla ma sa harara ta bi ta gefensa ta shige backyard zuwa traditional kitchen saboda ganin abin da mutanen gidan ke dafawa na sadaka.
Shima Hydar wani kalar harara ya banka ma ta tare da raɓewa ya bi ta kusa da ita ya fice daga cikin gidan, dan shi ya na mugun son ya ga ana jin tsoro a rayuwar sa.
Ko da ya isa gidan Mamin ko ina na gidan tsit, suma ya'n aiki na can backyard ana ta dafa abincin sadaka, ya na zaune a falo ya ji ana wani kalar ƙwanƙwasa ƙofa kamar za'a ɓalla sa, sannan daga bisani ya fara jin muryar Assultanah dake time ɗin har 10 O'clock na safiya ta yi.
Kuka take mai tsuma zuciya ta nufo falon, ganin Hydar a falon, shi ya sanya ta ƙara sakin wani kuka tare da faɗawa jikinsa ta na sakin wani kalar kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, sannan a hankali ta fara magana ''Yaya mai sa a ka binne ta ba tare da an jira ni ba.'' ta ƙarashe maganar cikin shashsheƙar kuka.
Sai da Hydar ya ɗan kalleta sannan ya ɗauke kansa tare da cire kanta daga jikinsa sannan a hankali ya ce ''Gidansu za ki je, sai ki shigar da ƙara.'' daga haka ya ɗauki wani Apple da ke cikin wani fancy basket dake kan center table ya nufi part ɗinsa dake nan tsaf.
Tashi ta yi ta nufi hanyar gidan Nenehn, duk ya'mmatan na zazzaune suna hira har da Liya da suka sa ki jikinsu da ita ana ta hira har Yusrah dake ta shishige musu.
Ko sallama ba ta yi ba ta shigo cikin falon ta na wani kalar kuka, ganin Liyana zaune ta na dariya hannunta riƙe da wasu guava da Hydar ya sa aka kawo ma ta ɗazun ne ya sanyata suman tsaye tare da kallon mutanen falon.
Wani kalar ihu ta saki wanda hakan ya ƙara janyo attention ɗinsu gabaɗaya tare da ƙafe Sultana da idanu.
Ta mugun tsorata da ganin Liyanar a cikin gidan, dan sai da tayi suman tsaye na ya'n daƙiƙu sannan ta dawo hayyacinta.
A na tsaka da shawo kan lamarin Assultanah Lily ta danno kai cikin gidan, a kiɗime ta fara addu'ar ta cikin Greek Words dan a tunaninta Ghost ce, sannan a hankali a ka fahimtar da su.
Har a ka yi sadakan uku da Jiddahn ya faɗa ko ƙeyar Rufaidhat ba'a gani ba a cikin gidan, wanda Abbhin ke sane da ita da hakan da ta yi, ita ma Mama Fatuh tun bayan zuwan su Sultanah da ta zo suka tafi da Yusrah a ranar suka wuce Niger.
Aranar sadakan ukun kan duk yadda aka yi da Neneh akan Liya ta yi bakwai a gidanta ƙi ta yi ta na faɗin cewa ''Kyan ya' mace gidan mijinta.'' a haka aka bar zancen Liyanar ta koma gidan Hydar ɗin da har ya dawo da workers ɗin gidan.
Bayan one week ta koma school dake duk ya'n school ɗin sun san da tashin na ta hakan ya sanya ta ci gaba da harkar gabanta kamar yadda ta saba.
HYDAR kam har wani kalar tsoron kusantarta yake kar ya zamana cewa sihirin dake tattare da kwanciyar ta su ba ta karye ba.
Ammi kullum cikin addu'a take inda soyyayar ta da Abbhi sai daɗa linƙaya take, amma dake ance zaman aure sai haƙuri ba za'a rasa abin da ke damun zuƙatan masoyan guda biyu ba.
Ɓangaren Neneh kuwa har yau cikin shige da fice take dan wajen gano waya'nda suka aikata wannan lamarin ga jikarta, duk inda taje siffofin mutane biyu kawai ake ba ta amma ta kasa gane su waye su.
Zaune take cikin shigarta na wani simple abaya mara nauyi, sai laɓɓanta dake sanye da wani lipstick mai ƙyallin gaske, kanta sanye yake da hula, hannunta riƙe da wani bowl mai ɗan girma da yake cike da kayan cikin naman saa da ya ci uwar garlic.
Ta na ci ta na kallo a TV ɗin falon dan yanzu sam wayar hannunta ba ya damunta tun da cikinta ya kai 5 months and 2 weeks, har yanzu da ta kusa sati biyu da dawowa gidan bai cika wani kulata ba illa ya tambayeta mai za ta ci a siyo ma ta ko a dafa mata.
Sanye yake cikin wani combat black color sai wani white designer plane shirt da ya ɗan kama jikinsa, fuskarsa idan banda ƙyalli babu abin da yake fitarwa banda zallar rich glowing skin.
Ƙarasa sukowa ya yi daga stairs ɗin tare da samun waje ya zauna kusa da ita, sidda kanta ta yi ƙasa dan wani kalar nauyinsa take, ga soyyayarsa dake mamayar zuciyarta.
Waro idanunsa ya yi ganin ƙaton plastic bowl ɗin dake hannunta cike da kayan cikin da sai a iya amfani da su na kwana uku zuwa huɗu.
Amsar bowl ɗin ya yi daga hannunta tare da tallaɓo kanta ya ɗaura akan kafaɗarsa, sannan a hankali ya fara faɗin ''I know it will be a little bit difficult for us to live like a couple, duba da yadda haɗuwar mu ta faro da kuma yadda muka yi treating junan mu a gidan nan, Liyana!." Ya ƙarashe maganar ya na mai kiran sunanta tare da yin yawo da hannunsa akan gashinta.
Cikin sassanyar muryarta mai daɗin sauraro ta ce ''Na'am Yaa Alih.'' ta ƙarashe maganar ta na wasa da hannun abayarta.
Sai da ya ɗan jinginar da kansa tare da shafa fuskarsa izuwa gemunsa sannan ya ce ''Ba zan iya cewa i can't accept you a matsayin matata ba, duba da yadda kike ɗauke da cikin da nayi sanadinsa, and ni ba zan ba ki haƙuri a kan wani laifin da yake a matsayin gyara na yi ba, soo can we friends, friends with benefits........
Jiya banda data Wallahi kuyi haƙuri 🥹😂
Manage please 💎🥀
Mutuwa kan kawo canji⏩⏮️🤝
''Ya Ubangijina ka basu daman share."
Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟
Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 🤧🥱😂😂💔
*THE REGRET*
PENDING AMARYA CE ✍️
JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
The Noble Writers Team.
**Pending Amarya 54.**
What goes around comes around ⏩ ⏮️ ⏩
Every ending is a new beginning 💎🥀 even if the heart disagrees.✅🌕🤝🦋
🤍 🫧 🤧
Not edited 🌟💔🥹
****
Sai da ya ɗan jinginar da kansa tare da shafa fuskarsa izuwa gemunsa sannan ya ce ''Ba zan iya cewa i can't accept you a matsayin matata ba, duba da yadda kike ɗauke da cikin da nayi sanadinsa, and ni ba zan ba ki haƙuri a kan wani laifin da yake a matsayin gyara na yi ba, soo can we friends, friends with benefits.'' ya ƙarashe maganar tare da ɗage girarsa guda ɗaya yana mai miƙa ma ta hannunsa alamun shaking.
Sidda kanta ta yi daga kallonsa sannan a hankali ta ɗago manyan idanuwanta tare da faɗin ''Babu duka babu zagi, only friends, and banda ranƙwashi.?" Ta ƙarashe maganar a ɗan shagwaɓe.
Matsowa ya ƙara yi sosai kusa da ita lips ɗinsa ya na brushing na ta, idanunsa a cikin na ta in a whispering voice ya ce ''Yeah of course, amma in one condition.'' ya ƙarashe maganar ya na bata wani light kiss a lips, sannan ya ɗora da faɗin ''Duk abin da na ce kiyi za ki yi shi, and when I want something, dolen ki ki bani, are we good to go.?" Ya yi maganar ya na ƙara matsowa kusa da ita.
Gyaɗa kanta ta yi sosai kafin ta yi maganar da take da niyyar yi ya haɗe lips nasu trying to get what he wants from her, sannan ya sunkucheta ya nufi ɗakinsa da ita, they made love.
Ita ta san ta na son Hydar, soyayyar da ko kwatan shi ba ta nunawa ƙaninsa ba, babu abin da zai ma ta a duniya da za ta ji tsanar sa a duniya.
Da ƙyar ta tashi ta mayar da kayanta haɗe da ƙoƙarin barin dakin na sa amma ya hanata.
Kwance suke waje ɗaya kanta na kan kafaɗarsa jikinta gabaɗaya na mata wani kalar laushi, hannunsa ɗaya na shafa yalwataccen gashin kanta, cikin wani kalar murya mai sanyi wanda ke ƙara jafa ta a cikin wani yanayi ya fara magana ''Ina kike son muje honey moon?." Ta tsinci muryarsa a cikin kunnenta.
Gyara kwanciyarta ta yi a jikin na sa tare da ɗan ɗago kanta ta na mai duban kyakkyawar fuskarsa, sannan a hankali ta ce '' Just suggest, abin da kake so nake so ni ai.'' ta yi maganar ta na wasa da kwantaccen gashin dake ƙirjinsa.
Sosai ya ji daɗin kalmar ta sannan a hankali ya ce ''From Saudi Arabia, sai mu wuce China and Switzerland are you okay with that.?"
Gyaɗa kanta kawai ta yi sannan ya ƙara gyara ma ta kwanciyya a jikinsa bacci mai daɗi ya yi awon gaba da su.
Da sassafe ta tashi ta nufi ɗakinta ganin ba ya cikin ɗakin kuma bai tashe ta ba, bayan ta idar da sallarta ma tilawarta ta cigaba haɗe da yin azkar sannan ta fito kitchen ta kamawa Salimah girki.
Cous cous ne sai pepe soup tare da bread suka dafa, sai coffee da ta haɗa ma sa a coffee mixer ta ajiye a kan kitchen island ɗin.
Within 2 mins ya shigo cikin gym wears ɗinsa hannunsa riƙe da bottle water da kuma hanky.
Already daman bayan ta gama girkin ɗakinta ta shige tare da yin wanka ta shirya cikin wide leg trousers ɗinta (palazzo) sannan ta ɗora da wani babban T shirt Wanda zai sa ka cikin jikinta balance sosai, sannan ta ɗora simple hula a kanta tare da saka slippers ɗinta ta fito falon.
Ta na zaune ya shigo cikin falon, murmushi ya sakar mata mai kyau sannan ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun dake falon.
''Girlfriend, you look beautiful today, irin wannan kyau haka kamar Zebra.''
Ya yi maganar tare da amsan coffee ɗin da Salimah take miƙo ma sa.
She just smiled at him, sannan ta ce ''Yaya ina kwana.'' ''Lafiya lau, ki shirya yau zamu fita siyayya.'' ya na faɗin hakan ya haura sama domin shiryawa.
Tun da ya shige ɗakinsa ta na cikin falon babu inda ta motsa sai ma Tvn da ta ƙurawa ido.
Sanye yake cikin wani plane designer t shirt black color, sai wani _Saint Laurent_ jeans black color, ƙafafunsa sanye cikin wasu Fendi slippers, sai car
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 31