Da ga haka ya kashe wayar na sa.......
After 2 weeks.
Sosai ta maida hankalinta kan lafiyar Mamin, dan yanzu kam baccin da take yawan yi ya ɗan sake ta, ta na ɗawainiyya da ita sosai.
Yau ɗin ma kamar kullum ta shirya cikin wani dark purple color hijab, sannan ta ɗaura da wani farin classic booth white color, sai kuma wani white designer bag na companyn dior.
Wayarta na hannunta ta fito tare da zama akan kujerar dinning ɗin ta na mai ɗaga tafasasshen madarar da ta saka Salimah ta dafa ma ta haɗe da kaninfari.
Ta ji daɗinsa sosai hakan ya sanyata shan kusan rabin mug ɗin, sannan ta fice daga gidan.
Sai da ta biya gidan Mami ta ga lafiyar jikinta wanda Alhamdulillah ta samu sauƙi sosai, sannan ta wuce school.
Bayan an gama lectures ɗin ma Lily ce ta nemi rakiyar ta hakan ya sanyata tashi haɗe da bin bayanta suka bar school ɗin acikin motar Lilyn.
Basu zarce ko ina ba sai gidan Lilyn, ba ta iya cin komai ba in banda wani milk shake da ta gani akan bedsides kawai ta ɗauka ta sha tare da ɗan kishigiɗa.
''Ahhh, i just dey wonder your situation OOO, anya ba ciki ne dake ba?." Lilyn ta faɗa tare da kanne ma ta ido ɗaya.
A zabure ta miƙe sannan kuma ta koma ta zauna tare da faɗin ''Ke kika yi min?, ni mai nayi ma da zan yi ciki.'' Liyanar ta faɗa a rarrabe.
Wani kalar dariya Lily ta yi tare da faɗin ''Wallahi you're very funny, ko da ace Hydar dutse ne , ba zai taɓa escaping hanyar da na sa ki ba.'' ta yi maganar tare da ɗaukan wani magani ta na mai watsawa a bakinta.
Wani tsaki Liya ta ja tare da faɗin ''Your hanya wey lead me to hell, ni na ƙara ɗaukar shawararki over my dead body.'' ta ƙarashe maganar tare da kunna datar ta.
''Jezz!, gist me wetin happen babe.?'' Lily ta faɗa tare da matsowa kusa da Liyanar.
A taƙaice ta faɗa ma ta duk abin da Hydar ɗin ya mata har da wani ɗan kukanta ta ce ''Lily if you see the kind wahala wey that guy give me, ba za ki so na zauna a gidan ba wallahi.''
Wani kalar ajiyar zuciya Lily ta sauke tare da faɗin ''Then leave, kar ki saka kanki cikin rayuwar da ba za ki iya ba.'' Lilyn ta ƙarashe maganar tare da shafa bayanta.
''Lily i can't leave him, kin san ina son shi, na tsani kaina idan na tuno rashin mutumcin da na yi masa, Lily I'm dying wallahi, idan da gaske ne ina da ciki, da sai na fi ko wace ya' mace sa'a a duniya.'' ta ƙarashe maganar tare da ɗaukan wayarta da jakarta ta na mai miƙewa.
''Where are you heading to.?" Lilyn ta faɗa tare da ta shi tsayen ita ma.
'' To the hospital.'' ta faɗa tare da zira slippers ɗinta.
''Let's confirm it first before taking any action babe, ƙila period ɗinki ne ya zo da hakan.''
''Noo Lily na fi tunanin cewa cikin ne, dan yau wata ɗaya da sati uku da ban ga period ɗina ba kenan.''
Ajiyar zuciya Lilyn ta sauke tare da nufar kan standing mirror ta ɗauki mukullin motar ta suka fi ce daga cikin gidan.
After 5 hours 🦚🌟
Ko da aka yi test ɗin kuwa result ɗin ya fito da cewa ta na ɗauke da cikin wata ɗaya da sati uku da kwanaki biyar, wanda hakan ya ɗirar ma ta da farinciki da kuma aka sin sa, duba da yadda course ɗin da take karantawa ya shaida ma ta da zafin haihuwa.
Daga hospital ɗin ma makarantar ta koma tare da ɗaukan motarta ta koma gidanta.
><><><><><>><>>><><
Zaune yake a makeken falonsa, hannunsa riƙe da wani book mac ya na duba kayan da suke out of stock domin a fara ƙera sabbi, da ma wasu colors ɗin.
Wayarsa dake gefensa ne ya yi ringing hakan ya sanya shi kai duba wajen da wayar ta sa ke ringing ɗin.
Sunan Abbhu ya gani akan screen ɗin wayar hakan ya sanya shi ɗaukan wayar tare da karawa a kunnensa.
''Assalamu alaikum Abbhu, ina wuni.'' Hydar ɗin ya faɗa ya na jiran amsar da Abbhun zai ba sa.
''Wassalamu alaykum, Son ya aikin.?"
''Alhamdulillah, Abbhu.''
''Daman na kira ne na sanar da kai ba kai kaɗai bane ba yanzun, you should come back home saboda matarka, ka ji ni.?" Abbhun ya faɗa ya na mai jiran amsar da ɗansa zai ba sa.
Wani ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin ''Eh Abbhu daman am planning na dawo next month in shaa Allah, ya jikin Mami.?"
''Okay, Allah ya maka albarka, jiki da sauƙi matarka na kula da ita sosai yadda ya dace, ta samu ƙarfin jiki, dan karaya ce ta samu a wajen ankles ɗinta.''
''Mami really try gaskiya, Allah ya bamu lafiya ba ki ɗaya.''
''Amin son.'' daga haka suka yi sallama.
><>><><>><><>><>><>
Gidan Ammi kam soyayya tsakaninta da Abbhi ba'a magana kafin ta faɗi abu har an yi ma ta shi, Rufaidhat yanzu babu dare babu rana kullum ta na yawon neman maganin infection wanda zai yi curing ɗinta.
Ko ta kan girls ɗinta ba ta bi, dan so take ta samu ta tara dukiya ita ma a gidan.
Zaune suke suna yin break fast a katafaran dinning table ɗin na su, Ammi na sanye cikin wani kalar abaya mai tsadar gaske, Abbhi na kusa da ita cikin wasu ƙananan kaya farare da suka yi ma sa kyau sosai, ya na shan wani fruit salad da Ammin ta haɗa ma sa.
Cikin muryarta mai sanyi ta ce ''Yaya yaushe ne family meeting ɗin.?" Ta tambaye sa tare da k'afesa da idanun, ɗago kansa ya yi a hankali, hakan ya basu daman haɗa ido da Abbhin, kanne ma ta ido ɗaya ya yi tare da faɗin ''I think is today, why are you asking.?"
Sauke kanta ta yi dan har yau ta na mugun jin nauyin sa.
Murmushinsa ya yi mai kyau tare da faɗin ''Ki daina jin wannan kunyar Iki, shekaru kusan 27 da kasancewar mu tare ba fa wasa bane, atleast said it out ki na son ganin Liyana, amma wannan noƙe - noƙen ki daina shi." Ya yi maganar ya na mai ƙafeta da idanunsa.
Gyaɗa kanta kawai ta yi tare da cigaba da shan water melon juice ɗinta.
Tsaki da suka ji a wajen ne ya basu damar juyawa suna mai kallon Rufyn da take ta doka wata uwar tsaki.
''Hajiyata ke ba za ki shirya ba ne, ko mu tafi ne.?" Abbhin ya faɗa ya na mai kallon Rufaidhat.
''Wllahi Nabil ka na ba ni mamaki, wannan abin da kake ka na nuna min banbanci, wanda hakan sam bai dace da kalar rayuwar da muka tsara ba kafin ya'r ƙunar baƙin waken nan ta raba.'' Rufaidhat ta faɗa ta na mai kauda kanta gefe daga kallonsu.
''Kar ya dace ɗin mana, damanta ne ki barta ta dama, kema da daman ki ya zo kin fi kowa zaƙewa ai.''
Abbhin ya faɗa tare da miƙewa dan a rayuwarsa ya na mugun son ya ga ya haɗa faɗa.
''Haka ka ce.?" Rufy ta faɗa tare da ƙafesa da manyan idanunta.
''Tsoronki nake ji ai, Mamma ta so mu tafi, ke kuma Ikimat zauna ta fasa miki kai kin ji.''
Daga haka ya sanya kansa haɗe da fita daga cikin falon.
''Shegiyya karuwa, wadda ba ta zo da budurcinta gidan mijinta ba, mai halin akuyoyi.'' in ji cewar Rufaidhat da ta tashi ta yi hanyar fita daga falon.
''Ammi idan ba ranar da na ci uban matar nan ba, ba za ta saurara da kiran wannan sunayen ba.'' Ily ta faɗa zuciyarta na ƙuna.
A zuciye Ilyn ta bi bayan Rufaidhat da ta nufi hanyar fita a falon domin zuwa wajen Abbhi, ita ma Ammi da saurinta ta biyo ta ganin kamar yarinyar ta fita a hayyacinta.
Cimma Rufaidhat ɗin ta yi tare da wani kalar hankaɗeta, Rufaidhat har ta sadaƙar za ta faɗi Abbhi ya yi saurin riƙe hannunta dan kaɗan ya rage maƙogwaronta ya caki wani ƙarfe da shi ya raba parking space da garden ɗin gidan.
Tare da janyota jikinsa, ''Mammah mai ya faru haka?, da za ki kasheta.'' ya yi maganar ya na tsare Ily da idanunsa, ''Abbhi just let me, ka barni na koya ma ta hankali.'' ta faɗa idanunta na zubar da ƙwalla.
''Shut up, shiga cikin mota, matar ta wa za ki koyawa hankali, kamar wa ta sa'ar ki?, get in.''
Fashewa ta yi da kuka tare da shigewa bayan motar, ita ma Rufaidhat bayan ta shiga, sannan Ammi da fitowarta kenan ta shige gaba.
><><>><><>><><>>><>><>><>><>
Bayan ta tashi daga baccinta sallah ta yi tare da yin miraja'a haɗe da azkar da ta sabawa kanta da su ayanzu, sannan ta wuce kitchen suka fara haɗa breakfast ɗin da zasu sama cikin su.
Bayan sun gama karyawan ɗakinsa ta shiga, tare da goge shi tass haɗe da sanya turaruka masu ƙamshin gaske, ɗakinta ta koma tare da shiryawa cikin wani abaya mai kyaun gaske, tare da sanya wani face mask haɗe da saka eye glasses ɗinta, safar hannu ta saka wanda hakan ya sanya cikar kamalarta fitowa.
Wayarta ta ɗauka tare da saka shi a cikin jakarta na companyn channel, tare da ɗaukar key ɗinsa ta nufi hanyar falon cikin gidan.
Ita ma Salimah a shirye take cikin abaya, daga falon kuwa compound suka wuce tare da ɗaukan motarta suka wuce gidan Nenehn.
Horn suka danna wanda atake mai gadi ya buɗe musu gate ɗin tare da shigar da motar nasu, compound ɗin dake cike da motoci na alfarma.
Wani kalar farinciki ne ya ziyarceta ganin motar Abbhinta a compound ɗin, dan ta san duk inda ƙarfe takwas yake a gidan yake musu idan za'a yi taron family.
Har kusan tuntuɓe ta yi tsabar farinciki, da ɗan gudunta ta iso cikin falon tare da faɗawa ajikin Ammi dake zaune cikin cousins ɗinta da suke sa'anni.
Gidan acike ya ke da jama'a, su Rashanda ne da su Unaisah da Classy Reeda suka fito da ɗan gudunsu jin muryar Liyanar a falon.
Umma Mansura ce ta fito hannunta riƙe da wani bowl dake cike da sararran rake ta fito daga cikin kitchen ɗin falon jikinta sanye da wani less mai kyau da tsada.
Da ɗan sauri ta saki Ammi tare da faɗawa jikin Umma Mansurar da saura kaɗan raken dake hannunta su ɓare.
Abbhi dake zaune ya na kallon ikon Allah ne ya ce ''Yau Daughter ni aka manta kenan.?"
Tsintar muryar Abbhi da ta yi ne ya sanyata saurin sakin Umma haɗe da rungume Abbhin, ta na mai ƙyalƙyala dariya.......
''Ya Ubangijina ka basu daman share."
Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟
Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 🤧🥱😂😂💔
*THE REGRET*
PENDING AMARYA CE ✍️
JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
The Noble Writers Team.
**Pending Amarya 48**
What goes around comes around ⏩ ⏮️ ⏩
Try to be a good father to your children not a cowed 🤍 🫧 🤧
Not edited 🌟💔🥹
****
Umma Mansura ce ta fito hannunta riƙe da wani bowl dake cike da sararran rake ta fito daga cikin kitchen ɗin falon jikinta sanye da wani less mai kyau da tsada.
Da ɗan sauri ta saki Ammi tare da faɗawa jikin Umma Mansurar da saura kaɗan raken dake hannunta su ɓare.
Abbhi dake zaune ya na kallon ikon Allah ne ya ce ''Yau Daughter ni aka manta kenan.?"
Tsintar muryar Abbhi da ta yi ne ya sanyata saurin sakin Umma haɗe da rungume Abbhin, ta na mai ƙyalƙyala dariya.......
Da ɗan sauri ta saki Ammin tare da faɗawa jikin Umma Mansurar da saura kaɗan raken dake hannunta su ɓare.
Abbhi dake zaune ya na kallon ikon Allah ne ya ce ''Yau Daughter ni aka manta kenan.?"
Tsintar muryar Abbhi da ta yi ne ya sanyata saurin sakin Umma haɗe da rungume Abbhin, ta na mai ƙyalƙyalewa da dariya.
''I can see you guys are all happy seeing me here right beside you, na yi farincikin ganinku sosai, Aunties and Mummies, da ma ya'n uwana, barkammu da haɗuwa da junanmu.''
''Ma shaa Allah daughter ya kike ya mai gidan.?" Umma Mansura ta faɗa tare da miƙa ma ta bowl ɗin raken hannunta.
''Lafiya lau Umma, ina su Rashidat?, ko ba'a zo da su ba.?" Liya ta yi maganar tare da ɗaukan raken da ke cikin bowl ɗin ta na mai fara sha.
''Daughter suna dakin ki ai, tun safiya suke jiran zuwan ki.'' in ji cewar Umma Mansura.
Tashi ta fara harraman yi da niyyar shiga cikin ɗakin, hannunta na riƙe da raken tare da cire veil ɗin abayarta mai ɗan faɗi da ya lulluɓeta sosai ta na mai miƙawa Abbhinata.
Ɗakinta na gidan Nenehn ta nufa, har ta kai hannunta kan handle ɗin ƙofar ta ji muryar Ammi cikin kunnenta.
''Liya, dawo nan ki zauna.'' Ammi ta faɗa ba tare da ta kalli mutanen dake wurin ba.
''Saboda mai?, haka kawai ba ƙawayenta ba ne , ke dai Salamatu ki rage baƙin halin nan na ki.''
Neneh da take saukowa da ita da Jiddah ta faɗi hakan, jikinta sanye da wasu ox blood color lifaya masu kyaun gaske.
Gaishe da Neneh da Jiddah ya'n falon gabaɗaya suka yi, Liyana kam jikinta har mazari yake taje wajen Jiddahn haɗe da ba sa side hug.
Murmusawa ya yi tare da shafa kanta ya na mai faɗin ''Ya Zahra na same ku lafiya.?"
Wani kalar frawn ɗin fuskarta ta yi tare da faɗin ''Allah ni Jiddah na yi fushi ma da kai.'' ta yi maganar a shawgwaɓe kamar yadda ta saba yi ma sa.
Murmushi kawai ya yi tare da zama akan kujerar da take a matsayin na sa wanda ko da wasa Neneh ba ta barin kowa ya zaunar ma ta.
Zame jikinta ta yi daga falon tare da shigewa ɗakin na ta wanda duk a idon Ammi da ta kasa magana saboda ganin idanun Neneh kurr akanta.
Ƙarasa shigowa cikin ɗakin ta yi ta tarar da su Rashanda da su Ilham da sauran counsins ɗinsu gabaɗaya suna ta hira, Yusrah na zaune daga gefen wajen book corner ɗin ɗakin ta na chatting da wayarta forming boss lady.
Shigowarta ya sanya su wani kalar ihu haɗe da murna kowannensu na ta shouting ''Awwn.'', ''Mrs HYDAR.''
Basar da su ta yi tare da faɗin ''Wai na fito rannan kuma ban ganku ba.?" Ta yi maganar ta na ƙoƙarin amsar coke ɗin dake hannun Ilham.
Tsaki suka ja a tare, sannan Unaisah ta ce ''Ai ni na manta, da wallahi babu wadda za ta miki magana acikin mu.'' ta yi maganar tare da harar Liya.
''Wallahi Yaya kin ɓata min rai, har yau idan na tuno kamar na yi kuka.'' Ilham ta yi maganar kamar ta kwashe Liya da mari.
''Wannan kuma matsalar ku ce, ai sai ku bar masu aure su shana, haka kawai da daddaren Allah ku wani kwaso jiki, wai za ku kwana.?"
Liyanar ta yi maganar tare da tashi da niyyar fita daga ɗakin.
Yusrah da tun ɗazu maganar Liya ke shigar ma ta kaine ta ajiye wayarta tare da juyowa ta na faɗin ''Toh dan ubanki sai ki aurar da waya'nda ba suyi auren ba.''
All of them were shocked, dan su har ga Allah sun manta da wanzuwarta a ɗakin.
Classy Reeda ce ta ce ''I don't understand, wani ya yi mention ɗinta a nan ne?, ko akwai sa'anta anan.?" Ta yi maganar tare da ajiye pillown da yake kan ƙafarta.
''The thing wonder me OOO." In ji cewar Rashidat.
''Yaya dan Allah don't respond to her, ki ƙyaleta dan Allah.'' Ilham ta yi maganar ganin Liyanar ta fara ƙanƙance ido.
Tsaki Liya ta ja tare da faɗin ''Ni nafi ƙarfin nayi dake kema kin san sai dai na yi da Fatuh mai warin hammata.''
Daga haka ta fice daga ɗakin tare da rufe musu ƙofar da ƙarfi.
''Kutumar......., wallahi sai gidan nan ya koma na yaƙi.'' Yusrah ɗin ta faɗa tare da ficewa ita ma daga ɗakin.
Su ma gabaɗaya suka mara musu baya.
Afalon su Mama Fatuh har sun fito daga backyard daga dafa abincin da suke yi a traditional kitchen ɗin gidan, yan aikin Neneh da Salimah da ta zame ta tafi can tun bayan zuwan su, suna ta rabon abincin da ya ji crey fish.
Yusrah ce ta zo ta tsaya akanta cikin fushi tare da faɗin ''Mama ki taso mu tafi ba zan iya ɗaukan wulaƙancin kowa a gidan nan ba.'' ta yi maganar hannunta riƙe da ƙugunta.
Umma Mansura ce da abin ya ɗaure ma ta kai ta ce ''Yusrah ban gane wulaƙanta ki ba ?, wa ya wulaƙanta ki ɗin toh.?"
Ko kallonsu ba ta yi ba ta ci gaba da yiwa Mama Fatuhn magana.
Ammi ce ta kai dubanta wajen Liyana tare da faɗin ''Hope nothing happened a tsakanin ku.?"
''Ammi zagi na ta yi na rama.'' Liyana ta yi maganar tare da miƙewa daga kusa da Ammin.
''Yusrah ki yi haƙuri ma na ki koma ki zauna.'' Ammin ta yi maganar a sanyaye.
Tsaki Yusrah ta yi tare da faɗin ''Ki ajiye kirkin ki na banza da na wofi a gefe, watarana za ta miki amfani.''
Daga haka ta ja wani tsaki tare da barin wajen.
''Idan kun san wata ba ku san wata ba, Ikimat ki gaya ma ɗiyarki da ta kiyayi ƙasar shuri, ko da kuwa ta na cin ko wani ƙasa ta zauna lafiya.'' Mama Fatuh ta yi maganar tare da ɗaukan jakarta.
''Yaya wallahi, ni ban san mai ya faru ba dan Allah ki yi haƙuri.'' Ammi ta yi maganar kamar za ta yi kuka.
''Wallahi Aunty kika ƙara ba ta haƙuri sai na kira Yaya na sanar da shi wannan maganar, tun da ke ba kida hankali, ta ya ana ƙoƙarin kashe magana ya'rta na wa mutane rashin kunya kuma ta na maganar a kiyayi ƙasar shuri, ita ma ta kiyaye sa, ubanwa rigimar ta kashe, ita ma kanta ta san Nabil ya ji wannan maganar ba a nan kaɗai za'a tsaya ba, daga can ki yi can.'' Umma Mansura ta faɗi maganar zuciyarta a ɓace.
Juyowa Mama Fatuhn ta yi tare da faɗin ''Ai ni ban yi dake ba Mansura, da ƙanwata nake.''
''Sai ki gayawa Awwalu maƙera na garin maraɗi.'' Mama Mansura ta yi maganar tare da ɗauke kanta gefe.
''Mansura za ki ci kaza - kazan ki, dan ubanki.'' inji cewar Mama Fatuh dake tsaye ta na huci.
''Idan kare ya na haushi ba'a tanka shi ai.''
Wani uban tsaki Mama Fatuhn ta ja haɗe da barin gidan.
''Umma ina su Abbhin suka je.?"
Liyana da tun ɗazu jikinta ya yi sanyi ta tambayi Umma Mansura.
''Daughter sun fita da Neneh da Jiddah taron Y'an Maiduguri.'' Mama Mansura ta ba ta amsan haka.
''Ilham zo ki raka ni gidansu Sultana.'' ta yi maganar ta na zira slippers ɗin da ta gani a palourn.
''Wace Sultanah da za ki kwashi jiki, ki tafi.?" Umma Mansura ta tambayeta tare da ƙafeta da idanuwa.
Cikin inda-inda ta ce ''Gidansu .........Ya Aliyu fa, nan maƙotan Neneh.'' ta yi maganar kamar za ta yi kuka.
Classy Reeda dake zaune kusa da Ammin ce ta ce ''Na biyo ku sisi.?"
Murmushi ta yi tare da faɗin ''Why not.''
Daga haka suka fice daga gidan.
><><><>><><><><>><><><>
Gidan tsaf yake a gyare masu aiki na ta haɗa hadan gyaran shi, ko ina na gidan tsit yake babu hayaniyya, sai kukan fararen tsuntsaye dake tashi a gidan.
Direct part ɗin Mami suka nufa su ukun cikin shigarsu na abayoyi masu tsadar gaske.
Cikin siririyar muryarta ta yi sallama haɗe da shiga cikin luxury living room ɗin da ƙamshin turaren wuta mai sanya nutsuwa ke tashi a parlourn.
Ƙarasa shigowa cikin parlourn suka yi Mami na zaune a tamkeken falon cikin wani holland atamfa da aka ma ta ɗinki na alfarma da shi.
Sultan na daga gefenta kansa akan cinyar Mamin da take ma sa massaging kan na sa, wanda alamu sun nuna kan nasa ciwo yake ma sa.
Ƙarasa shigowa ta yi ita da ya'n rakiyan na ta kanta a ƙasa har ta ƙaraso wajen da suke haɗe da durƙusawa ta na mai gaishe da Mamin.
Amsa gaisuwar ta yi, tare da shafa kanta ta na mai sanya ma ta albarka haɗe da amsa gaisuwar su Ilham ɗin da sai wani nannoƙewa take kamar sabuwar mayyar da ta lashe ɗan kishiyyarta.
''Daughter ya kaɗaici.?"
Murmushi kawai ta yi tare da faɗin ''Mami mai wankin ya miki ne.?" Ta yi maganar zuciyarta na ɗan faɗuwa.
''Laah, daughter tun jiya da yamma bayan tafiyarki ya min wankin, and kin san da washing machine ne, ai na gode sosai wallahi Allah ya yi albarka.''
''Amin Mami zamu wuce.''
''Noo wait yau ɗin nan na dafa miki favorite ɗin ki, ina ta jiranki ba ki zo ba, nake faɗawa Sultan zai kai miki after noon, buh tun da kin zo is better ki tafi da shi.''
Kunya ne ya kamata, dan tun da Mami ta san zancan cikin jikinta, ta koma tarairayarta fiye da da.
Hannunta riƙe da wani tray haɗe da wasu plates aciki dake cike da kayan ciki, sai miyan iwedu da amala wanda ya yi baƙi ƙirin.
Ji take kamar ta janyo hannun Mamin ta fara cin abincin, a hankali Mami ta sauke abincin tare da ajiye ma ta shi a gabanta.
''Daughter aci daɗi lafiya, dan ke kaɗai na girka, and I hope you will like it.'' Mamin ta yi maganar tare da amsar ruwa da lemon kankana daga hannun ya'r aikinta ta na mai dire musu shi.
''In shaa Allah Mami, kin san you're the best cooker ever." Liyama ta yi maganar a ɗan kunyace.
''Aunty Liyana ina wuni.'' Sultan ya faɗa ya na mai k'afeta da idanunsa masu firgita ta.
Ba ta amsa shi ba ta cigaba da cin abincinta.
Ƙarar buɗe ƙofar falon da aka yi shi ya ja attention ɗinsu gabaɗaya zuwa can wurin entrance ɗin. Amir ne cikin shigarsa na kaftan sky blue da ta ma sa kyau sosai, ya ƙaraso falon haɗe da gaisar da Mamin, kallonsa ta yi sosai tare da faɗin ''Son ya gida.?" ''Mami Alhamdulillah, daman Mami na ce mu ɗan gaisa ne tun da hanya ya biyo da ni ta nan ɗin.'' ya yi maganar ya na ɗan daddanna wayar hannunsa ya na kallon Liyana da ta kasa haɗa ido da shi.
''Mami ayi min package na shi na ƙoshi haka.'' ta yi maganar ta na mai marairaice face ɗinta.
Order ta bawa masu aikinta, Sultan kam silalewa ya yi ya bar parlourn, yayin da Amir ya duƙufa da chatting ɗinsa, a take wayarsa ta fara ringing, ganin mai kiran na sa ne ya sanya shi tuntsirewa da dariya a fili tare da ƙara kallon Liyanar.
Sai ta camerar wayarsa ya ƙara yi tare da zooming ɗin kyakkyawar fuskarta dan da ɗan tazara tsakaninsu ya ƙara ɗaukan pictures ɗinta kusan uku a dai-dai time ɗin da ta ɗago idanunta ta kalli Amir ɗin, tare da tura ma Hydar da ya addabe shi da kira tun first picture da ya tura ma sa.
Haka nan kawai ta ji da cewa Amir is up to something that will lead her to matsala ko akasin haka, hakan ya sanya ta tashi tare da faɗin ''Mami sai da safe.'' ta yi maganar a sanyaye.
''Mabaruka, packaging box ya zama allura ne.?" Mamin ta faɗa da ɗan ƙarfi.
''Ga shi Maa.'' Mabaruka ta faɗa tare da miƙawa Mamin.
''Ina wanda na zuba a warmer da nace Sultan ya kai ma ta.?" Mamin ta tambaye su.
''See it here Maa.'' Agnes ta faɗa tare da ƙarasowa wajen da wani lunch box mai kyau a hannunta.
Miƙawa Ilham lunch box ɗin ta yi, shi kuma packaging box ta miƙawa Reedah.
Sannan suka fara harraman tafiyya, tsayar da su Mami ta yi tare da kawo musu wa ta leda dake cike da turaruka.
''Amaryarmu har za ki tafi.?"
''Eh Yaya Amir, sai anjima.'' ''Okay dear.''
Daga haka suka fice daga gidan.
Tun a ƙofar gate ɗin suka fara dariya, Ilham na ta kwaikwayon Liya yadda take wani sissinne kai kamar mayya.
Banza ta yi dasu tare da shiga cikin gidan Nenehn da har motarsu Abbhin na pake, alamun sun dawo gidan.
<><><>><><><><>><><><>><
A kwance yake yau ɗin bayan ya dawo daga meeting ɗin da suka yi da ADAFAR VENTURES na Singapore akan kayan da suke son a siyar musu da shi, laptop ɗinsa a kan cinyarsa sai wayarsa a hannunsa ya na kallon wasu reels a Instagram. Sannan ya ga saƙon Amir alamun ya turo ma sa hoto.
A hankali ya ajiye laptop ɗinsa tare da shiga cikin message ɗin,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 31