Share this page
fito. ^^^^^^^^ Ƙarfe goma jirgin su ya sauka a ƙasar China a babban birnin Beijing, driver ɗinsa ya kira ya kaisa har gidan da yake tsaff komai a gyare. Wanka ya yi tare da yin alwala ya na mai gabatar da sallolinsa, sai da ya ƙara kallon zanen Acn sannan ya yiwa factory ɗinsa forward, saboda afara aikin kafin washegarin ranar. Har ya fara ƙoƙarin kwanciyya yanayin da ya tsinci kansa a shekaran jiya ya fara ƙoƙarin dawo ma sa sabo, ya na mai ƙara hango structure ɗin jikinta kamar ta na kusa da shi, saurin kauda tunaninta ya yi acikin brain ɗinsa, tare da rufe idanunsa da sleep mask ɗinsa. Da sassafe ya farka ya shirya cikin wasu farin suits, wanda suka matuƙar amsar jikinsa, car key ɗinsa ya ɗauka tare da nufar dinning da har mai aikinsa ta gama haɗa masa breakfast ɗinsa, gaishe shi ta yi da yaren Chinese, wanda shi ma ya mayar ma ta martani tare da zama akan kujerar ya na mai fara cin abincin. GPS app ɗinsa ya shiga ya na kallon duk inda taje da motar a jiya, gyaɗa kansa ya yi tare da ɗaukan tissue ya na mai goge bakinsa kana ya fice daga gidan gaba ɗaya. Sosai staff's ɗinsa suka yi missing ɗinsa, hakan ya sanya shi jin daɗi sosai. AFTER 3 WEEKS🎊🫧🦚 Sosai ta mai da hankali take shiga kitchen tare da Salimah, sannan ta na yawaita miraja'a saboda wajen da suka ɓace ma ta su dawo ma ta kan hanya. Around 10 O'clock ta shirya cikin dogon jallibab sky blue, tare da sanya wani niƙab mai mugun kyau sannan ta saka safar hannu da na ƙafa, sosai shigar ya yi mata kyau, ya fito da muslimah color ɗin da yake ɓoye ajikinta. A hankali ta fito cikin falon ta tarar da ko ina tsaf, tea kawai ta sha dan ba yunwa take ji ba, tare da ɗaukan wayarta da car key ɗinsa tare da barin unguwar ba ki ɗaya, Test da yawa sun wuce ta, amma anyi mata makeup, hakan ya sa ta ɗan sakin jiki a cikin school ɗin. Mutane da dama na mamakin nutsuwar da ta sa mu, yar gidan Nabil da niƙab, it seems weird to them, matar da ɗankwalin arziƙi ba ta sanyawa ita ce da chador?, dan abin da ta sanya ya fi hijabi, daga ƙarshe dai cewa suka yi ƙila content take shiryawa dan anan tafi kauri. Zaune suke cikin motar Hydar da ta ɗaukesa tamkar na ta, ta ƙurawa wayarta idanu, ta na kallon wani picture ɗinta ita da Abbhi, birthday ɗinta na shekara 19, kusan shekaru uku da suka gabata. Wani hawaye ne suka zubo ma ta ta yi sauri ta goge tare da shiga cikin call logs ɗinta ta na mai lalubo numbersa. Ya na fara ring aka katse tare da biyo kiran, ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗaga wayar da sauri ta na mai fashewa da kuka. Ata can ɓangaren shi ma Abbhin wani kalar zazzafar ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin ''Ya'r Abbhinta, why?, mai sa kike zubar da hawayenki masu daraja, Did you wanna hurt your Abbhi?." Ya yi maganar a sanyaye, ''Abbhina I'm soo sorry, dan Allah na zo na ganka, nayi missing na ku, ka ce ina gaida Ammi.'' ta ƙarashe maganar ta na fashewa da wani kuka mai karyar da zuciyar mai sauraro. ''Can you stop this babe, ba na son kina zubda hawayenki, kina ina yanzu?." Ya yi maganar a sanyaye. ''Abbhina ina school, ina so na koma gidana amma yanzun." ''It's okay then, mai zan siyo miki, ki na da yourghurt a gidan ki or na taho da su?." Murmusawa ta yi tare da faɗin ''Abbhina pizza kawai da ice cream nake so.'' ''Okay Allah ya miki albarka.'' ''Amin Habibi, sai ka zo.'' ''Yeah first fruit.'' Daga haka suka yi sallama. Lily ce dake cikin motar ta juyo ta kalleta, tare da faɗin ''Drama Queen, e kullum idan ba kiyi creating drama ba, ba kya jin daɗin rayuwar ki ne?, dubi wani kayan da kika saka kamar mascurate, ba kya jin zafi ne?, ni I'm even thinking idan Liya bae ɗin da na sani ce ma right beside me.'' Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce ''Lily ko oven ɗin da yayi shekaru ɗari ana amfani da shi bai gasu kamar yadda na gasu cikin 2 months ba, ke ni yanzu akan sanya hijabi zan iya rabuwa da kowa, ke hijab na da muhimmanci a rayuwata.'' ''Toh Liya Allah ya ba ki haƙuri.'' daga haka ta cigaba da yin video ɗinta. Bayan sun rabu da Lilyn ma gidan Neneh ta wuce dan ta daɗe ba ta ga baiwar allahrnan ba. A hankali ta yi horn, mai gadi ya buɗe ma ta ta shigar da motar na ta cikin gidan. Ko ina tsit babu hayaniya, hakan ya sa ta kutsa kai cikin living room ɗin da ƙamshin turare Mai daɗi yake tashi. Already daman 2 O clock ya ri ga da ya yi, Neneh na zaune ta na lunch ɗinta mai rai da lafiya, sallamar Liyana ne ya fargar da ita daga nisan tunanin da ta lula. Cikin takunta na isa ta ƙaraso wajen da Nenehn ke zaune, zaro idanu Neneh ta yi tare da faɗin ''Kee duniya, wannan wani kalar iftila'i' ne mayu da ranar Allah, mayyar ma a rasa wadda za'a aiko min sai aba kamar fly wood?." Tsaki Liyana taja tare da cire hijab ɗin jikinta tare da zama kusa da Nenehn tare da faɗin ''Kika jefa ni cikin iftila'i' Neneh, sai kuma kika ɗinga gulmata, kamar ba ke kika haɗa auren ba?." Ta yi maganar ta na ƙura ma Nenehn ido. ''Ooh ooh ni Ajiddeh matar Aliyu, da yaushe na yi gulmar ki, kai wani munafukin ne ma ya sanar dake wannan lahanin.'' ''Ai na san haka za ki faɗa, amma ai ni dai na san wallahi kin yi maganata, da ace dai ban san halinki bane.'' ''Toh ni dai gaskiya babu wanda na faɗawa zancen na ganki kin yi baƙi, kin babbake kin ƙone kamar lantarki, sai Maimu, ita kuma Maimu idan ba dan ba ki da hankali ba ai kakar ki ce ita ɗin." ''Ahaff ai na san sai kin faɗa, ke Neneh mai sa bakin ki ba ya shiru wai?, anya ya'r Mairo ba ta hau ki ba?." ''Uban ki Nabil da Uwarki Ikimat.'' ''Ni ba wannan ne ya kawo ni ba, yunwa nake ji wallahi.'' ta ƙarashe maganar tare da shigewa cikin kitchen. Bayan ta ɗebo abincin ma hirar arziƙi suka dasa da ita da Nenehn, har take sanar da ita akwai family meeting da za'a gabatar next month ,Kuma kowa ne zai zo, a gidan Nenehn za'a yi. Sai misalin ƙarfe shida ta shiga gidan Mami suka gaisa, ta ɗan jima a gidan sannan da misalin ƙarfe 8 ta bar gidan zuwa gidanta. Ko ina na gidan neat Salimah ta gama gyara shi sosai. Ƙarasowa falon ta yi tare da zama ta na jin ƙamshin turaren na hawar ma ta kai, ji ta yi zuciyarta na wani kalar tashi, wanda hakan ya sanyata tashi da gudu ta nufi hanyar stairs domin zuwa ɗakinta ta yi aman, anan wurin ta saki aman. Da sauri Salimah ta ƙaraso wajen ta na mai ma ta sannu. Ji tayi gaba ɗaya jikinta a take ya yi wani kalar sakewa, appetite ɗinta gaba ɗaya ta yi losing na shi. Da sauri Salimah ta gyara surface ɗin tare da ɗaga Liyana ta kaita ɗakinta. ****** Tun buɗewar ranar he's very busy, ko ina is occupied with ayyukan da za'a yi a samar da acn nan har a fara gwada shi. Alhamdulillah cikin 3 weeks aka samar da grake Ac ɗin yadda Amir ya faɗa masa ya saka, A office ɗin aka fara test ɗinsa. Ganin ya yi ne ya sanya shi bawa workers ɗin damar a fara buga shi. Kwance yake akan gadonsa idanunsa akan laptop ɗinsa ya na kallon yadda take ta kwarara amai a wajen corridor ɗinta, sosai ya ƙura mata ido ya na kallon kyakkyawar fuskarta da take ta struggling wajen fitar da abincin dake cikinta. Ganin har Salimah ta kaita ɗakinta ne ya sanya shi switch ɗin camera zuwa tsaftataccen ɗakinta, akan idanunsa ta cire kayan dake jikinta har ta shige toilet ɗin idanunsa akanta yake ko gigin cire idanunsa daga laptop ɗin bai yi ba. Ƙara switch ɗin cameran ya yi har cikin toilet ɗin ta yi wanka haɗe da fitowa da ƙyar, wani kalar fashewa ya ga ta yi da kuka tare da sanya kayan baccinta ta na mai yin kwanciyyarta. Ajiyar zuciya ya sauke tare da juyar da kansa, wani kalar jaa idanunsa suka yi, da sauri ya tashi tare da buɗe fridge tare da ɗaukan lemon tsami ya na mai matsa shi cikin ruwan zafin gami da shanyewa. A hankali ya buɗe laptop ɗin tare da kallon kyakkyawar picture ɗin kan screen ɗin laptop ɗin, wani kalar numfashi ya sauke tare da kashe laptop ɗin ya na mai gyara kwanciyarsa duk da , da rana ne hakan bai hana bacci mai daɗi ɗaukansa ba. Ringing ɗin wayarsa ne ya tashe sa daga baccin da yake, kallon wayar ya yi ya na mai jan wani kalar tsaki tare da amsa kiran da ya ga sunan Little ne ajikin wayar. A hankali ya ɗaga, cikin kiɗimammiyar murya Assultanah ta ce ''Yaya Mami babu lafiya, rashin lafiyanta ya yi tsanani, kuma babu kowa a wajenta.'' ta ƙarashe maganar hawaye na zuba a idanunta. Ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin ''Calm down Auta, ya'n aikinta ba sa nan ne?." ''A cikin su ne wa ta ta kira ni , gaba ɗayan su kuka suke yi, yaya I'm scared.'' ''Shut up, kafin na bubbuge miki baki yanzun nan, ki mai da hankali kiyi abin da ya dace bana son shashancin banza, sai lokacin mutuwa ya yi ake mutuwa Am I clear?." ''Yes Yaya.'' ''Okay then wipe your tears autar Mami.'' ''Toh Yaya ka kira ta fa.'' ''Zan kirata ƙila Prank take miki.'' Daga haka suka yi sallama, kasa komawa baccin ya yi, hakan ya sanya shi ɗaukan wayarsa tare da kiran Mamin, a hankali ta ɗaga wayar tare da faɗin ''Mami ina wuni.'' '' Lafiya lau Hydar, ya aikin?." ''Lafiya lau, Mami ya jikin?." ''Lafiya lau wallahi, Auta ta kira ka kenan?." ''Wallahi Mami ta tayar min da hankali, wai ya'n aiki na ta kuka,, ita ma ta na kuka ta kira ni.'' ''Son bar lamarin Sultanah, ba ciwo na ne ya tashi ba is just that, tsantsi ya kwasheni daga tiles na faɗi a ƙasa ne, su kuma suka tsorata da ganin hakan, amma da sauƙi, kuma kai ma ka san Agnes da zuzuta abu.'' ''Yeah hakane Mami, still dai zan aiko miki ita ta ɗan lura dake.'' ''Wai Fatima ko wa?." ''Eh ita Mami.'' ''A'a dai ka barta ita ma yau ta zo ai, kuma yarinyar ta na da buƙatar hutu.'' ''Toh shikenan Mami duk yadda ake ciki sai ki kira ni, Allah ya ƙara sawwaƙewa.'' ''Amin Son, Allah ya kare ka, ya dawo min da kai lafiya.'' ''Amin Maa.'' Daga haka suka yi sai an jima, juya wayar hannunsa ya yi tare da tashi ya cire kayan jikinsa ya shigewarsa wanka. A ƙudun dune take cikin bargo, jikinta ya na wani kalar kakkarwa, idanta ɗaya na zubar da hawaye mai zafi, wanda muke ma sa laƙani da hawayen masoyi, wayarta taji ya na ring hakan ya sa ta kai hannunta dake kakkarwa ta ɗaga wayar. ''Assalamu alaikum sis.'' aka faɗa a ta can ɓangaren. ''Wassalamu alaykum autarsu Yaya, what's wrong?." ''Aunty Liyana, dan Allah da safe kije gidan Mami ba ta da lafiya, take care of her dan Allah.'' ''Okay Sis, Sai da safe, kar ki saka kanki cikin damuwa she will be fine okay?!." ''Thanks sis à huta lafiya.'' ''In shaa Allah.'' daga haka ta kashe wayar, wani kalar zazzaɓi na bijiro ma ta, ga wani yunwa da take ji. A hankali ta sauko daga upstairs ɗin tare da kunna switch ɗin falon kwalin pizza ta gani da wasu abubuwan ƙwalama, hakan ya sa ta nufi wajen haɗe da fara cin pizzar. Yanka biyar kaɗai ta iya ci sannan ta rufe kwalin tare da shan wani soya milk da yake cikin wani kwalba mai kyaun gaske. Anan kan dinning ɗin wani bacci mai daɗi ya kwasheta, ta ɓingire tare da cigaba da baccin na ta. Sallahr farko ne ya tashe ta hakan ya sanyata miƙewa ta na layi ta nufi ɗakinta ta yi alwala haɗe da yin Sallah, tare da fara recitation na Alkur'ani mai girma da daddaɗen muryarta. Hizb ɗaya ta samu ta karanta, jiki ba ƙwari ta kamawa Salimah girki, face mask a hancinta. Ta rasa mai yake damunta daga jiya zuwa yau, she's feeling dizzy, ta rasa wani kalar matsala ne hakan. Suna gama girkin ɗakinta ta shige haɗe da yin wanka ta shirya cikin wani kalar dakakken abaya mai kyaun gaske, milk color, yau kam ɗayan wayarta ta ɗauka ba iphone 14 ɗinta ba, pink diamond iphone da shi za ta fita. Tea mai zafi ta sha kana daga bisani ta nufi hanyar fita daga cikin gidan, ba ta wuce ko ina ba sai gidan Mami, gidan as usual ya na nan tsaf kamar sabo, ya'n aikin gidan na kai komo acikin falon, falon ta shigo tare da yin sallamah a sanyaye, Agnes ce ta amsa tare da faɗin ''Welcome Maa.'' ''Yeah, how are you doing.'' ''Splendid Maa.'' ''Ma shaa Allah, where is Mami?." ''Wallahi since morning she neva come out, I think say na her body hold her.'' ''Okay is Abbhu around?." ''Noo an ce ya tafi wani meeting Germany.'' ''Okay.'' daga haka ta nufi hanyar ɗakin da take tunanin cewa na Mamin ne. Ƙwanƙwasa ƙofar ta yi daga cikin ɗakin Mamin ta ce a shigo, jikinta a sanyaye ta shigo cikin ɗakin, Mamin na zaune cikin shigarta na alfarma amma kallo ɗaya za ka ma ta ka san da cewa, ta na jin jiki. ''Welcome daughter, wannan sammakon na ki hope all is well?." Durƙusawa ta yi har ƙasa tare da faɗin ''Mami Good morning.'' ''Morning my dear, ya kike, ya gida, ya kwanan kaɗaici?." ''Alhamdulillah, ya jikin Mami?." ''Alhamdulillah, ai Naji sauƙi.'' Ƙamshin turaren ɗakin Mamin wani kalar hawar ma ta kai yake, so take ta yi amai, amma a haka ta danne, ta cigaba da murmushin yak'e. Ganin yadda take a takure like kamar she's not comfortable, ya sanya Mamin sauke ajiyar zuciya tare da faɗin ''Daughter kin yi waya da shi kuwa tun da ya tafi?." Sauke kanta ta yi tare da fara wasa da hannunta ta ce ''Ban da numbersa ai Mami.'' ta ƙarashe maganar ta na murmushi. Dailing numbersa Mamin ta yi ta Telegram, ring biyu wayar ta yi aka ɗaga, in a calm voice Mami ta fara magana dan ko sallamarsa da gaisuwarsa ba ta bi ba ta ce ''Aliyu ko akuya ka ajiye a gida, za ka tambayi lafiyarta, balle ɗan Adam, haka ka ga mahaifinku na yi min?, mai sa duk cikin ya'n uwanka ka fi kowa baƙin hali ne?, a ina ka gado halin ka ni ban sani ba.'' Sai da ya sauke wani ajiyar zuciya sannan ya ce ''Mami I'm sorry aikin ne ya yi min yawa, and besides I watch all her moves no need a ce sai na kirata.'' ''Aliyu ubanka.'' Shiru ya yi ta cigaba da sauraron Mamin kafin daga bisani ya ce da Mamin a bata wayar. A hankali ta saka hannu ta amshi wayar, Mami na bata wayar ta fice daga ɗakin. Murya a sanyaye ta ce ''Ina wuni.'' ''Lafiya, uban mai kika je kika faɗawa Mamina?." Kamar za ta yi kuka ta ce ''Babu.'' ''Ya jikin ki?, wannan wajen ya daina ciwo?." Firfito da idanunta ta yi tare da faɗin ''Wani waje?." ''Don't pretend hajiyata, kin san abin da nake nufi, did you miss me?." Banbarankwai ta ji maganar na shi acikin kunnenta, take zuciyarta ta yi wani kalar mummunan faɗuwa...... ''Ya Ubangijina ka basu daman share." Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟 Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 🤧🥱😂😂💔 *THE REGRET* PENDING AMARYA CE ✍️ JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION The Noble Writers Team. **Pending Amarya 46** What goes around comes around ⏩ ⏮️ ⏩ Try to be a good father to your children not a cowed 🤍 🫧 🤧 Not edited 🌟💔🥹 **** A hankali ta saka hannu ta amshi wayar, Mami na bata wayar ta fice daga ɗakin. Murya a sanyaye ta ce ''Ina wuni.'' ''Lafiya, uban mai kika je kika faɗawa Mamina?." Kamar za ta yi kuka ta ce ''Babu.'' ''Ya jikin ki?, wannan wajen ya daina ciwo?." Firfito da idanunta ta yi tare da faɗin ''Wani waje?." ''Don't pretend hajiyata, kin san abin da nake nufi, did you miss me?." Banbarankwai ta ji maganar na shi acikin kunnenta, take zuciyarta ta yi wani kalar mummunan faɗuwa.... Shiru ta yi ma sa na y'an daƙiƙu tare da sauke wani kalar nannauyen ajiyar zuciya, cikin muryarsa mai Amo ya ce ''Soo you are missing me right?.'' shiru ta ƙara ma sa, abin ya mugun ƙona ma sa rai, dan ko ba komai ta nuna damuwa ga mahaifiyyarsa shi yasa ma yake son ya ɗan yi ma ta magana ba dan komai ba. Tsaki ya ja tare da ƙara faɗin ''A haka za ki ƙare ai, za ki bawa mai wayar, wayarta ko dai na ɓillo ta wayar nan na sauke miki maruka.'' Wani ajiyar zuciya ta ƙara saukewa, kamar wadda ke yin bacci, sallama Mamin ta yi tare da shigowa, ta ga Liyanar a yashe a ƙasa bacci ya kwasheta, wayar na hannunta kamar wani zai ƙwace ma ta shi. Ƙarasowa wajen Mamin ta yi ta na mai ɗingisa ƙafarta, tare da zare wayar a hannunta. Baƙin ciki kamar ya kashe Hydar saboda banzan da ta ma sa, ko kan Amin dake ma sa magana bai bi ba ya katse wayarsa. Kallon fuskarta Mamin ta yi na ya'n sakwanni tare da ɗaukan blanket ta lulluɓeta da shi, dake akan Persian carpet ɗin ɗakin take a kwance. Around 2 O clock ta tashi daga barcin da take a dalilin wayarta da yake aikin ringing, wani kalar sara ma ta kanta ya yi, ta na mai ɗaure fuska ta nufi kan cushion ɗin ɗakin Mamin da jakarta ke ajiye a wajen. Ɗaukar wayar ta yi tare da kallon sunan Lily da ke yawo akan fuskar wayar , wani kalar tsaki ta ja tare da ɗaukan wayar haɗe da faɗin ''Hello.'' ''Yes dear, ba za ki shigo school ba, yau lectures ɗin Sadauki ne wallahi, ya kamata ki shigo, ten marks zai ba da.'' Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce ''Okay on my way.'' daga haka ta katse wayar. Mami ce ta shigo cikin ɗakin hannunta riƙe da tray ɗin dake shaƙe da pepe soup, sai kuma wani ɗan bread daga gefen plate ɗin dake cikin tray ɗin. ''Daughter you're awake, zauna ki ci abinci, kin ji.'' Sai da ta yi ƙasa da kanta, dan har ga Allah ta ji kunyar ganin Mamin da abinci, kuma wai ita aka kawowa, ita ta rasa ta ya ma ɗan iskan baccin da ta rasa dalilin yin sa ya kwasheta, dan ba ta san lokacin da baccin ya sureta ba. ''Mami na ƙoshi, yanzu wai lectures za'a yi a school, idan na dawo daga school ɗin zan biyo kafin na wuce gida.'' ''Noo ta ya za ki tafi da yunwa, zauna ki ci kayanki kin ji.'' Murmushi kawai ta yi tare da faɗin ''Tom Mami na gode.'' Daga haka ta zauna ta fara cin pepe soup ɗin. Ba ta wani ci sosai ba ta wuce ta yiwa Mami sallama tare da wucewa school ɗin. ><><><><><><><> Zaune yake akan office chair ɗinsa, jikinsa sanye da wasu suits masu tsadar gaske sky blue color, gemunsa na gyare tsaff da kyau, tsintsiyar hannunsa na ɗaure da agogonsa na Rolex explorer ll wanda ya saba sanyawa fararen hannun na sa. Wa ta Chinese Lady ce ta shigo cikin office ɗin, kayan dake jikinta shi zai ba ka tabbacin cewa ita ɗin clearner ce. ''Good day Sir.'' Chinese ɗin ta faɗa da muryarta da yake na zallar Chinese. Gyad'a kansa kawai ya yi tare da fara duba wasu documents ɗin da ta kawo ma sa tun safiyar ranar. Cikin muryarsa da ke da ɗan ɓacin rai ya ce ''Kira min Manager's.'' Da ga haka ya cigaba da scrolling ɗin cikin apple computer ɗin dake gabansa, agogon hannunta ta danna tare da yi musu magana ta agogon, sannan ta fita daga cikin office ɗin Hydar ɗin. Turo ƙofar office ɗin aka yi, dukkaninsu suka shigo atare jikinsu sanye da baƙaƙen suits dake ɗauke da logo ɗin companyn. Zama suka yi a wajen da suka saba tattaunawa a office ɗin nasa, sannan kuma a hankali ya fara magana. ''Mai ya faru da 500 billion ɗin da suka fita last upper month?." Shiru suka yi na ya'n daƙiƙu sannan Manager ya fara cewa ''An siyi business jets ne saboda yiwa mutanen wasu ƙasashe delivery.'' ''Eh haka ne Sir.'' Assistant manager ya amsa da hakan, kallon wasu daƙiƙu ya yi musu tare da faɗin ''Ina jets ɗin suke?." Ajiyar zuciya Manager Yhu ya sauke haɗe da faɗin ''An yi banning compayn daga ƙere-ƙere.'' Wani kalar baƙin ciki ya haɗiya sannan a hankali ya ce ''10 million will be deducted daga cikin albashin ku, har sai kun gama biyan 500 billion ɗin, and no more allowances, daga yau na yanke wannan, next time kuyi abu ba tare da kun shawarce ni ba.'' daga haka ya tashi ya fice daga office ɗin, suma suka bi shi jikinsu babu ƙwari. Ko da ya fito direct basement ya nufa tare da ɗaukan motarsa ya bar compayn gaba ɗaya, ya nufi hanyar gidan nasa. <><><>><>><>>><><> A school ɗin ma da ƙyar ta samu ta iya yin lectures saboda baccin da take ji, around 4pm suka fito daga cikin school ɗin, duk da ba ta wani biyewa Lilyn ba ta dawo gidan Mamin. Sosai ta hana idanunta bacci ta taya ya'n aikin gidan aikin bayan sun sanar da ita Mamin na kwance tun bayan fitarta. Sai ƙarfe tare ta dawo gidan nata, shima kamar jiya haka ta tarar da pizza da ice cream akan dining table ɗin. Murmushi ta yi mai kyau dan na jiya ma mantawa ta yi ba ta tambayi Salimah wanda ya kawo ba, amma ta na gani ta san wannan aikin Abbinta ne. Yanka ɗaya kawai taci ta ji gaba ɗaya ya gimsheta, hakan ya sanya ta tashi a hankali ta nufi hanyar ɗakinta dan wani kalar bacci ne a idanunta. Ko wanka ba ta iya yi ba balle cire kayan jikinta, tare da abayar ta kwanta bacci mai daɗi ya sureta. Kwance yake yana kallon yadda take baccinta hankalinta kwance, he's missing her badly, ya na son ya ƙara kasancewa da ita, ko wannan kukan na ta da take, missing komai na ta yake. Wayarsa ce ta yi ringing hakan ya sa shi kallon wayar domin ganin wanda ke kiran na sa, ganin Amir ne ya sanya shi ɗaukan kansa ya na mai maida hankali wajen kallon laptop ɗinsa. Sai da Amir ɗin ya jera ma sa miss call kusan guda uku sannan ya ya bi kiran na sa. Ring biyu wayar ta yi Amir ɗin ya ɗauka. ''Assalamu alaikum Man." Amir ya faɗa daga kwancen da yake shima Sai da ya ɗan ja wa Amir ɗin aji kaɗan sannan ya ce ''Wassalamu alaykum Dude.'' Hydar ya faɗa ransa aɗan ɓace. ''Mai na maka, da idan na kira ka ba ka ɗagawa?, ko ka fara shaye - shaye ne?.'' Amir ya iddashe maganar tare sakin dariya kaɗan. Wani kalar haushi abin ya ƙara bawa Hydar dan ya tsani a masa laifi kuma a ɗinga ma sa dariya. Cikin Wani kalar murya ya ce ''You're mad Amir, how could you?, you spoiled all my plans on that girl Amir, ka ɓata komai Amir, wallahi idona idon ka a Nigeria ba zamu kwasa da daɗi ba.'' Wani dariyan Amir ya ƙara kwashewa da shi tare da faɗin ''Ka yi, ko ba ka yi ba?." Wani ɓakin cikin Hydar ya haɗiya tare da faɗin ''That's not your business." Da ga haka ya kashe wayar na sa....... ''Ya Ubangijina ka basu daman share." Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟 Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 🤧🥱😂😂💔 *THE REGRET* PENDING AMARYA CE ✍️ JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION The Noble Writers Team. **Pending Amarya 47** What goes around comes around ⏩ ⏮️ ⏩ Try to be a good father to your children not a cowed 🤍 🫧 🤧 Not edited 🌟💔🥹 **** Wani dariyan Amir ya ƙara kwashewa da shi tare da faɗin ''Ka yi, ko ba ka yi ba?." Wani ɓakin cikin Hydar ya haɗiya tare da faɗin ''That's not your business."

Chapter 20 of 31