Share this page
izza, ya fito daga master room ɗin nasa ya nufi hanyar living room. Ko da ya fi to daga Master room ɗin na sa ƴar aikinsa ce a tsaye ta na goge dinning table ɗin da ke dinning area, cikin muryarta mai sanyi ta ce "Xiānsheng, zǎoshang hǎo." (Good morning sir). Amsawa ya yi a taƙaice sannan ya ce mata ta tabbatar kullum zata gyara mai gida sannan ba zai daɗe ba zai dawo. Da toh ta amsa mai sannan ta cigaba da gyaran gidan nasa. Ko da ya fito daga entrance ɗin gidan, parking lot kawai ya nufa, tare da shiga cikin motar da ke da kyau da tsari ya nufi hanyar office ɗinsa domin submitting some documents kafin ya bar ƙasar. Ko da ya ƙarasa compayn, companyn na da kyau da girma, komai na ciki contains white color, ga ko ina wani kalar securities aka baza, ko wani uniforms nasu na tattare da logo na Company da kuma sunansa H&K Ventures.(Hydar&Kyari ventures) H is for Hydar, K is for Kyari, which is his father, saboda mahaifinsa na da share a cikin companyn. Staffs and local staffs sai gaida sa su ke, sai dai ya kaɗa kansa ya cigaba da tafiya har ya ƙarasa cikin ƙantamemen luxury office ɗinsa da ke shaƙe da office equipment. A natse ya zauna tare da danna bell ɗin da ake kiran secretary da clearners, ta ke wata ƴar matashiyyar budurwa wadda daga ganin ta ka san Chinese ce ta shigo, ta gaida sa tare da tsayawa agabansa, "Coffee." Shi ne abin da ya furta cikin muryarsa mai amo da taushi kamar algaita. Sannan ya ƙara da faɗin a kira masa manager da assistant manager (shi CEO ne akwai manager da kuma assistant manager, su ne masu kula da lamarin compayn idan baya nan). Ba'a fi minti biyar ba su ka shigo. Bayan sun zauna aka kawo musu coffe gaba ɗaya sannan suka zauna can gefe da ya ke kama parlour acikin office ɗin CEO ɗin tare da CEO. Cikin muryarsa mai cike da nutsuwa da izza ya ce " Yau zan yi tafiya, a kula da companyn nan sosai, kar a ɓatawa manyan dealers rai in na dawo na tarar da hakan You people will be fired, am I clear? ." "Yes sir."." Sannan manyan dealers na mu kamar su Adafar Ventures na Singapore, da sauran dealers ɗin a haɗa musu fita shakatawa da iyalansu, ga documents ɗin da za ku buƙata na bar ku lafiya.". Sai da su ka amsa masa, daga haka ya bar office ɗin gaba ɗaya tare da bawa driver car key ɗinsa ya kai sa Beijing Capital International Airport (PEK). A motar ma babu wanda ya yi magana har ya ƙarasa drivern ya fito masa da Luggage ɗinsa, cikin mintuna ƙalilan jirginsu ya ɗaga. A cikin jirgin ma wine kawai ya sha sannan ya ci hamburger, jirginsu ya cigaba da lulawa. Ɓangaren Liyana kuwa bayan ta tashi daga bacci tai brush sannan ta ɗora da wanka ta ci kwalliyarta cikin shigarta na jeens trouser da black silky long sleeve da ya lafe a jikinta. Kitchen ta nufa ta bawa masu aiki order na pepe soup ɗin kidney da kuma French fries and egg. Daga haka ta nufi ɗakin Neneh can upstairs, sai da ta gaida Nenehn sannan ta zauna kusa da ita, tace " Neneh lafiya ba ki fito falo ba?, ko dai ba kya jin daɗin jikin ki ne?." " Wallahi ba na jin daɗi, kai na ciwo ya ke wallahi ni da ina da kishiya sai na ce ko ita ta aiko min da bama -bamai, wallahi ba ki ji kai na ba, Rafiƙ in zai fita business ɗin sa zan bi sa ya ajiye ni à asibiti." "Ayya Allah ya sawwaƙe ni na zata ma ƙaruwa za mu yi in fara tara kayan baby." Sai da Neneh ta ƙanƙance ido ta kalleta sosai, sannan ta ce "Ni wallahi ban san ke ɗin ma kin fita daga yarinya ba sai yau, dole na wa Rafiƙ magana a yi sauri a kau da ke kafin ki kawo wa mutane abin kunya, wallahi wannan iskanci ne, ni dai a wurinmu da safe ake wannan." " Ai da safe mu ke magana yanzu ba dare ba ne ba." " Libiya ki ke ko Liyana ki fi ta ido na na rufe." "An ƙi a fita ɗin, ki zo ki wuce in kin je ki ce a miki test ƙila a dace ma ba ki sani ba." Ta faɗa tare da gimtse dariyarta. Fitowarta daga ɗakin Neneh ke da wuya, Salimah ta jera mata komai a dinning ta na cikin ci Jiddah da Neneh su ka sauko cikin shigar alfarma. Tana zaune a dinning ɗin tai wa Jiddah barka da safiya, sannan ta kalli Nenehn ta ce " Allah ya raba lafiya." Harara kawai Neneh ta watsa mata sannan tai gaba suka fita daga gidan. Bayan ta kammala cin abincin, ɗakinta ta nufa tare da dailing number Sultan, su ka sha soyayyarsu, cikin mauryarsa mai daɗin sauraro ya ce " Big Brother na dawowa yau zuwa next week sai a fara maganar auren, tun da kin hana ni zuwa gidan Grand ma ɗin ta mu, kin dage a school za mu na haɗuwa." " Jehova of Nazareth", is not like that oo, kawai ban iya kwantace ba." "Bana hanaki ambatan Jehova ba ? Is like idan mun yi aure zan hana ki ƙawance da Lilian....." " Sorry Habibi bazan ƙara ba." Daga haka su ka shiga wani hiran. Ko da su ka kammala wayar arround 1 O clock, wanka ta ƙara yi tare da sa wani Classic Abaya ɗinta milk and brown color, sannan ta sa hula brown, tare da zura wani slippers masu kyaun gaske, da ya ƙarawa ƙafarta kyau. Message ta gani a wayarta na Sultan kamar haka "come online, I wanna talk to you dear." Da murmushi a fuskarta ta shiga what's app tare da shiga chat ɗinsu, su ka fara chatting, sannan ta nufi hanyar parlour ta zauna a ɗaya daga cikin lafiyayyun kujerun parlourn. Tana chatting ta na kurban strawberry Hollandia ɗin da ke kan side table ɗin kujerar falon. Hankalinta gaba ɗaya ya na kan chatting ɗin da take yi. Sallamar da ta ji ne har sau biyu da kuma salon canzawan da ƙamshin ɗakin ya yi shi ya bata daman ɗagowa da kanta tare da kai dubanta wurin wadda ke shigowa cikin parlourn. Mata ce ko kuma mu ce uwace ta shigo cikin gidan cikin shigarta na Atamfa Exclusive da ya mata kyau ɗinkin doguwar riga mayafin da matar ta yana akanta da ya ƙara mata kyau kuma ya fito da siffarta na uwa sannan baƙin mayafin ya ƙara fitar da colorn fatar ta ruwan ƙwai. Cikin sassanyar muryarta ta ƙara yin wani sallama a karo na uku, sannan liyana ta amsa tare da faɗin "Sannu da zuwa Maa, ina wuni." Tare da yi mata alamar zama akan ɗaya daga cikin kujerun masu kyaun gaske. Murmushi mai kyau matar ta sakar mata tare da amsa mata da " Lafiya lau ƴammata, ya kike?." " Lafiya lau Maa." " Neneh na ciki?." "A'a ba ta nan ta fita tun safe." Mai aiki ce ta zo tare da faɗin"Aunty Liyana mai za'a kawowa Mamin?." " Bar shi zan zo na haɗa ma ta." Daga haka ta shige kitchen ɗin tare da haɗa mata abubuwan motsa baki. Table ta janyo tare da ajiye tray ɗin a kai. Godiya matar da mai aiki ta kira da Maami ta mata sannan ta ce " Ina Nenehn ta je?." " Ai tun safe ba ta ji daɗi ba shi ne mijinta ya kai ta hospital." Ɗagowa matar ta yi, Liyana tai sauri ta ƙara faɗin " Jiddah kai." Murmushi matar ta sake yi sannan ta ce " Subhanallah, Allah ya sa kaffara ne, in ta dawo ki ce ma ta na zo amma zan dawo in ta dawo gida, ki ce mata Mamin Sultana ce ta zo, ya sunanki ƴammata?." Cikin sanyin muryarta ta ce " Fatima." Ma sha Allah fatiti." Sai da ta sha ruwan sannan ta ce mata ta tafi ta kula da kanta. Toh kawai Liyana ta ce ta na jin matar ta kwanta mata a rai, ga nutsuwar matar mai ratsa jini, dan ita kam matar ta yi mata kwarjini sosai.........✍️ Akwai ƙura faa a gaba 🤢😂😂🫵 > THANK YOU FOR READING 💜 To everyone who took the time to read The Regret, you’ve just held a piece of my heart in your hands. Kuna daga cikin dalilin da yasa zan ci gaba da rubutu. See you in the next chapter of our journey. With love, Pending Amarya 🦋 > Pending Amarya's book corner Extraordinary everyday 🦋 > Share for more pages in sharing ɗinku ya yi yawa zan ƙara typing da yawa. Pending Amarya as usual 🦋 🫠 I really love you readers 💎 > Pending Amarya's book corner Extraordinary Everyday > Mondays to Fridays from 8am to 12am follow for more 🎊🫂📚> Pending Amarya's book corner Extraordinary Everyday 🦋 posting channel 👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbAyucH7j6g0IDCpPi2V *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.💪 ::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::: The Noble Writters ✊ Dedication is our strong THE REGRET 🙆 when love meets temptation who survives? Na saba da ke 🫵😉 na aminta da ke soyayya da ke 🤧😪zaƙi kamar rake 🤫 Baby buɗe min ƙofa na zuciyarki nuna min hanya na zo gabanki😩 na lura kece ruhinaaa burina a kawo ki ɗakinaaaa😅😉🫵 BOYS KIDDO DUNIYA NE 🤗 THIS PAGE IS DEDICATED TO HIM 😂😂🫵 The Regret Mallakar pending amarya ce ban yarda a sauya min labari ba ta ko wani siga, idan hakan ko ta faru kotu ne zai rabani da ke!!!! Pending Amarya ni ce satellite ina haska su kamar ring light 😂😂💔 Mallakar Pending Amarya ce_ NDA DUBDO🦚 My Maiduguri ppl CHAPTER NINE : HYDAR & LIYANA 🦚💎 LONG CHAPTER ✍️ _PENDING AMARYA _ Page 18 Toh kawai Liyana ta ce ta na jin matar ta kwanta mata a rai, ga nutsuwar matar mai ratsa jini, dan ita kam matar ta yi mata kwarjini sosai.... Ko da yamma da Nenehn ta dawo Liyana ba ta yi mata maganar matar da ta shigo ba sam. Sai ma biyewa Nenehn da ta yi su ka cigaba da hira ta na ba ta labarin zamaninsu yadda maza su ka yi rubibinta, sannan Allah ya sa ta zama rabon Jiddah a yadda ta ce dan ita ba ta yarda da maganar Neneh. Sai wurin goma sannan su ka shiga ciki sai da su ka yi waya da Sultan sannan ta kwanta. Ɓangaren Mamin Sultana ku wa tun da ta koma ta sa Sultan ya je ya siya mata fresh fruits domin haɗa fruit salad, sai kuma snacks saboda Hydar na da son waɗannan ƙananan abunawan. Abinci su ka haɗa na alfarma, tun da shima Yallabai be daɗe da dawowa daga can ba. Shirye shirye su ke a gidan kamar biki, kuma ba shirye-shiryen wasa ba. Gida ne da ya amsa sunan sa gida, domin gidan su Liyana ba komai bane ba. Ga faɗi, ga kyau, uwa uba komai na gidan looks zamanious(🤭😂🫵). Komai na gidan is rich and elegant, babu wani tarkace na ƙyale -ƙyale, komai is neat and luxury. Ko da Sultan ya dawo waya maƙale a kunnensa. " Maƙale mata ƙarfe nawa jirginsu yayanka zai sauka?." Sai da ya katse wayar sannan ya ce " sorry Mami arround 6 O clock in the morning In Sha Allah." Allah ya kaimu toh, so na ke na shiga wurin Neneh kuma ga shi dare ya yi, wai naje ɗazu wai ba lafiya." "Ayya Allah ya ba ta lafiya." Daga haka ya shige ɓangaren sa. Mami wasu daga cikin masu aiki ta bawa ordern su gyara ɗakin Baban gida Hydar. Tun cikin daren su ka ci ƙarfin aikin na su tun da saukan sassafiyya ne zai yi. Ko da Alhaji Kyari ma ya dawo hira su ka dasa tsakaninsu banda Sultan da Assultanah da ke ɗaki ta na karatunta na final exam. Su Ammi na ta fama da Abbhi kullum cikin kiran Liyana ya ke ya ji zance amma kullum maganar ɗaya ne ba ta gama plan ɗinta ba. Itama Ammie ba ta zaman gidan sai dai ta bar Rufaidhat da Abbhin saboda ta buɗe wajen siyar da hijabai da kuma kayan kwalliyan mata ba ki ɗaya, sannan ta kan je gidansu wani sa'in dan in ta biye wa Nabil tsaf sai ta daina hulda da mutane. Liyana da ke zaune cikin shigarta na kullum wato palazzo trouser da long sleeve shirt white color, sai hulanta da ke kanta da gucci slippers ɗinta purple color. Salimah ce ta kawo mata hollandia strawberry ɗin ta sai kuma milky donut, tana zaune ta na daddana wayar hannunta tare da sipping ɗin yourghurt ɗin da ke cikin transparent glass cup ɗin ta yi crossing ƙafafuwanta ɗaya kan ɗaya. Neneh ce ta sauko cikin shigarta na lifaya white and golden color, "isasshiya, dubi yadda ki ka zauna jibge kamar kayan wanki ba aikin fari ba re na baƙi, in kin yi aure naga mai miki ai, kya bari bakwai ta yi kafin ki fara ciye-ciye, mutum ba auki sai ci kamar gara, gafara dallah in zauna." Nenehn ta faɗa tare da zama kusa da Liyanar. Ba ta tanka mata ba ta cigaba da abinda ta ke yi. "Ni ina da ke ai ba zan ma bari Abbihna ya ɗaukar min house maid ba, ki ka sa uniform irin na Salima ai ba ƙaramin kyau za ki yi ba, tun da kuma gidan kakannin ki ne sai ki zo ki bani time ɗin cin abinci." " Ni ki daina ambatar min wannan uban na ki a gida kar Mala'ikun rahama su daina shigo min." "Kya ji da shi kuma." Ɓangaren gidan Alhaji Kyari tun ƙarfe shida su ka nufi filin jirgin saboda tarban Hydar ɗin, ko wannensu ya ci ado cikin shiga na alfarma, sannan kuma na mutumci sakkowa ya ke cikin aura ɗinsa da ya gama bin jikinsa, ya doso wurin da ya hangin sanyin idaniyarsa ma'ana mahaifiyyarsa, a hankali ya ja LV trolly ɗinsa duk gajiya a tattare da shi, Assultanah ce ta fara ganinsa ta tafi da ɗan gudunta ta rungumesa, shi ma rungumeta ya yi sannan ya sakar murmushin sa mai kyau. Sannan su ka ƙarasa wurin parents ɗinsa ya gaida su ci ke da girmamawa, Mami ce ta kallesa tare da faɗin "Am proud of you Baamii, Allah ya sa Albarka." "Amin." ya ce sannan su ka shige motar da su ka zo da ita har guda biyu. Ko da su ka ƙaraso gidan sai da ya yi wanka ya rama sallolinsa sannan ya fito cin abinci shima snacks kawai ya ci sai fresh milk, sannan ya shige ɗakinsa domin hutawa. ****** Liya na gama cin snacks ɗin komawa ta yi ta kwanta bacci dan sai ƙarfe 12 ta ke da lectures shi ma ba za ta je ba wani birthday party za ta da Lilian. 12 dai-dai ta tashi tare da nufar toilet ta yi wanka tare da yin alwala dan har ƙarfe ɗaya ya yi, sannan ta yi sallar ta haɗe da shiryawa cikin simple dress mara nauyi, because sai ƙarfe 4 za ta kama hanyar zuwa gidan Lily because a Piccolo za ayi partyn. Wani kalar yunwa ke nuƙurƙusan cikinta dan haka kitchen ta nufa tare da buɗe fridge ta ga Salimah ta ajiye mata fruit salad, murmushi kawai ta yi tare da ɗaukan bowl ɗin ta fara shan fruit salad ɗin a hankali kwance. Neneh ce ta ƙara sakkowa amma wannan karan ta canza lifaya zuwa maroon, harara Liyana ta dallah mata sannan ta ce " ke ba kya ta shi sakkowa sai mutum na cin abinci? Ni fa bana son kwaɗayi." "Ni ba shi ya dameni ba Fatima, maza zira hijabyn ki mu je gidan Alhaji Kyari, kin ga ɗan nasa da na ke gayamiki ya dawo." "Babu in da za ni." Ta na faɗin haka ta cigaba da shan fruit salad ɗinta. "Sanyi ya haifi zafi wannan haka ya ke, mai tarbiyya ya haifi mara tarbiyya." Daga haka ta sa kai ta fice a falon. " Za ki dawo ki faɗa min waye mara tarbiyyar ai, tsohuwa sai bala'in tsiya, mtsww." Sannan ta shige ɗakinta tare da shiga app ɗin Instagram ta na duba wasu comments da aka yiwa pictures ɗinta. Wasu zagi ne wasu kuma zallar goyan baya ne daga followers ɗinta. Gidan da aka rubuta Kyari's mansion Neneh ta kutsa kai ta shiga securities na ta gaida ta dan duk cikinsu ɗauka su ke Nenehn mahaifiyyar Alhaji Kyari ce. Gidan ya rabu kashi da dama, ko ina kuma cike ya ke da kayan alatu. Ɗaya daga cikin ɓangaren da ke kallonta ta shige, Sultan ta fara cin karo da shi a living room ɗin, sai da ta yi a' uziyya sannan ta wuce shi ya na mata magana ko kallonsa ba ta yi ba daddagewa ya yi ya ce "toh yi haƙuri ƴar tsohuwa zan auri jikar ta ki." A ƙufule ta juyo tare da faɗin " ai ba neman kai na ke da ita ba." Dariya kawai ya yi sannan ya juya ita ma ta yi hanyar sashen Hajiya Khairat ɗin. Shiga ta yi tare da zama, Assultanah ta shigo ta yi ta yi wa Nenehn tsiya. Ko da Mami ta fito su kai ta hira, sannan ta kira layin Aliyu Hydar ta sanar masa Neneh na jiransa. Bai ɗauki lokaci ba ya fito sanye da T-shirt da jeens trouser black color sai slippers da ya zira. Shigowa ya yi tare da sallama tare da bayyanar da murmushinsa akan fuskarsa. Bayan sun gaisa da Nenehn su ka ɗan taɓa hira sannan ya ce " zai ɗan fita ya ga gari ya dawo, sannan Sultana za ta kawo mata tsarabar ta." Sannan ya sa kai ya fice daga gidan. Mami ce ta kalli Neneh tare da ɗan gyara zamanta ta ce "wallahi Neneh wa ta fulawa na gani a gidan ki in da hali na kamawa Babana ita." Ta ƙare zancen da murmushi. "Ki ganar da ni mana uwar Alkhairi, fulawa ai da yawa a gidana, yanzu in sa uzaifa mai gadi ya tsinko miki duk wadda ta miki." Murmusawa ta yi sannan ta ce"Neneh kenan, wannan ƴar budurwar ce wallahi da na ganta a gidan ki kuma ta burgeni shine na ce in ba'a mata miji ba ina son Hydar ya aureta." "Kamar ki na raina khairatu , wallahi ri ga ni faɗa kawai ki ka yi nima abin da ke raina kenan ai ko sun yi mata mijin sai sun since, in dai Hydaru ne, amma kin gayawa kyarin ko?." " Eh shi ya ce na tunkare ki da zancan." "Toh Ma shaa Allah ina zuwa zan sanar da Rafiƙ komai sati biyu masu zuwa ma ai sai a ɗaura aure tun da tuwo na mai na za'a yi." "Exactly, Allah ya tabbatar da Alkhairi." Daga haka su ka cigaba da hira har Nenehn ta koma gidanta. Ko da Neneh ta dawo daga gidan da wasu tsadaddun lifaya ta dawo, ta kalli Liyana ta ce "kin ga harkar arziƙi, wannan kwarɓaɓɓen saurayin na ki mai ya taɓa kawo min, kullum cikin wayar tsiya." "Ke abin duniya ya dama ai." Jiddah ne ke saukowa a hankali cikin jallabiya black color mai tsantsi ya kafa kansa da hula fara mai kyau, hannunsa riƙe da walking stick ɗinsa. "Jiddah! , ta faɗa tare da ƙarasowa wurinsa ta rugumesa, ta na kuma gaida sa duk a lokaci ɗaya. Ƙarasowa su ka yi su ka zauna ku sa da Neneh, cikin muryarta mai cike da manyantaka ta ce "Lale marhaban ya Rafiƙ." Murmushi ya yi tare da gyaɗa mata kai alamun ya na jinta...... Sorry da bana update kwana biyu yau da zafi na na taho 🥹💎 THANK YOU FOR READING 💜 To everyone who took the time to read The Regret, you’ve just held a piece of my heart in your hands. Kuna daga cikin dalilin da yasa zan ci gaba da rubutu. See you in the next chapter of our journey. With love, Pending Amarya 🦋 > Pending Amarya's book corner Extraordinary everyday 🦋 > Share for more pages in sharing ɗinku ya yi yawa zan ƙara typing da yawa. Pending Amarya as usual 🦋 🫠 I really love you readers 💎 > Pending Amarya's book corner Extraordinary Everyday > Mondays to Fridays from 8am to 12am follow for more 🎊🫂📚> PENDING AMARYA'S BOOK CORNER EXTRAORDINARY EVERYDAY POSTING LINK 👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbAyucH7j6g0IDCpPi2V *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.💪 ::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::: The Noble Writters ✊ Dedication is our strong THE REGRET 🙆 when love meets temptation who survives? THIS PAGE IS DEDICATED TO MY FRIENDS🫵 Rufaidhatah 💔 Afnan (My Khaldun). Rashanda, Princess minal, Fatimatuzzahra (K. M. A). Assultanah 🦧, Besty ss, My Hafsy Dear. Umty luv 🥀,, Sis Mansura. And so on. This page is dedicated to you guys. I love you all 🤫🌚 The Regret Mallakar pending amarya ce ban yarda a sauya min labari ba ta ko wani siga, idan hakan ko ta faru kotu ne zai rabani da ke!!!! Pending Amarya ni ce satellite ina haska su kamar ring light 😂😂💔 Mallakar Pending Amarya ce_ NDA DUBDO🦚 My Maiduguri ppl 🦚💎 LONG CHAPTER ✍️ _PENDING AMARYA _ Page 19 Ƙarasowa su ka yi su ka zauna ku sa da Neneh, cikin muryarta mai cike da manyantaka ta ce "Lale marhaban ya Rafiƙ." Murmushi ya yi tare da gyaɗa mata kai alamun ya na jinta...... Kallon Liyana ta yi sannan ta kalli Jiddah da ke zaune, ya gane abin da ta ke nufi dan haka cikin sanyin muryarsa ya ce "Ya Zahra." Ɗago da kanta ta yi because haka Jiddah ke kiranta, "Shiga ciki manya za su yi magana." Nodding kan ta ta yi tare da ɗaukan wayarta ta nufi ɗakinta ba tare da ta tankawa Nenehn ba. Matsowa ta yi sosai tare da kamo hannunsa ta ce "Rafiƙ, khairatu ce ta same ni da wata maganar da ta faranta min rai sosai, ɗan wajenta Hydar dai namu da kuma Liyana ta ke son a haɗa aure, ai kaga ɗaurewar zuminci kenan." " Liyanar ta ce miki ba ta da manemi ne?." "Ta doshi wata a gidan nan wallahi ban taɓa ji ko da wasa ance ana sallama da Liyana ba." "Zan ji ta bakinta toh dan ba za'a mata dole ba." " Toh Rafiƙ Allah dai ya tabbatar da Alkhairi shi ne kawai." Bayan shigar Liyana ɗaki kuwa waya su ka kuma yi da Sultan. Bacci ta ƙara komawa, ta yi baccin sosai, sannan ta tashi arround 4 , ta yi wanka tare da brush.sai da ta tsane jikinta sosai sannan ta ta fara shiri because partyn ma anko su ka yi ita da Lilian. Duk da ba wani tsada ne da kayan ba ta zaro su daga cloth set ɗinta da ke sheƙe da kaya saboda shopping ɗin da ta ke yi, carton colored palazzo trousers ne sai normal hand long sleeve shirt coffee color sannan ta ɗaura ɗankwalinta matar minister, gucci high heels masu kyau black color sai jaka shima gucci black, latest phone ɗinta wadda ake ya yi iphone 14normal ta ɗauka tare da cilla fresh mint chewing gum a baki sannan ta shafa lipstick a heart shaped full lip ɗinta, sai ya ƙara wa shigarta kyau da kuma tsari, ba za ka so ka mata kallo ɗaya ka ɗauke kai ba. Wani ɗan siririn eye glass da ke kama da medical glasses ta sanya amma kuma is for passion masu kyaun gaske da ɗaukan ido, sai da ta ɗauki wayarta ta sakarwa Instagram reels sannan ta fito parlour da Neneh ke ta kallon AIT NIGERIA. kallon Nenehn ta yi tare da ɗauke kai, ta nufi Jiddah da ya ke a zaune ya na kallonsu. " Jiddah! Dan Allah car key za ka bani." ta faɗa tare da siddar da kanta ƙasa,"ki amsa a wurin driver, sannan ina za ki je ?." Ba za ta iya faɗan birthday za ta je ba Jiddah is very judgemental, zai iya hana ta zuwa idan ta ce masa birthday za ta je. Ajiyar zuciya

Chapter 7 of 31